Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Zuhura iyakar sanina duk inda saki uku ya biyo bayan aure to baayi zaman dadi ba duk da cewa fadin Allah ne sai ya jarabci zukatan ma'auratan da mararin junansu amma fah naku yayi yawa kinasonsa fiye da tunani shima yana sonki amma ke kullum kina proud cewa ko rabuwa kikayi da Ahmad bazaki koma hannunsa ba, don Allah bani insha"
Girgiza kanta tayi tace “banson tuna baya a wannan lkcn Amma ba yanda na iya nayi Miki alqawari Kuma zan cika bijahi rasulullah kedai ki zauna kisha lbrn sarqaqqiyar dabaibayayyiyar qauna me cike da burgewa da ban tausayi, Suwaiba ki tanadi tisue domin tare hawayenki domin da kanki kika nemi zubarsu"






* 9-10*





Zama tayi bayan ta kawo Mata ruwa da abin tabawa tana nazarin ta inda zata fara taji an dafata, dago Idanunta tayi da suka canza kala ta ajiye numfashi tare da dauke qwallar idonta ta fara da cewa.



*_Waiwaye_.*



Fatima Abubakar Dandattu shine asalin sunana Alh Abubakar Dandattu shine mahaifina mun kasance mu bakwai ne a wajensa Wanda ya kasance Hajiya Rakiya itane mahaifiyarmu, Yaya Sani shine babba sai Yaya Yunus dake bi masa sannan Yaya Shamsu sai Yaya Hadi sai Autan maza Yaya Qasim sannan Aunty Naja'atu sai ni auta Fatima,
Dani da Aunty Naja'atu mun taso cikin gatan kulawar da bata sanyamu sangarta ba duk da kasancewar Babanmu bame dukiya bane Amma Allah ya hore masa zuciyar kula da iyalinsa harma dana wasu,
Kafin nan na manta ban sanar dake ba su babanmu su bakwai ne Suma Baba Abdurrahman shine babba sai Baba Uwa wacce take mahaifiya a gurin Yaya Noor su biyun nan dakinsu daya shiyasa na hade Miki lissafi a jimla yanda zakifi ganewa amma a lissafin haihuwa Baba uwa itace ta hudu domin kuwa Baba Abdulmuminu da muke Kira Baba me mota shine da na biyu a gidan dagaci Ummaru me turare sai mahaifina Abubakar shine na uku sannan baba uwa sai Baba Abdulqadir wadannan su ukun dakinsu daya wato babana da yayansa daya da qaninsa daya,
Baba Nuraddeen sannan baba zaibu wacce itace auta a gidan dagaci Ummaru me turare Suma dakinsu daya jimillar matan kakanmu sun Kama uku kenan, Ina fatan kina ganewa?"




Daga Mata kau suwaiba tayi tace “har nayi hadda Zuhurah ci gaba da lissafi"
Numfashi ta sauke taci gaba da cewa “baba Uwa da mahaifina Abubakar Dandattu suna da wata sihirtacciyar shaquwa da duk family babu kamarta har takai abin yana sosa zuciyar Baba abdurrahamanu saboda shi dama tun farko tasu batazo daya da babanmu ba, hakanne ya janyo suke takun saqa har takai ko gaisawa Basu cika yiba a matsayinsu na yan'uwa.
Lkcn da hankali ya ratsasu bayan mutuwar Ummaru me turare sai mahaifina yaso su dawo su hade kansu amma Ina abin yaci tura domin a lkcn Babanmu ya lura bawai dashi kadai Baba Rahamanu yake hamayya ba da dukkan yan dakinsu ne kasancewar sune suka lashe kaso mafi rinjaye na dukiyar da Ummaru me turare ya mutu ya bari,
Koda mahaifina ya matsa akan su dinke barakarsu gudan kada muma mu taso mu tarar da ita, haqansa ya gaza cimma ruwa a qarshen qarshe baba Rahamanu ya dubi tsabar idon babanmu da yan uwansa yace “Kunzo a bayana kun gaje komai da mukasha wahala da Tsoho muka tara hakan bai isheku ba yar uwartawa ma guda daya sai kun rabani da ita takai ta kawo batajin mgnta sai taka Abubakar" fasali yaja kana ya dora da cewa “hakane wannan damarku ce kaje nabar maka Uwa duniya da lahira karta qara kallona matsayin dan uwan da mukasha nono daya sannan Abu na qarshe shine zan aurar da uwa kamar yanda tsoho ya umarceni ga Alh Sadiqu"




Wannan taro ya tashi da hayaniya, azahiri ba kalamansa ne suka girgiza Fam ba aa mgnr auren Baba Uwa da Alh Sadiqu itace ta tashi hankalin kowa, sunyi duk me yuwuwa akan hana wannan aure Amma haqa ta gaza cimma ruwa ba komai yasa suke son hana auren ba sai ganin kwara da cutarwa qiri² kasancewar Alh Sadiqu amini ne ga Ummaru me turare wato kakanmu harma ana rade²n ya girmi kakanmu.
Sosai mamaki ya cika zuciyar Fam saboda su sanannune akan yanda tsoho yake da qoqarin tsayawa akan haqqin bani adamu to meye yaja ra'ayinsa akan hada wannan aure?"
Wannan tambaya ce da Basu da amsa haka sunaji suna gani Baba Uwa batason aurennan aka hadashi aka dauketa aka kaita gidan Alh Sadiqu cikin matansa uku da Kwantsin yaya sunfi talatin, Alh Sadiqu yayi aure aure sosai don a qiyasi ana hasashen ya auri mace sama da talatin kawai don yawancinsu basa haihuwa ne,




Hakanan baba Uwa tayi yan guje gujenta a qarshe dai Alh Sadiqu ya kafeta a gidansa shekararta biyu sai ga rabon ciki a jikinta haka ta rinqa haukan zata zubar da wannan ciki itace jiqa madaci jiqa kanwa jiqa gishiri amma ciki yaqi zubewa zamanin tsoron zuwa asibiti akeyi,
Babu Wanda baiyi Mata mgn ba taqi ji Amma ana fadawa mahaifina yaje har gidanta yayi mata fadan girma tana kuka tace “yaya wlh banason cikinnan na tsaneshi Amma tunda kace na barshi zan barshi amma da sharadin bazai rayu dani ba kaji shima Alh yaji idan na haihu zan bakashi ka tafi dashi ka hada dasu Sani sa Yunus ka riqe"
Babu wani jayayya Alh Sadiqu ya amince da wannan ta hqr ta haifemin fitinar rayuwata😭😭




Numfashi ta sake saukewa sannan ta dora da cewa lkcn haihuwa yayi Baba Uwa ta haifo danta namiji kyakkyawan gaske saidai baqine irin baqin fulanin Rano Ranar suna yaron yaci sunansa Nuraddeen sai Kuma me? Saiga baba uwa na cewa itafa abarta da danta idan ya Isa yaye ta badashi a babana, hakance ta faru taci gaba da rainon Nura har ya isa yaye ranar data yayesa kuwa ta hawo akori kura ta kawoshi gdanmu lkcn Ummah Rakiya nada tsohon cikin Yaya Shamsu haka ta karbeshi sukayi sallama ta riqeshi tamkar yayanta na cikinta babu wani babu wani bambaci da take nuna masa sai qauna da kulawa,
Wata daya da kawoshi Ummah ta haifi Yaya Shamsu daganan taci gaba da haihuwa har kawo kaina, Ummah tayi wani furuci ranar da aka haifeni lkcn Yaya Noor yanada 12 years bama ya gida yana kasuwa aka tashi dan aike domin a fadawa baba haihuwata kafin dan aiken ya dawo Yaya Noor ya dawo gda tana ganinsa tace.
“Miskili kafi mahaukaci ban haushi duk haihuwar da nakeyi ko barka baka taba yimin ba yanzun meye ya kawoka?" Tace sai kawai ya sosai Kai yana dariya yace “matata nazo gani" wannan kalma tabawa kowa mamaki aikuwa tundaga wannan rana wannan kalma ta zauna a bakin Fam tun Ina jaririya haka ake kirana Matar Nura Sai ya kasance sunan da mahaifina ya radamin ya bace bat dangi gaba da baya matar Nura sukece min shikuma Yaya Noor yana Kirana da Zuhurah dole iyayena ma suka maya bakinsa suke kirana da Zuhurah.




Kowa yana mamakin kulawar da Yaya Noor yake nunamin duk da dayawa suna daukan kalamansa shirme na quruciya amma ayyukansa suna bayyana gaskiyar girman yanda ya dauki lamarina Yaya Noor yanayin kuka idan Ina kukan yarinta na quruciya idan Ummah tayi masa mgn sai yace shifa baisan sanda yake hawaye ba idan yaga dama Ina kuka kawai yanajin kamar wani Abu nake buqata banida damar fada.
Haka zai miqe ya rakito wancan ya hado wannan duk ya hargitsawa Ummah gda don farin cikina ni kadai idan kuwa naqi Shiru to kuwa kudi kona uban waye zai dauka ya saceni mu fice daga gdan yaje ya kasomin bazai dawo dani ba sai yaga ina dariya
Miqewa Zuhura tayi Suwaiba ta riqota tace “ya zaki tashi Zuhura kin fara sanya idona tsiyaya Wai dama ana haka da gaske?" Kallonta tayi ta qaqalo murmushi me kama da yaqe tace “tun yanzu Suby ai baki fara kuka ba zan duba abinci ne na sauke haqqin me gda kada na shagala Allah ya hukuntani da hukuncin da yafi wannan wlh Suby haqqin Yaya Noor yake bibiyar rayuwata ya hanani kwanciyar hankali, ki dan jirani kadan kada ki gaji so nake kiyimin alqalanci keda me karatu.....




*FREE 11-12*



Bata jima ba ta dawo ta zauna tana duban Suby tace “haka rayuwa taci gaba da tafiya duk wani farin cikin Yaya Noor ya ta'allaqa ga farin cikina walwalarsa tawace kukansa nawane tsayin shekaru bakwai, zuwa lkcn na fara zuwa makaranta sukuma sunyi candy Baba yana nema musu ta gaba an gama yi musu komai har Jamb sun zana Yaya Noor da Yaya Shamsu Kuma duk sun samu amma kash...
Sai Alh Sadiqu yayi gardama yace shifa wannan karon a qyalesa yayi iko da dansa ai yayi kara, Koda Baba yaje sai yake fadawa baba karatun Islam zasu tafi Tumbuktoo dake qasar Mali shida yan'uwansa,
Sosai baba yaso yaga ya shawo kan Alh Sadiqu amma abin ya faskara a wannan lkcn Yaya Noor ya Kama wata matsananciyar rashin lfy duk likitocin Kano sun tabbatar da babu abinda yake damunsa Amma sai ramewa yakeyi yana tsotsewa daga qarshe ne aka gano ashe damuwar nesa dani da zaiyi ne yasashi yake wannan ramar cikin dare Kuma yayita firgita yana kuka yana Kiran sunana idan Baba ya tambayeshi sai yace gani yakeyi ana qoqarin rabasa dani.




Nikam baa sanar dani tafiyar ba sai wayar gari nayi na daina ganinsa da fari na shiga damuwa abin har ya shafi karatuna Amma daga baya sai Baba Rahamanu yabawa babana rubutu yace abani na dangana ne, aikuwa na dangana don saida komai daya shafi Yaya Noor ya bace bat a kwanyata kamar wankin ruwa na manta dashi da duk wani Abu daya shafeshi,
Baba da Ummah sunji dadin hakan shima Yaya Noor da aka fada masa yaji dadi saboda bashi burin rashinsa ya sanyani cikin matsala shidai ya yarda ya rayu tsayin shekaru bakwai din da zaiyi cikin damuwar rashina, Suby haka abubuwa sukayita tafiya har nakai matsayin secondary SS 1 sai a lkcn ne Yaya Noor ya dawo hutunsa na farko a Nigeria, abinka da kyakkyawa yaqara kyau yayi haske sosai saidai baiyi qiba ba saima rama da kamar idona ya nunamin yayi lkcn daya dawo Bai wucce gidan babansa ba saboda ya qudurce a ransa ni zai fara gani acikin dangi aikuwa burinsa ya cika ya isheni sanye da Airmles iya gwiwata Ina shanya a tsakar gda na wanke panties dina da bra na kasancewar Allah yayimin garin jiki don wasu madauka suke nice sama da Aunty Naja'atu, saboda cikar halitta ta,




Banyi aune ba sai kawai ji nayi anyi sama dani ya qanqameni yana dariya yana cewa “burina ya cika My Zuhr ke nayi burin gani Kuma ke na fara gani na gdewa Allah daya tsaremin kena tarar dake cikin kyakkyawan yanayi" hmmmm wani abun al'ajabi mai Kama da almara Suby sai na bude idona tar akan Yaya Noor inason gane inda nasanshi amma na kasa ke da na matsawa kwanyata da tunani ma sai ta nemi yin bombing ai babu shiri nayi baya da sauri Ina haki nace “Ummah waye wannan?"
Tambayar tawa saida ta sanya Yaya Noor sakin jakarsa yayi saurin zama saboda baitaba tsammanin hakan ba, sake kallon Ummah nayi nace “wlh bansanshu ba Ummah wai shidin waye?



*FREE 13-14*




Kallon kallo suka tsaya sunayi da Ummah da baba dashi kansa Yaya Noor din da jikinsa yake rawa qwanjinsa ya miqe, a Fam dinmu muna da wani sign na wata jijiya a tsakanin sumar kanmu da goshinmu da indai muka shiga tashin hankali itace alama ta farko, tabbatar tashin hankalinmu ya ta'allaqa ne da wannan jijiya to shima Yaya Noor yanada ita nan take ta fito sosai a goshinsa, ya bude baki kamar zaiyi mgn Kuma sai ya fasa ya miqe ya dauki jakarsa ya shiga dakinsu shida Yaya Shamsu,
Shiru tsayin lkc bai fito ba hakan yayi daidai da fitowar Yaya Shamsu daga wanka yace “Ina Nuran yake Wai meye yake faruwa naganku dako dako haka" Bai samu amsa daga gurinsu ba saini ce nace “yawwa Yaya Shamsu wai waye wannan da yazo yanzu nifa na kasa tunashi shikuma yana nuna yama dade da sanina"



Ga mamakina shima sai naga yayi kasaqe yana kallo na dake shi irin mutanen nan ne masu tsarge gsky komai dacinta sai kuwa cewa yayi “Eh mana butulu ai kinkai moro dole kice kin manta da Nuraddeen ai dama na fadanku ni tun farko da kuketa murnar yarinyar nan bata damu da rashin Nuraddeen ba nace muku ku kuma zaku damu a gaba"
Shigewa daki yayi nabi bayansa da kallo tare da tabe baki ashe shikuwa Yaya Noor tunda ya shiga dakin babu abinda yakeyi sai kuka da safa da marwa kamar qaramin yaro, dafashi Yaya Shamsu yayi yace “kaifa kanada matsala kaima Noor bansan meye yasa ka cika zafafawa akan lamarin wannan banzar yarinyar mara tuna alkhairi ba kutmar ubancan waifa ta manta dakai tace! Kai wlh wannan qaryane ma bama zai taba yuwuwa bane Noor dama ace ni tace ta manta saina yarda amma kaidai tace ta manta ka, haba kowa yaji yasan qarya ne"




Cije lebe Yaya Noor yayi ya dafa kafadar Yaya Shamsu yace “har cikin ranta take cewa waye wannan bansanshi ba Ummah waye? Shamsu abinda yake wasa daga farkon farashi zaka gane wasane, da gasken gaske Zuhurah takeyi ta mantani" daga haka bai Kuma cewa komai ba ya fice daga gdan Baba yanata jiran dawowarsa Amma Shiru Koda ya kirasa a waya sai yace shi bazai iya zama Ina kallonsa matsayin baqo ba.
Kwanaki uku ban sanyashi a idona ba nama manta da babinsa na shiga wata sabgar daban dake lkcn muna gaf dayin saukar qur'ani a islamiyyar mu hankalinmu yanakan bikin saukar dagani har Aunty Naja'atu munata qissima irin kyaun da mukeso muyi ranar sauka, ranar wata laraba munje kasuwa tun safe da Ummah siyo mana kayan sauka ashe mu munacan bamusan wainar da ake toyawa a gida ba,




Qarfe uku muka nufo gdan dukkanmu a gajiye muke musamman ma ni me garin jiki tafiya kadan ke wahalar dani, Ummah nata yimin tsiya Wai auta ta cika raki nikuwa sai zumbura baki nakeyi haka muka shiga gda da sallamarmu sallamar da ta maqale a maqoshinmu ta kasa samun lamunin fitowa,
Kinsan meye ya maqalar da sallamarmu Suby? Zuhurah ta tambaya, da sauri Suby tace “aa inajinki don Allah ki tafi a miqe ki daina kwana kwana" murmushi tayi me hade da hawaye tace “masomi kenan, mutane muka gani cike da gidanmu dangin babanmu matan yayyansa da qanwarsa Baba Zaiba a cike taf da tsakar gidanmu sunata hidindimunsu ga maqota nan sai kaiwa da komowa sukeyi,
Haka muka qarasa jiki a sanyaye idona yakai inda naga matan unguwarmu sun duqufa duba wani Abu kawai sai naga manyan akwatuna ne guda goma sha biyu kowannensu shaqe taf da kaya na gani a fada sunata dagawa suna "ahhh lallai Masha Allah Nuraddeen yayi qoqari Allah dai yabada zaman lfy yasa yin na Allah ne" tunda naji an ambaci Nuraddeen sai gabana ya yanke ya fadi na tsaya Ina kallon kowa daidai can wata budurwa Zuwai Abokiyar wasana ta makoni tace “Matar Nura kina sha'aninki yaudai Allah yayi aure da mara kwabo kin tabbata matar Nura kedai ke kika dace da miji bashi ya dace da Mata ba wlh"



Ban fahimci komai cikin kalamanta ba duk tunanina wasan data saba yimin ne don haka nace “nifa Zuwai kina damuna da surutunku na yan qauye ke bakinki ko ciwo bayayi ne?" Ina fadin haka Ina shigewa daki kawai sai jinayi ana fesheni da turare na rintse idona da sauri Ina Kai duka Ina cewa Allah zanci uban mutum banason hauk...."
Ji nayi an rufemin baki anci gaba da fesamin turaren tsintar kaina a wata duniyar laushi ta musamman ya sanya bakina mutuwa kasala ta maye gurbin zafin Raina, Saida aka gama feshemu da turarukan sannan matan suka fice daga dakin aka barni dagani sai shi sai lkcn na samu damar sauke ajiyar zuciya tare da bude idona kawai sai naganni kwance luf a faffadan qirjinsa, na kuwa zabura da sauri nace “subhanallahi meye hakan dinne wannan ma ai iskanci ne dama bakasan haushinka nakeji ba ranar nan kazo ka wani dagani a gaban su Ummah shine yanzu zaka rungumeni a gaban mutane wannan wanne irin haline na yahudawa" nayi tunanin yanda na haqiqice Ina zuba masa masifar zaisa yaji haushina amma maimakon hakan sai naga ya qara natsoni naja da baya da sauri ya cafki hannu na yana murmushi yace “kiyi hqr My Zuhr a baya dai nasan bakya fushi da Yaya Noor dinki ko kin manta?" Kawai sai sunan ya rinqa dawo min nace Yaya Noor! Yaya Noor!! Saida na maimata yakai sau biyar sannan yace “Yes kin tunashi?" Kawai sai naji hawaye sun wankemin fuska nace “Yaya Noor ai ya mutu..." yanda nayi furucin ya sanyashi dagowa da mugun sauri yace.



“Inji wa? Wanne maqaryacin ne yace miki na mutu bayan gani a gabanki matsayin da tunda aka haifeki na dauki kaina a matsayinsa a gunki wato miji Fatima kina hauka ne ke kina tunanin zan mutu batare da wannan burin nawa ya cika ba, waima meye ya goge Miki hadda akaina ne meye ya mantar dake ni dago Fatima dago ki kalleni sosai Zuhurah wlh nine Yaya Noor dinki babu abinda na canza saima rama da kalamanki na ranar dana dawo suka sanya ni"
Dagowa nayi na zuba masa ido sai Kuma nayi qasa da kaina saboda bazan iya jure kallon qwayar idonsa ba na tabe baki nace “tabdi waima miji kaidin injiwa zaka zama mijina qaryar banzan kare a gadar kura wlh Kama daina wannan mgnr donni sai nayi Masters sannan zaayimin aure......






*FREE 15-16*



Zubamin ido yayi yana kallon yanda nake motsa dan qaramin bakina zuciyarsa tana tariyo masa lkcn da Ina yar mitsitsiyata abar tausayi dani amma Wai yanzu gani har tsiwa nakeyi masa, mgnr da mukayi dazun nayi masa yawo wai Yaya Noor ya mutu to waye yace min ya mutu Kuma meye yasa akace min ya mutu?
Bai lura da ficewata ba saida yaji Baba yana cewa Ina nuraddeen din me yakeyi a cikin dakine Kamar mace, sai sannan ya samu qarfin gwiwar fitowa yabi kusurwar da nake zaune da kallon na jefa masa wani kallon tsana, wlh Suby har cikin Raina nakejin tsanar Yaya Noor, ji nayi Baba yana cewa “Auta idan kin gama rashin kunyar kizo inason ganinki" miqewa nayi nabisu Ina qunquni baba ya shiga dakin soro shida Yaya Noor nima nabi bayansu na rakuye a wani saqo Ina wasa da yatsun qafata,



Wuccewar mintuna biyar tabawa Baba damar gyaran murya tare dayin yan addu'o'insa sannan ya fara bayani da cewa “Fatima dake zan fara saboda kece bakisan meye yake faruwa ba" Shiru yayi sannan yaci gaba da cewa “haka Allah ya tsara Fatima idan baki manta ba shekarun baya nayiwa dan'uwanki alqawarin aurenki kafin Allah ya nufeshi da tafiya makaranta..."
Dagowa nayi da sauri Ina kallon Baba yace “hakane to abinda ya faru jiya ba me dadi bane babanku Rahamanu yaso ya taba martabar wannan tsohon alqawari ta hanyar Kiran Nura ya bashi auren yayarki Zaliha inda shikuma Nura ya kafe akan ra'ayinsa saike so wannan dalilin yasa mahaifinsa da mahaifiyarsa babarku Uwa suka nemi alfarmar tunda girmanki yakaiki a daura aurenku kawai inyaso sai yabarki anan ki qarasa karatunki kafin ya dawo, Zuhurah keda Nura duka nawane wannan dalilin yasa na amince na daura aurenki dashi...."



Dagowar da nayi a firgice ce tasa su dukka dagowa Suma na kalli Yaya Noor kawai sai nayi baya luuuuu ni a kankin kaina bansan yaushe na farka ba Suby tun daganan asalin wasan ya fara, sabuwar tsana da jin zafin Yaya Noor ya darsu a zuciyata ko ganinsa banson yin idan kuwa na bari na gansa din to babu kalma daya da zata shiga tsakaninmu sai harara kawai.
Hakanan muka dafa a dafe mukayi saukarmu iyakar rawar gani Yaya Noor yayimin a sha'anin saukar amma bangani ba qarshe daya dan matsa min ma akan hoto yanaso muyi hoto naqi ya takura sai munyi da alamun bacin rai a fuskarsa yace “abinkin nan yawa yake qarayi kullum. Zuhurah nifa mijinki ne Kuma yayanki yakamata ko banci arzikin zumunci ba naci na aure ki daina yimin wannan jisgin banajin dadinsa" batare da nasani ba na dago a zafafe nace “to dama na fada maka inayi don kaji dadi ne? Karkaji dadin mana Ina ruwana da jin dadinka ko dole akace ka rinqa matsata niwai Kai wanne irin mayene Kai a dangi ne me nacin masifa...."



Haka naci gaba da zazzaga masa masifa ta inda na shiga ba tanan nake fita shikuma yayi sukuti yana kallo na da fuskar mamaki cikin ransa yana rayo sanda yake daukana a towel ya kwantar dani yayita kallona lkcn da bazan iya hassalawa kaina komai ba Amma yau gashi Ina cinye masa mutunci kawai saboda quruciya irin tawa.
Lkcn dana gama yimasa tujara ta na fice daga soron gidan namu kawai sai na tarar da matasan unguwarmu da muke gaisuwar mutunci dasu Ina fita wani Yaroro yace “Yawwa Zuhurah zo muyi hoto" aikuwa kamar me jira na saki jiki mukayita daukan hotunan tarihi ashe Baba yana ganina shida Yaya Noor, Suby Yaya Noor irin mazan nan ne masu baqin kishi nandanan kamanninsa suka sauya jikinsa ya fara rawa ya zubamin ido yana kallona,
Takaicinsa da baqin cikinsa shi a matsayinsa na halaltacce ya roqi muyi hotunan naqi harma Ina jifansa da mugayen kalmomi amma a banza da auransa a kaina nazo na shiga cikin wasu yan' iskan yara sai yi mukeyi, ganin hakanne ya ankarar da Baba ya tura wata yarinya yace ta kirani, Ina mitar katsemin jin dadi na taho gabana ya fadi ganin yanda gabadaya kamannin Yaya Noor suka canza jikinsa yake rawa.




Qoqarin durqusawa nake naji yatsu a kuncina na tafi hutun kwatan lkc kwanyata ta tafi tunanin wanne me hikimar shammatar ne ya shammaceni haka, ban lura da hannun da nake ba saida na tsinkayo muryar Baba yana cewa “da aurenki Zuhurah kika biyewa yan iskan yarancan a gaban mijinki kuke irin wadannan hotunan ubanme zasuyi da hotonki wai meye ma hadinki dasu ne?" Sai yanzu na fahimci ashe wannan azababben marin daga Baba ne, tsawa ya sake dakamin yace “kuka nace kiyimin ko mgn?" Jikina ya sake daukar rawa na bude baki zanyi mgn sai naji Yaya Noor ya qara matseni a jikinsa ya sauke wata ajiyar zuciya me qarfi alamun ya jirge, yace
“ayi hqr Baba banzaci zai batanka raiba shiyasa nabarta amma bazaa qara ba" numfashi na sauke me qarfi jin ya dauki laifin ya dorawa kansa, nandanan kuwa Baba ya hau kansa da fada ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba yana cewa dama duk wata sangarta da iya shege da auta takeyi koyinka ne to gashinan kaidin ma bata qyale ba sai kaje kayita goyon bayan qarya nidai babu ruwana" Yana gama fadin haka fuuuu ya bar soron hakan ya bawa Yaya Noor damar sake matseni a jikinsa yana sunsunar wuyana yana lumshe ido tare da huramin numfashinsa da yake fita da sauri da sauri,
Nayi saurin tsayar da kukana na hada qarfina da nufin tureshi amma ni sai ya turani dakin soro ya faki ido ya fado ciki shima ya saki labulen, tuni cikina ya fara kartawa saboda tsoron wannan yanayin nasa gabadaya jikinsa tsuma yakeyi yana wani lumshe ido yana qoqarin kamoni Ina janyewa ina shirya yanda zan fice daga dakin amma ya hanani damar gashi daidai lkcn aka kece da wani ruwa me qarfi ta yanda ko nayi ihu babu me jina a gida da waje.




Ban ankara ba naji ya janyoni yana qoqarin hadani da jikinsa na rintse idona jikina yana karkarwa kamar mejin dari na zame na zauna a qasa naci gaba da rera marayan kukana inajin haushi da tsanar Yaya Noor na qara kwaranya a cikin ruhina nace “Allah ji nakeyi kamar na kasheka Yaya Noor don Allah kada kayimin komai ka budemin qofa na fice...."
Bansa meye ya rufemin bakina ba saiji nayi numfashina yana sama sama na fara qoqarin bude idona kawai naga ashe Bazar dani yayi a tsakar dakin kan dadduma yayimin rumfa da faffadan qirjinsa Kuma ya dora bakinsa saman nawa yasa hannunsa daya ya dafe kaina dayan kuma ya dora a saman qirjina saitin boobs dina Amma a

Please Login or Register in order to submit comment