Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuciyarsa ta kitsa masa ya amshe atm ɗin hanunta shiyyasa yabi bayanta. A falo ya sameta tana kumbure-kumbure Mom da su Salim zagaye da ita ana tanbayarta lafiya? Dan babu wanda yasan tama fita.
         “Wai bazakiyi magana bane Anam ana tambayarki kinyi shiru?”.
     Shigowarsa ta hanata bama Mom amsa, duk suka maida hankalinsu garesa yaran na gaishesa. Amsawa yay idonsa a kanta. Batare da yayi magana ba ya miƙa mata hanun fuska a tsuke. Ta fahimci mi yake nufi ta bashi dan haka ta zabura zata gudu.
     “Kika tashi a wajen nan sai kinyi kukan da baki taɓa yin irinsa ba bani”.
     Mom ta kalla idanunta cike da ƙwalla. Mom data kasa fahimtar inda suka dosa tace, “Babana miya faru ne?”.
    A taƙaice ya faɗama Mom abinda ya faru. Cikin mamaki Mom ɗin ta kalleta dan tasan dai Anam da tsoron dare, itada da dare yayi ko'a cikin gidan akace taje wani sashin aika saita nema ƴan rakiyya. “Anam”. Mom tai kiran sunanta. Ɗagowa tai ta dubeta sai kuma ta maida kanta ƙasa.
     “Ina zakije?”.
   A hankali tace, “Audiga zan siyo”.
Ɗan jim Mom ɗin tayi na nazari. Sai kuma ta girgiza kanta “Yanzu Anam har sai kin tafi siyen audiga basai ki tambayeni ba, idan ma babu ai za'a bada a sayo miki. Amma ko fitama bansan kinyi ba”.
    “Kiyi haƙuri Mom naje naga kina salla”.
    Girgiza kai kawai mom tayi, ta maida kallonta ga Shareff, “Ƙyale shashancin wannan Babana, nasan yanda zatai maka bayanin ne yay mata nauyi”.
     Janye idanunsa yay daga harar Anam ɗin, komai bai sake cewa ba ya fice. Binsa tai da kallo tana taɓe baki, sai dai shi baima san tanai ba.

                     ★★★★★★

   Kamar yanda Daddy ya faɗa game da matso da auren Shareff ɗin hakane ta kasance. Dan shirye-shirye aka cigaba da yi babu kama hannun yaro. Dama ankai komai gidan su Fadwa, sai gidansa daya rage a ƙarasama ayyuka wanda dama kamfaninsa keyin ginin shi kuma ya zana kayansa da kansa. Sosai yay busy a tsakanin, Anam ma wataran sai Ya Khaleel take bi ya sauketa ya kuma ɗakkota. Tana dai shan masifa idan ta makara. Ita dai yitake kamarma batasan hidimar da akeba a gidan, ko anko da aka fitar nata cewa tai bataso ita batason kayan zafin nan sai da Mom ta mata faɗa sosai randa zasuje wajen tela sannan ta yarda tabi su Aysha tanata kumbure-kumbure.

       ★Yau data kasance alhamis daya rage 1week bikin Shareff ƙarfe sha biyu ta baro wajen aiki sakamakon mura da take fama da shi. Dama cikin dauriya ta fita aikin har Khaleel na mata faɗa. Zazzaɓi daya rufeta ya hanata sukuni ga ciwon kai, Yaseer ne ya samu shugabansu yay complain aka bata damar zuwa gida. Karan farko data yarda ta shiga motarsa, dan tayi ƙoƙarin zame masa amma ya ɓata rai. Maimakon ma gida sai ya fara nufar asibiti da ita, taso masa magana ciwon da kanta keyi yasata hakura ta zuba masa ido kawai.
    Basu wani samun tangarɗar ganin doctor ɗin ba, kasancewar akwai sanayya tsakaninsa da Yaseer ɗin. Da ɗan mamaki Dr Jamal ke duban Anam ɗin, daga ƙarshe dai ya kasa daurewa ya jeho mata tambaya. “Anam baki ganeniba ko?.”
       Ɗagowa tai daga kwanciyar datai akan desk nasa ta ɗan dubesa, sai kuma ta maida kanta ta kwantar tana ɗan girgiza masa kai. Shiru yay yana kallonta na wasu daƙiƙu kafin ya cigaba da rubuta musu maganain ya bama Yaseer da tun tambayar da yayma Anam ɗin ya shiga tunani. “Babu wani damuwa Yaseer murane kawai kuje a sai waɗannan drugs ɗin tasha insha ALLAH fiver da headache ɗin zai sauka”.
   Godiya Yaseer yay masa da basa hannu sukai musabaha. Ya bisu da kallo lokacin da suke fita kansa a matuƙar ɗaure. Jiyay bazai iya haƙuriba ya ɗauka wayarsa domin lalubo abokinsa dan tabbatarwa. A kiran farko dai ba'a ɗaga ba, duk da yasan daliline ya hana hakan sai ya kasa daurewa ya sake kira....
      “Ai harna fara tunanin bazaka ɗaukaba nai tracing naka ninazo inda kake”.
      Daga can aka amsa da “Saikace wani ɓarawo”.
    Dariya Dr Jamal yay dakai hannu ya shafi gemunsa. “My Man ai baka da maraba da ɓarawon da ake nema ruwa a jallo yau a wajena. Dan nasan bazan iya haƙuriba”.
        “Ai dama koda yaushe kai ba haƙurinne da kai ba. Miya faru?”.
     “Muje a hakan bani da haƙurin. Wai dama mutuniyar ta shigo Nigeria amma ko labari?”.
            “Malam jeka kai tsaye kan maganarka waye mituniyar? Dan na kula kai baka gajiya da kwashe-kwashe”.
    “Oh ALLAH shaidar da kai min kenan? To Anam nake nufi. Dan yanzu suka bar wajena ita da wani yaro Yaseer ya kawota a dubata”.
          Ɗiff yayi kamar wanda ruwa ya cinye har Dr Jamal na tunanin kota yankene, wayar ya cire a kunnensa ya kalla, ganin yana online ɗin dai ya shiga faɗin “Hello! hello! Bakajina ne?”.
     Ɗin! Ɗinn! kiran ya yanke, bai wani kawo komai a ransa ba ya ajiye wayar da tabbacin bayaji ɗinne, shawarar daya yanke a zuciyarsa na anjima zaije har gida kawai ya sashi ƙin sake kira.

           ★★
  
     “To Alhmdllhi, indai banyi kuskure ba nan shine gidan”. Yaseer ya faɗa yana duban Anam da tunda suka baro asibiti ta kwantar da kanta jikin sit ta lumshe ido. Shiru bata motsa ba, yaɗan leƙa fuskarta yana murmushi da ɗan bubbuga gefen kujerar. Idanun ta buɗe a hankali ta kallesa. Kamar yanda yake mata murmushi itama saita ɗan sakar masa mai kama da yaƙe....
      “Nan ne ko?”.
Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa da narke mata idanusa. Janye nata tai daga garesa a ɗan daburce ta kalli gate ɗin. “Nan ne, na gode sosai ALLAH ya bada ladan zuminci”. Murmushi ya mata kawai ya buɗe ya fita. Side ɗinta ya zagayo itama ya buɗe mata. “Thanks”. Ta faɗa a hankali da ziro ƙafarta ƙasa zata fito idonta ya sauka akan Shareff da shima fitowarsa kenan daga gida hanunsa riƙe da key ɗin motarsa dake anan waje fake, ita sam bama ta lura da motar ba sai yanzu daya danna key tai ƙara. Ganin yanda ya kafeta da idanunsa ya sata yin ƙasa da nata ta ƙarasa fitowa gabanta na faɗuwa. Ɗan baya tai kamar zata faɗi saboda jiri Yaseer yay azamar kai hannu zai riƙota, dafe motar tai da sauri ta tsaya da ƙafafunta. “Ayya sorry Friend”. Yaseer ya faɗa a hankali yana janye hanunsa da bai kai ga taɓata ba.
     Ɗan satar kallon inda Shareff yake tai, yanzun kam zaune yake cikin motar sai dai ƙafafunsa a waje yana danna waya tamkar bai san da wanzuwarsu a wajen ba.....
     “Wancan ba Yaya bane?”.
Yaseer ya katseta yana fuskantar inda Shareff yake. Kanta kawai ta jinjina masa. “A to bara naje mu gaisa ko?”. Nanma batace komai ba, ganin ya nufi inda Shareff ɗin yake ita kuma gashi kwanciya kawai take buƙata, ga hararar daya mata sai kawai tai shigewarta gida...
         Shiru gidan babu gittawar kowa. Ta nufi sashen Mom da tunanin ko barci suke. Nan ɗinma shiru har ɗakin Mom ta leƙa bata samu kowaba, kitchen ta nufa inda take ɗan jin motsi. Iyami kawai ce tana ƙoƙarin ɗaura girkin rana. Gaisawa sukai kafin ta tambayi su Mom da hausarta da Iyami bawani fahimta take da ƙyau ba. Iyami ta bata amsa da cewar dukansu sun fita harsu Gwaggo amma batasan ina suka tafi ba. Fitowa tai ta shige ɗaki ta kwanta, ko mintuna biyu bata cika ba aka buɗe ƙofar, a tunaninta Iyami ce, sai dai kuma ƙamshin turaren da taji ya sata buɗe idanunta da sauri...
       Ido suka haɗa tai saurin janye nata ta maida ta rufe.
   “Tashi”.
  Sake buɗe idanun tai kamar zatai kuka, sai dai yanda yay kicin-kicin da fuska yasata kasa musa masa ta tashi zaunen. Hanyar ƙofa ya nuna mata. Saita waro idanunta da suka canja launi na mura ga ƙwalla a cikinsu.
    “Banda lafiya fa Yaya. Ina zanje?”.
   Ganin ya nufota ta miƙe da sauri hawaye na sakko mata saman kumatu. A falo ta kusa faɗuwa saboda jirin dake ɗibarta, a bazata taji tattausan hanunsa cikin nata. Gaba ɗayansu sai da tsigar jikinsu ta tashi, sai dai babu wanda yay yunƙurin cirewa musamman ita dake buƙatar taimako dama. A haka suka fito har waje, ya taimaka mata da kansa ta shiga mota sannan ya zagaya nasa mazaunin, tana sonyin magana tana jin shakka dan haka tai shiru, saima ta kwanta abinta jikin sit ta lumshe idanu..
       Wani clinic ya kaita dan a dubata. Data sanar masa sunfaje asibiti wata muguwar harara daya wulla mata bata sake magana ba. Doctor ya rubuta musu magani fuskarsa ɗauke da murmushi yake kallonsu da faɗin, “To amarya ALLAH ya ƙara afuwa kafin biki”.
     Idanu taɗan waro da kallon Shareff da shima kallonta yake, zatai magana ya harareta yana miƙama doctor hannu. “Thanks you doctor”.
     “No babu damuwa ango ALLAH ya ƙara lafiya sai ranar ɗaurin aure kuma”.
      Shareff ya saki murmushi yana jinjina masa kai. Yanzu kam bama ta jira sun jera ba tai gaba da sauri, koda ya fito harta buɗe mota ta shiga abinta. Sai da suka baro anguwar gaba ɗaya ya tsaya a wani babban pharmacy ya sayi magungunan da aka rubuta, ya kuma shiga gidan abincin dake gefen pharmacy ɗin yay mata takeaway. Duk batasan hidimar da yake ba saboda tunda suka baro asibitin barci ya ɗauketa, dan haka batasan inda suka dosa ba har sai da suka iso. Gefen kujerar yaɗan bubbuga, a hankali ta buɗe idanunta, ganin har ya fita ta yunƙura ta tashi, fitowa tai tana dube-duben inda suke “Yaya MM ina ne kuma nan?”. Bai tanka mataba, ya rufe inda ta fita yay gaba abinsa. Ƙara bin gidan tai da kallo, dagani dai sabone dan duk ma ga botikan fenti nan a tsakar gidan da kayan aiki, gabanta ya shiga faɗuwa, cikin zuciyarta take tambayar kanta (ina kuma ya kawota nan?).....
       “Idan kika bari na dawo nan ALLAH sai kinyi kuka”. 
    Da ƙyar ta iya ɗaga ƙafa ta nufi inda yake, koda ya buɗe ƙofar da key matsa mata yay ta fara shiga, ƙamshin sabon fenti dana sabbin furnitures ya daki hancinta. Sosai falon yay mata matuƙar ƙyau, danma ciwon kai ya hanata damar kallon komai da ƙyau. Ganin tana neman kaiwa kwance ya dakatar da ita. “No tashi kici abinci kisha magani first”.
       “Yaya banajin yunwa kadai ban maganin kawai”.
     “Dole kici abinci, kin taɓa ganin ansha magani ba'aci abinci ba”.
Yanda yay maganar babu wasa yasata yin shiru. Ya buɗe mata abincin tare da tura mata gabanta, “Kafin na fito ki tabbatar kinci”. Da kallo kawai ta bisa harya shige ƙofar daya buɗe..... Kusan mintuna goma sai gashi ya fito, ganin ya canja kaya yasa ta kasa haƙuri. “Yaya Shareff ina ne nan?”.
      Batare daya kalleta ba yakai zaune cikin kujera da faɗin, “Gidan ƴan shan jini”. Shiru tai, dan tasan baƙar magana ya mata. Ɗagowa yay yaɗan kalli abincin, ganin taci sai baice komaiba yaja ledan magungunan. Da kansa ya ɓalla ya bata, duk ta amsa tasha dan sam bata tsoron allura bare ƙin magani. Ganin zata kwanta a kujerar ya sashi faɗin, “Tashi kije ciki ki kwanta”. Kallonsa tai kamar zatai magana sai kuma ta haɗiye abunta ganin yanda kicin-kicin da fuska. Ya bita da kallo ta ƙasan ido harta shige, ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe ido ya buɗe yana furzar da ɗan huci. Sai kuma ya miƙe ya fita.
      Gidan ya shiga zagayawa, dan jiya masu fenti suka ƙarasa na katanga. Bai kuma samu shigowaba sai yanzu. Komai yayi masa yanda yake buƙata, shi kansa ya yaba da gidan duk da shine ya zana abinsa companynsa kuma ya fidda kayan aikin ginashi. Yanzu amarya kawai gida yake buƙata nanda kwanaki bakwai insha ALLAH. Motarsa ya nufa ya ɗauka lap-top ya koma ciki. Haka kawai yake jin nishaɗin zama a cikin gidan yau, saɓanin ƴan kwanakin nan da duk yake jin ransa a dagule, dan kayan sashen nasa ma sai da Mommy ta masa jan ido ya bada damar shirya masa su dan ita da kanta tai order ɗin komai tamkar itace mai aurar da macen ba namiji ba. Komai saida ta haɗa masa. Tunda kuma aka shirya kayan baizo ya zauna kamar haka ba......
    Ring da wayarsa tai ya sashi katse aikin da yake famanyi a laptop ɗin ya ɗaga. A tausashe yace, “Mommy barka da rana”. Daga can Mommy ta amsa masa da “Barka dai son kana ina ne?”. Ɗan jimm yayi kafin yace “Mommy kina son ganina ne?”.
      “Eh to kusan haka, amma idan zaka iya aika wani gidanka ya kai mana keys ma basai kazo ba. Dan gamu a hanya zamuje dasu gwaggo gidan, sannan Halima tai kirana ma danginmu na wajen baban Fadwa zasuzo da masu Company da zasu shirya kayanta su auna komai, shiyyasa muka yanke shawarar muzo muma ɗin kawai dan babu daɗi dangin uba kawai ko?”.
        Tun fara maganar tata zuciyarsa ke faman bugu da sauri, ya ture laptop ɗin cinyar tasa gefe, cikin dauriya da danne halin daya shiga yace, “Okay Mommy! kuna inane yanzu haka?”.
       “Ai gamu ma mun shigo street ɗin gidan naka kamar dai in ban mantaba”.
     Goshinsa ya dafe yana ambaton “Ya ALLAH a hankali”.
         “Mi kace?”.
  “No Mommy, canai ALLAH ya kawoku lafiya ai inama gidan nima na shigo ganin aiki daga nan na ɗan huta”.
     “Kaji ja'iri, bama ka bari iyayen naka su kaika ganɗoki muje biki”.
    Ƴar dariyar yaƙe kawai ya mata da faɗin, “Sai kun iso”.

        Da sassarfa ya nufi hanyar bedroom ɗinsa. Ya duba Anam dake barci hankalinta kwance harda naɗewa cikin lallausan duvet nashi dako shi bai taɓa lulluɓa da shi ba. Nufarta yay yakai hannu kamar zai tadata sai kuma ya fasa, ya ɗan furzar da huci tare da dafe goshinsa yana ambaton sunan ALLAH. Ya tabbatar su Mommy suka ganta ya shiga uku, dan baima san kalar ƙurar da zata iya tashi a family ɗin MD Shareff ba yau. Jin horn ya sashi sake ambaton “Ya ALLAH”. Tare da fita a ɗakin domin buɗe musu tunda babu maigadi har yanzu sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu yake saran Fharhan zai kawo shi.....

         Tunda ya buɗe musu gate bakin Mommy da Gwaggo ya sake washewa. Suma dai su Mom fuskarsu da murmushin jin daɗin ganin yanda ɗansu ya gina wannan gida dako maƙiyi ya gani zai yaba ko'a zuciyane.
      “Kai-kai! Anya kuwa Alhaji ƙarami bazan dawo nan ba irin wannan gida haka?”.
    Gwaggo ta faɗa tana riƙe haɓa dabin ko'ina da kallo. Murmushi yay mata da shafa kansa. “Indai bazaki dinga damuna da kwakwazonki ba sai na dawo dake”. Dariya su Mom sukasa, yayinda Gwaggo tai masa daƙuwa. Nanma murmushi yayi kawai. Da kansa yay musu jagora suka shiga ko'ina suna mai yabawa da masa addu'a, bakin Gwaggo da baya iya yin shiru tace, “Toni abinda ban ganeba anan, Alhaji ƙarami yanaga sashe biyu, gidan kamar na zaman mace fiye da ɗaya! Kar dai kacemin kaima halin Kakanka da ubanka zakai tara mata?”.
      Ganin duk su Mom sun juyo suna kallonsa, har fuskar Mommy ta sauya ya sashi ɗan hararar Gwaggo ta ƙasan ido. “Kai tsohuwarnan kedai bakinki bai iya shiru, kawai dan mutum yayi wadataccen waje a gidansa sai yazam na aure? Nayine saboda ke in kinzo kwaɗayin jar miya”.
        Dariya su Aunty Amarya suka sanya. Mommy ma ta ɗan saki fuska tana murmushi dan tun farkon fara ginin gidan da tazo ta gani ta masa irin wannan maganar ganin sashe biyu da nasa na uku, amma sai yace yayine kawai saboda baƙi. Haka kawai zuciyarta taƙi aminta da shi taita masa bin.....
       “To shikenan muje ka kaimu naka sashen muga namai gida”.
   Gwaggo ta katse mata tunani. Gabansane ya faɗi, zaiyi magana Gwaggo ta nufi ƙofar sashen da basu shiganba wanda tabbacin nasan ne, itama Mommy saita take mata baya. Hakan yasa dole su Mom ma binsu. Da ƙarfi ya rumtse hanunsa da cije lip ɗinsa. Ganin har Gwaggo ta shige yay saurin bin bayansu shima dan ya tabbata target ɗinta na biyu shine bedroom ɗinsa. Kamar yanda yay hasashen kuwa hakane. Dan ko falo bama tagama nutsuwa ta ganiba ta nufi ƙofar bedroom acewarta da nan zata fara a sashen. Shigowarsa tayi dai-dai da ɗaura hanunta a handle ɗin ƙofar.............✍

    *_🙆🏻Yau munga idi wagga tsohuwa babu man kai zata ɓaro aiki. Dangin Anam kuna ruwa, maganin masu bin mazan mutane kenan🚶🏻😂🤭_*
     

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
[10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*




*_12_*


..........A karon farko ta ɗago ta kallesa da mamaki ganin inda yay parking. Magana take so tayi, sai dai ta kasa. Shi kuma yaƙi cemata komai, sai ma wayarsa daya ɗauka yay ƴan danne-danne yakai kunensa. “Fito”. Kawai ya faɗa ya yanke wayar. Ba'a rufe minti uku ba wata budurwa mai tsananin iyayi ta fito daga shagon saloon ɗin tana tafiya kamar tarwaɗa. Haka kawai abin nata ya bama Anam haushi, taja siririn tsaki da taɓe fuska ta janye idonta. Duk da tayine a hankali sai da yaji, sai dai bai nuna yajinba balle ya tanka, sai ma faman daƙilar waya yake, amma ya buɗe murfin kafarsa ɗaya a waje take.
      “Assalamu alaikum Yah Musty barka da zuwa”. Budurwar ta faɗa murya a lanƙwashe lokacin da take isowa wajen. Kansa kawai ya jinjina mata yana janye kunne ɗaya na earpiece dake a kunnensa. Kamarma bata damu da abinda yay matan ba. Murya ta ƙara tausasawa cike da iyayi tace, “To Bismillah muje ko”.
       Nan ɗinma bai tankaba, sai da yaja wasu sakanni ma sannan yay yunƙurin fita a motar.
    Baƙin ciki, haushi da takaicin ballagazanci na wasu mata ya tokare maƙoshin Anam. Lokaci ɗaya taji tama tsani budurwar.
         “Sai an fito da ke ne?”.
Ya faɗa cike da gatse idonsa akan Anam. Jitai kamar karta fita ɗin, amma sai yaci darajar Yaya da yake gareta tabi umarninsa. Yanda budurwar batai mata magana ba itama bata nuna tama san da zamanta a wajen ba. Gaba sukai tana binsu a baya, budurwar sai ƙoƙarin dai-daita tafiyarta take da shi tamkar dole, ga baki ta saki sai surutu kai kace hanyar kasuwar wanbai aka buɗe da safe. Sosai wajen Saloon ɗin ya haɗu dan yaɗan birge Anam kaɗan, sai dai bata nuna a fuskaba saima kicin-kicin data sakeyi da fuska duk da gaisuwa da ma'aikatan wajen ke musu na girmamawa daya bata mamaki matuƙa. Wajen zama aka basu, harda ajiye musu abinsha kafin budurwar da taji ma'aikatan sun kira da aunty Deena ta dubesa cike da yauƙi da shauƙi.
          “Sir za'a mata kitso ne?”.
    Bai jita ba, saboda earpiece dake manne a kunnensa. Hannu takai ta cire kunne ɗaya, ya ɗago ya dubeta yana sake tsuke fuska. “Am sorry, nayi magana ne bakaji ba, nace za'a mata kitsone?”. Idonsa ya ɗauke daga gareta ya maida ga Anam datai kicin-kicin da fuska fiye da yanda suka shigo dan ta fahimci ita ya kawo kenan. “Komai ma daya dace kumata”. Ya faɗa a taƙaice da maida earpiece ɗinsa.
        “Ni wlhy bance inaso ba. Kuma kaina a wanke yake, hakama......” Hararta yay yana mai zare kunne ɗaya na earpiece ɗin, tai saurin sake haɗiye maganar tana matso hawaye. Ɗauke idonsa yay kamar baima ganta ba. Tanaji tana gani aka kwance mata kalbar kanta aka saka mata relaxer aka wanke fes. Bayan an rage ruwan da towel akai steaming ɗinsa. Wadda take mata gyaran tambayarta tai tana son kitso ne? Amma tai mata banza. Ganin haka ta juya ga Shareff dake zaune komai anayi gaban idonsa.
      “Sir za'a mata kitson ne ko a barta?”.
        “Barta kawai a mata lalli”.
Yay maganar batare da ya kalleta ba yana maida earpiece ɗin kunensa.
       Ana fara wanke mata ƙafa da gyaran farcen hanunta ya miƙe ya fita, Anam ta bisa da harara ƙasa-ƙasa tana tura baki. Cikin ƙunƙunai tace, “Gwarama da zakai aure mu huta da baƙin halinka”.
    Murmushi mai mata wankin ƙafa tai saboda jin abinda tace. Lokacin da aka fara zana mata lalle harda ɗaukar video, dan tana son lalli sosai kitsone dai kam saida dambe da Mamie tsaye kanta, dan ko Mamie ce tace zata mata ba yarda take ba da arziƙi. Abie kam lallaɓata yake ko yace a barta sai wani lokaci tunda bata so.
       Sosai ta fito ras tai ƙyau tamkar wata sabuwar amarya. Sai faman kallon kanta take a manyan mirrors na wajen tana murmushi da ɗaukar hoto kamar ba'itace ta gama rikiciba yanzun. Sai da tai mai isarta sannan ta fito waje kamar yanda Deena ta tabbatar mata Yaya Shareff na nan na jiranta a waje. “Okay”. kawai tace mata tai ficewarta. Deena da yaranta suka bita da kallo baki taɓe. Fuska ta haɗe tamau tana cika baki da iska lokacin da take fitowa, ta buɗe motar ta shiga tana wani kauda kai taƙi kallon inda yake.
        A jiyar zuciya ya sauke a hankali yana ɗagowa daga kwanciyar da yay jikin kujerar, murmushin daya tsaya iya laɓɓansa ya ɗan saki ganin yanda taketa faman kauda kai gefe wai ita a dole haushi take da shi. Hanunsa ya kai ya zame veil ɗin, tai saurin riƙewa tana tura baki. Kallon daya wulla mata ya sata sakin masa babu shiri, sai da ya gama ƙarema gashin kallo cikin ɗan lumshe ido da buɗewa ya maida mata ya rufe. Sosai gashin nata yasha gyara sai ƙamshi mai daɗi da ƙyalli yake.

      Koda suka iso a gate yay parking, tana fita yaja motar yay gaba abinsa. Da harara ta raka motar, sai kuma ta kalli hanunta da ƙafa da sukasha lalli tai murmushi. Gidansu tai shigewarta. Dan cikin gida tun daga waje kana iya jiyo hayaniyar daya sake ɗauka alamar baƙi sun ƙaru kenan. Gidan nasu ma cike ta sameshi da baƙin da suka iso bayan fitarta. Sai su Aysha dake shirin komawa gidansu amarya bayan magrib Arabian night. Tambayarta wanda yay mata ƙunshi suka shigayi kowa na yaba ƙyan da yayi. A takaice tace musu Yayane ya kaita wani waje kawai. Koda suka buƙaci jin wane Yaya a ciki bata amsa musu ba tama shige toilet dan son watsa ruwa kasancewar gab ake da kiran sallar magrib saboda sun jima a wajen ƙunshin nan ba laifi, gashi ko sallar la'asar batayi ba.    
      Ana idar da sallar magrib ƴammatan gidan suka sake ficewa wajen event na arabian da aka shirya amma banda Anam yanzu ma. Dan kwanciyarta taima tana kallo a lap-top hankali kwance kamar bata san bikin da akeyi ba. Har magana Amrah tai mata amma tace karta dameta. Yanda tai maganar cikin masifa yasa kowa bai sake magana ba sukai shirinsu suka fice.

          ★★★★★

Washe gari kam gida ya sake cika danƙam da ƴan uwa da abokan arziƙi na nesa dana kusa. Abokan Yah Shareff na Nigeria da wajenta duk wanda ya iso anan ake saukarsa gidansu Anam a

2 Comments On BABU SO
avatar
aisha-6-7-7

5 months ago

Reply

Inason littafinnan sosai

avatar
aisha-6-7-7

5 months ago

Reply

Inason littafinnan sosai

Please Login or Register in order to submit comment