Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dama jira take afadi gidan da jalal zaizauna su cika kudurin su ita da kawar ta madina.

bayan sun dauki hanya dukkan su gaba suka zauna ummi ta daga waya zuwa cen tace dona madina tama bayani ko ? , jalal beji amsan me aka bataba, ta kashe wayar tana murmushi Kara kiran wayar tayi tace madina har yanzun baku zoba, nagaji da jira gani ma zantafi gidan danki za a zuba kaya agidan , bayan ummi ta gama waya jalal yace ummi naga kina shashshare bikin nan ne.
tace ba haka bane jalal aini babu wadda yakaini farin ciki ayanzun na fahimci kana son safna da yawa dan haka nima na fara jin Ina sonta , saidai abu daya yake damu na , ban so ka aure yariyar da sultan yayi soyayya da ita ba, saboda sultan fa dan duniya ne.
Jalal be gane inda ummi ta dosaba yace ummi ki daina tuna wannan yariga ya wuce kuma sultan ai babu abinda ya isa yayi min, nidai burina kawai adaura auren.

ummi ma ta gane jalal be fahimce taba, da wannan tunani suka isa gidan, kan kace meye har angama gyara gidan, ummi tsayawa tayi tana kallon dukiyar da aka zuba agidan, alhaji ya kashe kudi saikace kairat zai aurar, badan madina tace tabi komai ahankali ba toh da yau saisun kwashi rigima da alhaji, haka suka kamo hanya ita da jalal amota jalal sai santin gidan yake.
gani inda yake ta murna ummi tace gaskiya jalal guri yayi kyau.
cikin murmushi ya waigo yace ummi ai bakiga kyauba sai safna ta shiga gidan, zakiga yadda zai kara haske.
kulewa tayi sosai amman bata bari ya gane ba tayi mai murmushi kawai.
Jalal kuwa dadi yaji ummi ta fara son safna tuni ya nemi haushin ta da yakeji da ya rasa, dan haka yashiga zuba mata shagwaba, ummi kinsan menene?
tace a,a yaro sai ka fada.
yace safna fah sai kin dan mata fada bata sakin jikinta dani, kamar ma tsorona takeji kuma dacen ba haka take minba, cikin shagwaba ya fadi maganar.

ummi daurewa tayi tayi murmushi tace jalal manya, kabari mana adaura aure duk zata Bari
da haka suka isa gida lakacin yamma tayi sosai, tana shiga falon sukayi ido hudu da safna tana kusa da hajiya a zaune ganin tayi ta kara kyau da sheki gawani zanen filawa wadan tunda take zuwa bikin yaran kawayen ta bata taba ganin wada yakwai haduwar wannan ba, sai satar kallota take , tare da kara jin haushin anty nusaiba tasan tayi ne dan jalal ya rikice, bayan ta gaida hajiya ta shige dakin ta.
hajiya ta kalli safna tace me yasa baki gaishe da ummin ku ba, maza ki bita daki ki gaida ta.
safna tashi ga da sallama ummi ta dago ta kalle ta, tace yaushe kuka dowa?
tace bamu dade da shigowa ba.
tasake cewa jalal yasan kundawo? nima basan ko yasani ba, tabe baki tayi tace fita kibani waje.

da daddare gidan ya kaceme gidan biki sosai sai haya niya ake aharabar gidan kuwa su jalal ne da abokan sa sai hayaniya sukeyi.
zuwa cen kawayen ummi suka fara shigowa wannan karon basu tsaya a falo ba barayin ummi suka shiga, zuwa cen suka saki sauti.


bayan ansaka safna alalle tana ta kuka yau itace za,ama aure ba dangin ta ko guda daya ita da zata samo ko goggo ce tagani agurin bikin nan da zatayi farin ciki da haka da ace babu kowa nata kasa bacci tayi sai juye take babu wadda tafi fado mata arai kamar iya taso Allah ya bar mata iya, haka taita share hawaye dan bata son anty nusaiba ta juwota, daga cen ta fara jiyo muryar alhji yana fadin innalillahi wa,ina ilaihir raju,un sai maimaitawa yakeyi mikewa tayi ta zauna ,tana kallon su hajiya suka fita akabarta ita kaidai adakin, dan haka tabiyo bayan su, gani tayi duk sun tsaya sunyi cirko cirko, alhaji ko sai share zuba ya keyi jalal na gefe daga shi sai gajeren wando, ummi kuwa sai rusa kuka take, cikin rudu safna tace me yafaru?
anty nusaiba tace karku gaya mata saida safe.
ummi tace ai gara agaya mata tunda kowa yasani, safna gidan da zaku zauna ya kone babu abinda aka dauka acikin sa.
safna neman kujera tayi ta zauna ta rufe ido bata sam ma me zata ceba.
jalal kuwa kansa akasa yake, yaki dagowa.
alhji yace bakomai kowa ya koma ya kwata saida safe Allah yasa haka shine mafi alheri.
ummi tace ai alhji bamuga ta barciba munfah gaiyata muta ne gashi gobe ne daurin aure, yaka mata asan abinyi, ni ina ganin kawai adaga bikin kawai hankali kwance.
bata gama rufe baki ba jalal yace ni gaskiya ban yaddaba ummi, ni dai kawai ayi.
cikin fada alhaji yace kai jalal baka da kunya ko ya manya suna magana zaka saka baki, ai biki yazama dole adaga shi, wuce kaba mutane waje.
da sauri yabar wajen ya shige dakin shi ya bogo kofar.
hajiya tace toh yanzun kayanke hukunci ne kabamu umarni mu watse koko shawara kake nema.
sai lokacin ya tuna mahaifiyar shifa tana wajen dan haka yace hajiya kiyi hakuri nayi kuskure, shawara nake nema yanzun yaya kamata ayi.
hajiya tace toh nidai ban yadda adaga ba kowa yaci gaba da abinda yake biki nanan babu fashi


07014197556.....✍
[8:48PM, 12/4/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘


Story
&
written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝


51-53


Alhaji yace shikenan hajiya duk inda kikace haka za,ayi,haka kowa ya koma ya kwanta kowa zuciya babu dadi, jalal kuwa bayan ya koma daki kuka ya saka gidan da aka dade ana ginawa saida aka gama kashe kudi, zargi kala kala ya ziyarci zuciyar shi gaskiya yana zargi sultan da mahaifiyar shi ,kafin safe idon jalal yayi jazur sun dan tasa .

karfe bakwai jalal ya fito sanye da jallabiya fara sol , da bakin glass a idon sa, saboda baya son afahimci halin da yake ciki , saida ya fara gaida su hajiya sannan ya wace dakin alhaji, yana shiga yacire glass din ya rike ahannun shi, alhaji ya kalli jalal yace wai kai ba kasan kaddara bane ji inda fuskar ka ta koma saikace ba musulmi ba.
Jalal yace daddy ba haka bane abin da yake bata min rai nasan gidan nan kona shi akayi kuma wlh nasan bazai wuce sultan bane dan nasan shi kadai ne zai min haka.
dakatar dashi alhaji yayi cikin fada karna kara jin kafadi wannan maganar mubarwa Allah kawai shiyafi, kuma daurin aure nanan insha Allah ajima za,a daura .
dadi sosai jalal yaji yace daddy nagode yana fitowa dakin ummi ya shiga suna saune ita da wata kawar ta data kwana agida.
ummi tace kardai kacemin kuka ka kwana kanayi jalal kana sone kayi kanka illa akan yariyar da badamuwa tayi dakai ba.
dokar dakai yayi yace ummi me yasa kikace haka, ni nasan safna nasona kawai domuwa ne ya mata yawa shiyasa ma nafi son adaura auran ko hakalin ta zai kwanta, nima kaina hakali na ba,a kwance yake ba bare kuma safna.

hajiya adama kawar ummi dake zaune agefe tace rabo da ita jalal kaji , ance maganar bikin nanan ko?
eh yana nan in Allah ya yarda
hajiya adama tasa ke cewa toh yanzun a ina zaka zauna kenan?
yace nima ban sani ba.
jalal ya gaji da tambayoyin su dan haka yace ummi bari naje

bayan ya fito yayi tunani yaje yaga halin da safna take ciki dan haka ya doshi daki, dakin cike yake da mutane, su anty nusaiba ne sauran dai duk besan suba, bayan yagaida su, ya hango safna daga cen bayan anty nusaiba, yace anty dan turomin yariyar cen, yajuya zaita fi anty ta tsaida shi tace zoka zauna kuyi maganar adaki dan abin ya fara bani tsoro, mikewa sukayi suka fita jalal yashigo cikin dakin ya zauna abakin gado yace safna tashi mana, ke wacce irin amarya ce har yanzun kina kwance.

mikewa tayi ta gaida shi, jalal yace safna kinji abinda ya same mu ko, dan Allah karki ce zakisa wannan abun a zuciyar ki ya dame ki,
tace bakomai yaya Allah yasa haka shi yafi alheri
ameen safna .
ta sake cewa yaya me yasame ka a ido naga yayi ja?
jalal yayi mamakin ya akayi ta gani bayan ba kallon shi take ba kanta akasa, dariya yayi yace ta yaya akayi kikaga idona bayan ba kallona kikeba?
juyar da kai tayi tace nifa gani nayi kamar yayi ja
Eh ai naji shine nake tambaya ko kina da ido ne atakiyar kai dan ni kanki kawai nake gani.
safna bata ce komai ba tayi shiro tana wasa da yatsun hannun ta.
daidai lokacin aka kirashi awaya yadauka yana fadin amir kun iso ne, ok to ganinan zuwa.
juyawa yayi yakalli safna yace, yarinya zama ki bari ne, dan yau a gado daya zamu kwana.
dasauri ta kalli jalal ta sake yin kasa dakai.
jalal yace a,a ki kalleni da kyau.


karfe 2:30 Jama,a da dama suka shaida daurin auren abduljalal da safna acikin wa,inda suka shaida daurin auran harda baffa wanda alhaji yaje ya taho dashi yaso yaki zuwa amman alhaji yace yayi danshi, dan haka ana daura auran alhaji yaba da mota aka mai dashi gida, jalal kuwa da ka ganshi kasan yana cikin farin ciki.
acikin gida kuwa safna ce da wasu kawayen ta su biyu bata san waya gaya musuba sai dai kawai ganin su tayi,tana ganin su kuwa suka shiga fira tuni ta manta da bacin ran dake damunta anty tashigo ta ajewa safna wasu kaya tace maza kisaka kije waje jalal na kiranki zaku gaisa da abokan sa.

tun safe safna bata fitoba sai yanzun tana fito falo su hajiya ne da mutanen ta cike afalo suka saka guda, safna kuka tasaka musu yau gata atsakiyan dagin miji bata da kowa, dagin miji sune gatan ta wannan abu kawai in tatuna yana sata cikin baccin rai sai a yanzun wani kalma na goggo yake fado mata ki zauna anan bari naje na dawo haka banzayen kakan ninki suka ma uwarki har ta mutu bata kara sakasu a ido ba, goggo tana nufen mahaifiyar tama haka abarta, ko shiyasa bata taba gani wani dan uwan mahaifyar taba kara rushiwa tayi da kuka hajiya tace fatima kawo ta nan, hajiya fatima ta kawota har gaban hajiya kwatar da ita tayi ajikinta taita mata nasiha.

bayan ta dan natsu hajiya tace tashi kije ki gaida ummin ko, sai ki wuce gurin su jalal din.

sun shiga ita da kawayenta ta gaida su suka amsa ba yabo ba fallasa.

sun doshi gurin rinsu jalal, jalal ya hango su tun daga nesa da sauri ya daga waya yace anty dan Allah ki leko ki mayar da safna gida tasaka hijjabi.
dariya tayi tace haba jalal kabarta mana yau daya dai


kafin yakara wani magana sun iso wajen dan haka ya daure fuska suka gaida su cikin sakin fuska suka amsa dayan daga cikin abokan ne wadda suke kira amir ya farawa safna tsiya amaryar mu kirike shi da kyau duk abinda yake so abashi dan kinsan shagwabebbe ne ko cokali be iya rikewa ba.
jalal yace toh malam ya isheka haka kuma.
amir yace be isaba safna kinajina nina san halin jalal tare mukayi karatu jalal bashi da matsala amman yanada fushi idan antaba shi, ya kalli jalal yayi murmushi sannan yace safna abu nagaba jalal nada tsananin kishi .
da sauri jalal ya kalli amir yace wai amir lfyr ka kalau kuwa, ke ku wuce gida.
amir yace yazaka koresu ka barsu mana ai ban gama ba, hirace ta barke takanin safyya kawar safna da amir amir , jalal zuwa yayi yakama hannu safna yashiga da ita har cikin gida.

da daddare mutane suka fara watsewa bakin hajiya kowa duk sun wuce gidan ta ,sai hajiya da anty nusaiba kawai suka rage barayin ummi kuwa daga ita sai kawarta madina safna kuwa na dakin su da ita sai kairat, kairat tace anty safna kikace da bikin ki zamuyi shagali amman yanzun sai naga ba,ayi komai ba, natabayi yaya yace wai kece baki so ayi.
Safna tace haka yace miki wayau yayi miki shine baya so,kairat tace ai dama yaya yacika wayau haka ma da yace in kukayi aure zai tafi dani yanzun kuma yace wai wasa yake min, kuma wlh bazan yarda ba saina biku yaya zaku tafi kubar ni ni kadai agida
safna tace ai bama inda zamu bakiga gidan ya kone bane.
suna cikin haka jalal yashigo dakin yace safna kizo hajiya nakiran ki tamike suka fito tare ahanyar su ne jalal ya ce safna koda an tambaye ki Ina kike son zama kafin musami wani gidan kice abarki adakina.
dauri safna ta fara kuka wlh yaya bazan iyaba .
yace daurewa zakiyi safna ,ko kin fi son hajiya ta wuce dake, ni indai hajiya ta wuce dake bazan iya barciba wlh me zanyi agidan nan, to sai dai nima na biko.

gani tayi kamar ba,a cikin hakalin shi yake ba, matsowa yayi yariketa safna ki taimakeni karki bari atafi dake.
safna ko azuciyar ta tafi son tabi hajiya dan gidan nan kwata kwata baya yi mata dadi jita take kamar a kaya take.


Suna shiga falan alhaji ,suka ga kowa kowa ya hallara har ummi da kanin alhaji bayan sun zauna aka fara yi musu nasiha kanin alhaji baba salisu yace to jalal hajiya nason ta tafi da safna gidanta kafin agama gyara ma gidan ka dan haka nace bari muje ta bakinka tukuna dan yanzun kai kake da iko da ita, meye ra,ayin ka?
shiru yayi kansa kasa.


Safna ko tunani take azuciyar ta wato jalal shi yakasa magana ita kuma zai sata tayi rashin kunya.

Jalal beyi magana ba saida baba salisu yakara maimaita tambayan shi.
sai da jalal ya juya gurin hajiya sannan yace toh hajiya harda ni zaki tafi ko?
duk falon dariya suka saka banda safna da ummi dan ummi kara tamke fuska tayi.
baba salisu yace ja,iri ai dani zakayi magana bada hajiya ba.
Jalal bece komai ba sai faman sosa kai yakai yake.
baba salisu yace indai na kula da kyau, jalal be yadda atafi mai da mata ba.
anty nusaiba tace toh hajiya kibar mai matarsa kawai tunda baso yake ba, da sauri ummi tace nima dai abinda nagani kenan.
hajiya tace a,a nima ba matsawa nayiba kusha zaman Ku, in ma dakinka zaka kaita bisimillah.

hajiya ta sosa mai inda yake mai kaikayi dan haka ya farawa anty nusaiba alama da ido , banza tayi dashi kamar bata gani ba.
baba salisu ya kula dan haka yace jalal kamar kwai magana abakin ka, nusauba me jalal yake gaya miki.
dariya tayi tace yaya nima ban fahimce shiba.
yace toh kuje waje kuyi magana duk abinda yake so ya fada kar yaji kunya ai matar sa ce.
anty tace jalal kayi hakuri mana kasan fa mamar ka bazata yarda dahaka ba.
anty nidai kawai ku kaita dakina ina da dalilina inhar kuka tafi baku kaita dakina ba nasan ganin safna ma sai ya gagareni ummi zata iya hanani shiga dakin su safna.

suna komawa anty tace yaya shifa wai so yake ta koma dakinsa.
baba salisu da alhaji suka hada baki to dan wannan shine ka kasa fada kai da matar ka, nusaiba kai mishi matar sa daki kizo mutafi.
ummi mikewa ta tasaka kuka agidan nan, za,yi wannan kwama calar wlh wlh bata isa ta hada gado da jalal ba
[7:43PM, 12/5/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘



Story
&
written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝



54-57

Han kalin kowa koma wa yayi gurin ummi safna kuwa hawaye ne ke zuba a idanun ta kamar an bude faffu hajiya tace me kike nufi da wannan kalmar taki?

hajiya nidai gaskiya ban yadda da wan shawarar ba kawai ya bari sai sun samo gida amman wannan ai bai dace ba.

hajiya tace to muna sauraran ki sai ki gaya mana yadda ya dace tun da kin fimu hankali.
bude baki tayi zata yi magana alhaji ya dakatar da ita yanzu nan dan baki da kunya magana zakiyi , mikiwa tayi tabar wajen .

hajiya ta juya tace ke nusaiba rakata dakin jalal

daga dakin alhaji aka wuce da ita dakin jalal ban da kuka babu abin da safna take, abakin gado ta zaunar da ita, rabon da ta shiga dakin jalal tun farkon zuwan ta gidan .

anty nusaiba juyawa tayi tace safna sai da safe Zan kiraki awaya kema idan kina son wani abu ki kirani kigaya min.
kasa amsawa tayi sai kuka take dan gaskiya dan zaman nan da sukayi da anty suyi matukar shakuwa da juna tanan zaune tafara tunanin wannan wani irin aure ne dan dai bani da gatane da inada gata baza akawo ni dakin jalal ba, da sai dai nazauna agidan iyaye na ,tana cikin tunani taji an turo kofar ta zata jalal ne sai taga anty tana shigo da akwatuna harta gama shigo dasu gaba daya sannan takuma yi mata sallama ta fita.

zuwa cen taji tashin motar su takara saka kuka.
shiko jalal bayan sun tafi yayi masu alhaji sai da safe ummi shiru tayi bata amsa ba.
bayan jalal ya wuce ummi ma ta wuce dakin ta ,alhaji ya bita da kallo ji yayi babu dadi suda suka aurar da dan su kamata yayi suyi farin ciki , dan haka yabi bayan ta yana shiga ya fara rarrashin ta sannan ya tambaye ta me yasa bata son auran safna da jalal.

ummi tace au sai yanzo ne zaka tambaye ni ,ai aikin gama yariga ya gama kuma, ba, anyi ba ,har kunsa masa ita adaki , to meye Kuma zaka zo kana tambaya ta.
alhaji dai da yaga ummi baza ta gane ba ya tashi yabar mata dakin.

alhaji na fita takira madina ta gaya mata halin da ake ciki.
madina tace gaskiya zaliha ke kike jawa kan ki nace miki kwatar da kai zakiyi karki bari kowa yagane baki son auran , irin wannan ai sai ki tona kin ki.
ummi tace yaushe kuma aisun riga ma sun gane, ni ba wannna bama, madina bakiga inda jalal ke rawar jiki ba, a yadda naga take taken sa ,yau bazai iya hakuri ba sai ya kusan ce ta, ni kuma abin da natsana kenan .
madina tace ni wlh mamaki kike bani ke baki san yadda zakiyi ki hana yarinyar kwana adakin ba cikin kissa da dubara, kuma karki kara nuna baki son yarinya shi kuma jalal kija shi ajiki kamar da, indai kikai haka sai kiga kafin su tare auran ya kare.

bayan sun gama waya da madina ummi ta fito ta nufi dakin jalal

jalal kuwa yana manne jikin safna sai rarrashin ta yake, bayan tayi shiru yace to ki saki jikin ki mana keda dakin ki, cire gyalen kisha iska, kara rike gyalan tayi , jalal yayi dariya yace kicire gyalan mana ki kwanta ni ba abin da zan miki.
safna shiru tayi kamar bada ita yake magana ba, dan haka jalal ya rike gyalan yana kokarin cire mata, suna cikin haka sukaji. anturo kofar jalal ya sake gyalen ya juwo da sauri sai da gaban shi ya fadi ganin ummi adakin safna kowa mikewa tayi afirgice.
jalal yaje ya rike safna ajikin sa , sannan yace ummi lafiya kuwa?

jalal lfy lau, safna ni kika gani kika firgita haka sai kace kinga dodo, daga na fada gaskiya, lallai dama jalal yace kina son sa sai yanzun na tabbatar da haka.
zuwa tayi har jikin jalal ta jawo safna jikin ta, tace ki kwatar da hankalin ki kinji yata, niba kin ki nake ba, duk abinda jalal ke so dole nasoshi


jalal dadi yaji har ran sa ,sai murmushi yake.
ummi jan safna tayi zuwa kojerar dake gefe suka zauna ta kwatar da ita ajikin ta tana shafa kanta, tace safna kinyi kyau sosai, sai dai nasan ba ,dan gyara kiba, da jalal zai yadda yadan kara mana kwanaki da an gyara ki.
jalal ya kalli ummi yace wani irin gyara ne wannan?
tace gyaran jiki mana irin namu na mata, kai nasan bazaka fahimta ba kabani ita kwai koma meye zaka gani.
au ummi gyaran ma har sai tabar dakin nan, to abar gyaran mana ko yanzu ma ai a gyare take.
ummi dariya tayi tace jalal ko sati biyu ne kabani na dan gyara ma ita, kai dan baka da kunya ma ina ma magana kana mayar min, ke safna rabu dashi tashi muje.
jalal bin bayan su yayi yana fadin ummi ni dai gaskiya bana son wani gyara.

tsayawa tayi tace au biyomu kayi, jawo safna tayi tace jeka da ita, ai bansan tsumuwar taka takai nan ba.
kunyar ummi ce ta kama jalal yace kai ummi me yayi zafi kuma toh shi kenan kuje, kafen ya gama magana ummi tayi gaba, dan haka jalal ya rike mata hannu yakai ta har dakin ummi yace ummi gata nan.
ya juya ya fita ummi ta juyowa tayi ta kalli safna tana murmushi tace jeki dakin ku, ki kwanta kinji 'yata.

cikin dare jalal kasa bacci yayi sai juyi yake agado yaso ya kasan ce da matar sa tunani kala kala ne azuciyar shi yana mamakin ummi, wani irin abu ne wannan da fah ta nuna bata son akawo safna dakin sa, har tana ikirarin safna bata isa ta hada gado dashi ba, lallai akwai wata akasa mikiwa yayi ya fara zagaye dakin to ummi me take nufe akwai abinda take shir yawa so take taraba ni da safna, lallai kwai rigima sai dai ummi tace bani da

Please Login or Register in order to submit comment