Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata saboda tsaki data dinga zubama su Husna kamar wata dangin tsaka, sai dai kuma fahimtar iya gaskiyarta ne yasa Ikram zuwa ta faɗowa Mom ɗin. Ganin akwatuna har set uku a falon Mom masu shegen ƙyau da tarin kayan sa rana ya sata tambayar Ya Khaleel first born ɗin Mom. Shima dai saurayine zangarere da shi dan yana shekara ta 26 a duniya. Khaleel ƙyaƙyƙyawa ne shima kuma nutsatstse. Sai dai akwai tsare gida da rashin son raini harma yafi Shareff zafi, dan shi Shareff inhar baka shiga gonarsa ba babu ruwansa da kai, sannan yana da sakewa da jama'a fiye da Khaleel. Shine na uku a haihuwa a gidan. Dan sanda Mom ta auri Abba haihuwar Mommy biyu ne. Daga Shareff sai Maheer da take goyo. Duk da Shareff ya bama Khaleel shekaru sosai hakan bai hana ƙaunar juna shiga tsakaninsu ba, dan tunda ya dawo daga Indonesia bashi da wani aboki a gidan kamar Khaleel. Da taimakonsa ya san wajaje da yawa daya manta, sannan tun a baya idan yazo hutu dama shine abokin yawonsa saboda nutsuwar yaron na birgesa. Yafi Maheer hankali sosai da sanin ciwon kansa, dan yanada himma da ƙwazon nema duk da ko maganar aure bayayi ma.
       Duk ɗaurewar Khaleel suna ɗan shiri da Anam, sai dai itama ba wani sake mata yake ba dan miskilanci a jininsa yake. Kamar bazai tanka mataba yanata aikin danna wayarsa sai kuma ya kalleta. “Kayan auren Yaya Shareff ne”.
      “Ya mi?! Dama aure zaiyi!?”.
A yanda tai maganar ya tilastashi sake dubanta da ƙyau, haka kawai yaji dariya ta taho masa. Amma sai ya gimtse.
       “Kinada matsala da auren nasa ne Granny”. (Dan haka yake kiranta mafi yawan lokaci).
     “Kuji Ya Khalel ɗin nan da wani magana. Ni ina ruwana da wani aurensa da har zai zamar min wani damuwa. Ai sai dai nai murna zai tafi can ya barmu mu huta matan ta kwashi baƙin hal......”
     Jin ta gagara ƙarasawa yasa Khaleel fashewa da dariya, dan dama dai tun ɗazun ya lura da Shareff daya fito daga bedroom ɗin Mom. Ita kuma sam ALLAH baisa ta lura ba sai yanzun da yaƙe ƙoƙarin baro corridor ɗin baki ɗaya dan dama kamar ya ɗan tsayane yana sauraren su, amma a zahiri waya yake dannawa. Duk da ba inda take yayo ba da gudu ta afka ɗakin barcin su harda murza key.
     Shiko dama daba inda take yayo ba harara kawai yawatsama Khaleel da faɗin, “Dalla tashi muje ka zauna kana abu kamar wani yaro”.
         Har yanzu dai dariya ƙunshe a bakin Khaleel ya miƙe. Idonsa na duban ƙofar da Anam ta shige. Suna ƙoƙarin fitowa yace, “ALLAH my best yariyar nan sam bata da wayo har yanzu. A hakan wai kuma ta kammala karatu. Bayan rashin wayon ƴan fari a jikinta harda taɓarama na ganin ita kaɗai ce a gaban su Mamie. Jiya fa harda kuka ta dinga yima su Mon wai zafi saida aka kawo fan aka kunna mata”.
      “Mom ɗince ta biye mata mtsoww ”.
Ya faɗa cikin halin ko in kula. Shi dai Khaleel yace, “Gara dai da aka kunna mata dan bata saba da zafin nan bane namu. Su da suke fama da dusan ƙanƙara ma wasu lokutan dan tsabar sanyi. Kaga ko tazo nan dole ta shiga wani yanayi dan kano ogace ta zafi..”
      Komai bai ƙara cewaba yay gaba Khaleel ya bisa.

     Kasancewar da Mom da Aunty Amarya sai wata ƙanwar Momy da yayarta za'aje yasa Anam maƙalema Mom sai taje. Mom bata hanata ba, dan ita tanada sauƙin kai sosai shiyyasa suke zaune lafiya da Mommy tsahon shekaru, duk da dai itama Mommy ɗin bawai tanada faɗa bane ko rikici, kawai dai ta tsani Mamie ne saboda tun farko akan hakan Gwaggo ta ginata, ta riga ta nuna mata shi Abie ɗan uba ne a cikin su Daddy duk da kuwa ba itace ta haifesu ba. Sai kuma ta kasance mace mai son komai ace itace sama da kowa, sannan a wajenta ake neman komai, a ganinta bazai yiyu ita matar farko a gidan ba, sannan mijinta shine babba ace wata a matan ta fita. Fin da Mamie ta mata kuma ya ƙara ƙiyayyar, itako Mom Abbah bai kai Daddy ba gaskiya, sai dai na waje bazai taɓa fahimtaba kasancewar ana ganinsu kansu a haɗe a koda yaushe kuma suna gida ɗaya ne.
      Kasancewar matar da Shareff ɗin zai aura ɗiyace ga gwaggo halima (ƙanwar daddy), kuma mahaifinta yaya a wajen mommy gawurtaccen ɗan siyasa mai muƙamin babba a jihar ta kano gidane katafare suka iso. Komai yaji na more rayuwa. Fadwa shine sunanta, ɗiya ga Alhaji Sadiq Dakata. Mahaifinta kamar Yayane ga Mommy. Dan da mahaifiyarsa, da Mahaifiyar Mommy da gwaggo duk uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Zumincine mai ƙarfi a tsakaninsu, dan haka ita da Gwaggo suka zaɓama Shareff Fadwa matsayin mata tunkan ya dawo gida Nigeria. Sunyi hakane a cewarsu dan kar Abie yay tunanin basa auren Anam. Da farko dai Shareff bai maida hankali ba duk da baice baya sonta ba. Sai da Mommy ta masa jan ido sannan ya ɗan ke kula Fadwa ɗin. Fadwa ƙyaƙyƙyawar yarinya ce gwargwado kuma ƴar gata, sannan kuma sele (celebritie) a social media, musamman tictok da istagram harma da twitter. Idan zan zauna fayyace muku wacece Fadwa zamu cinye labarinne a kanta. Kuje zuwa dai lokaci zai nuna muku ainahin Fadwa Sadiq Dakata.
     Sun sami tarba ta girma da girmamawa. Inda babu kunya Fadwa ta fito tare da tarin ƙawayenta da suka cika gidan kallon kaya tun a gaban su Mom. Yayinda su Abie ke can suna tattaunawa da su Alhaji Sadiq domin tsaida rana. Dama dai shine yace baya son aita jeka ka dawo, su haɗo komai rana ɗaya su kawo har sadaki sai kawai a tsaida ranar ɗaurin aure.
        Su dai su Mom wannan abu ya sakasu jin lallai akwai gyara a lamarin wannan amarya, duk da kuwa ƴar gida ce dan sun san wasu a cikin halayenta saboda kowa yasan ƴaƴan gwaggo Halima basu da ƙwaɓa. har cikin rai suna jin tausayin Shareff ɗin kasancewarsa bai wani cika zafi da yawan magana ba a mafi yawan lokuta. Amma sauran ƴan uwan Mommy da yake ƴan uwansune suma sai basuji komaiba a lamari, dan kuwa dai basu nuna a fuska ba sai dai in sun barma ransune suna nuna normal ne a zahiri.
       Fadwa tasan labarin Anam a wajen Mommy da Gwaggo da mahaifiyarta. Sai dai bata santa a zahiri ba sosai saboda gwaggo halima ba shiga duk abinda ya shafi su Abie take ba, tasha jin sunzo ƙasar tabi duk hanyar datai mata ta toshe haɗuwarsu sai idan wata fitinar suka shirya da su gwaggo shima ita kaɗai take zuwa babu ƴaƴanta. Hakan yasa yaranta basu wani san Abie ɗin bama balle ƴarsa, shima kuma bawani gama sanin ƴaƴanta yay ba tunda bata bari su raɓesa. Hakan yasa Fadwa bata nuna damuwarta da ganin Anam tare da su Mom ba. Amma dai yanda Anam ɗin ta zama miskila a wajen tana kallon komai ya ɗan ja hankalin su Fadwa da ƙawayenta gareta. Har takai babu kunya Fadwa na tambayar su Mom ina suka samo Anam ɗin?. Murmushi kawai Mom tai da faɗin “Itama ƙanwarki ce”. Daga haka ta tsuke bakinta duk da tambayar bin ƙoƙwanto da ƙawayen Fadwa ke cigaba da jefamasu Mom ɗin. Aunty Amarya dama bata tanka ba dan ita bata da farin jini a garesu kasancewarta kishiyar Mommy.
     Har dai suka baro gidan Fadwa da ƙawayenta basu san matsayin Anam ba. Ita kuma ta miskile ko ruwa bata sha ba a gidan har suka taho. Gwaggo halima ma duk da taga kamanin Abie a jikin ta kuma tasan sun zo bata tanka ba bata nuna komaiba.
Anam ma sai da suka ɗakko hanyar gida ta fara yima su Mom mitar Fadwa da ƙawayenta masu shegen rawar kan tsiya da nuna wayewa. Murmushi kawai Mom da Aunty sukeyi dan mota ɗaya suke su uku, ƴan uwan Mom ma na nasu su biyu.
      Bayan sun iso gida kowa yaji ainahin watan bikin a bakin su Abie. Nan da watanni biyu. Sauran yaran gidan nata murna duk da wannan ba shine karon farko da za'ai biki ba. Anyi bikin Rahma dake bima Khaleel, da Binta ƙanwar su Shareff dake bima Maheer. Yanzu Aysha ce a layi kuma sa'ar Anam ce dan watanni ta bama Anam ɗin kawai, itace ɗiyar Mommy ta biyar daga ita sai autoci su twins. Ga Anam kam babu dalili ta wani tsume sai kallonsu take da taɓe baki, har bayan magrib babu fara'a a tare da ita. Rashin walwalar tata yasa koda Aysha ta tambayeta. Sai tace ba komai.
     Sai bayan magrib suna hira duk kusan yaran gidan a falon aunty Amarya, gaba ɗaya hirar tasu ta ta'allaƙa ne akan shirin biki. Sai dai Anam taƙi tako tanka sai faman game take bugawa a waya. Sai dai kuma kunenta duk yana a garesu ne. Jin sun cigaba da damunta ta tashi zaune tana wani taɓe baki da harar Nusaiba mai gwada rehearsal na rawan da zasuyi wai a wajen dinner....
     “Kun wani dage sai tsara events kuke bayan amaryar ma ko aji bata da shi mtsoww!!”.
   Lokaci ɗaya falon yay tsit duk suka juyo suna kallonta. Hussaina ta ɗan waro ido da ƴar tsiwa tace, “Aiko dai aunty Fadwa nada aji gata ƙyaƙyƙyawa ƴar babban gida bama son jealous”.
       “Jealous!!. K! Hussaina dani kikeyi wai! kowa ma? Ni Juwairiyya ce zanyi jealous ɗin wancan farin ƙasan mai kama da ƴar tallan kasuwa. Baki da hankali”.
      A yanda take maganar a fusace yasa Hussaina tsorata, dan in tsiwa takeji Anam kakartace a iyawa. Amma shirun nata badan tsoron bane kawai, harda wanda idonta ya hango ya shigo falon ne yasa tai shiru. Anam kam da sam bataji ko sallamarsa ba sai faman faɗa take da sule Fadwa iya gaskiyarta. Tsaki ta doka da fisgar tab ɗinta dake hanun Hashim da nufin barin wajen, karaf idonta ya sauka a kansa. Yana tsaye tamkar an dasashi ya kafeta da manyan idanunsa masu razana wanda ya shiga gonarsa. Sosai gabanta ya faɗi, amma da yake ƴar gagiyar bata yarda aga gazawarta a fuska ba sai ta ɗaukesu cike da wani irin sallo da kaɗasu kamar mai harara ta nufi hanyar kitchen domin bi ta baya, dan tana shakkar bi ta gabansa tunda a ƙofar falo yake tsaye. Duk da bai nuna yama ji abinda tace ɗin ba hakan bai hana su Aysha ƙara nutsuwa ba.

         Washe gari Abie yay shirin komawa. Anam ta zauna taita kuka itafa sai dai su koma tare. Yasan halinta akan kafiya, baiyi da wasa ba yay mata fata-fata, sai su Abba ne da aunty Amarya keta lallashinta da Ya Khalel. Shareff kam duk da yana wajen ko tari baiyiba. Yamaƙi nuna yasan abinda akeyi. Sai da zai buɗema Abie baya zai shiga ne ya harareta. Ƙasa tai da kanta ta sake fashewa da kuka.
        Daddy da yaga hararar Shareff na ƙoƙarin shiga mazaunin driver ya dakatar da shi. “Kaga ku wuce da Mamana tai rakkiyar itama”. Kansa ya duƙar ƙasa fuskarsa na sake tsukewa da satar kallon Mommy. Murya a rissine yace, “Daddy zanje wani wajene fa bayan airport ɗin”.
    “Sai ku tafi tare da ita tama huce kafin ku dawo gida”.
    Sosai takaici ya sake lulluɓesa. Sai dai baice komaiba. Daddy da kansa ya buɗe gefensa ya sakata dan Abie baya ya shiga. Koda suka bar gidan shi da Abie ne kawai keta hirarsu. Itako tai tsit kamar bata a motar, sai ajiyar zuciya take faman saukewa idanunta a lumshe sanyin ac na ratsata. A airport ɗin ma Abie shareta yay har sai da aka fara shelar masu tafiya a jirgin da zaibi sannan yaɗan fara lallashinta da ƙara mata nasiha. Daurewa kawai takeyi, amma ita dai bata ƙaunar zama a ƙasar batare da iyayenta ba. Da ƙyar ya ɓanɓareta a jikinsa domin amsa kira, tana ganin ya shige ta dirƙushe a wajen. Takaici ya saka Shareff buɗe motarsa yay shigewarsa. Jin ya mata key ya sata miƙewa da sauri dan ta tabbatar kaɗan daga aikinsa ya wuce ya barta a wajen.

      Sunbar airport ɗin kaɗan kiran Momy ya shigo masa. Idonsa ya ɗan rumtse kafin ya kai hannu ya ɗaga. “Kana ina?”. Ta faɗa tunkan yay sallama. “Mommy can gidan mana”. Ya faɗa a tausashe. “What! Al-Mustapha kana da hankali kuwa? Da wannan yarinyar kake nufin kaje?! To ina mai tabbatar maka maza ka sakota a napep ta dawo gidan ko ranka ya ɓaci bansan iskanci”. Ɗan jimm yay na sakanni biyu. Sai kuma ya ɗan saki murmushi. “Okay Mommy ba damuwa”. Numfashi ta sauke a hankali da faɗin, “Yauwa ko kaifa. Bana son wannan karon naji abinda bai minba kaga dai yanzu akwai banbanci da da. Ka kula ka bita a yanda take so dan ALLAH”. Nanma murmushin kawai yayi batare da yace komai ba, sai dai har cikin kunnenta tajisa dan haka tai masa sallama ta katse kiran. Wayar ya ajiye shima ya cigaba da tuƙinsa a nutse har suka iso.
       Da sauri ta waro idanu waje ganin inda suka zo, ta dubesa idanunta nayin ƙwal-ƙwal na tahowar kuka. “Yaya! nidai ka kaini gida bazanje wannan gidan ba”.
       Harara ya zuba mata, batare da yace komai ba yay parking a ƙofar gate ɗin. Sanin abinda zatai nan gaba shine roƙonsa ko guduwa ya sashi dubanta, “Haɗiyemin wannan silly hawayen banzan kafin nai miki dukan mutuwa a wajen nan”.
     Babu wasa a zancen nashi, dan haka ta haɗiye sautin kukan sai dai hawayen kam sun kasa tsayawa. Wayarsa data fara tsuwwa ya ɗauka, ganin mai kiran ya sashi ɗagawa da kaita kunne. “Ina waje”. Kawai ya faɗa tare da yanke wayar. Ko mintuna biyar basu gama cikaba Fadwa ta fito cikin yauƙi da yanga. Wando da riga ne a jikinta parkistan ƙirar Egypt. Sosai kalar kayan ya fidda mata ƙyawunta. Musamman yanda ƙaton gilashin data saka ya kusan mamaye rabin fuskar tata da haska farar fatarta. A hankali Anam taja guntun tsoki da ɗan laɓe baki. Sarai Shareff ya jita, sai dai komai baice mataba har Fadwa takusa ƙarasowa garesu.
     “Fita ki koma baya”.
Yanda yay maganar a dake batare da ya kalleta ba ya sata juyowa ta kallesa. “Are you daft?!”.
     Maganar tasa tayi dai-dai da isowar Fadwa jikin motar tana ƙoƙarin buɗe gaban ta shiga dan batai zaton ganinsa da wani ba ma balle wata.  Da sauri Fadwa taja baya saboda yanda Anam ta buɗe murfin a fusace. Saura kaɗan ta bugeta ma ALLAH dai ya taƙaita abun. Ko kallon inda take Anam bataiba tai ƙoƙarin barin wajen maimakon baya daya bata umarnin komawa. Sai dai kuma Fadwa tasha gabanta da sauri....
     “K! K! Dakata k! Ƴar uban wacece a motar mijina?”.
     Ba kowacce hausa Anam ke ganewa ba, dan haka a yanzun ma bata fahimci furucin farko ba hakan yasata kasa haɗa ma'anarsa dana ƙarshe da ƙyau. Amma a yanda Fadwa tai maganar ta tabbata ba'abune mai ƙyau ta faɗa ba. Wani banzan kallo ta watsa mata kawai dajan tsaki ta ratseta zata sake barin wajen. Hannu Fadwa tasa ta fisgota ta maidota baya a wani irin fusace, kasancewarta mutum mai saurin zuciya da son yanke hukunci sai kawai ta ɗaga hannu da nufin zabgama Anam ɗin mari.........✍


*_Tofa babbar magana, wai ɗan sanda yaga gawar soja. Hajiya Fadwa daga ganin sarkin fawa sai miya tai zaƙi. To ku garzayo cikin tafiyar zafafa biyar domin ganin yaya wannan wasan zai kasance😂. Dan tabbas akwai cakwakiya, idan nace cakwakiya ina nufin cakwakiya ƴar gaske. Yanda Fadwa take a tsaye Anam ɗin ma ba kanwar lasa bace. Littafine daya ƙunshi abubuwa da yawa. Rikicin zumunci, makirci, son zuciya, kishi, cin amana, kai harma da SARAN ƁOYE. Wasa ne kashi-kashi, dake da players daban-daban. Karku bari ayi babu ku, zafafa dabanne masoya, musamman na wannan ƙarnin da zasu zo muku a cikin zafi na musamman. Karna cikaku ku dai ku garzayo kawai._*

_Dan girman ALLAH, dan girman ALLAH, dan girman ALLAH kizo ki mallaki halak ɗinki, idan baki da kuɗin saye ko baki da ra'ayin saye basai kin damu da karantawa ba dan baya cikin wajib. Mai tunanin siya ko mana mugunta ki fitar kiji tsoran ALLAH karki cutar damu bamu cutar dake ba, idan kinyi shirin haka da gayya ko izgilanci a garemu muna roƙon UBANGIJIN al'arshi mai rahama mai jin ƙai, mai sanya alkairi a zukatan dake ƙudurta sharri ya shiryeki ya ganar dake gaskiya ya kuma bamu kariya daga abinda zuciyarki ke ƙulla miki😊🙏🏻._



KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.

DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL

IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)
BIYU (400)
UKU (500)
HUDU (700)

KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

HAFSAT UMAR KABIR
ZENITH BANK
2270637070

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

07040727902

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09134848107


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽


[10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_07_*


.........Tunda suka tafi tsakanin shi da ita babu wanda yayma ɗan uwansa magana. Yanata tuƙinsa da amsa wayoyi itako tana buga game a wayarta cike da nishaɗi har suka iso. Motar ta buɗe tai ficewarta tana taɓe baki, sai da ta rufe masa ƙofar batare data kallesaba tace, “Jazakallahu khairan” tai gaba abinta. Fusgar motar yay da ƙarfi yay gaba har yana tada ƙura. Hakan yasata faɗin, “Kaji dashi in kayane dai”.

        Koda ya tashi a aiki baibi takanta ba yay wucewarsa gida. Tun Anam na jira da marmari har ranta ya fara ƙuna gashi bata sayi layin Nigeria ba har yanzun. Sosai ranta yake a ɓace ga yunwa dake bala'in cin hanjinta dan bawani abun kirki taci da safeba ta fito, da rana ko inibi data taho dashi a bag kawai tasha da strawberry. Ganin yamma na ƙara mata, gashi bata san yanda zata kira wani a gidan ba tunda babu waya ta fito domin samun abun hawa ko zata iya ganewa. Ga wani irin zafi dake ratsata duk da rana ta risina kasancewar anyi la'asar, sai dai ita zafi takeji matuƙa kodan inda ta fito akwai ac ne.
        Ta tare abin hawa yafi sau huɗu amma ta rasa yanda zata musu misalin anguwar, wasuma basa gane jagulalliyar hausarta da yaren malay ya cinye, turancin ma idan tayi wasu suce basaji wasu suce basu fahimci kwatancenta ba. Kanta ta dafe ƙwalla na cika mata ido dajin wani irin tsanarsa a cikin ranta, tabbas bata ƙaunar wulaƙanci shiyyasa bata wulaƙanta kowa, kai bama ta tashi taga iyayenta na wulaƙanta wani ba kowa abin girmamawarsu ne koda bai kaisu wani matsayi na duniya ba. Hannu takai a hankali ta share ƙwallar idanunta tana maijin kewar iyayenta da ƙaunarsu, waɗannan matsalolin na ɗaya daga cikin abinda ta guda a zuwanta hidimar ƙasa Nigeria, amma su Mamie suka kasa fahimtarta.......
        Harya gota ta ya dawo baya da mamakin kodai gizo idonsa ke masa. Dai-dai saitin da take yay parking da sauke gilashin motar. Tabbas itace inhar bai ruɗeba, dan yanda yarinyar ta shiga ransa bayajin zai manta fuskarta koda a barci ya tashi.
     “Beauty!”.
  Ya faɗa cikin tsantseni da taraddadin wasiwasi.
           Duk da tajisa tunma tsayuwarsa hakan baisa ta ɗago ba. Sai ma sake haɗe fuska da tai ta ɗauke kai gefe fiye da yanda ya sameta. Murmushi ya saki dan yanda tai ɗin ya tabbatar masa ita ɗince. Buɗe motar yay cike da farin ciki ya fito. “A gafarce ni. Assalamu alaiki ƙyaƙyƙyawa”. Duk da bata saki fuska ba ta amsa masa. Ya koma ta gabanta cikin sake raunana murya. “Inaji a jikina ke rabonace Beauty. Ranar Yayanki ko saurayinki ne ban saniba ya gudumin dake gashi yau ALLAH ya haɗamu daga ni sai k”. Karon farko ta ɗan ɗago ta dubesa, ya sakar mata murmushi. “Dan ALLAH kar kice baki ganeni ba”.
     “Bamma taɓa ganinka ba”.
Ta faɗa da ƙoƙarin barin wajen. Sauri bin bayanta yay. “Please dan ALLAH karkimin haka. Ni ne wanda muka taɓa haɗuwa a GJ restaurant da daddare”. Sarai ta ganesa tun kiranta Beauty da yay dan muryarsa bata bace mata ba. Amma sai ta sake ɓata fuska aɗan fusace tace, “Bani bace Please kabar bina”.
       “Kiyi haƙuri bazan iya daina binki ba wlhy dan kullum cikin addu'a da sadaka nake akan ALLAH ya sake nunamin ke. Ya kuma amsamin sai nayi sakaci da damata”.
   Sosai ya bata dariya a wannan gaɓar, wai sadaka. Dan kawai ya ganta zaiyi sadaka. Hararsa tai zata sake wucesa ya babbake ko'ina. “Dan ALLAH ki saurareni”. Kanta ta dafe dan yanata faman haɗata da abinda bazata iya jayayya ba. Hakan yasa dole ta nutsu ta sauraresa. Bawata magana sukaiba damar kaita gida kawai ya nema. Bata da mafitar data wuce binsa, amma maimakon gida da yace zai kaita sai kawai ta buƙaci ya kaita inda zata sai layin waya. Bai musa mataba, dan a ganinsa hakanma wata damace.
        Kai tsaye office ɗin mtn dake cikin wata plaza yakaita duk da yasan sun tashi aiki yanzu. Sai dai yanada alfarmar da za'a iya biya mata buƙatarta a wajen. Ilai kuwa tarba ta mutuntawa taga ana masa a wajen, yanda kuma suke gaisuwa da ogan wajen taji a ranta ɗan uwansane ko aboki.
      “Mutumina wannan ƴar shilar fa haka?”.
    Abokin ya tambaya cike da shaƙiyanci cikin zaurancen hausa da Anam ta kasa gane komai dan shima ya fahimci bata iya hausan ba, saboda yanda yay mata tambaya da hausa ta gagara bashi amsa mai ƙyau. Dole suka koma magana da turanci. Murmushi kawai yay batare daya bashi amsaba, sai ma danna waya da yake faman yi abinsa.
     “Wai ka zama kurma ne?”.
Abokin ya sake tambaya yana harararsa.
       “Sarai ina jinka. Kai dai yi aikinka  kawai ba buƙatar tambayar ne”.
   Dariya kawai abokin yay ya cigaba da ƙoƙarin ɗaukar Anam hoto. Tun a gurin ta ɗora layin akan wayarta, ta kuma tambayesu ko zata iya amfani da shi. Kasancewar abokin nasa babban ma'aikaci sai ya amshi wayar yay ƴan danne-danne ya miƙa mata. “Indai kiran gaggawa kike sonyi da shi bashi nan da mintuna talatin sai kiyi”.
    Godiya ta masa tare da duban saurayin da har yanzu ko sunansa bata sani ba. “Zamu iya tafiya?”.
     “Why note Beauty”.
  Ɗan murmushi kawai tai da mikewa. Shima ya bama abokin nasa hannu suka cafke. “Friend ina zuwa ka jirani Please ”.
     “Ba damuwa”.
Cewar abokin nasa yana dariya.
        
    Ganin sun ɗan gota plaza ɗin tace su ɗan tsaya mintuna talatin ɗin su cika. Bai musaba sai dai ya kalla agogonsa duk gudun kar lokacin salla ya shiga. “Beauty inaga muɗan matsa gaba akwai massallaci sai na shiga nai magrib ko”.
     “Babu damuwa”.
Ta faɗa hankalinta akan wayarta. Tun fitarsa a motar babu abinda take sai irga mintuna har ALLAH yasa suka cika. Kai tsaye number ɗin Abie tahau gwadawa dan ta loda kati daga kuɗinta na bank a ciki. Taƙi samunsa saboda network. Komawa tai kan Mamie itama dai yaƙi tafiya kiran. A take idanunta suka sake cika da ƙwalla, ta kife kanta a gwiwarta tana karanto duk

2 Comments On BABU SO
avatar
aisha-6-7-7

5 months ago

Reply

Inason littafinnan sosai

avatar
aisha-6-7-7

5 months ago

Reply

Inason littafinnan sosai

Please Login or Register in order to submit comment