Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yi bankwana da ita,
Ranar rabuwa na zamto ni daya
Na zamo babu aiki babu hali,
Babu aboki sannan babu zuciya
Ya abokina ka tsaya nan tare da ni
Mu yi bankwana ko da sau daya
Yayin da ya gama wannan wak’ar ya fashe da kuka ya fadi sumamme. Tajul Muluk ya dube shi cikin mamaki. Can jimawa sai ya farfado ya shaki iska sannan ya sake rera wannan wak’ar:
Ku rike rumfarku daga rudadde,
Madimauci da hanya ta bace masa
Kaura ta jefe shi ya shiga uku
Bai zamo mai tsira ba daga nahisa
Kun ga idon bakunci ya gaji
Da ganin kewa ba mai iya masa
Ku bar yi wa kurciya dariya idan-
Tana zancenta a al'amarinsa
Kun ga bacin raina ya zamto,
Mai dimauta hankali mai ji nasa
Ya yi kuka mai yawa har sai da ya shide, Tajul Muluk da ya ga haka sai ya dimauta da al'amarinsa. Ya tafi gare shi. Da yaron ya ga dan sarki a kan sa sai ya zabura ya mike tsaye ya sumbaci hannunsa cikin girmamawa. Tajul Muluki ya ce, "me ya sa baka kawo mana kayanka mun yi maka ciniki ba?" Saurayi ya ce, "ya shugabana kayan babu wani abin ku-zo-ku gani da zai kayatar da kai ka saya." Dan sarki ya ce, "babu makawa ka kawo abin da ke tafe da kai na saya, kuma ka ba ni labarinka. Ni na ga alamar kana cikin bak’in ciki ga shi kana yawan kuka. Idan wani ne ya zalunce ka mu kamo shi mu wulkanta shi. Idan bashi ne ya karya ka, ka fada mu biya maka. Ni kam tun lokacin da na gan ka zuciyata ta konu da halin da kake ciki." Tajul Muluk ya yi umarnin a kafa gado, aka kafa masa gado na li'aji mai alfarma, mai kafafun dinari, labulensa na alharini, aka shimfid’a shimfidun alharini, Tajul Muluk ya zauna. Ya umarci saurayi da ya zauna, shi ma ya zauna a kasa. Tajul Muluk ya ce ya dawo sama ya zauna kusa da shi. Sannan ya ce masa, "kawo mana kayanka." Saurayi ya ce, "ya shugabana kada ambaci haka gare ni, kayana ba su da wani amfani gare ka." Tajul Muluk ya ce, "ya zama wajibi ka fada mini abin da nake son ji!"
Ya umarci bayinsa su dauko masa kayan saurayin gabansa duk da ganin hawaye na cigaba da zubo masa bai kula ba. Saurayi ya cigaba da kuka yana ajiyar zuciya yana shessheka. Ya yi kaki ya gyara muryarsa sannan ya rera wannan wak’a:
Yaushe zuciyata za ta warke,
Daga azabtarwa daga gun ka?
Tauraron nan na surayya,
Ya fi kusaci daga gun ka
Wutar bege ta kone min,
Zuciyata domin na rasa ka
A sannu zai zamanto mun,
Yi tsammanin samu daga gun ka
Babu nisan da zai zamo kusa
Matuk’ar na dai rasa ka
Zuciyata babu sauki babu-
Jin kai domin babu ranka
Ba ni da hujjar mance ka,
Don haka jiddan na tuna ka.
Tajul Muluk ya yi al'ajibin wannan wak’a gayar al'ajabi, bai san dalilin wannan abu ba. Ya sa saurayi ya bude kayan ya dauko wata takarda da wani kyalle. Ya ce da shi, "wannan tsumman fa da takardar nan?" Ya ce ya shugabana ba ka da bukatar wannan tsumma." Dan sarki ya ce, ka nuna min dai abin da ke ciki." Saurayi ya ce, "ya shugabana, da ma saboda ita na ki yarda a kawo maka kayana."03 HIKAYAR AZIZA DA AZIZU MAISO DA WANDA AKE SO

dan sarki ya ce, ka nuna min dai abin da ke ciki." Saurayi ya ce, "ya shugabana, da ma saboda ita na ki yarda a kawo maka kayana." Dan sarki ya fusata ya ce, na fada maka babu makawa sai na ga abin da ke ciki.” Saurayi ya hada kai da gwiwa ya soma kuka yana ajiyar zuciya, can jimawa sai ya nisa ya wake wadannan baitoci:
Kada ku zarge ni kansa domin,
Zargi yana kona zuciya matuk’a
Na fada muku gaskiya tuntuni,
Amma kun ki saurarona hakika
Akwai kaunata a cikin tsumma,
Ya zamto Zaharau cikin Falukka
An yi nufin mu zamto tare sai naki,
Ta zamto tana kare ni da duk halaka
Hawayena suna zuba a idanuna,
Na rasa mai shafe min hakika
Ranar rabuwarmu na kasa barci
Domin kunar zuciya ba wandaka
Na kore rabona da hannayena,
Bak’in ciki ya same ni ga halaka
Na rasa mai shayar da ni ruwa,
Na sha a kasko na warke hakika
Yayin da ya gama wak’ar Tajul Muluk ya ce masa, “tun d’azu na lura da halinka, idan ka kalli wannan kyalle sai ka fashe da kuka. Fada min dalilinka game da haka.” Ya yin da saurayi ya ji haka sai ya ce, “ya shugabana, hakika labarina na daga cikin abubuwan mamaki, kuma game da wannan kyalle kuwa akwai ban al’ajibi da ma’abocinsa da wadda ta ba ni shi da wadda ta yi zanen.” Ya warware tsumman sai ga hoton barewa an zana da alharini an mata ado da jan zinari kusa da ita wadansu bareyin ne an zana su da zaren azurfa. A agararta an mata ado da jar zinariya da karrawa uku na zubarjadi rataye a wuyanta.Da Tajul Muluk ya ga wandannan zanen masu kyau sai ya ce, “tsarki ya tabbata ga Allah wanda sanar da mutane abin da ba su sani ba.” Zuciyar Tajul Muluk ta ratayu ga wannan yaro, ya ji yana kaunarsa. Ya kuma ji ya kagara ya ji labarinsa ya ce da shi, “fada min labarinka da kuma labarin wadda ta zana wadannan bareyin.” Saurayi ya ce “ka sani ya shugabana, mahaifina attajiri ne, Allah bai nufe shi da haifar wani da bayan ni ba. Akwai wata yarinya ‘yar baffana ana kiranta Aziza wadda muka tashi tare tun muna kanana. mahaifinta ya rasu, amma kafin ya bar duniya sun yi alkawari da mahaifina cewa za a hada mu aure idan mun girma. To ko a lokacin da na isa munzalin mazaje ita ma ta kai munzalin mace muna tare ba a raba mu ba har lokacin da na ji mahaifiyata na magana da mahaifina suna cewa, “wannan shekara ya kamata a daura auren Azizu da Aziza.” Da suka tsayar da magana sai mahaifina ya tafi domin shirya kayan hidimar aure. Duk da haka muna barcinmu waje daya da sauran al’amura ban san komai ba game da mata, kodayake ita ta fi ni wayo da fahimtar rayuwa kuma tana nuna min kauna.
Mahaifina ya kammala shirye–shirye babu abin da ya rage sai a rubuta takardar aure da shaidu ni kuma na shiga wajen ‘yar baffana na take ta. Ya sa ranar daurin aure ta zamana ranar wata Juma’a bayan an sauko daga masallaci. Ya tashi ya zagaya tsakanin abokansa attajirai da fatake ya sanar musu da wannan aure. Mahaifiyata kuma duk ta gayyaci kawayenta mata da dangi na kusa da na nesa. Da ranar Juma’ar ta zo suka gyara gida saboda baki, aka wanke tukwane da sauran abubuwan gida aka kawata ko’ina. Suka daddaura tufafin alharini ko’ina cikin gidan.
Mahaifina ya tafi ya sayo alewa da sukari da sauran abubuwan jin dadi, yanzu babu abin da ya rage sai kurum a shafa fatiha. Mahaifiyata ta umarce ni da na tafi gidan wanka na yi wanka ta ba ni wasu kaya masu kyau na alfarma ta ce na sanya su bayan na fito daga wanka. Bayan na fito na saka wadannan kayan, na fesa turare mai kamshin gaske wanda ya budade wajen da kamshi sannan na fito na nufi masallaci domin halartar sallar juma’a. A raina ina zucin idan an idar da salla zan je na taho da wani abokina domin ya shaida aurena. Na ce a raina, “bari na hanzarta dai kada lokacin sallah ya wuce.” Na soma hanzari domin na yi sauri na je na dawo kafin lokaci ya k’ure.
Ina tafiya sai na shiga wani lungu da ban tab’a bin sa ba, ina ta kamshi abina, ina tak’ama. Lungun yana da tsayi ga matsatsi na yi tafiya mai nisa ban kai karshensa ba. Na zo wani gida mai dakali sai na shimfid’a hankici na zauna a kai ina hutawa. Gumi yana ta tsattsafo min ga rashin wadatacciyar iska, kaina ya soma ciwo ga zufa na diga har ta soma b’ata min adon da nake tak’ama da shi. Ina so na sa hankici na goge amma babu dama saboda ina zaune a kan sa. Na yi nufin na tube rigata na sha iska kenan ba zato ba nufi wani farin hankici ya fado kan cinya ta. Na dauke shi na ji yana da laushi kwarai ga wani irin kamshi mai dadi yana tashi daga jikinsa, wannan kamshi kadai ya isa ya warkar da cuta. Na daga kaina ina dube – duben ta inda wannan abu ya fado, domin dai na hakikance ba daga sararin samaniya ya sauko ba. Daga kaina ke da wuya muka yi ido hudu da matar da ke da zanen wadannan bareyin' Ta leko ta tagar karfe, idanuna ba su taba ganin kyakkyawa irin ta ba. Harshena kuwa ya yi kadan ya fadi irin tsantsar kyawon da Allah ya ba ta. Yayin da ta ga ina kallon ta sai ta daga yatsunta biyu ta sa a bakinta sannan ta hada yatsanta na tsakiya da manuninta ta dora a kirjinta a tsakanin nonuwanta. Sannan ta maida kanta ta rufe tagar.
Daga rannan wuta ta huru a cikin zuciyata ta rika hauhawa tana cin dukkan tunanina, kallo dayan nan da na yi mata ya jawo min bukatar sake ganinta nan gaba. Sonta ya cika min zuciya na kasa samun sukuni. Ga shi ta yi min wasu alamu da nune – nune da hannunta wanda ban fahimci manufarsu ba, na samu kaina a mai dimaucewa na gigice saboda ban san abin da take nufi ba. Na sake duban tagar a karo na biyu amma na gan ta a rufe, na zauna a nan ina jiran na ga an sake bude kofar har rana ta fadi dare ya yi amma babu amo babu labari. Yayin da na gaji da jira na saddak’ar ba za a sake bud’e tagar ba, sai na tashi daga inda nake na bud’e hankici nan. Wani kamshi mai dadin gaske ya tashi har sai da ya buce kamshin turaren jikina. Wannan kamshin na almiski ne ya sa na ji na cika da farin ciki tamkar a aljanna. Na warware hankicin a hankali sai na ga wata takarda ta fado daga ciki. Na bude wannan takardar ita ma tana fitar da wani kamshin mai dadi. A jikinta na ga an rubuta::
Na aika masa da wasikar soyayya,
Na rubuta da hannuna domin kwarewa
Abokina ya ce me ya sa ki rubutun nan
Mai kyau siriri, karatun bai dacewa?
Sai na ce “ai mai kyau ya fita zakka,
Zurfin soyayya ya sa ni rubutawa
Daga nan na jefa ganina kan hankicin domin kare masa kallon kyawon tsarin da yake da shi, na ga an ja wasu layuka biyu an rubuta da zare da allura:
Kundukukinsa an rubuta layi biyu,
A bisansa ma da rubutun hannun Raihanu
Hasken wata na da ban mamaki kwarai
Jikinsa akwai ni’ima kama da ta almiskinu
A daya bangaren kuma an dinka layi biyu da zaren alharini kamar haka:
‘Yan matansa sun yi rubutu a kundukukinsa da lu’ulu’u,
Shedara biyu a tufa mai kyau da kyawon kallo
Yayin da na gama karanta wadannan wakoki da ke jikin wannan hankici sai wutar bege ta sake ruruwa a zuciyata, na ji na kagauta sosai domin na ga wannan matar. Na dauki wannan kyalle da takardar na tafi gida da su ba tare da sanin yadda zan yin a cimma burina ba, domin ba ni da basirar soyayya kuma ban san ma’anar wadannan alamun da ta yi min ba. Ban san na isa gida ba saboda tunani, dare ya yi nisa kuwa lokacin, na shiga wurin barcinmu na tarar ‘yar baffana tana zaune tana kuka da hawaye. Da ta gan ni nan da nan ta share hawayenta ta mike ta tare ni da murna. Ta cire min falmaran dina sannan ta zaunar da ni tana tambaya ta dalilin bacewa ta. Ta kara da cewa, “duk mutane sun hallara, tun daga sarakuna da manyan mutane da attajirai da sauran jama’ar gari da alkalai da shaidu duka ana ta nemanka za a daura aure a shirya takardar aure ka sa hannu. Amma da suka ga ba ka zo ba lokaci kuma yana kurewa sai suka ci abincin da aka tara suka yi tafiyarsu.” Sannan ta kuma cewa, “mahaifinka ya yi fushi mai yawa, har saboda fushin ma ya yi rantsuwar ba za a daura auren ba sai shekara mai zuwa, saboda yanzu ya kashe kudade masu yawa har da basussuka a yanzu ba shi da halin sake wani bikin.” Ta dube ni sosai ta ce, “kai kuwa ina ka shiga haka ake ta nemanka sai yanzu ka dawo?” Na bude baki na ce mata, “ba na so ki matsa min da tambaya.” Sannan na kwashe labari kaf na fada mata, na dauko hankicin nan da takarda na nuna mata, ta karba ta karanta, sai na ga hawaye na kwararowa daga idanunta. Nan take ta rera wannan wak’ar:
Duk wanda ya ce so a farko lokaci na da sauki,
Ce masa ‘ka yi karya!’ ciwon so wahala ne
Wahalar so da ciwo nai ba sa jin kunya,
Ciwon so yana shiga da wuya ka gane
Kudi mai kyau ba sa wuyar ganewa da na banza,
To ciwon so na da azabtarwa haba mutane
Ciwon so masifa ne a bisa hakikar gaskiya
Yana da wahala ka kamu da shi ka warke
So da kake ganinsa idan zan fada maka,
Shi kan sa ya rabu gida da dama ka gane
Sannan ta tambaye ni “me ta ce maka, kuma wad’anne alamu ta yi maka?” na amsa mata, “ba ta ce da ni kanzil ba, amma ta sa yatsunta a baki kuma ta dora su a kan kirjinta suna kallon kasa. Daga nan sai ta mayar da kanta ta rufe tagar. Daga nan ban sake ganin ta ba. Amma duk da haka zuciyata ta tafi wajen kaunar ta, a nan na zauna har rana ta fadi ina kallon tagar da zummar ko za ta sake lekowa. Da na ga dai babu alamar haka sai na hakura na taho gida. Wannan shi ne labarina, ina rokon ki taimake ni a wannan sha’ani” Da ta ji haka ta daga idanunta ta kalle ni sannan ta ce, “wallahi d’an uwana idan kwayar idanuna kake so zan ciro na ba ka, zan yi duk yadda zan yi ka cimma burinka, ita ma ta cimma burinta domin ita ma tana kaunarka fiye da yadda kai kake son ta ma.”
“Yanzu dai menene ma’anar alamun da ta yi min?” na tambaya a kagauce. Aziza ta ce, “yatsunta da ta sa a baki tana nufin kai kana matsayin mijinta a bisa jikinta, kuma ta k’uduri niyyar saduwa da kai a zimmar miji, amma mayani cewa shi tana nufin sallamawa masoyi abin da yake so. Takarda kuwa tana nufin ta mika kanta gare ka, amma abin da take nufi da dora yatsunta a kan tsakanin nonuwanta kuwa tana nufin bayan kwana biyu ka koma inda ka gan ta domin ku sake haduwa.” ‘Yar baffana ta ce, “wallahi da ina fita waje da sai na sada ku da juna har na lullube ku a mayafi daya ku ji dad’inku. Ka sani cewa ita mai bege ce a gare ka, amintaccen so take maka. Wannan shi ne ma’anar isharorin da ta yi maka.”
Saurayi ya ce, “yayin da na ji haka sai na gode mata bisa wannan fassara. Na tafi dakina na zauna kwana biyu ba na ci, bana sha. Na sa kaina a cinyar ‘yar baffana, ita kuwa tana ba ni magana mai dadi tana shafa min kai tana ce min, “ka saki ranka, ka k’arfafa aniyarka, ka cigaba da hak’uri kana mai dad’ad’a zuciyarka da tunaninka ka ƙarfafa aniyarka, ka cigaba da hak’uri kana mai dad’a ka sa kayanka ka tafi wurinta yanzu don ka nuna mata cika alkawari. Sa'annan sai ta tashi.

ZANCI GABA04 HIKAYAR AZIZA DA AZIZU MAISO DA WANDA AKESO

Sannan sai ta tashi ita da kanta ta sauya mini riga mai kyau, ta kuma turara mini turaren wuta, ni kuma zuciyata ta fara saki kadan-kadan, na fito daga cikin gida na kama hanya ina tafe ina nazarin hanyar har na shigo cikin wannan lungu mai zurfi na zuwa gidan nan mai dakali.
Na zauna kan dakalin nan daidai wurin da na zauna a farkon zuwana, zamana ke da wuya, sai na ga an bude tagar nan, na daga kaina sama na duba sai ga matar nan ta leko kamar yadda ta leko da farko. Sa'ar da muka hada ido fa sai na dimauce na rasa hankalina, jijiyoyin jikina duk suka yi sanyi lakwas na zauna kamar na suma. Don farin ciki har na rasa abin da zan yi. Yayin da hankalina ya komo gare ni sai na sake daga kaina na dube ta ai kuma duk abin sai ya sake rikice mini, na yi nadama da haka, sa'annan na sake dubanta na gan ta da madubi a hannu, da kuma wani hankici ja, ita kuma da ta dube ni sai ta d’aga damatsanta, ta bude su har na hangi abin da da ke cikinsu, hankalina ya girgiza. Sa'annan ta ware yatsunta guda biyar ta buga su a kirjinta, ta sake daga hannuwanta ta dauko wani ruwa da ke ajiye kan tagar nan, ta dauki hankicin nan ja ta saka shi cikin ruwan nan, ta kuma cire shi, ta zuro shi daga wajen wannan tagar, ta yi haka har sau uku sa'annan ta matse shi ta nada a hannunta, sa'annan kuma ta sunkuyar da kanta kasa ta dubo ni, sai ta mayar da kyauren tagar ta rufe, ba ta ce da ni kome ba, ta bar ni a cikin dimuwa da tunani ban san ma'anar duk abubuwan nan da ta nuna mini ba. Na zauna nan wurin ina jiran ta sake lekowa, amma shiru babu ita babu alamar ta, ban tashi daga wannan wurin ba har isha’i ta yi, sa'annan na taso na kamo hanya zuwa gida, ina ta tafiya ni kadai a tsakar dare har na iso gida.
Na sami ‘yar'uwar nan tawa ta hada gumi sharaf sai hawaye ke zuba a idonta tana rera wasu baitoci kamar haka:
Shin me ya sa kake zargina don ina son ka?
Na fada maka dole ne wurina kaunarka
Ni’imarka ta fi ta reshe gamsarwa
Duk da zarginka wajena yaushe ne za ni gan ka?
Na wahalta da wannan tsanani na kauna,
Ya fi takobi aibu idanuwa na Baturka
Wayyo ciwon so ya riga ya kama ni,
Na kwanta ciwurwuta don kaunar ka
Na ji haushin masu zargina kwarai,
Wai don na fadi kaunarka gabanka
Sa'ar da na ji wannan wak’ar tata fa sai baƙin cikina ya dad’u, raina ya dada ‘baci, na rasa ta kamawa, can na baro ba dadi nan kuma na zo na sami ba dadi, sai na fad’i a tsakiyar filin gida ina kuka da mirgina, ‘yar uwar nan tawa ta zabura da hanzari ta zo wurina, ta dauke ni, ta tuɓe mini riga, ta shafe mini fuska da hannun zaninta. Sa'annan ta tambaye ni yadda muka yi da waccan mata wadda na fito daga wurinta. Na kwashe duk abin da ya auku na gaya mata, sai ta ce, "nunin da ta yi maka na tafin hannu da kuma yatsu biyar, tana nufin wai bayan kwana biyar ka je can wajenta, nunin madubi da ta yi maka har ta fito da kanta ta taga ma'anarsa wai ka je ka zauna a rumfar marina za ka ga manzonta ta aiko shi wurinka." Yayin da na ji wannan fassarar ta ‘yar uwar nan tawa sai raina ya tafi, na kagauta matuƙar kagauta. Zuciyata ta dau zafin doki har na ce da ‘yar uwar nan tawa “don Allah ki gaya mini gaskiyar wannan fassara mana, shin ko kuwa kina yi mini ba'a ne. Lalle kam na hadu da wani Bayahude kan hanya a cikin lungun nan da nake bi zuwa gidan wannan mata” Sai na fashe da kuka don tausayin kaina, ‘yar uwan nan tawa ta ce da ni, "haba jinina, tashi ka ƙarfafa zuciyarka mana, ai ka san akwai wanda ciwon so ya auka masa ya yi kuwa haƙuri shekara da shekaru, yana daurewa zafin zuciyarsa ballantana kai mai jiyyar kwana bakwai kadai, a cikin wannan masiba, amma ga shi duk ka murd’e ka yanƙwane, sa'annan kuma duk ka dami kanka da al'amarin da yake galabaitarka. Ina a ce duhu ne kake suka ba gaskiya ba ?”
Bayan ta gaya mini haka sai ta riƙa rarrashina tana ba ni magana, ta je ta kawo mini abinci, na yanki loma daya kawai ita ma na kasa hadiyewa, shi ke nan kuma sai ci da sha suka gagare ni. Na kaurace wa abinci, kamannina suka juya nan take, kyawuna ya dushe, ya jirkita gaba daya, saboda ni tun da nake ban taba fadawa jarrabar so ba sai a wannan lokaci. ‘yar uwata ta rika yi mini tadin maza ma'abuta ciwon so saboda hankalina ya kwanta, a cikin wannan lokacin sai barci yakan rika diba ta kadan, amma idan na farka sai na gan ta tana zaune zugum ta kasa yin barci, saboda ni, sai kuka kawai take rabsawa, hawaye na zuba daga idonta, haka dai muka dinga fama da wannan al'amari har kwana biyar suka cika.

A daidai wannan lokaci ne sai ‘yar uwar nan tawa ta tashi ta d’umama mini ruwa ta dauke ni ta kai bayan daki ta yi mini wanka, ta kuma dauko mini wadansu tufafina masu kyawon gaske, ta bice su da turare, sa'annan ta sanya mini, ta ce tashi ka tafi wurin tauraruwarka, Allah ya biya maka bukatarka, Allah ya sa ka dace da abin nufinka game da wannan mace wadda kake so.
Lokacin da ta kare mini shiri kaf sai na tashi na kama hanya har na kai wurin lungun nan iska na d’ibana saboda rashin ƙarfi. Ranar Asabar ce kuwa, sai na samu rumfar marini amma a kulle, na zauna a wurin har aka yi kiran sallar La'asar. Ina nan zaune wurin har dai rana ta tasar wa faduwa, kai har dai ta fadi aka kira sallar magriba, isha’i ta kama aka yi salla duk dai ina nan zaune har dare ya kama sosai, ni dai ban d’aga ba, amma ban ga wannan matar ba, ban kuma ji motsinta ba, tsoro ya kama ni. Ina zaune ni kadai sai na mike tsaye na tashi, sai ka ce wanda ya sha giya, ina tafe ina tangadi cikina ya murd’e saboda zafin bak’in ciki, haka dai nake tafiya ina fad’uwa kan hanya a cikintsakar dare har na iso gida.
Sa'ar da na iso gida sai na shiga na sami ‘yar uwan nan tawa Azizatu ta rike wani turke wanda aka kafa a jikin katanga ta aza dayan hannunta a kirjinta tana rafsa kuka, tana ruri, sa'an nan kuma tana rera wak’a a cikin murya mai ban tausayi:
Shin mene ne bakin cikin Balarabiya
Wadda jama'arta suka yi mata nisa
Wadda kuma ta ke kuka saboda nisan Hijaz da Randuh.
Idan na hango ayarin matafiya sai ciwon sona ya karu da wutar gararsa,
Ga kuwa hawaye na zuba daga idanuna.
Watau don girman sonsa a guna
Shi har ganina yake na yi masa laifi babba
Wai don me nake sonsa kwarai haka.
Bak’in cikin balarabiya jama’arta sun mata nisa,
Ta kasa bambamce Hijaz da Farisa wanne ke da nisa,
Idan na hango ayarin tafiya sai ciwon ya k’aru rashinsa
Ga hawaye na ta zubar min idanuna saboda k’aunarsa
Ga shi ma ganina na tafiya saboda haushin rashinsa
To wai shin ina dalilin da ya sa nake a haka son sa?
Yayin da ta gama wak’arta sai ta juyo ta dube ni, ta ga ina kuka, sai ta shafe nata hawayen, ta zo ta shafe mini nawa hawayen da hannun zanenta, ta yi mini wani dogon murmushi ta ce da ni, "ya dan'uwana," Allah ya jiyar da kai dad’in abin da ya ba ka. Shin me ya hana ka kwana a wurin wadda kake s ? Me ya hana ku kwana tare, me ya hana ka biyan bukatarka da ita?" Yayin da na ji haka sai na sa kafa na dake ta, na sake zuba mata tafi, na mangare a kirji, ta fadi daga jikin katanga, goshinta ya je ya daki wani turken da ke jikin katangar, ta datse goshinta, jini ya yi ta zuba.

saurayi Azizu ya cigaba da shaida wa Tajul Muluk labarinsa, ya ce sa'ar da na sa kafa na doke kirjinta ta fad’i a gindin katanga har ta buge goshinta a kan turke

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

7 Comments On HIKAYAR AZIZU DA AZIZA
avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Telecharger

avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Telecharger

avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Download

avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Download

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to hamadou-8

idan ka gagara downloading ne zaka iya karantawa anan kyauta ai

avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Hamadou saadia

avatar
mustapha-6-6

2 months ago

Reply

Ai kamar bai kare ba

Please Login or Register in order to submit comment