Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
01. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN'UWANSA
SHAMSUDDIN.

Allah shi ne Sarki ma fi daukaka daga dukkan
Sarakuna, shi ne ma fi tsarki daga dukkan
abubuwa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga
Manzonsa, Annabi Muhammadu (S.A.W).

Ka sani, ya Sarkin Musulmi, a kasar Misira an yi
wani Sarki, ma'abucin adalci da kyautatawa. Yana
da Waziri mai hankali, mai rarrabe abubuwa da
dabaru, mai tarin ilimi da fasaha, sai dai ya
kasance tsoho ne, shekaru sun yawaita a kansa.
Wazirin nan yana da 'ya'ya biyu maza, kai ka ce
'yan tawaye ne. Ga su kyawawan gaske, babu
kamar su a duk fadin kasar. Sunan babban
Shamsuddin, sunan karamin kuwa Nuruddin.

Karamin, watau Nuruddin, ya zarce wansa ga
kyawo da cikkar halitta. Ya kasance a cikin wancan
zamanin babu tamkarsa ga kyawo. Labarin
kyawonsa ya watsu cikin manyan birane da
kauyuka. Mutane da dama sukan tafi tun daga
garinsu har zuwa Misira, domin ganin kyawo irin
na Nuruddin.
Kwanci tashi, ran nan sai Wazirin Misira ya kwanta
ya mutu. Sarki ya yi matukar bakin ciki a kan
mutuwar Wazirinsa. Sarki ya rungumi 'ya'yan
Waziri a jikinsa, ya ce, "Ku ne a matsayin ubanku a
wurina." Yara suka yi farin ciki. Aka yi zaman
makokin mahaifinsu aka gama.
Shamsuddin da kanensa Nuruddin suka zama su
ne a matsayin Waziri ga Sarkin Misira. Idan
wannan ya hau karagar mulki, bayan sati guda sai
ya sauka dan'uwansa ya hau. Sukan yi canji duk
ranar Jumu'a, idan kuma Sarki zai yi tafiya, sai ya
tafi da daya, ya bar daya yana mulkin gari.
Wata rana daga cikin ranaku, Sarki ya yi niyyar
tafiya wata kasa, aka yi gamo da katar, hukunci ya
fada za a tafi da babban ne, watau Shamsuddin.
Daren da za su tafi, Shamsuddin ya kira dan
uwansa suka zauna suna hira. A cikin hirar tasu
Shamsuddin ya ce da dan'uwansa, "Na yi nufin
idan Allah ya maido mu gida lafiya daga tafiyar da
za mu yi gobe da Sarki, mu yi aure lokaci guda, a
cikin rana guda."
Nuruddin ya ce, "Kai ne babba, kuma kai ne a
matsayin ubana a halin yanzu. Ka aikata duk
yadda ka so, za ka same ni mai biyayya a gare
ka."
Shamsuddin ya ce, "Insha Allahu da zarar na dawo,

zan nema mana 'yan mata biyu, mu aure su rana
daya, mu shiga dakinsu dare daya, su sami ciki
lokaci daya, su haihu rana daya. Matarka ta haifi
da namiji, matata ta haifi 'ya mace. Su tashi tare,
su yi wasa tare, idan suka isa aure mu aurar da su
ga junansu, su zama 'yan bappanni."
Nuruddin ya ce, "Allah ya sa haka. To amma idan
haka ta tabbata, me za ka karba gun dana a
matsayin sadakin 'yarka?"
Shamsuddin ya ce, "A matsayin sadakin 'yata, zan
karba gun danka, dinari dubu uku, da gona talatin,
da gidaje uku."

Yayin da Nuruddin ya ji haka sai ya ce, "Haba!
Wane irin sadaki ne mai tsanani za ka dora wa
dana haka, ko ka manta cewa mu 'yan'uwan juna
ne, kuma Wazirai muke, matsayinmu daya. Ya
zamanto wajibinka ne ka aurar da 'yarka ga dana
kyauta, ba tare da karbar ko dirhami daga gare shi
ba. Ko ba ka san namiji ya fi mace daraja ba?"
Shamsuddin ya harzuka da wannan zance na
kanensa, ya ce, "Babu shakka kai ba ka da hankali,
tun da ka ambata tarayyar Wazirtaka tare da ni,
kuma kana nufin danka ya fi 'yata daraja ne? Ni fa
na roki Sarki ya sa ka Waziri tare da ni saboda
tausayinka da nake ji, shi ne yanzu har kake hada
kanka da ni. Tun da har ka fadi haka, to Wallahi ba
ni aurar da 'yata ga danka, ko da zai biya zinariyar
da ta kai nauyin 'yar tawa a matsayin sadaki."

Yayin da Nuruddin ya ji zancen dan'uwansa, ya yi
fushi, ya ce, "Ni ma dana ba zai auri 'yarka ba, ko
da babu sauran mata a duniya sai ita kadai."
Shamsuddin ya ce, "Ni ma ban yarda 'yata ta auri
danka ba, ko da babu sauran maza a duniya sai
shi kadai. Amma yanzu na yi nufin tafiya, waccan
niyyar ta aurenmu lokaci daya na fasa yin ta, Allah
ya aikata yadda ya so."

A cikin wannan dare, Nuruddin da Shamsuddin ba
su kwana wuri daya ba kamar yadda suka saba,

kowa ya kwana daki dabam saboda bacin rai. Da
gari ya waye, Shamsuddin ya shirya domin tafiya
da Sarki, ya nemi dan'uwansa domin su yi sallama
amma bai gan shi ba. Don haka sai ya bi Sarki
suka tafi.

Ashe kuma tun da asuba Nuruddin ya riga
Shamsuddin tashi daga barci, ya shiga taska, ya
dauki jaka karama ya cika ta da dinari. Ya tuna
maganganun da dan'uwansa ya yi masa a daren
jiya, da kuma gorin Wazirantaka da ya yi masa. Ya
tuna wakar wani mawaki, in da yake cewa:
"Ka yi tafiya cikin duniya, za ka sami musayar abin
da ka rasa.

Ka kafu da kafafunka, farin ciki na ga wanda ya
dogara da kansa.
Ni na ga tsayuwar ruwa wuri daya tana gurbata
shi, ruwan da yake gudu shi yake tsarkaka.
Ba don farin wata yana fakuwa ba, da ba a dube
shi ba ranar tsayuwarsa.
Ba don zaki yakan rabu da surkuki ba, da bai sami
abin farauta ba.
Ba don kibiya takan rabu da baka ba, da ba ta
zama abin tsoro ba.
Komai kyawon sanda, idan tana jikin icce ba a
ganin kyawonta.
Zinariya tamkar kasa take, ba a ganin kyawonta sai
ta rabu da kasa.
Wanda ya zauna gida, ba ya daukaka har duniya ta
san da shi."

Bayan ya dauki abin da yake so ya dauka daga
cikin taska, ya umurci wani bawansa ya daura
masa sirdi ga wani farin dokinsa mai kiba, mai
gaggawar tafiya. Bawa ya daura wa doki sirdi da
likkafu kirar kasar Hindu. Ya shimfida shimfidar
Asbihaniya a kan sirdin. Bawa dai ya shirya doki da
kayan kawa masu tsadar gaske wadanda sai
sarakuna da attajirai ke yin amfani da su.
Da Nuruddin zai fita, ya ce wa bawan nan nasa,
"Ina so in fita zuwa bayan gari, zan tafi unguwar
Kalyubati in kwana uku. Kada kowa ya bi bayana,
ina da bacin rai tattare da ni, idan na sami nutsuwa
zan dawo."

Yayin nan ya yi gaggawa ya hau dokinsa, ya rike
wani abu kadan na guzuri a hannunsa, ya fita daga
Misira ba tare da ya san inda zai tafi ba. Burinsa
kawai ya yi nisa da kasarsu da kuma dan'uwansa
Shamsuddin, ya shiga duniya, duniya ta gan shi,
shi ma ya ga duniya.
***

Wannan shi ne farkon labarin mai cike da tu'ajibi
da mamaki da ban tausayi. Za mu ci gaba gobe daidai wannan lokaci (karfe 8 - 9
PM), Insha Allah.

A jibaga√002. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN
UWANSA SHAMSUDDIN

Nuruddin ya yi gaggawa ya hau dokinsa, ya rike
wani abu kadan na guzuri a hannunsa, ya fita
daga Misira ba tare da ya san inda zai tafi ba.
Burinsa kawai ya yi nisa da kasarsu da kuma
dan'uwansa Shamsuddin, ya shiga duniya,
duniya ta gan shi, shi ma ya ga duniya.
Ya fita daga Misira ya shiga daji, Azuhur ba ta yi
masa ba sai da ya shiga birnin Bilbis. Ya sauka
ya huta, dokinsa ma ya huta. Bayan ya ci abinci
ya kuma ciyar da dokinsa, ya sayi duk wani abu
da ya san zai bukata a kan hanya. Ya hau
dokinsa ya fita daga wannan birni ya kutsa kai
cikin daji.

Bayan tafiyar dare daya da yini, ya isa birnin
Kudus. Ya sauka ya huta, dokinsa ma ya huta ya
ci abinci ya ciyar da dokinsa. Ya yi shimfida ya
kwanta domin ya rama baccin da bai yi ba,
zuciyarsa na cike da fushin dan uwansa har
bacci ya dauke shi. Ya kwana a wannan wuri. Da
gari ya waye ya kama dokinsa ya hau ya ci gaba
da tafiya har ya isa birnin Halbi.
A birnin Halbi ya sauka a gidan baki, ya huta
sosai, ya sha iska tsawon kwana uku, bakin
cikinsa ya fara yayewa. Daga nan ya hau
dokinsa ya ci gaba da tafiya, ba tare da ya san
inda za shi ba. Bai gushe ba yana tafiya har ya
iso birnin Basara cikin dare, ba tare da ya san ko
wane gari ne ba. Ya nemi gidan baki ya kwana.
Da gari ya waye Nuruddin ya ce da mai kula da
kofar gidan baki yana so ya tafi da dokinsa rafi
ya yi masa wanka ya shafe shi da mai. Mai kula
da kofa ya kama ragamar doki ya ja ya nufi rafi,
aka yi gamo da katar hanya ta bi da shi ta gaban
gidan Wazirin Basara, yana kuwa zaune a cikin
soronsa.
Da Wazirin Basara ya kyalla ido ya ga dokin
Nuruddin da irin kayan kwalliyar da aka kawata
dokin da su, sai ya ce a cikin ransa, lalle wancan
dokin na wani babban Sarki ne ko Waziri, ko
kuma na wani babban attajiri ne. Ya dubi wani
yaronsa ya ce, ka zo mini da dokin can tare da
wanda ke jaye da shi.
Yaro ya tafi nan take ya zo da mai kula da kofar
gidan baki tare da doki. Da suka zo mai kula da
kofa ya durkusa ya yi gaisuwa ga Waziri. Wazirin
Basara ya kasance tsoho ne sosai, shekaru sun
yawaita a kansa. Ya ce da mai kula da kofa,
wane ne mai wannan doki?

Mai kula da kofa ya ce, "Ya shugabana, mai
wannan doki saurayi ne karami, mai karancin
shekaru, mai kyakkyawan hali na daga 'ya'yan
tajirai, yana da kwarjini da nutsuwa. Jiya ya
sauka a gidan baki, amma na yaba da
kyawawan halayensa, ya shugabana."
Yayin da Waziri ya ji wannan zance ya tashi
tsaye a kan duga-dugansa, ya ce da mai kula da
kofa, "Kai ni inda yake in gan shi." Waziri ya hau
dokinsa suka tafi zuwa ga gidan baki.

Da suka isa gidan baki, suka zarce dakin
Nuruddin, suka yi masa sallama, Nuruddin ya
leko da kansa waje, Waziri ya ga Nuruddin. Da
Nuruddin ya ga Waziri, duk da bai san ko
wanene shi ba, ya fito daga cikin dakin, ya
durkusa a gabansa, ya gaishe shi da lafazi mai
dadi cikin ladabi da biyayya.

Waziri ya sauko daga kan dokinsa, ya rungumi
Nuruddin, ya ce da shi, "Ya dana, daga wane
birni ka zo wannan birni namu? Kuma ina kake
nufin tafiya daga nan?"

Nuruddin ya ce, "Ya shugabana, na fito ne daga
birnin Misira, mahaifina shi ne Wazirin Misira
amma Allah ya yi masa rasuwa."
Nuruddin ya
labarta wa Waziri duk abin da ya gudana
tsakaninsa da dan uwansa Shamsuddin, da
yadda ya yi masa gorin wazirtaka, har ya yi fushi
ya baro garinsu, har Allah ya kawo shi wannan
birni.

Waziri ya ce da Nuruddin, "Yanzu mene ne
burinka a rayuwa?" Nuruddin ya ce, "Buri na
yanzu shi ne in ci gaba da zagaya duniya, ba
zan koma gida ba har sai na ga manya-manyan
birane da garuruka na duniya gaba dayansu."

Yayin da Waziri ya ji haka ya yi murmushi, ya ce
da Nuruddin, "Ya dana, kada ka biye wa bacin
zuciya ta jefa ka ga halaka, sai ka mutu ba ka ko
ji labarin wani birni na duniya ba, ballantana ka
gan shi. Ina rokon ka, ka tashi daga wannan
gidan baki, ka koma gidana da zama."
Nuruddin ya amince da bukatar Waziri, ya hau
dokinsa ya bi shi har suka isa gidan. Waziri ya
sa aka kawo wa Nuruddin abinci da abin sha
masu daraja. Da Waziri ya ga hankalin Nuruddin
ya fara kwanciya, sai ya ce da shi, "Ya dana ka
ga ni tsoho ne mai yawan shekaru, Allah bai
arzuta ni da da namiji ba sai mace, ita kenan na
haifa. 'Yar nan tawa kuwa idan ba ta zarta ka a
kyau ba, to kuwa za ku zo daidai da ita, kuma
ga shi sa'o'in juna kuke. 'Ya'yan sarakuna da
'ya'yan attajirai sun nemi aurenta amma duk na
hana su, domin duk cikinsu ban ga wanda
hankalinsa da halayensa suka dace da 'yata ba.

Tun lokacin da na dora ido a kanka, na san
cewa duk duniya babu wanda ya dace da ya auri
'yata sai kai. Shin ko za ka amince da wannan
tayin na auren wannan 'ya tawa?"
Yayin da Nuruddin ya ji wannan zance na
Wazirin Basara, ya sunkuyar da kansa cikin jin
kunya ya ce, "Na ji na kuma amince da wannan
babbar kyauta taka."
Waziri ya yi farin ciki da haka ya ce, "Tunda na
sami suruki, ni zan yi murabus daga karagar
mulki, a nada ka a matsayin Wazirin Basara, ni
kuwa in koma gefe in ci gaba da bautar Ubangiji
a cikin 'yan sauran kwanakin da suka rage mini
a duniya. Gobe za mu je in gabatar da kai a
gaban Sarki."

Waziri ya tara abokansa, ya yi kiran manyan
attajirai da alkalai na birnin Basara ya ce da su,
"Ku sani cewa ina da dan uwa a birnin Misira
wanda ya kasance shi ma Waziri ne a can.

Wannan dan uwa nawa yana da 'ya'ya biyu
maza, ni kuwa Allah ya arzutta ni da 'ya daya,
kamar yadda kuka sani. Kafin dan uwana ya
rasu ya yi mini wasicci da in aura wa daya daga
cikin 'ya'yansa 'yata, ni kuwa na amsa masa da
haka. Yanzu da na ga ta isa aure, na aika Misira
wannan dan dan uwan nawa ya zo domin cika
alkawarin da na daukar wa dan uwana. Ina so in
rubuta takarda a kan aurensu, ku kuma ku zama
shaida." Mutane suka ce, madalla da wannan
karimci da cika alkawari naka ya Waziri. Yayin
nan jama'suka sha madara da zuma, aka
yayyafa musu wardi, suka watse suna sa wa
Waziri albarka.

Waziri ya sa aka gyara wa Nuruddin wani daki
nan cikin gidan, aka zuba masa kayan kawa da
na ado masu kyau da tsadar gaske, sannan ya
sa aka fara gyaran wani gida daban wanda
Nuruddin zai zauna idan an daura musu aure da
matarsa 'yar Waziri.

Al'amarin Shamsuddin kuwa....

gobe zàmuci gaba Insha allahu

ayi hakuri kwana biyu anjini shuru hakan yafarune. sakßmakon. tàfiya danayi amma yanzu nadawo komai yayi dàidai03. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN
UWANSA SHAMSUDDIN

Waziri ya sa aka gyara wa Nuruddin wani daki
nan cikin gidansa, aka zuba masa kayan kawa
da na ado masu kyau da tsadar gaske, sannan
ya sa aka fara gyaran wani gida daban, wanda
Nuruddin zai zauna idan an daura musu aure da
matarsa 'yar Waziri.
Kashe gari, Wazirin Basara ya riki Nurddin ya tafi
da shi gaban Sarkin Basara. Da suka isa, suka
fadi suka yi gaisuwa gun Sarki. Nuruddin ya
kasance mai fasahar magana, mai natsattsiyar
zuciya da kyan hali, sai ya rera wa Sarki
wadannan baitoci:

"Wannan shi ne Sarkin da ya game jama'arsa da
adalci,
Idan ya yi fushi yakan kori rundunar mayaka
dukkanta,

Ba ya so a yabe shi domin aikinsa gun talaka,
Ya sani aikinsa gun talaka hakkinsa ne a gare
shi,
Ku zo mu sumbanci yatsunsa, domin mabudan
arzukka ne."

Sarki ya yi mamaki a kan fasaha da iya kalamai
na Nuruddin, ya dubi Waziri ya ce, "Wannan
wane saurayi ne, daga ina ya zo wannan birni
namu?" Waziri ya ce, "Wannan yaro dan dan
uwana ne." Sarki ya ce, "Ashe kana da dan uwa
wanda ba mu san da labarinsa ba?"

Waziri ya ce, "Ya shugabammu, dan uwa ya
kasance a gare ni, shi ne Wazirin Misira, ya mutu
ya bar 'ya'ya biyu. Babban dansa ya gadi
matsayin ubansa na Wazirin Misira, shi kuma
wannan karamin ya zo gare ni. Kafin dan uwana
ya mutu, ya yi mini wasici da in karfafa
zumuncinmu ta hanyar aurar da 'yata ga daya
daga cikin 'ya'yansa, na kuma yi masa
alkawarin yin haka. Yanzu da na ga 'yata ta isa
aure, na aika ga wannan yaro ya zo wurina
domin cika wannan alkawari da na yi wa dan
uwana, ya Sarki. Ni ina nufin aurar da 'yata ga
wannan saurayi, ina kuma rokon Sarki ya nada
shi a matsayina, yaro ne mai hankali da dabara
wanda ya gaji sarautar Wazirtaka. A halin yanzu
tsufa ya zo mini, karfina ya kare, ina so in koma
gefe guda in huta kafin zuwan ajalina."

Sarki ya dubi Nuruddin, ya gan shi yaro ne
natattse mai hankali da kuma iya zance na
hikima. Kodayake dai a cikin ransa, Sarki bai
yarda da labarin Wazirinsa ba cewa Nuruddin
dan dan uwansa ne, domin ya san Waziri ba ya
da wani dan uwa a Misira, duk da haka ya
amince da wannan bukata ta Waziri, saboda
girmama shi da yake yi. Aka sa ranar da za a
nada Nuruddin a matsayin Wazirin Basara, aka
kuma sa ranar ta yi daidai da ranar da zai auri
'yar Waziri.
Amma abin da ya kasance ga dan uwansa
Shamsuddin kuwa shi ne, bayan tafiyarsu tare da
Sarki, suka dauki tsawon lokaci kafin su dawo
gida. Bayan sun dawo, Shamsuddin ya huta,
dukkan mutanen gidansa suka zo suka gaishe
shi suka yi masa sannu da zuwa amma bai ga
dan uwansa Nuruddin ba. Ya tambayi bayi, ina
Nuruddin?

Bayi suka ce masa, tun ranar da ya fita tare da
Sarki, Nuruddin ya daura wa dokinsa sirdi, ya ce
zai tafi unguwar Kalyubati domin yana tare da
bacin rai, ya ce kuma ba ya so kowa ya bi
bayansa. Tun lokacin har yanzu ba mu kara jin
labarinsa ba.

Yayin da Shamsuddin ya ji wannan labari,
zuciyarsa ta yi baki, ransa ya baci, ya tuna
maganganun da suka yi da dan uwansa daren
da zai yi tafiya da Sarki. Ya ce a cikin ransa,
wannan duk laifina ne, ba shakka dan uwana ya
yi fushi ne sakamakon tsaurara masa zance da
na yi, daren da zan yi tafiya, ya zamar mini dole
in sa a nemo shi, a lallashe shi, a ba shi hakuri
ya dawo gida.

Shamsuddin ya fada wa Sarki abin da ya faru
tsakaninsa da dan uwansa. Nan take Sarki ya
aika da manzanni cikin kasarsa, kudu da arewa,
gabas da yamma, domin su nemo labarin
Nuruddin. Manzanni suka tafi, bayan kwanaki
masu yawa, suka dawo gun Sarki, ba tare da
sun ji ko da labarin hanyar da Nuruddin ya bi ba.
Shamsuddin ya yi bakin ciki kwarai da gaske, ya
debe tsammanin sake ganin dan uwansa, ya ce
a cikin ransa, "Kaito! Wallahi ni na tsaurara masa
zance a kan auren 'ya'yanmu, wannan yana
daga cikin karancin hankalina da kuma shairin
shaidan. Ina rokon Allah ya gafarta mini bisa ga
wannan kuskure da na yi."

Bayan wasu watanni da faruwar wannan
al'amari, Shamsuddin ya nemi auren wata
yarinya 'yar wani babban attajiri na Misira. Da
ranar daurin aure ta zo, aka yi shagalin buki irin
na Sarkuna da manyan attajirai. Da dare ango
ya shiga gun amaryarsa, bisa ga al'ada da kuma
addinin Musulunci, suka kwana suna
marunguma junansu.

Bisa kaddarawar Allah, yayin da ya zartar da
hukuncinsa a kan halittu, shi ne mai yin yadda
ya so, mai karbar addu'ar talikai. Allah da ikonsa
ya karbi fatar wadannan 'yan uwa biyu. Aka yi
gamo da katar, daren da Shamsuddin ya shiga
dakin amaryarsa a birnin Misira ya zo daidai da
daren da Nuruddin ya shiga dakin tasa amaryar
a birnin Basara. Dukkan matan suka dauki ciki a
daren farko na amarcinsu, tamkar yadda 'yan
uwan biyu suka yi fata.
Bayan wata tara, matar Shamsuddin ta haifi 'ya
mace, wacce a fagen kyau, ba a taba ganin
tamkarta ba, duk fadin Misira. Matar Nuruddin ta
haifi yaro, babu tamkarsa a kyau, duk fadin
Basara, kamar yadda wani mawaki yake fada,
cewa:

"Sassauka ne mai wadatar da abokin shansa
daga yawun bakinsa,
Yakan wadatar da mai gani da ganin kwayar
idonsa da kundukukinsa,
Idan an ce kykkyawa to babu shi a wurin, da
zarar ya zo maganar kyau ta kare,
Dukkan kyakkyawa yakan koma mummuna a
gabansa."

Aka rada wa wannan yaro suna Hassan
Badaruddin a ranar sunansa. Aka yi kasaitaccen
buki tare da walima, aka ci aka sha mai tsada da
daraja.
Tun ranar da aka daura musu aure da 'yar
Waziri, aka nada Nuruddin a matsayin Wazirin
Basara, ya ci gaba da zuwa fada kullum. Sarki
ya yi murna da shi domin iya lafazinsa da fasaha
tasa, ya so shi, ya kusata shi gare shi. Aka kara
masa albashi mai tsoka. Waziri Nuruddin ya rika
tara kudin albashinsa, da ya ga sun yi kauri, ya
sami amintaccin yaransa ya rika tura su, suna
shiga lungu-lungu da sako-sako na duniya
domin yin fatauci. Cikin dan kankanen lokaci,

Waziri Nuruddin ya mallaki jirage, da gonaki da
filaye, ya zama babban attajiri daga tajiran birnin
Basara.
***
Za mu ci gaba gobe iñsha allahu

YuSUF A JIBAGA. ke gaisheku04. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN
UWANSA SHAMSUDDIN

Waziri Nuruddin ya rika tara kudin albashinsa da
yake samu, da ya ga sun yi kauri, ya sami
amintaccin yaransa ya rika tura su, suna shiga
lungu-lungu da sako-sako na duniya domin yin
fatauci. Cikin dan kankanen lokaci, Waziri
Nuruddin ya mallaki jirage, da gonaki da filaye,
ya zama babban attajiri daga tajiran birnin
Basara.
Farin jinin Waziri Nuruddin ya karu ga Sarkin
Basara da jama'arsa, kowa yana son shi da
yabon kyawawan halayensa. Ya kasance dare
da rana Nuruddin na tare da Sarki, bacci kawai
ke raba su.
Dansa kuwa, wato Hassan Badaruddin, tun da
aka yaye shi, kakansa tsohon Waziri ya ci gaba
da renonsa a gidansa. Lokacin da yaro ya cika
shekara hudu da haihuwa, a lokacin ne kuma
Allah ya yi wa kakansa, mai rikon shi, rasuwa.
Aka yi masa jana'iza irin ta manyan mutane, aka
kai shi makabarta da ke bayan gari aka rufe.
Bayan kwana arba'in aka yi sadaka, Hassan ya
koma gidan ubansa Nuruddin, ya ci gaba da
rayuwarsa.
Lokacin da ya cika shekara biyar da haihuwa,

mahaifinsa ya nemo wani babban Malami yana
koya masa karatu da rubutu. Cikin shekara biyu
ya haddace Alkur'ani mai tsarki, malaminsa ya
shiga koya masa sauran fannoni na ilimi, irinsu
fikihu, hadisai, wakoki da lugga. Hassan
Badaruddin yaro ne mai hazaka da fahimta, duk
abin da aka koya masa sau daya, to ya rike shi
ke nan.
Hassan na kara girma kyawunsa na kara
bayyana, tamkar da wani mawaki yake cewa:
"Yana dada girma yana dada hankali da farin jini,
tamkar farin wata.
Rana tana samun haskenta daga hasken
kundukukinsa.
Hasken farin wata yana cikin kundukukinsa.
Marecen Miriha yana daidaita da kundukukinsa.

Baka na harba kibau daga makyabtansa.
Kyawun tsarin taurari na cikin dare ya bayyana a
gare shi.
Madaidaiciyar tsayuwa da haske sun tabbata a
gare shi.
Jauza'a suna hudowa ta cikin goshinsa.

Ya mallaki kyawo dukkansa, ka ce shi ne ya
tattara kyawun dukkan halittu.
Dukkan baiwa cikakkiya ta taru gare shi."

Malamin nan bai gushe ba yana koyar da
Hassan dukkan fannoni na ilimi a cikin gidan
ubansa har tsawon shekara goma sha biyu, ya
hardace dukkan kome da aka karantar da shi.

Duk tsawon wadannan shekaru Hassan bai taba
fita waje ba, wannan ne ya sa ba kowa ne ya
taba ganin shi ba.
Yayin da ya cika shekara goma sha biyar,
mahaifinsa ya yi nufin fara tafiya da shi zuwa
fada, domin ya fara koyon sha'anin mulki. Ya
tufatar da shi tufafi na alfarma, ya aza shi bisa
wata alfadara, zababbiya daga cikin alfadaransa,

ya tafi da shi zuwa fada. Duk inda suka wuce,
sai mutane su tsaya suna kallon Hassan, suna
shauki da begen kyawunsa, har suka isa fada.

Lokacin da Sarki da sauran fadawa suka ga
Hassan Badaruddin dan Waziri Nuruddin suka
dimauta da ganin kyawu da cikar halitta tasa.
Sarki ya yaba da shi, ya sa masa albarka, ya
umurci Nuruddin ya rika zuwa da shi fada
kullum.

Tun daga wannan rana, sai ya kasance Waziri
Nuruddin yana zuwa da dansa fada kullum, har
yaro ya kai shekara goma sha takwas, ya isa
mutum sosai. Da Nuruddin ya ga dansa ya fara
mallakar hankali, shi kuma ya fara tsufa, sai ya
kira shi ya zaunar da shi, ya ce, "Ya dana, ka
sani cewa duniya gida ce mai karewa, lahira ita
ce gidan tabbata. Ina so in wasice ka da
wasiyya, ka fahimci wadannan abubuwa da
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

1 Comments On HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN
avatar
rabiu-bello

3 months ago

Reply

Nice one

Please Login or Register in order to submit comment