Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ai ko bakin kine yake ciwo yau zaku tafi, nima hankali na ya kwanta tunda aka daura auran nan hakali na ba,a kwan ce yake ba, buri na kulum be wuce nagan ku acikin gidan Ku ba.
Safna shiru tayi ita gaskiya fushi take da jalal, muryar daddy taji yana cewa safna kuyi hakuri da junan ku ban da fada , kai jalal kaine babba banda saurin fushi , babba da hakuri aka sanshi, ke kuma safna ki sani jalal mijin ki ne dan haka kimai biyya, tuni safna ta fara kuka ji tayi auren ya dawo mata sabo.
alhaji juyawa yayi gurin jalal yace jalal ya maganar karatun safna, ina fatan dai kana da burin taci gaba karatu?
eh daddy insha Allah .
alhaji yace to yayi kyau Allah yayi muku albarka ya baku 'ya'ya masu albarka.
gaba dayan su kasa amsawa sukayi sai hajiya ce ta amsa.
safna kuwa ta kifa kai sai faman kuka take. alhaji yace jalal zan tafi ko anan zan barka?
a,a daddy tare zamu tafi ai ban fito da mota ba
sun mike zasu tafi safna ta dago jajayan idonta ta harari jalal, yace Allah ya huci zuciyar ki.

daddare kamar yadda alhaji ya tsara nusaiba tazo ita da matar baba salisu suka raka safna gidan ta, har bakin gado suka zaunar da ita sai faman kuka take.

wurin takwas suka ceto mufa zamu wuce dare nayi. safna tace anty dan Allah karku tafi tsoro nakeji.
nusaiba tace wani irin tsoro to bari na kira jalal.
shikowa jalal lokacin da anty nusaiba ta kira shi yana kokari zuba akwatunan su amota ta kofar dake baya yake fitar da akwatin daddy na sakawa amotar har suka gama, jalal yaso yayiwa ummin shi sallam ko bazata amsa ba amman daddy yace ya rabu da ita, dakan shi ya raka jalal har cikin falon su , su anty nusaiba kuwa suna jin zuwan su suka tafi
bayan daddy yasa musu albarka ya wuce gida , da niyar shima da safe zai wuce gurin aikin sa


alhaji na fita jalal ya mike ya leka dakin safna daga bankin kofar ya tsaya ya kalli fuskar ta da sauri ta dukar da kai kasa, murmushi yayi yace ina zuwa, waje ya fita yafara ciro akwatunan su daga cikin mota, saida ya fara shigar mada safna nata sannan yashiga da nashi daki, yana ajewa ya shiga wanka bayan ya fito yasa ka kaya marasu dauyi ya nufi dakin safna.
yana shiga ya same ta daidai ta fito wanka tana goge jikin ta tana ganin shi ta jawo hijjabi ta dake gefen gado tana kokarin sakawa.
dariya taba jalal sosai ya matso kusa da ita ya zauna, yace to meye kuma na saka hajjabi me zaki boye min.
gani yayi ta kara rudewa dan haka ya matsa ya riketa yace safna meya sameki?

cikin muryar kuka tace bacci nakeji.
murmushi kawai jalal yayi dan yasa ba gaskiya ta fada ba.
yace to waye ya hanaki bacci. shiro tayi.
Matsawa jalal yayi yace zoki kwan ta.
zuwa tayi ta kwata ta kudun dune cikin hijjabin ta
jalal ya fahimci safna bata sone ya nemi wani abu awajen ta, kollon ta yayi ko mai bata shafa ba, yace safna.
amsawa tayi batare da ta waigo ba, yace haka zaki kwanta baki shafa mai ba bare kuma turare.
yaya ai ni yanzun bana shafa mai.
saboda me?
tace wari yake min
jalal yace wari man nakine yake wari, kitashi kawai ki shafa ke da kin ga baki son abo saikice yana wari, haka ranan kikace ina wari.
Wlh yaya ban son warin man ne , sabolon ce ma na bayi na kasa wanka dashi ahaka niyi babu sabulu.
jalal yace kina nufin ba sabulu kikayi wanka, kice ba wanka kikayi ba kin jiko datti, ai irin wanna saiki fada irin wadda kike so asiyo miki.
batace komai ba ta juya tayi shiru
ganin ta kwanta shima ya hau gadon ya kwanta zuwa cen ya fara kai hannun shi jikin safna , yi tayi kamar tayi bacci ahankali tafara jin hannun shi acikin hijjabin ta har zuwa marrar ta taso ta rike hannun amman sai tai tunanin in yaga tayi barci zai barta dan haka tayi kamar tana bacci saiji kawai tayi yana kwance towel din da yake daure jikin ta dasauri ta rike hannun shi, tace yaya jikina fa akwai datti , bakace na tayar da datti ba.
cikin rauna nan niyir murya jalal yace ni banji wani datti ba yace gaba da abinda yake tun safna na ture jalal har sakon ya fara kaiwa gare ta, ta fara mayar mai da martani, nidai daga sun rikece, nayi waje aguje🏃🏼🏃🏼🏃🏼na jawo musu kofar.

washe gari da safe 9:10 akafara buga kofar falon su da karfi, safna dake kwance jikin jalal ta zabura shima mikewa yayi da sauri ya saka jallabiya ya fita har yanzun buga kofar ake
[7:25PM, 12/16/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘


Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝



92-95


Abduljalal a tsora ce ya isa kofar dan gani yake kamar ummi ce , yasa hannu ya bude kofar yariyar dake aiki gidan anty nusaiba yagani tsaye da kayan abinci a hannun ta wani haushi ya turnekeshi besan sanda ya daga hannun shiba ya wanke ta da mari.
a tsora ce yariyar ta dafa kuncin ta, ta ajiye abin cin ta arta aguje, abduljalal ya tsuguna ya dauki basket din yakoma afalo ya jiye yakoma dakin safna ya same ta sai faman raba ido take, yace ki kwatar da hankalin ki wannan yariyar ta gidan anty nusaiba ce, mikewa tayi cikin sauri tace bari naje nasan anty ce ta aiko ta kama hannuta yayi yace ai ta tafi abinci ne ta kawo, koma wa tayi ta zauna tayi shiru tafara tunani, lallai ummi bata son auren nan gashi yanzun tun daga gidan anty nusaiba aka kawo mana abinci kuma ai munfi kusa da ummi.
muryar abduljalal taji yana fadi safna tunanin me kike?
yaya tunanin kairat nakeyi mun barta ita kadai. yace karki damu idan muka gama cin amarcin mu zan dauko ta tadawo nan da zama gaba daya.
safna tace yaya ummi ko zata bari?
da sauri yace safna bar wannan maganar kisan tunanin me nakeyi .
gargiza kai tayi yasake cewa ina tunanin gashi kin haifi yaro me kama dani.
Safna tace nidai yariya nakeso.
nima inaso safna amman nafiso ki fara da namiji dan nasa mishi sunan daddy.
safna tace toh yaya in mace ce wani suna za,a sama ta. bude baki yayi ahankali yace na baki zafi.
safna ta sake cewa baza,a samata sunan ummi ba?
mikewa yayi yace taso muje muci abinci. safna ta lura yaya ko sunan ummi beson yaji ta Kira

suna cikin cin abin cin ne wayar abduljalal tayi kara ya dauka yasa akunne sa, yana fadin ina kwana anty.
anty bata amsa gai suwan shiba ta shiga yimai fada jalal me bilkusu tayi maka ka mareta har fuskarta ta kunbura haka?
anty zuwa tayi muna barci taita buga kofar, safna duk tabi ta firge
da sauri anty tace lallai jalal safnar yariyar goye ce da zakace wani an firgita ta, har yanzun dai kanan da bakar zuciyar ka , ita kuma safna tana kallo kamari yariyar muta ne ko, toh shike nan idan ka kuma ganin bilkisu agidan ka kasa bulala ka zaneta ba mari ba yana kukarin yin magana ta kashe wayar.
ture abincin yayi gefe ya sake kiran ta bata dauka ba mikewa yayi ya shige dakin sa.
safna binshi tayi da kallo domin bata fahimci abin da suke fada ba, ta fara kwashe kayan da suka bata takai kitchen saida ta wanke su sannan ta fito har lokacin jalal be fito ba, wuce wa tayi dakin ta tayi wanka kwalliya ta tsaya tayi sosai sannan ta nufi dakin jalal tana tura kofar tajita bude sallama tayi . jalal dake ciki ya amsa , tana saka kai ta ganshi tsaye ga dukkan alamu wanka yayi dan daga shi sai gajeran wando ga dogon wando a hannun sa yan kokarin sakawa.
safna naganin haka ta juya baya , murmushi jalal yayi ya aje wandon hannun shi ya iso gare ta jin shi kawai tayi ya rogumeta, ta baya yana kaimata kiss ta ko ina kamar zai hadiye ta, zuwa cen yadan dakata ya leko da kansa zuwa daidai fuskar ta dan jalal dogo ne sosai, yace har kinyi wanka, Allah yasa dai yauma ba haka kikayi wankan ba sabulu ba.
safna na rugume jikin jalal tace ai na samu wani sabulu acikin akwati na bashi da wari sosai.
jalal yace jinan safna in kinji abu namiki wari ki daina cewa yana wari cewa zakiyi bana son kamshin shi, dan kinsan Allah idan kika kara cewa ina wari saina fasa miki baki.
kallon shi tayi da mamaki tace yaya yanzo nan kai sai ka dake ni.
me zai hana na dake ki ,kiyi abin dokan kigani.
haba nina san bazaka dakeni ba in kuma zaka iya bismillah. jalal yace ai baki min komai ba yanzun.
dan tureshi tayi kadan ta rike hancin ta tace yaya jalal wari yake.
murmushi kawai yayi yace Ina binki bashin duka idan kika haihu zan miki.
a,a ni ban yadda ba yanzun nake so.
matso wa yayi ya riketa yace daidai ina zan daka.
safna cikin ta, tanuna tace ka daki nan
dariya jalal yayi yace lallai safna ke muguwa ce ,toh naki.


haka zaman su yaci gaba da kasan cewa
cikin farin ciki da kwanciyar hankali jalal yana nuna mata so daidai gwargwado har wani cika su kayi suka kara haske sukan leka gidan hajiya da daddare gidan ummi kuwa tunda suka tare ko jalal be leka ba bare safna, amman bata san cewa jalal baya zuwa ba gashi har sun kwashe sati uku da tarewa


alhaji kuwa tun washe garin ranar da ya raka jalal gidanshi yabar garin ko sallama bema ummi ba.

itako ummi ranar ta wayi gari daga ita sai kairat acikin gidan tayi tunanin wato jalal fushi yake da ita ko ganin shi baya bari tayi, alhaji kowa abakin kairat taji lbrin ta fiyar sa.
tun tana ganin abi kamar wasa ne har ta fara tsora ta.
kiran alhaji tayi har ta gaji be dauka ba, ta fara tunanin kiran jalal, amman kuma da kunya takira shi bayan tace mai bata son ganin shi, fadi tayi a fili me yake shirin faruwa dani ne, iyayena sunki karbata saboda halina dagin mijina basa sona saboda halina mijina dake takama dashi ya juyamin baya saboda yana kuka da halina, dana dake matukar so shima ya hakura ni ,afili take fadi kamar mahaukaciya zuwacen ta sake kuka haka taita yi babu me rarrashin ta

yau ummi ta tashi da matukar so taga jalal tuni ta lura jalal kwata kwata baya shigowa gidan a lissafin ta sati hudu kena da barin su gida wata zuciya tace kodai tare sukayi tafiyar da alhaji be.
mikewa tayi ta nufi dakin jalal tana tura kofar taji ta bude shiga ciki tayi me zata gani duk wani abu na amfanin jalal babu shi adakin, juyawa tayi gurin da aka aje a kwatunan safna nanma wayam babu komai.
rawar jiki ta fara tana haki take fadin na shiga uku, dakin ta tafada ta dauki gyale drive takira tace zoka kai ni gidan hajiya, rabota da gidan hajiya ta dade.
hajiya na zaune taga ummi tashigo kamar ankwato ta daga bakin kura

07014197556✍
[6:31PM, 12/17/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘


Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝



96-99

Hajiya tsoro ne ya kama ta cikin kidima tace zaliha daga ina haka?
cikin kuka take fadi hajiya nazo neman gafararki dan Allah kiyafemin a yanzun nagane kure na , kuka take sosai.
hajiya tace alhamdulillahi dama haka ake so naji dadi da kika fahimce haka ni daman ban kullace kiba tunda ismail yakawo ki amatsayin matar sa dole nasoki balle kuma ga yara har biyu atsakani.
ummi tace nagode hajiya tana share hawaye.
hajiya tace amman zaliha bayan wannan akwai wani abun da yake damunki ko?
hajiya aini duniyar gaba daya ta cakude min iyayena suki karbata amatsayi yar su saboda lefin da na aikata , nan ta shiga bawa hajiya lbr hajiya tace ikon Allah abin mamaki baya karewa , toh zaliha banda abinki ina kika taba jin mutun yaki iyayen sa, toh ai dole kirasa kwanciyar hankali kadan ma kika gani, ai iyaye ba abin wasa bane, karki kara ai kata nakaman cin wannan, kinji ko?
In Allah ya yarda bazan kara ba nagode hajiya.
hajiya tace tashi kije kitchen ki debi abinci. hajiya bana jin yinwa naci abinci agida.
shiru sukayi nadan wani lokaci sannan hajiya ta kalli zaliha tace megidan fa yaushe zai dawo?
tofah hajiya ta sosa ma ummi inda yake mata kaikayi wani sabon hawaye ne yake fita a idonta tace hajiya aini rabon da naga alhaji sati hudu kenan sanda zaitafi ma ko sallama bemin ba kuma ko kiransa nayi baya dauka jalal ma basan inda yake ba, hawaye take sosai.
hajiya ta tausaya mata tace ya isa haka share hawayen ki, kikace rabon ki dashi sati hudu? eh
hajiya tace toh ai yadawo yayi kwana biyu ya koma, yau kwana biyar da tafiyar sa, kina nufin ba,a gida ya kwana ba kenan,toh ko kin masa wani abune?
shiro tayi tana ta share hawaye.
hajiya tace toh kidaina kuka ai tunda kukayi aure shekara kusan talatin ban taba jin kan kuba, mijiki nasonki yayi hakuri da ke duk da cewa yasan baki son yan uwan sa, ina ganin dai akwai abinda kika masa.
hajiya wayar ta dauka ta shiga daki number alhaji takira bayan ya dauka tace me matar ka ta maka katafi kabar ta babu ko sallama?
alhaji yace lallai zaliha bata da kunya gidan ki tazo shakaran ta nawa batazo gidan ki ba.
hajiya tace nidai ba wannan na tambaye kaba babu ruwanka , koma me tayi maka kayi hakuri bakaga inda ta fita haiyacin taba ta rame tayi baki kai ko kunya bakaji abokan ka su ganta ahaka, ai sai ace wahala take Sha.
hajaya kirabu da zaliha makirar mata ce, inda kisan halin ta bazaki yarda da tubanta ba, kice mata kawai ta wuce gida saina dawo.
nidai nace ka kira ta, ka kwatar mata da hankali abin ya mata yawa jalal ma kai ka hana shi zuwa gidan kenan, toh yanzun yaya kake son tayi.
alhaji yace shike nan hajiya zankirata.
ummi bata tafi gida ba har dare gashi kuma har yanzun alhaji be Kira taba sai gurin 7:30 taga kiran shi jiki na rawa ta dauka tafara gaida shi be amsa ba yace kina ina ?
cikin sauri tace ina gidan hajiya.
yace toh maza kitattra kayan ki kije gidan iyayen ki sai Nazo, kin shirya wani munafuncin ne dan kirabani da mahaifiya ta, toh baki isa ba, kinyi kadan,maza ki bar gidanan .
hajiya nadaga daki tajiwo ummi tasaka kuka me ban tausayi, fitowa tayi tace zaliha yaya akayi?
ummi ta gayawa hajiya abinda ya faru, ran hajiya ya baci afili tace Ismail kuma abida beyi da kuruciyar shi bane yanzon zaiyi, toh shikenan, ke kuma wannan ya isheki ishara dan yasan baki da gurin zuwa ne shiyasa yace kitafi .
ummi kuka take sosai tace yanzun hajiya yaya zanyi baffa yace idan nakara nufu gidan shi batare da nacika sharadin da yabani ba Allah ya isa.
hajiya nisawa tayi tace kizauna anan kafin yadawo muji abinda yake nufi kuma ko yakiraki awaya karki dauka, ke kima kashe wayar baki daya, dan naga alamar ran shii a bace yake dake kar yazo ya aikata abin da yafi haka . godiya tayima hajiya sosai suna zaune sunyi jugun jigun saiga kairat ta shigo tana kuka ummi shine kika tafi kika barni, kwantar da ita tayi akan ciyarta tana rarrashin ta.
ranar da ummi ta wayi gari agidan ummi, jalal kuma agidan sa ya tashi da matsanan cin mura da zazzabi tun yana daurewa har ya gaji yace safna zoki rufeni, zuwa tayi ta taba jikin shi taji zafi rau tace yaya katashine muje asibiti .
cikin rawar murya yace safna bazan iya tuki ba, bari sai anjima, rufeshi tayi ta fita zuwa kitchen domin karasa girkin da ta daura.
bayan ta gama takoma dakin tasame shi ya ture bargon sai faman kira sunan ummi yakeyi, ta dauka wasa yake saida ta karasa kusa dashi ta gane da gaske yake yi, dariya ta fara tace meye haka yaya saika ce kairat.
ai ko sauraran ta beyiba kiran ummi kawai yake yi zuwa cen ya jawo safna zama tayi agefen gadon ya dago kanshi ya daura aciyar ta sai faman sanbatu yake tun abin nabata dariya har yasoma bata tsoro zuwa cen taga ya fara kuka hawaye shabe shabe, da sauri ta sauke kan jalal daga jikinta karamin hajjab tasa tayi waje.
tana fitowa gate din gidan su gidan dake jikin nasu ta nufa dan taga me gidan suna yawan gaisawa da jalal, gate din gidan ta fara bugawa me gadi yazo ya bode yace lfy ?
safna ta rasa me zatace dan ko sunan mutumin bata sani ba, hango shi tayi rike da hannun matar sa zasu shiga mota hango safna da me gadin su ya hana su shiga karasowa gurin sukayi safna ta gaida mutumin tace ni makociyar kuce anan gidan nake ta nuna gidan su da ahannu ,miji nane bashi da lfy dan Allah ku taimaka min ku kaimu asibiti.
mutumin yace kece matar abduljalal dakai ta amsa, yace toh babu damuwa muje na dubashi, duk suka rankayo har matar sa, suna shiga falon suka tsaya, safna tace muje yana ciki, mijin yace a,a je kigaya mai idan zai iya fitowa yafito inkuma bazai iyaba saina shiga.
safna tana shiga tasame shi yadda tabar shi be daina surutun ba,tasan jalal batashi zaiyi ba tace yaya dan Allah kadaina magana kayi shiru gayinan za,aduba ka, bece komai ba sai kokari riketa yake taje tace wa mutumin yace kashiga.
safna bata koma ba zama tayi kusada matar, ta kalleta tace ki kwatar da hankalin ki in Allah ya yarda zai samu sauki , tasake cewa gashi muna kusa amman bamu sanjuna ba, ya sunanki?
waigowa tayi gefen ta tace sunana safna kefa? tace nikuma khadija, suna cikin haka mutumin ya fito yana murmushi yace madam karki damu murace tamai mugun kamu amman dazaran yasha magani zai samu sauki, yajuya barayi matar sa yace khadija zomuje nabaki magani ki kawo mata.
bayan kadija takawo magani tare da yi mata bayani ruwa ta dauka ta nufi dakin ta same shi kwance yadai rage surutun da yakeyi tace sannu yaya tashi kasha magani.
jalal ya bude baki cikin murya kalan na me sambatu yace aini bana shan magani safna ki tambayi ummi kiji.
kalon shi tayi da mamaki tace toh ai ko saika sha yama za,ayi kace wani baka shan magani saikace wani karami yaro.
nidai gaskiya katashi kawai kasha.
jalal ya sake cewa safna ki aje maganin nan ko ganin shi bana son yi.
kuka ta saka da karfi, tana fadi toh ni ya kake son nayi gashi bacci nakeji kaikuma sai faman sambatu kakeyi.
jalal yana kokari jan bargo ya rufe jikin shi saka makon zazzabin da ya dawo mishi yace zoki kwanta na bari.
ni sai kasha maganin zan kwata
yace toh naji kawo nasha. mika mishi tayi ya karba yasa abaki ya karbi kofin ruwa yakai bakin sa, kasa hadiyewa yayi ya fara sheka amai.
safna na rike dashi har ya gama hawaye nata zubo mata gashi itama ba kwari gareta ba haka ta kamashi takai shi bayi ta wanke mai jiki, dakinta ta wuce dashi sannan ta dawo ta gyara wajen tanayi ne tana kuka bayan takoma gurin jalal ta dauki wayar jalal takira alhaji.
yana dauka yace jalal, safna tasaka kuka tace daddy yaya bayi da lfy kuma yaki shan magani, saikiran sunan ummi yakeyi.
alhaji yace toh fah, tashin hankali, ciwon jalal wuya gare shi, to ya isa ki daina kukan, share hawayen ki, bari nusaiba zata zo yanzun
[8:23PM, 12/18/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘


Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝


100-102

Bayan ta aje wayar ta zauna ta zuba tagumi zuwa cen taga bacci ya dauki jalal itama kwanciya tayi nan da nan bacci ya dauke ta

lokacin da anty tazo gidan shiru ,tai ta sallama babu amsa zama tayi afalo ta shiga kiran wayar safna, aza bure ta tashi ta nufi wayar tasa akunnen ta, anty tace safna gani afalo, wani sanyi taji azuciyar ta ta nufi falo da sauri

bayan sun gaisa anty tace yaya yace jalal babu lfy ko, yana Ina
safna tace yana kwance ya samu bacci. jeki tasoshi yasha magani
anty ai baya iya tashi bakiga inda ya ragwar gwabe ba.
anty tace muje nagani
Suna shiga anty ta fara tashin jalal yabude ido yafara fadin ummi kaina zai fashi
cikin fada anty tace ya fashe din dan baka da lfy kuma duk sai kabi ka damu mutane da surutu saikace karamin yaro.
jalal yasake cewa safna kira min ummi. safna hannu tasa ta dauki wayar jalal anty nusaiba tace safna ajiye wayar nan baza akirata ba idan kamatsu katashi katafi da kan ka katon banza kawai, haka zaka haifi yara suga ubansu yana wannan tabaran

jalal yace toh naji tashi ki tafi gida. tace babu inda zani tashi zakayi kasha magani dan me shagwaba kan bata nan.
kalon safna yayi yamaida idon shi ya rufe daker anty ta shawo kan jalal yasha magani saida ta dama mai acukali.
bayan yasha be jima ba bacci ya kwasheshi .

washe gari jalal yatashi jikin shi yayi sauki sosai ya shiga bayi yayi al,wala yafito ya fara tashin safna tashi kiyi sallah.
mamaki ne ya kamata ta kasa daurewa tace yaya kaji sauki ne?
daure fuska yayi yace eh.
safna kwashewa tayi da dariya tana fadin Allah yakara sauki.


Please Login or Register in order to submit comment