Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»Ώhttps://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€



*✍🏻writting by*
~*Binta Umar*~
~*[MAMAN ABDUL WAHABU*~]

~*Mrs Ahamad gwadabe*~



_Bissimillahi rahamanir rahimi_


_DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI_


~*WANNAN LITTAFIN QAGGE NE DA GA NI BINTA WANDA YAGA YAYI DAIDAI DA RAYUWARSHI A RASHIN SANI NE*~



~*_WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU KACAL IN KANA BUKATA SAI KAYI MAGANA*~
08089965176


*INA ALFAHARI DA MASOYA NA MASU SON RUBUTU NA ALLAH YAKARA KAUNA TA DAN ALLAH*😘


_ban yadda wani ko wata ya joya min littafi ba batare da izini na ba Ayi hattara_



~*DEDIGATED TO: MY FAN'S*~




*πŸ…Ώ1*



Ba kajin komai a gurin sai busa gami da sarewa da sawun doki kowa a gurinshi kokari yake yaga wucewar sarki *Almustapah* ma Adalin sarki kenan Wanda Al'umarshi take jin dadin mulkinshi gami da Adalcin A tsakanin talaka da mai kudi babu Wanda ya ware a ciki kowa nashi ne ,



Gurin ya karade da hayaniya can jama'ar dake gurin suka fara jiyo wata Murya cikin Lasifiqa Ana cewa jama'a Ku dakata Ku nutsu kafin fitowar mai martaba sarki mai Adalci yanzu Yarima Mai jiran gado zai fito tare da ta wagarshi Allah yaja da ran Yarima *Almansor* takawar ka Lafiya ,gaba salamin baya Salamun Dan sarki jikan sarki sarauta gadarta kukayi bata haya bace wannan tsantsan tace a jini take

Ba fade sai faman zabga kirari yake yi har yanzu bamuga fitowar Yarima Al'mansor ba ni kaina na qago in ga waye wannan Yarima n ,da ake tai wa kirari haka lailai sarauta ikon Allah masu Abu da Abunsu!


Bakin shi yaqi yin shiru har ila yau zabga kirari yake gami da banbadanci ga Yarima Amma shiru kakeji tamkar an shuka dosa Wanda a keyi dominshi babu Alamarsa,


Wani mugun tsaki *Balaraba* taja A fili tace Aikin banza Kawai Mtsss gaskiya wannan ma Dan rainin hankali ne kawai ya fito shine sai ya tsaya bata mana lokaci dubi fa time tafada tana kallon Agogon dake daure a hannuta gami da kallon kawarta Bushira wacce suke zaune a tare A wata katuwar rumfa cikin "yan Uwansu dalibai da'Alama Saukar Alk'urani Sukayi ganin tarin Alluna gami da kyauttuka a zube a gurin,gefen maza daban na mata daban hakanan gurin zaman malamai daban ,gurin zaman iyayen yara daban gurin zaman manyan baki daban ,sai wani guri keban tacce Wanda a ka tanadar wa da mai martaba domin zama shida Mai jiran gado Wato yarima gurin yasha shinfidu iri iri na Alfarma ga wasu bayi biyu a tsaye a bayan kujerun hannuwansu riqe da wasu tafka tafkan mafitai suna fiffita tun kafin Masu sarautar su zauna a gurin,


Bashira tace wallahi kuwa dama naji rade radin cewa ae mugun girman kai ne dashi Yariman shiyasa ban so Malam Idiris ya kawo saukar fadar sarkin ba yafi kawai dacewa sarkin yaro makaranta mu karbi Allunan mu sabida kin San sha'ani da masu sarauta a kwai matsala ,


Tsaki Balaraba tayi a karo na biyu cikin gadara tace wallahi Dan kar in tashi in yi tafiya ta Abin ya zama laifi gurin Malamai dama mutum yayi kaurin suna komai sai ace kai ,da tafiya ta zanyi babu wani banzan da zan tsaya batawa kaina lokaci a kanshi sauka ce dai nayi nasan nayi ae ba lailai bane sai na karbi Allon ba,


Ke Balaraba! Bushira tafada cikin mamaki tace kardai maimar taba kike zagi kin San dai nan ba gurin gadara ba ne gami da girman kai Dan haka ki iya bakinki,wallahi ,kasa kasa Balaraba ta karashe zancan tana waiwayawa bayanta domin dogarawa ne ke waye dasu ko wanne riqe da gora Kansu yasha tafka tafkan rawani idonsu ranbade da kwalli sai zarewa sukeyi


Babu wani tsoro ko kadan a Furucin ta tace ke rabu dani Dan Allah shikkenan sai in zauna a kan wani ina batawa kaina lokaci sanin kanki ne fa su Sadiya suna can na jira na kin san basu da kowa sai ni nasan suna can a takure ,shikkenan sai in zauna wani ya bata min lokaci,nifa ba da sarki nake ba,ke kin San da Wanda nake yi tafada tana wani ciccije baki!


Bushira tace wallahi balaraba ki rage wannan zafin kan naki sai ki riqa Abu cikin gadara tamkar wata "yar wani ki yi tunanin nan fa gidan masu mulki kika shigo wallahi ni dai babu ruwana to!!


Mtsss ke nifa wallahi babu Wanda zan ji tsoro uwata da ubana kawai zan ji tsoro sai Allah da Annabi Amma babu wani mahalokin da ya isa yana kashi ina kashi in ji tsoro ni babu ruwana da wani sarautarsa,



Shiru Bushira tayi ganin Balaraba tana faman daga murya dama dama tayi kaurin suna a makarantar ,bata karacewa mata komai ba,



Can suka kara jin busa gami da sarewa wannan bafaden dake tsaye bakin katowar kofar da Mai martaba za fito yayi saurin zubewa a gurin kanshi a qasa gami da dunqule hannunshi Alamar jinjina, cikin banba danci yace Allah yaja da ran Yarima *Almansur* sarki mai farin baya baka fito ba sai da ka shirya mai takalmin karfe wannan haka yake sarautar ma suna taci in kana guri ,Dan gidan Fulani Dan gidan zainaba Dan gidan Fadim......



Tsitt! Bafaden yayi sakamakon da katar dashi da Wanda a keyiwa banbadanci yayi,


Nayi ta kokarin in ga fuskar sa Amma ina nakasa gani sakamakon tarin jama'ar da ta take masa baya da yawa daga cikinsu Abokannanshi ne sai "yan uwanshi da kyar da jibin goshi na hango bayanshi sakamakon sunkuyawa da bafaden dake take masa baya yayi domin tattare masa rigar da yake sanye da ita domin samun damar zama cikin kujerar Alfarmar da a katanadar dominshi.



Wannan bafade da yake ta zuba kirari yakara dawo wa kusa dashi fadi yake tuba nake yi *Jimina* A gafarci na Tuba!!



Wani Abokinshi mai suna Shahid ya kalle shi yace kaje ya yafe maka Amma ka kiyaye gaba kasan sarai ba ya son wannan Abinda kake yi masa saunawa naji yana hanaka"



Sunkuyawa yayi yace tuba nake ranka yadade bazan karaba ,In sha Allahu,


Daga Kai shahid yayi yayi masa Alama da ya tafi,



Tunda ga can nesa balaraba take ta faman daga kai domin hango Dan mulki sunan da tasa masa kenan ,Amma ta Gaza ganinshi, takasa daurewa sai tamike tsaye cikin wayancewa tana gyara daurin zaninta gami da gyara zaman hijab dinta,



Da kyar ta hango shi ba sosai ba sabida yadda fadawa suka kewayeshi kuma da a kwai taxara mai yawa a tsakaninsu da inda take zaune,



Idan ba'idonta ne yake mata gizo ba sai taga Yariman da a ke tawani zuzutashi yaro kankani, tabbas ko ita ta girmi wancan yaron tafada cikin zuciyarta gami da komawa ta zauna tana tabe baki,





~*BINTA UMAR ABBALE*~




_MARUBUCIYAR_

_*NANA KHADIJA*_

_*YARO DA KUDI*_

_*GIMBIYA BALARABA*_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

😘





*_Acigabah da gashi_*✍🏻
[04/05, 02:50] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€



*✍🏻Writting by*

~*[Binta Umar*]~
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~


~*MRS AHAMAD GWADABE*~😘



_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE DARI BIYU KACAL IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_
08089965176



*πŸ…Ώ2*


Ko min ti biyar bai yi da zama a gurin ba mai martaba sarki Almustaph yafito tare da mutananshi ,nan da nan guri ya nutsu ,fadawa ne a bayanshi cikin Nutsuwa ya riqa ratsa mutune fuskarsa a sake yana karbar gaisuwa,


Ya na zama wani bafade ya gyara masa zaman Alkyabbaur dake jikinshi ,da sauri yaje ya zauna jikinsu na rawa gami da yin gurfene sai kace wani mai nai man gafara,


Cikin Nutsuwa mai gabatarwa ya mike ,yayi gyaran murya cikin lasifiqa yace Masha Allah ,Alhamdullhi yanzu zamu fara gudanar da wannan taron sakamakon fitowar mai martaba Allah yaja da ranka ya kara maka lafiya gami da Adalci,



To Masha yanzu zamu saurari jawabin sarki mai Adalchi kafin jawabin Manyan baki da malamai da iyayen yara"



Cikin kamala da dattako mai martaba ya mike tsaye ,wani bafade ya karoso gurin hannunshi riqe da wata zungureriyar lasika ya sai ta ta daidai bakin sa ,


Sarki ya bude taro da Addu'a cikin Lafazin sa mai kyau da lumana yayiwa dalibai nasiha da iyayen su sabida jajircewarsu gurin ganin "yayansu sun samu ilimi in gan tacce.


Kana ya kuma ya zauna ,gurin zamanshi cikin nutsuwa da qasaita irin ta sarautar da ta Amsa sunanta,


Da dai dai da dai dai malamai da masu jawabi gami da iyayen yara kowa yayi nasa jawabin sannan mai gabatarwa yayi gyaran Murya yace "yanzu zamu kira daya daga cikin dalibanmu masu hazaqa zata yi mana karatu kafin mai martaba ya mikewa ko wanne Allonshi muna wa kowa fatan Alkairi gami da ko mawa gida lafiya"



Muna bukatar
*BALARABA AYUBA TANKO*
Tafito nan ,mai gabatarwa yafada cikin lasifiqar,



Hankalin kowa ya koma kan taron Matan dake zaune can cikin wata katuwar Runfa a ke 6ance a gurin,



Shiru Balaraba tayi gabanta yana faduwa domin Sam bata taba tsammanin ita ce zatayi karatu ba,

Gaskiya duk rashin kunyarta tana jin nauyin ratsa dubban mazan dake zaune a gurin ,gani take ma baza ta iya karatun ba domin ita kam ta tsani kallo wallahi,


Bushira ce take zungurinta ,tana jinta tayi mata banza,


Mai gabatarwa yakara maimaita Balaraba Ayuba tanko ta fito ,mana"



Shiru taqi fitowa,


Dago kansa yayi cikin ginshira yana bin ilahirin jama'ar dake gurin da kallo cikin izza ,ya dinga karade tarin "yan matan da Kallo so yake yaga ta inda wannan yarinyar zata fito ,wacce tun dazu a ke shalar tafito tayi kunnen Uwar shegu da jama'a,



*Wai ina BALARABA AYUBA TANKO TAKE NE*?

mai gabatarwa yaqara mai maitawa A Dan Fusace,



Ko gama rufe bakin sa bai yi ba ta mike tsaye tana gyara zaman hijab din ta sosai ,kana ta gyara zaman glass din dake fuskarta ,tafara ratsa Jama'a domin zuwa gurin da 'a tanadar domin ita din



Tun da tafito cikin jama'a sosai hankalin mutane ya koma kanta, banda Almansor ,domin kallo da yayi mata ya kauda kai yana Jan tsaki,



Taje ta tsaya gami da gyara lasifiqar sosai ,tayi gyaran murya cikin Nutsuwa ,tafara kwararo karatun Al'kurani mai girma tamkar wata balarabiyar kasar Saudiya yadda take fitar da harafi dallah dallah take bawa kowa nashi hakkin ga wata murya mai dadin sauraro gami da kashe jiki





*BINTA UMAR ABBALE*😘



_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š




*✍🏻,,,,,,,,*
[04/05, 02:50] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€
*🐾GIMBIYABALARABA*🐾
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€



*✍🏻WRITTEN BY*
*Binta Umar*
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~


~*MRS AHAMAD GWADABE*~😍



_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_
08089965176



*πŸ…Ώ3*



Shiru gurin ya dauka jikin duk Wanda yake gurin ya Mace sakamakon karatun Al'kur'ani mai girma da yake ratsa gurin.


Sai da ta karanta Ayoyi goma na farkon Suratul bakara ,kana tarufe da Addua'a cikin Nutsuwa a je lasifiqar Hannuta ,a ma'ajiyarta tafara kokarin barin gurin


Ida nun mutane sukai caaaa! A kanta Sai tafiyarta tafara hardewa tamkar zata fadi.



Cikin isa Ya dago kanshi dalilin Da yasa Abokinshi Shahid ya takura masa da Magana kasa kasa wai lallai sai ya kalli ita wannan mai karatun



Yana ya mutse Fuska gami da Limshe ido yabi bayanta da kallo domin baiyi nasarar ganin Fuskarta ba ,Wata irin ingarmar Mace ya hango game tsawo ga qiba dai dai Misali ga wani Uban Sharp Wanda sai da yafito ta cikin hijab din a nagani ,Sakamakon yadda Allah ya wadata ta dasu ,kafarta ya kalla cikin bakin takalmi Fara Tass tass da'ita ,Da'a lama jikin ma haka take


Ajiyar zuciya ya sauke yayi saurin dauke idonsa daga kanta,jin zuciyarsa tana darsa masa wani Abu,A rayuwarshi yana son farar Mace kasan cewarshi Mai dun fata .Sai tarin kyau Wanda Allah yayi masa


Shiyasa yake son Farar Mace inji hausawa Alkyabbar Mata,




Shahid ya zungure shi kadan yace"yaya ka ganta Yarinyar tayi fa wallahi irin kallar ka gata zata dace da Sarauta dubi zubin tsarin jikinta dagani A kwai qasaita"




Gyaran Murya yayi kadan "yace "yar wane sarki ce ? Waye Babanta a garin nan ? Da kake hada ni da'ita haka kawai daganin Sarkin Fawa sai Miya tayi zaqi!
Yafada Cikin izgili gami da qasaita Wanda hakan yazame masa jiki,

Shiru Shahid yayi sabida yasan halin Abokinshi Dan daukar zafi ne yace"yanzu dai mubar maganar sai muntashi daga nan"


Ta6e baki Sarki! Yayi dake haka yanwancin suke kiransa dashi Sabida isa da takamar da yake da'ita wacce shi kanshi sarki Almustapa baya yi a Matsayinshi na sarkin ,shi da kanshi yake kiran Almansor din da Sarki zamu'iya cewa shine ma yasa masa sunan Sabida yadda yakeyi din tun yana yaro. To shine fa Abokanshi suke kiranshi da sunanan ,cikin gida kuwa da yarima suke kiranshi.



Mai gabatarwa yakara fitowa a karo na biyu ,bayan Maryam taje ta zauna Cikin nutsuwa yace'Alhmdullhi mun saurari karatu daga bakin Dalibar mu Maryam Ayuba tanko dalibar datayi fice tayi zarra cikin Makaranta sabida hazaqarta da tsaftarta biyyarta Nutsuwarta Tabbas Muna Alfahari da ita Kuma munai mata fatan Alkairi gami da samun miji nagari.


Yanzu batare da bata Lokaci ba Mai martaba sarki Mai adalci Uban talakawa Mai tausayin Al'umma ,zai fito ya rarrabawa ko wanne Alonshi gami da sauran kyautittikan da muka tanada ga dalibanmu da Suka Sauke Al'kurani mai girma kimanin Mutum Dari Uku da sha bakwai Muna fatan wata shekarar dalibai na kasa zasu bada himma da jajijrcewa Musamu ninkin waddanda muka yaye Allah yakarawa Mai Martaba Lafiya da Imani,yafada gami da aje lasifiqar ya bar gurin a nutse .


Gurin yayi tsitt! Mai Martaba yayi gyaran Murya Cikin Abin Maganar ,Wanda yana zaune gurin zamanshi wani bafade yake riqe dashi,


Ya dauki Allon Farko

Sunan *BALARABA AYUBA TANKO* yagani jiki yace'Alhmdullhi.



*Balaraba Ayuba tanko*


Wannan karon ba tayi nawar fitowa ba ta mike tafara ratsa jama'a a karo na biyu Cikin qasaitarta da yanayin tafiyarta ta durfafin inda Mai martaba yake zaune


Idon Mutane yayi caaaa! A kanta kamar dazu ,tsaki taja a ranta tace wallahi na tsani kallo ko kadan"



Ta kasan idonshi yake kare mata kallo har tazo ta durqusa kusa da Mai martaba gami da gaidashi Cikin Nutsuwa,


Yayi saurin dauke idonshi daga kanta ganin ta dago kai ba yaso taga yana kallonta duk da cewar ta kasan idonshi ne idan ba mai kurrala ba ma babu Wanda zai fahimci ita yake kallo ciki ko harda ita balaraba n.




*BINTA UMAR ABBALE*



_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
*✍🏻,,,,,,,,,*
[04/05, 02:51] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€



*✍🏻Writting by*
~*Binta Umar*~

~*MAMAN ABDUL WAHABU*~


~*MRS AHAMAD GWADABE*~



_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_
08089965176



*πŸ…Ώ4*



Mai martaba ya Maka mata Alo gami da kyautitikan ta na musamman ,Masu photo da video sai aikinsu suke a gurin.


Sannan ta mike hannuta riqe da Allon Fuskarta cike da Walwala,Mai martaba ya kara lasifiqa a bakinshi yace" Ma haifin wannan Yarinya mai Albarka yafito a kwai kyauta ta musamman da na tanadar domin ku iyayen yara"


Raurau rau idanunin Balaraba yayi jin Furucin Maimartaba sai ta fara kokarin mayar da kwallar da tataro a kwarmin idonta domin bata son zubowarta anan.

Tana tsaye masu hotona da Video sai daukarta a keyi.


Mai gabatarwa ya Mike yaje yatari lasiqa yace"Allah yaja da ran sarki mai Adalci wannan yarinyar marainiyace Ubanta ya rasu shekuru goma da suka wuce ita kanta batayi wayo ba Mahaifiyarta ma haka yanzu shekarunta uku da rasuwa sai ita da qqnnenta Guda biyu"



Mai martaba yayi gyaran Murya cike da tausayin Balaraba"yace Allah ya jikansu da Rahama to yanzu muna bukatar waliyyinta yafito domin ya karbar mata Abinda muka tanadar mata"




Diri Diri Maigabatarwa yayi yana waige wai ko zaiga Sallau ,Amma ko Alamarsa bai gani ba cikin mutuwar jiki yakara tarar Lasifiqa yace Allah shi taimaki sarki sarakuna ae wakilin nata bai samu damar halartar taron ba"




Girgiza kai Maimarta yayi yana Nazarin wani Abu kana yagara Murya A nutse yace"ina bukatar *Sarki!! Yarima Almansor yafito na wakiltashi ga wannan yarinyar mai tarin Albarka*



Yana zaune a hakimce yaji wannan Furucin na Maimartaba sai yaji faduwar gaba kadan Amma kwata kwata Fuskarshi bata nuna ba ,shifa ba kowane kare da doki yake so Maimartaba ya riqa Alaqantashi dashi ba yanzu fisabillahi inashi ina jera kafada da kafada da wancan "yar gidan fukara'u wacce ba'asan Matsayin taba.


A nutse ya mike cike da qasai ta gami da izza kamar yadda ya zame masa jiki ya karasa kusa da da maimartaba gami da mika gaisuwa domin yana mutukar girmama Mahaifin nashi sosai da sosai baya son bacin ranshi ko kadan shine yasa ma duk Abinda maimarta ba yace baya musawa ko dako Abin baiyi masa ba,



Cikin nutsuwa Mai Martaba ya mike tsaye wani bafade biye dashi a bayanshi riqe da tarin mukulai da wasu takkadu cikin Ambulan,


Maimartaba ya karbi Mukuuli guda biyu ya mika Sarki!! daya na gida ne da yake ginasu can bayan gari sabida irin haka daya kuma na wani katafaran shago ne cikin wata kasuwa datayi shura cikin jahar tasu nan ma ya mika mata a karo na biyu ko wanne da takkadunshi na mallaka hade da sa hannun shi maimartaba.



A nutse Sarki! Ya karba gami da karasawa in da take tsaye gabanta na dukan Uku Uku,



Da sauri wani bafade ya karaso gurin ya kara lasifiqa bakin Sarki! Domin yasan zaiyi magana dole.



Gyaran Murya yayi yana duba takkadar farko,


Ya Mika mata Cikin Wani irin Voice yace Maimartaba Sarki Almustapah ya Mallakawa Balaraba Ayuba tanko daya daga cikin gidajensa na bayan gari halak malak sakamakon kokarinta da tayi gurin saukar Alku'ani maigirma Allah yaja da ran sarki Yakara maka Lafiya Balaraba na godiya,yafada yana Dan ya mutse fuskarsa kadan gami da mika Mata takkadun ,Akwain guri ya dauki kabbara gami da kirari ga sarki Almustaph Masu photo da vidio suka fara Aikinsu ,duk wani Masoyin Balaraba a gurin ya tayata murna makiyanta kuwa tamkar su mutu.
Sallau wanda ke can rabe jikin katanga ji yake kamar yaje ya cinnawa kanshi wuta ya huta da wannan bakin ciki



Ta sanya hannu biyu ta karba fuskarta cike da walwala Amma taki yadda ko kadan ta kalli Fuskarsa haka masu photo suka riqa daukarsu.



Kamar yadda ya mika mata takkadar farko haka ya mika mata tabiyu hade da Dan mukkulin shagon da yin bayani domin kowa ya shaida

Zubewa Sallau yayi gumi ya tsinke masa yana mamakin yanzu Balaraba ce ta mallaki shago cikin kasuwar sha tambaya Wanda shiga wannan kasuwar sai wane da wane domin kasuwa ce ta masu kudi ,nuffashin sa ya riqa fita sama sama tamkar zai bar gangar jikinshi tsabar bakin ciki ae bai gama dawowa daga dimuwar da ya shiga ba yajiyo muryar Sarki!! Yace "Ni Almansor Almustapah na baiwa Balaraba Ayuba tanko kujarar Maka sakamakon hazakarta da kokarin ta muna fatan sauran dalibai zasu kara zage damtse gurin jajircewa da bada himma a kan karatu muna fatan wata shekarar daliban dazasu sauke Alku'ani mai girma su ninka na yanzu.

Yana gama fadar haka ya Fara kokarin barin gurin cikin ginshera wacce tazame masa jiki cikin kasaita yaje ya zauna gurin zamanshi yana kallon kowa daidai.

Gefe guda yana mamakin yarinyar da Girman kanta ganin ko kallon in da yake taqiyi ko dame take taqama oho!




*BINTA UMAR ABBALE*


_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šβœπŸ»
[04/05, 02:51] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€




*✍🏻writteng by*
*Binta Umar*
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~


~*MRS AHAMAD GWADABE*~



_WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU_
08089965176



*πŸ…Ώ5*



Daya bayan daya dalibai suka riqa fitowa suna karbar Allonsu hannun maimartaba kamar yadda yayiwa Balaraba kyauta haka ya riqa yiwa kowa daidai da Matsayinshi.



Sulaiman Ahamad shine yasamu kyauta kwatankwacin ta Balaraba nan shima Sarki! Almansor ya bashi kyautar kujerar maka kamar yadda yabawa Balaraba,



Guri ya hautsine kowa yana taya nashi murna gami da karbar Allon ana sanya Albarka ,nan kaf dalibain da malamai gami da iyayen yara suka jero reras gaban sarki masu photo suka riqa daukarsu domin tarihi .


Sarki ya jiro wasu takkadu ya mikwa shugaban Makarantar wato Arrama Malam Idiris yace" ni Almustaph na malakawa wannan Makaranta Filina dake hayin diga halak malak kuma Na dauki nauyin ginashi da izinin Allah muna fatan zaku kara zage damtse gurin kula da tarbiyar yara da basu ilimi mai amfani.



Allahu Akubar Allahu Akubar Allahu Akubar


Guri ya hautsine da Akabbar Malam idirs ya zube gaban sarki tamkar zaifashe da kuka sabida dadi sai zanba godiya yakeyi




Kankace komai guri ya karade da busa irin ta gidan sarauta mai taken jinjina game sarki.




Sarki Almustaph ya mike da Alama gida Ai shiga Aikuwa fadawa suka baza manyan riguna domin take masa baya.



Dama A Al'ada sai sarki ya tashi sannan kowa yake tashi sabida girmamawa,



Mikewa Sarki!! Yayi tare da tawagarshi domin bin bayan Mahaifinshi ,wan an Dan kanzagin bafaden ya soma Aikinshi na banbadanci har ya Manta da gargadinsa na dazu

Busar da ake masa daban take da wacce a kewa maimartaba domin kanaji tasa yadda take tafiya slow tana tafiya da Yanayinshi na taqama!!

Gyara kintsi Dan sarki jikan sarki nan gani nan bari dawisu sarkin Ado dawinsun ma dole ya saurara Maka Farar Aniya Farar zuciya Farar Alkyabba Dan gado masu sarautar gaskiya arziqinku bai rufe muku ido ba Allah dai ja da kwana Dan sarki jikan sarki!

Tuni guri ya kacame Kiowa yanaso yayi ido hudu da wannan Dan sarki da'aketa wasa shi haka Mussaman Matan dake gurin da masu saukar da "yan kallo.


Balaraba na gefe duk tururrubin da'ake gurin gami da hayaniyar baisa ta zuwa gurin da yake kokarin wucewa ba sai zabga tsaki takeyi yana kallon bushira sai faman kutsawa take wai lallai sai ta ganshi.


Gefe can taja ta tsaya domin yadda a ke bangajeta gashi Sam Sam bata son hayaniya da jira da tana da damar tafiya da tayi tafiyarta wallahi domin kwata kwata bata son batawa kanta lokaci sanin da tayi cewar kannanta nacan na jiranta a gida,

To ganin yadda makarantar ta karramata a matsayinta na daliba ta farko yasa bataso ta watsa musu kasa a ido


Duk a zaton ta Sulaiman Ahamad shine na farko ganin yadda yake da kokari domin ko musa bakace shine yake cinyewa Amma Abin Mamaki sai taji sunanta a farko ,Tabbas ta yadda da kanta tunda Ita kanta tasan tana da masifar kokari domin wani sa'in itakewa "yan ajinsu kari idan malami bai shigo ba ita dai

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment