Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai na quntata masa naje na buga gdan dake yamma ce yazo ya bude Ina tafe daqyar na shiga gdan ya biyoni da sauri yana fadin.




“Zuhurah Ina kika shiga tun jiya ake nemanki?" Murmushin takaici nayi na miqa masa yaron da yaketa mamular hannu yasa hannu ya karba babu ko riga a jikin yaron da dankwalina na nadeshi na juya zan fita yayi saurin shan gabana yace “danane wannan Zuhurah ya akayi kika haifeshi bai Isa haihuwa ba?" Hawayene ya zubomin nace “saboda banason duk wani Abu daya shafeka a tare dani Nura ga tsiyarka nan kasan yadda zakayi da ita"
Ina fadin haka na juya na fice ya biyoni da sauri yace “ki tsaya Zuhurah na kaiki gda bakida qarfi fah" ko sauraronsa banyi ba na fice daga gdan na hau sahu ya qarasar dani gda Ina zuwa na tarar dasu sunyi dako dako suna ganina sukayo kaina kowa nayimin kallo baibai Ummah ce tace “Zuhurah Ina cikinki?" Ban bata amsa ba sai zama da nayi Ina haki ta sake nufoni daidai lkcn da Yaya Noor ya shigo dauke da jaririn dan watanni bakwai dukka sai sukayi kansa ya qaraso ya miqawa Baba yaron yace “takaimin shi Baba bansan me take nufi ba" kallona baba yayi ya nufoni da yaron na tashi da sauri nayi baya luuuuu jini na dibana zan fadi Ummah tayi saurin tareni tana sallalami nace “wlh Baba banida wata alfarma da zan iya yiwa yaronnan da ubansa idan yaga dama ya mayar dashi inda ya fito dashi nikam mun rabu har abada idan ya rayu na barmasa duniya da lahira idan bai rayuba Kuma dama haka nake...."



Wata fuzga Baba yayimin ya kwadamin mari yace “ubanki yaci uwatar mahaukaciyar zamani dan uwarki kanki aka fara mutuwar aure da zakije ta qarfin tsiya ki raba yaro da ma'ajiyarsa sannan kikai masa shi to ubanme kikeso yayi masa tunda kema uwa kin kasa" maimakon na rusuna saima na qara hawa na shige daki na kullo bugun duniya magiyar duniya naqi budewa yaron sai numfarfashi yakeyi duk suka rude bama ya Yaya Noor da yake kuka kashirban yana kiran sunana yana cewa “zai mutu Zuhurah ki taimaki rayuwar danki bakida tabbacin sake samun wani anan gaba kada kiyi abinda zakiyi nadama mara amfani a gaba Zuhurah kada kibari rayuwar yaron nan ta salwanta ki taimakeni ko dumin jikinki yaji zai samu sassauci...."
Hmmmm in kinajin asalin kunne uwar shegu to shi nayi musu duk Wanda ya Isa ya fada ya fada ni kaina a ranar bansan Ina imanina ya tafi ba Shiru ta ratsa na wani lkc ashe duka akan yaron suke can naji Yaya Noor ya rushe da kuka yace “burinta ya cika ta kashemin dana a karo na biyu ta zubarmin da cikin wata hudu ta kashemin cikakken da dan watanni bakwai Allah kafi kowa sanin komai Kaine me sakayya Allah ka sakamin, ya mutu Baba ya mutu shikenan na rasashi shima baniga tsuntsu baniga tarko na rasa Mata na rasa dana wayyohhhh rayuwata Allah kayimin sakayya"........



*P 49-50*




Shiru naji sunkumayi sai shassheqar kukan Yaya Noor lkc zuwa lkc daga baya naji baba yana cewa “bai mutu ba Nura akaishi asibiti su sashi a kwalba idan akayi saa zai rayu" daga haka naji gdan yayi tsit hakan yabani damar bude qofa na fito kamar dama Ummah jirana take ta cafkoni da qarfi ta hada kaina da bango jini ya balle hakan baisa ta qyaleni ba taci gaba da dukana kamar Allah ya aikota daqyar Baba Uwa da Yaya Yunus suka qwaceni.
Ta dubeni tace “tur da baqar zuciya irin taki Zuhurah kekam kin shiga uku mugun halinki da aqidarki ta rashin yafiya ashe tananan baki barta ba yanzu me dan cikinki yayi miki da zaki dauki fushin ubansa ki sauke akansa kinje kinyi qoqarin kasheshi ta qarfi Allah baiga damar ya kasheshi ba shine kika sabi wata hanyar to wlh indai kinason mu shirya dake kibi Nuraddeen asibiti ki karbi danki ki raini abinki idan ba hakaba kuwa to kema ki sake uwa nikam na yafeki...."



Jikina yayi sanye amma zuciyata ta kasa rusuna Ina kuka Ina maqale jikin baba uwa nace “wlh Ummah banason Nuraddeen da duk abinda ya shafeshi bana fatan wani Abu nashi ya rabeni balle ya rinqa jin yanada wata alaqa dani dama dansa ne Kuma nabasa abinsa nikam na yafe masashi har abada bana buqat....
Mazga Ummah ta sake kawomin baba uwa ta riqe hannunta tace “ya Isa haka Sa'adatu ki daina dukan Zuhurah anyi Mata abinda ya kamata ta nuna fushinta Kuma ba itaba koni bazan riqe masa dansa ba ni da na haifeshi kenan yaje ya kaiwa wacce ya zabi rayuwa da ita ta riqe masa" duk yanda Ummah taso fahimtar da baba Uwa abin ya faskara nan Ummah tayi rantsuwa akan bazan zaunanta a gda ba muddin ban karbi dana ba inda take Baba Uwa ta shiga daki ta dauko akwatuna tajani muka fita,
Baiwar Allah me son zumunci ashe tun ranar da Baba yaje ya fadawa Alh sadiqu abinda ya faru Baba Uwa ta biyo Baba ranar Alh Sadiqu ya saketa itama, wani qaramin gda muka nufa asalin gdan na Yaya Noor ne ya ginashi tun Ina shekara bakwai yake cemin gidanki ne anan zamu zauna kafin Allah ya bani ikon Gina Miki babba, ashe anan ta dawo da zama muna shiga ta budemin daki guda na shiga komai anzuba Mata harda A.C nasan duka aikin Yaya Noor ne nikam dakin data bani harda TV da katifa qatuwa ko ledarta baa cire ba.




Kallona tayi tace “kwanta bari na dafa ruwa na gasa Miki jikinki yo ni nataba ganin wannan zalumci a dakeka a hanaka kuka Allah dai ya saka Miki wlh iyayenki basuson gaskiya duk mutumin qwarai ai yasan an zalinceki yarinya qarama dake ya mayar dake bazawara" tana fada tana komai ta kunna gawayi ta dora qatuwar tukunyar Almunium ta cikata da ruwa.
Har bacci ya fara daukata ta shigo ta tasheni muka shiga bandaki tanamin wankan Ina kuka saima data zuba sabon ruwan zafi tasani na shiga ciki wayyohh nan ne na gane banida wayo ashe gurin tsami yayi naci kukana Baba Uwa na dannani tanamin sannu bayan ta gama gasani muka koma ciki ta yaga tsumma me kauri tabani nayi amfanj dashi ta hadamin shayi me kauri ta zauna ta rinqa bani inasha daqyar Ina gamasha kuwa na dawo dashi wai ashe yunwa ta shigeni ta gyarani na koma na kwanta da zazzabi me zafi a jikina.




Fita Baba Uwa tayi ta kulle gidan bata dade sosai ba ta dawo ta siyomin duk wani Abu da tasan me jego zata buqata, tanata yimin sannu Ina kadanta Kai da dare Ina kwance nade da bargo naji muryar Yaya Noor gabana ya fadi amma sai na dake ya shigo har parlourn yana Shirin shigowa dakin Baba Uwa ta fita tace.
“ya akayi? Zama yayi yace Mata “na ajiye aikina na Mali na zan tafi qaro karatu Misra Uwa don Allah ki shiga mgnr nan subani matata inafa da sauran dama akwai malaman da sukace saki uku cikin kalma daya zaa iya barinsa a guda daya" bata katseshi ba saida ya gama ta dubesa tace “dama taqamarka kenan shiyasa kayi saki uku? To bazaa barshi dayan ba" inajinsa yanata yimata magiya Amma tayi biris dashi qarshe ma ta tashi ta shigo daki ta mayar da qofar ta rufe.




Dole haka Yaya Noor ya tafi jiki babu qwari tun daga wannan ranar banqarajin lbrn yaron ba bansan ya akayi dashi ba haka na wanzu a gdan Baba Uwa batare da Yaya Noor yasan inda nake ba zaizo gidan naji yanata yimata magiya yana kuka da idanunsa duk wata kafa ta ganina an kulle masa yakance shi bashida wani maijin tausayinsa a rayuwarsa nan da yakesaran jin qai ankasa jin qansa can Kuma gdansu Alh Sadiqu ya matsa masa lamba cikin biyu sai ya zabi daya yayi aure kodai Uzaira yar Baba Rahamanu ko Kuma Zaliha yar abokin Alh Sadiqun.
Shikuma zuwa lkcn zuciyarsa ta fara rauni wajen boye abunda ke cinta Allah sarki Yaya Noor har susucewa yayi a wannan karon yana tafe yana sambatu idan mgn akayi masa da sunana zai amsa kowa sunansa Zuhurah a wannan karon, zuwa lkcn nima Kuma sai Allah ya jarabceni da tausayinsa lkcn da nayi arba'in na fara dawowa hayyacina kewar Yaya ya da nadamar abinda na aikata ta fara nuqurqusar zuciyata kullum cikin damuwa nake inajin yanzu da ace banyi sanadin salwantar rayuwar dana ba da ko arziqinsa zanci nake ganin Yaya sai hawaye ya zubomin nakan yini Ina kuka.
Ranar wata asabar tun safe baba Uwa tayi asubancin tafiya Rano saboda wata rasuwa da muka tashi da ita naso na bita tace nayi zamana bangama yin qwari ba sannan kowa fushi yakeyi dani saboda labarin abinda na aikata ya fantsama duniya bama iya bakin dangina ba hakan yasa tace na bari komai ya qara lafawa.




Ina kwance a daki Ina bacci ashe na manta ban kulle gdanba daidai lkcn Yaya yazo unguwar mamaki ya cikashi ganin gdan a bude ya shigo gdan yana dube dube ko Ina baiga kowa ba hakan yasashi shiga parlour ganin inda akayi break yasashi sanin lallai da mutum a gdan a hankali ya bude dakin ya leqa ya hangeni kwance qudundune da bargo mamaki ya cikashi a ransa yana tambayar kansa to waye a gdan dama Baba Uwa ba ita daya bace?
Matsawa yayi jikin gadon yana qaremin kallo kafin yasa hannunsa a hankali ya janye bargon sai ya zubamin ido cike da farin ciki ya zauna kusa dani Wanda qamshin turarensa ya sabbabamin tashi mukayi ido biyu na miqe zaune da sauri tare da ja baya na yayumo blanket na rufe jikina kasancewar rigar bacci ne kawai a jikina wata ajiyar zuciya ya sauke me qarfi ya matso jikina sosai ya kafeni da idanunsa da suke narkar dani yanata matsata Ina janyewa har mukaje qarshen bangon ya janye blanket din da qarfi nayi saurin dunqulewa waje daya jikina sai rawa yakeyi,





Nayi tunanin rufeni zaiyi da duka Amma sabanin haka sai naji saukar ruwan hawayensa a kafadata na dago da sauri nima hawayen ne da ban shirya fitarsu ba suka zubomin kawai banyi aune ba sai jina nayi a jikinsa ya sanya duka qarfinsa ya matseni yana sunsunar wuyana cikin rikitar yanayi yace “Ma...matata Ina....sonki don Allah kada ki yarda su rabamu dauriyata ta qare akanki zan iyayin komai nasan kinaso na kema........
Ashe duk zancen baka nakeyi qarya nakewa kaina da nake cewa banason Yaya Noor yanzu ne na fara sonsa, Suby sai na shige jikinsa na rushe da kuka me qarfi Ina lalubar kansa da hannuna na dora hannuna a tsakiyar kansa Ina shafa bayansa nace “Yaya haka ka shekara sama da goma kanaji a kaina ashe haka so yake Yaya Noor me nayi maka ka yankemin wannan hukuncin meyesa ka zabi yankemin hanzari ta hanyar datse igiyoyin aurena dakai meyesa Yaya Noor meyesa ka zabi fifita bare ka sakeni sakin wulaqanci akanta ka cutar dani Yaya ka tursasa zuciyata ta koyi sonka da qaunarka sannan kayi watsi dani, yanzu ya kakeso nayi kenan Ina na Kama a rayuwata ta gaba Ina dana Yaya ka bani dana don Allah........




*P 51-52*



Bansan ya akayi ba saiji na nayi a qasan Yaya ya hade bakina da nashi yanayi masa wata fitinanniyar tsotsa wadda ta sanya numfashina daukewa na kasa hassala komai na daga qoqarin hanashi har ya dire bakinsa a tsakiyar qirjina yaja wani numfashi tare da bude idonsa akaina idona a lumshe suke suna zubar da hawaye amma inaji a jikina ni Yaya yake kallo.
Na yunqura da niyyar miqewa sai ya sakemin nauyinsa tare da sanya hannunsa biyu ya damqi nonona da suke a cike tamtsam da ruwa muka saki numfashi a tare tuni na manta da mgnr sakin dake tsakanina dashi kamar yanda ya manta na tura masa kan nonona a bakinsa ya cafka da sauri yana sha da salonsa me haukata tunani yana wani irin nishi me shiga jiki da ratsa kwanya nikuma inajin zafin yanda yake zuqar nonona yana hariyar yawu Amma nakasa hanashi saima dafe kansa da nayi,
Wasa ya fara nisa saiga harshen Yaya a HQ na yana lasarsa da saurinsa yana karkada hannunsa Ina janyewa a hankali saboda zafi nakeji bansan ns meyene ba kuma yanzun na fara dawowa hayyacina na fahimci barnar da muke Shirin aikatawa na fara qoqarin hana afkuwar wani Abu amma na makara domin yallabaina yakai geji sai nishi yake yana lalubar HQ na yana hawaye yana cewa.




“Inasonki Zuhurah wlh tallahi babu abinda ya Isa ya rabani dake har yanzu ke matatace bazan iya rayuwar farin ciki babu keba....Ohhhhh Zuhr ki bani dama muyi rayuwar da tafi ta baya dadi"
Da wadannan kalaman Yaya ya yaudareni muka aikata abinda har gobe nake kuka akansa bayan komai ya lafa naci gaba da kukana inajin takaicin biye masan da nayi shikuma yanata rarrashina da kalamansa da har gobe suke tsinkamin lakar jiki da haka yajani mukayi wanka tare sai gashi na ware nice harda tayashi wanka na manta da abinda yake cin zuciyata,
Suby tun daga wannan lkcn muke rainawa iyayenmu hankali suna can shanye da baki akan cewa Nura baisan inda Zuhurah take ba nan kuwa ko yaushe muna tare da kaina na bawa Yaya damar yaje ya fadawa baba cewa akwai sauran aure tsakaninmu muka tafi wani malami yabamu wata fatawa me rauni cewar idan anyi duba da wani qauli me rauni zamu iya komawa matsayin ma'aurata tunda munason juna Kuma a cikin kalma daya akayi saki ukun,




Mukayita murna duk da Yaya yasani yasan komai Amma dake a yanayine na neman mafita hujja yake nema komai qanqantarta sai ya dauki qafa da raunanan hujjojinsa ya nufi rano saboda zuwa lkcn baba ko saurararsa bayayi yaje ya samu dagaci da mgnr Baba Muminu yayi shiru yana nazari ganin zamu shigar dashi cikin dimuwa yasashi nemo limamin masallacin garinmu da wasu manyan malamai yayi musu bayanin abinda yazo masa dashi.
Take Mal Liman ya cancelling na wannan tawili da cewa “zamanin manzon Allah (S.A.W) an samu irin wannan cukumurdar har takai ga cewa anyiwa muminai na wancan zamanin sassauci game da hukuncin saki uku cikin kalma daya akace idan mutum ya saki matarsa cikin halin fitar hayyaci madamar ba wani abin gusar da hayyacin yasha ba to bata saku ba, idan Kuma tsautsayi ya gifta yayi saki uku cikin kalma daya to barinsa a daya shine yafi dacewa idan dama yayi daya a baya yazo yayi biyu a hade to zaa dauki saki dayan baya a dauko daya a Wanda yayi yanzu a mayar dashi biyu idan sunaso su koma aurensu da igiya daya, idan ya sakeyin daya to shine aure ya haramta"




Dakatawa Mal Liman yayi Yaya Noor yacika da farin ciki can Kuma Mal Liman yace “amma lkcn khalifancin sayyadina Abbakar (R.A) wato bayan wafatin ma'aiki (S.A.W) sai sake sake ya yawaita saki uku da kalma daya ya zama ya cika gari sannan mutum sai yaje ya saki matarsa idan an koma gefe yace ai baya cikin hayyacinsa wannan dalilin yasa aka zauna meeting na gaggawa Khalifofi da sauran yan majallisar Ma'aiki suka canza wannan hukunci ta hanyar amfani da ayoyi da manyan hadisai da suka sauka bayan zartar da wannan sassauci Wanda ya zamana cewa indai tsautsayi yasa ka saki matarka saki uku da kalma daya ako wanne irin yanayi Kuma komai son da kake Mata to ta haramta gareka harsai tayi aure wani namijin ya kusanceta tsautsayi ya gifta ya saka sannan zata halatta gareka, wannan shine abinda muka sani game da wannan jumurda Allahu warasuluhu a'alamu"
Tashin hankali kenan tunda Yaya ya sunkuyar da kansa babu abinda jikinsa yakeyi sai rawa daqyar ya iya dagowa idonsa ya kada yayi jajir yace “yanzu bakuda wani taimakon da zakuyi mana wlh munason junanmu bazamu iya jurewa wannan yankan qaunar na qaddara ba"



Haushine ya cika Baba Rahamanu yayi dariyar mugunta yace “to yanzu da hukuncin Allah kake jayayya kome Nura yaudai naga qarshen soyayya banda masifa me Zuhurah tafi sauran Mata ka qwallafa ranka akanta tun tana tsumman goyo anbaka qanwarka Uzaira kace aa anbaka zaliha kace aa to yanzu ai dole tasaka kaje ka nemo a duniya ka aura itama Kuma dole tasa ta auri wani abinda kakewa ya zama halalin wani muga ta qaryar so"
Duk da Yaya a lkcn baya cikin nutsuwar fahimtar kowacce kalma Amma kalaman Baba Rahamanu sunyi masa ciwo dayake bashi da lkcnsa sai ya miqe ya shiga mota ya nufo Kano ikon Allah ne kawai ya kawoshi Kano ya tsaya a Baico hotel ya kirani lkcn na fita kuwa naje kitso da lalle yace nazo na sameshi a Baico.




Yanda naji muryarsa yasa jikina yayi sanyi anayin kitson na tafi banyi lallen ba na hau sahu ya saukeni na shiga ciki ashe tsautsayi ya gifta Yaya Lawan yazo wuccewa a Napep dinsa ya ganni, Ina shiga na fadi number dakin aka nunamin hanya na nufa na qwanqwasa ya bani izinin shiga na iskeshi kwance rigingine ko takalmi bai cire ba jikina ya qara sanyi na zauna kusa dashi nace.
“Yaya babu nasara ko?" Miqewa yayi daga kwanciyar da yayi ya dubeni sosai yace “babu Zuhurah na rasa ya zanyi da rayuwata inason tursasawa zuciyata hqr dake na kasa ya zanyi Zuhurah ki fadamin ya zanyi?" Ya fada yana jijjigani na shige jikinsa na fashe da kuka cikin kukan nace “duk Kai kaja mana Nuraddeen ya zamuyi hqr kawai shine yafi mana tunda haka ka zaba mana.
Zuba mata ido yayi yana furzar da iska me zafi yace “bazan iyaba Zuhurah Abu daya zamuyi duk da Ina kishinki Amma Babu yanda zamuyi haka qaddara ta zaba mana zan kawo miki Miki kiyi aure....." Bai qarasa mgnr ba saboda bugun qofar da mukaji anayi na tashin hankali na miqe da sauri shima ya miqe tare da furta waye?" A zafafe mukaji murya baba yace.........





*P 53-54*



Kallon juna mukayi ni da Yaya Noor gabanmu dukkanmu na faduwa idona ya ciko da qwallah daidai lkcn da aka qara dukan qofar Baba yace “wai Nura bazaka bude bane sai ranka ya baci..." Da sauri ya bude qofar kamar dama baba ya saita ya daukeshi da mari yace “ashe kaima haka ka zama Dan iska bansani ba ashe gaskene da ake cewa dani ana ganinku a wasu gurare nake musawa turr da wannan rayuwar da kuka zabawa kanku, waima kanku aka fara mutuwar aure ne?"
Cafka Baba yakaimin ya watsani waje yana me nuna Yaya Noor da hannunsa yace “tunda kazama dan iska kada na qara ganin qafarka a gdana daga yau na yanke duk wata alaqa dakai har sai Zuhurah tayi aure" yana gama kora masa ya fito shida Yaya Lawan Yaya ma ya biyosu baba ya dakamin tsawa na shiga adaidaita muka tafi gida.




Muna zuwa gda sabbin dokoki suka hau kaina ciki harda ta tafiya ta karatu Niger American University a cewar baba wani ubangidansa ni yakeson aurena harma yace masa idan na amince a daura Amma ni a Niger zan zauna saboda harkokinsa sunfi acan.
To dake dama neman mafita muke Kuma faduwa tazo daidai da zama ban jaba na amince inda amincewar tawa tabawa kowa mamaki, da dare nake fadawa Yaya Noor a waye cikin qaraji naji yace “what?" Sai jikina yayi sanyi na Kama kuka shima hakan ya sanyata mass jiki yayi qasa da muryarsa yace “bazan iya jure ganinki da wani ba Zuhurah amma banida yanda zanyi na dawo dake gareni dole sai hakan ta faru karki damu dani kiyi aurenki Amma don Allah kiyimin alqawari daya tak"
Da sauri muryata na rawa nace “wannene Yaya?" Shiru yayi kafin ya busarda iska yace “kiyimin alqawarin sau daya tak zaki amince da mutumin nan sannan kiyimin alqawarin wata daya zakiyi a gidansa ki dawo kiyi idda mu mayar da aurenmu"



Numfashi na sauke batare da tunanin komai ba nayi masa alqawari mukaci gaba da hirarmu Ina kwantar masa da hankali daqyar na samu ya saduda, abin mamaki wai kwanaki uku dayin wannan mgnr saiga su Yaya Shamsu da Yaya Lawan sun shigo gida wai daga Rano suke gurin daurin aurena,
Hakanan gabana tayi kwance² ta fadi cikin razani na shiga daki na Kira number Yaya Noor yana ganin kirana ya daga yace “Baby gabana yau sai faduwa yakeyi na rasa meye yasa" numfashi na sauke nace “Yaya an daura fah" da sauri yace “me...me aka daura?" A sanyaye nace “auren..." Wani salati da Yaya ya saki kawai saijin faduwarsa nayi can naji Baba Uwa tana Kiran “dannan Kai dannan meye haka..."
Daga haka ban sakejin komai ba wayar ta yanke na miqe Ina safa da marwa zuciyata na gurin Yaya Noor inason fita naje naga halin da yake ciki Amma Babu hali da canma an hanani fita balle yanzu Ina cikin wannan zulumin naji sallamar wasu manyan mutane uku su Yaya sunata masu sannu da zuwa aka shimfida musu darduma qatuwa suka zauna suka gaisa dasu Ummah da fara'a.




Can naji wani cikinsu yace “Mama wannan shine Alh Lukman shine surukin naku" gabana ya fadi sosai Ina tsaye Amma Saida na zauna kafin daga bisani naji Ummah tace “Allah Sarki ya iyalin naka?" Amsawa naji yayi da cewa “lfy Lau suke" can Ummah tace “bari a kiranku ita tana ciki"
Miqewa Ummah tayi ta shigo dakin ta isheni na hade Kai da gwiwa sai kuka nakeyi ta gallamin harara tace “hqr shine ya kamaceki da istigfari na sabonki da kikayi ki tashi kije suna jiranki" Shiru nayi ban bata amsa ba ganin zanzo da tsalle yasata dakamin tsawa tace “banson iskancin ki Zuhurah ba qananun mutane ke jiranki ba" ganin ranta ya baci yasani miqewa na dauki hijjab dina na fito,
Daqyar na gaishesu suka amsamin da fara'asu ganin babu kowa yasa wannan sarkin azagwaigwai din fara yimin bayani a zahiri sauraronsu nake Amma a badini zuciyata tana gurin Yaya ganin basuda niyyar sallamata na miqe zan shiga daki sai lkcn Alh Lukman ya magantu da cewa “bakiji ba?" Tsayawa nayi ya miqe inda sukuma suka fice ya matso bayana dake dogone ya kereni sosai ya sunkuyo ya sanya hannunsa ya dago fuskata.




Hawayen da naketa shanyewa suka zubo a kuncina sai ya sakeni da sauri yace “Sorry please bansan bakiso ba dama inason nace Miki ki shirya gobe zamu wucce wani Abu na gaggawa ya tasomin na fadawa Baba harma ya fadawa wadanda zamu tafi tare dasu saboda ganin guri.
Yana fadin haka ya zaro kudi masu kauri 10 back 1500k ba qaramin kudi bace ya bani yace nayi gyaran jiki ban karba ba saiya ajiye min nikuma na shige daki na fada gado na rushe da sabon kuka, Suby kinsan meye yake sani kuka? Kawai tunawa cewa yanzu fah shima Alh Lukman jin kansa yakeyi a matsayin mijina.
Idan na tuna haka sai na sake fashewa da kuka qaddara tayimin yankan qauna mutum daya nakeso a matsayin nan duk duniya gashi yayi wasa da damarsa, inanan kwance naji yara suna shigo da kaya shirgin kayan abinci da qwalam sai wani qaramin akwati yaron yace ance abani Wai abinda nake buqata baby na kirashi na fada masa.




*P 55-56*



Ummah ce ta karbi kayan ta shigomin dasu dakin lkcn Ina kwance zazzabi ya rufeni bata kobi ta kaina ba ta fice hakanan na qarasa yinin har dare yayi bani da walwala da safe na tashi da sabon tashin hankali ashr wai tun jiya da na Kira Yaya Noor na fadinsa daurin aurena yake asibiti ya samu heart attack,
Wai Suby zo kiga tashin hankali s gurina nayi duk me yuwuwa na samu naje na gansa Amma yan cikin gda sunqi bani dama lkcn dana gama shirya yanda zanyi in fita lkcn Alh Lukman yazo da drivernsa akan dole na hqr da fitar Ina kukana mecin zuciya na rabuwa da masoyin gsky da ban qara tantance babu madadinsa a duniyata ba sai a wannan rana haka Baba yasani a gaba da fada² nasiha² da yayi iya isarsa Kuma ya Kama hannuna baba Uwa itace a gaba wajen kaini sabon gidan mijina dake qasar Niger Sai baba Iyannan qanwar Ummah.




Hakanan Ina kukana Ina komai muka isa airport muka hau jirgi sai Nymie lkcn da mukaje duhu ya fara drivernsa na nan yaje ya daukomu ya kawomu gidan wayyoh Basu baba uwa

Please Login or Register in order to submit comment