Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jini ya soma zuba sai hankalina ya tashi matuk’a, amma ita sai ta yi shiru ba ta ce kome ba, sai ta yagi haɓar zanenta ta daure wurin mikin, ta shafe jinin da ya zuba ga jikinta, ta gyara jikinta, ta goge fuskarta sarai, ta gyara shimfid’ar da take barci. Ta sake shirya wuri ya zama kamar dad’ai babu abin da ya faru a wurin, sa'annan ta rarrafo ta zo wurina tana murmushi, ta shiga ba ni magana, tana rarrashina, tana kuma shafa ta, ta ce, "haba d’an uwana, ai wallahi ba izgili ne na yi maka ba, kuma ba gatse ne na yi maka ba, ko kusa kada ka zaci haka. Ina son ka huce, ka ba ni labarin abin da ya gudana tsakaninka da waccan masoyiyar taka."
Nan take na kwashe duk abin da ya gudana na gaya mata, sa'annan rashin hak’uri ya same ni na fashe da kuka. ‘yar uwan nan tawa ta ce, na yi farin ciki da yi maka albishir cewan bukatarka dai za ta biya a tare da wannan mata, saboda wannan shi ne alamar yarda a tsakaninku, watau dalilin da ya sa ba ta aiko maka da sako ba, tana auna ka ne, tana son ta san irin tsawon hak’urinka, har kuma ta gane matsayin son ka da ita. Yanzu na shawarce ka da ka sake komawa gobe a can wurin haduwarku na farko, saboda ka ga abin da za ta sake nuna maka. Duk wannan magana da take ba ni sai hushi ke kara hawa mini, raina ya ɓaci ƙwarai. Ta tashi ta kawo mini abinci, na sa ƙafa na haure abincin, ya warwatse ko’ina, sai ta ce, "kaico, lalle duk wanda ya hadu da ciwon so mahaukaci ne, shi da mahaukaci daidai suke."
Yayin da ta ga haka ita ma sai nata hankalin ya tashi, hawaye suka zubo daga idonta ta ce, "wallahi dan'uwana, ni ban ga laifinka ba, wannan shi ne alamar soyayya." Sa'annan sai ta tashi, ta kwashe abincin nan da ya watse a ƙasa, ta share wuri, ta debi kwanukan abincin ta wanke, ta sake komowa wurina tana rarrashina, tana ba ni magana, amma duk a banza ni sai roƙon Allah nake ya wayi gari don na tashi na tafi wurin aminiyata. Kashegari sai na tashi a firgice ina cikin mayen so tsundum, na kama hanya da hanzari, har ma nakan had’a da gudu, har na iso ga wannan lungun, na shiga na je kan dakalin nan na zauna.zauna. Zamana ke da wuya sai na ga an bud’e tagar nan, ta fito da kanta, tana murmushin dariya, ta mayar da kanta, jim kad’an kuma ta sake leƙowa na biyu da madubi da wata jaka, sa'annan kuma da wani kasko wanda aka shuka hatsi a ciki. Hatsin ya yi tsiro, kore shar, d’ayan hannun kuma ga fitila ta riƙe.
Abin da ta soma yi shi ne ta d’auko madubin nan ta sa shi a cikin jakar nan ta d’aure, ta jefa jakar cikin gida, sa'annan ta taro gashin kanta ya koma a gaban fuskarta har ya rufe fuskar, ta sake d’aukar fitilar nan ta saka a cikin shuka. Nan da nan kamar ƙiftawar ido sai shukar ta kama wuta ta ƙone ƙurmus, bayan da ta ƙare wadannan isharori sai ta mayar da tagar ta rufe. Ganin haka fa ni ko sai zuciyata ta tsinke, sai zuciyata ke bugawa na shiga tunani, na kasa gane abin da ta ke nufi da wad’annan isharorin, na tashi na nufo gida raina ɓace har na shiga na sami ‘yar uwata tana tsaye a jikin katanga ta manna fuskarta a jikin katangar.
Yayin da na ga haka kuma sai zuciyata ta dad’a tsinkewa, cikina ya d’uri ruwa na rasa manufa, ita kuwa wannan ‘yar uwar tawa kome na yi mata ba ta kula ni, saboda so na da take yi, amma ni ban damu ba hankalina gaba d’aya ya koma wurin waccan mata, ita ma ‘yar uwan nan tawa ta dauki hak’uri ta d’ora wa zuciyarta, ba ta damu da duk wad’annan abubuwan da nake mata ba. Sa'ar da na dube ta na ga ta d’aure fuskarta wuri biyu, sai raina ya sake b’aci, da na duba sai na ga wuri d’aya don rauni ne ta daure, dayan kuma saboda zuban hawayenta har wurin ya yi gurbi. Lokacin da ta gan ni sai ta rera wad’annan baitoci:
Kai me tafiya da zuciyata na amince,
Duk inda kake Allahu ya amince maka.
Na sani Allahu yana nan tare da kai,
Masoyina ni kam wallahi ina kaunarka.
Ni kam bak’in ciki sai karuwa yake yi,
Gare ni domin na kusan na rasa ka
Ya mai ceton jama’a daga ciwuta,
Ga ni gare ka na zo don ludufinka
Hawayena suna ta zuba a idaniyata
Kaico idan na san kana wurin zan neme ka
Yayin da ta gama wannan wak’a tata sai ta dubo ni, sa'annan ta shafe hawayenta, ta zo wurina amma sai ta kasa yi mini magana, ta yi shiru har wani lokaci, sa'annan ta ce, '"d’an uwana," gaya mini abin da kuka yi da yarinyarka. Na shaida mata, sa'annan ta ce da ni, "ka dauki hak’uri, lokacin saduwarku da ita ya kusanta, lalle abin da kake buk’ata game da ita, za ka samu. Watau madubi wanda ta saka a cikin jaka, tana nufin wai ka yi hak’uri har rana ta fad’i, sakin gashin kanta da ta yi har ya rufe fuskarta, tana nufin wai idan dare ya yi duhu ya kama, har ya rufe hasken rana, tana son ka je can wurinta. Dalilin shuka ta cikin kaskon kuwa, wai ka shiga cikin gona wadda ke nan kusa da lungun. Nufinta da fitila kuwa wai ka je can gonar ka shiga cikinta za ka sami fitila mai haske, idan ka sami wannan fitilar ka nufi wurin, ka je ka zauna, za ka gan ta ta zo, har ma ta k’ara da cewan wai sonka da take yi ya kusa halaka ta.”
Sa'ar da na ji haka sai hankali ya kwanta sa'annan na ce da ‘yar uwar nan tawa, sau da yawa fa kina kwatanta mini cewar in hak’ura in koma, alhalin kuwa ko na tafi sai in dawo hannu wofi, ba abin da yake faruwa daga cikin buk’atata. Ni dai ban ga wata ma'ana ba a cikin wannan fassarar taki ba. Sai ‘yar uwan nan tawa ta yi dariya, ta ce da ni, "hak’urinka na wannan yini kad’ai kafin fad’uwar rana, in dai har dare ya yi, za ka sadu da abin da kake buk’ata, wannan magana tawa gaskiya ce, wadda ba ta buk’atar wata rantsuwa. Can kuma da ta nisa sai ta rera wata wak’a:
Kwanaki na shigewa dare ya yi,
Dakunan masu bak’in ciki bai waye ba
Duk abin da samunsa ya zam wahala.
To sauk’in lamarin na nan a gaba
Lokacin da ta k’are wak’a sai ta zo wurina ta soma rarrashina, tana ba ni magana, amma ba ta sami damar kawo mini abinci ba don gudun zuciyata, sai ta tub’e mini rigata, sa'annan tace mini, "zo ka zauna nan d’an uwana saboda ina son in yi maka wata hira wadda za ta kwantar maka da hankali, kafin nan zuwa fad’uwar rana, in Allah ya so dare ba zai yi ba sai kana tare da wadda kake so." Ni kuwa ko kula ta ban yi ba. Ban ma san abin da take yi ba, ko wajenta ban juya ba, balle har na san tana wurin, ni a lokacin zuwan dare kad’ai na sa a zuciyata, sai fata nake Allah Ubangiji ya gaggauta zuwan daren nan a cikin zuciyata.
Yayin da dare ya yi sai ‘yar uwata ta fashe da kuka, ta dauko k’wayar miski guda na asalin, ta ce da ni, hak’ura ka sa wannan k’wayar a bakinka, idan ka sadu da wadda kake mutuwar so sa'ar da ka biya buk’atarka da ita sai ka biya mata wannan baiti ka ce, "ya jama'ar masu ciwon so, ku ba ni labarin yadda in son mutum ya same ka za ka yi." Sa'an nan ta ce idan na je na sami wannan matar kuma buk’atata ta biya game da ita, na wak’a mata wannan baitin, amma kuma sai ta rantsar da ni cewan kada in yarda in yi wannan baitin sai bayan mun k’are dukan sha'aninmu, watau yayin da zan fito zuwa gida daga wurinta.
Yayin da ta k’are yi mini wannan bayanin, sai na ce da ita, “na ji, na kuma yarda” Sa'annan sai na fito daga cikin gida kamar lokacin sallar isha’i na kama hanya, ina tafe har na iso wurin gonar nan da muka yi alk’awari.

ZANCI GABA5 HIKAYAR AZIZA DA AZIZU MAISO DA WANDA AKESO

ina ta tafiya harna iso wurin gonar nan da mukayi alk’awarin had’uwa da matar nan, na shiga cikin gonar na hangi wani haske da nisa a cikin gonar, sai na nufi wajen hasken. Yayin da na isa wurin hasken nan sai na sami wata makekiyar shimfid’a a wani muhimmin wuri, wanda aka bi duk aka bice da shimfid’u na alharini fari mai adon dinari, an kuma yi masa wani irin zanen fulawa na azurfa. An yi masa k’ubba da hauren giwa a samansa, ga kuma wani ginshik’i a wurin, ga fitilu an rarrataya, a tsakiyar k’ubbar, sa'annan kuma ga sham’a an kunna a cikin wani kasko na zinari. A k’arshen fitilun kuma an yi wad’ansu hotuna iri-iri a jikin wani abu mai kamar bangon littafi.
A wurin kuma akwai akusa na abinci wadanda aka rufe su da mayani na hariri, akwai kuma wata babbar randa ta k’arfe wadda ba kome a cikinta sai giya mai darajar gaske, sa'annan kuma a gefen randar ga kofuna iri-iri an daje su da zinari. Kusa da wannan wurin kuma ga wani faifai babba na azurfa an rufe wani tire shi ma na azurfa da shi, sa'annan an kawo tumak’asa an d’ora a kai. Sa'ar da na ga wannan shiri, sai na yi karambani, na bud’e na ga babu kome a ciki sai ‘ya’yan itace cike fal masu zak’in da laushin gaske. Har wa yau kuma a kan wani d’an teburi mai k’yalli ga turare a cikin wadansu ‘yan kananan kwalabe an dasa, wurin ya bice da k’amshi wanda ke busowa a hankali kad’an-kad’an. Lokacin da na ga wannan k’asaitaccen shiri sai na d’imauta, na zama kamar dadai da duniya ban taba ganin inda aka shirya abin arzik’i kamar wannan ba. Na yi farin ciki matuk’a, duk bak’in cikin da na sha fama da shi ya gushe nan take. To amma duk wannan shiri a banza yake wurina, saboda ni dai buk’atata saduwa da wannan matar. To, bayan na k’are kallon duk abubuwan nan sai na duba ko’ina ban ga wani mahaluki ba a cikin gonar ba.

Saurayi ya ci gaba da shaida wa Tajul Muluk labarinsa ya ce, na duba ko’ina ban ga wani bawa ba balle kuyanga, na hak’ura na nemi wuri mai ni'ima na zauna, ina jiran zuwan matar nan, har wajen sa’a guda, amma ba ta zo ba, na zauna shiru sai k’ura ido nake in ga b’ullowanta, amma ban ganta ba, yunwa kuwa ta addabe ni, hankalina ya tashi, tuni dai bak’in ciki ne ke hana ni jin yunwa, yanzu kuwa da hankalina ya kwanta, sai duk abin ya cakud’e saboda tsananin yunwa. K’amshin abincin nan yana bugu na kad’an-kad’an, na kasa hak’uri sai na matsa kusa da kwanukan abincin nan, na bude mayanin da ke kan wani kwanon, na sami wani faranti da ke ciki an saka gasassun kaji guda hud’u, an kuma zuba musu kayan k’amshi da na yaji, a d’ayan farantin kuma ga wani romon ‘yan shila, wani farantin kuma ga toye-toye iri-iri na alfarma. Na ji wani yawun kwad’ayi na zubo min, sai na sa hannu na yanki kad’an daga cikin wannan kayan tuya. Na ji wani irin dad’in mai gamsarwa, na hangi wani kayan tire a wani gefen can daban, na juya can na bud’a sai na sami wata waina narkakkiya ga nama a jere, sai na zaci ko ina gidan Aljanna ne, don na ga abincin kamar yana zuwa wurina da kansa ne, na hau da ci, shi ma na ci gwargwadon cikina, sa'annan kuma na nufi wurin ‘ya’yan itace, su ma na yanki kamar loma hud’u, na juyo ga kajin nan, su ma na d’an gutsura sai na ji cikina ya cika fam, na yi shakkar kada wani abu ya auku na rashin kunya, na je na nemi ruwa na wanke hannuna, sa'annan na koma wurin zamana. Na zauna kenan gyangyad’i ya soma d’iba ta, na d’ora kaina a kan wani matashi mai laushin gaske, ban san lokacin da barci ya kwashe ni ba, ban farka ba sai da na ji zafin rana na buguna.
Yayin da na farka sai na gan ni a rigingine, sa'annan kuma ga gawayi da gishiri a kan ruwan cikina, na mike tsaye na karkad’e rigata na duba kudu da arewa ban ga kowa ba, sa'annan kuma nan wurin da na farka babu wata shimfid’a wadda na sani tun kafin barci ya kwashe ni. Na yi mamakin haka gaya, na d’imauta, raina ya b’aci ainun, hawaye suka zubo mini, raina ya yi bak’in k’irin. Na tashi na nufo gida, na sami ‘yar uwata tana dukan k’irjinta tana faman kuka. Da ta ji motsina sai ta rera wadansu baitoci kamar haka:
Iska ta taso, ta bice furanni masu k’amshi,
Ta motsa wa tsananin so ciwonsa.
Haba iskar kudu zo mana nan wurimmu,
Kowane yana bakin iyakar son sa
To kuma lalle da iyakar rabonsa a wurinsa
Kai, wannan ciwon so ina jin zafinsa
Ina ma ina da iko na yi runguma tamkarsa
Tamkar da ya rungumi kirjin abar sonsa.
Idan dai har dan uwan nan nawa ya mutu,
Ya Allah ka haramta min rayuwa bayansa
Kada Allah ya jiyar da ni dadin duniya in ya mutu,
Aaa’aha yanzu ne zuciyata ke zafin son sa
Haka shi ma tasa take kunar son waccan mata,
Amma fa ni ga wannan ba na ganin laifinsa.

Sa'ar da ta waigo ta gan ni sai ta zabura cikin hanzari ta shafe hawayen da ke idonta, ta zo wurina ta shiga yi mini magana kamar yadda ta saba, ta ce mini. Allahu Akbar, d’an uwana har yanzu kana cikin ciwon son matar nan, ni kuma ina cikin ciwon son ka, mutane suna yi da ni cewar wai na cika rashin hankali tun da na dami kaina da son masoyin wata, amma ni duk wannan bai dame ni ba, na riga na yafe maka komai a kan wannan al’amari, ba na fatar Allah ya saka mini duka wani abin da ka yi mini."
Bayan ta k’are wad’annan maganganu sai ta yi murmushi, ta zo ta tub’e mini rigata, ta shanya sai ta sunsuna rigar ba ta ji kome ba sai ta ce, "wallahi wannan rigar babu wani k’amshin saduwar masoyi da masoyiya."
Sa'ar nan ta dawo wurina ta ce, na gaya mata abin da ya gudana tsakanina da waccan mata, ni kuma na kwashe duk abin da ya faru gare ni na gaya mata. Sa'ar nan da ta ji sai ta yi dariya ta ce, Allahu Akbar, wannan mata tana wahalar da kai dan uwana, babu shakka ina ji maka tsoro game da wannan mata. Gishirin nan da ka samu an zuba a jikinka wai tana nufin kai mai nauyin barci ne, saboda haka take son ka sa wa ranka gishiri tun da yake ka bayyana kai mai ciwon so ne, alhalin kuwa barci haramun ne ga dukan mai ciwon so, wai har ta ce maganar son da kake yi mata k’arya ne, saboda haka ta bayyana maka cewa ita ma k’arya take maka ba ta sonka, ta dai rud’e ka ne kawai. Lalle kuwa da son da take maka gaskiya ne da ta tashe ka daga barci. Ma'anar gawayi da ta d’ora a kan ruwan cikin ka kuwa, wai tana nufin Allah ya bakanta fuskarka tun da ka yi da'awar sonta bisa ga k’arya, har ta ce, wai kai yaro ne, ciwon so bai kamace ka ba tukuna, ta kuma k’ara da cewar ba abin da ya kamace ka sai cin abinci da shan abin sha da barci. Da ‘yar uwar nan tawa ta gama fassara mini ma'anar wadannan abubuwa sai ta ce mini, '"dan uwana, na roki Allah ya kiyayeka ya kub’utar da kai daga sharrin wannan mata." Saurayi ya ce yayin da na ji wannan jawabi na ‘yar uwan nan tawa sai na bugi k’irjina na ce “wallahi wannan jawabi naki gaskiya ne, hak’ik’a ni kam na yi barci, lalle kuwa masu fama da ciwon so ba sa barci, babu shakka na cuci kaina yayin da na ci abincin nan, sai na tambayi ‘yar uwata na ce, to yanzu mene ne abin yi gare ni, domin duk lokacin da bak’in ciki ya taso mini sai na fashe da kuka. Na ce da i “don Allah ki gaya mini yadda zan yi na sami saduwa da wannan mata, na rok’e ki don Allah ki ji tausayina, ki taimake ni domin kuwa in ban sami saduwa da wannan mata ba, mutuwa zan yi.

saurayi ya ci gaba da ba da labarinsa ga Tajul Muluk dan Sarki Sulaiman a sa'ar da suka sadu a cikin wani lambu. Ya ce yarinya ‘yar uwata ta ci gaba da gargad’ina a kan wannan mata da nake mutuwar so, ta ce “amma tun da yake har yanzu hankalinka na kan ta zan yi matuk’ar k’ok’arina na ci gaba da taimakonka har zuwa matuk’ar iyawata.” Sa'annan ta ce da ni, “ka tafi can wurin nan da kuke saduwa ka zauna, idan ka je wurin kada ka yarda ka ci wani abinci, kada kuma ka yi barci, yawan ci shi ke kawo barci saboda haka na shawarce ka duk yadda yunwa ta matsa maka ka daure, yunwa ba ta kisa sai dai wahalarwa, wahala kuwa tana tare da wanda Allah ya d’ora wa masifar son wani, amma ka ga bak’in ciki babu shakka yana kashe mutum. Ita wannan mata za ta ci gaba da jarraba ka har zuwa wani lokaci. Idan ka je wannan wurin ka tabbata za ta zo amma ba za ta zo ba sai wajen asubahi. Na roki Allah ya kiyaye ka daga sharrin wannan mata.”
Saurayi ya ce yayin da na ji haka sai na yi farin ciki, na zauna ina jiran dare ya yi don na je can, sa'annan da daren ya yi na kama hanya zan tafo sai ‘yar uwan nan tawa ta ce idan har kun sadu ka rera mata baitin wak’ar nan tawa a lokacin da za ku rabu, sai na ce da ita, "To." Yayin da na fito na kamo hanya, ina tafiya har na iso wurin, na sami wurin an shirya shimfid’u kamar yadda na same su da farko, ga abubuwan ci da na sha iri daban - daban, ga kuma kayan ci na marmari daga ‘ya’yan itace zuwa kayan alfarma na toye - toye babu iyaka, sa'annan ga turare iri - iri masu k’anshin gaske, su ma an shirya su gwanin ban sha'awa. Da na k’are kallon wadannan abubuwa sai na koma wurin zama na zauna, k’anshin abincin nan yana buguna, zuciyata ta afu matuk’ar game da son in ci abincin nan amma sai na daure na k’i ma kula shi.
Ni dai wallahi ban san lokacin da na rud’e ba, na kasa hak’uri, sai na zagayo na zo gun abincin nan, na bud’e mayanin da ke rufe a kai, na ga naman kaji soyayye da romo mai kyau, akwai abubuwan ci iri hudu kowane kuwa kan gaba ne wajen dad’i. Sai na kasa yin kome, na bude na yanki loma guda, guda a cikin kowane tsibin, sa'annan na koma wajen kayan zak’i su ma na ci gwargwado, na kuma dauki yankan nama guda na saka a bakina, na juya wajen kayan sha na bude na sha na cika cikina tab. Sa'annan na ce kome ta fanjama, fanjam,ni dai ba zan yarda na sake da cikina ba, saboda haka na ga ya fi kyau in kintsa. Kafin a jima sai na ji idanuna sun soma lumshewa, na jawo matashi na tada kaina, na auna cewan zan dan kishingid’a ne na huta har lokacin da za ta zo ta same ni, na sani dai barci ne ba ta son ta same ni ina yi, amma ko ta sami na ci abinci ba za ta damu ba. ‘Dora kaina ke da wuya a kan matashi sai na rufe idanuna, shi ke nan sai barci ya yi awon gaba da ni, shiru ban farka ba sai da rana ta fito ta soma buguna.
Sa'ar da na farka sai na ga an d’ora wani makeken akushi a kan ruwan cikina tare da tubali daya na d’an dabino, da kuma k’wayoyin harub. Sa'annan kuma na duba ko ina ban ga kayan nan da na bari ba, ba kuma wani mahaluki a wurin sai wad’annan tarkacen da aka d’ora kan ruwan cikina. Na tashi na mik’e tsaye, na karkad’e jikina, na fito daga cikin gonar na kamo hanyar gida, ina tafe cikin haushi, ainun, na sami ‘yar uwata tana kuka tana gwama numfashi, sa'annan kuma tana rera wad’ansu baitocin wak’a kamar haka:
Jiki ya rame zuciya na ciwo,
Hawaye na zuba a idanuna,
Wanda nake so yana da wuyar gani,
Na rasa yadda zan yi da al’amarina
Ya dan uwana na fa shiga damuwa,
Ta ciwon son ka da ciwon idanuna
Saurayi ya ce, da na ji tana wannan wak’a sai na kifa mata mari, na kwarara mata zagi yadda raina ke so, na doke ta yadda raina ke so, sannan na rabu da ita. Ita ko kula da ni ba ta yi ba, sai kawai ta share hawayenta ta zo wurina, ta kama ni ta runguma, ta hada k’irjina da nata. Ni da goga min k’ irjinta da nawa sai na ji kamar garwashin wuta ne aka goga min, sai na ja da baya na shiga k’ok’arin k’wacewa. Ita kuma tana shafa ni tana matsewa har dai ta gaji ta k’yale ni, sa'annan ta tambaye ni, ta ce, '"dan'uwana, kada dai in ce jiya ma ka yi barci ne da dare!” Sai na ce mata, “haka ne kuwa, domin ni da na je cikin gonar na ga k’asaitaccen shirin da aka yi sai na zauna na kwashi kab’aki. Ban san komai ba sai barci ya d’ebi kayansa ban farka ba sai da rana ta fito. Da na farka sai na ga an d’ora wani makeken akushi tare da tubali guda, da k’wallon dabino, da kuma k’wallon goriba. Na tashi na karkad’e su daga jikina na kamo hanya na zo gida, amma ni ban san abin da take nufi da wannan ba.” Yayin da na fad'a wa ‘yar uwan nan tawa wannan abin sai kuma zuciyata ta rufe na rasa abin da zan yi sai na fashe da kuka na matso gun ‘yar uwata na ce ta gaya mini ma'anar wannan aiki na wulak’anci da wannan mata ta yi mini.
‘Yar uwan nan tawa ta shiga fassara mini ma'anar abubuwan nan da aka d’ora mini a ruwan ciki, ta ce, "abin da take nufi k’wallon goriban da ta zuba kan cikinka, wai tana nufin kai ka zo wurin domin ta amma zuciyarka na can wani wuri, saboda haka ta gargad’e ka da cewar shi al'amarin so ba haka yake ba, har ma ta ce ko kusa kada ka saka kanka cikin masu iya rik’on al'amurran so. K’wallon dabino kuwa, tana nuna maka cewar da kai mai ciwon so ne, wanda har zuciyarsa ta k’una da so, da ba ka sake har ka ji dad’in barci ba, ka sani jin dad’in so kamar d’an dabino yake, tubali kuma abin da take nufi da shi, wai ta ce da kai, zuciyar mai so a warware take ba kome sai son kurum, ta sa a gaba, don haka ta ce ka dai hak’ura da rabuwar da za ku yi, har ma ta shawarce ka da ka tanadi irin hak’urin nan na Annabi Ayyuba, amincin Allah ya tabbata a gare shi.
Saurayi ya ce, sa'ar da na ji fassarar wadannan tarkacen da aka d’ora mini a ruwan cikina, sai zuciya ta sake b’aci, na auna a zuciyata cewar Allah ne ya k’addara mini yin wannan barci tare kuma da rashin rabona a wurin wannan mata. Sa'annan na ce da ‘yar uwata domin darajar rayuwata a wurinki ina son ki nuna mini dabarar yadda zan sadu da

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

7 Comments On HIKAYAR AZIZU DA AZIZA
avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Telecharger

avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Telecharger

avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Download

avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Download

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to hamadou-8

idan ka gagara downloading ne zaka iya karantawa anan kyauta ai

avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Hamadou saadia

avatar
mustapha-6-6

2 months ago

Reply

Ai kamar bai kare ba

Please Login or Register in order to submit comment