Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai tsayi da safna baki gane taba, hannu tasa ta daga safna, safna ma gani tayi kamar mamarta sunyi kama da mamarta sosai dan haka ta rungume ta tana kuka take taji son yaya rabi ya kama ta jinta take kamar mahaifiyar ta, duk da cewa da kaga yaya rabi kasan tana cikin yanayi na talauci.
aliya tazo ta baya ta tsaya tace anty safna. Cikin sauri ta waigo sukayi arba da juna safna sakin yaya rabi tayi ta rike aliya haka sukaita murnan ganin juna sai gurin la,asar suka fito, safna na rike da aliya wai ita adole sai dai sutafi da ita.
mama rabi tace safna kibari ran suna in munzo sai tazauna tamiki kwana biyu kinga yazon kayan ta duk suyi dauda.
safna tace mama toh basai ta saka nawa ba. ummi tace yaya ai hakuri zakiyi kawai mutafi da ita.
mama rabi tace toh Allah ya tsare sai munzo suna.
bayan sun dauki hanya hajiya tace toh kodai zamuyi gaba daya ne daga nan mu wuce gidan goggo safna cikin murna tace eh Hajiya.
alhaji ne yace toh bari akira jalal agaya mishi dan motar sa daban kar ya wuce gida.
bayan alhaji yagama waya da jalal yace yaran dai zamani basu da kunya kunga wai jalal tunanin yaran shi yake wai cewa yayi za,a kwasar musu iskar mota, dariya sukayi ummi ta kara rufe jariran ta rungume su ajikin ta, suna isa gidan malam musa alhaji da hajiya ne kadai suka sauka amotar suka shiga gidan da sallama, goggo ta fitoh daga daki tana fadin wai wai hajiya kece da kanki sannun ku da zuwa tabarma ta shin fida bayan sun gaisa goggo tace bari naje na sowo muku shinkafa da wake.
hajiya tace a,a ni ba zama nazoba nazone naga jikokina.
cikin fadowan gaba tace aiko basa nan iro yana gun yansan da an kamashi itako salame yanzon ta dauki tallan gyada.
cikin mamaki hajiya tace a,a batayi aure ba?
hawaye ta fara sharewa tace ai ya fasa tunda yagano ciki gare ta.
hajiya ta girgiza kai tace toh kizo ki raka mu gidan da dayar yariyar take naganta.
goggo tace ayya ai sun bar garin nan kwata kwata yanzon bansan inda suke ba.
alhaji yace tohfah mukuma gashi ganinta mukazo ya sunan tane ?
baki na rawa tace safna , suna cikin haka saiga ummi sun shigo da jalal goggo ta zabura tamike tami tana fadin yau na shiga uku karya ta takare dan Allah ku rufamin asiri wlh bansan inda safna take ba, nan da nan tashiga basu lbr tana kuka .
bayan ta gama ne hajiya tace to yanzon meye ribarki?
babu wlh kawai bakin kishi ne ya debeni har na aikata haka gashinan alhakin ta na bibiya ta yara na duk babu nagari kuka goggo taci sosai babu me lallashin ta hajiya fadi take kigama kukan kije ki ne momin jikata dan ba yadda zanyi ba.
Idon goggo duk sun fito waje kuka harda majina.
alhajine yama jalal umarnin ya shigo da matar shi, dan haka ya juya ya shigo da safna safna na shigowa goggo ta kara tsorata , tace dama kunsan safna ne, a Ina kuka same ta, zuwa tayi ta fara duba jikin safna tace ikon Allah safna ce haka kamar yar wani hamshaki , ni inan cikin bakin ciki da tashin hankali muta ne na nunani wasu suce min uwar karuwa wasu sucemin uwar barawo, cikin kuka take maganar ki yafemin safna na tuba bazan kara ba.
hajiya tace kima Kara mana, ina zaki ganta bare ki kara ita da take dakin mijin ta cikin fada tace ku kuma kutashi mutafi, duk mikewa sukayi suka fita safna ko tsayawa tayi tana kokarin daga goggo hajiya tazo ta jata
[10:21AM, 12/28/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘



Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝


126-130


Lokacin da suka koma gidan hajiya mangariba tayi dan haka alhaji yana sauke su hajiya da su safna suka wuce gida harda jalal, jalal dai fushi yake da safna sosai dan har suka rabo basuyi magana ba.
suma suna sauke ummi masallaci suka wuce saida sukayi sallar ishsha suka dawo gida.
bayan sunja girki ne jalal ya mike yace daddy bari naje gida.
alhaji yace me zaka je kayi agida bayan matarka batanan kayi zamanka mana anan, koba haka ba zaliha?
ummi tabe baki tayi tace alhaji ni yanzo jalal yafi karfi na. Alhaji yace me kuma ya faru kai jalal dawo nan ka zauna, jalal na zama alhaji yace me yake faruwa, me ka mata?
sunkuyar dakai yayi yace daddy akan maganar safna ne, yanzun kwata kwata ta rainani rashin kunya take min, kuma wai ummi tace wai dole ni zan bata hakuri, daddy ai ni ya kamata taba hakuri, amman yaya za,ayi kuma ace ni zan bata hakuri ai sai taji dadi nan gaba ta kara yimin.
alhaji yace zaliha yaya haka, haka ake hukunci?
alhaji nifa bana son ganin safna cikin bacin rai, dan haka ni dai kawai kaje ya bata hakuri, shi wanene da bazata mai rashin kunya ba, ai nima gashi nan kanamin rashin kunyar, wlh inhar bakaje ka rarrashi yariyar nanba zakaga abin da zan maka.
kallon ummi yayi yace toh shike nan ummi naji, a han zar ce ya bar wajen dakin sa ya nufa.
alhaji yabi jalal da kallo yace zaliha bafa haka akeyi ba kina nufin yanzon kinfi son ganin nashi bacin ran akan na safna?
Alhaji aishi babba ne kuma cewa nayi yayi hakuri yabata hakuri.. Katseta alhaji yayi yace aiko indai haka zaki ringayi bakice su zauna lafiya ba dan zaki samai tsanar ta, ai shi amatsayin shi na namiji baxai so matar sa ta raina shiba, kuma nina tabbata ta bata mai rai ne shiya sa yayi fushi da ita amman yana son matar sa bakuma wai dan jalal yana dana bane na yabe shi, dukkan su yaya nane kuma daidai gwargwado nasan halin su. haka alhaji yayita ma ummi nasiha me ratsa jiki.
zuwa cen ummi ta fara kuka bakin ta yana rawa tace alhaji akwai abin da yake damuna ina tunanin idan kaji mgnr zaka tsora ta dani amman yazama dole na fada dan innemi gafarar ka amman dan Allah ina neman wani alfarma karka gayawa kowa wannan maganar dan idan maganar nan ta fito toh lallai naji kunya kukanta karuwa yayi saida ta waiga ko akwai wani dake tahowa sannan tace alhaji gidan jalal daya kone... Alhaji be Bari ummi ta karashi maganar taba yace nasan komai xaliha bake da madina kuka shirya komai ba ai tuni nasa aka kama madina da kanin ta duna sai da madina ta kwashe sati buyu gurin yan sanda, shiko duna har yanzun yana hannu .
kuka ummi take sosai tana rokon alhaji gafara tana fadin sharrin zuciya ne.
alhaji ya fara share mata hawaye yace bar kuka zaliha ni tuni na yafe miki komai yawuce sai dai muce Allah ya kiyaye gaba.
nagode alhaji har ina tunanin inkaji wannan maganar zaka sakeni ashe kai kallona kawai kake.
alhaji yake yayi yace aitun lokacin tarewar jalal nasan komai dan lokacin na tsane ki shi yasama dazan tafi ban miki sallama ba dan gani nake zaki iya kisa.

washe gari karfe 7:30 jalal ya fito cikin shirin shi na zuwa office sallama yayi ma ummi ta amsa bakamar yadda jalal ya zata ba, sannan ya mike yace nafi.
waigowa tayi tace zaka biya gurin yan biyu ne sannan ka wuce ko?
Jalal yace a,a saina tashi office saina tsaya acen.
a,a jalal be kamata ba kadai biya ko atsaye ne ka gansu sai ka tafi, ga kairat cen katafi da ita daman ta dame ni wai bataga yan buyu ba.
suna isa gidan kairat ta fita aguje ta shi gidan lokacin da jalal ya shiga ya same tana rike da yaran sai faman jagwalgwala su take wai ita tana musu wasa .
saida ya gaida hajiya ya tabaye ta anty nusaiba bataxo ba, hajiya tace na nan tafe.
safna nazaune kusa da hajiya tace ina kwana.
kasa kasa ya amsa yamike yaje gaban kairat ya tsuguna ya sunbaci yan biyu ya mike yace hajiya na tafi.
safna ta mike tabi bayan shi, yana fita daga falon ta rike shi, juyowa yayi yace safna sakeni karki ya mutsamin kaya anjima zan dawo .
kara shagwar gwabewa tayi tana buga kafa kamar yanda kananan yara keyi tare da kuka ahankali .
murmushi jalal yayi yasa hannu ya riko safna yace toh ya isa haka safna, me kike so.
cikin kuka tace bakai bane kaketa fushi ko kallona baka yi. Jalal yace safna kenan bake kikace na daina miki magana ba, har kina min rashin kunya.
toh kayi hakuri banzan kara ba.
dadi jalal yaji yace shikenan safna ya wuce shiga ciki idan na dawo zan zo .

haka safna tacigaba da zama gidan Hajiya cinkin kwanciyar hakali kowa kokari yake ya faranta mata rai Ana gobe suna su yaya rabi suka iso gidan hajiya ita da mama rahane washe gari akayi suna nagani na fada alhaji da ummi sun kashe kudi sosai, jalal kuwa ya tara abokan shi sosai itako safna dama bawasu kawaye gare taba dan haka bawasu mutane ta tara ba daga safiya sai halima su kadai ne adakin sai kuma kanwar ta aliya haka taro ya tashi lfy yaran sukaci sunan ummi da daddy wato yusuf da zaliha.
Washe gari suna saiga goggo da salame sunayin sallama hajiya tace su fita mata daga gida kuka goggo ta saka tana fadin hajiya dan Allah kiyi hakuri ki bari na neme gafarar safna.
safna tana daki ita aliya suka fara jiwo kukan goggo fitowa tayi da sauri , goggo nagani safna tace safna naxo neman gafarar ki ne karna mutu da wannan nauyin dan Allah ki yafemin
itama safna share hawaye tayi sannan tace goggo kitashi ni dama na yafe miki komai ya wuce, kallon salame tayi taga cikin ta har ya fara fitowa sai yama suka tafi safna ta roko su har bakin gate ta basu kudi masu yawa tare dace ma goggo idan suna bukatar wani abu su mata magana.


bayan shekara uku jalal da safna ne tafe a mota daddy da ummi suna baya sai faman surutu suke , safna tace yaya wai ina zamu ne?
yace yau gidan ummi zamu tun da ke baki cewa zaki, ke sai dai gidan mama rabi ko kunyar ummi bakiji sai dai ita idan taji ganin ku tazo.
kunya ce ta kama safna tace ba haka bane yaya abin da yasa nafison gidan mama rabi muna hira da aliya. hararan ta jalal yayi bawani ai ummi ma tana jinki da hira saiki ta wani zilzillewa. daddy ne ya leko da kanshi saitin jalal yace abba ni gidan baffa nake so bana son gidan ummi. tsawa jalal yayi mishi tare da fadi daddy In na sake jin kace baka son gidan ummi saina zane ka.
cikin murna ummi tace yauwa abba kamai balala ni ban da ni inason gidan ummi. Jalal yace yauwa ummina ashe dai kin gane. Jalal ya juya barayin safna yace kinga kin koya ma daddy kin gidan ummi ko.
safna shiru tamai domin miyau ne ciki da bakin ta daha suka isa gidan Kairat ta fito da gudu ta rike hannun ummi da daddy suka shiga ciki, sun same ummi da alhaji afalo gudu ummi karama tasake hannun kairat ta fada jikin ummi daddy ma da gudun shi ya nufi alhaji cikin dariya alhaji yace au wato kun raba kenan safna ce ta shigo jalal nabinta abaya sai fada yakeyi.
alhaji yace na kula jalal so yake yazama mafadaci daga shigowa sai fada.
daddy wai yariyar nan idan bata son tamin magana sai ta tara miyau abikin ta.
ummi tace a,a jalal bada gangan take ba saidai idan ciki gare ta. cikin sauri jalal yace ummi ai idan tana da ciki bahaka take yi ba daddawa take ci
dariya sukayi gaba dayan su sannan ummi tace jalal ai ko wani ciki da kalar sa.

*ALHAMDULILLAH*
_anan na kawo karshen wannan lbrn_
Fadeela Lamido
Mmn yazeed
07014197556
*Ni makauniya ce ido na baya ganin comment din kowa saina masoya na😜*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment