Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

11/25/20, 1:08 PM - Messages to this chat and calls are now secured with end-to-end encryption. Tap for more info.
11/25/20, 1:08 PM - Princess soja ✍🏻✍🏻: ♥️♠️♥️♣️

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏

♥️♠️♥️♣️
```Love and romantic story```


_Na_


_Hassy soja_



```Wannan labarin nawa salon sa na daban ne ban yarda wani ko wata su canza mani labari ba sai akiyaye```




*MARUBUCIYAR*


_BANI CE BA (ALJANA CE)_

_ASHE YAN UWA NA NE (MU BIYAR)_

_MUFIDA KAWAR ALJANA_

_SUMAIYYAH SUMEE BABY GIRL_

_HAKURI_

_SAI NI YAR DAJI NI KUMA YAR BIRNI CE_

_MUHSEENA DA MUHSEEN_


_AND NOW_

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏


_*BISMILLAHAR RAHAMANI RAHIM DA SUNA NA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI*_




_*SADAUKARWA GA MAHAIFIYA TA DA MAHAIFINA ALLAH YA JIKAN MAHAIFINA YAYI MASA RAHAMA MAHAIFIYA TA ALLAH YA KARA MAKI LAFIYA DA NISAN KWANA*_🤱🏻🤱🏻




PAGE... 3️⃣&4️⃣


*________________*📚


Innar Rabi "Tace *innalillahi wa inna ilaihir raji un* Allah ya shirya wadin yaran sannan ta ta shige dakin ta tana mamakin irin su Asiya.



Bayan sun fita sai *Asiya sarkin tsiwa yar Gaggo* ta tsaya tana kallon su Shatu da Rabi "Tace yo sai kiyi tsaye kuna kallo na eeeyyee ina mangwaro na ne?.



Gashi nan fa *Asiya yar Gogga* kuma aradun Allah ya nuna cewar Rabi.



To ku bani na zaba sannan kowa ya dauka ko tana kallon su.



Eh hakane kwaliya cewar Shatu tana murmushi.



Sannan ta dauka ta fara ci sai ta hango wani yaro da awara yana tallah "Tace yauwa Allah ya kawo ka yaro dan wallahi yau sai nayi maka shegen duka kuwa kuzo muje.



Da gudu suka iske yaron mutane sai Asiya "Tace kai zo nan dan uwar ka tana kallon sa.



Yaron "yace Allah ni dai ba uwata ba yana kallon Asiya.



*Asiya sarkin tsiwa yar Gaggo* ta zaro ido "Tace Eyyee to sai uwar wa nace sai uwar wa eeyye?.



Rabi "Tace yasin sai mu ci uban ka gurin ga kuwa ko kwaliya tana kallon Asiya.




Shatu "Tace gaskiya ne yaron nan mu zakayiwa rashin kunya ko?.



Asiya "Tace wawa da wasali saman shine wa asa masa wawa da gudu suka kwace bukitin awara suka gudu sai da sukayi nisa sosai sannan suka tsaya suna nishe.




Suka samu guri suka zauna sai da suka canyi gaba d'aya sannan suka hau saman bishiyar mangwaro.



Yaron ya fadi kasa yana kuka yana shure shure sai ga wani bawan Allah yazo wuce wa sai ya kalle yaron sai ya tsaya "yace kai hafizu lafiya dai kayi zaune kana kuka haka?.



Cikin kuka "yace wallahi su *Asiya sarkin tsiwa yar Gaggo* suka kwace mun awara ta kuma innata tace duk ta bata sai ta dake ni sai ya kara fashewa da kuka.



Shikenan yaro kashiga tarkon su yarinya nan bata jin maganar kowa wallahi *innalillahi wa inna ilaihir raji un* Allah ya shirya su cewar wannan bawan Allah.



Su Asiya ne Zaune suna hutawa saman bishiyar mangwaro sai Rabi "Tace *Asiya yar Gaggo* wai kun san wani abu kuwa?.



Da sauri Asiya "Tace Aa sai kin fada menen halama?.




Wallahi naga dan mai gari ya shiga da wata yarinya dakin sa ya rufe kuwa cewar Rabi tana kallon Asiya da shatu.



Asiya "Tace jar uba shege dan iska ku tashi muje gurin wallahi sai na gano abubuwan da yake aiki tawa.



Shatu "Tace kan uban can shege dan iska haihuwa bakin titi.



Haka suka ji gurin dakin dan dan mai gari ko da Asiya ta kara kunnen ta sai taji nishin sa yana cewar ki tsaya mana kada naji maki ciwo gaskiya kina da dadi sosai ga manya manya nonowa su Asiya "Tace kan uban can shege dan iska haihuwar bakin titi wato dama 'dayan mutane yake kawowa kenan.




Lallai ne yaron nan yau zaka ci uban ka cewar shatu.



Asiya "Tace kuzo muje gida mu dawo ko zuwa Dare ne kafin a fara dandali dan wallahi yau sai na bashi tsoro kuwa.



Yauwa kawaliyar mu muje gida gurin Gaggo ko?.



Da gudu suka wuce sai gidan su *Asiya sarkin tsiwa yar Gaggo* wata mata ce ta fito daga cikin daki sai taga su Asiya sun shigo da gudu Asiya "Tace uhm uhm sannu Gaggo.



Tsaye Gaggo tayi tana kallon su Shatu da Rabi "Tace kai ku lafiya zaku shigo cikin gida ko sallama babu bale gaisuwa?.



Uhm yasin ni dai babu wata sallama da zanyi yauwa Gaggo wallahi yunwa nake ji tana kokarin zaunawa.



Yawon ki da kuka saba ya baki wato dama kun can kuna dukan yaran mutane ko?.



Asiya ta mike tsaye "Tace jar uban can wane munafuki ne zo har cikin gida nan ya fada maki ne?



Gaggo "Tace haba haba dai dama nasani sai kun aikata mtss to Allah ya shirya ku.



Amin ya Allah sai Gaggo cau cau sai Gaggo Allah dai ya bar muna ki Gaggo cewar Asiya da shatu da Rabi.



Gaggo dai ta saba da irin halin su Asiya "Tace wai ke Asiya yaushe rabun ki da wanka ne?.



Asiya sai da tayi tunani sannan "Tace yo ina ga bazai wuce mako biyar ba kawai.




*innalillahi wa inna ilaihir raji un* kai jama,a Yanxun fisabillahi Yau fa satin ki biyar babu wanka wannan wane irin kazanta ce yo dole kirin ka tsamin dauda mtss to Allah ya shirya ki to Yau kam sai kinyi wanka sannan zan baki abinci.



Wayyo Allah na Wayyo na mutu na dawo sai tuma takeyi tsakar gida Wayyo jama, a kuzo ku ce ce ni.



Gaggo sai kallon Asiya takeyi da mamaki "Tace *innalillahi wa inna ilaihir raji un* Allah ya shirya ki wallahi baki da hali mai kyau da kinyo halin uwar ki da kin huta wallahi mtssw.



Sai da Gogga tayi da gaske sannan ta samu Asiya tayo wanka bayan ta fito daga wanka sai Asiya "Tace kai ku lafiya zaku saka mani ido ne? tana hararar su.



Shatu "Tace haba kiyi hakuri mana kwaliya kin san akwai abun da zamuyi fa.



Kiran isha,i ne yasa Asiya tayi sauri ta dauko fara huda "Tace bari ku gani ta sanya doguwa riga fara ce har kasa sai ta sanya kayan sannan ta dauko fara huda ta bursu na ta ga fuskar ta kamar aljana sannan ta kalle Shatu "Tace yayi dai dai ko?.




Eh wallahi sai kace aljana hhhh cewar Shatu.




Rabi "Tace yo dole sai dan mai gari yayi kasa awandon sahhh.




Duka kowa sai da ya sanya kayan sannan suka fita sai kofar dakin dan mai gari.




Asiya ta zubo gashi ta har ga fuskar ta idan ka hango su sai ka tsorata saboda shigar da sukayi kamar aljannu.



Dan mai gari ne kwan ce saman gado yayi d'aya d'aya sai sharar bacci yake su Asiya ne suka shigo cikin dakin sa.



Duka suka bushe da dariya hhhh lallai ne dan mai gari kana nan ka hutawa.




Asiya "Tace ku tashe shi mana.



Da karfi shatu ta dake sa sai da ya zabura "yace uban waye nace waye ne?.




Asiya "Tace hhhh hhhhh mu aljannu ne munzo gurin ka ne?.



Jikin dan mai gari ya fara rawa "yace Wayyo Allah na dan Allah kaka aljana kiyi man rai.



Mu ba, a bamu hakuri dama Ana fada muna kana lallata yan matan mutane ko?.




Dan Allah Inna aljana kiyi hakuri wallahi bazan kara ba.



Ku dan koya masa hankali.



Suka kama dukan sa sai da yayi fitsari sannan suka rabu da shi.




Asiya "Tace gobe kaje fada ka fadawa mai gari kace kaika lallata yaran mutane kaji ko?.



Tooo inna aljana zan fada masa wallahi.




To shikenan gobe duk baka fada masa ba ko zamu dawo.



Too shikenan zan fada masa wallahi.




Cikin tsawa Asiya "Tace To dan uwar ka baza muna godiya bane?.



Aa zan maku nagode wallahi sosai.



To rufe idanuwan ka.



To shikenan sai ya rufe idanuwan sa.



Da gudu suka fita waje suna dariya mugunta.





****************************


Saheeb ne kwan ce saman makekin gado yana kallon saman sai ya tashi Zaune "yace mtsss ni wallahi Ammi ta bata mani rai na wai kauye tab Allah ya tsare ni da naje kauye.



Wata yar yarinya ce ta shigo da gudu "Tace uncle uncle uncle Grandma na kiran ka.



Saheeb "yace oyoyo my baby yaushe kuka shigo ne?.



Yarinya "Tace uhm uhm tun dazu muka zo yauwa uncle ina alawa na?.



To muje ko guri Ammi haka ya rika hannun yarinyar suka fita.



Ammi ce zaune da ita da wata yarinya mai kama da Saheeb.



Da gudu yarinya ta zo gurin Ammi "Tace uhm uhm Grandma ga uncle nan fa.



Saheeb ne ya sauko daga saman bene sai ya hango wata mai kama da shi "yace to yau kuma bakuwa mukayi ne sannan ya kara so gurin da su Ammi ida suke Zaune.



Yarinyar "Tace uhm eh wai kai yaya Saheeb baka zuwa gida na ko to nayi fushi da kai sai ta bata fuskar ta.



Saheeb yayi murmushi sannan "yace haba dai ni na isa nace bazan je gurin my Humaeera ta yar kanwata.



Ammi dai tana kallon su tana murmushi jin dadi "Tace uhm Saheeb an gama fushi da ni?.



Haba Ammi dan Allah Yanxun fisabillahi bazaki dai na wannan maganar ba?.



Ammi "Tace kasan Allah sai kaje kauyen nan kuwa.



Cikin bakin ciki da takaice ya tashi "yace ni fa gaskiya bazan je wannan kauyen ba fa.




Ammi ranta ya bace "Tace to shikenan bari Alhaji ya dawo sai na fada masa kuwa kuma wallahi kaji na fada maka dole sai kaje ka gano mani 'yata da Gaggon ka.



Afusa ce ya fita daga cikin falo yana cewar mtss wallahi har zuciyata ta fara tashi akan zuwa wannan shegen kauyen mtsss ....



*MASOYYA NA ALLAH YA BAR ZUMUNCI*💃🏻h💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻



*Hassy soja*😘🤪🤪🤪



*Comment and share*
11/25/20, 1:08 PM - Princess soja ✍🏻✍🏻: ♥️♠️♥️♣️

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏

♥️♠️♥️♣️
```Love and romantic story```


_Na_


_Hassy soja_



```Wannan labarin nawa salon sa na daban ne ban yarda wani ko wata su canza mani labari ba sai akiyaye```




*MARUBUCIYAR*


_BANI CE BA (ALJANA CE)_

_ASHE YAN UWA NA NE (MU BIYAR)_

_MUFIDA KAWAR ALJANA_

_SUMAIYYAH SUMEE BABY GIRL_

_HAKURI_

_SAI NI YAR DAJI NI KUMA YAR BIRNI CE_

_MUHSEENA DA MUHSEEN_


_AND NOW_

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏


_*BISMILLAHAR RAHAMANI RAHIM DA SUNA NA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI*_




_*SADAUKARWA GA MAHAIFIYA TA DA MAHAIFINA ALLAH YA JIKAN MAHAIFINA YAYI MASA RAHAMA MAHAIFIYA TA ALLAH YA KARA MAKI LAFIYA DA NISAN KWANA*_🤱🏻🤱🏻




PAGE... 1️⃣&2️⃣


*________________*📚


*A CIKIN GARIN ABUJA KUWA AKWAI WANI HADADEN GIDA KAI GASKIYA GIDAN YA HADU BA KARYA*




Wata mata ce zaune meki manin shekara 60 tana shafar gashin wani hadaden sauraye wanda baze wuce shekara 34 ba kwan ce yake yana hutawa saman kafar wannan mata.




Matar "Tace uhm saheeb wai yaushe zakaje kauyen nan ne?.




Saheeb"yace haba haba Ammi dan Allah ki daina maganar zuwa na kauye dan wallahi har kin sa zuciyata ta fara tashi.




Ammi "Tace gidan ku nace gidan ku Allah ka kiyaye ni fa Yanxun ina bakai ba wa zayaje gurin Gaggon ka ne?.




Saheeb "Yace to ni dai ba Yanxun ba.



Ammi "Tace Ka san Allah sai kaje garin nan kuwa kaji na fada maka.



Cikin bakin ciki da takaice ya tashi ya wuce dakin sa ya fada yana cewar ni fa wallahi na tsani kauyen nan fa haba dan Allah ba za, a bari mutum ya huta ba mtsss bari ma na kira daddy najiya.




*************************

*A KAUYEN KANO KUWA*




Wata yarinya ce na hango fara ce sosai kamar balarabiya gashin ta har ga bayan ta idan kaganta sai kace aljana ce tana tafiya tana rawa saman hanya tana cewar Eyyee yaraye ah ah ah eyyee yaraye muyi soyayyah.




Shatu ce ta fadu mata a raye sai "Tace ko ina zanga shatu ko naje gidan su Aa kai bazanje ba saboda masifafin tsohon nan kuwa tana kalle kalle sai ta hango shatu na karasowa.




Gaban shatu sai faduwa yake tun da ta hango asiya to akwai matsala sai dai bata nuna "Tace lallai *Asiya yar Gaggo* daga ina haka?.




Wata uwar harara da Asiya ta watsa mata "Tace ban sani ba wai ma ina mangwaro na ne? eeeyyee sai girgizar jiki takeyi.




Shatu "Tace yana gurin Rabi yar malam.



Asiya "Tace yo ina ruwa na da wata Rabi muje ki amso mani abuna dan wallahi ko hanjin malam ina gani akan mangwaro na kuwa.



Shatu ta zaro ido "Tace hanjin malam fa yo ina laifin ki kama dukan Rabi.




Asiya "Tace kan uban can wallahi muje kuma dama ina da haushin ku wallahi yau sai nayi maku dukan tsiya eehee tana hararar shatu.




Jikin Shatu ya kama rawa dan tun da taji Asiya tace zata dake su to mai Raba su sai ya shirya sai "Tace haba *Asiya yar Gogga* kiyi hakuri ni fa kawaliyar ki ce fa haba *yar Gogga*.




To naji muje gidan su Rabi amman duk abu na ya bata ko hee hee hee zaku sha dukan tsiya ga *Asiya yar Gaggo* kuwa.




Shatu sai hadi yawu kawai take "Tace too insha Allah bazai bata ba kuwa.



Ni dai babu ruwa na kuwa muje dai ko.




To shikenan da gudu suka wuce sai gidan su Rabi yar malam suna isowa da gudu suka shiga cikin gida ko sallama babu bale gaisuwa.




Wata mata ce zaune sai dai taga su Asiya sun shigo da gudu Asiya bata kalle wannan mata ba sai kira Rabi kawai take "Tace Rabi ke Rabi wai ina kika shiga ne? to wallahi ki fito kuwa sai girgizar kunkuru take.




Wai ke Asiya baki iya sallama bane bale gaisuwa?.




Sai ta jiyo tana kallon innar Rabi "Tace yo dole ne sai nayi sallama ne to baza, ayi din ba tana murgudar baki.




Allah ya shirya ki yarinya kullum rashin kunya Bata rufe baki ba sai ga Rabi ta fito da gudu dauke da mangwaro.




Dan Allah *Asiya yar Gaggo* kiyi hakuri wallahi Baba yace wai kar na fita ni kuma shiyasa na gudo cewar Rabi.




Rabi kada ki fita kin san malam ya hana ki fita da su ko.




Asiya "Tace tooo yar bakin ciki to sai munje ko kawaye na sai mundawo yeeee yeeee da gudu suka fita daga cikin gidan.




Innar Rabi "Tace *innalillahi wa inna ilaihir raji un* Allah ya shirya wadin nan yaran....



*Topa*



*Waye wannan saheeb din?*. 🤔🤔


*Meyasa baya son zuwa kauye ne?* 🤔🤔



*Wace ce Asiya sarkin tsiwa yar Gaggo?* 🤔🤔



*To masoyya na ku biyo ni dan jin amsoshin ku*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻




*IDAN YA SAMU AMSUWA ZAN CIGABA DA SHI INSHA ALLAH*🥰🥰🥰💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻



*Hassy soja*😘🤪🤪🤪



*Comment and share*
11/25/20, 1:08 PM - Princess soja ✍🏻✍🏻: ♥️♠️♥️♣️

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏

♥️♠️♥️♣️
```Love and romantic story```


_Na_


_Hassy soja_



```Wannan labarin nawa salon sa na daban ne ban yarda wani ko wata su canza mani labari ba sai akiyaye```




*MARUBUCIYAR*


_BANI CE BA (ALJANA CE)_

_ASHE YAN UWA NA NE (MU BIYAR)_

_MUFIDA KAWAR ALJANA_

_SUMAIYYAH SUMEE BABY GIRL_

_HAKURI_

_SAI NI YAR DAJI NI KUMA YAR BIRNI CE_

_MUHSEENA DA MUHSEEN_


_AND NOW_

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏


_*BISMILLAHAR RAHAMANI RAHIM DA SUNA NA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI*_




_*SADAUKARWA GA MAHAIFIYA TA DA MAHAIFINA ALLAH YA JIKAN MAHAIFINA YAYI MASA RAHAMA MAHAIFIYA TA ALLAH YA KARA MAKI LAFIYA DA NISAN KWANA*_🤱🏻🤱🏻




PAGE... 5️⃣&1️⃣0️⃣


*________________*📚



Afusa ce ya fita daga cikin falon yana cewar mtss wallahi har zuciyata ta fara tashi akan zuwa wannan shegen kauyen baza, a bari mutum ya huta ba mtss kiran da yar yarinya takeyi masa ne "Tace uncle uncle uncle shiyasa ya tsaya.



"Yace uhm uhm my baby ya akaye ne?.



Yarinya "Tace uhm uhm uhm uhm ina zuwa inda zakaje.



To ina zamuje ne Yanxun?.



Yawo muje shopping ko uncle?.



Ok babu damuwa muje ko sai ya rika hannun yarinyar suka shiga mota suka fita daga cikin gidan sai gurin shopping.



Ammi ce zaune tayi tagume tana mamakin irin halin Saheeb "Tace oh ni Hauwa ban sani meya sa Saheeb be son zuwa kauye ba.



Humaeera "Tace uhm ni fa wallahi halin yaya Saheeb yana bani mamaki sosai gashi daga ni sai ku kawai yake ma magana idan kika ga fuskar sa kamar wanda aka aiko ma da sakon mutum to Allah ya kyau.



To amin ya Allah ni fa Yanxun 'yata nake son gani fa gashi ma Alhaji yace man sati mai zuwa zai dawo.



Wow masha Allah Allah ya kawo muna shi lafiya wallahi nayi missing din sa sosai wallahi kwan da yawa ba mu hadu ba.



Amin ya Allah hakane Yanxun dai ina jiran sa yadawo na fada masa wallahi.



Sallamar Saheeb ce ya katse masu fira.



Assalamu Alaikum.



Amin wa Alaikum sallam har kun dawo?.



Eh Grandma har da sweet da alawa ta tana murna.



Ok babu damuwa yau sai dai kin gaji da surutun Baby walida.



My baby muje sama ko?.



Eh uncle da gudu tabi sa dakin sa Ammi dai ta besa da ido "Tace wai fushi yake yi da ni fa kuma akan zuwa kauye ne.



Hhhh Ammi da 'danta babu mai shiga tsakan ku wallahi.



Bayan Saheeb ya shiga cikin daki sai baby walida "Tace uhm uhm uncle yaushe zamuje gurin Anty na tana kallon sa?.



Antyn ki kuma wa cece kuma antyn ki yana kallon ta?.



Sai ta kama tunani sannan "Tace Matar ka mana inason zuwa gurin ta.



Cikin ran sa "yace Wayyo Allah na wallahi wannan yarinya ta cika shegen surutu.



"Tace uncle lafiya kake tunani? .



Babu komai fa kawai dai ina tunanin zuwan mu gurin ta gashi bata nan Nigeria fa.



To yaushe zata dawo ne?.


Sai dai muyi waya da ita.



Kiran wayar sa ne yasa ya duba sai ya ga sunan Daddy na aciki da sauri ya dauka .



Hello daddy.



Hey dan daddy ya akayi ne kana lafiya dai ko?.



Lafiya Qlau daddy wai yaushe zaka dawo ne?.



Sati mai zuwa insha Allah da nadawo za, ayi bikin bude war companyn ka insha Allah.



Wow thanks daddy gaskiya naji dadin wannan maganar.




Ok zamuyi magana idan na dawo sai ya kashe wayar sa.



Sai da Gaban Saheeb ya fadi "yace Allah ya sa ba maganar zuwa na wan can shegen kauyen bane?.





****************************

Su Asiya tafiya suke suna dariya hhhh gaskiya naji dadin tsoratar da dan mai gari wallahi cewar Shatu.



Ai wallahi har da mai garin nan nake so mu baiwa tsoro kuwa cewar Asiya.




Rabi "Tace too abari a kwan biyu ko kwaliya tana kallon su Shatu.




To shikenan Yanxun dai muje gida gurin Gaggo.



Asiya tun Yanxun ba zamuje dandali ba ne?.



Ni aradun Allah na gaji fa cewar Rabi.




Ok to shikenan ku bari sai zuwa gobe sai muje gidan su halima burtuka.



To ni dai nayi gida da gudu shatu ta wuce gida.



Rabi "Tace too kwaliya sai gobe ko.



To shikenan da gudu Asiya ta wuce gida ko da ta shigo cikin gida sai ta kama leke ko zata hadu da Gaggo "Tace Allah ya sa Gaggo tayi bacci tana kallon kofar dakin su.



Ashe Gaggo tana kallon ta tun sanda ta shigo cikin gidan nan.



Asiya zata shiga cikin daki sai taga Gaggo Zaune tsakar gida tana kallon ta "Tace uhm wai Gaggo bakiyi bacci ba?.



Haba Asiya ya zan iya bacci baki dawo gida ba ke kullum kina gurin bakin yawo na tsiya mtss wallahi ki kiyaye ni fa Yanxun dai ga abinci can sai kije ki dauka.



Kai Gaggo ke kullum fada haba haba dan Allah sai ta dauko abinci ta fara ci can sai "Tace wai ke Gogga bamu da kowa ne?.



Wato bazaki tashi yin magana ba sai kina cin abinci ko?.



Kai Gaggo daga tambaya ni fa da gaske nake muna da yan uwa ne?.



Eh muna da yan uwa da yawa ko yayar mahaifiyar ki yana nan kuma yana da yara guda biyu akwai Saheebu da Aishatu wato humaeera kuma yana da kudi sosai.



Wayyo Allah na Wayyo dadi kai gaskiya har na hango ni *Asiya sarkin tsiwa yar Gogga* ina cin naman kaza.




Ikon Allah wato dama har kin hango kan ki cikin gida

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

1 Comments On ASIYA SARKIN TSIWA YAR GWAGGO
avatar
ali-boukary

12 months ago

Reply

Ina jindadin litafinna allah kara zakin hannu

Please Login or Register in order to submit comment