Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fad'a ba wai yana kishi bane kawai tsabar kauyancin da sukeyi shine yake bashi haushi.....Bai iya ce masa komai ba ya kalleta tana tsaye sai tauna gefan dankwalinta take yace."Dauki kayan tallan ki wuce gida."! Shiru tayi tana kallonsa tare sa zu'baro baki.

Kwata kwata baya son dukanta shiyasa ma kafin ya isa gurin ya saisaita tunaninsa domun a yanda zuciyarsa ke masa zafi da yarinyar yana gani zai iya yi mata mugun rauni saboda duka shiyasa taushi zuciyarsa akanta bayan haka kuma yanajin tausayinta saboda maraicinta gaba da baya.


Talle yayi wani 'kas! da hannu irin na gayu na 'kauye yayi wani juyi da kafafunsa da suke sanye da wani fatattakaken kambos yace."Baby sai gobe zamu had'e naga wannan gayen shima kamar yana sonki to karki damu da komai baby tunda ni kike so nima ina sonki."

Talle Ya fad'i wannan maganar ne domin ya cuzgunawa Sadam!! saboda a tunaninsa son Sayyadar yakeyi......Sadam! kam kallo ya bishi dashi cike da tsabar takaici ya ma rasa bakin magana ya dawo da kansa kanta "Dauki kayan tallan muje gida."

"To ai gyadar bata 'kare b......." Wani bahagon mari ya kai mata! Allah yasa bai same ta ba don da ta sake marin nan ya same ta to sai tayi jini da majina! da sauri ta dauki farantin gyadar ta kama hanya tana waiwayen sa.

Ya biyo bayanta cikin yanayi tafiyarsu ta sojoji.


"Allah ya isa ban yafe ba mugu azzalimi d'an iska." ! Ire iren surutan da takeyi kenan tana waiwayensa Sadam! na gani tana motsa bakinta amma baya jin abinda take cewa saboda kasa kasa take maganar.

Tana shiga kofar ta sa kuka a guje ta shiga ciki tana fad'in "Allah ya isa."!! Baba Ladidi! Kinga Ya Sadam! ya koroni ya hanani na siyar miki da gyadar ki kuma sai cini ki akeyi ya kori mutane."

Baba Ladidi dake kishingid'e kan tabarma ta mike zaune tana gyara daurin dankwalinta tana kokarin magana ya shigo gidan.


Kai tsaye inda suke zaune ya nufa ba tare da ya zauna ba yace."Baba ashe dama tallah kike d'orawa Sayyada yanzu don Allah me kika nema kika rasa da zaki dinga dora mata tallanta gyada da daddare tana shiga tsakiyar maza ke kin san sayyada ba nutsuwa ce da ita ba kike dora mata tallah."


Tace."Haka kawai sai na zauna 'kuda yabi bakina ba zan nemi na kaina ba kenan? meye laifi don na dora mata tallah ai ko babu komai kudin cinikin yana toshe mana wata kafar saboda haka daukar tallah yanzu Sayyada ta fara idan kaga ta daina to tana dakin mijinta."

Yace."A haka kike cewa in aureta kenan."!? Tace"Kwarai kuwa wai me kuke nufi ne? duk wanda zai ga Sayyada na zama gindi bishiya tana saida gyada sai ya fassara da wata manufar ni nasan halin sayyada baza ta aikata abinda kuke nufi ba ku kyale mu kawai mu nemi na kanmu."


Cike da tsabar takaici yace."Babu rashin ci babu rashin sha babu rashin gurin kwanciya kike wata maganar, A gaskiya to kan wannan al'amari muna iya 'batawa dake domin wannan ba tarbiya bace da daddare kawai ki kasa mata tallah ta shiga cikin maza ke kina kwance a gida ba fata nake ba idan wata matsalar ta faru me zaki ce mana saboda haka kome zakiyi daga yau Sayyada ta daina daukar tallah."


Baba tace"Sayyada ba zata daina daukar min tallah ba sai dai idan aure nayi mata wai ina ruwanku ne? kai kake wata magana idan kaji haushi yau ka turo sadakin auranta sai a daura muku aure ka dauke kayar ka amma matukar muna tare da ita baza ta daina tallah ba."


Yace."Ai ni na gama magana ba zan aureta ba kuma tallah sai ta bari domin yanzu idan na fitar daga wannan kofar zan nufi gurin Sarkin 'kofa in shigar da 'korafina akanki."


Ai sai Baba tasa kuka tana fad'in"Ni za ka kai 'kara gurin Sarkin 'kofa saboda baka da mutunci."

Yace."To kece ai kin'ki ki zauna ki fahimci mutane kawai kina bin son zuciyarki."


Tace."To naji zauna sai mu fahimci juna."

Ya samu gefanta ya zauna tace"Maganar dai ta kare idan kana so sayyada ta daina tallah to ka yarda a daura muku aure kafin ka koma amma kar ka sake ka kai maganar gurin Sarkin 'kofa to kaji."!

Yace."Shikkenan zanyi tunani kan maganar ki amma don Allah ko bayan na tafi karki 'kara dora mata tallah." tace"Haba ai magana ta 'kare bari na kawo maka abinci."

Yace."Bari dai naje can kofar Kawu Tanko naci a can."

"To babu laifi ai duk d'aya ne."

Yana fita Sayyada tace"Baba yanzu da gaske kike kin daina soya gyada kuma na daina daukar tallah? kinga fa yau dari da ashirin nayi sannan Talle ya bar min sanjin talatin d'insa kinga d'ari da hamsin kenan."

Baba ta kar'bi kudin tana lissafawa tace"Rabu dashi zai tafi ai sai mu cigaba da abinmu a kan wane dalili zasu hanani neman kudi."

Sayyada tace"Nima dai abinda na gani kenan." Mikewa tayi taje ta zubo abinci ta zauna tana ci tana tunanin abinda ya faru tsakaninta dashi da safe duk sanda ta tuno da lokacin da ya dora hannunsa a kan nononta sai tsigar jikinta ta tashi wanda tunda suka fara fitowa bata taba jin wani yanayi a jikinta ba sai a wannan karon da sukayi ita dashi.

****

Washe gari da safe dake tana riga kowa tashi a gidan Baba Ladi da Baba Marka na cikin dakin suna bacci ta share gidan ta had'e kwanuka ta wanke ta nufi bandaki domin ta wanke tana tura kofar bandakin lokacin shi kuma yana daure igiyar wandonshi karf suka had'a ido a razane! ta sauke idonta 'kasa ta saki kofar jiki na 'bari ta bar gurin....."Wayyo Allah wannan meye a mararshi kamar gashin jinjiri a kwance bakikirin a jiki dama haka jikin maza yake da gashi to me ya kawo gashi a marar sa.

Jiki a sanyaye taje bayan Baba Ladi ta kwanta ta rintse ido tsigar jikinta sai tashi takeyi.


Sadam! kam yaji takaicin ganin da tayi masa yana daure tazuge wato Allah ne ma yaso shi ya riga ya gama uzirinsa da yarinyar nan ta cuce shi.......Ya fito ya dauki brush dinsa inda ya aje ya goge bakinsa tsaf ya koma masaukinsa cike da takaicin yarinyar.







27/5/2020




*BINTA UMAR ABBALE*
[6/12, 12:15 PM] Bintu: *NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*

*BINTA UMAR ABBALE🍒*




*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION🖊📚*
*M W.A*



_'Kungiya d'aya tamkar da dubu masu Nazari da aiki da Iliminsu, burin 'kungiyar a ko da yaushe ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyansu_
_________________________ _____________






*_Littafin Ni da Yaya Sadam! na kud'i ne 1 _ 2 ga mai bukatar karanta littafin zai tura #400 kacal ta wannan accont d'in.......0542382124......Binta Umar Gtbank.....Idan kuma katin waya zaka tura to sai ka tuntu'beni ta wannan numbars din nawa zan fad'i yanda zaka/ki biya kudin......08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar karanta wannan littafi to zaku tura katin airtal ko orange na dala dari a wannan numbars......90899076 _88137740.....Dala d'ari itace a madadin d'ari uku kud'in Najeria_*




Free Pege 3




Amina na hangoshi ta nutsu cikin nutsuwa take tafiya har suka had'u ta saki fuska sosai tace"Ya Sadam! ashe kazo sannu da hanya yasu Kawu da Yaya Sule dasu Muniba."?

Yace."Kowa lafiyar sa lau Amina dafatan na same ku lafiya."?

''lafiya kalau wallahi."Tafad'a tana sinne kai. tsai yayi yana kallonta ya lura yarinyar na jin kunyarsa ya rasa kuma meye dalili hankalinta da nutsuwarta yana mugun burgeshi ba kamar waccan mahaukaciyar ba Sayyada.

Yace."Ina fata dai kina zuwa makaranta."?

Tace"Eh ina zuwa a boko ma nice nazo ta d'aya Isilamiyya kuwa sai da aka bani kyauta saboda na haddace izifi biyar da ka."


A take ya saki fuskarsa sosai tamkar gonar audiga yace."Babu shakka nima ta 'bangarena dole in miki kyauta Aminatu kin burgeni gaskiya da zan koma kaduna yau amma saboda ke zan zauna inyi kwana biyu ina so in saurari karatunki idan anjima da daddare."


Amina tayi murmushi tace"To shikkenan Yaya Sadam!.

Yace."Bari in shiga mu gaisa da mutan gida ko."

Tace."To." Ya wuce ya barta tsaye a gurin Amina bata dauke kanta daga kansa ba har sai da taga ya shige kofar su sannan ta wuce ta tafi.



"Wai Sayyada wannan kukan da kikeyi na menene."!? Baba Ladi ce tsaye kan Sayyada wacce ke zaune a dokin 'kofa tana kuka harda majina.


Baba tace" Wai ba magana nake miki ba kinyiwa mutane shiru wallahi Sayyada ki bar ganin ina kyaleki kan abunda kikeyi min ina tara ki ne akwai ranar da zan zane ki da bulala da kaina ai banji takaicin dukan da Sadam! yayi miki haka kawai saboda tsabar rashin ji kika fasa min 'kwan fitila shekarar abina biyu amma kinyi min sanadinsa." Baba Ladi ta dage sosai tana mata fad'a irin wanda bata ta'ba yi mata irinsa ba. Sayyada ta kwanta a kasan gurin tana kuka lokacin ne kuma Amina ta shigo.


"Baba wai me akayi mata take wannan kukan."!? Amina ke tambayar Baba Ladi.

Baba Ladidi na 'kokarin kad'e tabarma tace" Oho mata ai ta saba laifi idan anyi mata fad'a tazo tana kuka."


"Nifa Baba ba haka bane ba za'a tsaya a ji ta bakina ba sai kawai ayi tayi min fad'a."!! Sayyada ke wannan maganar lokacin da take dafe 'kirjinta da hannunta.


Baba Ladi tace" Ai sai ki fad'i dalili ba ki zauna kina kuka ba."

Tace."Baba nan d'ina ne yake min ciwo."! nononta da ya murd'e take nuna mata.


Baba Ladi ta aje ta barmar ta karasa inda take kwance tace"Tashi zaune ki nuna min."

Sayyada ta mi'ke da kyar tana nuna mata brest din nata wanda yafi ciwo tace"Yaya Sadam! ne ya murd'e min."!! Baba Ladi ta buga salati tana tafa hannu tace"Kika ce Sadam ya murd'e miki nono kan wane dalili? ai wannan mugunta ce kowa ya sani idan mace ta fara 'kirgar dangi sunayi mata zafi idan ba so yake ya kashe ki ba kan wane dalili ma zai ta'ba miki jiki bayan ance ya aure ki ya'ki."!!! Baba Ladi ta shiga sirfa bala'i inda ta nufi kofar d'akinta inda mayafinta yake rataye a kofa ta nan nad'e shi ta d'ora aka sai kace wacce tayi gammo wai ita nan yafa mayafi tayi sai ta nufi hanyar fita tana d'ingisa 'kafa "Wannan ai kafirci wato yaje yayi mu'amula da turawa 'yan bana bakwai sun 'bud'e masa ido da iskanci shine yazo zai dinga latsa yaran mutane to kuwa zai ci ubansa."!


Bayan fitar ta Amina ta Kalli Sayyada dake goge hawaye tace" Wallahi Sayyada 'karya kikeyi kice Yaya Sadam! ya ta'ba miki nono wallahi kiji tsoron Allah meye abinda zai burgeshi a jikinki mutum da yake mu'amula da 'yan gayu yaje 'kasar waje yayi karatu yayi cud'anya da turawa masu kyau da ilimi shine har zaki ce ya ta'ba miki nono ni dai ban yarda ba."


"To kada Allah yasa ki yarda mana dama ai ba so nake ki yarda ba aikin banza kawai kamar yanda yake dan uwanki nima haka yake dan uwana harda zaki wani tare masa ai dake ya ta'bawa ba zakiji dad'i ba ke ko kishina ma bakya yi wallahi nasan irin zaman da zanyi dake."


Amina tace"Ai halinki na sani na sharri da shirya magana sai kiyi ta rantsewa kan abunda ba'ayi ba wallahi Sayyada kiyi hankali ki daina abunda kikeyi."


Sayyada haushi ya sanya ta soma zagin Amina kafin kice kwabo sun kaure da fad'a har da kokawa Sayyada tayiwa Amina lilis ta zaneta tace"Idan kinje kice yazo ya rama miki shi wanda kike tarewa fad'an."


Amina na kuka ta nufi 'kofar su....Ita kuwa Sayyada sai ta kama hanya ta fice daga cikin kofar gabad'aya gidajan amare ta fara bi tana musu wanke wanke da shara yayi al'kawarin ba zata dawo gidan ba sai dare sai ta tabbatar ya bar garin sannan zata dawo.



Baba Ladidi ta nufi kofar su Kawu Tanko saboda tayi ya'kinin yana can aikuwa samunsa tayi zaune kusa da Baba iyatu da Marka suna hira ga 'kwaryar fura a gabansa yana sha.


Tana shiga ta sauke mayafin dake saman kanta ta rataye kan igiya.....Tace."Kai ja'iri gurinka nazo yanzu zan tona maka asiri ehe! wato dama abunda kaje ka karanto kenan iskanci."!


Sadam! Ya aje ludayin dake hannunsa ya had'e fuskarsa sosai yasan hargitsi irin na Baba Ladidi shiyasa yaci mur yana kallonta.


Ita kuma ta kalli Marka tana numfarfashi tace"Yanzu Marka dai-dai kenan abunda Sadam! yayi iye!? Haka kawai saboda son zuciya yarinya na irgar dangi ya kama mata nono ya murd'e wannan ai iskanci ne da yahudanci yarinya kamar Sayyada me ta sani."!?


Marka da Iya suka sanya salati suna tafa hannu." Sai su mayar da hankalinsu kansa......Dake mutum ne mai mutukar 'kwarjini da iya waskewa ko alama basu fuskanci razana a tare dashi ba sai ma wani kwarjini da yayi musu wanda suke ganin kamar ba zai iya aikata wannan d'an yan aikin ba.


Baba Marka tace"Haba Ladi! Wai kin manta halin Sayyada ne? hummm! gaskiya banji dadin jin wannan maganar ba haba jama'a! ai a fad'i abunda zai faru amma wannan dai karya ce Har guda nawa Sayyadar take haba jama'a!!!!


Baba Iya tace"To nima dai abinda na gani kenan Sadam! ba zaiyi wannan al'amarin ba.


Yace."Baba Marka ku kyalesu don Allah ni nasan saboda me yasa ta fad'i haka saboda d'azu ta tisa ni a gaba wai dole sai na auri sayyadar nace bana so a kai kasuwa shine suka 'bullo da wannan zancan to ni me zanyi da wannan mahaukaciyar yarinyar 'kazamiya."


Baba Ladi ta maka masa da'kuwa tana fad'in"Ubanka ni ce nake maka 'karya ko? Wad'annan kafiran idanun naka menene ba za ka iya ba Ai ni na yarda da abinda Sayyada ta fad'a su dai da kayi musu kwarjini sai su 'karata maganar auran Sayyada kuma ni na yanke hukunci."


Murmushi yayi kawai ya sadda kai 'kasa yana me cigaba da 'kur'bar furar sa.

Baba Marka ta kalleshi a nutse tace"Haba Sadam! ashe kana so ka bamu kunya kenan."!?

Ya kalleta a nutse yace."Wace iriyar kunya kuma."? Tace."Naji kana maganar kai ba zaka auri Sayyada ba karka manta da cewar Kaine kayiwa mahaifiyarta al'kawari zaka aureta kafin rasuwarta kayi 'kokari ka cika wannan al'kawari."


Yace."Baba lokacin da nayi alkawarin zan auri yarinyar Baba Indo na cikin halin ciwo lokacin inaso taji sau'ki ta dawo cikinmu mu cigaba da rayuwa kuma a lokacin da 'kuruciya a tare dani amma ni har ga Allah ba wai na amince bane zan auri yarinyar ina me baku hakuri kuma ina mata fatan kan Allah ya bata miji nagari wanda ya fini nutsuwa da komai da komai.

Baba Ladidi ta saka kuka tana fad'in"Wallahi kai ba d'an halak bane Sadam! yanzu meye laifin Sayyada umm? yarinya san kowa 'kin wanda ya rasa yarinyar ma tafi 'karfin ka matar manyar mutane ce amma saboda muna so mu cika al'kawari muna ta binka kana mana wulakanci kar Allah yasa ka aure ta d'in." Ta dauki mayafinta dake rataye a kan igiya ta nufi hanyar fita tana share hawaye.

Amina ce ta shigo tana kuka.

Baba Marka tace"Ke kuma meye kike kuka.
Ba tace komai ba ta shige daki tana share hawaye duk sanda zasuyi fad'a da Sayyada ita take cin galaba akanta ta rasa menene dalili.


Baba Marka ta dinga rarrashin sa kan ya daure ya auri Sayyada kamar yanda yayi alkawari a can baya....Domin ya kwantar mata da hankali yace."Zai yi tunani kan al'amarin.








24/5/2020




*BINTA UMAR ABBALE*
[6/12, 12:15 PM] Bintu: *NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*


*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________
[6/12, 12:15 PM] Bintu: *NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*


*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________




Free pege 6





Baba Ladi ta daga labule dakin ta shiga da sallama a bakinta. Sayyada ta bude lumsassun idanunta ta amsa tana kokarin mikewa zaune Baba ladi ta sami guri ta zauna tana fad'in"Ki tashi kisha kunun ga kosai na siyo mana yau gurin marka babu jama'a sosai shiyasa na dawo da wuri."


Sayyada ta mike zaune tana mutsika ido Baba Ladi ta bita da kallo tace"bacci kikayi ne naga duk kin sauya lokaci kankani."

Sayyada ta sunkuyar da kanta girgiza kanta tayi ba tace komai ba.


Baba Ladi bata kawo komai cikin ranta ba tace "Idan kin karya sai ki kwanta naga alama bacci kike ji." Ita dai Sayyada ba tace komai ba kwata kwata ma bata cikin nutsuwarta tun bayan fitarsa daga dakin.



Mazubi ta samo ta d'ibar masa kosan tana nufin shiga dakin shi kuma ya fito tace"Ina zakaje kuma ga kosan na kawo maka."

A dakile yace."Zanje can sashen Kawu Tanko na karya a can."

Ya kama hanyar futa Baba Ladi ta bishi da kallo tana gyda kai har sai da ya fita daga kofar ta dauke kanta tana girgiza kai tare da fad'in"Miskili kenan."


Kofar Kawu Tanko ya nufa lokacin Kawun tuni ya tafi gona suka gaisa da Baba Iyatu Amina ta fito daga daki a nutse ta gaisheshi ya saki fuska yana amsawa tace"Yaya Sadam! jiya kace zaka duba litattafai na makaranta."

Yace."Na manta ne amma yanzu jeki dauko in duba miki."

Ta mike da sauri ta nufi daki. Baba Iya tace"Kafin ku fara karatun bari in kawo maka kunu ka karya ko ayi maka wani abincin ne."!?


Yace."Kunun ma ya isa Baba." Tace."To." a cikin mazubi mai kyau ta kawo masa kunun tsamiya sai kamshi yake gwanin sha'awa gefe guda kuma ga wainar gero cikin wata Samira taji kuli-kuli tayi kyau.

Yace."Gaskiya Baba naji dadin wannan wainar na kwana biyu rabona da inyi irin wannan karin kummalon."


Baba Iya tace"Ai dama ku mutanan birni bakwa damuwa da cima irin wannan amma tafi gina jiki da kara lafiya."

Yace."Gaskiyar Baba." Hira suke da ita har ya kammala karyawa Amina ta dauko jakar makarantar ta ya duba sosai ya yaba da kokarin ta nan ya rasa kyautar da zaiyi mata yace."Me kike so na siya miki."!?

Mirmushi tayi yace."Ki fada mana aini nayi miki alkawari zan baki kyauta."


Tace."Ni kam Yayana kome ka bani ina so." Yace."Sai kin fadi me kike so kayan kwalliya ko zani ko mayafi."!?


Girgiza kai tayi yace."okey fadi me kike so."

Hannunsa ta kalla tana nuna wata siririyar azirfar dake hannunsa sai she'ki take.

Tace"Wannan zoben nake so kabani yana bani sha'awa."

Yayi tsai! yana kallonta na minti biyu yace."Wannan azirfar tawa tana da muhimanci Amina ki za'bi wani abun bayan ita."

Sai ta girgiza kai tace"Shikkenan kawai ka barshi."


Murmushi yayi yace."Bani hannunki na sa miki."

Ta matsa gurinsa da sauri tana dariyar farin ciki Azurfar ya ciro ya kama hannunta ya fara gwadawa duk tayi mata yawa dake Amina bata da wata 'kibar arziki haka ya tsunta ma suke sirara yace."Kinga tayi miki yawa ko." Dariya tayi tace"Kasa min a wannan hannun zata shiga." Sai ya kama hannun da ta nuna masa yana gwadawa......Sayyada ta shigo dakin taga abunda suke tsayawa tana kallonsu ta 'bata rai!!! fuuuuu! ta fice daga dakin tamkar zata fashe! duk suka bita da kallo Ta'be bakinsa yayi ya cigaba da abinda yake.


Sayyada kam da kuka ta shiga kofar su Baba Ladidi na shimfida tabarma ta tsaya tana tambayarta abinda ke faruwa.

Cikin kuka tace"Baba Nifa ban gane ba kunce Yaya Sadam! ni zai aura to me yasa naga kamar yana son Amina wallahi ni bazan yarda ba sai dai ta hakura ta bar min mijina."

Baba Marka ta fito daga dakinta tana fadin"Wace magana nake ji haka."?

Baba Ladi tace"To nima dai yanzu nake jin maganar gurin Sayyada wai me ya faru ne Sayyada."!?

Tace"Yanzu na shiga kofar su naga yana sa mata zoben al'kawari a hannu kawai ya fito ya fad'i gaskiyar magana ni yake so ko Amina."!?

Baba Marka tace"To aikuwa dai wannan maganar abar dubawa ce Sayyada bari na shiga inga abinda yake faruwa babu shakka Sadam yana nema ya mai damu kananun mutane."!


Baba Marka na fita Baba Ladidi tace "Zauna muyi magana Ta zauna tana share hawaye Baba Marka tace" Sayyada yanzu idan Sadam! yace zai had'aku ya aura da 'yar uwarki ashe ba zaki zauna da ita ba ko."? Wallahi baba ba zan zauna da ita ba sai dai ya za'ba ni ko ita shikkenan."
tsakaninta da Allah take maganar.

Baba Ladidi tayi shiru tana nazarin maganar lallai akwai matsala kenan. Yanzu idan Sadam! Amina yake so za'a samu matsala daga 'bangaran Sayyada kenan al'kwarin dake tsakaninsu zai iya rugujewa tunda shi Sadam! din yana da kafewa akan magana.


Baba Marka na shiga ta tarar dasu suna hira cikin fahintar juna cikin zuciyarta tace"Babu shakka, da gaske Sayyada takeyi.

Ta zauna kan kujera 'yar tsuguno tace"Kai Sadam! fito nan zamuyi magana."

Yace."Yanzu dama zan fito ina so in le'ka cikin gari gurin 'yan uwa za muje tare da Amina."

Tace"To babu laifi ai ke Amina kema zonan."

Suka fito tare tsugunawa yayi a gefanta amina kuma ta zauna kan tabarma.

Baba Marka tace"Ina so ku fad'a min abunda yake tsakaninku bana son munafurci kai Sadam! duk kaine me laifi."

Yace."Baba ban fahimci maganar ki ba."!?

Tace"Sayyada taje mana da wata magana shin da gaske ne kasawa Amina zoben al'kawari kana so ka aureta ne ko yaya."!?

A take yayi kicin-kicin da fuska yace."Wannan wace iriyar magana ce Baba."!?

Tace"Magana ce me mahimanci shin tsakanin Amina da Sayyada wa kake so kana kokarin kayi mana wasa da hankali."

Kai tsaye yace."Cikin su babu wacce nake so."!

Baba Marka ta bud'e baki tana kallonsa cike da mamaki tace"To wannan zoben da kasa mata fa na menene."!?

Yace."Kawai nayi ra'ayi ne ba na komai bane Sayyada da Amina babu wacce nake jin zan aura a cikinsu duk na daukesu a matsayin 'yan uwana ne.

Baba Marka tace"Aikuwa baka isa ba sai ka auri daya daga cikinsu."

Miskilin murmushi yayi ya mike yana kallon agogon dake daure a hannunsa yace."Baba naga alama zan daina shigowa garin nan mutukar zaku cigaba da damuna kan wannan maganar wai shin ni kadai ne namiji a wannan family din gasunan da yawa amma sai kuyi ta takura min da wata magana! Ke Amina tashi dauko gyalanki mu tafi ni duk garin ma ya fice min daga rai."! Yafada yana zura takalminsa.

Baba Marka tace"Ai komai zakayi sai dai kayi kana maganar ga Samari nan a famly ko wanne yana da matarsa a hannu kai kadai ne kayi shaura bakayi aure ba sai kace kuma mu zuba maka ido to baka isa ba to kaji."!

Yace."Sai kuyi ai." ! hanyar fita ya nufa Amina ta bi bayansa tana sanye da hijab har kasa takaici duk ya isheta da jin maganar sa inda yake cewa baya sonsu ita da Sayyada.


Sayyada na zaune a bakin kofar su suka fito tana ganinsu ta 'bata rai!! ko kallonta baiyi ba ya nufi babbar 'kofar da zata sada mutum da kofar gidan.....Amina tabi bayansa cikin sanyin Jiki.

Cike da takaici da bakin ciki ta bar gurin kan gadon karfen Baba Ladidi ta kwanta ta dinga kukan bakin ciki tana bala'in son Yaya Sadam! shiyasa bata son kowa ya ra'be shi ta lura kuma shi ya tsaneta kamar yafi son Amina akanta.


****

Sai Yamma li'kis! suka dawo gida Sadam? sam bai shiga ciki ba sai yayi zamansa a majalisar Samarin garin inda ya saba zama idan ya shigo garin sai kusan tara da rabi na dare ya shigo gidan......Dama yayi zuciya yace ba zai kwana bangaran su Baba Ladidi ba saboda yasan zasu takura masa sai ya nufi kofar Kawu Tanko yana sanya kafar sa ya hango Sayyada jikin kyaure('kofa) tana tauna gyalanta shi kuma saurayin yana tsaye a kanta, kamar ma zai rungume ta gabansa ya fad'i! da sauri ya dawo da baya kai tsaye ya nufi inda suke.

Yana isa yaji muryar ta tana fad'in"Nifa ba wai bana sonka bane kawai an riga anyi min miji dan uwana ne don haka kayi hakuri don Allah yanzu ma Baba Ladidi ce tace nazo na baka hakuri ka daina zuwa zance."!

Talle ya cire hular dake kansa yana fifita da ita yace."Haba baby ai al'kawari bai ce haka ba ki duba lamarin da kyau ki tausayawa masoyink......Kafin ya karasa suka ganshi a tsaye a kansu fuskarsa kamar hadarin

2 Comments On NI DA YAYA SADAM
avatar
hauwa-abdullahi

1 year ago

Reply

I love the story

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to hauwa-abdullahi

Thanks be with us for more stories

Please Login or Register in order to submit comment