Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kara tamke fuska yayi yace to meye abun dariya kuma, juyawa yayi yana tafiya yana fadin bari nadawo zaki sani.

12:42 alhaji ya faka motar sa ahabar gidan jalal awaya yakira shi yace yajiki jalal yace yayi sauki daddy yaushe zaka dawo?

alhaji yace nadawo gani ma akofar gidan ka mikewa yayi cikin sauri ya bude kofar ya fita , yana isa ya rugume daddy.

har cikin falon alhaji ya shigo ya zauna jalal yace daddy bari nakira safna.
cikin murna tafito tana yashe hakora bayan ta gaida alhaji bata zauna ba kitchen ta nufa ta fito da abinci.
daddy ya kalli safna yace wanna fah nida nazo duba mara lfy kuma sai na bige da cinye muku abin ci
safna ta bata rai tace dan Allah daddy kaci ai shi yaji sauki dama fa mura ce kawai amman duk yabi ya langwabe harda su kuka. dariya alhaji yayi safna ma dariya take yi
daddy yace jalal wai haka ne kayi kuka?
jalal yace karya take daddy ,ya juya yana hararan safna.
alhaji kalon jalal yayi yace nasan kayi ne jalal idan bakayi ba bazata fadaba, kaga irin abinda nake fada maka ko?
jalal yayi murmushi yace daddy dandai ba ita bace shi yasa take fadan haka bata San abinda nakeji bane, kuma kukan ma ai itama tayi.
safna kasa tayi da murya tace amman aini ban ta kiran sunan ummi ba , duk da tayi kasa da murya be hana daddy jin abinda tace ba.
jalal kuwa filon dake hannun sa ya wurgawa safna, tare da fadin ina wasa dake ne.
daddy dariya yayi sosai sannan yace wlh jalal ka canza halinka kai ga son girma kuma ga.... jalal ne yayi wa daddy alama da hannu karya fada, dan haka daddy yabar maganar, bayan alhaji yaci abinci yayi musu sallama ya tafi, tare da dubin farin cikin yadda ya samesu gwanin ban Sha,awa.

*************

gidan hajiya ya nufa yana shiga yaga ta daure fuska bakamar daba.
bayan ya gaisheta yaji bata kara cewa komi ba dan haka shima yayi shiru, zuwace yaga ummi tayi sallama ta shigo ya daga kai ya kalleta , batace mishi komai ba ta shige dakin hajiya.

alhaji yace hajiya zaliha kuma me takeyi agidan nan?
cikin fada tace inaruwan ka da ita dama jiranka nakeyi kadawo kagayamin abinda kake nufi, tunda ninayi magana baka dauki maganata abakin komai ba.
alhaji yace hajiya kiyi hakuri bawai nakijin magarnar ki bane, Ina sone ta gane wani abu wanda shekara da shekaru ta kasa fahimta.
aikoma Meye tunda nasa baki sai ka bari yanzun bakajin kunyar jalal yaji ka korar mai mahaifiya.
alhaji yace hajiya ai jalal yasan halin ta, shima ba magana take masa ba , dan ko gaisheta yayi bata amsawa .
hajiya tace me yayi mata shi kuma?
duk akan auran nan ne bansan abin da yasa ba zaliha kwata kwata bata kaunan yariyar nan.

Hajiya ta daga murya takira zaliha bayan tazo ta zauna alhaji azuciyar shi yake fadin jita kamar mutuniyar kirki.
hajiya tace zaliha zokibawa mijinki hakuri kuma duk abinda kike kinsani ki gyara halinki.
tun anan ta fara bawa alhaji hakuri , baza yayi da ita bece mata komai ba.
hajiya tace bakaji tana magana ne ko maganar bata wuce bane, da girman ka inda kuma jalal yayi kace masa me?
alhaji yace to shikena hajiya ya wuce, ki shirya anjima zamu tafi gida.
ummi dadi taji sosai, ta farawa hajiya godiya.
Firace ta barke tsakanin hajiya da alhaji ahirar ta sune ummi ta fahimci jalal yatare agidan sa, dan taji yana bawa hajiya lbrin ciwon jalal.
basu tashi tafiya gida ba sai yamma, alhaji yace ni nafita kisame ni a mota .
ummi gyalan ta ta dauka tana cikin yiwa hajiya sallama saiga alhaji da wata mata yar kwaye yana rike da kullin kayan ta, suna shiga falon matar ta zauna akasa, hajiya binta tayi ido dan bata gane taba, alhaji ya lura da haka yace hajiya baki gane ta bane, matar marigayi yaya musa ce.
hajiya tace Allah sarki kiyi hakuri bangane ki bane, yaya yaran.
tace suna lfy yanzun ma bikin salame ne ya tashi nace bari nazo na fada muku.
ummi ji tayi kamar tasan muryan dan haka tazo har gaban matar, take gabanta ya fadi tace kamar goggo kishiyar saudatu


07014197556โœ
[7:01PM, 12/20/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜


Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed๐Ÿ“

103-105


*โคโคโค godiya agare ku makaranta wannan novel gaskiya naji dadi sosai ganin jiya kadai banyi typing ba na samu kiran muta ne da dama, suna tambayar lfy ta nagode sosai ina muku fatan alheri๐Ÿ’•๐Ÿ’•๐Ÿ’•๐Ÿ’•๐Ÿ’•*

Itama matar dago kanta tayi takali ummi gaban ta yake ya fadi cikin da burcewa take fadi a,a bani bace, ina ganin dai kama ce.

ajiyan zuciya ummi tayi sannan tace amma ko kamar tayi yawa bayan sun gaisa da matar ummi ta karayi wa hajiya sallama ta fita tana waiwayen matar.

itama hajiya kara gaisawa sukayi da goggo sanna ta farawa hajiya bayanin bikin salame ne ya taso nace bari naxo na sanar lokaci sai kara tahowa yakeyi amman bani da komai da zan kai mata.


hajiya ta nisa tadayi murmushi sannan tace hanne kenan sai yanzon kika tuna da mune dangin ubanta, aida cen kin manta damu dan kinga babu idon iya sai yanzon da matsala ta kawoki?
goggo tace hajiya wlh ina son zuwa kudin mota ma gagara na yake, yanzon ma mokota nashiga na ranto.

toh aishi kenan yanzon wacce ce zatayi aure , yar wajen kice ko yar wajen amaryar ki?

tace ta wajena ce ai waccen tana gurin dagin mahaifiyar ta.

hajiya tace Allah sarki ai lokacin rasuwan iya tana karama yanzon nasan itama ta isa aure, me yasa baki turo mana su , zumun ci fah ba abin wasa bane, irin wannan saika hadu da naka baka san shiba, niyanzon ba kamar da bane girma ya kamani .

toh hajiya in Allah yarda zanturo su, shiru sukayi na dan wani lokaci zuwa cen goggo ta kalli Hajiya tace hajiya wannan matar da suka fita da alhaji wacece ?
hajiya tace matar sace.
goggo ta sake cewa ya kara aure ne?
a,a itace dai matar sa maman abduljalal , suma basan zumun cin suke ba, ai inaga ko iya ma bata santa ba bare ke.
haka suka ci gaba da tattaunawa goggo ta tsorata sosai da taji ummi surukar hajiya ce dan tasan indai asirin ta ya tonu ta shiga uku, dan haka washe gari goggo na tashi tashirya tayiwa haji sallama bayan ta hada mata sha tara ta ar ziki.

itako ummi bayan sun koma gida hakalin ta kara tashi yayi so kawai take taga ta daidaita da iyayen ta dan haka ta farawa alhaji kuka ya taima keta ya daidaita da iyayen ta

hakuri ya shiga bata ki kwatar da hankalin ki baffa yayi rantsuwa babushi babu ke tunda kikai silar rabowan shi da 'yar shi har ta mutu basu ganta ba, zaliha nazaci idan baffa yasan cewa saudatu ta rasu hankalin shi zai kwanta amman sai naga hankalin shi ya kara tashi, zaliha abinda na lura dashi babu abinda baffa yake so ayanxon illa yaga yariyar da saudatu ta haifa.
kukanta karuwa yayi tace nima haka alhaji ina matukar son naga yariyar nasan yanzon ta girma , kuma alhaji idan nakalli huto yariyar sai naga kamar na taba ganin hoton.
alhajj yace kin taba gani mana tunda yariyar da saudatu take kama.
haka sukaci gaba da ta tattaunawa akan yariyar saudatu , zuwa cen ummi ta sako maganar jalal alhaji ashe jalal ya tare shine ko kugaya min
atakai ce yace eh ya tare.
ta sake cewa Amman alhaji ya kamata ace yana zuwa gida ana gaisawa.
toh ganinayi gurin wa zaizo ni bana gari ke kuma ba amsa masa gaisuwa kike ba, toh me zaizo yayi.
toh alhaji komai ya wuce kabashi hakuri dan Allah yazo gida.

washegari da safe daddy yayiwa jalal waya ya tambaye shi jiki yace yayi sauki, dan haka alhaji yace idan zaka iya fitowa kazo gida ummin ka nason ganin ka .
toh kawai jalal yace, ya juya yace safna shirya muje gida cikin sauri suka shirya suka kama hanya.
Suna shiga jalal ya nufi dakin daddy safna kuwa falo ta zauna tana raba ido.
lokacin da jalal ya shiga dakin ya samu ummi sunata hira da alhaji dan haka murmushin dake fuskar shi ta ragu, daddy ko murmushi ya saki yana fadin jalal ka iso.
kusa da alhaji yaje ya zauna bayan ya gaida alhaji ya juya barayin ummi yace ummi ina kwana.
cikin sakin fuska ta amsa tare da tambayan shi jikin shi, bayan ya amsa ta sake cewa ya safna?
dadi sosai jalal yaji yace lafiyar ta lau tare muke tana falo.
alhaji fada ya farawa jalal yazaka bar ta afalo saikace wata bakuwa jeka shigo da ita.

jalal zuwa yayi ya riko hannun safna suka shiga falon alhaji bayan ta gaida alhaji ta juya ta gaida ummi ta amsa ba yabo ba fallasa.
ummi kara kallon safna tayi sosai gani tayi takara cika tayi kyau sosai cikinta harya fara fitowa, juyawa tayi gurin jalal ta fara janshi da hira harya fara sakin jikin shi.
sai yamma su safna suka bar gidan su ummi jalal sai washe hakora yake .

kwanci tashi ba wuya gashi har cikin safna ya isa haihuwa suna jiran haihuwa ko yau ko gobe , komai sun tanada anty nusaiba na kula da safna sosai dan akai akai take zuwa dubata da tace ina son kaza anty nusaiba saita nemo
itako ummi ta rage nuna tsanar safna afili jalal kuwa jitake kamar ta hadiye shi, babu abinda yake damun ummi ayanzo ila rashin samun yar da saudatu ta bari .

safna ce ta fito daga daki tana fiya daker, har ta isa gurin jalal tana zama ta kalli jalal dake kwance ya rufe ido, taba shi tayi tace yaya ka tashi nasan idonka biyu.
tashi yayi ya zauna yace safna nasan maganar muguwar matar nan zakiyi min, ni kuma bana sojin ko sunanta.
[7:06PM, 12/20/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜



Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed๐Ÿ“


106-108


safna kasa tayi da murya tace yaya dan Allah kayi hakuri ka kaini inason naga nima ina da 'y an uwa kamar kowa kaga ko badan goggo ba kodan yaya iro da salame ai naji .
kara daure fuska yayi yace yan zon kina nufin harkin manta da wula kancin da mahaifiyar su tamiki toh bazaki ba indai nine mijinki bazaki wajen wannan muguwar matar ba idan ma kina tunanin ni zan kaiki toh kima cazan tunani dan wlh bazan jeba, waima me kike nema awajen su, me kika nema kika rasa da zaki nace sai kinje wajen su?
kuka safna ta fara tace yaya yan uwa nane fa, bani da kowa fa sai su

kara kulewa jalal yayi ya fara magana cikin fada baki da kowa saisu ko, haka kice ko, ni ma ba komai bane awajen ki ko, duk abin da ake miki baki gani, kin raina ko?
a,a yaya ba haka nake nufi ba nidai kawai inason naje naga yan uwa na dan Allah kayi hakuri ka barni naje.

Jalal kara daukan zafi yayi yace wlh safna idan kika kara cemin 'yan,uwan ki saina mareki susan tarajar kine suka wurgar dake a titi.

safna ta kara fashewa da kuka tace yaya gori kuma kake min?
eh ammiki gorin kiyi abinda zakiyi wawiya kawai mara wayau.
safna daki ta nufa cikin matsanan cin bacin rai taita kuka.
shikuwa jalal bayan ya gama fadan gidan ya bari sai dare ya dawo, ya samu dakin safna rufe dakinshi ya wuce dan yasan fushi take.
Washe gari bayan ya gama shir yawa ya fito yaga falon na nan yadda yake yagane safna fata fitoba ji yayi babu dadi a zuciyar shi ya isa bakin kofar yayi ta bugawa taki budewa hankalin shi ya kara tashi waryar shi ya ciro ya dannan number daddy yana dauka ya fara fada mai safna ta rufe daki tun jiya taki budewa.
alhaji yace wani abu ya farune ko kunyi fada ne?
shiro jalal yayi bece komai ba dan ya tuna kargadin daddy akan safna.
Alhaji yace jalal baka da gaskiya kenan, bari nakira safna.
safna dake zaune adaki taci kuka ido duk sun kunbura taji ankira wayar ta tana dubawa taga daddy ne tasa wayar akunnen ta tana kuka ahankali alhaji yace safna me ya faro ne, jalal ne ko, gayamin me yayi miki?
kasa magana tayi ta kara fashewa da kuka.
alhji yasake ciwa jinan safna daina kuka bakisan wannan kukan zai iya miki ila ba, tashi maza ki shirya ya kawaki koma me yayi miki zanyi maganin sa, kinji ko.

jalal na zaune amota safna ta fito ya kalli fuskarta yaga tayi jawur saboda kuka dogowar rigace jikinta da hajjab madaidaici .
suna isa ta bude motar ta fita , ta samu alhaji shida ummi afalon ummi ta mata wani irin kallo, zamatayi akasa ta gaida su, suna cikin amsawa jalal ya shigo alhaji yace kai jalal baka da hankali ko, waya gaya maka ana tayar ma me ciki da hankali?
shiro yayi yanemi guri ya zauna.
Alhaji ya kara cewa ina murna zan samu takwara ko mata zaka mana sa... be karasa maganar saba ummi tace Allah ya kiyaye karku sake kusa sunana dan ni ba sa,ar wasan ku bace asa mata sunan uwar ta amman bani ba.
safna ta daga jajayan idanun ta, ta kalli ummi ta fashe da kuka, tare dajin matsanan ciyar tsanan ummi azuciyar ta .
alhaji yace zaliha tashi ki bamu guri tunda ke ba,a magar hakali dake.
tana tashi alhaji yace safna gayamin me jalal yayi miki?
Cikin dashashiyar murya ta gawa alhaji abinda ya faru.
alhaji yace ah ah jalal yayi laifi sosai toh kai jalal banda abinka haka akeyi ba yafiya, tunda tace tanason ganin su aisai kayi hakuri ko baka so kabarta taje, itama ta hakura ta yafe bare kai.
sai alokacin jalal yayi magana daddy ai itama dan bata da hankali ne shiyasa ta yafe.
murmushi alhaji yayi yace jalal ai wannan abinda tayi shine hankalin abun da kawai ban yadda tashi ba tafiya da ciki dole kiyi hakuri har ki haihu nida kaina zan sa akai ki, kai kuma ka kiyaye bakin ka inrai ya baci hankali baya gushewa, haka alhaji yayi ta musu nasiha sannan yace kutashi kuje gida.
tana mikewa jalal yace zomuje muyiwa ummi sallama haka safna tabi bayan shi badan ranta yaso ba.
sun sami ummi zaune abakin gado tayi ta gumi jalal yace ummi zamu tafi tace ku gaida gida safna ta juya zata fita ta daga kai taci karo da tangamemen hotun iyayen ta tana rike ahannu su, daga hannun ta tayi sama tana nunawa jalal , yaya kallah bata karasa ba jalal yaga tana kokarin faduwa
[6:51PM, 12/21/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜


Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed๐Ÿ“


โ€‹ *dedicate*โ€‹
โ€‹โ€‹dis page to
hajiya amina lamido Kilishin yamma๐Ÿ‘๐Ÿป


*gaisuwa agereki*
*Aysha mazoji* *marubuciyar*
*Zaheedah*
*Jaleelah*
_The boss wife_

โ€‹
109-1012


Da sauri jalal ya tare safna ta fada jikin shi, ganin inda safna keta nuna hoton yasa ummi ta zaro ido ta mike tazo kan safan tana fadin kar dai ace safna yar saudatu ce, jalal be saurari me ummi take fada ba kiran sunan safna kawai yake amman shiru babu amsa ummi ce ta lura jini na zuba ta kasan safna da gudo ta fita tana fadi
alhaji dauko mota safna babu lfy .

da ummi da jalal ne suka kinkimi safna suka sakata amota, jalal ya fita haiyacin shi ummi ko kamar mahaukaciya sai fifita takewa safna da gyalen ta,
bayan sun isa asibitin aka shiga da safna ciki jalal yaso ya shiga suka dakatar dashi.
Komawa gefe yayi amman ya kasa tsayuwa guri daya sai naushin hannun shi na hagu yake da hannun shi na dama.
ummi kuwa tunani ne ya dame ta dan haka ta matsa kusa da alhaji tana share zufa tace alhaji kasan abin da safna ta gani ta shiga wannan halin, hoton saudatu ta gani.
da sauri alhaji ya mike ya cire hular sa ya fara fifita da ita ya na zaware kamar yadda jalal keyi, ummi ta mike tabi bayan shi tana kokarin magana alhaji ya dakatar da ita karki ce komai kibari muga lfyr yarinya tukuna.
komawa tayi ta zauna zuwa cen ta sake mikewa.
daga cen su kaga an turo kofar Dr sulaiman ne ya fito dasauri alhaji yabi bayan shi, jalal ma mikewa yayi amman alhaji ya waigo yace koma jalal.
bayan ya shiga Dr sulaiman yace alhaji haihuwa ce sai dai muna tunanin yariyar bazata iya haihuwa dakan ta ba sakamakon jinin ta ya hau sosai saida kuyi ta mata andu,a .
haka alhaji ya fito jiki babu kwari jalal ya mike yace daddy mutuwa tayi.
a,a jalal tana nan daran ta haihuwa ce amman jalal kayi ta mata andu,a Allah ya rabasu lfy .
jalal be yadda da abinda daddy ya fada ba dan haka ya fara share hawaye.
alhaji yakira anty nusaiba yagaya mata halin ta suke ciki nan da nan saiga su ita da matar baba salisu suna rike da kayan baby ganin ummi agurin abin ya basu mamaki.
2:46pm sukaji safna tayi kara mikewa jalal yayi zai shiga anty ta rike shi ta bude baki zatayi magana suka sake jin wani ihun, wannan karon sai da alhaji yasa hannu suka iya tare shi, yana fadi daddy kuka fah takeyi haka sukai ta bashi baki juyawa yayi ya fita yasamu wani dan dutse ya zauna yata share hawaye.
yana zaune agurin anty ta fito da gudu tana dariya jalal albishirin ka.
mikewa yayi yana kokarin share hawayen shi yace anty ta haihu ne?
Jalal mu godewa Allah safna ta sauka lfy mun samu yan biyu.
jalal ya zaro ido yace anty da gaske cikin sauri ya nufi ciki ya same su alhaji sai dariya suke alhaji ya dafa jalal yace jalal kuka ya kare ko?
kunya ce ta kama jalal yayi kasa dakai yana murmushi yace daddy wai da gaske yan biyu ne?
alhaji yace 'yan buyu ne jalal mace da namiji kana mamaki ko, ikon Allah kenan.
bayan angama gyara jarirai aka basu damar shiga ummi ce kan gaba tana shiga ta sauke idanun ta akan safna da sauri ta rintse ido gurin ta ta nufa takira sunan ta taji shiru, alhaji yace zaliha kirabu da ita kila bacci takeyi daidai lokacin nusaiba ta dauki macen takalle ta sannan tamikawa alhaji tace yaya ga matar ka ta juya zata dauki dayan ta ganshi hannun matar baba salisu haka suka taro suna kallon yaran gwanin ban Sha,awa.
Shiko jalal gurin gurin matar sa yake son zuwa amman ummi tana jikin gadon dan haka ya kasa zuwa wajen.
alhaji ne yace jalal yanaga ka koma gefe kazo kaga yaran mana.
sosa kai yayi ya kalli safna yace daddy ina zuwa.
alhaji ya fahimce shi yace kazo ka gansu mana safna ai bacci take.
da saurin sa yace daddy ba bacci take ba idon ta biyu.
sai da alhaji ya kalli safna sannan yace zaliha fito daga nan gurin.
cikin sauri ummi ta fito daga gurin duk arude take so take kawai safna ta tashi .
Jalal yana isa gurin ya duka yanawa safna magana cikin kunne zuwa can ta fara magana ahankali cikin kuka, jin safna na kuka yasa duk suka maida hakali gurin su, amman basajin me suke fadi, jalal ya dago hankalin shi atashe ya kalli ummi ya hada rai.
ummi ta tsargu tace jalal me safna tace maka.
yi yayi kamar beji ba ya mikawa alhaji hannu ya bashi yaran ya kure su da ido.
lokacin da aka sallame su ,alhaji yace awuce da ita gidan hajiya motan jalal ta shiga su anty nusai ba ma haka.
hajiya ta tare su da murna nusaiba ta mika mata yaran ta kalle su tace ikon Allah ga jalal ga safna , hajiya fatima ta shigo rike da safna ta zaunar da ita akan kujera jalal ma ya shigo dauke da kaya ya ajiye agefe hajiya ta kalli jalal tace yaya haka kuma jalal menene haka kaida ka samu karuwa kuma menene naka na hada rai, ta kalli safna tace au kema kuka kikeyi toh abin naku bana lfy bane
anty tace jalal nima nakula akwai abun da yake faru har anty zaliha ma akwai abun da yake damun ta ko kallon yaran batayi ba
hajiya tace tunda sunki mgn ku kiramin alhajin har zalihar ,wannan ai iskanci ne Allah yayi muku kyauta kuzo kuna tur bune mana fuska.
suna cikin haka alhaji ya shigo ummi na bishi abaya hannu ta rike da wanan huton.
bayan sun zauna hajiya tace nifa kun sani aduhu wai me yake faruwa ne?
alhaji yace hajiya wani babban al,mari ne yake shirin faruwa ya karbi huton ahannu zaliha ya mikawa hajiya yace wannan haton safna ta gani kawai sai gani sukayi ta fadi shine muke tunanin ko ta sansu ne .
hajiya kallon huton tayi tace wannan ai musa ne.
alhaji yace hajiya wani musa kuma ?
tace musan iya mana ko kana nufin baka gane shi bane.
alhaji kallon huton yayi sosai yace innalillahi wa,inna ilaihir raju,un

Safna na daga gefe kuka kawai take murya hajiya taji tana fadin safna kinsan musa ne?
cikin dashewar murya tace babana ne.
hajiya ta zaro ido a,a safna ko dai kama suka miki wannan fa dan yayata ce uwar mu daya uban mu daya, yanzun nan kina nufin ke jikar iya ce.
cin kuka tace eh.
kowa afalon gumi ne yake karyo mishi itako ummi hankalin ta yafi na barawo tashi.
hajiya ta share zufan da ya karyo mata tace ke zaliha Ina kika samu wannan huton ?
jalal najin anyi ma ummi wannan tambayan ya fita afalon dan yanajin kunyar abin da ummi tayi.
cikin kuka tace hajiya wannan matar itace kanwa ta da nake baki labari, zaro ido safna tayi ta mike tace ummi kina nufin kece yar mahaifiyata, ina wlh wlh bazai

Please Login or Register in order to submit comment