Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana k'araminshi har kawo yau indai yana gida to zaka sameshi tareda Momma yana tayata aiki , wani lokaci ma har shara da wanke wanke shi yakeyi kamar wani mace
,har wannan lokacin Abba yana zaune Yana duba jarida ,
Juyowa yayi da sauri jin yadda k'amshin abincin ya bugi hancinshi , dama shima yunwar ce ta tayar dashi daga bacci , murmushi yayi yace "sannu da aiki Son Bari na taso na cika cikina ,"

Dariya Hisham yayi yace " Abba bazaka jira Momma ba yau kai kadai zakaci abincin ne,"

"Babu ruwanka d'an sa ido " cewar Abban lokacin da yake zama kan kujerar , dariya kawai Hisham yayi baice komai ba yafara zuzzuba masu dankalin da wainar kwai tayi kyau har tagaji sai kamshi ke tashi, sannan ya haษ—a masu tea suka fara karyawa , sunaci suna dan ta'ba fira da wasa da dariya in ka gansu sai ka dauka abokai ne ,

"Sannunku wato kuna nan kuna karyawa kun manta dani ko" cewar Momma da tun dazu take tsaye tana kallonsu cike da so da kauna tana alfahari da mijinta dakuma d'anta kallonsu kawai yana sanyata cikin farinciki ,

Da sauri duk suka kalli inda take , taci kwalliya sosai tayi d'as abunta kai bazakace ta ajiye kamar Hisham ba , tashi Hisham yayi ya riko hannunta yana cewa "zo muje Momma ki karya Abba ne yace wai mu k'yaleki muci abunmu,"
hararshi tayi bata ce komai dagashi har Abban dariya sukayi mata , gaida Abban tayi sannan Hisham ya gaisheta daga nan ya hada mata nata abincin tafara ci , haka suka gama cin abincin suka koma kan kujerun falon suka zauna sunata fira cike da annashuwa , haka suke ko yaushe kowaye yazo gidan sai wannan family ya burgeshi saboda yadda suke matukar bawa junansu kulawa kullum zaka samesu cikin farinciki da wasa da dariya,

Kallon Hisham Abba yayi yace Son anfara siyar da form na *aikin dan sanda* har na siya maka ma na mantashi a office Amma gobe zanzo dashi sai ka cike ko? Yayi maganar Yana kafeshi da ido,

Tunda yafara maganar banda kallon Abban ba abunda yakeyi acikin zuciyarshi kuwa mamakin dalilin Abba na kafewa sai ya gajeshi da aikin *dan sanda* yakeyi ,miye acikin aikin inbanda wahala kullum sukenan basu nan basu nan wajan kama tantiran masu laifi duk don su samu k'asarsu ta gyaru kamar sauran k'asashe amma abun yana tashi a banza ,duk girman laifin da mutum zai aikata ga hujja da kwararan shaidu kiri kiri amma hakan bazai hana manyan mu shige da fice don ganin an saki wannan mai laifin ba saboda duk wani babban laifi da ake aikatawa mafi yawa zaka samu da hannun manyanmu aciki , haka kwanaki kiri kiri a unguwar su aka kama wani matashin saurayi da yara sama da biyar ya sacesu yana shirin hallakasu aka kamashi amma abun takaici ko sati baiyi ba aka rufe case din aka sakeshi, to in irin haka na faruwa tun farko miye amfanin kamashi kenan taya za'a samu wani cigaba ,in hakane miye amfanin aikin ma gaba daya ,shi wannan abun naci mashi rai sosai ba komai yasa yake k'in aikin *dan sanda* ba saidon wallahi in ya shigeshi abubuwan da zasu faru ba masu kyau bane don duk wanda ya kama da aikata babban laifi irin na kisa ko fyade bare kuma satar yara wlh zai iya kashe mutum komai za'ayi sai dai ayi , wannan dalilin ne yasa yak'i yarda ya karbi tayin Abba don bafa zai iya dagawa kowa k'afa ba , yayi zurfi acikin tunanin da yakeyi gaba daya idonshi sun kada sunyi jajir ga jijiyoyin kanshi duk sun tashi sunyi rida rida gaba daya fuskarshi ta sauya tayi jajir alamar ranshi ya ษ“aci matuk'a, gefe daya Kuma wani irin tausayin Abbanshi ne ya kamashi , ya tsaya kai da fata yana aiki bisa gaskiya da amana duk da burin samun cigaba ga k'asarsu amma kullum abun k'ara ta'bar'barewa yake ,

Hisham yanada hakuri da fara'a uwa uba wasa da dariya to ammafa yanada matukar fushi idan ranshi ya ษ“aci komai zai iya aikatawa , shiyasa yake dannar zuciyarshi ba kasafai yafaye bari wani ab
[6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง *JAMI'IN 'DAN SANDA*. ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง

*Mallakar*

*Maryam Umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*
*Minene Asalina*
*Mutum ce kuwa*
*Husna ko Huzna*
*And now*๐Ÿ‘‡๐Ÿป
*Jami'in d'an sanda*


*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*
*____________________________________*

*๐ŸŒˆ๐Ÿ‡ฐAINUWA ๐Ÿ‡ผRITER'Sโœ๐Ÿผ*
*๐Ÿ‡ฆSSOCIATION๐Ÿค๐Ÿป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*๐Ÿ˜๐Ÿ˜



๐Ÿ…ฟ๏ธ_14



.................har k'arfe biyu bai dawoba ,gaba d'aya Momma tashiga damuwa gashi sai kiran wayarshi takeyi amma a kashe ,tunani takeyi to mi ya tsayar dashi har wannan lokacin bayan yace mata bazai jima ba ,sannan ga al'adanshi ma baya fita ko ina in weekend ne wuni yakeyi a gida idan kuwa har wani uzuri ya fitar dashi tofa bazai jima ba zai dawo,

Tunda ya fita daga gidan bai zame a ko'ina ba sai gidansu Ibrahim , yana zuwa ko cikin gidan baishigaba ya wuce dakin Ibrahim ciki ciki yayi sallama ya shiga dakin,

Ibrahim na zaune Yana aiki a laptop dinshi yaji sallamar abokin nashi , kamun ma yayi wata magana har Hisham ya haye kan katifarshi yayi ruf da ciki batare da ya ko kalli inda Ibrahim yake ba ,

Ganin hakan yasa Ibrahim ya kyaleshi don yasan ko yayi mashi magana bazai kullashi ba juyawa yayi yacigaba da aikinshi ,

Yana nan kwance tsawon wani lokaci kamun bacci 'barawo yayi awon gaba dashi, fiye da awa biyu yana bacci kamun ya tashi a firgice yana nanata kalmar innalillahi wa inna ilaihin raji'un, cikin kankanin lokaci ya hada wani uban zufa, sai fama sauke ajiyar zuciya yake , duk sakamakon mummunan mafarkin da yayi akan Abbansa, mafarkin yayi Abbanshi na cikin wani surkullen daji mai matukar ban tsoro sai faman gudu yakeyi kamar ba gobe yayinda wasu mutane suke biye dashi da muggan makamai suna neman su kasheshi , shikuwa Abba banda gudu da kiran sunan Hisham ba abunda yakeyi har yakai ga ya k'ure hanyar ba sauran inda zai gadu ganin hakan yasa ya runtse idonshi yafara maimaita kalmar shahada , yayinda mutanen suka tsaya akanshi sai faman babbaka dariya sukeyi wanda dariyarsu ke amsa kuwa acikin dajin , daya daga cikinsu ne ya daga takobinshi ya sarewa Abba kai wanda hakan yayi daidai da k'arasowar Hisham a wajan , wani irin ihu yayi kamun yayin kan mutanen nan amma kamun yak'arasa sun 'bace 'bat babu su babu alamarsu , haka ya karasa wajan Abba aguje saidai kamun ya k'arasa ne ya farka a razane,

"Lafiya dai Hisham "? Cewar Ibrahim da shigowar shi kenan ya fito daga cikin gida,

Girgiza kai kawai Hisham yayi don yama kasa magana gaba daya jikinshi da harshen shi sunyi mashi nauyi ga wani bugu da zuciyarshi keyi , a hankali ya mike tsaye ya sanya takalminshi batare da yacewa Ibrahim komai ba yakama hanyar fita daga dakin,

Ganin hakan yasa Ibrahim ajiye abincin da ya karbo masu wajan mamanshi ,janyo kofar dakin yayi ya rufe da sauri yabi baya Hisham don sam bai gamsu da yanayin da yagani a tattare da abokin nashi ba , ฦ™arara yake hango tsananin tashin hankali a cikin kwayar idonsa,

Jiki a sanyaye yayi sallama akofar falon kamun ma Momma ta amsa mashi ya d'age labulen ya shiga,

Zaune take akan kujera ta buga uban tagumi ,gaba daya jin yanayinta takeyi ba dadi saidai tarasa abinda yake damunta , shiyasa ta alamk'anta hakan da rashin dawowar mijin nata,

Zama yayi ya gaisheta kamun yace " Momma Abba fa"?
"Abbanka ya fita tun d'azu tun bayan fitarka amma har yanzu bai dawoba sannan nayita kiran wayarshi amma bata shiga ," tafad'a cikin matukar damuwa ,

Dum dum dum gabanshi yayi wani irin bugu da karfi , amma tuni ya daidaita nutsuwarshi ya zaro wayarshi yafara kiran Abban , shima dai bata shiga ba ,suna haka Ibrahim yayi sallama ya shigo , bayan ya gaida Momma ne ya nemi waje ya zauna , ganin damuwa ฦ™arara akan fuskokinsu ne yasa ya dubi Momma yace
"Momma lafiya dai naga kamar kuna cikin damuwa?"

Murmushin karfin hali tayi tace ba komai Ibrahim kawai muna jiran Abbanku ne ya fita tun d'azu amma har yanzu baidawoba , "

"Ayya Momma kila wani abun ne ya tsareshi amma insha Allah zai dawo bada jimawa ba "

"To Allah yasa , ku tashi kuje kuyi sallah sai kuzo ga abinci can kuci kamun yazo",

"To Momma" cewar Ibrahim,

Shikam gogan ko bakin magana baisamu ba don sosai ya tsorata da mafarkin da yayi,

A hankali ya furta " amma Momma Ina yace maki zaije ne?"

"Wallahi bai gayamun ba yadai ce mun zasu fita ne shida inspector Haruna"

Jinjina kanshi kawai yayi sannan ya tashi ya koma dakinshi , alwala yayi yayi Sallah shida Ibrahim sannan suka koma falon Momma alokacin itama ta idar da salla kenan. Zamansu kenan sukaji ana buga get din gidan


******************

Acan 'bangaren su Abba kuwa lokacin da abun ya faru akan idon wasu bayin Allah su ukku aikuwa a firgice suka rafka salati tareda juyawa aguje suka nufi motar da Abba ke ciki , zuwa lokacin kuwa tuni mutanen dake wucewa sun fara tsayawa kamun kace mi wajan yacika da jama'a haka aka taru da kyar aka 'ban'baro Abba daga karkashin motar , gaba daya fuskarshi tayi dameji ga kafafuwanshi da hannayenshi duk sun karairaye jini kuwa yace ina bakayi bani waje tuni wajan ya jike da jini , ahakan kuwa cikin ikon Allah yana numfashi saidai in yaja numfashi sai yayi kusan minti biyu kamun numfashin ya dawo , gaba daya mutanen dake wajan suncika da tausayinshi masu raguwar zuciyar tuni sun fara kuka , ganin har lokacin yana numfashi yasa wani saurayi ciccibarshi ya sanya mota suka nufi hospital mafi kusa dasu ,

Sai bayan tafiyarsu ne sannan wasu suka lura da inspector Haruna yashe a kasa cikin halin suma shima nan suka kwasheshi sukabi bayansu


Suna zuwa basuyi wata wata ba suka karbeshi ganin kakin 'yan sanda ajikinshi , emergency aka nufa dashi ,likitoci biyar ne akanshi suna faman ceton rayuwarsa , duk da kuwa su kansu sunsan ba lallai ne ya rayu ba ganin irin halin da yake ciki ,

Haka suka share sama da 30mnt kamun Allah yayi ikonsa , Allahu Akbar Allah mai yin yadda yaso alokacin da yaso duk da Abba yana cikin mawuyacin hali kuma baisan inda kansa yake ba amma Allah yabashi ikon yin kalmar shahada yayin fitar rayuwarsa wanda su kansu likitocin sunyi mamakin jin magana a bakinshi, bayan sun cire mashi kowace na'ura da suka sa mashi ne sukaja farin kyalle suka rufeshi, sannan suka fara fitowa dai bayan dai,

Nan suka sanar da mutanen da suka kawo shi Allah yamashi rasuwa ,
Duk da basu sanshiba amma sunji mutuwarshi sosai wannan saurayin kuwa harda hawayenshi , ganin kayan yan sanda ne ajikin Abba yasa ya fito yanufi babbar HQ ta yan sanda , nan ya zayyanemasu duk abunda ke faruwa , haka aka hadashi da wasu yan sanda suka nufi asibitin,

Lokacin da sukayi arba da gawar ba karamin firgita sukayi ba ganin fuskar inspector Abdulrahaman nan suka kira HQ suka fadin abinda yake faruwa , ai kamun kace mi asibitin yacika da jami'an yan sanda kota ina , masu jin dadi naji masu jin ciyon tashin nagartaccen Jami'i nayi , a haka aka tura wasu daga cikin yan sandan akan suje su sanar a gidansa , shine fa suka zo suna buga get din gidan,



Jiki a sanyaye Ibrahim yaje ya bude get din, ganin yan sanda abakin k'ofar ba karamin kayar mashi da gaba yayi ba wanda baisan dalili ba,
Gaisawa sukayi kamun suka ce mashi suna sallama da matar gidan ne ,

Jin haka yak'ara hautsina ma Ibrahim hanji , amma haka nan ya daure yace "to shikenan kushigo daga nan zanje in gayamata , " suka amsa da "to"

"Momma Wai wasune keson magana dake" ............. Kamun yak'ara magana Hisham yayi zubur yace " su waye"?

"Bansansu ba amma dai nagansu da kayan yan sanda" cewar Ibrahim

Ai kamun ma su farga har Hisham yakai waje inda Momma da Ibrahim suka rufa mashi baya,

Daga Momma har Hisham saida gabansu yayi mugun faduwa lokacin da sukayi arba da wadan nan yan sandan , cikin sark'ewar murya Hisham yafara jefo masu tambayoyi batareda ya tsaya gaisawa dasu ba,

"Lafiya mi yake faruwa mi kukazoyi nan ina Abbana yake yanadai lafiya ko" ?? Haka yayita jera masu tambayoyi ,

D'aya daga cikinsu ne yayi karfin halin cewa "ka kwantar da hankalinka dama munzo tafiya daku ne saboda sir yasamu had'ari a hanyarsa ta zuwa gwangulori yanzu haka yana hospital shiyasa mukazo tafiya daku,

Wani irin sarawa kan Hisham yayi da k'arfi kamar an buga mashi guduma da sauri ya sanya duka hannayenshi ya tallabe kanshi da yakeji kamar ba'a jikinshi yake ba sai maganar wanna mutumin kemasa amsa kuwwa a kunne tabbas wani mummunan abu yafaru da Abbanshi koda ganin yadda mutumin ke magana yana sunne kai ,kamun kace mi juwa tafara daukarshi taga-taga yayi zai fad'i da sauri Ibrahim ya rikeshi , basu ankaraba sai jin faduwar Momma sukayi timmm ak'asa ta fadi babu numfashi,
Da sauri Ibrahim ya sakeshi ya nufi Momma yana kwala kiran sunanta a firgice , Hisham kam tuni yayi mutuwar tsaye kwakwalwar shi ta tsaya cak yakasa tuna komai a hankali idonshi yafara rufewa sai gashi shima a kasa a some..............โœ๐Ÿผ




*Littafina yakoma na kud'i 200 Kuma kowane lokaci zan iya dakatar da post dinshi har sai a paid grp Wanda rashin comment ne ya janyo hakan , kuma ko yanzu kuka canza ton zan canza Nima nabarshi a free dinshi kamar yadda nayi niya daga farko*๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž

*Sannan na rokeku ku taimaka ku tayani share*๐Ÿ‘๐Ÿผ๐Ÿ‘๐Ÿผ๐Ÿ‘๐Ÿผ๐Ÿ‘๐Ÿผ๐Ÿ‘๐Ÿผ
[6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: .a๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง *JAMI'IN 'DAN SANDA*. ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง

*Mallakar*

*Maryam Umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*
*Minene Asalina*
*Mutum ce kuwa*
*Husna ko Huzna*
*And now*๐Ÿ‘‡๐Ÿป
*Jami'in d'an sanda*


*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*
*____________________________________*

*๐ŸŒˆ๐Ÿ‡ฐAINUWA ๐Ÿ‡ผRITER'Sโœ๐Ÿผ*
*๐Ÿ‡ฆSSOCIATION๐Ÿค๐Ÿป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*๐Ÿ˜๐Ÿ˜


_wannan page nakine my *khairat isiyaku* kiyi yadda kk so dashi๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ


๐Ÿ…ฟ๏ธ_15


โ€ฆโ€ฆ...................wata irin k'ara Ibrahim ya fasa tareda kiran Hishammm sakin Momma yayi ya dawo wajan shi yana bubbugashi duk ya firgice yama rasa abunda zaiyi ,ganin hakan yasa wani daga cikin yan sandan yin azamar fita daga gidan motar da suka zo da ita ya bude ya dauko ruwa a gora yakoma ciki da sauri , nan yashiga yayyafawa Hisham ruwan ba'a dau lokaci ba ya farfado a razane yana kiran sunan Momma , hangota da yayi a kwance a wajan data fadi ne yasa ya zabura da karfi ya nufi wajen da take , d'ago kanta yayi ya d'ora bisa k'afafunshi yafara kiran sunanta da k'arfi ,
"Momma Momma ki tashi ki tashi nace muje mu gano halin da Abba yake ciki , ki tashi Momma Abbana Abbana kazo kace ta tashi arikice yake maganar daga nan kuma sai yafara sambatu wanda sun kasa fahimtar abunda yake cewa , ganin Momma bata farfado ba kuma suna k'ara 'bata lokaci da Hisham ma baya hayyacinshi yasa d'aya daga cikinsu kallon Ibrahim yace ku kamata musata amota muje asibiti zaifi , haka kuwa akayi Ibrahim shi kadai ya dauketa ya sanyata amota sannan ya kamo hannun Hisham suka shiga , direc suka nufi asibitin da aka kai Abba. Suna zuwa likitoci suka rufu akan Momma cikin ikon Allah bata dauki lokaci ba ta farfaษ—o , sai dai tana farfadowa da kuka ta farka sai kiran Hisham takeyi, likitan ne yafara kwantar mata da hankali akan ta tsaya za'a kira mata shi amma ina sam tak'i k'arin ruwan da aka sanya mata ma tuni ta fisge hannunta ta mike tsaye ,ganin hakan yasa yabada umurnin a je a kira Hisham ,

Banda Safa da marwa ba abinda yakeyi har wannan lokacin yakasa tambayar halin da mahaifinshi yake ciki saboda yana fargaban abunda za'a gayamashi wani irin zufa ne mai zafin gaske ke keto mashi ta ko ina kamar an masa wanka da ruwan zafi , ahaka wannan ma'aikacin jinyar ya taddashi , nan ya gayamashi likita na nemanshi , tun bai k'arasaba ya juya da sauri ya nufi inda aka shiga da Momma,

Tana ganinshi ta k'arasa wajanshi da sauri tace " Hisham ya jikin Abbanka mi yasameshi ka ganshi kuwa yanadai lafiya ko ??
Tunda tafara jero mashi tambayoyin ido kawai ya zuba mata yana kallonta , a wannan lokacin sam bazaice ga abinda yake tunawa ba gaba daya komai ya tsaya mashi tunda yaga irin yadda asibitin yacika da jami'an tsaro sai shige da fice sukeyi yasan tabbas sai Allah idan Abba yana raye ,
Jan hannu Momma kawai yayi batare da ya bi takan likitan ba suka fita daga dakin , direct wajan mutanen da sukazo dasu ya nufa yana zuwa cikin sark'ewar murya yace masu "a ina Abba yake"?

Duk diriricewa sukayi kamun daya daga cikinsu yayi masu jagora zuwa dakin da gawar Abba take,

Tunda suka nufi wajan gabansu ke wani irin bugu kamar zai fashe a haka har suka shiga dakin,
Dukkansu cak suka tsaya a inda suke suna k'arewa farin k'yallen da aka rufa mashi kallo wanda gaba daya ya 'baci da jini ,
Jiri ne yafara d'iban Momma a haka tarink'a tafiya har ta k'arasa inda gawar take a hankali ta sanya hannunta wanda yake rawa sosai tafara janye farin k'yallen, runtse idonta tayi da k'arfi kamun kuma a hankali takoma budesu ta zuba mashisu ko k'yaftawa batayi yayinda a lokacin komai tsaya mata yayi tana kallon abun kamar a mafarki sai fatan take Allah ya tayar da ita daga wannan mummunan mafarkin da takeyi ,
Shafa fuskarshi tayi a hankali tare da furta " "Abban shalele" Abban shalele da gaske mutuwa zakayi kabarmu , ? Kar ka mana haka Yaya ka tashi Sam bazamu iya rayuwa ba in babu kai ganin har yanzu bai motsaba yasa tafara magana da karfi tana Kiran sunanshi tareda jijjigashi tana kiran karya mutu ya tashi ,

Matsawa dan sandan yayi kusa da ita sannan yasa hannu ya janyo farin kyallen yakoma rufe Abba dashi ,cikin matukar tausayawa yace " Hajiya saidai muyi hakuri Allahn da yabamu shi ya karbi abunsa , sai dai mubishi da addu'a kawai ,

Girgiza kai Momma tafarayi tana ja da baya har takai da bango durk'ushewa tayi a wajan tana wani irin jan numfashi zuciyarta kuwa kamar zata fasa kirjinta ta fito tsabar bugun da takeyi , kamun bugun zuciyarta ya tsaya cak ta koma sulalewa ta fadi a wajan a some ,

Dan sandan ne yayi saurin fita kiran likita yayinda akabar Hisham nan tsaye ba um ba um um shi baiyi gaba ba kuma baiyi bayaba yayinda idonshi ke kafe akan gawar mahaifinshi duk da faduwar da Momma tayi hakan baisa ya juya ya kalleta ba ,kalaman wannan ma'aikacin kawai yakeji yana mashi amsa kuwa acikin kunne *_Allahn da ya bamushi ya k'arbi abunshi_*

Ahaka wasu likitoci biyu suka shigo suka shiga bawa Momma taimakon gaggawa yayinda wannan dan sandan yaja hannun Hisham suka fita haka yarinka bin shi kamar wani wawa sam yakasa gane komai yakasa fahimtar komai yakasa aikata komai sai zuciyarshi dake mashi wani irin lugude mai tafe da tsantsar fargaba,

Office din babba likita suka nufa don yin duk wani cike cike don karbar gawar , haka akasa Hisham ya rattaba hannu aka gama duk wani cikwu-cikwu aka basu gawar ,
Haka suka dauko gawar a motar asibiti suka nufi gida ,

Lokacin da suka zo har kofar gidan tafara cika da mutane nan aka shiga dashi aka mashi wanka aka shiryashi cikin likkafani , har wannan lokacin Hisham yakasa furta koda kalma d'aya ne yayinda idanunshi da zuciyarshi suka soye sam ba alamar hawaye a idonshi ,

Acan asibiti kuwa Momma tana farfadowa bata sauke idonta a ko ina ba sai akan gadon da taga gawar mijinta a kwance ,dubawa tayi da kyau tare da sake murza idonta amma har lokacin bataga komai ba a zabure ta tashi tana fadin "ina mijina ina kuka kaimun mijina , ?
"Kiyi hkr Hajiya sun tafi da gawar gida kizo muje akwai wad'an da aka bari idan kin farka sai su tafi dake cewar likita,

Gawa gawa gawa fa yace kenan da gaske ne tarasa mijinta uban danta majinginarta kuma majibincin lamarinta , a hankali cikin wata irin murya ta furta " *Innalillahi wa inna ilaihin raji'un Alhamdulillah ala kulli halin* a hankali taji wata irin natsuwa da tawakalli ya ziyarceta , tunawa da tayi ai tanada Allah kuma shine gatan kowane bawa , sannan Allah baya barin wani dan wani yaji dad'i daga nan taci gaba da ambaton sunan Allah yayinda a hankali wata irin nutsuwa ke k'ara shigarta , ahaka har suka isa gida ,

Lokacin da tayi arba da taron jama'a k'iris yarage bata koma faduwa ba haka dai ta daure tana tafe tana dafa bango har ta shige cikin gidan ,

A falo ta tarar da mata dank'am matan abokanshi ne da makota sai k'awayenta nan ta ra'basu ta shige cikin bedroom dinta ta mayar da kofar ta rufe kamun ta zame anan wajan ta saki wani irin kuka mai ban tausayi,


Bayan an shirya shi ne aka nemi Momma da Hisham da suje suyi mashi addu'a ,

Addu'a sosai Momma tayi mashi tanayi tana kuka mai tsuma zuciya yayinda Hisham yakasa koda motsa bakinshi ne bare yayi magana sai dai idanunshi da suka kad'a sukayi jajir ga wani girma da suka k'ara abun tsoro , ganin yakasa yin komai ne aka dauke gawar akayi waje da ita inda za'ayi mashi sallah,

Bayan angama sallah ne aka nufi mak'abarta , sai a lokacin Hisham yafara dawowa hayyacinshi , lokacin da aka bashi gawar ne don ya sanya mahaifinshi da kanshi wani irin sanyi mai haษ—e da makyarkyata suka kamashi gada daya jikinshi rawa yakeyi sam yakasa rike gawar sai da aka taimaka mashi bayan an sakashi ne aka rufe kamar yadda akema kowane mahaluk'i alokacin ne wani marayan kuka ya kwace mashi mai tafe da wani irin sauti mai taba zuciya lokaci daya wani tari mai karfi ya sark'eshi kamun kace mi yazube a wajan a some ,
Nan aka daukeshi wasu suka nufi wajan amsar gaisuwa abokanshi kuma suka nufi asibiti dashi ,

Kwana sambatu Hisham yayi kamar wani mahaukaci sabon kamu , Ibrahim da wani abokinsu Aliyu ne a wajanshi , Momma kam tuni k'arfin imani ya shigeta ta fawwalawa Allah komai sai addu'a take ma mijinta saidai duk da hakan takasa tsayar da hawayenta musamman in ta tuna da Hisham ,

*Washegari*

K'arfe 10am na safe a Lagos tayi masu , Abdullahi ne da Inna Asabe sai matarshi da yaranshi , suma tunda labari ya riskesu jiya suke cikin tashin hankali musamman ma Abdullahi yayi kuka kamar ba gobe yayi dana sani tafi cikin kwando haka kawai akan mace ya dauki tsanar duniya ya daurawa tilon d'an uwanshi akan *mace* yafita sabgarshi baya shiga duk wani abinda ya shafeshi yayi watsi da zumunci duk akan mace yanzu wa gari ya waya gashi nan yarasa tilon d'an uwanshi da bashida kamarshi duk duniya , mahaifinsu har ya mutu yana masu nasiha akan su kula da zumunci Amma duk da haka baisa ya gyara tsakaninshi da dan uwanshi ba to ga irin ta nan yarasashi a lokacin da yafi buk'atarshi

Kuka yake sosai yana neman yafiyarsu lokacin da yakewa Momma da Hisham gaisuwa da yake tun da sassafe Hisham ya baro asibitin batare da an sallame shi ba , duk da har wannan lokacin bai gama dawowa daidai ba ,

Nan Alhaji Abdullahi da iyalanshi suka zauna har aka gama amsar gaisuwa , saida akayi kwana bakwai sannan yayi shirin komawa tareda matarshi bayan ya ajiye masu duk wani abunda yasan zasu buk'ata tareda gaya masu duk abunda sukeso su kira su gayamashi , anan aka bar inna Asabe don tace anan zata zauna tarink'a debewa Momma kewa har

Please Login or Register in order to submit comment