Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

1 week insha Allah




Fira sukaɗanyi sama sama daga bisani sukayi sallama......... ..







*INAMA ƊAUKACIN JAMA'AR MUSULMAI BARKA DA ZAGAYOWAR SABUWAR
SHEKARA ALLAH KAHAƊAMU DA ALKHAIRAN CIKINTA YAKAREMU DAGA FITINTINUNTA ALLAH KABA ƘASARMU NAGERI'A ZAMAN LAFIYA 🤲🇳🇬🇳🇬 HAPPY NEW YEAR ALL🥰💃💃💃💯💯💯😍 FROM MUJAHEEDAH MATAR MALAM*






(BASEERATA ITACE ARZIKINA😍)






WhatsApp number 09030835117







➰ BARRISTER KHALEEL➰


*FREEBOOK*

🅿️17&18




DEDUCATED TO MY FANSS ONLY👌😉






STORY AND WRITTEN BY ✍🏻 🥰MUJAHEEDAH🥰 (MATAR 💖 MLM) HEEDAH HAYDAR OSTHMAN




*1/1/2022 Forst january Saturday*





Alhaji lawal kuwa saida yayi tafiya mai nisa sannan yatsaya inda bakowa yafito yaduba gabas da yamma kudu da Arewa baiga kowa hakan yabashi damar buɗe boot ɗinsa yatallabota haryanzu bata motsi jefarda ita yayi Abola sannan yashiga motarsa yafice Abinsa baiko waiwaye halinda take cikiba



Saida yayi nisa yaduba wayarsa yaga missed call ɗin khaleel saida gabansa yafaɗi Afice yace"Allah yasa wannan ɗan banzan yaro bayadawo yau bane dan nasanshi da bin ƙwaƙwaf zai iya ganoni wllh"




*********-;;-**********




Tinda Umma tashiga palourn takejin faɗuwar gabanta yatsananta dama sbd wannan faɗuwar gaban datakekine yasa tadawo gida yanzu


Bakowa ɗakin Alhaji lawal takutsa kai tindaga farkon ɗakin taganshi wani iri gashinan dik hargitse musamman kan gadon idanta yasauka kan ɗan sauran jinin daya goge baigogu dukaba garin sauri

Afili tafurta inna lillahi meke faruwa Anan?



Fitowa tayi tafara kwaɗa kiran saleeha amma shuru ba labarinta ɗakin tasake komawa taɗaura hannu Akai tace"nashiga uku ni kubra ya kashe ƴar mutane kenan" durgushewa Anan tayi tafara zubda hawaye




Kamar Anjehoshi ta kibiya yashigo yana kumfar baki yana masifa ""meye haka kubra? sbd me zakizo nan kinason tonamun Asiri ne komai"?



Cikin masifa tace"Alhaji ka kashe ƴar mutane ko? ina kakai gawarta? Alhaji meyasa baka tsoron Allah? meyasa kake da budurwar zuciya wadda bata wuce jikarkaba ita zakama fyaɗe ? ina zaka da hakken mutane? nashiga uku wannan wace irin masiface"?






Ɗaure fuska yayi yace"kinga kubra ni bankashetaba kawai nafiddata gidannan ne kuma kisani idan kikayi yunƙurin tonamun Asiri ko kikabari my son yaji wannan labarin to wllh zan rufe idona namanta ke matatace dama soyayyarda mukayi wllh naɗau mummunan mataki Akanki kisani sbd samun mulkina ba Abinda bazan iya yiba"


Yana gama faɗin hakan yabar gidan gabaɗai




Tajima tana kukan bakinciki haɗida nadamar sanin Alhaji lawal


.........




*COMMENTS AND SHARE🙏🙏🙏🙏*







[BASEERATA ITACE ARZIKINA]






```WhatsApp num 09030835117```




➰ BARRISTER KHALEEL➰


*FREEBOOK*

🅿️19&20






DEDUCATED TO MY FANSS ONLY👌😉






STORY AND WRITTEN BY ✍🏻 🥰MUJAHEEDAH🥰 (MATAR 💖 MLM) HEEDAH HAYDAR OSTHMAN




*1/1/2022 Sunday forst january*






Kusan 3days ba saleeha ba labarinta Ahankalin mama yatashi sosai ida ƙanwar saleeha Hafsat ƙaramace iyakacinta 10 years amma tanada hankali da shegen wayo tanason yayarta sosai

Mama tace"Hafsatu maza ɗauko wayar nan nakira hajiya naji ko lafiya yau kwana 3 saleeha batazo dubamu ba"




Miƙomata wayar tayi takira tana tafaman ruri amma ba'a ɗaga ba


Lokacin hajiya kubra tana zaune tana tinani saiga kiran mahaifiyar saleeha tsoro yabayyana kan fuskarta ƙin ɗaga kiran tayi dan batasan mezatace mataba kuka kawai yasubuce mata tahau rerawa..





Ganin kiran yasake yankewa mama tace"kinga bata ɗaukaba nashiga uku indai bawani Abu yasameta ba"



Hijab ɗinta tasa tanufi gidan baba idi shine maikulada flowers A gidan Alhaji lawal kuma shine yasamama saleeha Aiki A gidan


Awaje tasameshi shiƙaɗai yana tafama da ƴar redi'on sa
dasallama taƙarasa gurinsa tace" mlm idi wai ko lafiya yau kusan kwana 3 saleeha batazo gidaba kuma kasan ba Acan take kwanaba ganin bata dawoba yasa nakira hjy amma taba ɗauka ba inaji Ajikina kamar ba lfy"




nisawa yayi yace"kada kidamu insha Allah tana lfy watakil aikine yamata yawa amma bari naje nabincikamakiki yanzu dan nima yau kwana na 3 banjeba kinsan banakin daɗi"



Godiya tamasa sannan takoma gida



Shiko yanufe gidan Alhaji



A conpound Alhaji nashirin fita Hjy tarakoshi



Matsowa yayi kusa sasu yagaidasu


Umma ta ansa tana mai tdanbayarsa jikinsa



Yace"dasauƙi hjy yanzu dai Abinda yakawoni maganar yarinyar nan saleeha"




Ba umma ƙaɗaiba hatta shikanshi Daddy saida yaɗan firgita da maganar Amma yawaske


Yace"Badai kana nufin tabar Aiki nan gidan ba"




Mlm idi yace"A'a dama mahaifiyar tace tazo tasameni yanzu a gida akan yau kwana 3 batazo ba bayan kuma ba aikin kwana takemukuba shinen nazo naji ko lfy"?





Umma kasa magana tayi takafe daddy da ido irin kabada ansar dakanka ɗinnan




Cikin wayewa da duniyanci irin na Alhaji garba yayi taslima yace"badai bataje gidaba? Ai yau kwana 3 kenan datafiyarta tinsannan haryanzu batadawo ba yanzuma magana muke nida hjy Akan Anemeka Aji ko lfy"?





Mlm idi yace"innalillahi wa'ainna ilaihin raju'un kenan saleeha taɓata? dan wllh bataje gidaba nashiga uku ni mlm idi gashi nine kawota wannan aikin dama can bason aikatau takeba mahaifiyar tace dani muka takurata"




Dikansu suka ɗau taslima kamar basusan komai ba hk suka waske




Alhaji yace"kada kadamu zankai report ɗin ɓatar ta yanzu nan zatadawo insha Allah"



Dahaka sukayi sallama shiyakoma gida shiko yafita umma takoma ciki tacigaba da kukanta






.
.................




Shara wasu Almajirai sukazo zubarwa Anan sukaga tana motsi A bargon ɗayan yadake yaduba yace"wllh mutum ce kuma bata mutuba"




Ɗayan yace"muje mugayawa mlm"




Aiko dagudu sukaje suka sanar bawani bata lokaci Akataru Agun dataimakon mai Anguwar Aka kaita Asibiti ɗayan ɓangaren kuma suna binciken iyayenta




Saida Akasa police Sannan Aka dubata


Amma dai takamu da matsalar yoyon fitsari...




Sanin Alhajine yasa yakawai police ƙuɗi magana tamutu komai yawuce




Ansallameta takoma gida basuda gata bakomai hkn yasa tadawo yin bara ga tsana haɗida kyara datakesha gun mutane bara tadawo yi


Matsalar yoyon fitsarinta kuwa saidai Abinda yaƙaru kowa gudunta yake sbd matsalar dan wari take sosai


Kuka kam tasha hartagaji tadaina ......








*COMMENTS AND SHARE PLZZZ🙏🙏🙏🙏*








[BASEERATA ITACE ARZIKINA]




WhatsApp num 09030835117







➰ BARRISTER KHALEEL➰


*FREEBOOK*

🅿️21&22






DEDUCATED TO MY FANSS ONLY👌😉






STORY AND WRITTEN BY ✍🏻 🥰MUJAHEEDAH🥰 (MATAR 💖 MLM) HEEDAH HAYDAR OSTHMAN




*1/1/2022 sunday fosrt january*







Bamai ja da mai ƙuɗi dama talaka shi Akaraina dik wani maiƙuɗi kallon ƙasƙanci yakama talaka yazalunceshi amma Azauna lfy tinda yanada ƙuɗi





Ɓangaren khaleel kuwa cikin kwanakinnan Abu yamasa tsaye saiyawan mafalkai yake waɗanda baisan kansuba


Yaudai yashirya tsaf A filin jirgi nagonshi yasha suit black dark da white glass A idansa sai danƙareriyar jacket dayasa




Ahankali yasauko jirgin


Kiran Brr. muda yayi Yace"gani Air port plxx kazo kaɗaukan yanzu"


Baijira ansarshiba yadatse kiran



Bawani bata lokaci yaƙaraso yatayashi ɗaukar Akwatunansa yayi suka shiga motar


Kwantarda kansa yayi jikin kujer yalunshe idansa gabansa nacigaba da faɗuwa musamman dayasauko nan 9jar




Driver muda yake yanata magana yaji shuru yawaigo yadubesa


Taɓasa yayi yace"wai ko barrister Are you owk"?



Dawowa yayi daga duniyar tinanida yafaɗa yanisa kafin yace" nikaina bansan meke damuna Abban Ameera kawai inaji Ajikina Akwai matsala amma bansan inda matsalar zata fitomunba"




Numfashi muda yasauke yace"yau Abban Ameera nasamu? Hunm lalle kana cikin damuwa amma inasan kasani dik tsanani yanatare sauƙi kawaita Anbaton Allah thats best solution"



Danjar hanya tatsaidasu


Still idansa rufe ɗan sauke glss ɗin motar yayi nagabansa dan shigoda iskar waje gabanasa natsananta faɗuwa



Sheƙowa tayi gun motar daidai gunsa tatsaya inda yabuɗe glss ɗin tanafaɗin dan Allah kutaimakamun zansaye magani da Abinci yunwa nakeji tinjiya rabona da Abinci dan Allah Alhaji kutaimakamun" taƙarashe maganar cikin rawar murya kuka nason ƙwacemata"





Muda yabuɗe gaban motar yazaro naira 100 yace"brr. dan Allah bawannan yarinyar"



Shiko jinkamar yasan muryar amma yakasa tina inane yasa yaƙi buɗe idansa wari yakeji dazuwan yarin gun ga Abban Ameera nadamunsa wai yabata sadaka




Buɗe idansa yayi daniyar dashi damai barar dik ya Zazzagemusu kwandon masifa Amma me idansa zaigani.....................





*Hmmmmmmmmmm to saimun sake haɗewa bazan cigaba ba sainaga comments dayawa💃💃 yadda nakeson ganin*






*COMMENTS AND SHARE🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏*








_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_







WhatsApp num 09030835117




➰ BARRISTER KHALEEL➰


*FREEBOOK*

🅿️13&14



DEDUCATED TO MY FANSS ONLY👌😉






STORY AND WRITTEN BY ✍🏻 🥰MUJAHEEDAH🥰 (MATAR 💖 MLM) HEEDAH HAYDAR OSTHMAN




*3/1/2022 MONDAY FORST JANUARY*





Buɗe bakinsa yayi datsananin mamaki fargaba tsoro sukamasa dirar mikiya lokaci ɗaya Zuba mata ido yayi ko ƙyaftawa bayayi tabbas itace itaɗince wllh yafaɗa Afili




Abban Ameera yace"itaɗin wace kasantane? wannanfa mabaraciyace kadubeta dakyau bakafa santaba nikaina sainabi taɗan ɗin nake ganinta kuma dika baiwuce 2 week dafara ganintaba kuma lokacin bakanan yaunefa kadawo 9jar inamai tabbatarmaka dacewa bakasantaba ke ungu barnan ƙarama dake kisawa ranki rayuwar bara Atiti" miƙamata ƙuɗin yayi



Hannu tazura danta ƙarɓa dan itasam bata gane khaleel ba dan rabonta dashi za'a shekara


Zoben hannunta yagani wanda ko wancan lokacin yaganshi



Dasauri yariƙe hannunta yace"Saleeha cikin rawar baki shinwai kece"?



Dasauri tajanye hannunta tace"inakasanni mlm"?



Yace"bakece kike Aiki gidanmuba gidan Alhaji lawal maidala....."


Ɗanrazana tayi dajin sunanda tafi komai tsana Arayuwarta tace cikin rawar murya badai kaine ɗansa barrister khaleel ba"?





Yace"of cause its me saleeha what Are you doing here"? me........


Girgiza kai tafara tareda wurgamusu 100 ɗinsu tace"gaƙuɗinku nan banaso ku mayaudarene kuma macuta bazan taɓa yafemukuba"

Dagudu tabar gun tana ƙoƙarin tsallaka titin Akabada signal damar wucewa Aiko wani maimota yada ƙagu Abasudamar dan sunjima tsaye cikin sauri yafisge motarsa jikake kafffffffffffff yaɗauketa damotar saida tayi sama kafin tadawo ƙasa timmmm take jini yatsartu A bakinta maimotar kuwa tini yaja motarsa A tsorace yagudu yabar tanan dik da wasu sunbishi Amma basu cimmasaba



Tinda take faɗamusu maganganun yadasƙare Agun yanajinta tanbaya yakewa kansa me akamata kodai tahaukacene? idansa nakanta kuma tanaƙoƙarin tsallaka titin yaga mai motar yanufota keeeee yafaɗi cikin ɗaga murya amma ina saikawai yaga Anbigeta ɗin ganin yadda tayi sama zuwa ƙasa yatsoratardashi

Buɗe motar yayi dik da har muda yafara tafiya amma haka yafito ga motoci naneman kaɗeshi shima amma baidamuba gunda take yanufa yana kiran sunanta daƙarfi SALEEHAA! SALEEHA!! SALEEHA!!!..........






(IDAN HAR BA COMMENTS KUSANIFA BA TYPING🤷‍♀️🤷‍♀️🤷‍♀️🤷‍♀️🤷‍♀️🤷‍♀)






_BASEERATA ITACE ARZIKINA_




WhtsApp num 09030835117





➰ BARRISTER KHALEEL➰


*FREEBOOK*

🅿️25&26






DEDUCATED TO MY FANSS ONLY👌😉






STORY AND WRITTEN BY ✍🏻 🥰MUJAHEEDAH🥰 (MATAR 💖 MLM) HEEDAH HAYDAR OSTHMAN



*5/1/12022 FORST JANUARY*






_KUMUN AFUWA FANSSS NARASHIN JINA JIYA GABAƊAYA HAKAN TAFARUNE BISAGA RASHIN WAYATA DANAYI WAYATA TAFAƊI KUMA SIM ƊINA NACIKI NA 09030835117 NAKIRA AMMA INA WANDA YATSINCE WAYAR YAKASHE INSHOURT SAI YAHANANI WAYAR DA SIM ƊIN DIKA SUNZAMA NASA , YANZU DA WANNAN 07031012948 ZAKURIƘA JINA SHINE SABONDA ZANKOMA WHATSAPP DASHI SBD WANCAN SHIDA WAYAR ANRIGA ANSACE SAI HƘR😢_





Hankalinsa Amatiƙar tashe yakutsa kai cikin taron jamar yaɗaukota direct motar Abban Ameera yasata yaja suka nufe Asibiti magana yake yana faman murza hannunta yanacewa"kitashi kada kimutu kigayamun meya faru dake"






Kasancewar brr. khaleel shida brr. muda sanannune musamman khaleel yasa Aka ƙarɓeta cikin sauri Akafara dubata safa damarwa kawai yake sam yakasa zama
.......



Agida kuwa koda Akazoma mama da labarin Ankaɗe saleeha hankalinta yatashi sosai


Baba idi ne yashigo yahau kwantarmata sa hankali yace"ai yasan Asibitinda Aka kaita dan wanda yaƙaɗeta yagudu wani ne daban yakaita Asibiti kifito muje"




Rankayawa sukayi su 3 mama hafsat sai idi sukanufe Asibitin







Sallama baba idi yamusu sugaisa ganin khaleel ne yasa baba idi sake baki




Khaleel yace"lafiya baba naga ka kafeni da ido wani Abu yafaru ne"?




Mama tace"kodai shine yaron Alhaji lawal naga kamarsu"



Jinjina kai khaleel yayi yace"sosai ni ne"




Ganin mama Zatayi mgn dasauri baba idi yadakatar da ita


Yace"Ah bakomai kawai ina mamaki dawowarka ne"




Fitowar likita yasa dik sumaida hankali gurinsa yace"kubiyoni office"



Dika suka shiga


Likitan yace"amma yanaga kunƙara yawa bayan ku kawai nace kushigo"?




Baba idi yayi saurin cewa ba bare Anan ni babanta ita mamarta"



Jinjina kai likitan yayi yace" to mijinta fa"?





Dasauri khaleel yace"miji kuma? dama tayi Aure ne"?



Hafsat tajefa baki tace"A'a yaya batada miji wllh"




Zaro glss ɗin idansa yayi yakafe mahaifiyarta da ido yace"ƴaƴa Amanace garemu wadda Allah yabamu kuma Allah zaitanbayemu Amanar kesam banga kinriƙe Amanarba kinbar ƴarki gatanan kamar mahaukaciya bamufa dubataba saida Aka mata wanka kunbarta tana gantali gashi kenan fyaɗe Akamata to inshourt dai yarku tana yoyan fitsari sannan cikin jikinta na wata 1 ne yazube sakamakon dakuwarda cikinta yayi ga motar da Aka bigeta"






Khaleel yace"ciki kuma ya akayi hkn tafaru wayamata fyaɗen nifa nakasa fahimta" yafaɗe maganar yana maida kallonsa gun mama







Sunkuyarda kai ƙasa kawai tayi takasa magana





Khaleel yace"kenan da gaske batada Aure kuma taɗauki ciki 15 years kukayi wasa da rayuwarta harwannan Abun yafaɗamata? da Anyi magana kuce talauci talauci kanku Akafara? mutum nawane talaka amma yakeɓe yaransa yahanasu talla balantana aikatau meyasa kuke kashe yaranku da kanku"?





Kuka kawai mama take takasa magana dan tahimta baisan waye yamata fyaɗen ba







Khaleel yamatso kusada ita yariƙe hannunta yace"calm dwn dik tsanani sauƙi yana tafe ki kwantarda hankalinki yanzu kugayamun waye yamata hakan"?





Tabbas A yanzu likita yagano yarinyar itace wadda Aka taɓa kawowa kwanakin baya wadda mahaifin khaleel yaɓata kuma shikanshi Alhaji lawal yagargaɗeshi Akan yarufe bakinsa Akan wannan maganar har dubu 100 yabashi zufa tafara karyomasa





Ɓangaren baba idi da brr.muda ma haka


Muda yace Aransa tabbas "Akwai cakwakiya"







Tina irin gargaɗinda Alhaji garba yamusu dama irin murɗiya da Akamusu yasa tace"bamusan kowaye ba bamusanshiba itama bata sanshiba saida yarufe fuska sannan yamata saiyajefar da ita yakuma gudu" taƙarasa maganar cikin kuka





Shifa barrister ne takan maganar mutum ko fuskar mutum yakan fuskance gaskiya ko ƙarya

Baigama wannan tinaninba Hafsata tariƙesa tabayansa tace"nizan gayama gaskiya dik ƙarya suke sunsan kowaye cikin yarinta take maganar



Sunkuyawa yayi yace"yauwa tofaɗamun zansiyamiki choculate da Alawa"





Cikin jindaɗi tafar magana dik da tanaganin mama na bangamata harara amma batayi shuru ba tace" mama kince mufaɗe gsky kullum kada muyi ƙarya Amma ke kinyi ƙarya, wanine inda take masu Aiki waia Alhaji lawal maida.. yauwa natina maidala shine yama Auntyna fyaɗe kuma yajefata A bola wasu suka tsinceta kuma yace"idan muka sake mukagayawa wani sai yakashemu ko ƴansanda sunce baruwansu muyi haƙuri kuka tafara tace"kullum Aunty kuka take kuma wari take kowa gudunta yake bamai sonta"





Motsi kasayi khaleel yayi sam yadaina gane komai jinsa ganinsa dika yaɗauke kallama ɗaya takemasa Amo Akunne Alhaji lawal maidala yamata fyaɗe luuuuuuu yayi baya zaifaɗi.. ............












*COMMENTS AND SHARE🙏🙏*











_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_









WhatsApp num 07031012948








➰ BARRISTER KHALEEL➰


*FREEBOOK*

🅿️27&28



DEDUCATED TO MY FANSS ONLY👌😉






STORY AND WRITTEN BY ✍🏻 🥰MUJAHEEDAH🥰 (MATAR 💖 MLM) HEEDAH HAYDAR OSTHMAN




*9/1/2022 forst january Sunday*




Cikin Azama brr. Muda yariƙesa dataimakonsa yakai zaune


Gumi ketsatstsafomasa yana furta innalillahi wa'inna ilaihin raju'un mahaifina? wannan wane irin bala'ine Mahaina da aikata ɓarna irin wannan nashiga uku ni Khaleel inama banzo duniyaba inama banzo ta tsatson Alhaji lawal ba"?
Abban Ameera daure kacemun mafalki nake" jijjiga hannun brr. muda yake yana zubda hawaye A idansa


Cikin tausayi muda kebashi haƙuri shida mama



Mama tace"kayi haƙuri hakan Allah yaƙaddara kuma mu munyafe"



Daidai lokacin saleeha tafito dama tajima Agun tsaye tanan kallonsu kuma tanajin Abunda suke faɗa tausayi khaleel yabata dama tajima da fahimtar shida mahaifinsa Akwai banbancin hali


Dawaye kan fuskarta tace"Abunda mama tafaɗa tayi gaskiya munjima da rufe labarin kawai tsanace daga mutane muke fuskanta Amma mu munyafe Zamubar wannan garinma dama bamada kowa Anan babana yarasu wannan gidanma na hayena gwanda mubat garin konasamu ƴanci"






Miƙewa tsaye yatsaye Khaleel yayi yazuba mata ido cikeda tausayi yatace"Ba inda zaku zakucigaba da zama Anan kuma ƴancinki zaidawo indai harnni BARRISTER KHALEEL ne tabbas zansaka wuyan riga ɗaya da babana tabbas zantsayamiki harkisami ƴancinki daga yau kufara shirin zuwa kotu daga yanzu!"
Yanagama faɗin hakan yafice ransa Amatiƙar ɓace.............







_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_







*WhatsApp or call number 07031012948*
.






➰ BARRISTER KHALEEL➰


*FREEBOOK*

🅿️29&30



DEDUCATED TO MY FANSS ONLY👌😉






STORY AND WRITTEN BY ✍🏻 🥰MUJAHEEDAH🥰 (MATAR 💖 MLM) HEEDAH HAYDAR OSTHMAN





```NIFA NAGANI DAGANIN COMMENTS NA STICKER KO WANI THANKX YADDA NATSAYA NAYI TYPING HAKA NAKESO ATSAYA ABANI NICE COMMENTS DA SHARHI AKAN LITTAFINA INHAR HAKAN BAZATA SAMUBA SAINABAR TYPING WLLH😡```







Mama tace"munshiga uku indai ba muzama silar farraƙa Uba da ɗaba"





brr. muda yace"wllh da kwai matsala nasan waye khaleel dik Abinda yaƙudurta wllh saiyayishi inatsoron Abinda zashi yadawa" bayansa yabi amma ina tini khaleel yabar gun




Direct gidansa yanufa yafaɗa toilet ko kayan jikinsa baicireba yasakarwa kansa shower ruwa sosai kedukan kansa zuwa jikinsa amma sam baijin sanyinsu wani irin Azababben zafi raɗaɗi yakeji Aransa haɗida zuciyarsa



Yajima Aha kafin yasami sa'ida cire kayan yayi yafito yazura jallabiyarsa yatayarda sallah
Yajima kan priyer mat wayarsa yajanyo yayi dailing number D.S.P SURAJ MAGAMI Batareda yagayamasa ainahin waye mai laifinba amma yasashi yarubuta statement yabada kawomasa
Bairuntsaba saida yagama komai yasami sahannun justice Emeker yasaka hannu Akan A aikawa Alhaji lawal maidala sammaci


Koda dare yayi yakwanta sam kasa bacci yayi baƙincciki damuwa dik sun Addabe ransa saifaman juyi yake dakyar bacci ɓarawo yasaceshi




Aɓangaren muda kuwa yayita kiran khaleel amma wayar taƙi shiga haka yakwanta badaɗi daniyar gobe suhaɗu




Su mama kuwa damuwa taƙara ninkuwa Aransu da tsoron Abinda zaije yadawo






Alhaji lawal kuwa harya manta babin saleeha da Abinda ya aikata yakoma sheƙe Ayarsa

Umma kam dik tarame damuwa tama ranta yawa kullum cikin zulmin Abinda zaifaru idan khaleel yadawo yasame wannan labarin




(HUNMMM UMMA BARI TSORATA DAN YANZU GAYYA TAGAMA AIKI DAN KHALEEL YASAN KOMAI)




COMMENTS AND SHARE PLZZZ




_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_






WhatsApp or call number 07031012948






➰ BARRISTER KHALEEL➰


*FREEBOOK*

🅿️31&32



DEDUCATED TO MY FANSS ONLY👌😉






STORY AND WRITTEN BY ✍🏻 🥰MUJAHEEDAH🥰 (MATAR 💖 MLM) HEEDAH HAYDAR OSTHMAN




*10/1/2022 Monday*






Tinda safe yasami yaro yabashi wata envelope yabashi yace"kayi nocking wancan gidan dik wanda yabuɗe kabashi kawai idan yace wayace kakawo kace wani yace Aba Alhaji lawal maidala" 500 yaba yaron Aiko da murna yanufi gidan yaron


Shiko yawuce Abinsa





Direct yanufi Hosbitals ɗin Tasamu sauƙi yatarar har Ansallameta dakansa yakawosu gida


Yace"mama kushirya gobe A round 10:00 zamushiga kotu kuyi Addu'a Akan musami nasara"



Saleeha tadubeshi tace"Amma yaya sainake ganin........."




Ɗaga hannunsa yayi Alamar dakatarwa yace" fatan narasa kawai nake buƙata dagoyon bayanku bana ƙarya nayi rantsuwa Akan Aikina zanyishi bisaga gsky haɗida Amana so ko nine nakeda laifi sainaga Anyankemun hukunci inama baki haƙuri da wannan matsalar tafaru A ɓangarena"



Kayanda yazomusu dasu na Abinci yakawo sannnan yatafi Abinsa Albarka kam yashata





Yaron yayi nocking sani maigadi yauɗe yabashi yace"gashi inji wani mutum yace Abaiwa Alhaji lawal maidala wannan saƙon"
Baijira Ansawar sani ba yafice dagudu..





Damamakin waye to sani yakoma ciki direct palourn yashiga da sallama Umma nagefe zaune tarafka uban tagumi


gogan yaɗaura kafa ɗaya kan ɗaya yana karanta news paper Abinsa



Yace"ƴallaɓai gasaƙo Akace Abaka"




ƙarɓa yayi yana dubawa yace"inji waye"



Sani yace"bansaniba kawai yaro yakawo yace Abaka"



yace"owk tafi kawai "




Buɗa envelope ɗin yayi yaciro takardar yafara warwareta Abinda yagani dakuma wanda yakai ƙararsa Har kotu tayanka masa wannan sammacin yasashi miƙewa tsaye Amatiƙar razane!!!!!!






*KO ME YAGANI? MUHAƊU NEXTH PAGE DANJIN YAZATA KAYA KADA KUMANTA DA COMMENTS IDAN BA COMMENTS BA TYPING BARRISTER KHALEEL INSHA ALLAH*





*INAYINKI FATEEMA °FANAN A-A MARUBUCIYAR DOCTER EYSHA👩‍⚕️ INAYINKI ZUWA BOOK ƊIN SOSAI🥰*






_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_







WhatsApp or call number 07031012948






➰ BARRISTER KHALEEL➰


*FREEBOOK*

🅿️33 &34





DEDUCATED TO MY FANSS ONLY👌😉






STORY AND WRITTEN BY ✍🏻 🥰MUJAHEEDAH🥰 (MATAR 💖 MLM) HEEDAH HAYDAR OSTHMAN




*11/1/2022 Second's january tuesday*





Daƙarfi yafurta what's? sammaci daga kotu ni espicially my son? khaleel kai ina na lie nace ƙaryane ƙaryane wllh"?



Jefarda takardar yayi yana safa da marwa yafara Aɗakin yana sabbatu yana neman layin khaleel Amma swecth off


Umma ta taso tana faɗin lafiya Alhaji wayayi ƙararka


Ganin dik baicikin hayyacinsa yasa taɗauke takardar taduba ita kanta mutuwar tsaye tayi



Afi tafurta dama khaleel yadawo 9jar? ya akayi yasami labarin? waya haɗasu da ita? meyasa khaleel yazaɓe tozartamu A idan duniya"?




*(NIKO 🥰MUJAHEEDAH🥰 NACE DOMIN SAMUN ANSAR TANBAYARKI KINEMI KHALEEL BADAI NIBA KO KINEMI READERS NA NOVELS OF 🥰MUJAHEEDAH🥰 DAN SAMUN CIKAKKIYAR ANSA NIKAM NAYI NAN NAGA HALINDA KHALEEL YAKE CIKI*)






Dakansa yabiya yaɗibesu suka wuce Hegher court dake Anan f.c.t




Bayarda mama da muda basuyi dashi Akan yajanye wannan maganar Amma yaƙi



Anzauna zaman kotu shuru ba Alhaji lawal danhaka Aka tura Azo dashi



Nocking gate ɗin yayi pole man yayi



Sale yabuɗe yace"yadai lafiya kazo kana......"


Maganarsa tamaƙale ganin police da gandrover



Police ɗin yace"Alhaji lawal yana nan"?



Cikin inda.. inda.. yace" eh...eh ...eh yanaciki"




Tokaje kace munzo muje dashi haɗida matarsakai harda kai donsamun shaida A kotu mukawai Akejira"




Cikin rawan murya sale yace"nikuma Ogerh meye nawa Aciki nifa maigadine kawai"




Gandrover yace"Sanin kana maigadi yasa nace kazo muje"




Hayaniyarsu tafito da Alhaji lawal shida Umma jin maganarda suke yasa yajinjina kai yace"basai kuntaramun mutaneba kuje zamuzo yanzu"




Police ɗin yace"Umarnine daga Alƙali kada mukoma saida ku"




Jinjina kai yayi yasa Akafito da motar suka nufe Higher court



Ran Alhaji Amatiƙar ɓace yake zuciyarsa kamar zata fasa girjinsa tafito Abin kamar Almara wai ɗansa ɗancikisa ɗaya tilo shine zainemi walaƙantasa A idan duniya shifa haryanzu yakasa gasgata lamarin Harsuka iso bakin kotun Akayi parking suka fito Alhaji baidana wasi wasi da ganin Abin kamar film ba



Sanya ƙafarsa kotun yayi yana shiga yaci Arba da khaleel A zaune yakame gun lauyers masu gabatarda ƙara




Hakama Umma dikansu Kallon tuhuma suke watsamai



Shiko kallo ɗaya yamusu yaɗauke kai Amma Aransa yanajin kamar idan yayi hakan bai kyaitaba kuma duniya zata zagesa kamar yadda Abban Ameera yake faɗamasa to shi yanzu meye mafita kodai janye maganar zaiyi..............







_...COMMENTS AND SHARE IDAN KINKARANTA DAURE KIMUN SHARE ƊINSA DAN ALLAH🙏🙏🙏🙏 ,,,,, INAƘARA GAYAMUKU COMMENTS KAWAI NAKESO BANDA STICKER TYPING NABAKU BAWAI STICKER BA DAN HAKAN NIMA TYPING ZAKU BANI INBAZAKU IYABA NADAINA,,,, KUMA INSHA ALLAH BAZAN CIGABA DA TYPING BA SAINAGA COMMENTS ƊIN MUTUM 20 MAIKYAU HAƊEDA SHARHIN LITTAFIN BARRISTER KHALEEL INKO BABU TO BA TYPING INSHA ALLAH..._










._BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_.







WhatsApp or call number 07031012948








➰BARRISTER KHALEEL➰



*Free book*



🅿️35&36





DEDUCATED TO MY FANSS👌 ONLY 😉😉






_STORY AND WRITTEN BY 🥰MUJAHEEDAH🥰 (MATAR 💘MLM) HEEDAH HAYDAR OSTHMAN_







```INAƘARA GABATARMUKU DA LITTAFINA MAISUNA DOCTOR HEESHAM LITTA NE DAYAƘUNSHE ABUBUWA DA DAMA SOYAYYAH GIRMAN KAI IZZA DADAI SAURANSU DOMUN SAMUN WANNAN ƘASAITACCEN BUK ƊINA SHINDA MAIZAMAN KANTA KAWAI KU HANZARTA BIYAN 200 KUNIMENI TA WANNAN NUMBER WhatsApp 07064904617 INKO KIRANE TA WANNA 07064904617```









taɓosa Brr. Muda yayi yace"saikatashi ka kunyata mahainfika tinda hakan kakeso kazaɓi waccan yarinyar sama da Ahlinka Anya kuwa kama kanka Adalci kuwa khaleel"?





Hurzarda iskan bakinsa yayi yamiƙe yace"yamai lord Sunanan *BARRISTER KHALEEL AUWAL MAIDALA* Inaƙara Akan cinzarafi dana fyaɗe da Alhaji lawal yama yarinya ƙara kuma ƴar aikinsa Idan kotu taban dama inason Agabatarmun da mailaifin Agaban kotu"






Alƙali yace"idan wanda Aketuhuma yana kusa kotu nasan ganinshi"





Baɓata lokaci Alhaji lawal yashiga inda masu laifin suketsayawa yatsaya






Ahankali brr. khaleel yaƙaraso

Please Login or Register in order to submit comment