Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dajin muryar ta
Sai hankalina ya tashi nara mezance ma dady Sai
Nace mai Dady Batanan Sai yace man Ina tatafi?
Sai Nace mai taje gidan kawarta Indo Sai ya fara
man fada Dan ubanka neyasa zaka bar Sameera
tafita cikin wannan daren ? Nayi Shuru Sai
yaceman Ai gobe zamu dawo Idan wani Abu
yasami Sameera to Ranka sayya 6ace bai bari
nayi magana ba Sayya yanke wayar, WASHE GARI
misalin karfe 11:46am Su dady suka shigo Zaria
suna zuwa Zaria Sai Dady ya kirani awaya Ina
dauka Sai yaceman My son Kamai su Sameera
gida Mundawo yanzu Can Sai yakara Ceman Sikin
Sanyin murya yace man My son Nakosa naga
Sameera Bala'i Abunda Nace acikin zuciyata Sai
na fata tunani wai mema zancecma dady ne Ina
cikin wannan tunanin Ne yakara kira My son don
Allah kayi Sauri kadawo dasu gida Da sauri na
hada kayan Anwar dana Adnan Nasaka su a mota
nuka tafi gidan Su dady
Muna zuwa natarar da dady a harabar gidan a
tsaye Muna fitowa ya kalleni jikina Sai rawa yake
Buda bakin dady Sai yace man My son Ina
Sameera? Nayi shuru Sai ya kara ceman Sameera
ta byata ne? Nayi shuru Sai yace man cikin
tsawa Bakajini Ina maka nagana Buda bakin
Anwar Sai yace Dady Sameera ta byata Guduwa
tai tabar gidan kuma tace har abada bazata
dawo ba wai karma ayi wahalar nemanta dan
baza aganta ba Sai naga dady ya fadi Ya suma
da sauri na daukeshi nayi cikin gida dashi Bayan
ya farfado Sai nabashi labarin abinda ya faru
Komi na fada mai amma ban fada mai cewa
kauraye sunyi zina da Sameera ba Haka mukaci
gaba da Neman Sameera harna tsawon 4week
amma bamu ganta ba bata ba a lamarta Har
muka hakura Momy tayi kuka kamar ranta ya fita
ni kaina nasan Suna Son Sameera sosai, Ashe
Sameera bayan ta bar gida na Mota tahau
Daniyyar zata Bauchi Gun wata kawarta wadda
suka hadu tun a Secondary School Lokacin dataje
bauchi Sai gidan kawar tata Mai suna Polina
itama ba musulma bace dataje gidan Sai tatarar
gidan Babu kowa
Sai akayi ma Sameera kwatancen Gidan kawar
Polina mai suna Manasa Bayan Sameera ta je
gidan su Manasa Sai ta samu yaro daya kira
mata Manasa a gidan Sameera na yatsaye Sai
yaron yafito yace ance Manasa batanan Amma
Idan zaki iya jiranta to Bazata dadeba zata dawo
Sameera tun karfe 4:25pm take jiran manasa
Amma Manasa bata dawo ba Sai bayan magriba
Yunwa nadamun Sameera gashi kudin dake
hannunta Saura naira 200 Tana tsaye Sai ga
Wata Moha jeep Tatsaya agaban Sameera
Sameera natsaye tana kallon
Motar Sai taga Manasa ta fito Daga cikin motar
Sai manasa ta zo inda Sameera take Sai take
Cema Sameera anyi man Waya ne ance man
Wata bakuwa tana kofar gidan mu tana jirana
kece ?
Sameera tace Eh nice Kece Manasa? Manasa
tace Eh meke tafe dake? Sameera tace Nazo
gidan Wata kawata mai suna Polina naga gidan a
rufe Amma Ance nazo gunki kila kinsan Inda suka
koma Ance man ke kawarta ce Manasa tace
gaskiya Bansan inda polina suka koma ba
Manasa ta juya zata tafi Sameera taduka tarike
mata Riga tace Manasa kitai makene da gun
kwana Kona bar nan bansan inda zanje na
Kwanta ba Manasa ta Tambaye ta daga Ina kike?
Kuma maye sunanki? Sameera ta Ce sunana
Sameera Ina Zaune a katsina a wani kyauye mai
suna Dandume.
*** CIKIN DARE Part 8 ******
Nan dai sameera suka yi jinga zata rinqa yi ma
su masana aiki. A wanchan bangaran kuma ina
ta kiran sameera A waya taki dagawa da kyar na
samu ta dauka. Sameera na daukar wayar tace
Hello, Banji taba Tanata Hello bana jinta Sai na
kashe wayar Saboda bana jinta Sameera ta ije
wayar Inda taganta tatafi wajen aikinta. A
wanchan bangaren kumah na shirye naje bauchi
ziyara wajen abokina munnir. Muna tsaye da
abokina Munir ya kira Yayan Manasa Mai suna
Rahul Ya Ce mai Rahul Kazo Inda Muka Saba
haduwa zakaganni nida Abokin nawa Rahul Cikin
sauri yace Ganinan zuwa Ina tsaye Sai ga Yayan
manasa Yana fitowa daga mota Muka hada Ido
dashi Hankalina ya tashi Yana zuwa yace ma
Munir wannan ne Wanda kukazo tare dashi?
Munir yace Eh Shine Kasan shine? Rahul yace
wannan Da kake gani Shine yayi wa Manasa Ciki
Cikin sauri Munir ya kalleni yace Abdul Dama Kai
Mazina cine? Nace mai A'A yace man Rufe man
baki Rahul Kayi hakuri bansan hakan tafaru ba
Dakar munir ya lallashi Rahul Har Rahul yaji yana
son yayi Abota dani, Rahul shine ya kaimu gidan
su Lokacin da muka kaje Sameera tana kasuwa
Rahul shine yayi kokarin Hana mahaifiyarshi
abunda tayi niyyar yimin Maman Manasa Wuka ta
dakko da Niyyar zata kasheni Hankalin yayi
matukar tashi Dakar Rahul Ya lallasheta Harta
hakura Amma dai duk da haka taki Sakin jiki dani
Munir Shikanshi Naga chanji atare dashi Saboda
yaji Ance nayiwa Manasa Ciki,
Muna zaune a falo Sai ga Manasa ta shigo gidan
Tana zuwa falo ta kalleni Sai Murna da sauri ta
kawo mana Abinci Mukaci muka koshi Manasa Ce
ta kirani Izuwa dakinta don mu tattauna Gaskiya
Manasa tana dakyau Amma Duk kyanta bata kai
Sameera ba Manasa tace man Baffa banta6a
haduwa da Namijin daya shiga rayuwa ta Lokaci
guda ba Sai Saikai daga wannan lokacin na
yadda da Soyayyar Manasa Kafin Sameera ta
dawo Manasa ta shaida Ma iyayenta cewa Ni
take so ta Aura Iyayenta Sunyi Farin ciki
A daidai wannan Lokacin Mahaifin Manasa ya
shigo yana masu Albishir dacewa Gobe Zasuje
Gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi Zasu
musulinta Matan gidan sunyi Farin ciki dama
suna Sha'awar shiga musulinci Dadyn Manasa ne
kawai baya so A wannan Lokacin Naji dadi
Saboda nasan zan iya auranta tunda ta Musulinta
Munir yana A falo ni kuma natashi na tafi dakin
manasa Nabar Munir A falo Ina shiga dakin
Manasa Dai dai lokacin da Sameera tashigo
Gidan Su Manasa da Leda A hannunta Kayan
miya ne tasiyo Tana shigowa Rahul yace to kaga
yarinyar Bayan ta gaishi ta wuce ciki dan yin
Aikin dake jiranta Munir yaji tausayinta Saboda
ganin yadda take tafiya a Karkace jikinta duk ga
Alamun Bulala nan, Kwance natarar da Manasa a
dakinta tana tunanina
Tana ganina a dakin Nayi Sauri Narun gomota.sai
nayi tunanin kar abin ya faru baya ya kara
faruwa.da sauri na saketa na fito dakin. Ina
fitowa daga Dakin Manasa nayi sa'a ba Wanda
ya ganni Ina zuwa Munir yace Abdul-rahman
naga 'yar aikin gidan su rahul Wllh har tabani
tausayi Abdul-rahman bara a kirata ku gaisa Sai
Nada katar dashi Nace karabu da ita Watarana In
na sake dawo zan ganta Munir kazo mutafi
Yamma tayi Bayan munyi Sallama da Mutanen
gidan Mun fito Sameera kau duk batasan abinda
ke faruwa ba tana Kicin Sai aikinta take,
Lokacin da zan shiga mota Manasa ta kalleni
Cikin tausayi tace man Baffa yanzu Sai yaushe
kenan? Sai Nace mata Sai munyi Waya Muna
tsaye nida Manasa mahaifin ta ya fito daga cikin
gida ya kallemu yace Baffa daga gani kai
mutumin kirkine don haka idan har dagaske kake
to katuro Iyayenka Ayi maganar aurenka kai da
Manasa, Bayan muntafi
Sameera ita batasan abinda ya faru ba Data
gama aikin datake Shine taje daki ta zauna
Ananne tayi tunanin dazu dazata shigo gida taga
taga mota Irin ta yayanta Baffa A guje ta fito
izuwa harabar gidan wai koda zataga motar Tana
zuwa Sai taga babu motar Tana dawowa falo Sai
taga Manasa Sai tace ma Manasa Don Allah
suwaye sukazo gidannan dazu?
Manasa tace Meya faru? Sameera tace naga
motar da sukazo tayi man kama data Yaya na
Manasa taja tsaki Mitswwewww Tare da fadin ke
dai dabbace wllh dallah ga fara can wuce kibani
gu wawuya kawai, Sameera ta shiga daki tana
kuka Ananne tayi Data Sani bata Bar zaria ba Da
tana da kudi da zaria zata koma rashin kudi ya
hana Sameera yin kwalliya Ko kwalliya bata yi
Saboda bata da kayan kwalliya Sameera Tayi
kuka kamar ranta zai fita Rahul Yayi duk iya
kokarinsa Wajen kawo mata Samiri Abokansa
Amma ita takekashe Tana da Wanda zata aura
Amma takasa Fada masu Sunan Wanda zata aura
Rahul ya kawo mata Manyan mutane amma bata
son kowa Sai ni Wannan dalilinne yasa take
sanya likabi Idan aka Aiketa kasuwa Idan
Sameera tazauna ita kadai tunanina Kawai takeyi,
Rahul jiyayi Kamar kiyayyar Sameera takara
dasuwa a cikin zuciyarshi Wata rana Sameera
tana a kasuwa Rahul Zata siya naman miya
Rahul Yazo inda take ya wanketa da Mari Saboda
yasa ta gugar kaya Kafin ta fara Hajiya Wato
Innar Rahul ta aiketa kaasuwa Amma tayima
Rahul bayani amma duk da haka yaci gaba da
dukanta A tsakiyar kasuwa
Sameera dataji bugu batasan lokacin data
zageshi ba Cemai tayi Allah ya isa banyafe maka
ba mugu kawai.
MU HADU A PART 9 DA SAFE, KUNA TARE
**** CIKIN DARE Part 9 ******
Rahul yayi matukar mamaki da Sameera ta
zageshi A guje ya Debi motarsa Izuwa gida Yana
shiga gida Sai Hajiya tace Rahul Ya kashigo
gidannan ranka A6ace meyasa meka? Rahul yayi
shuru Hankalin Hajiya ya tashi Ta kara cewa
Rahul Don Allah kafada man Waya 6ata maka
rai? Rahul cikin fushi yake cewa Hajiya Wai Hajiya
yanzu kamar Sameera Ita Ce zata zageni a
tsakiyar Kasuwa Hajiya tace Sameeran Ce
tazageka? Yace Eh Hajiya! Hajiya Tace kaje ka
dakko wayar Redio Idan tadawo kai mata Kafirin
duka Rahul yaje ya samu Wayar Redio Manasa
ma Itama tasamo wayar Redio Wai harda ita za'a
daka Sameera saboda tazagar mata Yayanta,
A falo suke tsaye suna jiranta Manasa da tadawo
gida tana zuwa harabar Gidan Taji gabanta yana
fadi, Kamar tajuya ta fita gidan amma hakanan ta
tashiga gidan Tana zuwa falo Manasa tayi saurin
kulle kofar falon Sameera ta zaro Ido Tace
Manasa Lafiya? Manasa ta wanketa da mari
Rahul yacire hijabin dake jikin Sameera kukaci
gaba da dukanta Sai da sukaimata ti6is Suka far
fasa Mata jiki Ko ina ajikinta ya fashe Fuskarta
Ce kawai batayi komai ba Saboda itama tana rife
fuskar Sameera tayi kuka kamar ranta ya fita
Bayan sun gama bugunta 3 Awos Bata iya tashi
Sameera da rarrafe takai dakinta Jikinta gaba
daya duk bakarfi Kankace haka ciwon kai mai
karfi Ya kamata zazza6i Idonta biyu Ita kanta
Tana tausaya wa kanta Gari nawayewa Rahul ya
shigo yacewa Sameera Ke Ga kayana can dana
Manasa Dana Hajiya Ki wanke Mana Kitabbatar
da kin wanke su kafin Mu dawo daga Jos Cikin
sauri Sameera ta Amsa Saboda gudun bugu, Yaja
tsaki ya fita,
CIKIN DAREN bacci yaki yuwuwa man Saboda
tunanin Sameera Shin tunanin danakeyi Wane hali
Sameera take ciki kuma Ina take Ammsar Dana
kasa Samu kenan, Gari na wayewa nayi wanka
Nadau Key din motata Naje gidan su Dady Ina
zuwa nagaida momy na da Abba Sannan Nasanar
dasu Yadda mukayi da Abban Manasa nacewa
naturo Magabata na da ayi Maganar Aurena da
manasa Dady yayi farin ciki Itama mahaifiya ta
Buda bakin Momy Sai tace dannan Wlh harga
Allah naso ka Auri Sameera Allah nedai bai
nufaba yanzu nata Raye ko bata Raye Wallahu A
alamu Sai dady yace man yaushe Iyayen Manasa
sukace katuro mahaifan ka Sai nace mai Dady
2week suka Ce Dady yace Allah ubangiji ya kaimu
lokacin Momy tace Ameen,
Jingine nake ajikin motata a kofar super market
din dake Tudun wada Zaria Tunanin Sameera ya
hanani walwala da Kwanciyar hankali Ni Sai naga
kamar 6atar Sameera batazana Ce ga Rayuwa ta
Ina tsaye nayi tagumi Sai ga wata kyakykyawar
Yarinya taci kwalliya Tazo tasameni tayi man
Sallama, Salamu alaika? Na6ata rai nace mata
Wa'alaiki salamu, Sai tace naga Malam naga
kamar kana cikin damuwa kozan tayaka fira? Sai
nasha kunu Na daure fuska Nace mata Dan Allah
malama kirabu dani kona Ce maki Ina Son mutun
yataya ni fira ne?
6ace man dagani ko kuma nayi maki wula kanci,
Sai tayi murmushi tace Allah ya baka hakuri Sai
munsake haduwa Natabbata idan kadaina fushi to
zaka saurare ni Saboda ni kyakykyawa Ce, Sai
nayi tsaki Naja motata izuwa gida, Ranar da Su
Dady suka shirya zasu Bauchi zuwa kar6o aure
na Sameera ji tayi gabanta nafadi kamar wani
Abu zai sameta Su dady suka isa Bauchi Amma
su Kansu sunji ajikinsu kamar zasu ga Sameera a
bauchi Saboda suna isa Bauchi tunanin Sameera
ne kawai ke yawo a zuciyar su, Ita kanta
Sameera Baccin data danyi na mintoci Har
mafalki tayi wai sun hadu dasu dady Da mom da
kuma ni Lokacin Da muka isa harabar gidan su
Manasa Kowanne Acikinmu gabanshi bugawa
yake Muna Isa Falon Kawai Sai naga,,,,,
Muna shiga falon gidan su Manasa Sai Mukaga
Manasa Tafito ban daki Sai kunya ta kamata A
guje tatafi dakinta Sai nacewa dady Wannan
Wadda taruga Itace Manasa Sai dady yayi dariya
Hajiya Ce taje tacewa Sameera Kada tasake
Tafito Kicin din indai tasan bata gama Abincin ba
Sameera ta Amsa dato Muna zaune Sai ga Abban
Manasa ya shigo suka gaisa da Mahaifana ni
kuma Natashi natafi dakin Manasa A wannan
zuwan da mukai gidan su Su Manasa Shine Aka
gama Komai har sukasa Ranar Aurena da
Manasa Wata daya ne akasa Saboda Dady Yana
so yatashi kasar England Har Muka gama komai
Muka tafi Sameera batasan Abinda ya faru ba Sai
bayan wuce Sameera ta gama girki Sannan
tasamu damar fitowa Daga kicin tana zuwa falo
Sai taji Ana Maganar Dame dame ya kamata ayi
A daurin Auren Manasa Da Muhammad Abdulhadi
Sai taji gabanta ya fadi har tanayiwa Manasa
murnar Saranta da akayi Manasa Cikin Fushi ta
iya Amsawa Saboda tatsani Manasa sosai
Sameera ahankali cikin kasala ta tatafi Dakinta
Tana zuwa dakinta tazauna tayi tagumi Sai Taji
sallamar Wani yaro An aiko shi ya kirata, Yana
shigowa Inda Manasa take Yace mata Sameera
kizo ana kiranki Awaje Sai tasha kunu Tace wake
kirana?.Sai yaron yace Wani mutimine Tana cikin
fadin haka Sai Ga hajiya tashigo Dakin tana fadin
Dan ubanki kitashi kije Abokin Rahul ne yake
kiranki Idan baki jeba Rahul Zaici Ubanki kuwa,
Sameera da sauri tatashi tatafi Saboda Tsoron
Rahul datake yi, Tana zuwa gum matashin dake
kiranta Mai suna Bala Sai tayi mai Sallama Sai ya
amsa mata tare dayin murmushi Sai tace malam
Don girman allah karabu dani wllh akwai Wanda
make so Buda bakin Bala Sayyace Waye kike so
Sai tace Inarunka dole Sai kaji sunansa?
Sai yace a'a Amma don girman allah Kitai maka
kifada Man Sai tace mai Sunansa Abdul-ahad Sai
bala ya zaro ido yace Wanda zai auri Manasar
Shine kike so? Sameera tace don Allah karufaman
Asiri wlh bashi bane Wannan nanine daban kuma
Ai anayin suna Iri daya Sai yace Hakane Amma
wlh Koki bar garinnan konace wa Rahul Saurayin
Manasa Shikike so, A guje Sameera ta shige gida
Saboda taji bala yace zai gayawa Rahul shiyasa
Sameera tayanke Shawar Barin gidan Sameera
tana zuwa daret tana nufa Dakinta Ta Hado
kayanta Duka Tasa acikin Leda Sai da ta fahimci
falon Bakowa Sannan Tayo waje da gudu .Sai mai
gadi ya tareta yace Mata Sameera Nasan kina
Shan Wuya acikin gidannan Garama ki gudu Ni
kuma zan taya ki da Addu'a Sameera a tsorace
tace mai Nagode tafita da gudu Ashe Bala wasa
yake mata Shikanshi baya jin dadin dukan da
Rahul yake mata, Sameera Tana zuwa tasha
Tasamu wani mai kudi Taroshi alfarma daya tai
maka mata da kudin mota Zuwa Zaria city
Mutiminnan Dubu 10,000 Ya bata Saboda tausaya
mata da yayi Ganin yadda tazo A gigice,
Ina zaune Dady Ya kirani Bayan mungaisa
Sayyace man My son Yau wata daya kenan
dagama gidajena na Kaduna Nawa da naka Don
kada Gidan da kake ciki nasiyar dashi Da Wanda
mu muke ciki don haka gobe kashirya da Sassafe
Nasa azo man da Tirela ta kwashe kayanmu duka
Sai naji dadi amma tsoran danayi Karmu bar
gidan kuma yaza mana Sameera tadawo gidan
nemanmu gashi dady yace kada Wanda ya fada
makowa Inda zamu zauna A Kaduna Gari
nawayewa Tirela Tazo ta kwashe kayanmu duka
A wunin muka gama Kwashe kayanmu Muka
koma Kaduna Su dady Suka zauna A Tudun wada
ta Kaduna Ni kuma Nazauna a Kawo A gidan
dazan zauna Nida Amaryata Sameera,
Satinmu Daya da komawa Sameera Bayan tabar
gidan su Rahul Gidan wata kawarta taje A jos mai
suna Fadeela Isma'il Satin ta ukku A gun Fadeela
dayake ta bata duk Labarin Abunda ya faru da ita
Sameera tayi matukar Tausaya mata Sosai
Shiyasa har bata so Sameera tatafi Watarana
tace ma Sameera Ya kamata muje Zaria Kudaidai
ta da Iyayenki da kuma Baffan Saboda kisamu
kiyi Aure kinsan Yanzu zaman aure shiyafi komai
Dadi Lokacin Da Sameera Sukazo Zaria sukatarar
da muntashi Adaidai wannan Lokacin Ake Daura
Aurena Da Manasa, Sameera tayi kuka sosai
Hakanan ta hakura ta koma Jos sukaci gaba da
zama da Fadeela,
Bayan aurena abokai Kowa ya watse Aduniya
banda iyayena Babu Wanda nake son gani Sai
matata Manasa Manasa tana Mani son Da bata
ta6a yiwa wani ba Shekararmu daya da wata biyu
Manasa tasamu Ciki Wanda ya kai munzalin
haihuwa
Watarana zani office Manasa tarakoni Izuwa
harabar gidana Sai nashafa mata cikin ta nace
Insha allahu Kafin nadawo Sai dai naji Anyo man
Waya ace kin haihu Sai tayi nurmushi tace Ameen
Sai nasunbaceta na ja motata nayi gaba,saneera
kuwa Sai Alokacin ta kara wayewa haduwarta da
fadeela ta koya mata Kwalliya Da salon tafiya Kai
idan baka san Sameera ba Sai karantse kace 'yar
shugaban kasace Watarana Sameera taje Super
market Sai ta hadu da Polina Polina tayi matukar
far in ciki da taga Sameera Bayan rungume Polina
tace Sameera wllh Kinyi kyau ko Gomna Ai
yaganki dole ya kyasa Sai polina tace wa
Sameera Kishirya kizo muje Kaduna gun Manasa
Wata kawatace wadda muka hadu a bauchi
Jikin Sameera yayi sanyi Sai taba Polina labarin
Zawanta bauchi Polina tatausaya mata Sai
tacewa Sameera karki damu ai yanzu kinfi karfin
Manasa tata6aki barinma mujinta yaganki Ai kau
Dole shima ya kyasa Sai sukai dariya Sukayan Ke
shawarar Gobe da safe misalin karfe shida zasu
wuce Kaduna Saboda basaso sukwana Sai
Sameera tacewa polina kinsan Inda Manasan Tayi
Aure?
polina tace Naje gidansu aka bani Address Din
gidan Ammace man Tana da ciki haihuwa yau ko
gobe Ahaka suka rabu akan gobe zasu hadu Sai
suwuce Kaduna, Gari nawayewa Sukakama
hanyar zuwa Kaduna Misalin karfe Ukku suka Isa
Kaduna Sai kai sa'a sukaga Gidan su manasan
Ananne Sameera taji gabanta nafadi Suna zuwan
falon Manasa Sai Sameera taci karo da Makeken
hotona wanda muka Dauka Da Manasa Ahotan
kamar zanyi magana Hankalin Sameera yayi
muguntashi.
MU HADU ANJIMA.
** CIKIN DARE Part 10 ******
Sameera tana tsaye tana kallon Hoton da mukayi
da Manasa shiyasanya hankalinta yayi matukar
tashi Wai Baffa na shine zai auri Makiya ta Lallai
kam za'ayi ta Abinda keyawo cikin zuciyarta
kenan Shigowar Manasa ne falon yayanke tunanin
da Sameera take Ciki
Manasa Tana Sakkowa kasa Sai suka hada Ido
da Sameera shiyasa hankalin Manasa ya tashi
Manasa na zuwa Tacewa Sameera meyasaka
kika zo gida na?
Sameera taja dogon tsaki Mitswww Tare fadin ai
yanzu daidai nake dake wlh Saboda yanzu ba a
karkashinku nake aiki ba Ehe,
Manasa tayi mamakin jin abinda Sameera take
fada mata Polina ce ta dunga ba Manasa hakuri
Buda makin Manasa Sai tace wa Sameera Bara
nakira mai gidana wlh Zakici Kutumar Ubanki
Shegiya Kawai Sai ta hau sama kirana polina
tacewa Sameera zomubar gidan nan Bansan haka
zata faruba Sameera tacewa Polina barta ta kira
Mijin nata shima daidai nake dashi yana bude
man huta nima Zan bude masa
Polina ta kalli Sameera tace lallai Sameera baki
da hankali, Ina Kishingide A makeken dagon dake
dake Dakina Manasa tashigo a firgice Tazo ta
zauna kusa dani tana kuka,
Sai na My dear Meya faru ne?
waya ta6a manke ne?
Sai tace man wannan shegiyar 'Yar aikin tamuce
tazo gidannan Shine take zagina don Allah my
dear kayi man wani Alkawari Sai nace mata
Manasa kifada buka tarki Insha allahu zan Cika
maki gurinki nayi maki alkawari,
Sai tace Baffa don Allah ina so Ka dakko mata
Police sutafi da ita Sai tayi 1week sannan Asake
ta kaji my dear na Sai nace mata karki damu
muje naga Shegiyar da tata6a manke,
Da suri Manasa ta mike Ina biye da ita abaya
A hankali na sakko Kasa
Kujerar da Sameera ta zauna tana Facing Waje
Ni kuma Banga Sameera ba bayan ta kawai nake
nagani,
Ina sakko wa Nace Ma Manasa acikinsu Wace
shigiyarce ta zageki Nanasa tace man gatacan da
Hannunta tayi man nuni,
Buda bakina cikin fada Nace mata Ke dan ubanki
kijuyo fuskarki jiki abinda zan fada maki Sameera
taki joyowa Sai nace mata Nan gidan ubanki ne?
Sameera tajuyo ahankali tare da fadin A'A
bagidan ubana bane, Ta juyowa naga Sameera CE
dama nayi ma wannan zagin
Ashe Itace 'Yar aikin da take shan duka a gidan
iyayen su Manasa
abinda keyawo daga kwakwal wata kenan,
Hankalina yayi matukar tashi danagan ta
Sameera tayi matukar kyau Kyenta ya kara
karuwa Gashi taci arniyar kwalliya kyenta ya fito
Buda bakin Manasa Sai tace man Baffa na
mekake kallo anan kaje ka dakko mata police
mana,
Cikin sauri da firgici nace TO To Nararimi Hula
nadorata akai ta kalminma barau da bawa nasa
Nafice a guje Ina zuwa kofar gida Nasamu wuri
nazauna Ina jiran Sameera su fito,
Manasa tayi jiran tayi jiran amma bandawo ba
Taita kirana awaya naki dauka Tun karfe 1:30pm
suke a gidana har zuwa karfe 6:00pm suna ciki
Idan Sameera Zata fita gidan Manasa CE kerike
ta tare da fadin dan ubanki kijira ya dawo mana,
da Sameera taga banda woba nan tabar polina
Tafito daga gidan lokacin data fito Manasa bata
saniba tana Kicin amma nasan data ganta to
bazata barta ta tatafiba har Sai na dawo,
Ina zaune Sai ga Sameera tafito daga gidan Sai
nayi sauri na mike duk jikina babu karfi Sameera
tana gani na Sai tayi kamar bata ganni ba zata
tafi
na janyo mata gyale natace mata Ina kuma zaki
batare da munyi magana ba?
Sameera taja tsaki Mitsww Dalla gafara can
kaban hanya nawuce
Abun mamaki wai yau ni Sameera takewa tsaki
Nadunga bata hakuri
Sai nace mata Sameera bara na dakko mota na
Muje gidan su Daddy
Tunda nasan farin ciki zasuyi idan suka ganki
Sai tace HMMMM Jeka dakko Motar A gigice na
shiga gida natarar da Manasa da polina suna firar
guduwar Sameera
komagana ban masu ba na dau key Ina fitowa
daga gida na tarar da Sameera bata gun Dana
barta
Muhadu gobe dan jin cigaban
**** CIKIN DARE Part 11*****
Bayan nafito daga gida na Sai natarar banga
Sameera a inda nabarta ba, Duk nakewaye
Unguwar nan ina ta tambayar Sameera Babu
Wanda ya San Sameera ballanta idan nayi masa
kwatan centa a ganeta Sai naja motata Sai da
nayi Nisa da gida Sannan nanemi gu na parka Na
kunna AC motata Amma duk da haka jikewa nake
da zufa hankalina yayi mugun tashi
Sai da nayi dana sanin Shiga gida nabar Sameera
a waje, Dakyar na iya Jan mota izuwa gida Ina
zuwa na zauna a falo Sai da nayi awa daya a falo
Amma Manasa duk bata San nadawo ba,
Can ta fito Sai ta tarar dani zaune Sai ta zauna
kusa dani, Sai tace man Darling Meke faruwa ne?
Naga jikinka yayi sanyi Nayi mata shuru Sai ta
kara ceman Darling Meyasa dazu baka dakko ma
waccan shegiyar sameerar Police ba?
Sai na harareta Jinai kamar natatta kata Don da
ta kara zagin Sameera a wannan lokacin to Sai
nayi Kasa kasa da ita, Sai bata kara ba Sai tace
man Darling ai Polina ta bani Address din gidan
da Sameera take a garin Jos Wlh Kauraye zan
tura mata har jos Naji dadi da maganar da tayi
man nacewa an bata Address din gidan da
Sameera take amma ban nuna mata cewa naji
dadi ba Sai nace mata Ki bani address gidan ni
dakai na zan dakko mata police Sai Manasa tayi
tsalle tace yawwa mujina Goben kenan zaka jos
din?
Sai nace mata Eh Sai ta rungume ni muka Wuce
daki, Ranar banyi Bacci Tun da sassafe nayi
wanka nace ma Sameera In zan tafi jos don na
daukar maki fansa, Bayan nayi Breakfas Na kama
hanyar zuwa gun Sameera misalin karfe 12:30pm
na isa Jos kuma nagane gidan da Sameera take
Sai natura yaro nace Kira man Sameera Nan
gidan Jim kadan yaron ya fito yace man ance
gata nan zuwa Sai nayi masa godiya Ina tsaye
Sameera ta Fito Muka hada Ido tajuya zata shiga
cikin gidan nasha gabanta cikin zauren Sai tace
man daga yau Sai yau bani baka, don idan kai ba
maye ne .miyasa ka biyoni har jos.lalle yau na
tabba kai babban sakarai ne.nache kabar wurin
nan.bana son ganinka.sai taja wani gogon tsaki
mtswwwwwww. Ji barka ko kunya baka da
ita.wai kai ka biyo sameera. To bari kaji yanxuh
ni dai dai dakai ce. Na bar gidanku zalinchi da
kake man ya isa.hakanan.yanxuh kana so ka
maidani gidan ku.kasa man hawan jini ko.to
Allah ya fika.
Nayi mamaki da sameera ke ta gayaman
maganganu.ammankawai Sai nayi murmushi ni
dai bakinta kawai nake kallo Sameera tana sona
Jan ajine kawai. .
sameera sai maganganu take gayama man da
habaice habaice.naga abin yana niyyar wuche
gona da irin.cikin katuwar murya na daka mata
tsawa nace YA ISAH SAMEERA nasan nayi maki
babban laifi amman ki sani bani nace ki gudu
kibar gida ba.
Nasan yanzuh zuciyar ki tsuma take ji kike kamar
kisa bakin gatari ki sassareni ki huta. Ki sani
nazo garin jos ne don na baki haquri akan abinda
ya faru.na durkusa kasa ina cewa sameera don
Allah kiyi hakuri ko Allah idan mukai mashi laifi
idan muntuba yana yafe mana.sameera badan ni
ba ko dan su mama da dady kiyi hakuri ki bini
zariya mu koma gida.
Na kaiki wajen su umma da dady ba karamin
farinciki zasuyi ba. Idan suka ganki. Sameera ko
kallo na bata yi ba ta juya fuskar daga gareni tai
shuru sai da nace kinji sameera sannan tace man
naji ka tafi zanyi tunani.sai ta shige gida ta barni
nan tsaye. Lakaci da ta shiga gida daidai lokachin
ne manasa matata ta kirani ta waya take ceman
darling naji ka shuru har kasa ankama wannan
shegiyar ko. Lokacin naji dama manasa na kusa
dani da sai make ta.saboda zagin sameera da
take. Kawai tsaki nayi na kashe wayar.
Manasa tai ta kiran waya ta amman ban
dauka.sai da naga 17 misscalls nata. Lokacin da
nadawo zariya misalain karfe 9:12pm nazo gidana
nayi sallama amman manasa tana jina taki
amsaman sallamar naje na bude dakina na
kwanta ina jiran manasa ta kawo man abinchi na
domin na dawo da wata mahaukachiyar yunwa
amman manasa shuru har kusan karfe 11:30pm
manasa shuru. Na tashi na bude kofa naje kitchin
naga ko zanga abinchi.ina budewa naga alamar
andafa abinchi amman an cinye ni ba'a aje man
ba.
Lokaci ne naje dakin manasa naga ta kwanta
amman itama ba barchi take ba.nace mata ina
abinchi na. Manasa tace nayi baki sun cinye.nace
abinchi na kika ba bakin. Manasa tace kwarai
kuwa ai bakon ka annabinka. kaje kitchin ka
sulala indomie kaci mana. Sai ta jawo bargo ta
lullube duka jinkin da fuskar ta. Lokacin ji nayi
kamar na kama manasa cikin daren nan nayi
mata shegen duka

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment