Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nasa dadin ya haqa sosai shima ya zubar da nasa ruwan kana mu huta.




Wannan nishadi daya bani ya mantar dani komai muka shirya muka fita cike da annashuwa bamu dawo gdanba sai dare muna zuwa abinci kawai mukaci muka kwanta bacci washegari da asuba wayar Yaya tayi ring kamar baya dagaba nice ya daga ya daga ashe Baba Rahamanu ne suka gaisa sosai yana tambayarsa ni yace Ina bacci sai naji yayi ajiyar numfashi dake wayar a free take yasa naji sanda yace “qanwarka Uzaira ce take asibiti ciwon zuciya ya kamata" da sauri na miqe shima ya miqe yace “for what?" Numfashi Baba Rahamanu ya sauke yace “sabods sonka da qaunarka data rayu dashi Kuma ta lura wannan makirar yarinyar ta dauke maka hankali baka kallon kowacce mace sai ita Nura ka dawo cikin hayyacinka kasan inda yakeyi maka ciwo wlh Abubakar da iyalansa harma da Zuhuran ba son Allah da annabi sukeyi maka ba dukiyar ubanka suke hari idan ya mutu kunci gado qanwarka Uzaira itace ke sonka domin....."
Dakatar dashi Yaya yayi da cewa “don Allah ya isa baba waini meye yake damunka ne da rayuwata da iyalina matata tanasona inasonta Amma duniya tasamu a gaba kowa so yake yaga ya cutar damu to nifa gsky banson haka Baba kaja mutuncinka akan iyalina zan iya batawa da kowa Kuma aure da Uzaira wlh banyi ba kuma zanyi ba Kai nifa na Zuhurah ne ita kadai insha Allahu...."




Baba Rahamanu bai gamajin kalaman Yaya Noor ba ya kashe wayarsa gabadaya nanfa Yaya Noor ya rinqa masifa bansan ya iya fada ba sai ranar nikam bance masa komai ba domin Raina ya baci sosai bantaba tunanin haka dangi suke kallonmu ba game da Yaya Noor sai yau da naji daga bakin Baba Rahamanu jikina yayi sanyi, daqyar na tashi na fito na fara ayyukana Yaya da yayi wanka yazo ya kamamin yanata kawarmin da damuwa to kasancewata bamai riqe abu araiba tuni na manta mukaci gaba da rayuwa,
Munci gaba da gudanar da love dinmu me ban sha'awa Ina damuwa da damuwar mijina shima yana damuwa da damuwata komanmu tare mukeyi takai har office wani lkcn dani yake tafiya cikina kuwa na qara girma har ya shiga wata na shidda yanashan tattali da kulawa hatta motsi idan yayi sai Yaya ya tambayeni me babynsa yake buqata,
A lkcn ne Kuma al'amura suka qara lalacewa duk da muna qoqarin nunawa juna babu komai Amma fah a zahiri da koman nidai yanayin dana shiga a baya na firgici da razani shi na qara shiga idan Yaya Noor yana tare dani na rinqajin zafin zuciya dana jiki na rinqajin kamar na kurma ihu ga cikina da nakejin kamar ana kartata ta ciki ciwon mara ya hanani sakat, kullum cikin damuwa nake na qara lalacewa na fige sai ciki a gaba.
Lkcn da cikina ya shiga wata na bakwai wata rana bana mantawa ranar data zamo mafi muni cikin ranakun rayuwata wacce banjin zaa qara yimin kamarta da dare Ina kwance na yini Ina ciwon ciki dan har Suma na rinqayi ranar Yaya ya shigo jikinsa a sanyaye ya kalkeni muka hada ido sai naga ya kawar dakai yacemin.




Ki shirya gobe idan Allah yakaimu zaki tafi 9ja ciwonnan naki yana buqatar kulawa nikuma wani uzuri zai kaini California kafin na dawo lkcn haihuwarki yayi kinga saiki haihu a gda idan na dawo sai mu dawo" wayyohhhh Suby zo kiga murna a gurina har rawa nayi saboda murna Yaya ya zubamin ido yana kallona ga mamakina sai naga ya share hawaye ya dauki key din daya dakin ya fita na tsaya sororo kamar dashe Ina tunanin wannan canjin,
Zuwa lkcn nakai mace don haka nayi wanka na shirya na feshe jikina da turare na fito na nufi dakin na bude na shiga gabana ya fadi ganin Yaya a kwance yanata rawar sanyi na matsa da sauri nace “yaya meye hakan bakada lfy baka fadamin ba...." Dagamin hannu yayi yace “kije ki kwanta don Allah saida safe" na zaro ido zanyi mgn ya miqe tare da dakamin tsawa yace “fice nace Zuhurah ki qyaleni naji da abinda yake damuna Zuhurah mutuwa zanyi na rasa komai nawa ki fita nace!"
Yanda yake mgnr jikinsa na rawa yana nunan hanya saina firgita gani nake idan na tsaya dukana zaiyi na fice da sauri na koma dakina na kulle Ina haki Ina kuka naje na dauro alwala nayita nafila saboda nariga na saba da kwana jikin mijina bazan iya bacci baa jikinsa ba ranar ban rintsa ba kamar yanda Yaya bai rintsa ba da asuba nayi sallah na shiga dakinsa ga mamakina ya gama kammale kayansa tsaf ya dubeni fuskarsa a daure yace “kin shirya?" A tsorace nace “a...eh na hada kayan tun jiya" ajiyar zuciya ya sauke ya fita ya shiga dakina ya dauko kayana muka fita yajamu a mota har airport muna zuwa jirgi na qoqarin tashi akayimin duk abinda ya dace nidai duk jikina a sanyaye na juya zan tafi Yaya Noor ya riqo hannuna ya doramin wata envelope yace.




“ki kulamin da bebyna don Allah saboda arzikin zumunci kada ki bude envelope dinnan sai kinje gda kin kwanta kin huta kinji qanwata na fadawa Yaya Yunus zaizo ya tareki a airport"
Murmushi nayi masa tunanina gift ne na soyayya daya saba bani lkc zuwa lkc na Kama hannunsa nayi kissing nasa na juya na shige jirgi da sauri cike da shauqin qaunar mijina.
Muna zuwa Aminu Kano International airport Yaya Yunus ya daukeni sai gda shima cike da shauqin ganina yanata zolayata inata murmushi Amma hankalina na gurin mijina, muna isa gida Ummah ta rungumeni tanata nannan dani tana auta meye yake damunki kika rame haka kwanaki naga da Noor ya turowa Shamsu hotunanki kinyi qiba abinki" murmushi nayi kawai ta hadamin ruwa nayi wanka hankalina nakan envelope dinnan fah inayin wanka naci abinci nace ni kwanciya zanyi Ummah tace “to kije ki kwanta mana" shiga nayi na kwanta na dauko envelope din na sunsuna na sauke ajiyar zuciya saboda qamshin turaren Yaya Noor danaji na rintse idona kamar yanda yake cemin duk lkcn da zai bani gift Ina yan waqoqina “Oh My darling I love you..." Na yaga envelope din tare da bude idona wata qaramar takarda ta fado ban damu da meyene a cikinta ba hankalina yanakan wani kyakkyawan kati me kama da Invitation na daukoshi duk tunanina yana bani wasu kalamai ne masu tsada ya bugamin a jiki domin debe kewa, idona yana arba da rubutun da akayisa da ruwan zaiba na miqe da sauri Ina karantawa cikin kidima,
Kinsan meye a jikin katin Suby? Katin gayyatar daurin auren Yaya Noor ne da Asma'u wanda aka daura qarfe goma na safiyar ranar dana taho 9ja, katin ya subuce nima nayi zaman yan bori jikina yana tsuma zuciyata tana harbawa a dari da tamanin nakai hannuna ga qaramar takardar dason ganin meye a jiki ni a tunanina zai rubutamin April fool a jiki dake muna watan April ne Amma Ina wani rubutune da yayi sanadin katsewar numfashina" cikin wani kuka me gigita tunani tace “Suwaiba rubutune kamar haka a jiki
_“NI NURADDEEN SADIQU ATTAJIRI, NA SAKI MATATA ZUHURAH ABUBAKAR DANDATTU SAKI UKU BATARE DA NASAN DALILIN SAKIN BA"_



*P 45-46*




Sakin takardar nayi nayi wata miqewa da bansan a rayuwata zan iya irinta ba aikuwa jiri ya debeni nayi kasa na saki qara me qarfi tare da faduwa kasa luuuuu cikin daukewar numfashi da fitar hayyaci Ummah tayo dakin a guje har tana jifa da buhun garin tuwon dake hannunta suna rigen shiga ita da Yaya Yunus suka rufu a kaina suna Kiran sunana Yaya Shamsu ya dagoni cikin tashin hankali yaga jini yanabin cinyata a razane ya kalli Ummah yace “jini take fitarwa Ummah"
A azama Yaya Yunus ya fita sai gashi sun dawo da Yaya Lawan ƴan  takife ɗin gidanmu kenan suka could ciccibeni suka sanyani a sahun Yaya Lawan dukkansu suka fita harda Ummah ya rage gdan daga Yaya Shamsu sai Yaya Sani babban yayanmu sai Aunty Naja'atu har sun juya zasu fita Yaya Shamsu yayi bal da invitation din da yake cikin jini ya tsaya yana nazarinsa inda idonsa ya qara kaiwa ga takardar  zuciyarsa ta qawatu dason ganin abinda ke ciki domin yanada yaqinin shine ganina na qarshe kafin na shiga wannan yanayin.
Ya kuwa sunkuya ya dauka hankalinsa yafi karkata a takardar da yaga anyi rubutu da manyan baqi to Koda canma tsiya mukeyi masa na bai iya karatu a zuciba ya bude murya kuwa yace.


_“NI NURADDEEN SADIQU ATTAJIRI NA SAKI MATATA ZUHURAH ABUBAKAR DANDATTU SAKI UKU BATARE DA SANIN DALILI BA"_
tashin hankali wai gobarar gemu dukkansu sai suka kalli juna Yaya Sani zuciyar Mata gareshi kawai sai jiri ya debeshi ya zauna daɓar a qasa yana furta "Innanillahi wa Inna ilaihirraji'un Allahummah ajirnih fih musibati wa'akalifni khairin minha" shima Yaya Shamsu zama yayi inda Aunty Naja'atu ta karbi invitation din ta fara dubawa tuni kuka ya qwace Mata tace.
“Innanillahi Yaya NURADDEEN wannan wanne irin wulaqancine da tozarci kayiwa qanwarka jinin jikinka wadda kake iqirarin ba'ayi kamarta ba bakuma zaayi ba wannan wanne irin lkcne me cike da qunci da tashin hankali? Wannan wanne irin mugun ganine ashe dama abinda ka shirya kenan ka turomana ita gida ashe dama saboda zakayi aure kayi Mata wannan sakin wulaqancin Ina hankalinka Yaya Noor Ina tunaninka suke Hasbunallahu wani'imal wakil wannan rana! Wannan rana!! Wannan rana!!! Saki uku Zuhurah ga tsohon ciki dole ki shiga kowanne irin yanayi don Allah qanwata me kikayiwa Yaya Noor wlh hankalina yaqi daukar babu dalili yayi sakinnan..."


Tana gama wannan mgnr ta fada jikin Baba dake shigowa tace “shikenan Baba tafaru ta qare qanwa taqi aurennan kuka dage har Kuna dukanta akansa yanzu ga tukuicin halaccinku nan yayi muku Allah ya isanmu wlh Allah ya isan qanwa ya lalata Mata rayuwa ya kashe Mata burukanta na rayuwa sannan ya hadata da ciki ya sakota sakin tozarci saki uk....."


Baba da yakasa gane inda batun ya dosa saboda shi kiransa Yaya Lawan yayi yace masa yazo gida babu lfy Zuhurah na asibiti rai a hannun Allah shine dalilin zuwansa, dubansu yayi yaqa qaratan yayan nasa madaka qato dukkansu suna sharar hawaye yace “ta mutune?" Miqewa Yaya Shamsu yayi yace “ba gare mutuwa ba akan wannan wulaqancin da wannan dan iskan yayi mana saki uku a Zuhurah me tayi masa ta cancanci wannan wulaqancin?"
Zama Baba yayi ya karbi takardar dake hannun Yaya Sani farko invention din ya fara dubawa yagani ya girgiza Kai tare da cije lebe yakai dubansa ga takardar sakin ya karantata a zuci, ji yayi zuciyarsa taqi lamunta hakan yasashi karantowa a fili
_“NI NURADDEEN SADIQU ATTAJIRI NA SAKI MATATA ZUHURAH ABUBAKAR DANDATTU SAKI UKU BATARE DA SANIN DALILI BA"_  tuni Baba ya zabura ya miqe yace “eh lallai ne shege bai gaji halacci ba wato ni Nura zaiciwa mutunci na dauki yar nabashi a mutunce ya wulaqantata ya dawomin da ita babu komai zai gane yayi da dan sunnah wlh tallahi muddin Ina raye Zuhurah tabarshi har abada kamar yanda ya yanke shawarar barinta Allah ya sauketa lfy" 



Yana gama fadin haka ya juya fuuuuu ya fice yana hada hanya Allah sarki uba na gari mahaifina ya shiga tashin hankali da wannan sakin wanda hakan yayi sanadiyyar girgizar zumuncin mu domin kuwa Baba yana fitowa gdansu Nuraddeen ya nufa ya tarar da Alh Sadiqu a zaure anata fadanci ya shiga Koda ganinsa sai Alh Sadiqu ya miqe saboda yana ganin girman Baba sosai suka gaisa hawaye ya zubowa Baba yace.
“Alh kanada masaniyyar cewa Nuraddeen ya qara aure?" Babu wani alamun jin nauyi Alh Sadiqu yace “eh ya fadamin shekaran jiya wani abune?" Kallonsa Baba yayi da mamaki yace “aa babu komai Amma nasan qila bai fada maka cin mutuncin daya shirya yi mani ba ko?" Da mamaki Alh Sadiqu yace “name fah?" Hawaye Baba ya Kuma sharewa yace “ya turomin Zuhurah yau da asuba ya kirani yacemin zata taho saboda batada lfy shikuma zai tafi California so na dauka abin na arziqi ne ashe ba haka bane yanzu Ina kasuwa aka kirani nazo Zuhurah tana halin dimuwa data fitar da fitar da ita daga hayyacinta sannan tana zubar da jini yanzu haka suna asibiti, hakan yasani rufe shago na taho gida Ina zuwa na tarar da sabanin tunani Nuraddeen ya yanke alaqar aure tsakaninsa da Zuhurah kwata² ta hanyar yimata saki uku batare da wani dalili na shari'a ba ba sakin ne yafi damuna ba domin nasan idan zama ya qare babu tsumi babu dabara Amma yaronnan dake ba dan mutunci bane bai duba girmana da darajata da Kuma arziqin zumunci ba saki uku Alh Sadiqu saki uku a yata ta cikina Nuraddeen ya iya rubutashi?"




Abin mamaki maimakon Baba yaga Alh Sadiqu ya shiga damuwa sai yaga yayi murmushi yace “to banda abinka Alh Abubakar kanka aka fara? Ai kawai kayi hqr yana da dalilinsa qila yar taka batada tarbiyya ne zata dagansa hankali akan aurensa shikuma yaga hakan itane kadai mafita saboda haka nima banji dadi ba Amma sai abawa zuciya hqr idan da rabo gaba a sake haduwa...."
Baba Uwa ce ta fito daidai lkcn da Baba ya miqe ya kalli tsohon nan yace “Ah haba Sadiqu rabo kuma? Hmmm ai rabo kuma ya qare indai da jininka ne wlh ko zan mutu saina sharewa Zuhurah hawayenta dama ba arziqinka Nuraddeen yaci ya samu auren Zuhurah ba arziqin qanwata yaci ki daina kuka Aishatu muna tare ke tawace har abada Amma dakai da danka billahil lazi la'ilaha illah huwa babuni babuku har gaban abada Sadiqu jini ai baya qarya tabbas Nuraddeen yayi mugun gado shikam tunda ya gado baqin halinka da zararka to zai kuwa qare da gindi a waje kamar yanda ka qare, Kuma a rashin tarbiyyar ta yata tayi maka rana nima da banida tarbiyyar nayi maka sannan nayi masa....."



Yana fadin haka ya juya zai tafi Baba Uwa daketa kuka tace “Yaya don Allah ka tsaya kayimin bayani wlh bansan komai ba" kallonta kawai yayi ya fice da sauri ya ta biyosa da gudu Amma baiko kalleta ba ta zube a qasa tana kuka tana cewa “nikam wannan rikitaccen al'amari ya isheni meye yake faruwa ne me Nuraddeen ya aikatawa Yaya haka....?"
Ta bayanta taji ance “to meye kawai fah don yaqara aure Kuma ya sako masa yarsa shine yake wannan kumfar bakin...." Baba Uwa bata gamajin wannan tashin hankali ba ta zabura ta miqe tana “innanillahi wa Inna ilaihirraji'un Alh wannan shine kawai wacce shegiya ya aura ya wulaqantamin ya haka Hasbunallahu wani'imal wakil wannan masifa dame tayi Kama...." Miqewa tayi ta shiga ciki ta zaro mayafi tayi waje Alh Sadiqu yana kallonta baice Mata qalaba ta tari dan sahu ta nufi unguwar Hausawa zoo road cikin saa ta tarar da Ummah ta dawo daga asibiti tana wankin kayan dana bata da jini suka kalli sai kawai Baba Uwa ta fashe da kuka tace “Sa'adatu bansan me zance Miki ba wannan yaro ya cucemu wlh tallahi bansan komai ba akai sai dazu daya kirani yake cemin yana hanyar zuwa nan din ya fasa zuwa California zuciyarsa bugawa take Shirin yi"


Murmushin takaici Ummah tayi tace “babu wani Abu Aishatu qaddara ta riga bata haka Allah ya shirya mana shikuma Allah yabasu zaman lfy da matarsa" daga haka ta duqa taci gaba da wankinta itakam baba uwa Banda kuka babu abinda takeyi, bayan Ummah ta gama wankin ne Yaya Yunus da yaci wuta yake fidda hayaqi ya shigo ya kalli Ummah yace mata.
“Ki faje gurin yarki inba hakaba wlh zaki rasata a banza akan wani dan iska tanacan sai kuka takeyi tana Kiran sunansa tana fadin a tambayesa me tayi masa ya yanke Mata wannan mummunan hukuncin" sai kuwa Baba Uwa ta sake rushewa da kuka tace “Yau munshiga uku wannan wacce irin masifa ce ne" da haka suka fice yanda sukaje suka tarar dani cikin halin bacci me nauyi saboda haukana ya wucce qima sai Allura akayimin na samu bacci cikin yini dayan duk na fita hayyacina haka suka zauna tare dani har zuwa ranar dana kwana uku sannan na dawo hayyacina da taimakon addu'a da Baba yasa aka rinqa yimin.




Ashe tun daren da na dawo Yaya Noor shima ya dawo qasar nan Kai tsaye ya nufi gdanmu a haukace yana zuwa sukayi karo da Yaya Yunus ya dawo dashi baya da sauri yace “kai daga Ina Kuma Ina zaka?" A mamakance Yaya Noor ya dubi Yaya Yunus yace “yaya nine fah gurin Zuhurah zan...." Bai rufe bakinsa ba Yaya Lawan ya sauke masa tafi ya nunashi da yatsa yace “kaga dan iskan qarshen zamani aminin Abu lahibi wan Ummuh jamil da aka saukar da sura guda saboda tsinuwa da la'ana a garesu, to maza dawo hayyacinka Dan durun uwarka inkai wutane ni ruwane cinyeka zanyi qaramin dan tasha ka sako mana qanwar saki uku kasa Mata ciwon zuciya ciwon da zata mutu dashi sannan ka biyota kayi Mata me sakarai kawai to wlh tallahi muddin naga ka taka gidanmu ko asibitin da take agaban uban kowa zan sare maka jijiyoyin Kai jininka yayi tsartuwa a sama ka fadi rijib matsayin gawa kowa ya huta"




Bawai barazanar ce ta hanashi shiga gdanba jin ance Ina asibiti ne ya hanashi ya juya da sauri ya bar gurin yana hada hanya a hanyar suka hadu da Baba ya nufeshi da sauri Baba ya tsaya a gabansa shikuma ya zube ya Kama qafarsa ya rushe da kuka yana jijjiga kai Amma ya kasa mgn duk da yanda baba yakejin haushi da tsanar jinin Alh Sadiqu saboda cin mutuncin da yayi masa saida Noor ya bashi tausayi ya darsa masa wasu-wasi yace.
“Kai lfy?" Cikin kuka Yaya Noor yace “Baba badon niba kaji qaina ka aminta da kalamina wlh tallahi bansan ya akayi na rubutawa Zuhurah sakinnan ba kawai naji kamar idan ta qara kwana matsayin matata dagani har ita wani mugun abun zai it's samunmu Baba wlh tallahi na fasa auren Asma'u saboda mahaifinta ya sanar dani itama da ita a cikin assasa wutar rabuwata da matata Baba kayiwa muhammadur rasulullah ka rufe mgnr nan kabani matata kadama wani yaji ance ai ana yanka baqin dan taure da tattabaru aure idan irin wannan qaddarar ta gifta sai igiya daya ta dawo toni daren nan zan nemosu a yanka wlh da gaske Baba...........😭😭






*P 47-48*



Kallon qurilla Baba ya rinqa yi masa kafin ya sanya hannu ya dagoshi yace masa “banson sakarcin banza NURADDEEN dakai da Zuhurah duka nawane ni bazan wofintar dakai ba domin nafi mahaifinka sanin ciwonka saboda haka kaje ka kwanta da safe ayi mgnr" baba ya fadi mashi hakane kawai domin hankalinsa ya kwanta amma maimakon hakan sai ya rinqa maimata kalmar “in kwanta? In kwanta?" Yana qara tambayar kansa ya kwanta anan dai baba ya tsallakeshi ya shiga gida.
To duk yanda yaso ganina ya rasa wannan damar saboda haqiqanin fushi kowa yakeyi dashi a dangi banda mahaifinsa da Baba rahamanu da sauran yan fadarsu sai wan babanmu Baba Muminu wato dagaci da yadauki girma ya azawa kansa duk da yaji ciwon abin sosai Amma yakasa nuna inda ya dosa ya tsaya akan katanga saboda ya fahimci nuna bacin ransa ba qaramar baraka zai haihar ba,





Kwana na shidda a asibitin banida aikin daya wucce kuka anqi fadamin cewa Yaya Noor yana garin duk da zuwa lkcn nasa dutse me nauyi inata kokawa da soyayyarsa burina shine danneta da mantawa dashi Amma taqi dannuwa saidai naci burin saina qunsa masa abinda yafi wanda yayimin naci alwashin dole saina raba kaina dashi kamar yanda ya yankeni daga jikinsa ya zabi kasheni nima sai nayi masa abinda zai tsaya a ransa har mutuwarsa,
Suby kinsan meye na qudurta a Raina? Na qudurce ne Koda ace wannan cikin na jikina zai zama shine qwai na na qarshe to kuwa bazan taba haihuwarsa ba na hqr dashi har gaban abada haka nayita saqa a mugun zare hardai na qarasa kwanakina na warware saboda sanyawa Raina dangana da nayi bani nasa Allah ne yasamin ita da taimakon addu'a da iyayena suka tsayamin akai, ranar da muka koma gda ranar ne nasan ashe yana garin mun fito daga mota zamu shiga gda idona ya sauka kansa yana tsaye a rakube jikin qofar gidanmu duk ya fice a hayyacinsa yayi mugun datti kayansa duk sunyi qura kamar wani sabon kamu.
Banko qara kallonsa ba muka shige gda Ummah ta kwantar dani ta fita ta daukomin shayi tazo tana bani ya samu ya shigo kasancewar matasan gidan basanan Yaya yunus da Yaya Lawan suna gidajensu shikam Yaya sani salamatu ne ko yananan babu abinda zai iya baiyi sallama ba kawai sai ganinsa mukayi a kanmu Ummah ta miqe da sauri tace




“Lfy Nura?" Sosa kansa yayi yana kallona inda nikuma nayi qasa da kaina yace “umm Ummah Zuhurah gurin My Zuhr nazo da baby na yau zamu tafi ko My Zuhr tunda kinji sauqi, don Allah karkice aa kawai komai ya wucce su bazasu gane ba Amma ke zaki gan...." Uhmm bansan inada zafin zuciya haka ba Saida ya sunkuyo kaina na daukeshi da marin da tunda uwarsa ta haifeshi Ina tunanin baa tabayi masa irinsa ba yaja da baya da sauri yana kallona Ummah tace “meye haka Zuhurah bakida hankali ne..." Daga mata hannu nayi na dubesa nace “babynka ko babynka kazo gani ko? Kaje ka kwanta kayi bacci insha Allahu bazai qara kwana a jikina ba wlh tallahi ko shine qwai na na qarshe na hqr dashi Nuraddeen dadai na hada jini dakai gara na mutu wajen abortion din cikinna....."
Rufemin baki Ummah tayi ta dubeshi tace “kaje Nura bazata saurareka ba yanzu" hawaye yake zubarwa ya matso gabana yace “Ummah zata iya fa Zuhurah kada ki tabamin dana don Allah wlh inasonsa dukan zaiyimin yawa"




Keda baki gurin idan kin kulashi na kulashi qarshema ma na miqe na fice daga dakin Ummah dake taga bani da qwari batayi tunanin fitata daga gdanba shiyasa basuyi azancin biyoni ba hakan ya bani damar ficewa daga gdan cikin saa kuwa dan sahu ya aje wasu Mata na haye nace yakaini yan santsi wato kasuwar rimi Ina zuwa na kwance sarqata da dankunne na dana daure a gefen zanina na siyar suka auna suka bani kudina na karba na tafi, kinsan wace ta fadomin?"
Girgiza Kai Suby tayi Zuhurah tace “Merry Ina tunanin zuwanki unguwarmu Basu tashi ba kinsan dai wace Merry na fito da wayata domin na dade da number ta na kirata bugu biyu ta daga nayi Mata mgn tanajin muryata ta gane muka gaisa nace Mata tana Ina? Tace tana Sabon gari nace ta fito inason taimakonta na gaggawa aikuwa babu bata lkc tazo inda nake na zayyane Mata komai, tare da fads Mata qudurina ta Jinjina lamarin tace “Zuhurah babyn ya girma zakisha wahala wajen abortion dinsa fah" daga mata hannu nayi nace “ko zan mutu saina cireshi" haka muka tafi cikin sabon gari wani gida ta samu likitan tayimasa bayani dama aikinsa ne yasa na kwanta a gado ya dubani sosai yace saidai ayimin allurar janyo naquda na haihu kawai amma fah yaron ba lallai ya rayuba domin bai cika wata bakwai cif ba"




Kuka ta saki me ciwo tare da dafe qirji tana maimaita kalmar “innanillahi wa Inna ilaihirraji'un" Suby dake tayata kukan tace “Allah yasa dai baki kashe danki ba?" Cikin kuka tace “na kashe Suby! banyi wata wata ba wajen amincewa da sharrudan da aka gindayamin a zuwan karuwa ce ni yanke take ya bani wasu magunguna nasha yayimin Allah har uku sannan ya sanyamin wani ruwa a hannuna, muna zaune tsayin lkc ciwo ya fara kankama babu kowa nawa sai Merry Abu kamar wasa sai gani Ina Shan baqar wahala naquda gadan gadan nayita ta kwana da yini a qarshe Saida dabaru aka cire yaron cikina dan qarami kyakkyawan gaske me kama da ubansa, lkcn da na dawo hayyacina na zubawa yaron ido inajin zuciyata tana bugawa da qarfi abin Ubangiji yaron yanata motsinsa likitan ya dubeni shima da mamaki yace Madam babynki fine boy" Merry ce ta karbeshi bayan an gyarashi muka tafi kasancewar duk irin halin da take ciki indai angama aiki baa kwana Kai tsaye gdan Yaya Noor na nufa Merry tace bazata ba nikuwa zuciyata ta bushe so nake

Please Login or Register in order to submit comment