Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Zani ta daura kan rigar baccin amma bata rufe kirjinta ba ko dankwali babu ta dauki tire din abinci da aka jera masa ta nufi dakinsa.....Yana tsaka da zage tazugen wandonsa ta shigo da sallama kasancewar dakin akawai duhu yasa ba taga komai ba shima nasa 'bangaran yaji dad'in hakan....Tsawa! ya daka mata "Malama me ya shigo dake d'akina da wannan lokacin." !? Tace"Baba ce tace kar nayi bacci har sai ka dawo na baka abinci sannan sai in kwanta."

Ya dauki wayarsa ya kunna torchlight yana haskata gabansa ne ya fad'i ganin irin rigar dake jikinta ya dauke kansa da sauri yace."Me yasa ba aje min ba tunda dakin ai a bude yake ko dole ne sai kin bani da hannunki." Tace."To aini ma ba laifina bane." Tsaki yaja yace."Meye abincin."!? "Dafadukan shinkafa ce da busassan kifa." Shiru yayi na minti biyu ita kuma ta aje tiran kayan abincin zata fita yace."Dawo ki zuba min abincin sai ki tafi." Ta dawo da baya tana sanja tafiya wai ita dole ga budurwa sai ta janye hankalinsa.



Ta sunkuya tana zuba masa abincin shi kuma yana haske ta da hasken wayarsa 'yan 'kanunun nonowanta yake hangowa daga cikin rigarta ya kura musu ido yana kallo hannunsa ya duba yaja tsaki! tayi saurin kallonsa harara ya watsa mata ta dauke kanta tana ta'be baki hannunta ya kurawa a ido yana kallo yace."Ke! wane zobe nake gani a hannunki."!? gabanta ya fad'i! sai tayi saurin 'boye hannun yace."Ina wasa dake kenan ba tambayar ki nake ba don Ubanki."! Cikin rawar baki tace"Zobena na ne."!? yace."A gidan Uban wa ya zama naki ashe dama bakijin magana ba cewa nayi ki mayarwa da Amina ba ashe baki mayar mata ba shin wai ke me kike so ki zama ne."!?

Tace"To ai gani nayi zoben bai dace da ita ba shiy....."Rufe min baki anan gurin ko kuma yanzu in mareki wallahi! maza maza! ciro min zoben nan ko yanzu in 'ballaki."!

Da sauri ta nufi hanyar fita....Ya mi'ke cikin zafin nama ya cafko tsintsiyar hannunta yana murd'ewa zubewa tayi nan bakin 'kofar ya sanya 'kafa ya tura 'kofar ta rufe gam!! d'aukar ta yayi kamar jaririya ya jefa ta kan katifar ta mike da sauri tana kallonsa, yace."Zaki ciro zoben nan ko kuwa zaki tsaya gaddama."!

Shiru tayi tana motsa baki ya hayo kan katifar da sauri ta matsa yace."Dama na fad'a miki idan kinyi min laifi da abinda xan hukunta ki zaki Ubanki yanzu yanzu."!

Sayyada shaf ta manta da irin hukuncin da zaiyi tace"Ni wallahi bazan ciro zoben nan ba tunda ina sonsa kuma dai naga an gama tsayar da magana a tsakaninmu da kai idan auran Aminar zakayi sai ka fad'a mu sani."

Ko kallonta baiyi ba ya matse ta jikin bango yana me d'amkar brest dinta guda d'aya al'amarin yazo mata a bazata! ta bude baki zatayi ihu! ya rufe mata baki da tafin hannunsa.

Jikinta ne yake ta kyarma! tsigar jikinta na tashi duk ta rasa yanda zatayi shi kuma sai mulmula mata Brest yake.!!!

Sai da yaga tayi la'kwas! sannan ya bar abinda yake ya kama hannunta ya zare zoben murya a hard'e! yace."Tashi ki bawa mutane guri."! Simi! simi ta sauko ta dauki zaninta ta d'aura ta kama hanya ta fita.

Tana fita ya sauke wata zazzafar ajiyar zuciya ya mai da zobensa hannunsa minti biyar a tsakani ya fito sanye da jallabiya bandaki ya nufa dole sai ya tsarkake jikinsa don wannan abin da yayi sai da yaji alamun fitar ruwa a tare dashi.


Sayyada kam! bayan Baba Ladidi ta kwanta tana ta takure jikinta motsi kad'an sai tsigar jikinta ta mi'ke wani irin yanayi takeji a jikinta mara misali ga kan nononta duk ya kumburo sai kyaikyayi suke mata kuka ta farayi jin al'amarin yana so ya wuce gona da iri


Yana fitowa daga bandaki ya ji shashshakar kukanta da sauri ya shige daki ya rufo kofa tare da jan dogon tsaki.

Baba Ladidi ta farka tana kokarin mikewa zaune tace"Ke Sayyada kukan me kike da wannan daran."

"Baba cikina ne ke ciwo."! tafada tana shashsheka...." Assha!! to ba sai ki tashi ki dauko kanwa ki kad'a ba sai kawai kiyi kuka." Baba ta fad'a a lokacin da take kunna fitila Sayyada ta mike da jiki a sanyaye ta dauko kanwa da ruwa a kofi ta kad'a tasha ta koma ta kwanta.....Baba Ladi kuwa zama tayi har sai da sayyadar tayi bacci sannan itama ta kwanta.

*Asubah ta gari*

Karfe bakwai ya fito a shirye da nufin tafiya nan duk ya gansu suna karyawa ya gaisa da kowa ya nemi gefe guda ya zauna fuska a daure Baba Marka tace"Ni dad'ina da kai kenan baka da fara'a wallahi kowa na cikin walwala da farin ciki kai kana d'aurewa."!

Yace."Haka kawai sai na hau dariya kamar wani mahaukaci."! tace"Oo! ni ba haka nake nufi ai dai ka saki fuskarka tunda ka fito ka ganmu a zaune muna raha." Murmushi yayi sai yayi wani masifar kyau tabbas da ya san yanda murmushi ke masa kyau da ya dinga yi.....Baba Ladidi tace"To ko kaifa ai wannan zaman da mukayi duk naku ne kai da Sayyada muna shirya yanda al'amarin biki zai kasance domin mun riga mun tsayar da cewar sati hud'u kacal xa'a daura aure."

Ya d'ago kai yana kallonta cike da d'umbin mamaki!

Alhaji Auwal yace."Kwarai kuwa naga kamar kana mamaki! to wannan maganar ma ba daga gare mu ta fito ba daga can gidan maigari ne domin dai ka san sune suke da iko akanta da asubah bayan mun fito daga sallah can gidan maigarin muka nufa domin mu tsaida magana."


Yace."To sai naga al'amarin kamar akwai cutawar wa a ciki maganar karatun ta kuma fa kada ku manta fa wannan shekarar ta gama 'karamar makaranta pramiry zata shiga secondary mai zai hana a bari ta kammala tukkuna nima kafin lokacin na samu nutsuwa."


Alhaji Auwal yace."Maganar karatu ai mai sauki ce Sadam! ina gani ai zata iya cigaba a dakinta wannan ba matsala bace." Sulaiman yace." 'Kwarai kuwa." Wata harara ya watsa masa yace."Ni wannan ba ra'ayina bane Abbah kasan kowa da tsarinsa mutukar kuka d"aura min aure da Sayyada a irin wannan lokacin to gaskiyar magana shine ta gama karatu saboda bana da ra'ayin iyalina na cud'anya da maza da sunan karatu."


Baba Ladidi tace"Wai shin karatun dole ne! jama'a! ku kyaleshi kawai ai yayi tsinkaye da hangen nesa kuma hakan ya nuna mana cewar yana kishin kansa da iyalinsa don haka maganar karatu a bar ta Allah ya amfana wanda ta samu."

Sulaiman yaji wani irin takaici da 'bakin ciki ya turnukeshi yanzu yarinya 'kan'kanuwa kamar Sayyada za'a tauyewa rayuwa ayi mata aure da 'kananun shekaru sannan kuma saboda tsabar kin gaskiya da son kai a goyi bayan hanata karatu a dakinta wannan tauye hakki yayi yawa tabbas in da shine ya samu nasarar auran yarinyar sai ya gatanta ta ya barta tayi karatu mai amfani ta hau matsayin da duk wata mace mai matsayi take hawa Ya lura Sadam! ba wani son yarinyar yake ba kawai don dai sun tursashi ne zai aureta a wannan ga'bar bashi da tacewa sai dai kawai ya roki Allah kan abunda ke damun ransa.


Alhaji Auwal bai so Mahaifiyarsa ta goyi bayan hakan ba to amma saboda yasan bashi da abinyi sai kawai yace."Dama ai karatu ga 'ya mace ba dole bane suturarta da mutuncinta shine dakin mijinta to shikkenan mun bar maganar Allah ya sanya alkairi."

Sadam! da Alhji Auwal ne kawai suka tafi a ranar shi kuma Sulaiman yace sai ya kara sati guda tukkuna sannan zai koma.

***
Sayyada kam murna kamar ta zuba ruwa a kasa tasha daga jin an tsayar da ranar daurin auransu da Sadam! ta dinga yiwa Amina habaici 'kawayenta kuwa babu wanda bai san zancan ba in sun zauna zancen kenan na aure suna koya mata abubuwa da yanda zata dinga yiwa mijinta kullum idan antashi daga makaranta sai su nufi gidan Mariya suyi ta zungurarta ita kuma tai ta fayyace musu yanda auran yake.


Amina ta shiga wani irin mawucin halin lokacin da taji maganar auran Sayyada da Sadam! ya tabbata kullum sai tayi kukan bakin ciki duk ta tsargu da kanta gashi idan taje makaranta 'yan ajinsu suyi ta nunata suna mata dariya mai son wanda baya sonta da yake sunan da Sayyada take kiranta dashi kenan ganin zata halaka kanta ne yasa ta yanke shawarar duk lokacin Yaya Sadam! din yazo zata sanar masa da abinda Sayyadar take mata sannan zata roke shi ya had'asu ya auresu ko don ma'kiya suji kunya




*Tofa shin wannan al'amarin zai yiwu kuwa? wai ma Sadam! na son Sayyada da gaske ko sha'awarta yake!? Meye matsayin Amina a zuciyar Sadam! Wane irin xama za'ayi tsakanin Sadam da Sayyada? Wane al'amari ne zai faru anan gaba!?*



_Muje Zuwa_





2/6/2020

*BINTA UMAR ABBALE*




_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kudi ne 1_2 #400 ga duk mai bukatar karantawa sai ya tura kudinsa ta wannan accont din......0542382124.......Binta Umar gtbank idan kuma katin waya mutun zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din zan fad'a masa yanda zai biya kud'in....08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar littafin to sai ku tura dala dari ta wannan numbars.....90899076 _88137740 katin airtal ko orange.....Dala dari itace a madadin dari uku na najeria.*_
[6/12, 12:15 PM] Bintu: *NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*


*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________



Pege 12


Gaba mai tsanani ce ta shiga tsakanin Sayyada da Amina ta inda har sai da tsofaffinsu su gane basa kula juna wanda da can baya suke mutukar shiri da junansu duk inda kaga Sayyada to zaka ga Amina a gurin tare suke cin abinci su tafi makaranta tare komai nasu tare sukeyi amma tunda al'amarin auran ya tabbata shikkenan suka raba gari wanda inda ta Amina ne zasu iya cigaba da mu'amularsu to kullum taje makaranta 'kawayenta sai sun zugata sunce kar ta sake sakin jikinta da Amina xata shiga tsakaninta da masoyinta wannan dalili ya sanya Sayyada sake nuka wulakancin da take wa Amina yafi na da yawa.

Cikin 'yan kwanakin da Sulaiman yayi a garin *Dabi* yayi sune cikin takurewar zuciya gami da tsananin damuwa mutukar zai bud'e ido ya dinga ganin Sayyada a matsayin matar d'an uwansa zai ji kamar zuciyarsa zatayi buga saboda takaici da 'bakin ciki a ganinsa sam! Sayyada bata dace da Sadam! ba dashi ta dace, sai kawai ma ya dinga jin tsanar d'an uwan nasa na d'arsuwa a cikin zuciyarsa a daddafe yayi kwana biyar ya had'a kayansa yayi musu sallama ya tafi......Wannan karon Sayyada bata damu da tafiyarsa ba kamar da inda duk sanda yazo garin to da kuka suke rabuwa da juna, al'amarin sai ya bashi mamaki! mutuka ya lura yarinyar na masifar son Sadam! ganin irin rawar jikin da takeyi kwata-kwata ma bata zama suyi hira kamar da zuciyarsa ta cika fal da takaici da bakin ciki had'e da masifaffan kishin 'Dan uwansa a duniya yana ganin bashi da babban ma'kiyi sama dashi.

****

Sadam! kam tunda ya koma bakin aiki ya manta da wata Sayyada tinda dama can ba itace a gabansa da ita da babu duk d'aya suke a gurinsa babban abunda yafi damunsa shine yanda zai d'aukota ya ajeta cikin brecck d'insu wanda ya tara mutane mabambamta ra'ayi da addini kowa yana yin abinda ya ga dama duk kuwa da cewar wasu daga cikin su akwai iyalinsu a ciki hakan baya hanasu shaye-shayen su da neman mata idan ta kama suje club ranar da suke hutu haka kowanne zai fita cikin mota wasu su dawo wasu kuma su kwana can marasa kunyar cikinsu kuwa har mata suke kawowa al'amarin dai ya 'kazanta babban abinda yake tunani kenan zaman Sayyada a bracck din yasan halinta da shegen rawar kan tsiya kuma duk da ba wani sonta yake ba to dole ne yayi kishin auransa sam! baya so wani shege ya kalleta balle ya 'kyasa....! Sadam mutum ne mai kawaici da kau da kai ga abinda bai shafeshi ba shiyasa suke ganin mutuncinsa shaye-shaye da neman mata duk Allah ya tsare shi kawai ku barshi da busa haya'kin sigari yana shanta sosai mussaman idan yana cikin 'bacin rai! le'bansa ya d'an soma ba'ki kad'an amma sai wanda ya 'kura ido yake ganewa sam baya shan sigari a idon jama'a shiyasa iyayensa basu taba sanin yana sha ba kuma baya ta'ba yarda kaji warinta a jikinsa mutum ne mai tsaftar gaske kuma yana da ri'kon addini dai-dai gwargwado sai dai fa mugun muskili ne wanda baka ta'ba sanin abinda ke cikinsa saboda tsabar zurfin ciki ko yana son abu baya ta'ba nunawa komai yana bi a sannu baya rawar kai.....Ga yanayin 'kwayar idanunsa zaku gane cewar shi d'in mutun ne mabukaci ina nufin mutum ne mai yawan sha'awa shiyasa yake yawaita azimi saboda wannan matsalar amma saboda tsabar cutar kai ya'ki ya tsaya ya kalli mace ma ballanta yayi tunanin aure....Duk cikin family d'insu shi kad'ai ne ba'ki shima ya d'auko fatar mahaifiyarsa ne kasancewar ta 'yar asalin garin Maiduguri kasuwanci ya kawo mahaifinta Kaduna amma yawanci danginta na can barno da zama Hajiya Fatsima tana da kyau sosai sai dai 'bakace Sadam! sai ya dauko yanayin fatar ta amma kuma ya fita haske saboda shi tasa fatar sai ta kasance tamkar ta ba'ka'ken turawa black America yana da dogon hanci da manya idanu wanda kusan kullum suke a lumshe sai yana filin daga sannan za kaga ainihin hallitar idanunsa amma haka kawai gari banxa baka isa kaga ya ware maka dukanin idanunsa ba ko kallon mutum zaiyi ta 'kasan ido yake kallonka saboda tsabar munafurci haka duk yake 'karewa matan mutane kallo dake yana da yalwar gashin ido idan yana kallonka baza ka ta'ba ganewa ba.....Dogo ne shi amma ba sosai ba yana da fad'in kirji da murd'ad'an jiki wanda yasha training sannan jikinsa du gargasa ce mussaman kirjinsa da kafafunsa kusan kullum cikin gyaran fuska yake saboda yanayin hallitarsa domin ita kanta sumar kansa abin kallo ce yana bala'in ji da ita da kashe mata kudi wanda baza su ta'ba lisaafuwa ba.

Sayyada Fara ce tas saboda tsabar haskenta har yalo takeyi mussaman idan taji rana to ita abun ne ya had'e mata biyu can bangaran mahaifinta fulani ne suma sannan bangaran babarta ma haka shiyasa abin yayi mata yawa tana da gashi sosai gashi ba'ki mai santsin tsiya wanda ko kitso ma ba ya zama a jikinda sai dai kawai ta gyara tayi gammo dashi......Siririya ce tamkar ka bushe ta ta fad'i amma kuma idan ka kalli yanayin jikinta mussaman tsintsiyar hannunta da zara zaran yatsunta zaka fahimci cewa gaba kad'an idan ta samu kulawa da abinda take so zata cika ta batse.....Tana da wani irin sharp mai fizgar hankali cikinta a shafe tamkar bata cin abinci sai dai kas! babu nonowan arziki a kirjinta kananu ne wanda itama duk kankantar hannunta baza su cika su ba, Ko da yake ai akwai sauran shekaru a gaba zasu fito sosai.

Sayyada mai kyauce wanda kallo daya kayi mata zaka so ka sake kallonta tana da kyawu bayyanan ne kewayayyiar fuskarta na dauke da dogon hancinsa sa siraran le'bunanta masu d'an tudu kad'an bata da manya ido sosai sai da Allah ya wadata ta gashin gira dana ido gazar gazar dasu abin sha'awa idonta kamar tasa sanya kwalli shiyasa sam bata damun kanta da lallai in tayi wanka tasa kwalli ba saboda ita Allah ya zana mata a idonta.


Sayyada nada rawar kai sosai bata cuta amma ba yarda a cuceta ba Allah ya sanya mata kauna da son Sadam! tun bata kai shekarun haka ba take sonsa idan yazo garin takan shiga cikin wani yanayi mai dadi haka kurrum yanayinsa da yanda yake tafiyar da rayuwarsa yake burgeta tsaftarsa da kamun kansa na burgeta da bata sha'awa tun lokacin data girma taji labarin auransu tayi ta murna da farin ciki tana fadin mutukar ta auri Sadam ta gama dace da mijin aure.


****
Sulaiman fari ne tas dogo dan ya d'ara Sadam a tsayi sai dai Sadam din ya fishi cika ido Sulaiman kyakkyawa ne ajin farko kuma dan boko ne duk a 'kidunsa na nasara ne domin ma bai cika tu'ammali da manya kaya ba sai da kananu Yayi aure shekaru biyar da suka wuce matarsa ko 'batan wata bata ta'ba yi ba sai wannan karon ta samu ciki yanzu dai cikin nata nada watanni takwas.

Amina tana da hankali da nutsuwa ta girmi Sayyada da shekeru uku shiyasa tafita hankali Amina gajera ce bata kai tsayin Sayyada ba amma tana da kirar jiki mai kyau fatarta luwai luwai sannan Allah ya wadata ta da nono masu daukar hankali tana da sauki hali mutuka don magana ma bata dame ta ba, ba kamar Sayyada ba da in tana guri sai ta gundiri jama'a.
A tsakaninsu akwai sha'kuwa sosai da fahintar juna Amma tun sanda Sayyada ta lura da yanda Aminar ke shishshigewa Sadam yasa taji ta soma tsanarta Sai ta rage shiga kofarsu sai dai Aminar ta shigo to idan ma ta shigo kofar tasu Sayyada watarana basa wanyewa lafiya da fada suke rabuwa.


Duk Wasu abubuwa na bukatar rayuwa Alhaji Auwal da 'yayansa na kokarin ganin sun kawo musu don haka basu da matsalar abinci da abun bukatar rayuwa Baba Ladidi ce kawai 'yar rigima ita lallai sai ta dorawa Sayyada tallah,ita kuwa Baba Marka tana kad'a lagwanin risho ne 'yan yaran matan dake unguwar wanda basa aiki da itace suke siya wannan shine sana'ar da takeyi daga zaune. itama Baba Ladidin ganin Sayyadar ne yasa take d'ora mata tallah amma da babu ita dole ne ta hakura tayi sana'a irinta Baba Ladidi.


Wannan kenan.



****



Yana zaune a ofis Captain Habu ya shigo hannu ya bashi suka gaisa kana ya zauna kujerar dake fuskantarshi hankici ya ciro daga aljihunsa ya goge gomin fuskarshi ya kai kallonsa kan Sadam! da yake faman duba wasu takardu yace."Wai ya zamuyi ne da tafiyar da take tun karo mu kasan Allah ni jin tsoron tunkarar wannan 'kauyen da babu wani dan adam din da yake rayuwa a cikinsa Ina jin tsoron mutanan sosai domin sharrinsu yafi na tsohowar mota."


Ya d'ago kansa yana kallonsa fuskar nan a murtuke yace."Wai ke me yasa kake hakane? tamkar ba namiji ba kar fa ka manta da cewar wannan aikin da kakeyi ka dauke shi ne da al'kawari ko kashe ko a kashe ka gabakidaya rayuwarka kar ka sanyata a ranka komai zakayi to kayi da zuciya d'aya tare da taimakon neman taimakon Allah, ladanka yana gurin Ubangiji Sannan kuma ka daina jin tsoron wani hallita in ba Allah ba Allah da manzonsa su kadai ne suka cancanta da muji tsoro ba wata hallita ba, ni ka ganni ko Wallahi Wallahi! Wallahi! kaji nayi maka rantsuwa sau uku ko!? mutukar kaga ba'ayi wannan tafiya dani ba to bana nuffashi a doron duniya, a yanzu babu abinda yake gabana sai tunanin yaya za'ayi mu ci galaba kan wad'annan azzaliman mutanan."

Captain Habu ya girgiza kai yana kallon Abokin nasa yace." A gaskiya ni ina jin in shigar da uzirina gurin Yalla'bai domin jikina na bani gagarimun al'amari zai faru kaga ni ina da iyali da yara gwara kai baka aje kowa ba kuma a zahirance kai ka fimu taurin zuciya da jajurcewa da hikimar ya'ki ina ganin zaka iya tseratar da ranka in wata matsala ta afku"

Murmushin takaici yayi ya aje biron dake hannunsa yace."Wai Habu don Allah waye meyi ne."? Habu yace."Allah ne." Sadam! yace."To amma ka kasan da haka ka kasa yin tawakalli ka bar masa lamarinsa, idan fa mutuwa kake tsoro to ko kaje ya'ki ko ba kaje ya'ki ba idan lokacin ka yayi sai ka mutu gwara ma a kashe ka gurun ya'ki kasan kayi jihadi makomarka Aljanna kuma kana maganar Iyali ni waye ya fad'a maka bani da iyali ina mai tabbatar maka da cewar yau saura sati biyu kacal daurin aure na." Captain Habu yayi saurin d'ago kai yana kallonsa da mamaki a tare dashi....Sadam! ya d'aga masa kai yana so ya tabbatar masa da gaskiyar magana yace."Iyayana sun had'ani aure da 'kanwata dake can garinmu *Dabi* So kaga magana Iyali ba kai kad'ai zakayi ba har dani."

Habu yace."Amma wannan magana ta bani mamaki wallahi wato kai da sai ranar daurin auran sannan ne zaka sanar damu."?

Ta'be baki yayi yace."Auran ne bana so kawai shiyasa sam! bana d'okinsa har so nake lokacin tafiyar yazo in matsa in basu guri."

Captain Habu yace."Amma ka bani mamaki wallahi!!! Sadam! murmishi kawai yayi baice komai ba, Habu yace."In tambaye ka mana."
Yace."Ina sauraronka." Yace."Yanzu ya zakayi da Halima idan taji maganar auranka baka tunanin abinda zai faru da ita."?

Sadam! ya 'bata fuskarsa yace."Wai shin Habu ni nake son Halima ko kuma ita ke sona."!? Captain Habu yace."Itace take sonka." Sai ya d'aga kafad'a yana ya mutsa fuska yace."To kagani ni banda matsala tunda dai ni da bakina ba'a ta'baji nace ina sonta ba ballanta kuce na yaudareta itake yaudarar kanta tunda tasan ni ba mahaukaci bane da zan aureta bayan kowa ya mayar da ita rigar sanyawarsa Kawai ina biye mata ne saboda darajar son da take min wannan shine dalili."

Captain Habu ya girgiza kai yace."Tabbas to amma ni ina tunanin al'amarin da zai faru taji labarin auranka wallahi zata iya kashe kanta saboda bakin ciki."

Sadam! yasa dariya yana kallon abokin nasa yace."Na lura kana tausayawa Halima da yawa kaje kawai ka aureta na bar maka kai nifa har yanzu banga wata 'ya macen da zata ya mutsa min tunani ba wallahi idan ba Uwata ba bana daukar wata mace wani abu saboda dukaninsu basu da kirki.''

Sulaiman yace."Me yayi zafi kake wannan maganar mace ni'ima ce ga d'a namiji sa'ida ce kuma salama ce ba zaka san da haka ba sai ranar da kayi aure sannan zaka gane abinda nake so ka gane."

Murmushi kawai yayi Habu yace."Don Allah abokina ka dinga 'kimanta mata kuma idan na baka shawara ka dinga dauka kamar yanda idan ka bani shawara nake dauka."

Yace."To na dauka." Habu yace."To yanzu yaushe zaka kaini inga amaryar tamu."?

'Bata fuska yayi yace."Kaji ka da wani zance kuma ka bari kawai ai in an daura auran nan zan kawo ta kaduna."

Yace."A'a dole fa kafin daurin aure muje in ganta gaskiyar magana kenan.'' Okey Zamu je insha Allah sati me zuwa."! Habu yace."Allah ya kaimu lafiya." To da wannan magana sukayi sallama Captain Habu yayi masa sallama ya koma ofis din sa.

*****

Sulaiman kuwa bayan komawarsa Kaduna sai da yayi jinyar zuciyarsa na sati guda sannan ya shirya tsaf ya nufi kasar india domin cigaba da gudanar da harkokinsa na kasuwanci Sulaiman komai da ruwanka ne shi ko wace sana'a tashi ce ya fita 'kasashen waje da dama domin gudanar da harkokinsa shiyasa kullum Allah yake kara yalwata masa arzkinsa gashi yana d'an ta'ba siyasa in lokacinta yazo.
Da tunanin Sayyada ya nufi 'kasar hindu.


****

Sayyada fa ananan ana rawar kai da giringid'ishi kullum ana gidan Mariya ana maganar aure ita kuma mariyar in ta kad'a magani da madara na 'karin ni'ima sai ta tsiyayawa Sayyadar tace ta shanye duk sanda mijinta ya soma kwanciyar aure da ita zaji dad'inta aikuwa Sayyada ta bada himma har ta zo gida tana fad'awa Baba Ladi tace"Ta had'a mata maganin Ni'ima wanda Sadam! zai dinga gamsuwa da ita yayin kwanciyar aure.

Baba Ladi da Baba Marka suka dinga salati da sallalami! Baba Ladi tace"Don Ubanki a ina kikaji waannan maganar." ? babu kunya tace"Mariya ce ta fad'a mata. Tundaga ranar Baba Ladi ta hanata fita tace tana zuwa gidan Mariya tana koya mata rashin kunya.....Sayyada kam! tace"Lallai Baba kar! kar! nake kallon kowa idan Baba Ladi ta idar da sallahar walha bacci ya kwashe ta sai ta lalla'ba ta fice daga gidan bata dawowa sai yamma Baba Ladidi ta dinga fad'a kamar ta ari baki.

Suna zaune a tsakiyar dakin Mariya Ummi ta shigo sai suka hau shewa harda tafawa Ummi tace"Wace wainar kuke toyawa ne? Sayyada akayi wani fari da ido akace "Ke ma kin san wainar."!

2 Comments On NI DA YAYA SADAM
avatar
hauwa-abdullahi

1 year ago

Reply

I love the story

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to hauwa-abdullahi

Thanks be with us for more stories

Please Login or Register in order to submit comment