Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shawarar tunkarar momma da maganar don Susa lokacin auren anan kusa,

__________________________

"Subuhanallahi ita samra CE tace hakan ? To amma mi yake faruwa naga kamar tana farinciki a lokacin sai kuma yanzu daga baya tabamu matsala ,?"
Daga can aka amsa da cewa " wallahi kuwa hajiya maryam gatanan duk ta rame kullum cikin kuka tun ina daukar abun a wasa har tafara bani tsoro batada aiki sai kuka da damuwa shine nace ko zamusa lokacin auren nan kusa kila in taga an daura auren ta hakura ?"
"Aa hajiya bazamuyi hakan ba ai yanzu andaina yayi auren doli kidai kara lallabata har kisamu ta yarda zaifi yaran yanzu in basason Abu to ba'a tirsasamasu don in aka sasu doli to abun bazaiyi kyau ba,"
"To shikenan zank'ara lalla'bata insha Allah," nan sukaci gaba da tattaunawa kamun sukayi sallama suka ajiye wayar,

Hisham da yake zaune a gefe yana cin abinci tuni ya zubama Momma manyan idanunshi don tuni ya fahimci inda zaican ya dosa , kallonta yake cike da damuwa a fuskarshi kamar gaske acikin zuciyarshi kuwa ji yake kamar ya taka rawa sai dariyar mugunta yakeyi , cikin marairaicewa kamar gaske yace " Momma mi naji kuna fad'a ne ? Badai my samra CE tace batasona ba to amma ni miye abun k'i ajikina Momma , dama irin wannan nake gudu shiyasa banason wannan tallan nawa da kikeyi yanzu gashinan kin jamun zasu wulakantani bayan kuma na kamu da son yarinyar yanzu ya zanyi kenan , yafada kamar zakiyi kuka,

Dafashi momma tayi tace "karka damu shalele insha Allah komai zaizo da sauki tunda iyayenta naso nasan zasu shawo kanta, (ba doli su so ba tunda zasu yimun shak'e inba shiba wane namijin ne zai kwashi wannan yarinyar da gabad'aya babu kayan wasa a jikinta) ya fad'a a ransa , Sam baisan cewa a fili yafad'a ba saida yaji momna tace " mi kake cewa ,?" Dan daburcewa yayi yace aa Momma cewa nayi akwai abarta tunda tace banyi mata ba kar a tsaurara bincike Ku kyaleta kawai don ni nayi alk'awarin bazan ta'ba auren yarinyar da ta furta cewa bata so na ba , kuma nasan girman alk'awari don haka bazan karya shi ba taje can Allah ya had'a kowa da rabonsa amma tabbas bazan aureta ba tunda har ta furta da bakinta bata sona ,yayi maganar yana had'e fuska sosai ,Momma zatayi magana ya tareta da cewa " don Allah Momma kibar maganar nan Sanin kanki ne bazan taba karya alk'awari ba duk alkawarin da nayi to sai na cikashi kawai kiyi hakuri , "
Cikin sanyi Momma tace to shikenan Shalele dama kai nakeji gashi ka fad'awa soyayyarta karkazo abun yana damunka , Mahaifiyarta kuwa banida matsala dasu tunda ta 'bangarensu ne aka samu matsala," wani shu'umin murmushi yayi tareda cewa " karki damu Momma acin watan nan zan kawo maki yarinyar da zan aura. Nayi maki alk'awari, nan da nan Momma ta washe baki tana cewa to alhamdulillah shalele nasan zaka kawo tunda kace kayimun alkawari Allah yabaka ta gari " yace "amin"


__________________________
Agurguje take shiryawa ta fito tsaf cikin uniform dinta a tsaitsaye ta dauki kunun da inna Inno ta jiye mata tafara sha , batasha da yawa ba ta ajiye ta juyo tana kallon iyayenta tace "Baba Inna ni zan tafi makaranta sai na dawo , "
Atare sukace "to Mariya adawo lafiya Allah ya tsare, cikin jin dadi ta furta "amin amin , " kallonta ta mayar ga Yayanta Sulaiman tace " Yaya na shirya muje ko ," karkacewa yayi ya sanya hannunshi a aljihu ya dauko kudi Dari ukku yabata yace " yau ilyasu baya nan wani uzuri yasa yafita da mashin din nasa bare na amso na kaiki gadai wannan ki hau nafef kuma ki saye wani Abu kici in antashi insha Allah zanzo na daukoki nasan kamun sannan ya dawo, "
"To shikenan yaya nagode sai na dawo" tajuya tanufi hanyar fita daga gidan, "anty ki sayomun awara in zaki dawo kinji ," cewar Asmau yar autar Inna inno , cikin murmushi da kaunar 'yan uwan nata tace " to Asmaun inna zan kawo maki insha Allah , daga haka ta fice daga gidan tana sauri don yau ta makara sosai ,
Asmau da khadija ma bayan sungama karyawa makarantar suka wuce inda sukabar Yaya sulaiman sai Baba , Inno tana kicin tana shara yayinda Baba yake gefe shida yaya sulaiman suna tattaunawa , cikin jimamai Baba yace , " to yanzu kai sulaiman ya kakeganin zamuyi nidai banida kudin nan wallahi kasani kaikuma abubuwa sunyi maka yawa naso Mariya ta canza karatun nan amma ta kafe ita sai karatun aikin jinya takeso to ni Ina naga kudin da zanyi mata laluran makarantar dashi , "
Nisawa yaya sulaiman yayi yace " karka damu Baba insha Allah komai bazai gagaraba , kaga Mariya tanata kokari sosai banason kokarinta yatashi a banza sannan wannan karatun ne kawai zatayi kaga tasamu aiki kai tsaye yanzu ni ba gashi nan ba shekara ta ukku da hada degree na amma aiki ya gagareni sai dinki doli nakeyi , to ita in Allah ya taimakemu tana gamawa zakaga tasamu aikin nan kuma albashinau yanada tsoka kaga shikenan abubuwa zasuyi mana sauki sosai ,akwai wasu kudi da nake Tarawa acikin asusuna zan fasashi nayi mata laluran makarantar nasan insha Allah zasu isa Allah dai ya shige mana gaba, daga Inna har Baba murna suka farayi don sunason cikar burin 'yar tasu sosai wadda ta taso da wannan ra'ayin ne tun tana k'arama , nan sukaci gaba da Sanya mashi albarka da yi mashi addu'o'in samun nasara a rayuwa yadda yake dawainiya da kannenshi batare da gajiyawa ba yanasa iyayen farinciki da alfahari dashi,

____________________________

Zaune suke a office din Hisham , Baban Safiya ne da k'aninshi sai Babban yaronshi Zakari , nan suka koro mashi bayanin abunda yake tafe dasu da kuma yadda akayi suka zo wajanshi don an tabbatar masu da zasu samu adalci a wajanshi shiyasa direct sukazo wajanshi,

Tunda suka fara magana ido kawai ya zuba masu cikin tafasar zuciya ,ba k'aramun bak'inciki yaji ba da suka gaya mashi bayanin da likitan yayi masu na cewa ba mutum d'aya ne yayi mata fyad'e ba ,tunanin yakeyi irin azabar da zai ganama wad'an nan azaluman idan yakamasu , ga tausayin mahaifin yarinyar ganin yadda yake zubar da hawaye da tsufanshi da komai cikin k'wafa da takaicin abun yace , Inason Ku kawomun yarinyar da abun yafaru agabanta yanzu sannan samarin da sukace sunga lokacin da aka dawo da ita suma inason ganinsu , nan da 40mnt , nuna zakari yayi yace "kai zan hadaka da yaranmu biyu kaje ka kaisu inda abun yafaru daga nan kuzomun da samarin da yarinyar , kaikuma Baba inason ka kaini asibitin yanzu inason ganin yarinyar da kuma likitan da ya dubata , " cikin farinciki duk suka mik'e ganin yadda ya kar'bi k'orafinsu hannu bibbiyu ba zancan wulakanci ko yawo da hankali , wani sanyi sukaji acikin zukatansu don suna ganin kamar ma an kama masu laifin angama,

Lokacin da Hisham yaga Halin da safiya take ciki saida yaji kamar ya zubarmata da hawaye har lokacin bata cikin hayyacinta don data farka da bige bige da ihu da sambatu take farkawa wannan yasa suke banka mata alluran bacci , yaso yasameta acikin hankalinta don doli akwai tambayoyin da yakeson ta amsa mashi , haka dai ya hak'ura doli ya nufi office din likitan,
Likitan na ganinshi ya mik'e tsaye tare da bashi hannu suka gaisa cikin mutuntawa , nan yayi wa likitan bayanin abunda yake tafe dashi,
Murmushi likitan yayi yace " nasani yalla'bai hasalima ni nabasu shawarar su damk'a case din a hannunka ko zasu samu adalci Don wallahi an cutar da yarinyar nan cuta mai yawa Wanda sai tsananin rabo ne in zata rayu sunyi mata raga-raga da mutuncinta cikin rashin imani , wallahi na tausayawa iyayenta sosai , zan baka sakamakon binciken da akayi mata ka gani , nan ya dauko wani file ya mik'awa Hisham yana kara yi mashi bayanin abunda Ke ciki,
Hisham gyad'a kai kawai yakeyi idanun nan nashi sun kad'a sunyi jawur fuskarshi ma tayi ja sosai kallo daya zakayi mashi kasan cewa yana cikin tsananin fushi da tafasar zuciya, Yajima a office din kamun yayi ma likitan sallama yabar office din , nan yabar su Baban akan zai nemesu in bukatar hakan ta taso,

______________________________

Daga asibitin ofishinsu ya koma ,koda yaje har Zakari yazo da yarinyar nan maisuna haulatu k'awar safiya dakuma su iro mai shago, da hannu kawai yayi masu alamar da su biyoshi , da sauri suka mik'e tsaye sukabi bayanshi , yana shiga ya d'ane kujerarshi yana jiran shigowarsu ,

Jiki a sanyaye suka fara shigowa bakinsu dauke da sallama Don sun tsorata da yanayin shi sosai kallo d'aya sukayi mashi suka tabbatar da ba wasa acikin al'amarinshi, a hankali ya amsa sallamar tasu batare da ko su sunjishi ba , tsaye sukayi suna jiran suji abunda zaice , jikinsu sai k'yarman tsoro yakeyi musamman ma Haulatu , gyara zamanshi yayi tare da sassauta fushinshi Don ya kula sun tsorata dashi yace " Ku zauna tambayarku zanyi kuma Ku tabbatar kun sanar dani abunda kuka sani, Da sauri suka gyada Kansu alamar amsawa , ta kan Haulatu yafara , kallonta yayi yace "ki gayamun abunda yafaru daki-daki a wancan ranar , sannan ki gayamun abunda zaki iya shaidawa agame da mutanen , "
Cikin hawaye tafara bashi labarin abunda yafaru tun daga farko tashinsu daga makaranta har kawo sanda suka dauke safiya, jinjina kanshi yayi yace " to zaki gane samarin su nawa ne ?? Sannan zaki iya gane mutanen in kika gansu ? "
Cikin rawar murya tace " aa bansan kosu nawa bane amma zan iya gane d'aya daga cikinsu Wanda shine ya fito ya janyota motar , jinjina kanshi yayi yace " to bayan wannan ba abunda zaki iya tunawa , ? Cikin tabbatarwa tace " *narik'e number motarsu yalla'bai* "
Cikin jin dadi yace wow good yan mata kinyi kokari maza rubutamun number anan , kindai tabbatar da itace ko ?"
"Eh yalkabai ", to da kyau maza rubutamun , saida ta rubuta ya dauka ya duba sannan Yakoma kan samarin suma dai tambayoyin yayi masu kamun ya sallamesu su tafi , zakari sai dadi yakeji gani yake kamar ma ankama mai laifinnan sai jinjinama Haulatu yakeyi da har tayi kokarin rik'e number motar,

Wunin yau gaba daya Hisham akan wannan case din yayi shi sai misalin goma na dare sannan Yakoma gida bayan yagama duk wani bincikenshi kuma yagano ko suwaye masu laifin jira kawai yake gari ya waye ya kaddamar masu don sai ya gurfanar dasu agaban koto saidai duk abunda zai faru yafaru,
Wanka yafarayi bayan yaje gida sannan ya ci abinci kamun yayi shirin kwanciya , kamar daga sama tunaninta ta ya fad'o mashi sai kyakkyawar fuskarta keyi mashi gizo ,wani sanyayyan murmushi ya saki Wanda baimasan lokacin da yayi ba a hankali ya furta Preety kinada kyau,
Tunawa da yayi cewa yanada number ta yasa ya dauko wayarshi yafara kiran layinta ba tare da yasan abunda zai CE mata ba, a hankali wayar tashiga kuma duk bugun da zatayi dai dai yake tafiya da bugun zuciyarsa, a dai dai wannan lokacin kuwa Laurat na zaune adakinta abun duniya ya dameta ko yau saida Abbansu ya titsiyeta akan ta fito da mijin aure inba haka ba lokacin da ya diba mata ya cika to zai bayar da ita ga Wanda yaga dama ba ruwanshi, tayi zurfi cikin tunani kamar daga sama taji ringing din wayarta , a hankali ta dauko wayar ganin bak'uwar number yasa ta share wayar har ta katse sai da aka sake kira sannan ta dauka , cikin sanyin muryarta ta furta " *Assalamu Alaikum*" wani luuuuu yayi da idanunshi jin muryarta har tsakkiyar kanshi....................nagaji tunda ko comment bana samu😼😼😼😼😼



*wlh nakusa mayar da book dina na kudi akan rashin comment dinku musamman yan GRP din *Jami'i fans 2 da maman Yusuf fans da sauran grps saidai duk Wanda yakemun comment to zancigaba da bashi a kyauta Don dama banyishi da niyar siyarwa ba amma da biyu babu gara daya*

____________________________

Mmn Yusuf Dr mata sokoto



πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *ASLM GANI FA NA SAKE DANNOWA DA SABBIN KAYA MASU SABON SALO*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»

*takuce mmn Yusuf Dr mata mai gyaran mata ciki da wake*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»

Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kijiβœ‹πŸ»βœ‹πŸ»βœ‹πŸ»

Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka,πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»
*Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi*

Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje

Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir

Maganin nono Dana hips
Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar,
Maganin gashi
Maganin hawan jini
Maganin sugar

Sabulun wanka na gyaran jiki
Sabulun dilka na amare
Dilkar amare

Kwallin mallaka (daga ni sai kai)
Maltinar mata
Bobintan mata
Set na lalata gindin kiahiya
Set na ukku bala'i
Set na rantse bakida kishiya,

Kalolin gumba
Kalolin gari
Kalolin matsi
Kalolin sabulan tsarki
Zumar mata
Zumar ridi
Zumar goron tula
Tsumin mallaka
Tsumin jaraba
Tsumin sabon budurci
Tsumin kankana
Tsumin tabaje
Tsumin makalemata
Shayin mata
Sirrikan mallaka
Dan goshi da mahadinshi
Dan goshi na Mara
Kyallen al'ajabu
Rakumi da akala
Bita zai zai
Dahuwar kalolin kaza zabo zakara
Dahuwar zuciya
Dahuwar ciccibi
Dahuwar zuciya
Dambun nama
Dahuwar yan shila
Yajin mata
Yajin maza domin Karin karfi


*Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜ wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani ,
Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mataπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°

Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah ,
Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi maganaπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° 07069711327
[6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§

*MALLAKAR*
*Maryam umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*πŸ‘‡πŸΌ
*Mutum ce kuwa*
*Minene asalina*
*Husna ko Huzna*
*and now*πŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌ
*Jami'in Dan sanda*


*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍


πŸ…ΏοΈ--27

........................cikin tsuke fuska ya k'arasa shiga d'akin , don ya lura wannan matar yar rainin hankalice yanzu sai ta nemi kawo mashi wargi in taga fuska , itama cikin had'e fuska ta dauke kanta daga kanshi tana mamakin yadda kayan yan sanda sukayi mashi wani irin kyau kamar sabodashi akayi su , bata ta'ba ganin Wanda kakin yan sanda sukama kyau irinshi ba ,a hankaki ya k'arasa kusa da tsohuwar nan da sauri wani saurayi dake zaune kusa da ita ya mik'e tsaye cikin girmamawa yace " barka da wuni yalla'bai , ga wajan zama" yayi maganar yana k'araso mashi kujerar da ya tashi akanta ,
Kai kawai ya d'aga ma saurayin kamun ya k'ara janyo kujerar ya zauna a hankali ya kalli tsohuwar da kulawa yace " Sannu iya ya jikin , " ? Cikin muryar jin jiki tace "naji sauk'i d'an nan kuma nagode da taimakonka gareni Allah yayi maka albarka Allah ya shige maka gaba a dukkan al'amarinka Allah ya tsareka da sharrin duk wani abun sharri allah yasa kagama lafiya ngd sosai , "
Cikin jin dadin addu'arta yace Amin iya ba komai ai yiwa Kaine Allah ya k'ara sauki , dukkansu da amin suka amsa ,

Laurat tunda ya matso kusa da ita tarink'ajin wani iri ga gabanta dake fad'uwa kusancin da suka samu yasa tana shak'ar daddadan k'amshin turarenshi gaba daya sai taji ta daburce rubutun da takeyi ma takasa k'arasawa wannan yasa ta juya da sauri tabar d'akin , yayinda Hisham ya bi bayanta da wani irin kallo ta k'asan ido Wanda ba Wanda zai fahimceshi , 'boyayyar ajiyar zuciya ya sauke a zuciyarshi yake cewa , wai wannan wacece ne ??
Laurat ma tana fita ajiyar zuciya tayi sannan a hankali ta nufi office dinta tana tunane tunane,

Kallon saurayin yayi yace "am bawata matsala dai ko ? Ko akwai abunda kukeda buk'ata ne?"
"Aa ranka ya dade alhamdulillah babu matsalar komai sai dai tunjiya take rigima akan itadai a sallameta ta tafi gida ko yanzu kamun ka shigo rigimar da takeyi kenan , "
Jinjina kai yayi yace OK zanyi magana da likitan inba damuwa sai subata sallaman tunda jikin da sauki sosai ,"mik'ewa yayi tare da zaro kudi masu yawa yabawa yaro tareda cewa Allah ya k'ara lafiya , nan yaron da tsohuwar suka hau godiya da yi mashi kyawawan addu'o'i yayin da shikuma yafita yana mai jin dadin , don a duniya ba abunda yakeso kamar yaji ance *Allah yayi mashi albarka*

Direct office din likitan ya tambaya aka nuna mashi , ba tare da tunanin komai ba ya murd'a hannun gambun ya shiga bakinshi dauke da sallama ,
Fitowarta daga bayi kenan daga ita sai doguwar rigar jikinta sai wata lallausar hula bak'a dake kanta ,kasancewar rigar tata black and red ce sai tak'ara haska farar fatarta tayi mata cif ajiki ksancewarta mace mai murzajjen jiki gashi Allah ya hore mata k'ira mai daukar hankali tanada cikar kirji da baya sosai Wanda in tana tafiya komai na jikinta Ke kad'awa Baren ma wannan rigar data kamata sosai , ganin ba ko wane yasa ta cire hijabinta da rigarta ta likitoci ta shiga bayin Wanda fitowarta yayi daidai da shigowarshi office din,

Da sauri taja baya kamun cikin sauri ta janyo hijab din ta ta Sanya ,

Kallo d'aya yayi mata ya kauda kanshi tareda jin wani irin yanayi Wanda bai ta'ba fuskantar irinshi ba , a zahiri kuwa ta'be bakinshi yayi ya lumshe idonshi ya bude a hankali tare da d'aga k'afarshi zuwa inda take tsaye , zaro manyan idonta tayi ciki hade fuska da fushi tace " kai waye , akanmi zaka shigomin office bada izinina ba , oya maza ka ficemun anan tayi maganar a tsiwace tana nuna mashi hanya da hannunta,
Murmushi yayi cikin ranshi afili kuwa wani banzan kallo ya wurga mata sannan yaci gaba da tafiya saida yazo daidai inda take tsaye kamar zaiyi magana saikuma yafasa ya juya ya janyo kujerar da marar lafiya Ke zama ya zauna yana fuskantar babban teburin da Ke office din ,
Hararar bayanshi laurat tayi kamun tayi k'wafa ta zagayo ta gabanshi ta zauna akan kujerarta suna fuskantar juna, sun jima a haka kowannensu yakasa yiwa danuwanshi magana , ganin sun kwashi mintina bashida niyar magana ne yasa ta d'ago a hasale tace "wai malam lafiya kuwa ko bashinka naci da zakazo har office dina kayimun zaune batare da izini ba kuma kaja kayi shiru kana k'arewa mutane kallo tayi maganar tana yamutsa fuska , don harga Allah tagaji da kallon da yake mata tanajin yadda idanunshi Ke yawo ajikinta , ba tare daya dauke idanunshi daga kanta ba yace " awace unguwa kike ?kallonshi tayi da mamaki jin yadda yayi mata tambayar a kausashe kuma ya fuske kamar bashi yayi maganar ba , ganin kamar yazo da rainin hankaline yasa ta janyo laptop dinta tafara wasu yan Danne danne aciki,
Ganin hakan yasa shikuma ya kai hannu ya dauki wayarta dake ajiye a wajan , cikin sa'a kuwa ba Lock numbarshi ya sanya ya kira sannan ya ajiye mata wayarta ya tashi cikin tafiyarshi ta cikakken namiji yabar office din nata , batare dayayi abunda ya kawo shi ba, da wani irin kallon mamaki ta bishi kamun tayi k'wafa tana hararan inda yabi ya wuce,

Hisham kam k'iris ya rage ya saki layi don ganinta a wannan shigar ba karamun hautsina mashi man kai yayi ba , karfin hali kawai yayi bainuna ba don gudun raini mamakinshi shine ai bayau yafara ganin mata kala kala da shigar da take nuna tsiraici ba amma bai tabajin irin wannan ba sai a kanta to mi hakan Ke nufi kenan , kuma da yaje ya dauki number ta mi zaiyi da ita ne mrtsss yayi tsaki yana maijin haushin kanshi , karfa yarinyar ta dauka wani abune ta nemi rainashi a banza a haka ya karaso inda yabar su sajan sale , nan yabashi umurnin yaje ya nemawa tsohuwar sallama in ba wata matsala , "okay sir " yace ya juya ya tafi shikuma yashiga mota yana jiranshi,


____________________________

Kallo daya zakayi masu kasan suna cikin matuk'ar tashin hankali , kowa ka kalla zaka hango tsantsar tashin hankali da wani irin fushi akan fuskokinsu , a hankali dattijon yafara basu hakuri yana cewa " kuyi hakuri wannan itace kaddararmu wadda bazamu iya kauce mata ba , hakika an cucemu anyi mana tabon da har mu mutu bazamu iya mantawa dashi ba , ina rokonku da kuyi hakuri don inku kuna wannan koke koken to ita kuma *Safiya* fa ya kukeso tayi doli sai mun kawar da tamu damuwar don ganin tasamu kwanciyar hankali ,yanzu likita yana nemanmu bari muje muji mi ake ciki, "
Har yagama maganarshi ba Wanda yace k'ala saidai masu kukan sun yi shiru sai ajiyar zuciya sukeyi , hannun k'aninshi Dattijon Yakama suka nufi office din likitan,

Da sallama suka shiga bayan sun gaisane yabasu izinin zama , zama sukayi suna fuskantarshi saida yagama wasu rubuce rubuce sannan ya cire farin glass dinshi ya dubesu cike da tausayawa yace , "to alhamdulillah Baba mun samu mun shawo kan matsalar don gaskiya da farko har naji tsoro don k'iris yarage yarinyar ta kamu da ciyon *yoyon fitsari* to Allah ya tak'aita mun shawo kan matsalar , sai dai duk farkawan da zatayi a firgice take farkawa tana sambatu shiyasa mukeyi mata alluran bacci , a gaskiya an lalata rayuwar yarinyar nan anzalunceta sosai don bincikenmu ya nuna ba mutum daya bane yayi mata fyade akalla zasukai mutum ukku ko hudu ,
Da sauri Dattijon ya runtse idanunshi yanajin zuciyarshi kamar zata buga saboda wani irin nauyi da zafi da takeyi mashi , wasu hawaye masu zafi suga gangaro mashi , shima dayan dattinjon hannu yasa ya goge kwallar data cika mashi ido ,Wanda halin da suke ciki yasa sunma kasayin magana sai ajiyar zuciya,

Cikin tausayawa likitan yaci gaba da cewa abunda yasa nayi kiranku shine saboda inbaku wata shawara na tabbatar duk wad'an da sukayi wannan aikin to ba kananan mutane bane doli akwai abunda suka taka ,duba da bayanin da muka samu na irin motar da suka dauketa aciki ,don haka nake ganin mi zai hana Ku damk'a wannan case din a hannun mataimakin commissioner *Hisham Abudrahman* inaga shikadai ne zai iya tsaya maku akan wannan case din har a kwatowa yarinyar nan hakkinta inba hakaba wahala kawai zakusha arink'ayi maku yawo da hankali , ina da tabbacin insha Allah zaku samu adalci a wajansa,

Cikin murya mai tsananin rauni da karaya dattijon Wanda ya kasance mahaifin yarinyar yace " kayya d'an nan bana tunanin zamu samu wani adalci anan tunda har yanzu bamusan ma waya aikata mata wannan aikin ba , cuta ce dai anriga a cucemu saidai Allah zai sakamana , "

"Aa Baba Ku daure Ku nemawa yarinyar nan hakkinta an cuceta sosai Wanda yakamata ace an hukunta koma waye ,saboda barin irinsu a doran k'asa bala'i ne bai kamata a zuba masu ido ba suna yadda sukaga dama ba , karka damu da rashin sanin su waye

Please Login or Register in order to submit comment