Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan mata. Na fashe da kuka ta ce, "ya Azizu d’an uwana. hakika raina a b’ace yake har ba zan iya yin wani tunani ba a halin yanzu amma na shawarce ka in dare yayi ka tafi wurin, kada ka yarda ka yi barci, za ka sami abin da kake so, wannan ita ce shawarar da nake son ka d’auka, wassalam."
Sa'ar da na ji wannan shawara tata sai na ce in Allah ya so ba zan yarda na sake ba har in yi barci. ‘Yar uwan nan tawa ta tashi ta je ta kawo mini abinci ta ce na ci har na k’oshi yadda ba zan yi sha'awar cin wani abinci ba, na zauna ina jiran lokacin tafiya ta yi. Lokacin da dare ya yi ‘yar uwata ta tashi ta d’auko mini wad’ansu tufafina masu kyau, ta saka mini, sa'annan ta yi mini magiyar cewa idan na je can duk lokacin da zan dawo na rera baitin wak’ar nan nata na farko, ta sake jan kunnena a kan kada in yarda in yi barci a can na jira har lokacin zuwan matar nan ya yi yadda za ta zo ta same ni a farke.
Bayan na kammala dukkan shirina sai na kamo hanya da hanzari har na iso wurin da gonar nan take, na shiga ciki na sami shirin wurin kamar yadda na saba samunsa tun farko, na sami wurin zama na hard’e, na yi shiru domin kwarjinina a matsayin jarumi. Ina cewa lalle ne yau na yi nasara kan wannan mata. Na zauna nan ni kadai ina koda kaina a cikin iska har dare ya yi tsari sai na girgiza kaina, na bude idanuna don kada barci ya kama ni..06 HIKAYAR AZIZA DA AZIZU MAISO DA WANDA AKESO

Saurayi yaci gaba da fada wa Tajul Muluk labarinsa, ya ce, sai na sami wurin zama na zauna, ina cika, ina batsewa, na shaki iska har kaina ya kumbura ina hura hanci kamar gwauron bajimi. Duk lokacin da na ji barci zai kama ni sai na girgiza kaina, ina nan cikin wannan hali na jaruntaka sai k’anshin abinci iska ta soma bugo shi a wajena, yunwa kuma ta motso mini gaba d’aya, na tuna cewar "sa raina ga abinci shi ke kawo jin yunwa." Saboda haka sai na daure, na kawar da kaina a wani gefe daban. Amma duk da haka na kasa hak’uri, na nufi wajen da abincin nan yake, na je na tsuguna a kan abinci, na yi zugum da kaina, na tank’ware gefe guda ina shawara da zuciyata, yunwa kuma sai matsa sallama take, da dai na ga yunwar ta daina sallama har duka na take, na kuwa ga alamar ba za ta bar ni ba, za ta yi min dukan falan d’aya, da na ga haka sai na cire mayanin da ke yafe a kwanon abinci, sa'annan na bud’e murfin kwanon da abinci ke ciki, na yanki loma guda na ci, na kuma ciri yankan nama d’aya na saka baki, sa'annan na juya a wajen da giya take da nufin zan wanke idona da moda guda. Na sha na farko, sai na ji marmarin na kara, na sake cika mak’ogwarona da moda ta biyu, na k’ara ta uku har dai zuwa na ashirin na ji ta kama mini daidai cikina, sai na zarce na shiga aikina daidai, na sha har na soma tumbatsa, sa'annan na juya kan mai sanyi ita ma na dibi wadansu ‘yan kananan kofofi sai iska ta bugo ni na tuntsure, daga kan kujera kamar matacce, daga nan kuma sai barci ya d’ebi abinsa, na yi ta sharar barci, ban farka ba sai bayan da rana ta fito har ta karya zuwa muhtarin la'asar.
Yayin da na farka sai na ga ashe har an fitar da ni daga cikin gonar ne, an jefar da ni can gefen hanya ga ungulai kewaye da ni suna jiran tsammani. Bayan da na farka na ga wurin da nake na duba kusa gare ni, na ga wata zandamemiyar wuka mai kaifin gaske ta fad’o daga ruwan cikina, a can gefen kuma ga tanderu na bakin karfe. Yayin da na ga haka fa sai hankalina ya tashi matuk’a, na rasa inda zan saka kaina, na d’ebi wadannan munanan abubuwa na kamo hanya zuwa gida. Da na zo gida sai na sami ‘yar uwata tana cike da kewar ganina. Da shiga ta cikin gidan sai na yanke jiki na fadi k’asa ina birgima, na watsar da wuk’a da tanderu a gabanta, nan take na suma, hankalin ‘yar uwan nan tawa ya yi mummunan tashi, ta yi shiru tana tunanin abin da ya faru gare ni, sa'ar da na farfad’o sai na gaya mata duk abin da ya faru, na shaida mata cewan na kasa samun biyan buk’atata game da wannan mata. Da taji haka ranta ya b’aci ainun, ta ce min, "babu shakka, ni kam na gaji da yi maka nasiha game da al'amarin matar nan!" Saurayi ya ce sai na ce da ita, '"ya yar uwata, ina son ki gaya mini, ma'anar wuk’ar nan da tanderu." Sai ta ce da ni, ma'anar tanderun nan na bak’in k’arfe da ta dora kan ruwan cikinka, watau wai ta rantse da Ubangijin talikai Allah Madaukakin Sarki, da kuma idon nan nata na dama idan har ka yarda ka sake komawa wurinta, sa'annan ka yi barci, to, lalle kuwa za ta yanka ka, da wannan wuk’ar, kamar yadda ake yanka rago, ta yi alk’awarin za ta yi maka mummunan kisa. Wannan shi ne fassarar abin da take nufi game da kai, saboda haka, dan uwana ka sani dai ni kam ina ji maka tsoro game da sharrin makircin wannan mata, babu shakka a halin yanzu, zuciyata a b’ace take game da kai, don haka ina jin ba zan iya gaya maka wata magana ba, amma idan ka ji ka amince da cewar idan ka koma wurin matar nan ba za ka yi barci ba, to, shi kenan sai ka shirya ka koma. Ni dai na rok’e ka don Allah ka fita hanyar matar nan, idan kuwa ba ka fita hanyarta ba, to, kome ya faru gare ka ba ka da kaico, idan har ka yi sake ka koma wurinta, ka tabbata idan har ka kuskura ka yi barci lalle za ta yanka ka.
Ni dai ban ji ba, sai na ci gaba da neman taimako daga wurin yar uwan nan tawa har dai ta ce, “to, na yarda zan taimake ka amma fa sai ka tabbatar min cewan za ka yarda da dukkan abin da na gaya maka. Nan da nan a cikin marairaicewa na yarda, na ce mata zan yarda da dukkan abin da ta gaya mini, sa'annan ta yi mini alkawarin za ta gaya mini kome da kome a lokacin da zan tafi, in yamma ta yi. Can kuma sai ciwon so ya motso mata ta rungume ni a k’irjinta, ta ciccib’e ni ta d’ora ni kan shimfid’a ta shiga yi mini tausa har barci ya d’auke ni.
Yayin da nake sharar barcina sai ta dauko mafici ta shiga yi mini fifita a fuska da sauran sassan jikina har yamma ta yi sa'annan ta tayar da ni daga barci. Sa'ar da na farka sai na ganta a zaune daidai kaina da mafici a hannu tana ta rafsar kuka, hawaye na zuba a idonta har zanenta ya jik’e don sharar hawaye da take yi da shi. Lokacin da ta ga na farka daga barcin sai ta tashi ta kawo mini abinci, ta ce na ci amma ni kuma sai na k’i cin abincin. Da ta ga haka sai ta ce lalle ban yi zaton za ka ji maganata ba ke nan, ta dai shiga rarrashina a kan in yarda in ci abincin nan nikuma na k’i. Da ta ga lalle ban da nufin cin abincin sai ta rik’a gutsurawa tana saka mini a baki saboda ta fahimci cewar ina bukatar cin abincin, amma rashin sabo da shi ne ya hana ni ci, da haka dai na ci abincin har na k’oshi. Sa'annan ta d’auko mini tataccen ruwan inabi ta ba ni na sha. Da na gama ta zo ta wanke mini hannuna, ta goge mini hannaye da mayani, ta kawo turaren miski da wardu ta shafe mini hannuwana da jikina sa'annan lokacin da dare ya yi ta shiga yi mini gargad’in cewan kada in yarda in yi barci, ta shaida mini cewan matar nan ba za ta zo wurin da zan jira ta ba sai kusan k’arshen dare, ta kuma yi mini kyakkyawar addu'a ta ce, "Allah ya kiyaye ka, Allah ya ba ka sa'a ya kuma dawo da kai lafiya". Daga k’arshe kuma ta ce, “ina fatar dai ba za ka manta da maganar biya mata baitin wak’ar nan idan kun sadu ba, amma kuma ta sake nanata mini cewan kada in biya wannan baitin wak’ar sai bayan mun gama za mu rabu, na komo gida.
Yayin da ta ga na kama hanya sai ta fashe da kuka har ni kaina a rannan sai da hankalina ya tashi game da kukan ‘yar uwan nan tawa. Sa'annan na ce da ita shin wace wasiyya ce taki, da kike bukatar gaya mini, ta ce da ni, ba ta da wata wasiyya sai dai baitin wak’ar nan da ta ce in rera wa matar nan a lokacin da za mu rabu.Shi kenan sai na shirya na fito gida na kama hanya cikin kuzari da jin k’arfin jiki da na hali har na iso inda gonar nan ta ke. Na shiga cikin gonar, na sami wurin an shirya shi sosai, babu abin da ya ragu daga shirin farko sai ma abin da ya k’aru na daga kayan kyalli da na faranta ciki.
Da zuwana sai na kama wurin zamana na zauna ina cike da farin ciki da fara'a, na shiga nishadi da zuciyata, na k’i yin barci kuma bisa sa'a a rannan babu maganar yunwa, balle barci. Na zauna a nan wurin idona biyu har wajen asubahin. Da na ga har gari zai waye ban yi barci ba babu kuma alamarsa ga idona, sai kuma na shiga damuwa saboda ni duk na rud’e da murna saboda wannan bajinta da na yi, sai na ga kuma duk daren a rannan ya yi mini tsawo saboda d’oki, a rannan daren nan ya yi tsawon shekara guda a wurina, na daure dai na k’i yin barci, har zakaru suka soma kuka, na cika da jin dadin wannan bajintar tawa.
Babu jimawa duk sha'anin ya juya, abubuwa suka soma cakudewa, yunwa ta yi wo mini sallama baki daya, hankalina ya fara kad’uwa, na rasa abin da zan yi sai na tashi na nufi gefen da abinci yake, da zuwana kamar dabba sai na bude abinci, na zauna na ci, na k’oshi. Nan da nan na ji kaina ya yi nauyi ana yi mini motsi a cikin kai ta ko’ina, sai na kwanta a kishingid’e zan yi barci. Allahu mai Girma, na kishingida kenan sai na ji motsin yarinya tana zuwa daga nesa sai na mik’e tsaye na je na wanke hannuna, na goge bakina, sa'annan na kintsa jikina daidai na zauna.
Bayan duk na k’are wannan sai ga yarinya ta iso tare da kuyangi su goma suna biye a bayanta. Sa'ar da suka iso wurin sai suka saka ta tsakiyarsu. Lahaula Wala Kuwwata, tsarki ya tabbata ga wanda ya halicci kwad’o, lokacin da na juya na dubi matar nan, sai na ga wurin ya yi haske, yarinyar tana k’yalli sai ka ce wata a tsakanin taurari, kayan tufafin da ke jikinta na wani koren had’alashi ne, wanda aka yi wa baza da zinari ja. Kyawunta ya kasance kamar yadda wani mawak’i ya yi mata wak’a yana cewa:
Wannan mata tana yanga ga masoyanta,
Musamman idan ta sa kaya koraye
Na tambaye ta ‘yaya sunanki gimbiya’,
Ta amsa ‘ni ce mai k’ona zuciyar mazaje’
Na ce ‘to ni dai kam ina kaunar ki’
Ta ce ‘to ka fad’a wa dutse kai waye’
Sai na ce idan zuciyarki tamkar dutse take,
To Allahu ya fitar da ruwa daga dutse.
Yayin da ta gan ni a zaune sai ta yi dariya, ta ce, “yaya aka yi ka farka daga barci? Tunda na ga ba ka yi barci ba a wannan karo, to lalle na tabbata kana so na, domin kuwa rashin barci shi ne halin mai ciwon so.” Ta juya wurin kuyangi ta yi musu alama da idonta, ni kuma ina fake da ita, sai na ga kamar walk’iya ce aka yi saboda hasken idon nan nata da ta kada. Sa'ar da ta k’ifta musu ido sai na ga sun juya sun tafi nasu wajen daban. Yayin da suka tafi sai na ga ta zo wurina, ta kama ni ta rungume ni a k’irjinta ta kama leb’en saman bakina ta tsotsa, ni kuma na tsotsi na k’asan. Na rik’e duwawunta na matsa su, na shafa, na shafa, na yi mata cakulkuli sai dukanmu muka fad’i k’asa, sumammu. Yayin da muka farfad’o sai na ga ta sassauta daurin kamfanta zuwa daidai k’wauri muka fad’i muna runguma da shafa da sumba muna magana da juna a hankali, k’afafunmu da hard’ewa da juna muna juye – juye. Na hau bisa ruwan cikinta na yi nink’aya, na yi sukuwa na kai fage, na sake juyowa, sa’annan muka kawo numfashi baki d’aya, gab'ob'inmu suka saki. Kowannenmu ya cika da farin ciki da jin dad’i. Na samu shiga wuri mafi daraja a wurinta. Wannan dare ba zan iya kwatanta shi da kowane dare ba game da farin ciki, kamar yadda wani mawak’i ke cewa:
Dare daya tak ya fi dukkanin darare,
Ni’ima da jin dadi a dukkan rayuwata
Lokacin da na sha kofi na girma sassanya
Na zam tare da yari da awarwaro b’arya ta
Nan muka kwanta rungume da juna muka yi barci, yayin da gari ya waye na tashi zan tafo gida, sai matar nan ta kama ni ta ce, "tsaya na gaya maka wata magana."

Saurayi ya ce da Tajul Muluk, yayin da na tashi zan tafo gida sai ta ce da ni in tsaya ta fada min wata magana ta wasiyya, sai na tsaya cif da k’afafuna, sa'annan sai ta kwance wani mayani ta fito da wannan k’yalle ta shimfid’a shi a gabana, na duba na ga wadannan surori na hoton barewa kamar yadda yake d’in nan, mamaki ya kama ni matuk’a, har na yi sha'awarsa, na karb’e shi daga wurinta. Muka yi alkawari da ni da ita, kowane dare zan tafi wurinta in same ta a cikin gonar nan da muka hadu tun farko. Na kama hanya na taho gida ina cike da farin ciki, don tsananin murna da farin ciki har na manta ban rera wak’ar nan da ‘yar uwata ta ce min na yi ba. Yayin da ta ba ni mayanin nan mai zanen bareyi ta ce min, “ka adana wannan da kyau, wata ‘yar uwata ce take yin su.” Na tambaye ta yaya sunanta? Ta ce min sunanta Nurul Huda.

TALLA
Zaku iya karanta wasu hikayoyinmu na daban a zaurenmu na sirri akan kudi 200 kacal zamu baku labarai da dama acikin kwanaki talatin akan 200 kawai' sannan kuna iya samun karashen HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN, DA HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI'.07 HIKAYAR AZIZA DA AZIZU MAISO DA WANDA AKESO

Nace mata yaya sunanta ita mai yin zanen tace'' nurul huda,
Yayin da na shiga gida wurin ‘yar uwata sai na same ta a kwance, da ta ji zuwana sai ta taso hawaye na zuba a idonta ta zo wurina ta kama ni ta rungume a k’irjinta, ta tambaye ni ta ce, "shin ko ka yi mini abin da na gaya maka na game da baitin wak’ar nan da na ba ka na ce ka rera wa wannan mata idan ka sami biyan bukatarka game da ita a lokacin da za ku rabu ?" Na ce da ita, "ai kuwa na manta, babu kuma abin da ya sa sai rudewar da na yi game da surorin hotunan wannan barewa na jikin wannan kyallen." Na jefa mata k’yallen a gabanta, sai ta zabura, ba ta sami ikon yin hak’uri ba, hawaye suka rik’a zubowa daga idanunta, har ta yi wak’a tana cewa:
Haba mai neman rabo saurara,
Kada yawan runguma ya rud’e ka,
Dakata dai ka k’ara hak’uri,
Da sannu za ka cimma burinka
Lokacin da ta gama wak’arta sai ta ce da ni, 'dan'uwana. Ina son ka ba ni wannan k’yalle. Ban yi wata wata ba sai na d’auka na ba ta. Ta karb’a ta shimfid’a ta ga abin da ke ciki. Sa'ar da lokacin komawata wurin waccan mata ya yi, sai ‘yar baffana ta ce da ni, "kada ka damu, je ka abin ka cikin kwanciyar hankali da jin dadi, amma idan za ku rabu ka wak’e mata baitin wak’ar nan wanda na gaya maka tun farko kada ka yarda ka mance shi."
Na tashi na kama hanya bayan ta sake biya mini baitin wak’ar ina tafe kurum, na kamo hanyar gona har na iso gun gonar na shiga ciki na sami wurin zamana an shirya shi tsaf, a gefe daya kuma ga yarinya har ta riga ni zuwa, ta ma dad’e tana jira na, da gani na sai ta tashi ta kamo ni ta rungume ni sa'annan bayan ta numfasa sai ta zaunar da ni a kan cinyarta, bayan mun d’an huta kadan muka shiga cin abinci, ina zaune a kan cinyarta muka ci, muka sha, muka yi wasa, sa'annan muka biya buk’atarmu kamar yadda muka yi tun farko.
Da zan tafi sai na wak’e mata baitin wakar nan na ‘yar uwata wanda ta koya mini ina cewa:
Ya ku masoya na gama ku da Allah ga tambaya,
Shin menene abin yi da maganin ciwon so?
Da ta ji haka sai ga hawayen na zubowa daga idanunta. Lokacin da take kukan nan sai ta rera mini wannan baitin:
Matuk’ar yana bukatar maganin ciwon so
Ya zam mai hak’uri da boye so da dauriya
A lokacin da take rera wak’ar na yi k’ok’arin haddacewa, na yi farin ciki da ganin bukatar ‘yar uwata ma ta biya, na cika mata burinta kamar yadda nata nema daga gare ni. Da na isa gida na tarar da ‘yar uwata tana kwance, a gefe d’aya kuma ga uwata zaune kusa da ita a daidai kanta tana kuka saboda ganin irin halin da yarinyar take ciki. Da shiga ta cikin dakin sai uwata ta yi mini tsawa ta ce, "amma kai dai baka da kirki!" Yaya za ka fita ka bar ‘yar uwarka kwance ba ta da lafiya sa'annan kuma bayan ka dawo ba za ka tambayi yadda ta k’ara ji ba?"
Lokacin da ‘yar uwata ta ji fad’an da uwata take yi mini, sai ta d’aga kanta ta dube ni, ta ce, "ya Azizu, ko ka wak’e wa budurwarka baitin wak’ata ? " Sai na ce mata, “eh na wak’e mata shi.” Sa'ar da ta ji haka sai ta fashe da kuka ta sake wak’e min wad’annan baitoci:
Hak’uri tuni ya kare babu abin yi,
Firgitar zuciya da ciwo ya yi tsanani
Sa'annan ta ce na fad’a mata abin da waccan matar ta fada bayan na rera mata baitin wak’arta. Na rera mata, da ta ji sai ta b’arke da kuka, ta yi kuka mai tsanani. Sa'an nan ta ce mini idan na je wurin budurwar nan tawa kamar yadda na saba in wak’e mata wannan baitin, na ce mata, “na ji na yarda.” Da safiya ta yi lokacin tafiya ya yi na fito gida, na kama hanya har cikin gonar da muke haduwa da wannan mata. Muka shiga sha’anin holewa da jin dadin juna fiye da yadda harshe zai bayyana. Yayin da na tashi zan tafi bayan wayewar gari sai na rera mata baitin wak’ar da ‘yar uwata ta sake ba ni .
Yayin da matar nan ta ji wannan baitin wak’ar sai hawaye kuma suka zubo mata a k’irjinta. Ita ma sai ta wak’e wani baiti guda ta ce:
Matuk’ar hak’uri da ciwon so ya gagara,
Babu shakka dai mutuwa ce magani.
Na sake haddace baitin wak’ar na kamo hanya sai gida, da shiga ta cikin gidan sai na sami yarinya ‘yar uwata tana kwance, ta yi kuka har ta some, ga kuma uwata a zaune kusa da kanta tana kallon halin da yarinya take ciki. Yayin da ta ji motsin shigowa ta sai ta bud’e idanunta ta ce da ni, "Azizu, yaya ka karanta mata wak’ata?” Na ce mata “eh ban manta ba na karanta mata, amma fa na ga ta fashe da kuka kuma ta ce na fada miki cewa, ‘Matuk’ar hak’uri da ciwon so ya gagara, babu shakka dai mutuwa ce magani.” Da ta ji abin da baitin wak’ar ya k’unsa sai ta fad’i kan gado a some, jim kadan sai ta farfad’o ta sake ba ni wani baiti guda, ta ce,
Mun ji mun yarda, mutuwar ce za mu yi,
Mun nemi aminci da saduwa da wanda muke so.
Bayan da dare ya yi sai na tashi na kamo hanyar gona kamar yadda na saba, na sami yarinya tana zaune tana jira na a cikin gonar, muka zauna muka ci abinci, muka sha abin sha, sa'annan muka shiga yin masha'a har barci ya kwashe mu, ba mu farka ba sai bayan da gari ya waye tangaram. Na taso zan komo gida sai na rera mata baitin wak’ar da ‘yar uwan nan tawa ta ba ni, yayin da ita kuma ta ji wannan baitin wak’ar sai ta fashe da kuka. Ta yi kururuwa, ta kid’ima, ta firgita, ta cefirgita, ta ce wallahi mai wannan wak’a ta riga mutu, ta sake fashewa da kuka ta ce, "masoyina, yaya kusancinka da wannan mai wak’ar yake ?" Na ce mata, ‘yar baffana ce. Ta ce, “k’arya kake, wallahi da ‘yar baffanka ce da kai ma babu shakka ka so ta kamar yadda ita ma take son ka, kai ne ka kashe ta, Allah kuwa ya kashe ka kamar yadda ka kashe ta. Wallahi da ka gaya mini kana da ‘yar uwa wadda ke mutuwar son ka, da ban yarda ka yi kusa da ni ba!
Na ce mata ai ‘yar uwata, ce kuma ita ce ke fassara mini dukkan isharorin da kike yi mini, da yadda zan yi da ke duka, ba domin ita ba kuwa, da ban sami saduwa da ke ba. Ita ce ta shirya mini yadda zan yi na sadu da ke, sa'annan ta ce da ni, ‘yar uwan nan taka kuwa har ta riga ta san ni ? Na ce mata, "na’am, ta sanki mana. Bayan ta numfasa sai ta ce, "Allah ya tab’ar da k’uruciyarka kamar yadda ka tab’ar da tata k’urciyar!"
Bayan ta yi mini wannan mummunar addu'a, sai ta buga min tsawa ta ce da ni, “maza je ka ka kula da ita!”Na kama hanya ina tafiya hankalina ba ya tare da ni, har na kai gida. Yayin da na isa gida sai na sami gida ya cika da kururuwa da hargowa. Na shiga na tambayi abin da ya faru a gidan aka ce mini Azizatu ce ta mutu, an tsinci gawar ta a bayan kyaure. Na fad’a cikin gida a firgice, uwata ta dube ni ta ce, "yau ka cimma burinka, alhakin wannan yarinya duk ya hau kanka, Allah ba zai yafe maka alhakin wannan yarinya ba, sai ya saka mata a kan ka.”Allah ba zai yafe maka alhakin wannan yarinya ba, sai ya saka mata a kanka.” Ubana ya zo da sauran jama’a aka had’a ta, muka dauki gawar yarinya, muka je muka rufe. Sa'annan muka dawo gida muna karb’ar gaisuwa ga mutanen da suka zo yi mana ta'aziyya har kwana uku.
Bayan nan sai uwata ta zo ta ce min, “fada min abin da ka aikata mata ya sa ta ciwon zuciya. Ka sani ya d’ana na tambaye ta ya fi a k’irga amma ta k’i fada min dalilin ciwonta. Yanzu dai Allah na kallon ka kuma ya san abin da ka aikata mata ta mutu.” Na ce wa uwata, “Ni dai ban mata komai ba.” Ta girgiza kai cikin takaici ta ce, “Allah zai mata sakayya a kanka, kodayake ba ta fada min komai ba, ta kiyaye sirrinta a wajenta har ta mutu, amma na tabbata ciwon son ka ne ya kashe ta. A lokacin da mutuwar ta karato mata ina wurinta ta bude idanunta ta ce min, “ya matar kawuna,

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

7 Comments On HIKAYAR AZIZU DA AZIZA
avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Telecharger

avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Telecharger

avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Download

avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Download

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to hamadou-8

idan ka gagara downloading ne zaka iya karantawa anan kyauta ai

avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Hamadou saadia

avatar
mustapha-6-6

2 months ago

Reply

Ai kamar bai kare ba

Please Login or Register in order to submit comment