Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina rokon Allah kada ya kama d’an uwana da laifi a kaina saboda abin da ya yi min. Yanzu Allah zai tafiyar da ni daga wannan duniyar wadda ke cike da kunci zuwa inda zan huta wa raina.” Na ce mata, “ya ‘yata, Allah ya kiyaye ki kuma ya kiyaye kuruciyarki.” Na cigaba da tambayar ta dalilin rashin lafiyarta ta ki fada min sai murmushin karfin hali kurum take yi. Ta ce min, ‘ki fada wa d’anki cewar ya kiyaye wad’annan kalmomi cewa ‘cika alk’awari na da dad’i, warwarewa kuwa mugun abu ne.’ wannan shi ne zai zamana cewa ina kula da shi. Kuma zai nuna na damu da shi a lokacin da nake raye da kuma bayan mutuwa ta.” Sannan kuma ta ba ni wasu abubuwa ta ce kada na ba ka sai lokacin ka zo min kana kuka saboda bak’in cikin mutuwarta. Abin da ta ba ni yana nan hannuna ba zan ba ka yanzu ba sai na lura ka shiga taitayinka sannan na ba ka.”
Na ce wa uwata, “ba ni abin na gani.” Ta yi mirsisi ta hana ni. Na zauna ina mai cike da bak’in ciki saboda mutuwar ‘yar uwata, kodayake ban damu sosai ba duk tunanina ya tafi wurin abar k’aunata wadda dare da rana na kasa samun sukuni saboda abin da nake samu a wurinta. Na zauna a k’agauce ina jiran dare ya yi, da dare ya yin na tafi gonar nan da muke had’uwa, yayin da ta gan ni ta zabura ta taso ta tarye ni, ta kama ni ta rungume, sa'an nan ta zaunar da ni ta tambaye ni labarin ‘yar uwata na ce mata ai ta mutu. Hankalinta ya tashi, ranta ya b’aci matuk’a, sai ta ce mu je mu yi mata addu'a, muka je wani wuri muka zauna muka yi zikiri da addu'a sa'annan muka shiga sha'animmu na holewa da nishadinmu.
Bayan nan ta tambaye ni yaushe ne ta rasu? Na ce mata, “jiya kwana hud’u yau ne na biyar.”

Ana karanta wannan labarai ne zaurukanmu na sirri wanda iya masu rijista kadaike samun daman shiga
Domin yin rijista kuna iya tura kudinku 200 kacal ta sakon waya kota hanyar transfer'dauke da sunaka na Facebook izuwa 0803276754708 HIKAYAR AZIZA DA AZIZU MAISO DA WANDA AKESO

Da ta ji haka sai ta fashe da kuka ta yi kururuwa ta ce, “ba na fad’a maka kai ka halaka ta ba? Da ka bari na san da ita kafin ta mutu da babu shakka na sakanta mata abin da ta aikata mini na alheri. Ta kyautata mini ta sada ni da kai, domin na tabbata ba domin ita ba da ba za mu taba haduwa ba balle mu biya buk’atar mu. Ni kam ina jiye maka aukuwar wani mugun abu gare ka, sakamakon abin da ka aikata mata.” Na ce “ai ta yafe min kafin ta mutu.” Na habarta mata abin da uwata ta fada min. Ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Allah ya jikanta, wadanne kalmomi ‘yar uwarka ta bayar da sallahun a fad’a maka?”
Na amsa na ce, “kafin rasuwarta ta ce a fada min cewa, ‘cika alk’awari na da dad’i, warwarewa kuwa mugun abu ne’. Yayin da matar nan ta ji haka sai ta yi kururuwa, ta yi kuka ta ce, “Allah ya gafarta mata. Wannan kalmomi na nufin ta bar min kai. Kuma ta nemi na kyale ka daga sharrin abin da na yi nufin yi maka. A gaskiya da na yi nufin cutar da kai amma yanzu na hakura ba zan cuce ka ba.” Na cika da mamaki na ce mata, “yaushe kika yi nufin cutar da ni alhali kuwa ga shi muna soyayya?” Ta ce, “ba za ka gane komai ba saboda yarintarka da karancin tunaninka, ba ka san kaidi da makircin mata ba.
Da a ce tana nan a raye na tabbata da za ta kare ka daga fadawa hadari bisa dalilin makircin mata. Yanzu na hore ka da kada ka sake kula wata mace, kada ka yi mata magana ballantana ka sadu da ita ko aurenta. Yarinya ce ko tsohuwa. Ka ji na fada maka, ka kiyayi kan ka, ka kiyayi rayuwarka domin ka zama ba ka da mai kiyaye ka. Wadda ke fassara maka isharun nan ta riga ta mutu. Ni ina kaunar ka, bana son na ga ka fada wata masifa da ba za ka iya fita ba.

Saurayi ya ce da Tajul Muluk matar nan ta ci gaba da nuna mini girman hasarar da ya same ni saboda mutuwar ‘yar uwar nan tawa. Bayan ta k’are yi mini bayani sai ta tuma tana kururuwa, da birgima a k’asa tana marin kanta tana cewa, “wallahi ban san da zaman wannan yarinya ba, da na ba da tawa gudummawa. Allah ya ji k’anta, ta kasance mai girman ladabi da biyayya, kai wannan yarinya da zurfin ciki take, ta rufe sirrin cutarta, amma ba ta ci riba ba, da ta cimma burinta, da ba ka shiga wannan hanya ba.” Da ta k’are kukanta sai ta ce da ni tana son abu guda a wurina, watau tana son in kai ta wurin da kabarin ‘yar uwar nan tawa yake ta yi ziyara, na amsa mata cewan kashegari zan kai ta wurin. Bayan mun k’are hayaniyarmu muka kwanta barci, amma bayan ko wace sa'a matar nan takan juya ta numfasa ta ce, "da ka gaya mini tun da sauran wuri da ba haka ba."
Maganar ‘yar uwar nan tawa a bakin wannan mata ya dame ni, na rasa yadda zan yi in fitar da zuciyarta ga wannan zance na kasa, sai na tambaye ta cewar ta gaya mini ma'anar kalmomin nan guda biyu da aka bar wasiyyarsu a wurin uwata, amma sai ta kyale ni ba ta ko dube ni ba. Na yi ta tambayarta amma a banza ba ta gaya mini ba.
Kashegari da muka farka daga barci sai na ga ta dauko wata jaka da dinari a ciki, ta ce na tashi na kai ta wurin da kabarin ‘yar uwata yake. Na tashi na shiga gaba, muna tafiya, tana ba da sadaka a kan hanya, har muka isa, koyaushe ta ba da sadaka, sai ta ce ta bayar saboda ‘yar uwar nan tawa.
Yayin da muka isa na nuna mata kabarin sai na ga ta yanke jiki ta fadi, tana mirgina, tana kururuwa, sa'annan na ga ta fito da mabugi da karfe ta zauna kusa da kabarin ta rubuta wad’annan baitoci:
Na wuce kaburbura da dama cikin tausayi,
Amma wannan ya fi matuk’ar girgiza ni
Na tambayi mazaunin cikinsa da ladabi,
Aka ce min ta mutu da ciwon son zamani
Na roki Allah na cika da so cikin raina
Aljannar Firdausi ki zauna babu gunaguni
Su kuwa masu cutar da ma’abota son su,
Za su ga k’ask’anci komai tsawon zamani
Ina ma wata ran kabari zan zo ziyara,
Na yi maka kuka na zubar da hawayen jini
Bayan ta k’are rubuta wannan baiti kan kabarin nan sai ta sake fashewa da kuka, ta yi salati, sa'annan ta tashi muka koma cikin gonar da muke zaune, muka zauna muna hira sai na ga ta yi shiru. Ta d’aga kanta sama ta dube ni ta ce, "na had’a ka da Allah wanda ya halicce mu, kada ka yarda ka dauke mini k’afa ko da da rana d’aya." Na amsa mata cewa, “na yarda da haka.” muka ci gaba da zamanmu tare da ita, koyaushe tana nuna mini karimci da kyautatawa, wani lokacin takan tab’o ni da maganar kalmomin nan da ‘yar uwata ta bar wasiyyarsu, idan ta tambaye ni sai na yi murmushi sa'annan in biya mata su in tambaye ta ma'anarsu, amma sai ta k’i fad’a mini. Haka muka zauna muna ci tare, muna sha tare, muna kuma holewarmu kamar yadda muke so har zuwa wani lokaci mai tsawo har bak’in cikin mutuwar ‘yar uwata ya rabu da ni, hankalina ya zauna, na murje har na yi k’iba na yi kaurin wuya, na yi taib’a abin gwanin ban sha'awa, da ban al'ajibi, kullum ina sa tufafi mai kyau na yi shigar da nake so. Rannan sai na shiga d’akin wanka na yi wanka na komo cikind’akina na zauna a nan na sami wata moda an cika ta da wata zuma mai kauri da na shak’i k’anshinta gwanin dad’i. Na yi k’arfin hali na dauki zumar nan na sha, sai maye ya kama ni, lokacin sallar lisha ya yi na tashi zan yi salla na ji ba zan iya ba sai na koma na kwanta, ina nan har lokacin da zan tafi wurin matar nan ya yi, na tashi zan tafi wurinta ina had’a hanya. Ban san yadda aka yi ba na gan ni a cikin wani lungu da ban taba shigarsa ba. Ina tafiya cikin lungun nan na hadu da wata tsohuwa tana tafiya, tana rik’e da wata fitila da kuma takarda a hannunta, an nad’e ta.

Saurayi Azizu ya ce da Tajul Muluk, lokacin da na ke tafiya na hadu da tsohuwar nan sai na gan ta tana kuka idanunta sun yi sharaf da hawaye, tana cewa, kaiconka samari shin ba ka ganin jama’a na maka maraba? Ni na dade a wurinta, ina kallon su, ina kuma sauraren muryarta mai sanyi mai dadi, ina ma a ce zan iya cire wadannan kayan wuyan in ba ka kyauta, ai kuwa da zuciya ta karaya a cikin sa'a guda."
Da ta gan ni sai ta matso kusa da ni ta ce in karanta mata takardar nan da ke hannunta. Ta miko mini takardar ta kawo fitila kusa da ni, na bude takarda sai na ga ba a rubuta kome ba a ciki sai gaisuwa da tambayar lafiyar masoyi, na mika mata. Sa'annan tsofuwar nan ta yi mini bishara da cewan bakin cikina zai yaye kamar yadda nata ya gushe. Yayin da ta juya ta tafi sai na tsuguna zan yi fitsari. sai ga tsohuwar nan ta dawo wurina cikin hanzari, ta kama hannuna ta ce in biyo ta mu je wani katon gida da ke kusa da wurin. Na nuna mata ba ni da bukatar zuwa gidan, amma sai ta dage har na yarda na bi ta, muka je na tsaya bakin kofar gidan, ta ce mini in shiga na ki, na tambaye ta inda ta sami wannan takarda, ta ce mini wai wani d’anta ne da ya yi tafiya kamar shekara goma bai dawo gida ba, shi ne ya aiko mata da takardar, ta ce mini wai yana da wata ‘yar uwa a cikin wannan gidan, wadda tun lokacin da ya tafi take kuka dare da rana. Kuma ta dage a kan cewar sai an kawo mata wanda ya karanta wannan takarda ta gan shi da idonta sannan za ta yarda da abin da ke ciki.
Tsohuwa ta shiga rarrashina tana ba ni magana, dad’in baki, har dai na saki jiki da ita, na bi ta, muka shiga cikin gidan. Na tsaya a bakin k’ofa, sai ta ce, "haba dana, shin ba ka ji Manzon Allah (mai tsira da aminci) ya fad’i cewa, "wanda ya gusar wa Musulmi da bakin cikinsa daya. Allah zai gusar masa da nasa sau saba'in da biyu, a ranar Alkiyama ba? Ko kuwa kana gudun ganin wannan yarinya ce, idan haka ne na yi maka alkawarin zan saka labule a tsakaninku, har yadda ba za ku had’a ido da juna ba. Ka sani dai kai dana ne, ba ni kuma da nufin kullin sharri zuwa gare ka kada ka yarda ka gwale ni a cikin wannan al'amari."
Tsohuwa ta hura min wuta kan sai na shiga gidan nan, daga bisani na ce mata ta shiga gaba na bi ta. Muka kama hanya muka shiga tana gaba ina biye har muka isa bakin wata k’ofa, wadda aka yi wa ado mai ban sha'awar gaske. Kyauren k’ofar an yi shi da k’arfen tagulla ja ne, an daje shi da jauhari. Da muka isa wannan wurin, sai na tsaya a nan, na ce da ita ba zan shige nan ba. Bayan ta ba ni magana na ki ji, sai na ji ta fasa kururuwa, tana kiran wadansu sunaye da ban tab’a jin irin su ba a cikin wani harshe da ban tab’a jin sa ba. Jim kadan sai ga wata kyakkyawar yarinya ta lek’o tana murmushi. Da zuwan ta sai na ji ta yi mini magana a cikin murya mai dad’in gaske, maganar kuma mai cike da fasaha da ma'ana, sa'annan na ji ta ce, "Umma, wannan shi ne wanda ya zo karanta mini takardar dan uwana ? "Tsohuwa ta ce da ita, "na’am shi ne, amma na sha fama a kan sa kafin mu zo da shi."
Yarinya ta fito da takarda ta mik’o mini, na mik’a hannuna zan karb’a sai ta rik’e ni, ta fizgo ni, har kaina ya shige cikin labulen da ke tsakanimmu, kafin in ankara sai na ji tsohuwa ta cuso kanta tana tura ni ciki, na turje, sai suka yi ta turi kafin lokaci kad’an sai ga ni na fada tsakiyar gida. Ashe wannan k’yauren da na rik’e yana tafiya da ni ne ni ban sani ba. Yarinya ta ja ni ta kai cikin wani makeken daki ta zaunar da ni, tsohuwa kuma ta shigo ta kama k’ofar dakinta saurayi Azizu ya cigaba da ba wa Tajul Muluk labarinsa, na waiwaya na ga kaina a cikin gida, tsohuwa ta yi hanzari da gaggawa kamar walkiya, ba ta yi wani abu ba face ta kulle k’ofar. Yarinya ta gan ni daga mashigar zaure ta taso zuwa gare ni ta rungume ni a kirjinta sannan ta matsa cikina da hannunta tana bugawa da kyau har sai da na kusa fita hayyacina. Ta rike ni da hannunta ba ni da ikon kubcewa, muka cigaba da tafiya tsohuwa tana gabanmu rike da sham’a har muka je zaure na bakwai sannan muka isa wani fili mai rairayi da yawa, wanda ya isa masu sukuwar dawaki su yi tsere a cikinsa.
Incomplete

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

7 Comments On HIKAYAR AZIZU DA AZIZA
avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Telecharger

avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Telecharger

avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Download

avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Download

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to hamadou-8

idan ka gagara downloading ne zaka iya karantawa anan kyauta ai

avatar
hamadou-8

1 year ago

Reply

Hamadou saadia

avatar
mustapha-6-6

2 months ago

Reply

Ai kamar bai kare ba

Please Login or Register in order to submit comment