Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ummi ta bata hannu suka tafa suna dariya.

Mariya tace" Wai Ummi kinji so ta take ta samu maganin da zai 'kara mata girman nono saboda tana so ya dinga cikawa angon nata hannu." Sai suka kwashe da dariya Sayyada tace"Wallahi da gaske nakeyi ni kunya nakeji duba fa ki gani nono kananu ne ko rigar nono bana sawa fa."

Ummi tace"Ke Dallah! banza kawai Wallahi ki kwantar da hankalinki nononki zai fito yayinda aka kai ki gidan miji shikkenan kullum idan yana ta'bawa shikkenan sai dai kiga suna girma sun cika riga." Sayyada ta bata hannu suka tafa tace"Da gaske kike don Allah."?
Ummi tace"Wallahi da gaske nake." Mariya tace"Hakane nima fa lokacin da aka kawo ni gidanan ba nonon arziki gareni ba amma ko wata uku banyi ba naga nonowana sunyi manya manya." Dariya sukayi suka tafa Sayyada tace"Wayyo Allah na ni wallahi har na 'kagara lokacin nan yazo wai don Allah Mariya yaya mutum yake ji idan yana sha'awar d'a namiji wayyo."!!!!!!!
Ta kare maganar tana kwanciya tare da lumshe ido.

Ummi tace"Kai! Sayyada gaskiya ke fitananniya ce anya kuwa."!?? Sayyada ta kai mata duka tana dariya tace"Ke sonsa ne kawai yayi min yawa shiyasa sai kunyi min uziri." Mariya tace"Wai yaushe zamu ganshi ne nifa ban san shi ba nafi sanin Yaya Sulaiman."! Ummi tace"Wallahi nima ban sanshi ba jikina na bani kyakkyawa ne dan gayu."

Sayyada aka lumshe ido ana murmushi mi'kewa tayi zaune tace"Sojana kenan." Suka kalleta gabadaya sukace "Au! Soja ne dama."!? Daga kai tayi tace " Eh mana ai ba zaku gane shi ba tunda ba sosai yake zuwa ba sannan kuma idan yazo baya dad'ewa yake tafiya watarana ma yini guda yake ya tafi sannan shi bashi da fara'a kamar Yaya Sulaiman kullum fuskarsa a murtuke take nima fa baya wani sakar min fuska."

Mariya tace"Ai dole mana Amina tace shi take so shegiya ni wallahi haushinta ma nakeji." Sayyada taja tsaki tare da fad'in"Rabu da tsinanniya kawai ai tuntuni na daina kulata."

Mariya tace"Kinyi min dai-dai 'kawata." Tafawa sukayi suna dariya *To ni dai fitowa nayi na barsu na lura hirar tasu ba zata 'kare ba*


*****

Sayyada sam! bata sanya Amina cikin sabgarta da kawayenta kawai take harka ko Aminar ce ta shigo kofar su Sayyada ba tayi mata kallon arziki Ballanta ta kulata Baba Ladi tayi mata fad'a har ta gaji......Wannan lamari na masifar 'batawa Amina rai! shin wai meye duniyar ne akan Namiji Sayyada duk ta tayar da hankalinta tana gaba da ita itafa bata zafafa ba duk da tana son Sadam! to idan shi baya sonta ya zatayi dole ta hakura kuma idan yace ba zai aureta ba nan ma dole ta hakura ta fito da mijin aure ita a ganinta wannan ba abun tayar da hankali bane.
To ammafa a cikin ranta tanan da wannan kudiri na duk sanda Sadam! d'in ya shigo garin zata sanar masa halin da take ciki a kansa tasan idan ya hadasu duka ya aura ai ba haramun ya aikata ba.

****

Saura Sati guda daurin aure Baba Ladi da baba Marka tsaye gaban wani katon turmi me zurfi ko wanne da ta'barya mai tsayi a hannunsa dagab tukud'i suke da gumbar mata.

Tsaf! suka daka suka kwashe sannan suka zauna zaman had'awa! lokacin Sayyada nacan gidan Mariya wai nan dilka ake da kurkur Mariya ta dage! tana wa Sayyada dilka wai lallai sai tayi kyau kafin Ranar daurin aure.

Amina ce ta shiga kofar taga abinda sukeyi tace"Baba Wannan meye?"? Baba Marka tace"Zaki san ko meye idan lokacinki yazo maza kije gidan Mariya ki kirawo Sayyada." Amina tace"To." Ta nufi gidan Mariya dake bayan layi.


Tsakar gida ta tarar dasu sunyi d'an malele da yaji da manja harda tumatiri da albasa suna sha suna dariya da hirar aure kamar yanda suka saba.

Babu wacce ta amsa gaisuwarta sai kallon banza da suka watsa mata Amina tace"Sayyada kije Baba Ladidi na kiranki." Ta juya zata fita Sai taji Sayyada na kwaikwaiyar maganar ta da hanci "Wai Sayyada kije Baba Ladidi na kiranki yan! yan! yan!!!!! Ta juyo tana kallonsu sai suka kwashe da dariya Amina ta bar gidan da sauri takaici kamar ya kasheta wai Sayyada ce take biyewa wasu bare suna wulakantata......Sayyada ta wanke hannunta tare da zura hijab dinta tace" Bari naje na dawo yanzu." takalmanta tasa ta fice daga gidan.

Amina ta hango tana tafiya so take ta isketa har inda take ta ci mata Uwa! tana karya kwana taga motar da ya saba zuwa da ita garin tayi parking irin motocin nan ne na gurin aiki.Kafin ta an kara Taga ya fito daga motar tare da Abokinsa sai gabanta ya hau dukan uku uku! ta hau kallon jikinta wani ko d'ad'd'an zanin atamfa ne a jikinta da wata t_shirt mai karamin hannu kanta ko d'ankwali babu sai hijab data zurma "Wallahi ba zai ganni a haka ba." a fili tayi wannan maganar la'bewa tayi tana le'kensu inda taga Amina ta iskesu ta tsuguna har 'kasa ta gaishesu, girgiza kai tayi haushi ya turnuketa tana kallon sanda Yake amsawa yana mata dariyarsa mai tsada Sayyada kamar ta kurma ihu! sai cije baki take tana gyada kai tana kallonsu suka nufi cikin gidan tare........Sai bayan taga shigewarsu ne sannan ta fito daga inda ta 'buya. Gidan ta nufa duk ranta babu dadi.






6/6/2020



*BINTA UMAR ABBALE*



_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kudi ne 1_2 #400 ga duk mai bukatar karantawa sai ya tura kudinsa ta wannan accont din......0542382124.......Binta Umar gtbank idan kuma katin waya mutun zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din zan fad'a masa yanda zai biya kud'in....08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar littafin to sai ku tura dala dari ta wannan numbars.....90899076 _88137740 katin airtal ko orange.....Dala dari itace a madadin dari uku na najeria.*_
[6/12, 12:15 PM] Bintu: *NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*


*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________



*Free Pege 13*
Cike da farin ciki Baba Marka take fad'in"Sannuku da zuwa sannu kunsha hanya ashe dai angon nawa yana tafe da har ina cewa zanzo biko ashe dai ana sane dani." Tabarma ta shimfida musu suka zauna Captain Habu sai murmushi yakeyi karamcin matar ke bashi sha'awa gaisawa sukayi a mutunce tana tambayar mutanan gida Sadam! ya kalli 'kofar dakin Baba Ladidi yace."Ina sauran mutanan gidan suke."!? Baba Marka tace"Baba Ladidi dai bata dad'e da fita kasuwa ba ita kuma Sayyada yanzu yanzu na aika kiranta tana gidan Kawarta Mariya." Ta kalli Amina dake tsaye tace"Ina Sayyadar."? Amina tace"Tana kan hanya." Kafin Baba Marka tace wani abu Sayyada ta shigo bakinta dauke da sallama.
Baba Marka tace"Yawwa gatanan ma." Sayyada ta karaso inda suke fuska babu yabo babu fallasa take gaishe su, Sadam! ya kalleta yana wani ya mutsa fuska sam! bai amsa gaisuwar ta ba Captain Habu ne ya amsa da fara'a a fuskarsa Sadam yaji takaicin yanda Habu yaga sayyada kaca-kaca duk da cewar bai tabbatar da cewar itace ba.

Dakin Baba Ladidi ta shiga ta cire kayan jikinta dogon hijab ta sanya har kasa ta fito kai tsaye bakin rijiya ta nufa ta jawo ruwa cikin rijiya bandaki ta nufa tayi wanka tana fitowa idanunsu suka game da juna yayi saurin kauda kansa yana kur'bar damammiyar furar da Baba Marka ta damo musu


Baba Ladidi ce tayi sallama ta shigo hannunta rike da wani buhu mayafi a saman ka tace"Ai tunda na doso bakin layi na hango motar sojoji a kafe nace to Soja yazo ganin amaryar tasa." Ta karashe maganar tana dariya hade da kokarin aje buhun a gefe ta cire mayafin dake saman kanta tana fad'in"Ai fa wannan ranar dama nasan dole ne ta tambaye ni." Baba Marka tace"Ai sai da na fad'a miki cewar ki bari ranar tayi sanyi in yaso sai ki tafi."

Ya d'ago kansa a nutse yana kallonta yace."Wai shin ma ina taje da wannan ranar."!? Baba Marka tace"Haba kaiko sai kace wani kurma kana ji fa nace kasuwa ta tafi."

Ya kalli Baba Ladidi dake firfita da mafici yace."Baba ashe dai baki fasa yawon kasuwar nan ba ko."!?

"Oo! ni ba abinda kake tunani ne ya kaini kasuwa ba ato tawa ce ta kaini ta wani gefan kuma sai in ce ta dalilin ka na shiga kasuwar."

Ta'be bakinsa yayi ya mayar da kansa 'kasa Baba Ladidi ta washe baki tana kallon captain Habu tace"Ashe tare kake da ba'ko sannu da zuwa samari ya mutan gida da fatan duk sunannan lafiya ko."?

Captain Habu yace."Kowa lafiya lau ai sunce ma a gaisheku da kyau."!

Baba Ladidi tace" Alhamdullhi ." Sai ta fara zazzage abinda ke cikin buhun tana dubawa tace"Kinga na samo saiwowin maganin nan da duk abinda ake bukata saboda haka yanzu yanzu zan sanya 'Dantani ya yanka min kazar."

Baba Marka tace"Hakan yayi sai ya had'a da Zabi gudu uku ya yankawa ba'ki ayi musu miya ko."!?

Tace"Kwarai kuwa kinga kuwa naga kayan miya masu kyau a kasuwa wallahi wannan ranar da ake kwalawa itace ta hanani na tsaya na siyo."

"Aifa! gwara da kika nufo gida a aika Dantani ya siyo yanzu." Baba Marka tafada tana kokarin mikewa mayafi ta dauko jikin kyauran dakinta ta yafa ta fito tana fad'in"Bari in kira Dantani d'in nasan dai yanzu ya dawo cin abinci daga gurin sana'arshi."

Har ta kai kofar fita Baba Ladidi tace"Wai Ina Sayyada ne? ko bata dawo daga gidan kawar tata ba."

Marka tace"Shigowarki ta shiga daki tana ciki tana jinki." Labule ta d'aga ta fito

Tana sanye da riga da siket na atamfa soso tayi wata irin kwalliya ta d'ige-d'ige a da kwalli kumatunta da saman goshinta sai le'banta data mulke shi da jan janbaki fuskar nan jazur da jar hoda abinka da farar fata. kanta babu dankwali sai ubangashi data daure shi a tsakiyar kai yana reto ga wani uban kyalli da yake saboda man data lafta masa

Sadam! na ganinta ta fito a haka ransa ya 'baci indai ba idonsa ne ke masa gizo ba har cibiyar ta sai da ya hango lokacin da take kokarin zama kusa da Baba dake rigar karama ce sannan hannunta me fad'i ne wanda tana d'agawa za'a iya ganin hamtarta Gashi kanta babu dankwali duk ta fito da surar jikinta, Rai a 'bace ya daka tsawa tare da fad'in"Maza ki tashi ki sanjo kaya wannan ai sun matse ki sannan dake ke mara hankali ce kin fito babu dankwali wai ke kinyi ado."

Cikin jin haushi ta watsa masa harara! ta dauke kanta tana zumbura baki.

Baba Ladidi tace"Dad'ina da kai kenan kai ba'ayi maka gwaninta a maimakon ka yaba da kwalliyar da tayi maka sai ka kushe hakan bai dace ba." Ta kalli Captain Habu tace"Don Allah ka dinga bawa abokinka shawara ya rage fad'a! da jarabar masifa yarinyar nan dai marainiya ce."


Captain Habu yayi dariya yana d'an kallon Sayyada ta 'kasan Ido gaskiya abokinsa yayi dace da mace nan gaba kad'an yasan yarinyar zata zama cikakkiyar mace.

Yace."Muma can gurin aikin haka muke fama dashi Baba Sadam! din ne ai ya cika zafi shiyasa ko a filin daga! ba'a cin galaba a kanmu."!

Baba Ladidi tayi dariya tana fad'in"Ai filin ya'ki daban damu da iyalinsa bana so a daura aure yazo ya tsawalawa yarinyar mutane."

Captain Habu yace."Karkiji komai Baba insha Allahu zamu rike Sayyada da kyau da kulawa." Baba tace"To nagode Mai gidana na kaina."!

Mikewa tayi ta shige d'aki Sayyada ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da 'yan ya tsunta na hannu Sadam! sai dalla! mata harara yake yana ya mutsa fuska. Shi ko Captain Habu sai janta yake da wasa tana murmushi.

Tsaki yayi yace"Wai don Allah Captain me ka hango naso a jikin wannan yarinyar ne? dube ta da kyau ka gani in banda iyaye iyayene Allah da ba zan takurawa kaina ba Duk tsiya nasan Halima ta fita komai da komai."!!!

Sayyada ta d'ago kai ta kalleshi ranta ya 'baci idanunta suka kawo ruwa wacece kuma Halima? Captain Habu ya 'bata fuska yana fad'in"Aboki meye haka wannan ai cin fuska ne." Sadam! ya kauda kansa gefe waya ya ciro yana dubawa

"Kiyi hakuri kinji amarya." Captain Habu ya fada da kokarin ganin ta saki fuskarta, Kallonsa tayi tace"Abokinka yace bai ga abinso a tare dani ba Allah yasa bashi kad'ai gareni ba ko yanzu yace baya so akwai dubanninsa masu so saboda haka nima ba wai sonsa nake ba Umarnin magabatana kawai nake bi." Tana gama maganarta ta mike ta shige daki hijab ta zura ta fito Baba Na daki tana fad'in"Sayyada kar ki fita ina zakije dawo ki shanye maganin nan na dama miki kar ki fita fa."

"Baba nifa na tafi gidan su Ummi domin ba zan zauna a cikin gidan nan ba mutukar yana cikinsa sai ya tafi na dawo." Tana gama maganarta ta fuce daga gidan cikin bakin ciki da takaici, tana daf da fita babban soro suka ci karo da Amina hannunta rike da wata leda da alama daga shagon Magaji take lemon kwalba ne fenta da mirinda ta siyi da sanyi 'kara-'kara!! Sayyada ta tare mata hanya rai a 'bace tace"Dama neman ki nake.


Amina tace"Menene kuma."!? Sayyada ta rike 'kugu tana fad'in"Tambaya ta ma kike menene lallai ma Amina! dan kutumar ubanki wannan lemon ubanwa kika siyowa? Amina tace"Kar dai ki sake ki zageni Sayyada lemo kuma babu ruwanki da wanda na siyowa! Wallahi sai naji Uban da kika siyowa lemo sannan me zakiyi idan na zage ki." ? Amina tayi murmushi tana kokarin ratse ta ta wuce tace"Ni dai ba karya bace da zan zauna ina haus........Ai kafin ta 'karisa Sayyada ta buga tsalle ta kaud'a mata mari! "Nice karya dan babanki." Sai ta wafce ledar hannunta a take kwalbar lemukan suka fashe lemon ya zube a kasan gurin......Kwalbar lemon da ta fashe ta d'auka tayi kan Amina tana huci! wallahi sai nayi miki zane a fuskarki ni zaki kira karya ki shiga gonata ki kirani karya lallai Amina kin ta'bowa kanki bala'i! Amina da taga Sayyada na nema ta lahanta ta sai ta fara neman hanyar tserewa Sayyada ta jawo hijab dinta wanda gari jawo hijab din ta taka karamar kwalba a take ta huda mata kafa amma ko a jikinta kokari kawai take tayiwa Amina zane a fuska.....Ihu! Amina take tana fad'in "Wai Sayyada ke mahaukaciyar ina ce ne? me nayi miki.? A fusace tace" Mahaukaciyar gidaj Ubank....Kafin ta karasa taji saukar mari a fuskarta Yana tsaye ransa a 'bace yace"Sakar mata hijab." Sai ta rushe da kuka tana fad'in"Ai kamata yayi kafin ka yanke hukunci ka tambayi ba'asi kawai sai ka mareni alhalin itace da rashin gaskiya." Hararta yayi yace"Ban tambaye ki komai ba saketa ki wuce cikin gida." Sayyada ta sakar mata hijab Ya kalli Amina dake motsa baki yace."Ke Amina meye ya had'aku."? "Wallahi Yaya Sadam! ban san abinda nayi mata ba kawai karo mukaci tazo fita ni kuma zan shigo naje shagon Magaji na siyo muku lemo shine fa ta tareni da kokawa tana zagina."

Ya kalli Sayyada rai a bace! zai hau surfa bala'i Captain Habu yace."A'a ba haka ake ba ai kaji magana daga bakin Amina itama sai ka fara jin ta bakinta haka ake hukunci."
Hararasa yayi yace."Baka san halin wannan yarinyar bane Habu Sayyada batajin magana wallahi nasan itace da tsokana." Captain habu yace."Eh duk da haka dai kaji ta bakinta."
Ya jiyo da hankalinsa kanta ganin jinin dake fita daga hannunta yasa jikinsa yin sanyi ya kura mata ido a hankali yace."Meye ya had'aku?"

"Itace take cewa dani Karya shine nace sai ta fad'a min inda nayi karuwanci tunda dai ni nasan karuwa kawai ake kira da wannan kalmar."

Sadam! yaji takaicin wannan kalmar ta Karya ya kalli Amina da jan ido yace."Amina da hankalinki kike kiran 'yar uwarki da wannan kalmar."!? Amina tayi rau!rau! da ido tace"Wallahi zuciya ce ta ciyo ni kuma Sayyada ta dad'e tana min abubuwa shiyasa ban san sanda na kirata da wannan suna ba."

Yace."To daga yau sai yau kar ki sake kiranta da wannan kalmar kinji ko." Tace."To insha Allahu."

"Ko wacce ta shige 'kofae su." Sayyada ta kalli Amina tana mata gwalo Amina tayi rau! rau! da ido tana kallon Sadam din da ya juya baya da niyar barin gurin tace"Yaya Sadam! idan anjima akwai wata magana da zamuyi da kai." Sayyada tayi saurin juyowa tana kallonta Amina ta dauke kanta Sadam din yace."To babu laifi Allah ya kaimu lafiya." Fita sukayi shida Captain Habu, Ita kuma Amina ta juya zata shiga kofar su Sayyada tace"Banza jaka mayya kawai Wallahi duk nacin ki sai dai ki hakura banza kawai."!!!

Amina ko waigowa ba tayi ba ta shige kofarsu tana addua Allah yasa hakanta ya cimma ruwa.....Sayyada ta jima a tsaye a gurin tana sake sake daga bisani ta nufi babbar kofa aifa ba zata basa zuwa gidansu Ummi ba sai dai kome zaiyi sai dai yayi.






7/6/2020



*BINTA UMAR ABBALE*





_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kudi ne 1_2 #400 ga duk mai bukatar karantawa sai ya tura kudinsa ta wannan accont din......0542382124.......Binta Umar gtbank idan kuma katin waya mutun zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din zan fad'a masa yanda zai biya kud'in....08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar littafin to sai ku tura dala dari ta wannan numbars.....90899076 _88137740 katin airtal ko orange.....Dala dari itace a madadin dari uku na najeria.*_
[6/12, 12:15 PM] Bintu: *NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*


*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________





*Free Pege14*
Koda Sayyada ta fita can ta hangosu tsallake kan wata katuwar tabarma tare da matasan samarin garin irin su malam Bashir, dauke kanta tayi tazo ta wuce ta gabansu Sadam! ya bita da kallo yana girgiza kansa kafin ya ankara ya hango Talle ya tare mata hanya harda dogare hannunsa a jikin bango magana yake mata kasa-kasa ita kuma sai waiwayen bayanta take tsoro take ji kar yayiwa Talle ilah! dan ga dukanin alamu Talle ya mance karonsu dashi......"Haba baby yawa kikeyi karfa ki manta da cewar ni masoyinki ne me kaunarki a cikin ko wane hali.'

Sayyada ta juya tana kallon bayanta aikuwa sai ta hangoshi yana tafiya tamkar wani zaki har ya kusa riskarsu....."Wai baby kallon me kikeyi ni nefa Talle masoyin......Yana ganin Sadam! sai ya sunkuyar da kansa kasa hanyar fecewa yake nema


Sadam ya 'karasa gurin tare da tare masa hanya fuskarsa babu annuri yace."Kai tsami guy ya kake? wato ka manta gargadin da nayi maka kwanakin baya da suka wuce ko."?

Talle yayi kasa da kansa tsoro duk ya dabaibaye shi mussaman da ya lura da wandon sojojin dake jikin Sadam! Baki na rawa yace."Ayi hakuri yallabai soyayya ce ta jawo."

Sadam! yayi murmushin takaici yace."To kaje ka nemi dai-dai da kai domin wannan dake tsaye a gabanka ba sa'ar auranka bace."

Baki na rawa Talle yace."Insha Allahu na daina kulata daga yau na fahimci komai." Sadam! yace."Kai dai ka sani na fad'a maka duk ranar da na sake ganin ka nuna ka santa ranar zaka 'bakunci lahira." Talle ya dinga bashi hakuri kokari kawai yake ya bashi hanya ya wuce.

Talle na barin gurin ya mai da hankalinsa kanta.
Kasa tayi da kanta gabanta na fad'uwa yace."Ina zakiji ba cewa nayi ki koma gida ba."? Baki na rawa tace" Gidan su Ummi zani." Ya watsa mata kallon banza "Wuce cikin gida ko ranki ya 'baci! Kafin ya ankara tayi gaba ta barshi a tsaye a gurin.....Baki a sake yake binta da kallo waigowa tayi tana kallonsa sai ta gumtse baki tana dariya ta juya ta cigaba da tafiyarta.

Ya jima a tsaye yana mamaki! Wato yarinyar nan ta raina shi da yawa amma yasan maganinta zai daina shiga sabgarta tunda bata jin maganarsa.
Majalisarsu ya koma cike da takaicin abinda Sayyada tayi masa.

***

Can cikin gida kuwa Amina na shiga kofar su ta rushe da kuka Baba Iya na tatar gasara ta dakata tana kallon 'yar tata tace"Ke kuma lafiya? kin shigo kina kuka menene ya faru naga hannunki da hijab dinki da jini.

Amina na share hawaye ta sanar da mahaifiyarta abunda ya faru tsakaninta da Sayyada Baba iya ranta ya 'baci ko wane lokaci Sayyada itace take cin galaba akan Amina amma ba'a ta'ba d'aukar mataki ba ana kallo Sayyada nayin abinda ta gadama a cikin gidan ba'a yi mata fada ita da take ma 'yar mace ba 'yar namiji ba gaskiya wannan karon ba zata yarda ba.

Tana gama tatar gasarar ta dauki mayafi ta yafa ta nufi kofar su Sayyada.....Baba Ladidi na gaban murhu tana dahuwar kazar amare ita kuma Baba Marka na gyara kayan miyan da za'ayiwa su Sadam! farfesu Baba Iyatu ta shiga suka amsa sallamar ta Baba Iya taja ta tsaya tana fad'in"Baba Ladidi a gaskiya na gaji da irin wannsn abun da yake faruwa a gidan nan, Kullum Sayyada ke cin galaba akan Amina ba'a ta'ba daukar mataki ba haba abun yayi yawa gaskiyar magana ya kamata a gyara al'amarin yanzu gashi Sayyada ta farfasa mata hannu da kwalbar lemo jini sai zuba yake."

Baba Ladidi tace"Subahanallahi! abinda ya faru kenan? Baba Iya tace"Kwarai kuwa baba gaskiya a jawa Sayyada kunne abinda takeyi yayi yawa."

Baba Marka tace"To in banda abunki ma ai Sayyada ba maxauniya bace nan da 'yan kwanaki ta bar gidanan kuyi hakuri kan abinda tayi kuma za'a ja mata kunne."

Baba Iya ta kama hanya ta fita tana bala'in jin takaici Sayyada zata riga 'yarta aure don dai babu yanda zatayi ne ta hakura shiyasa take so ta tayar da hankalin kowa a gidan kafin lokacin bikin.


Ummi tace"Wai don Allah da gaske kikeyi Yaya Sadam! yazo." Sayyada tace"Lallai Ummi dama ina yi miki karya ne."? Ummi ta mike da sauri tana jan hannunta tace"Tashi muje na ganshi don Allah." Sayyada ta kalleta tace"Wai don Allah wannan rawar jikin da kikeyi na menene? ni bana son rashin kamun kai fa."
Ummi tace"Wane irin rashin kamun kai mtwsss! dan ma kin samu zanje na ganshi na fasa zuwa."

Sayyada tace"Yi hakuri tashi muje amma don Allah kiyi komai a nutse karki ta washe masa baki."

Ummi tace"Wallahi Sayyada baki da mutunci." Dariya sukayi sannan suka fito tare Sayyada tayi wa babarsu Ummi sallama suka fita.


Tun daga nesa Sayyada ke nuna mata shi Ummi sai kallon majalisar take tana so ta tantance waye Sadam! din Sayyada tace"gashi can me koriyat riga a jiki da wando irin na sojoji." Ummi tace"Na gane shi wai! gaskiya Sayyada kin dace da miji dan gayu dan birni gashi kuma soja." Sayyada akayi dariya,

Sadam! takaici kamar ya kashe shi yana daga inda yake yana hango sayyada na nuno shi da hannu sai kace wata 'yar kauye dauke kansa yayi saboda tsabar bakin ciki Shi kuwa Captain Habu dariya kawai yake musu.........Garin kallon sa kafarta guda ta subce ta fad'a ramin kwata ihu!! ta kurma ta riko hannun Ummi! Yana kallon abinda ke faruwa yace"Allah shi 'kara dauke kansa yayi kuma baiyi niyyar mikewa ba....Habu ne ya mike da sauri ya isa gurin.....Yayi yayi ya jawo 'kafar Sayyada ya kasa sai kuka takeyi Ummi duk tayi kalar tausayi.

Captain Habu ya isa inda yake zaune yace."Haba aboki ka tashi mana kaje ka ciro mata kafar Yarinyar nan fa garin son da take maka ne yasa ta fada cikin ramin haba mana."

"Rabu da ita Habu idan ta gaji zata fito da kanta naji dadi data fad'a cikin ramin." Habu yace."baka da imani wallahi." komawa yayi gurin yana janyo hannunta ta ma'ke hannun kuka takeyi harda majina Captain habu ya koma gurinsa sai da ya nuna masa 'bacin ransa sannan ya mike ya iski gurin.....Tana ganinsa ta sake lanjarewa tana kuka kafar wandonsa ya tattare ya afka ramin Ba tare da wani bata lokaci ba ya sa'bata a kafad'arsa ya kama ya fito Sayyada rike shi tayi gam! tana sauke ajiyar zuciya....Ko da yayi nufin sauke ta sai ta'ki ta cikwikwiye masa riga hade da rike

2 Comments On NI DA YAYA SADAM
avatar
hauwa-abdullahi

1 year ago

Reply

I love the story

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to hauwa-abdullahi

Thanks be with us for more stories

Please Login or Register in order to submit comment