Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sashen Shareff ɗin da tuni Abie ya ware dominsa duk da ba zama yake ba a hanunsu yanzun. Duk hidimar da ake Anam na ɗaki batako fitowa sai yunwa ta isheta. Bamai ganin ko fara'arta. Mamie tayi faɗan harta watsar da lamarinta, hakama Aysha fushi take da ita dan ita bataga mi Anam ɗin kema fushe-fushen ba tunda babu wanda ya mata wani abu ai. Aima gaba ɗaya ta tsame kanta daga shagalin bikin tamkar Shareff ba ɗan uwanta ba. Da yamma kusan rabin jama'ar gidan suka wuce gidansu Fadwa amarya kamu amma nanma Anam bataje ba. Kai barci ma suka wuce suka barta tana sha hankali kwance. Koda suka dawo kuma su Aysha nata labarin yanda kamu ya kasance da ƙayatarwa Anam sai tai tsaki tama fice a ɗakin gaba ɗaya. Da kallon mamaki duk suka bita, sai dai babu wanda ya kawo komai a ransa game da al'amarin nata tunda ansanta da miskilanci da kuma tsanar da sukaima juna ita da ƴan gidan su Fadwa batun yanzu ba.

        *_WASHE GARI* ta kama ranar ɗaurin aure, har sha biyu Anam na ɗakin Abie tana shaƙar barci. Dan tun bayan sallar asuba ta gudo daga ɗakinsu saboda hayaniya tafi ƙarfi acan downstairs. Duk tashin da Mamie ta mata taƙi, sai kawai ta shareta ta cigaba da hidimar baƙinta, dan nan ɗinma dai ya cika taf da dangin Mamie da ƴan uwa da abokan arziƙi kasancewar wannan shine karo na farko da zata fara aurarwa, duk da ba'ita ta haifi Shareff ba an mata karar riƙesa da tai tamkar ɗanta auren ya koma tamkar a hanunsu ne.
      Mutane sai tambayar ina Anam akeyi, sa'ointa ma na family ɗin sunata zuwa nemanta. Bata tashi ba sai kusan ƙarfe ɗaya, batare da tayi ko brush ba ta fito sanye cikin kayan barci fuska a kwaɓe dan yunwa takeji. Fitowar tata yayi dai-dai da shigowar ango da tawagar abokansa, yayi ƙyau har ya gaji cikin ɗanyer shadda fara tas sai baza ƙamshi yake yi. Ga wani kwarjini na musamman da kwalliyar ta basa tabbacin yau ɗin ta daban ce a garesa. Hakama abokansa kowa ya sha ƙyau.
     Anam ta kafesa da manyan idanunta da barci ya sa su yin wani luf-luf da sake girma, shima tunda ya shigo nasa idon a kanta suke, sai dai lokacin ɗaya ɗan murmushi dake a saman fuskarsa ya bace ɓat, ya ɗan harareta ya ɗauke kansa kasantuwar caa da ƴan uwan Mamie sukai masa kowa na faɗin albarkacin bakinsa cikin yabawa.
     Murmushi ya ƙaƙaro yana kaiwa rissine domin gaishe su kamar yanda abokansa sukayi suma, kafin ya miƙe zuwa gaban Mamie da tun shigowarsu idonta ke kansa tana murmushi. Gabanta ya durƙusa ciki sanyin murya mai nuna rauni yace, “Mamie zamu tafi masallaci”.
      Hannu ta ɗora saman hularsa, itama muryarta a raunane da sanyi  tace, “ALLAH yay maka albarka Al-Mustapha. ALLAH yasa a ɗaura a sa'a, kuma yasa abokiyar arziƙinka ce har a aljannah”.
    Gaba ɗaya falon aka amsa da amin. Shareff da kansa ke ƙasa ya kasa ɗagowa, hakan yasa Mamie kamo haɓarsa da yatsunta biyu ta ɗago fuskarsa. A hankali hawayen dake maƙale a idanunsa suka gangaro, murmushi ƙarfin hali tayi da ƙoƙarin son danne nata hawayen dake son zubowa amma hakan ya gagara. Itama sai kawai ta saki kuka mara sauti tana goge masa nasa hawayen da hanunta duka biyu. Sun birge kowa, sun kuma bama kowa tausayi, duk da wasu basu san dalilin kukan nasu ba kai tsaye.
    Mamie dake murmushi ga hawaye tace, “Tashi kuje karku makara su Abie ɗinku sun wuce tun ɗazun. Kai Shareff ya gyaɗa a hankali, sai kuma ya kai hannu shima ya share mata nata hawayen, ta saki murmushi da shafa kansa. “ALLAH yay maka albarka”.
      Da amin aka sake amsawa. Ya miƙe idonsa na kallon ɗan lungun da zai sadaka da hanyar upstairs inda Anam take. Har yanzu tana gurin, hasalima leƙensu take baki a taɓe dan ita bataga miye na kuka ba inba gulma ba. Harda faɗin, “Su Mamie an iya kalan dangi, Mommyn sa batako kallona da arziki amma ke kinama ɗanta wannan kulan”. Ganin ya miƙene yasata komawa ta maƙale, jin kamar sun nufi hanyar fita ta sake leƙowa. Ido suka haɗa dashi yana tsaye shi da Aunty Mimi suna magana. Fuska ta taɓe da murguɗa baki tabar wajen. Numfashi ya saki a ɗan fisge da lumshe idanunsa ya ɗauke kansa shima. Aunty Mimi da duk taga komai tai murmushi kawai tana kallonsa.
      Fuska ya ɗan kwaɓe. “Miye kuma small Mom?”.
   Dariya tayi da faɗin, “A'a babu komai My son. Kuje karku makara ALLAH yasa a ɗaura a sa'a.”
     “Humm”
kawai yace mata yay gaba abinsa. Ta sake ƙyalƙyalewa da dariya. “Ita dai wannan Humm ɗin bata magani Yarona”.
       Murmushi kawai yay batare daya juyo ba ya fice abinsa. Dr Jamal da Fharhan da suka rage na take masa baya..

       Bayan ficewarsu Aunty Mimi bin bayan Anam tai. Ganinta zaune tana kallon su Aysha daketa faman shiryawa ta korata itama tai wanka. Ta kuma tabbatar mata idan har ta sake shigowa ta ganta bakamar kowaba saita ɓata mata rai matuƙa. Babu yanda ta iya dole tabi umarninta, su dai su Aysha sai faman dariya suke. Bata kulasuba ta shiga tai wanka, ta fito ta shiryawa a ɗaya daga cikin kayan fitar biki da su Daddy sukai musu. Sai dai kalar nata daban tasa saɓanin ƴan uwanta da duk suka saka atamfa. Sosai lass ɗin yamata ƙyau kasancewarsa skirt da riga kuma bata saba sakawa ba. Tai ɗas abinta kamar itama amaryar ce (Anam team😜).

_________________________________

        Alhamdulillahi bayan idar da sallar juma'a dake massallacin juma'a na anguwarsu ɗunbin al'ummar musulmi daga sassan daban-daban na Nigeria da wajenta suka shaida ɗaurin auren *_Al-Mustapha Muhammad Shareff_* da amaryarsa *_Fadwa Sadiq Dakata_* akan sadaki naira dubu ɗari biyu. Ɗaurin aurene daya tara manyan mutane masu alaƙa da ango da iyayensa harma da ɓangaren amarya.
        Kamar yanda nan gidan su  Shareff ke cike da ƴan uwa da abokan arziƙi acan gidansu amarya Fadwa ma hakane. Taci ado na faɗa aji daya amsa suna ado irin na amare ƴan ƙwalisa masu ji da lokaci (😘😍Sai dake tawan😂😉). Tana tsakkiyar ƙawayenta daketa aikin zuba hotuna da videon ɗorawa a tiktok. Tun kafin yau amarya Fadwa ta roƙi angonta da zarar an ɗaura aure ya taimaka ya kirata ya fara sanar mata da kansa. Da farko bai amsaba, sai dai yanda ta dinga nacin damunsa da maganar tsahon lokaci yace zaiyi. Shi mutum ne dabai ɗaukar alƙawari bai cikaba, sai dai hakan ta kasance bisa akasi. A yanzun ma harya shafa'a alƙawarin ya faɗo masa a rai. Yana tsaka da gaisuwa da abokansa yay excusing kansa ya koma gefe yana mai ƙoƙarin cikawa. Ga amarya Fadwa kam harta fidda rai zuciyarta sai faman kaikawo take kamar ta fasa kuka. Ta riga ta gama shiryawa da ƙawayenta domin jiran wannan lokaci, sai dai shiru kakeji sun fara jin kishin-kishin na cewar an ɗaura auran. Dama tasan itama gangancine kawai, Shareff ba irin mazan da ke ɗaukar kowane kalar shirme bane, hasalima ita har yanzu bai san tana harkar yanar gizo ba, da tana da tabbacin sai sun kwashi ƴan kallo da shi.......
      Ring ɗin wayarta ya katse mata tunani, tamkar maijin tsoro ta ɗauka wayar tana dubawa badan ta saka ran ganin shi ɗin bane. Kasa ɗagawa tai har sai da babbar aminiyarta Sima ta ɗaga mata tasa a hansfree dan sunada tabbacin abinda suke zaman jiran ji ne daga angon dama. Sassanyar muryarsa data ratsa cikin wayar ta saka ɗakin ƙarayin tsitt, masu video recording na faman ɗauka. Cikin rawar murya ta amsa, dan haka kawai taji kuka ya taho mata batare data san dalili ba. Daga can yay murmushi saboda jin yanayinta, ashe da gaske aure yaƙin mata ne, dan yasan abinda zai saka Fadwa karaya ba ƙarami bane. Yay ɗan gyaran murya da sake kwantar da murya. *_“Habibtie kin zama Matar Al-Mustapha, ina roƙon UBANGIJIN daya nufemu da ganin wannan rana ya bamu lafiya da zuri'a masu albarka, tare da haƙurin zama da juna, mai cike da kulawa da soyayya na har abadan. Finally Al-Mustapha ya zama naki”._* Kalamansa sun ratsata daga ita har ƙawayenta da abun yay matuƙar burgesu, sai kawai ta sakar masa kukan da taketa faman haɗiyewa. Murmushi yayi, da sake faɗin, “Congratulations once again dear, i love you”.
       “I love you too”.
Ta amsa masa da sake fashewa da kuka. Gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki wani irin ihu da sowa harda masu guɗa. Jama'a dake waje kuwa har ture juna ake wajen son shigowa aga mike faruwa.

      Cikin ƙanƙanin lokaci video ɗin da ƙawayenta suka ɗauka suka ɗaura a tiktok, istagram ya fara yawo fiyema da yanda sukai zato ko tsammani a kowane shafi na sada zumunta kamar yanda sauran hotunan da suketa ɗaurawa na sauran kwanakin ke yawo dama . Wanda ma followers ɗinsu basu kaiba tuni ƙaruwa suke. Comments da like kam ai bama a magana. Ƴammata sai alwashi ake ɗauka da zuwan tasu makamanciyar wannan rana. Wanda ko bikinsu ke shirin zuwa next week dama cikin satin tuni sun fara neman angunan nasu da ƙawaye yanda zasu tsara nasu suma. (Hummm media-media gidan kashe ahu😣).

      ★★★  

   Daga wajen ɗaurin aure gayyar abokan ango da abokan su Daddy dama sauran jama'a suka ɗunguma hall ɗin da aka shirya walimar cin abinci domin su. Anci ansha anyi hotuna kafin ango da tawagarsa su nufo gida. Yanzun kam sai da suka fara shiga gidansu yakai kansa ga Mommyn sa. Rungumesa tai cike da farin cikin yaronta ya zama babban mutum yau burinta ya cika. Ƴan uwa da abokan arziƙi nata tayasa murna da masa fatan alkairi. Anyi hotuna shida dangin Mommy dama sauran jama'a har da wanda ke a tsakar gida na kusa. Daga nan gidan su Anam suka nufa da gayyar abokansa tunda dama nan ne masaukin nasu, Mamie kuma tama sake shirya musu wasu abincin anan dama.
       Nan ɗin ma gidan cike yake da ƴan uwa da abokan arziki. Shigowarsu ta saka wasu fara sakin guɗoɗi, yayinda maroƙa keta aikin kirari na al'adar biki. Su Aysha da duk suke zaune a harabar gidan suma kan kujerun roba da aka zube miƙewa sukai cike da farin ciki suka nufi Yayan nasu dan tayasa murna suma. Anam dake faman latsa waya duk hayaniyar da ake gidan batako ɗaga kanta ba taja siririn tsaki, tare da gyara zamanta dan babu alamar zata bisu.
       Har aka fara ɗaukar hotuna bata  ko kalli sashen da suke ba. Sai ma mikewa tai da nufin barin wajen taji an riƙo hanunta. Juyowa tai a fusace da tunanin cikin su Amrah ne, sai tai arba da aunty Mimi. Baki ta tura idonta na tara hawaye, aunty Mimi ta girgiza kanta da faɗin, “ALLAH ya shiryeki Mamana”. Hanunta taja har cikin taron, ta kaita har gaban Shareff ta tsayar.
      Ƙoƙarin haɗiye hawayen dake son zubo mata ya hanata iya ɗagowa ta kalli kowa take, ga idanu tanaji a kanta da maganar da aunty Mimi ke mata akan ta ɗago mai hoto zai ɗauka. Aunty Mimi zata ƙara magana Shareff ya girgiza mata kai, tare da yima camara man ɗin nuni daya dauka kawai. Aiko ɗaukar ya farayi abinsa, bayan an musu su kaɗai kusan kala uku mutane suka fara shiga, daga haka aka cigaba da ɗauka batare da ko sau ɗaya Anam ta kalli camara ba. Daga ƙarshe ma ƙoƙarin zame jikinta a wajen ta shiga yi dan kukan da take dannewa ƙoƙarin fin ƙarfinta yakeyi. Taku ɗaya tai taji an riƙo hanunta, cak ta tsaya, tare da juyowa da sauri zuciyarta na ƙara zuwa wuya. Ɗaukewa numfashinta ya nemayi a dalilin shigar idanunta cikin nasa, ya kuma sarketa da su da iyakar ƙarfin ikonsa. Ga hanunta har yanzu yana riƙe a cikin nasa. Tuni camara man ya maida hankalinsa a ɗaukarsu hoto. Ƙoƙarin janye hanunta tayi ya hana hakan, ga idanunta ma sun gagara fita a cikin nashi. Hawayen da take maƙalewa ne suka silalo a fuskarta a hankali, ta fisge hanunta da sauri tabar wajen harda ɗan haɗawa da gudu. Waɗanda hankalinsu ke kansu duk suka bita da kallo kamar yanda shima ya bita har sai da ta ɓace. Ido suka haɗa da aunty Mimi yay saurin ɗaukewa shima yana barin wajen..........✍

*_Ko anƙi ko anso, aure dai ya ɗauru, murna muke daga zuciya har zuwa ranmu💃🏻😍😜. (Anam team ya take ne🤣😂😉😜?)_*


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
0913484810_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107 ko



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽
[10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*




*_11_*


.......Ɗin! Ɗinn!! Horn dake nuna alamar isowar dangin amarya Fadwa ya saka Gwaggo juyowa baki a washe tana faɗin, “A to ga masu ganin gidan nan ma sun iso ai? Kai Alhaji ƙarami muje ka buɗe musu ƙofa ɗin saina tarbesu ai ko”.
      A hankali ya lumshe idanunsa da sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya. Mommy ma bin bayan Gwaggo tayi, suma su Mom sai suka bisu kawai dan abu kaɗan zai iya jawo Gwaggo taita surutu. Har zai bisu ya dawo da baya, zuciyarsace ta bashi shawaran ya sakama ƙofar key, dan haka ya kulle da sauri ya fidda key ɗin ɗakin a cikin keys ya saka aljihu sannan yabi bayansu...
       
       Mota uku ce a jere kai kace jeren kayan sukazo. Motar farko Fadwa ce ta fara fitowa a ciki, sai ƙawayenta uku. Ta biyu kuma ƙannen babanta ne su biyu da cousin ɗinta biyu suma dai duk masu aure ne. Sai aminiyar Gwaggo Haliman. Motar ƙarshe babban yayan Fadwa sauran kuma ƴan kamfanin da zasuyi aikinne dan motarma akwai tambarin kamfanin. Cikin mutunta juna aka gaisa tunda dama akwai alaƙa, kafin su ɗunguma gaba ɗaya zuwa can. Fadwa sai satar kallon Shareff take amma yayi kicin-kicin kamar ma bai ganta ba. Dama tun waccan ranar ko kiransa tai baya ɗagawa, idan tai masa magana koda yana a online kuwa ko buɗewama bayayi. Tabi duk hanyar daya dace su sasanta amma yaƙi kulata dan yayi alwashin koya mata hankali a wannan karon.
     Ko'ina sai da suka shiga kowa na yabawa dan gida kam yayi sai dai maƙiyi. Ma'aikatan kamfanin da zasu saka kayan kuwa nata faman gwaje-gwajensu tunda dama amarya ta gama zaɓar wanda take buƙata tun a gida. Zare jikinsa yay ya koma sashensa batare daya amsa tambaya ko ɗaya ba akan ɗayan sashen dasu Gwaggo sukai magana suma. Shi dariya ma suke bashi da mamaki, ina ruwansu da sashen to tunda basu suka basa kuɗin ginin ba, sashen dama ko ƙarasa masa ayyuka ƙananu ba'aiba ya tsolema kowa ido.
    Baifi mintuna biyar da shigowa ba Fadwa ta biyo bayansa. Bai nuna alamar yasan da shigowar tata ba. Duk da shariyar tasa ta sosa ranta sai ta shanye ta shiga yaba yanda sashen nasa yay matuƙar ƙyau shima. Yanda tsarin ya kasance na black and milk da ratsin ash ya matuƙar ƙayatarwa.
      “Soulmate!”.
Ta kira sunansa a hankali tana kaiwa zaune kusa da shi. Bai amsa ba, bai kuma ɗago ya dubeta ba yanata aikinsa kamar yanda ta samesa. Murmushin takaici ta ɗanyi tana kallonsa, ta lumshe ido ta buɗe akansa zuciyarta na raya mata abubuwa masu yawa dan ba ƙaramin haɗin kayan mata tasha ba. Sake matsawa tai jikinsa a kasalance ta ɗaura kanta a shoulder ɗinsa ta saki kuka.
      Cak ya tsaya da aikin da yakeyi, yaja numfashi ya fesar yana mai rufe idonsa da buɗewa a lokaci guda.....
          “Dan ALLAH kayi haƙuri ka daina fushi dani haka nan Yaya Al-Mustapha. Karka manta kwanaki takwas kacal ya rage mu zama abu guda, ina buƙatar ganin murmushi a fuskokinmu yayinda jama'a zasu fara taruwa dominmu daga gobe. Naji nayi laifi kuma na amsa na kuma bada haƙuri bazan sake ba mijina”.
      Kalamanta sun ɗan saka masa sassauci, sai dai baida alamar cewa wani abu a zahiri. Kanta ta ɗago daga kafaɗarsa tana kallonsa idanunta na rige-rigen matso hawaye, ta riƙo hanunsa dake dafe da lap-top har yanzu sai dai ba aikin yake ba. “Baka haƙuraba ko My Soulmate? Shike nan na baka damar kaimin kowane irin hukunci amma dan ALLAH banda naƙin kulani na tuba”.
       Karon farko ya ɗago idanu ya dubeta, kafin ya maida ga hanunsu dake cikin na juna. Nasa ya janye tare da ɗan bada tazara daga kusancinsu. “Naji ya wuce, sai dai ki tabbata kika sake hukuncin dazan ɗauka bazakiji da daɗi ba. Ni da ke zamu zauna bada iyayenmu ba, dan haka matsalarmu mune ya kamata mu fuskanceta basai wasu sunyi alƙalanci a ciki ba”.
      “Insha ALLAHU zan kiyaye mijina”. Tai maganar tana faɗawa jikinsa ta rungumesa. Hannu yasa ya janyeta. “Nasha faɗa miki bana son ɗabi'ar nan sam. Domin babu wani hallaci daya halatta hakan garemu”.
           “To kayi haƙuri, amma karka manta kwana takwas ya rage kacal mu zama ma'auratan ai ko, kaga kenan akwai banbanci da da yanzun”.
    “Sai ki bari sai mun zama ɗin, a yanzu dai haramunne”.
     “Hummm” kawai ta faɗa dan bata bukatar su sake wani rikicin kuma saboda kar yay amfani da damar yaƙi halartar duk events da suka shirya gara ta lallaɓasa ayi a tashi lafiya karya kunyatata ga ƙawayenta. “My Soulmate bara na ɗanyi using toilet Please”.
     Ɗagowa yay ya ɗan dubeta dan harya sake maida kansa ga aikin gabansa. “Yanzu a barowanki gida har sai kinzo wani waje kin shiga toilet?”.
           Murmushi tayi daya sake ƙawata ƙyawun fuskarta. “Oh My Soulmate nan ɗin aiba wani waje bane na daban, shine fa gidana nanda kwanaki kaɗan zan dawo rayuwar cikinsa. Bawani abu zanyiba part zan canja dan bana iya wuce awa ɗaya da shi a jikina”.
      Idanunsa ya ɗauke daga kallonta, haka kawai yaji wani iri a ransa ganin babu ko ƴar kunya tattare da ita take faɗin part zata canja. Da hannu ya nuna mata toilet na falon.
           “Ah-ah my Soulmate bara dai na shiga bedroom mana. Nan kuma idan cikin su Mommy wani ya shigo fa”. Komai baice mata ba, harta nufi hanyar bedroom ɗin Anam dake barci a ciki ta faɗo masa. Dakatar da ita yayi. “No ki shiga wannan ɗin can ƙofan nada matsala ne, sai angyarasa a rufe yake”.
    “Okay! To bara naje naga bedroom ɗin namu ko?”. A ɗan kausashe yace, “Shi nake nufi”. Ɗan jimm tai tana kallonsa. Sai kuma tayi murmushi cikin rausaya kai ta nufi na falon kawai. Shima aikinsa ya cigaba dayi, a zuciyarsa yana ALLAH-ALLAH su kammala su tattara subar gidan.
       Addu'arsa kam ta karbu, dan koda ta fito bata zauna ba kasancewar ƙanwar abbanta nata faman kiranta a waya akan ta fito zasu wuce.. Tare da shi suka fita, yaji daɗi sosai da su Mommy sukace suma zasu wuce ne magrib na gabatowa.

     Bayan duk wucewarsu ya dawo ciki, kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa, key ɗin daya cire yasa ya buɗe babu zato ko tunanin ta tashi a ransa.... Kusan a tare ƙofofin guda biyu suka buɗe. Shi yana shigowa ita tana fitowa daga bathroom. Wata irin ƙara ta fasa da ƙanƙame guntun towel ɗin data ɗauro a jikinta dake ɗigar ruwa tareda faɗawa saman gado ta cukuykuye zanin gado da duvet ɗin gaba ɗaya a jikinta....
        “you are vary stupid!!”.
Ya daka mata tsawa jin tana barazanar fasa masa dodon kunne.
     “Na shiga uku ni dai ka fita, dan ALLAH ka fita, Yaya wlhy babu ƙyau ganin tsiraicin wani. Wayyo ALLAH Mamie banji maganarkiba nashiga halaka.......
    “Shut up! Stupid!”.
Ya sake faɗa da matuƙar takaicinta. Bedsheet ɗin ta tusa cikin baki tana gyaɗa masa kai ga hawaye na faman mata gudu a fuska kai kace wani abu yace zai mata. Shiko gaba ɗaya idanunsa sun birkice dan takaici, ya ƙarasa takowa gaban gadon yana watsa mata mugun kallo. “Ubanwa ya saki yin wanka anan ɗin? Ko an faɗa miki nan gidan wanka ne?”. Kanta take girgiza masa tana ƙara maƙurewa waje guda, dan ita a yanzu ba faɗan nasa take tsoro ba a yanda ya ganta da a yanda take. “Dan ALLAH kayi haƙuri Yaya. ALLAH zafine ya dameni kamar fatana zai ɗaye zufa ya jiƙani ina ƙyanƙyami shiyyasa nayi”. Rasama mizai ce mata yay, ga jikinta sai rawa yake matuƙa. Tsaki yaja ya juya ya fita kawai. “Mintuna biyar na baki”. Ya faɗa dai-dai yana jan ƙofar har saida ta zabura saboda bugata da yay.
      Kanta ta cusa tsakanin ƙafafunta ta ta sake sakin wani kukan na baƙin cikin ya ganar mata jiki abinda wani mahaluki bai taɓayiba bayan Aunty Mimi da Mamie. Duk da bawai tsirara ya ganta ba a ganinta ƙanƙantar towel ɗin baida maraba da hakan ita kam. Tuna abinda ya faɗa na karshe da yay yasata zabura. Durowa tai a gadon ta nufi ƙofar ta saka sakata, da sauri ta kwashi kayanta duk da ɗunbin ƙyanƙyamin da take musu ta shiga maidawa a jikinta da sauri-sauri. Bata kammala ɗaure igiyar abayar jikinta ba ta fito. A falo ta samesa tsaye sai faman kai da kawo yake tamkar mai safa da marwa. Tai ƙasa da kai dan a yanzu kam babu abinda take gudu kamar su haɗa ido, wani irin matsanancin kunyarsa takeji har ƙarƙashin zuciyarta. Shima bai dubi inda takenba ya nufi bedroom ɗin nasa, bai koyi mintuna biyu ba ya fito da kayansa da sukazo gidan suna jikinsa. Magungunanta da lap-top ɗinsa ya ɗauka yay waje. Da sauri tabi bayansa dan dama kamar jira take ace ar ta kwasa ana kare.
        A motar ma hankalinta ta maida gaba ɗaya waje badan tana fahimtar abinda take kallo ba, sai dan bata buƙatar koda kallonsa. Shima ɗin dai aikin tuƙinsa yake kawai lokaci-lokaci yakan amsa waya har suka iso gida. Yana gama parking ta fice. “Waye zai biki da wannan?!”. Baya ta dawo kanta a ƙasa ta ɗauka ledar magungunanta daya ɗaura saman mota ta wuce har tana harɗewa saboda yanda take tafiya da sassarfa.
     
     ★★★★

   Shirye-shiryen biki ya ƙara kankama, yayinda Anam ke faman wasan ɓuya da Shareff. Sam ta daina yarda su fita aiki tare, kafin ya fito ta shirya tabi bus ɗin su Fawwaz da ake kaisu school. Data tashi aiki kuma zata saka wani abokan aikinta ya tare mata Napep ta dawo gida. Bata yarda dai ta faɗama kowa abinda ya faru ba, sai dai tun ranar har yanzu bata sake ganin Yaseer ba. Ya daina shigowa aiki ta daina samun number ɗinsa kuma. Ta tambaya iya wanda suke mu'amula a wajen aikin nasu duk sun sanar mata suma basu san miya hanashi zuwa aiki ba. Amma dai ance ya kawo reason nashi wajen oga. Haƙura tai tabar bin kowa, sai ma haushinsa ya kamata. A yanda suke tana ganin ya dace ace ya sanar mata idan zaiyi tafiyane kokuma wani abu ya samesa ai.
        Ranar laraba gidan aka tashi da shirin isowar su Abie. Wannan ne ya ɗauke mata dukkan hankali ta manta da batun Yaseer. Taso ace da ita za'aje tarbo iyayenta airport sai dai batasan waye zaije ɗakkosu ba, dan haka ta haƙura kawai tai zaman jiransu a gida. Aiko ƙarfe huɗu da rabi

2 Comments On BABU SO
avatar
aisha-6-7-7

5 months ago

Reply

Inason littafinnan sosai

avatar
aisha-6-7-7

5 months ago

Reply

Inason littafinnan sosai

Please Login or Register in order to submit comment