Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ranki hakuri ba ko uwar gidana?'' Kmr tana jiran yayi maganar kawai ta fashe da kuka tare da shashsheka kmr zuciyarta zata tarwatse haka takeji. Kara rungumeta yayi a jikinsa sosai yasa bakinsa a cikin kunnenta yana furta mata kalamai masu dadih, da kyar yasamu ta tsagaita da kukan amma still tana hawaye sbda batayi kukan daya wadaceta ba, ta dago knta dake jikinsa ta zuba masa ido kana ta fara magana "Zuciyata ta gaji da hkri....dan Allah Yallabainah yaushe saraki zezo gareni kmr yadda ko wacce uwa d'anta ke zuwa gareta? Zuciyata na cike da karaya a kan jalaluna dan Allah ka kirasa a waya kace yazo ya ganni inaso insa kansa a kirjina yaji dumin zuciyar uwa kmr yadda ko wanni d'a keji shima yasan shi d'a ne ba maraya ba..." Yadda take mgnr tini me martaba ya fahimci kmr tana neman fita a hayyacinta ne, Cikin muryar kwantarda hankali me martaba ya fara magana ta yadda knta ze dauka yasan abinda takeji a zuciyarta tanada dauriya a matsayinta na uwa kuma mace me rauni. "Zezo gareki insha Allahu salma, ki kwantardamin da hankalinki dan Allah kinga shekaran jiya dr ya duba jininki yaga ya hau..dan Allah salma kiji tausayina kisawa ranku dauriya kici gaba da Adduarh kmr yadda kk saba karki sabauta min rayuwarki dan Allah zan kirashi ince yazo ya ganki..." Ya fadi mgnr karshe ne dan hankalinta ya kwanta amma yasan koya kira dannasu da wuya ma ya daga, inma ya daga ba lallai yazo ba, gabaki daya tamkar basu suka haifesa ba haka yake rayuwarsa. Ajiyar zuciya ta sauke tasan mgnr daya fadi kawai danya kwantar mata da hankali ne, hawaye keci gaba da zirya a idanuwanta ta fara magana. "Nasan baze zoba me martaba,,," ta fadi hkn tana jinjina kai. Daura hannunsa yayi a kn cinyarta yace "muci gaba da Adduarh insha Allahu komi ze zama labari..." Girgiza masa kai tayi tana fadin "Kullum kullum inatayi Nagaji Wallahi, kasan zuciyata na cike da son yaronnan shi kadai Allah ya bani duk duniya wallahi me martaba ba wanda yasan me nakeji a zuciyata ko yau na fadi na mutu da yaronnan a zuciyata na mutu, San duniya da Allah yasamin duk ya tabbata ne a kan yaronnan, inaji a jikina kamar ba ranar da yaronnan zuciyarsa zata dawo garemu, .." Rufe mata baki me martaba yayi da hannunsa yace "karkiyi sabo knji iyalina, karki mnta da babu abinda yafi karfin ubangiji dan Allah kici gaba da hakurin danasanki dashi pls..." Daura kanta tayi a fuskar gadonta, ita kadai tasan wani hali zuciyarta ke ciki, gani takeyi abinda takeji ma a kan Abdoljalal koshi dayake ubansa bejin rabin abinda takeji, (wani abin se uwa kan uba baze dauka ba?. "Inaji a jikina da kunci zan mutu a zuciyata na Soyayyar Jalaludden...'' Ta fadi hakan yayinda zafafan hawaye ke kara wanke mata kumatuna.. Me martaba ya fuskanci zafin datakeji ne a zuciyarta yake kokarin fitar da ita a hayyacinta maganganun datakeyi ma daji bata hayyacinta. "Dan Allah ki dena irin wadannan kalaman, bansan sake jinsu daga gareki dan Allah ki fawwalawa ubangijin sammai lamarinki, yaronnan Allah ne ya bamushi kuma ya rubuta komi na kaddarorinmu da nashi kaddarorin , dan Allah ki maida lamarin nan inda muka saba maidashi wato ga ubangijinmu banason irin wadannan kalaman na fitowa daga gareki gimbiyata, ki kwantarmin da hankalinki dan Allah na rokeki kiji tausayina hajjajuna...." Ya karashe maganar hadi da jawota jikinsa, still se kwallah takeyi, gani takeyima kmr mijin nata be fahimtarta kwata-kwata itama bata fahimtarsa ko kadan, Son danta tilo kadai ke dawainiya da zuciyarta, a haka ma tayi kwarin zuciya dan babu jinsin balaraben daze iya jure abinda take jurewa, saboda a yarirrika da dama na duniya babu jinsin yaren daya kai balarabe san yara musamman ma ita da kwara daya tall Allah ya mallaka mata a duniya, ita fa bata ki koda yaushe ta dinga sashi a idanuwanta ba, amma yanzu shekara da shekaru be zuwa inda suke ai dole tashiga damuwa iya damuwa....lallashinta me martaba ya dingayi har yasamu ta dan fara nutsuwa ya saka mata karatun alqur'ani ba jimawa taji zuciyarta ta kuma sanyi ta dawo hayyacinta nan take bacci nannauya me cike da mafarkin Jalaludden dinta ya kwasheta.




*Akwai wata a kasa fa...*


*Vip 1k normal 500 0542703718 Saadatu Abdullahi gt bank. shedar biya ta nan 08101626484 ko M.T.N card duk ta wancan sim din.*





selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*WATA KISHIYA*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*Littafin ma'aurata ne*
SAADATU BINTU ABDULLAHI✍🏽(writer of Kyautar Allah)
Last free page😊

*DEDICATED TO HUBB, MY HAPPINESS*
Last Free page 10
Tin daga ranar daya ganta be kuma gangancin rashin ganinta ba a rayuwarsa, wato de yazamana kullum se sun hadu, inta kawo masa abinci, kasawa yakeyi ya tsare dole seya ganta. a hankali a hankali shakuwa me karfi tashiga tsakaninsu musammanma shi gogan, wanda zuwa yanzu wallahi baccin kirki ma be iyawa sena sata. the more yake ganinta the more kwad'ayin ganinta ke kuma taso masa a ransa, idan tazo kawo masa abincin se yaji kmr karta tafi, ji yakeyi kmr ta zauna yayita kallonta har ya kare rayuwarsa yana kallonta, akwai wani sirri a tattare da ita dashi kadai yasanshi, wato ganinta nutsuwar jikinsa yake dawo masa dashi, tinda idanuwansa suka gauraya da yarinyar abincinta ya kara masa dadih a harshen baki, zuwa yanzu ya fahimci yarinyar bebiya ce, ranar daya matsa mata kan dole seta mishi magana ranar ta nuna masa ita bata magana, a fari yasha wasa takeyi daga baya ya fahimci ashe da gaske ne ita din bebiya ce, wani irin tausayinta ne yayi wankan tsarki ya cika masa zuciya, a ranar be rintsa ba, har kwallar tausayinta seda ta zubo daga kwayoyin idanuwansa, ze iya cewa ya mance when last hawayen tausayin wata halitta ta duniya ya fita a idanuwansa, amma se gashi a ranar shike kuka da idanuwansa, kmr wani small baby, yanayoyin dayakeji a kan yarinyar ya yawaita a zuciyarsa, be tabajin tausayin wani a duniya ba kamar yadda yakejin tausayin yarinyar a rayuwarsa. A bangaren al-muqri'ah kuwa a tsorace take dashi, sbda tunawa datakeyi da kalaman hajiya saude a kan mijinta. "Zan iya kisan kai a kan mijina..." Itace kalmar datafi tsawa al-muqri'ah a rai, kuma take tsananin tsoron kalmar ko ince kalmar ke kara sa mata tsoron hajiya saude a zuciyarta.....

Yau ya tashi da shirin barin garin zuwa garin abuja saboda yanada wani emergency meeting jiya ya dace ayi meeting din amma saboda rashinsa a gun meeting din ya Hana ayi shi jiya, aka barshi zuwa jibi wato inya iso garin yau se ayi meeting din gobe. 10:am ya shirya tsaf cikin danyar shadda royal blue, se zallar uban sheki da kwalkyali shaddar keyi, ba karamin amsarshi shaddar tayi ba ta amshi launin fatarsa ainun kansa sanye da hular zalla bukhar wadda ta dace da kalar shaddar jikinsa, fuskarnan tasa ta fito tayi fayau da ita har wata yar kiba ya kara na zallar kwanciyar hankali A bayyane amma inside shi kadai yasan gashin dayake karba . Feshe jikinsa yayi da perfume dinsa, ya daura dankareren watch dinsa ya daura a hannunsa, ya zira takalminsa ya fito hannunsa rike da bag dinnan da wayoyinsa, se azabar kamshi yake zubawa hannunsa rike da yar karamar jaka Baka wadda ke dauke da takaddunsa daze bukata a abujar sam ko kaya be dauka inzeje abujar kasancewar canma yanada komi na bukatuwarsa a can. Allah-Allah ya dinga yi ya sakko kasan, sbda so yakeyi yaga yarinyar, da zallar tunaninta ya kwana a ransa ko bacci beyi ba kwana yayi a kan dadduma yana ibada. Yana sakkowa downstairs din ya daga kai ya kalli kofar dinning room dinsa, nan take yaga ta nuna farin wuta, wato harta ajiye masa breakfast dinsa, kallon dankareren watch din hannunsa yayi yaga har goma ma ta wuce, karasawa dinning room din yayi jiki a sanyaye saboda so yakeyi kawai ya ganta, kuma yasan da wuya ya ganta yanzu. Zaunawa yayi ya danyi breakfast din a gaggauce saboda sauri yakeyi, yana gamawa kenan daya daga cikin wayoyinsa tayi ringing dubawa yayi yaga sunan dr mus'ab karara ya bayyana, haushi ne ya kamasa, shi yama manta da mus'ab din zasu tafi abujar, saboda dashi za ayi meeting din, meeting din na siyasa ne, kin dagawa yayi danyasan mus'ab da wutar ciki, shi kuma yayi alkawarin yau seyaga yarinyar dan yasan in be gantaba wallahi dawuya inyaje abujar yaji dadinta. Yana gani mus'ab din yayi masa miss call har uku amma yaki dagawa, sema ya gyara zama a kan kujerar dinning din ya tsurawa kofar dayasan tabbas ta nan zata shigo ido, yanaji kiran dr-mus'ab ya kara shigowa wayarsa, amma yaki dagawa har seda ya kara masa miss call har uku amma yaki dagawa yana nan zaune amma zuciyarsa na knta. Har wuraren 11:20am amma bata shigo ba, zuwa lokacin dr mus'ab ya masa kira yafi goma, dan haka ya gaji ya daka, wayar ya kara a kunne, cikin tsananin bacin rai dr mus'ab ya fara magana. "Amma kasan yau zamuyi tafiya ka kwanta kana bacci bayan fly din daza mubi ma 11:am ze tashi kaga kasamu yin missing din fly din munyi asarar kudi kuma..." "Kai kudin fly ya dama ni abinda ke damuna yafi yawan duniya da abinda ke cikinta..." Abdoljalal ya Fadi hakan a zuciyarsa ba tare dayasan maganar ta fito ba har Dr-mus'ab yaji, murya cike da mamakin daya doke ma Dr-mus'ab bacin ransa ya jefo masa tambaya "Mekace?" Zuciya cike da mamaki ya masa tambayar danshi be tabajin irin wadannan kalaman daga bakin Aminin nasa ba. Firgigit Abdoljalal yayi jin xancen zuciya ya fito fili saurin dakewa yayi yace "Am sorry wani tunani nakeyi daban bansan ma mena ceba..." Dr mus'ab yace "ba haka bane wallahi dole akwai abinda ke damunka, ka fadamin pls...." Abdoljalal yace "Malam ni ba abinda ke damuna...kawai ka kara siya mana wani Private jet din bari in shirya dole se kmr 12:pm zamu tafi gaskiya..." Mamaki ya kuma rufe dr mus'ab jin wai yau abokinsa ne ke African time, mutumin da dawuya a jirasa amma yau shine ke maganar wai se 12:am zasu tafi a memakon 11:am . "tabbas akwai abinda ke damunka...tafiyar daya dace muyita 11:am saboda zamuyi meeting 12:pm yau, gana gobe 10:am za a shigesa, amma shine zakace se 12:pm zamu bar kaduna zuwa Abuja..." Cewar dr mus'ab. "Au ni na mnta ma xamuyi meeting yau , kawai ka kirasu kace a bar meeting din yau a bari se gobe duka ayi biyun a goben insha Allah...." Haushi ya Kara rufe dr mus'ab dan haka yace "Amma de baka da lafiya ne ko jalalu? Yaza ayi ace jiya baka jeba, kace a bari daya ayi yau yanzu kace a bari duka biyun ayi gobe dayake an gaya maka suma basu da uzuri ne, se kai keda uzuri... '' Abdoljalal ya ci gaba da magana cikin isa da zallar mulki yace "toh a hakura da meeting din ni de wallahi se 12;pm zan bar kd kila wa kala ma..." Yana gama fadar hakan ya ajiye wayar, ba tare daya jira me dr mus'ab zece masa ba. Har 12:30pm bata shigo ba, zuwa lokacin dr mus'ab ya kara kiransa harya gaji, amma yaki dauka sede ya tura masa da message din kawai inya siya jet din ya kara siyan wani na 1:pm, haushi daya kama dr-mus'ab be masa reply din sakon ba. 12:35pm ta shigo side din idanuwanta suka sauka a kansa, yayi matukar mata kyau Ainun, shima din itan yake kallo, murmushi ta sakar masa domin itama data kawo masa breakfast din bata gansa ba bata ji dadih ba, dashi ta kwana a ranta knr yadda shima ya kwana da ita a ransa. "Al-muqri'ah...'' Ya ambaci sunanta da dadd'ar muryarsa wadda ke ratsa mata dodon kunnuwa. Wani murmushin ta kara sakar masa wannan karan seda kaf dimples dinta suka lotsa, shima murmushin ya sakar mata yana mejin tausayin yarinyar na ratsashi, ganin tanada komi na duniya amma bata da bakin magana. Tsugunnawa tayi ta masa alama da hannu na gaisuwa, amsawa yayi a bayyane, yana gane kome tace masa da bebanci, yana mamakin yadda akayi yake gane maganarta dukda be taba ganin bebayeba a rayuwarsa se ita, haka itama tana mamakin yadda akayi yake gane kwatancen da duk me take nufi. Sosai ya kureta da ido tana tsugunnan yana mejin wani irin mashi na kwanciyar hankali na sukarshi tako ina, tinda ya tashi a yau din beji natsuwa ba se yanzu daya sata a kwayoyin ruwan idanuwansa, babu abinda yake daga masa hankali kamar tafiyar dazeyi yayi kwanaki be ganta ba yasan duk se ya shiga damuwa da tashin hankali mara misaltuwa. "Karaso mu gaisa sosai..." Ya fadi ba tare ma dayasan ya fadi ba, shi fa a kan yarinyar nan ya fuskanci kamar tongue dinsa beda control. Mikewa tayi ta karaso duk idanuwansa na kanta, se yanzu ya kula da hijjabin jikinta pink ne ya matukar amshi farar kyakyawar fuskarta yadda kasan dan ita aka halicci hijjabin haka hijjabin ya amsheta. "Taso ki zauna kan kujerar nan..." Ya fadi hadi da nuna mata dayar kujerar dinning din. Tsura masa ido tayi da kujerar daya nuna mata, nan take ta daga masa kafada alamar bazata zauna ba, se yaga ta masa kyau a daga masa kafadar datayi, saboda yadda ta saki jikinta har yaga nonuwanta bata taba yarda ta saki jiki yaga nonuwanta ba se yau dayakeda tabbacin shafa'ah tayi, cikin kissa yake kallon nonuwan nata kai bakace nonuwanta yake kallo ba ko ita bata isa ta gane me yake kalloba. "Yarinyar akwai manyan nonuwa masu kyau..." Ya fadi a ransa yana kara kure nonuwanta da ido hatta da kan nonuwan seda suka nuna shadi ta saman hijjabin jikinta, wani irin yanayi jikinsa ke amsa wanda ya kara zamo masa bako sosai. "Meyasa bazaki Zauna ba?" Ya tambayeta still idanuwansa na kn kaciyar nonuwanta, wanda yakeji kmr ya dawwama a kallonsu, domin dadih yakeji a jikinsa. A zahiri al-muqri'ah tasha ko ita yake kallo sam bata fahimci nonuwanta yake karewa kallo ba. Da bebanci tace masa saboda su basa zama a kan kujerar da babba ke zama... Murmushin dake kan fuskarsa ya kara fadad'a, daman ya jima da fahimtar yarinyar ta samu tarbiya daga tushe. "yau zanyi tafiya ne zuwa abuja..." Jin abinda yace yasata jin rashin dadih a zuciyarta nan take fuskarta ta chanza. Adduarh Allah ya tsare ta masa da bebanci dukya fuskanci me take nufi ya amsa da Amin zuciya fal jin dadih ya fahimci chanjin fuskar tata, daya gaya mata zeyi tafiya... Tambayarsa tayi da bebanci waze dinga dafa masa abinci inya tafi... Yar dariya yayi wadda ya mance ma yaushe yayi irinta ya bude baki ze bata amsa, Daya daga wayoyinsa tayi ringing dubawa yayi yaga Sunan Ahamad ya bayyana wato babban guard dinsa wanda in zeyi tafiya dashi yake tafiya. Daukar wayar yayi ya kara a kunnensa, daga cikin wayar Ahamad din ya gaishesa amsawa yayi still idanuwansa na kan Almuqri'ah,. "Yallabai, Sir dr-mus'ab ya iso yace yanata kiranka bakayi picking ba,..." Daga cikin wayar Ahamad yace hkn. Abdoljalal yace "okay ya iso ina?" Ahamad yace "Gashi nan a kofar gidanka..." Abdoljalal yace "Okay ganinan Zuwa an shirya mota zuwa airport din dazamu hau jirgi?'' Cikin ladabi Ahamad yace "A, an shirya tin dazu sir..." Abdoljalal yace "Okay ganinan yanzu insha Allahu..." Ahamad yace "Toh sir a fito lafiya..." Abdoljalal ya amsa da "Allah yasa..." Ya katse wayar, duk al-muqri'ah najinsa duk duniya babu muryar dake mata dadin saurare kmr tasa, ko mace bazata nuna masa zakin murya ba. Mikewa yayi batare daya gaji da ganinta ba, sedan jin dayayi ahamad ya sanar dashi wai Dr mus'ab na kofar gidansa, tinda ya auri Hajiya saude suke gidan dr Mus'ab be Taba zuwa gidan ba se yau yazo ya tsaya a wajen get, Abdoljalal nada tabbacin dr mus'ab besan gidan ba kila ahamad ne ya bashi address din gidan. Al-muqri'ah tabishi da ido ganin ya mike tsaye ya kwashe wayoyinsa, itama ta mike ya kara bin hips dinta da ido seda ya ciza lebensa na kasa saboda wani irin azababben yanayi daya ziyarcesa kaf seda tsigar jikinsa ta tashi. A wannan karan ta fahimci hips dinta yake kallo dan haka tayi hanzarin ture hijjabin daya kwanta mata a hips din da hannunta ta cikin hijjabin. Basarwa yayi hadi da dan dauke kansa gudun kada girma ya fadi kuma alhalin yarinyar na ganin girmansa. "Zan tafi knji..." Ya fadi idanuwansa na kan kyakywan labbanta. Marairaicewa tayi kmr zatayi kuka, ba tare dasanma tayi hakan ba. Hakan datayi ya kara narke masa zuciya, nan take yaji kamar ya fasa tafiyar ya zauna kawai tana dafa masa abinci yana ganinta yanajin dadih, uwa uba kuma kayan jikinta duk zeta ganinsu dan yana bukatar ganinsu. Da kyar ya iya daurewa zuciyarsa ya fara kokarin barin falon cikin dakiya, yakai bakin kofar harta bude ya juyo yaga ta zubo masa ido, ganin ya juyo dinne yasata dauke danuwanta tayi kasa dasu. "Zanyi missing din Abincinki,...'' Ya fadi da golden sexy yum-lum voice dinsa me narkar da zuciyar maza. Dagowa tayi ta sakar masa murmushi kawai tana mejin maganar har kasan zuciyarta. "Kema zanyi missing dinki..." Ya fadi maganar ne direct daga zuciyarsa. A wannan karan ce masa tayi da bebanci itama haka..." Yayi matukar mamakin jin hakan daga gareta, ji yayi zuciyarsa ta kara narkewa da yanayoyi a knta, sosai ya tsaya ya kureta da ido, ita kuma kanta na kasa, ji takeyi kmr tafiyar dazeyi bazata sake ganinsaba. Da kyar Abdoljalal ya iya yaki da zuciyarsa ya fice a dinning room din yana mejin wani irin azaba a cikin zuciyarsa ji yakeyi watannan daya da yayi yana ganinta byn wata dayan datayi tana dafa masa abinci yanaci ba tare daya ganta ba, ji yakeyi kamar sunyi shekaru talatin da juna, sbda yadda yakejin zuciyarsa na amsawa a kn yarinyar Be tabajin kwatankwacin hakan ba a kn wata, se a kanta,. Karasawa yayi kn kujerar 2ct inda ya ajiye yar bag dinsa daya sakko da ita daga upstair dinsa, ya dauka hadi da zuge wani zip a gefe ya zuba wayoyinsa duka guda goma a ciki, tsayawa yayi yana tunanin tabbas akwai abinda ya mance dashi, nan take ya tuna ashe system dinsa ce ya mnta da ita yasan duk dan sanadin tunanin yarinyar ne yasashi rafka wannan mantuwar dabe taba irin taba se yau. Cikin hanzari ya nufa upstairs din ya dauko jakar systems dinsa, ya dawo ya dauki dayar bag din daga kara ajeta a kn kujerar 2ct din,ya rataya daya gefen dama daya gefen hagu, harya nufa kofar ficewa a side din, ya dawo ya koma dinning room din abinda ya basa mamaki ya ganta nan inda ya batta tsaye, ta zubawa kujerar daya tashi daga kai ido. Yana shigowa ta dago ta kalleshi ya sakar mata shu'umin murmushinsa me narkar da zuciyar mata. "Zanyi kewarki!'' Ya kara mai-maita mata kalmar daya fadi dazu, wani irin zazzafar bugu zuciyarta tayi, sbda jin kalmar a wannan karon ta haifar mata da wani irin zazzafan bugun zuciya me wuyar kwatantuwa, yayin da jijiyon jikinta suka amsa....ta zubo masa ido shima idon ya zubo mata,.. seda suka kwashi 10mnt a haka suna kallon juna ido cikin ido, a wannan karan ta gaza janye kwayoyin idanuwanta daga cikin nasa. A daddafe shi gogan ya janye nasa idanuwan daga knta, ya juya ze bar dinning room din ya sake juyowa. "Ki kulamin da kanki knji yarinyata..." Yayi wadannan kalaman ba tare dayasan sun subuce masa a baki ba. "Yarinyata!..." Dukkaninsu suka maimaita kalmar a zuciyarsu a lokaci guda, musammanma al-muqri'ah wadda kalaman suka mata tsananin dadih, fiye da duk kalaman dake bakinsa. "yarinyata..." Ta kuma maimaita sunan a zuciyarta yayinda duk wani lungu da sako dake birnin zuciyar tata ya cika da zallar farin cikin daba kowa bane ya haifar mata dashi bace Gogan. Juyawa yayi ya fice a dinning room din dan zuciyarsa na kokarin raya masa karma yayi tafiyar, kuma ga kira nata shigowa dukkanin wayoyinsa ba kakkautawa, ta bishi da Adduarh dawowa lafiya, yaji dadin adduarhta garesa, ya fice a side din , babu abin yake gani a ruwan fararen kwayoyin idanuwansa bace yarinyar. "Yarinyata..." Shima ya maimaita sunan daya kirata dashi a zuciyarsa, seda yayi wani irin kayataccen murmushi a fili danko boyesa ma ya gazayi. Ma'aikatansa na ganin ya fito a guje suka karaso suka amshi jakunkunan daya rike, suka sa maza a mazaunin bayan motar daze hau, wadda akayi packing dinta a dai-dai side dinsa, kallon side din hajiya saude yayi, yasan yanzu tana can tana bacci bata tashi ba, dan haka kawai aka bude masa gidan bayan motarsa ya shiga ya zauna hadi da zuge gefen bag din dayasa wayoyinsa ya dauko daya daga ciki ya dubo lambarta wadda akayi saving da *Saude* yayi typing message kmr haka. *Ni natafi abuja, Sena dawo,* ya tura mata kana ya ajiye wayar a gefensa. Dreva dinsa lukman, ya tada motar suka fice a gidan, yayinda ma'aikatan bakin get din keta koro masa addu'ur'in dawowa lafiya. suna tafe motarsa a tsakiyar motocin securities har motoci biyu se tashi Ta uku....

A waje get din gidansa yaga motar dr mus'ab a gefe, cikin hanzari yasa akayi packing tasa motar, Abdoljalal ya fito da niyar ze karaso inda motar dr din take, kawai dr-mus'ab din ya umurci dreva dinsa daya tada motar suka bar gurin. Murmushi Abdoljalal yayi, yasan haushi mutumin yaji, kuma dole ma yaji haushi dan dashi akama hakan baze taba jure ko rabi bama, dr dinma baze fara masa hakan ba. Motarsa ya koma , drevansa yaja zuwa airpot din. A can suka hadu da dr mus'ab, tini mashi ya hau jet din, se dreva dinsa dake tsaye yana jiran tafiyarsu kana shima yaja motar ya maidata gidan dr din. Abdoljalal da Ahamad na hannun damansa suka hau kerarren jirgin ma'aikatansa nata binsa da adduarh dawowa lafiya. Yana shiga jirgin ya tadda dr mus'ab kamar ze fashe ya cika ya batse sbda shi a zatonsa wannan matar tasa me kama da mazannan ce ta hanashi fitowa dawuri., Abdoljalal bebi ta kansa ba ya zauna a kusa dashi, yasa belt, Ahamad ya zauna a bayansu, ba afi 10mnt ba aka tada jirgin suka fara yawo a sararin samaniya. Har suka isa de mus-ab be masa magana ba, har zuwa washe gari yaki masa magana kuma gida daya suka kwana, washe gari sukaje gun meeting din suka gama lafiya, tin a gun meeting din Dr ya fukanci Abdoljalal nada wata damuwa amma kuma seyaga yayi kiba, dan be kallesa ba, se yau a gun meeting, yaga mutumin nasa yayi bul-bul har fresh ya kara, amma fa ya fuskanci rayuwarsa ta chanza ba kamar sanin daya masa ba tinda ya Auri hajiya saude wadda ita ce ta chanza masa kaf rayuwarsa, zuwa dagaja dagaja. Kwanansu biyu a garin abuja Amma Abdoljalal shi kadai yasan irin izayar dayake ciki, wallahi kwana biyun da yayi beganta ba ji yakeyi tamkar yayi shekaru dubu uku da hansin ne be ganta ba, ga wani yanayi yana ciki wanda be taba jinsa ba a kan ko wacce mace ba se ita, duk dare yanzu be iya bacci, kawai surar jikinta ke masa yawo a kwa-kwalwarsa, daya kwanta in akaci sa'arh bacci ya kwasheshi se ya hau mafarke mafarke a kan gashi

2 Comments On WATA KISHIYA
avatar
khadija-4-1-9

12 months ago

Reply

Please I want next page 13

avatar
daiy

12 months ago

Reply

Replying to khadija-4-1-9

This is a paid novel you have to contact the author to buy complete from her

Please Login or Register in order to submit comment