Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace."Duk gasunan a kusa dani." Yace."okey bata wayar zanyi magana da ita." Sayyada najin haka sai gabanta ya fad'i! da sauri ta aro dauriya da jarumta ta kar'bi wayar da malam Bashir din ke mi'ka mata.




_Afuwa bani da change sosai kuyi manege_




31/5/2020



*BINTA UMAR ABBALE*



_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kudi ne 1_2 #400 ga duk mai bukatar karantawa sai ya tura kudinsa ta wannan accont din......0542382124.......Binta Umar gtbank idan kuma katin waya mutun zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din zan fad'a masa yanda zai biya kud'in....08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar littafin to sai ku tura dala dari ta wannan numbars.....90899076 _88137740 katin airtal ko orange.....Dala dari itace a madadin dari uku na najeria.*_
[6/12, 12:15 PM] Bintu: *NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*


*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________


Free Pege 10

Dakakkiyar muryarsa mai cike da amo taji yana fad'in"Ina Sayyada."!? Baki na rawa tace"Gani." Yace."Wai ke me yake damun kwakwalwar ki ne? don Ubanki! ni da kaina kinji nace zan aure ki da har kike tozarta 'yar uwarki a kaina! ni me zanci dake ai idan aure zanyi Aminar zan aura tunda tafi ki komai da komai.....Tayi saurin katse shi ta hanyar fad'in"Ni wallahi Amina bata fini komai da komai ba."! Yace."Ni nake magana kina katseni wato nima zakiyi min rashin kunyar ko."? Shiru tayi bacin rai da bakin ciki yayi mata yawa, yace."Tun muna shaida juna dake ki cire zobe nan ki bata ai ina sane dake ban baki ba saboda ba ki dace dashi ba sai ita kuma wallahi kinji na rantse kada wata magana ta sake biyo bayan wannan a tsakanin ki da Amina idan kika kuskura nazo garin akace ga wani abu da kika sakeyi makamancin wannan to dama kin san sauran sai jikin ki ya fad'a miki kinji ko baki ji ba."!? Ba tare da ta amsa ba masa ta kashe wayar....Cike da mamaki! ya bi wayarsa da kallo wato yarinyar shi ta kashewa waya ashe haukan banza yake ba sauraransa take ba lallai Sayyada wuyanta ya isa yanka.

Kiran wayar ya sake yi sai tayi saurin mi'kawa Malam Bashir wayar ya dauka tana jin sanda yake cewa malam Bashir din duk sanda ta sakeyin wani abu ya sanar dashi zai zo da kansa ya dauki mataki a kanta.
Sukayi sallama da juna malam bashir ya kashe wayar sannan ya Umarci Sayyada da ta mayar wa da Amina zobenta tana zum'bura baki tace"Zoben baya hannunta tunda ta cire a cikin aji ta neme shi ta rasa. Malam Bashir dai yasan karya take saboda kar yaja maganar tayi tsaho yasa yace su koma aji Sayyada ta duba ko ina mutukar bata ga zoben nan ba to sai ya zaneta.

To koda suka koma aji bata sauya zani ba don Sayyada habaici ta dinga yiwa Amina tana fad'in "Duk abunda xa'ayi sai dai ayi amma ba xata bada zobe ba.

Ita dai Amina bata ce mata komai ba ta zauna cikin kawayen ta kunya duk ta isheta ganin irin kallon da wasu suke mata.

*****

To haka suka cigaba da rayuwa tsakanin Sayyada da Amina babu jituwa kullum fad'a kuma Sayyadar ce ke takalo fad'an har ta kai ta kawo suka daina kula junansu saboda Sadam! wanda shi da suke abun dominsa ma bai san sunayi ba.


" Oyoyo Yayana" Oyoyo sannu da zuwa." Sayyada ke wannan ihun tana tsalle tun sanda taji Sallamar Sulaiman a 'kofar su da gudu taje ta rike hannunsa shi kuma ya dan rungume kafad'anta fuskarsa dauke da murmushi wanda ya kara masa kyau da kwarjini yana mata wani irin kallo yace."Babyna kece kika girma haka.'"! Cikin kunya ta rufe fuskarta tana kokarin kar'bar jakar kayansa....Murmushi ya saki yana d'an shafa siririn sajen sa yace."Masha Allah babu shakka Baba Ladi ta iya raino akwai gwaggwa'bar kyautar da zanyi mata." Baba Marka ta d'aga labule ta fito daga d'aki tana fad'in"Murya wa nake ji ne kamar ta soja." Da Sulaiman tayi tozali tace."Au! ashe bature ne to sannu da zuwa lallai yau za'ayi ruwa da 'kankara *Dabi* tana da babban 'bako." Sulaiman yace."Kwarai kuwa baba yau naso nayi suprise d'in ku ne shiyasa kawai kuka gani ba tare da kunyi tsammani ba." Baba Marka na shimfid'a masa sabuwar tabarma tace"Aikuwa dai munyi mamaki kwarai da alama ma zaka kwana biyu a garin tunda na ganka har da guzirin kaya." Yace."Zanyi sati biyu insha Allahu kafin in koma, wai ina d'aya matar tawa ne."!? Yana nufin Baba Ladidi Sayyada tace"Yanzu yanzu ta tafi sabuwar kasuwa, amma dai nasan yanzu zata dawo."
Yace."Okey. Baba Marka tace"Bari in dama maka fura kafin a d'ora abinci." Yace."Nagode Baba sosai nayi kewar wannan furar taku mai dad'in gaske." tana dariya ta mike ta shiga daki....Sulaiman ya tsirawa Sayyada ido yana kallonta sosai yake masifar son yarinyar a cikin ranshi yana ganin idan da babu maganar aure a tsakaninta da 'kaninsa da babu abinda zai hanashi auranta sonta ya riga ya zama jinin jikinsa.

Rife fuskar ta tayi tana murmushi tace"Wayyo Yayana wai na sauya maka ne naga sai kallona kake tun da kazo." Ya saki murmushi mai kyatarwa yace."Sosai kika sauya min Sayyada kin girma kin zama cikakkiyar mace alhamdullahi ina rokon Ubangiji ya baki miji nagari wanda zai kula dake."
Murmushi kawai tayi tace "Yayana ina auntyna." Yace."Tana nan lafiya lau da da tare zamu zo to saboda yanayin jikinta ne ya sanya nace ta bari sai ta haihu sai na kawo ta ta kwana biyu tare daku."

"Wayyo Allah ashe auny Luba ta kusa haihuwa kai gaskiya naji dad'i wallahi Allah ya sauke ta lafiya." Yace."Ameeen ya rabbi Sayyada ya karatu ina fatan kina mai da hankali ko." ? Tace"Eh Munayi yayana A dai taya mu da addua."Yace."Idan kina so in tafi dake can kaduna mana sai ki cigaba da karatun ki a can ni sai nake gani kamar bakya mai da hankali anan." Jiki a sanyaye tace"Wallahi ina karatu Sosai Sai dai kasan makarantun cikin birni da irin namu ba d'aya bane amma nima ina ganewa sosai." Yace."Okey zanzu kuna jiran jarrabawa ta fito kenan." Tace"Eh kuma isilamiyya ma mun had'a izifi ar'bain." Yace."Alhamdullahi to kafin in koma za muyi karatu ni dake sai in gani shin da gaske kike kina fahinta ko kuwa." dariya tasa tace"Tom ai kuwa zan baka mamaki."! Mikewa tayi tace"To bari dai in dora maka abinci ko." murmushi yayi ya bita da kallo yana ayyana abubuwa da dama a kanta.

Baba Ladidi ta shigo da daurin buhu a hannunta wani a kanta tana ganinsa a ki shingide ta saki fuska da fara'a ta karaso tana fad'in"Ashe bature ne a gidan namu sannu da zuwa ai jikina yayi ta bani dama zanyi babban bako." mikewa yayi zaune yana mata sannu da zuwa tare da bin buhuhunan da take ajiyewa da kallo.
Mayafin dake saman kanta ta cire ta rataye a giya tace"Sayyada kawo min ruwa nasha kafin mu gaisa da mai gidan nawa." Sayyada ta mika mata ruwa cikin kofi da ta d'ebo a randa Baba Ladidi ta shanye ruwan tas ta aje kofin kafin kice kwabo gumi ya yanke mata sai ta fara neman mafici Sayyada ce ta mika mata ta hau fiffita tana fad'in"Kai nasha rana wallahi ai da yake yau juma'a shine kowa ya fito ya ci kasuwarsa amma ai bukata ta biya tunda na samo abinda nake so."! Yace."Wai Baba daga ina kike haka kin dauko rana gaki dauke da buhuna sai kace wacce zata bar gari."


Baba Ladi ta gyara zama tare da jawo buhun da ta shigo dashi tana fad'in"Naje na d'an yo sare-saren kayan siye da sayarwa kasan zama babu sana'a babu dad'i ko yaya kana d'an motsawa sai kaga asirin ka ya rufu."

Yace."Idan na fahinta kina so kice asirin ki a tone yake yanzu."!? Tace."Oo!! ni ban fad'a ba ni nace asiri na a tone yake ai idan nayi haka nayi wa Allah butulci.'' Yace"To meye kuma zaki dinga d'aukar rana kina shiga kasuwa salon ki jawo mana zagi menene ba a siya muku na abinda kuka bukata."? Tace"Sulaiman rabu dani don Allah nifa ba zan zauna haka kawai na rungume hannuna ba bana sana'a kawai sai in dogara da wani kuje ku ri'ke abunku ni ku barni na nemi kud'i na." Girgiza kai yayi yace."Ai kaji irinta ita baba Marka me yasa bata sana'ar sai ke ? ke dai kawai kice kina da son kudin tsiya kuma haka zaki tara mana ki tafi ki bari."

Tace"Eh ai haka yafi akan in mutu mutanan gari na fad'in ban bar muku komai ba. Sai dai duk abinda zakuyi kuyi sana'a kam yanzu na fara wancan miskilin ma da ya fika 'bakar zuciya yayi ya gama kuma ya hakura ya kyaleni bare kuma kai."! Dariya ya sanya yace."To ai shikkenan Baba kiyi sana'a Allah ya bada sa'a." Tace"Ameen."

Baba Marka ce ta fito daga daki dauke da kwanon sha ta damo fura tayi luwai taji nono mai kyau ta aje gabansa yace."Ina godiya Baba gyara zamansa yayi ya sanya ludayi ya fara shan furar cikin nutsuwa.

Baba marka tace"Ashe kin dawo to ya kasuwar yau dai da alama babu cikowar jama'a naga kin dawo da wuri." Baba Ladi tace"Aikam akwai cinkoso Allah ne kawai yasa zan dawo da wuri na samo mangwaro masu kyau da za'ki irin wanda yara suke so."

Baba Marka tace"Aikuwa yanzu xaki ga ya 'kare yara da son mangwaro." Baba Ladi ta zazzage buhun mangwaron tace"Kinga irinsu so."!? Da sauri Sayyada tazo gurin tana fad'in"Gaskiya baba mangwaron nan zaiyi za'ki."! Baba Ladi tace"Maza jeki dauki wannan katon farantin ki kasa mangwaron a ciki kije can bakin darbejiya ki zauna wannan mangwaron ba yara kad'ai ba har da manya sai sun siya saboda yana da 'kwari."
Baba Marka tace"Aikuwa dai gaskiya yau kinyi sa'ar zuwa." Sayyada ta dauko katon faranti ta shiga jera mangwaro akai Baba Ladidi tace"Guda daya naira goma shida hamsin." Sayyada tace"To fara bani nawa in sha tukkuna."Tace"Kije ki dawo gashi na ajiye miki masu za'ki." hijab din ta ta zara ta zura ta dauki katon farantin dake ciki da mangwaro zata fita Sulaiman yace"Ke Sayyada dawo da kayan tallan nan." Sai taja ta tsaya ganin fuskarsa a hade yasa jikinta yayi sanyi sam bata son taga yana fushi da ita sai ta dawo ta zauna....Ita kuma Baba Ladidi ta hau zazzaga masifa kan bai isa daga zuwansa ya hanata abinda takeyi ba har da cewa Ubansa ma yayi kadan bashi ba, shi dai sulaiman baice mata komai saboda yasan halin jarabar ta bayan ya ci abinci ne sai da ya tabbatar Sayyadar ta tafi isilamiyya sannan ya fita daga gidan kai tsaye gona ya nufa inda Kawu Tanko yake....! Sosai ya nuna masa 'bacin ransa kan ya akayi suka sake har Baba ke fita cikin kasuwa tana sare sare sai kace wacce ta rasa ci da sha sannan babban abin damuwar yanda take dorawa Sayyada tallah wannan ai zubar da mutumnci ne, Kawu Tanko yace"Shima ba a son ransa hakan take faruwa ba Baba dai mahaifiyar sa ce dole yayi mata biyayya amma yana ganin wannan karon dole yayi ta maza tunda dai abin nata na kokarin wuce gona da iri sannan maganar tallan da take d'orawa Sayyada kuwa zai sanar da ita cewar zai je ya shaidawa iyayenta tunda dai su basu suke da iko da ita ba yasan can gidan maigarin basu san abinda ke faruwa da tuni sun dauki mataki kan al'amarin domin kankaro da martabarsu tabbas ya fada mata haka yasan zata daina dora mata tallah tinda itama bata so mutuncin ta ya zube a gurin mutane.
Sulaiman yace"Wannan hukuncin da ka yanke shine ya dace tuntuni a dauka a kanta.....Sai daf da magariba suka nufo gida a tare abin mamaki suna dosowa layin suka hango Sayyada gindin darbejiya tana sai da mangwaro Talle na zaune a gefanta sai hira suke...Kawu Tanko yace."Ka gani ko Sulaiman duba ka gani." Sulaiman ya kalli inda yake nuna masa hankalinsa ya tashi ainun kai tsaye gurin ya nufa ransa a 'bace!


Talle na ganin ingarmar namiji ya doso gurin sai yayi sauri ya mike duk a tunaninsa ko Sadam! ne domin bai manta da marin da yayi masa a watannin baya sai da Sulaiman ya karaso gurin sannan ya gane bashi bane domin shi wancan yafi wannan fad'i da murd'ewar jiki sannan bai kai hasken wannan ba amma dai duk da haka dole ya kiyaye domin ya lura shima wannan d'in babu sauk'i a fuskarsa.Gurin yayi saurin bari Sayyada na kwala masa kira yazo ya 'karbi sanjinsa yace."Ki rike na bar miki." Tace"To nagode." Sulaiman yace"Sayyada ashe kema baki da kamun kai ashe baki san ciwon kanki ba Sayyada! bayan fitata ashe dai sai da kika d'auko tallan mangwaro kika fito bakin bishiya shin wai me kuke nema ne ke da Baba Ladidi? babu rashin ci babu rashin sha babu rashin suttura kuke nema ku zubar mana da mutunci a gari dai dai gwargwado muna sauke hakkinku banji dadin abinda kikeyi ba shin wannan saurayin da yake zaune a kusa dake meye matsayinsa a gurinki.'!? Tana kuka tace"Saurayina ne Talle." Sai yaji gabansa ya fad'i! Yace."Saurayin ki ne Talle ."!? Daga kai tayi girgixa kansa yayi yace."Dauko kayan muje gida." Ta sunkuya ta dauki farantin mangwaron suka nufi gida Sulaiman takaici na cin zuciyarsa dole tilas kafin ya bar garinan ayi wacce za'ayi Dole ne Sadam! yayi wani abu akan lamarin nan sam! shirun da yayi bashi da wani amfani kawai ya fad'i abinda yake ransa shin yana son yarinyar nan ko baya so idan baya so to babu shakka shi kam kafin ya koma bakin aiki sai ya tabbatar da cewar an d'aura masa aure da ita ya tafi da matarsa inda yake da wannan tunanin suka isa gidan

Kawu Tanko na tsugune gabanta yana magana 'kasa-'kasa da son ya fahintar da ita cewar abinda takeyi ba dai-dai bane ita kuma sai furjewa takeyi tana kawo 'kauli da ba'adi! Sulaiman najin tababar da suke yace."To shikkenan tinda kin'ki fahinta mu zamu shigar da 'korafin mu gaban maigari in yaso sai ki fad'a musu dalilin da ya sanya kike d'orawa 'yarsu tallah."! Ai sai ta fashe da kuka tana fad'in Sulaiman bashi da kunya yana kokarin zaginta ya fad'a mata magana in dai kan Sayyada suke wannan maganar to ta zare hannunta daga kanta.

Sulaiman yace."Shikkenan kin gama magana tace"Ban gama magana ba ai tunda kunce Sayyada ba zata yi min tallah ba to sai ku sanar da wancan miskilin mai kafirar kafiyar tsiya ya fito a daura auran in daina ganinta a gabana idan kuma ya'ki to wallahi nima ba zan daina d'ora mata tallah ba."

Sulaiman yace"In dai wannan ne babu matsala ni da kaina yanzu zan kirashi a waya mu gama magana nima nagaji idan yana so ayi dashi idan baya so sai ya barwa masu so ko ba haka ba Kawu."!? Kawu Tanko yace."Kwarai kuwa maganar nan itace gaskiya amma ka fara sanar da mahaifinka halin da ake ciki idan da hali ma yazo sai ayi maganar shima Sadam! din yazo a taru guri guda a tsayar da maganar." Baba Marka tace"Wannan itace shawara mai kyau." Sayyada kam d'aki ta shige ta dauki pilo ta rungume tana lumshe ido hakika tana son Yaya Sadam! taji dadi kuma da manya suka shiga cikin maganar dole ko ya'ki ko yaso ya aure ta tinda manya sun sanya baki yanzu Allah Allah take yazo garin ayi wacce za'ayi.


Sulaiman na shiga masaukinsa ya fara neman numbar wayar Sadam!! Sai da ya kira sau kusan hudu bai dauka ba sai ana biyar d'in sannan ya dauka gaisawa sukayi babu yabo babu fallasa domin dama can babu wata kyakkyawar jituwa a tsakaninsu....Sulaiman yace."Tuntuni nake kiran wayarka ka'ki dauka saboda wulakanci ko."!? Sadam! ya dafe kansa cikin 'kosawa yace."Shikkenan mutum bashi da wani uziri a rayuwarsa lokacin da ka kira wayar nan ina tare da mutane ne kai ka fiye 'korafi wallahi."! Yace."Okey ba wani abu bane dama Kan maganar Sayyada ne yanzu haka ina cikin *Dabi* kuma duk naga abinda ke faruwa da Sayyada shin wai kai a wace matsayar ka tsaya ne kan al'kawarin daka d'auka a kanta."

Ransa ya d'an 'baci da jin abinda d'an uwan nasa yake fad'a yace."Ban gane abinda kake nufi ba."!? Sulaiman yace."Ina nufin ya maganar auranka da Sayyada zaka aure ta ko yaya? muna so muji magana guda daga bakinka." Kai tsaye! yace."Ba zan aure ta ba."!!! Sulaiman yaji wani iri a jikinsa....Yace."Ko zaka fad'a min dalili."? "Bani da lokacin wannan magana a yanzu akwai aiki a gabana."! Sai ya kawai ya kashe wayar takaici ya cika zuciyar Sulaiman Sadam! zai aikata abinda ya fi haka yanzu dai dole ya sanar da mahaifinsu halin da ake ciki a waya ya kira shi ya sanar masa da abinda ke faruwa Alhaji Auwal yace." Insha Allahu zai shigo garin domin ayi magana d'aya saboda shima al'amarin ya soma damunsa kuma dole ne Sadam! d'in yazo shima ayi zaman dashi kowa yaji ta bakinsa. Da wannan maganar sukayi sallama da juna.

Da 'kyar! Alhaji Auwal ya shawo kansa kan cewar ya iske su a can *Dabin* da da farko yayi ta kawo Uzirirrika Alhaji Auwal yace"Duk wani Uzuri da yake dashi tilas ya aje yaje Kiran da ake masa ba yanda ya iya tilas ya shirya tsaf ya nufi garin Jigawa cikin 'kauyen *Dabi*


****

Sayyada najin ance yazo ta fito daga daki ta cika bokiti da ruwa a gurguje tayi wanka ta fito sabuwar atamfar ta tasa ta gyara dogon gashinta sosai sai kyalli yake daurin dankwali tayi mai kyayatarwa ta fesa turare mai sauki kamshi idan ka kalleta ba zakace a kauye take ba saboda tana da d'an waye wa ba kamar Amina ba Sayyada na 'kawance da 'yan matan da suka girmeta shiyasa tasan komai na fanni aure domin idan sun zauna yasu yasu basu da wani zance sai na aure da yanda ake rayuwar aure.


Sadam! bai wani samu tar'bar arziki ba kowa haushinsa yake ji yaga duk suna binsa da kallo kamar wanda yaci bashi zama yayi gefan dan uwansa ya mika masa hannu suka gaisa sannan ya gaishe da iyayen nasa da kakanin nasa, Baba Marka tace"Bari ka fara cin abinci tukkuna sai komai ya biyo baya." Abinci taje ta kawo masa da ruwan randa mai sanyi ta aje a gabansa ganin towon shinkafa ne da miyar taushe yasa ya zage cikinsa yaci ya sha ruwa sannan ya kauda kayan abincin dake gabansa guri ya nutsu Alhaji Auwal yace."Abinda yasa kaga mun taso ka daga gurin aikinka da gaggawa magana ce mai muhimanci kuma wannan maganar itace karshen magana a tsakaninmu da kai insha Allah, maganar ba wata sabuwa bace nasan idan kai mai fahinta ne zaka gane inda na dosa to amma dai yana da kyau mu sake fad'a maka shin dukaninmu anan muna so mu san inda maganar auranka da Sayyada ta kwana shin zaka aureta ko kuwa."?







1/6/2020




*BINTA UMAR ABBALE*




_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kudi ne 1_2 #400 ga duk mai bukatar karantawa sai ya tura kudinsa ta wannan accont din......0542382124.......Binta Umar gtbank idan kuma katin waya mutun zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din zan fad'a masa yanda zai biya kud'in....08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar littafin to sai ku tura dala dari ta wannan numbars.....90899076 _88137740 katin airtal ko orange.....Dala dari itace a madadin dari uku na najeria.*_
[6/12, 12:15 PM] Bintu: *NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*


*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________


Free Pege 11

Shiru yayi tare da sunkuyar da kansa Alhaji Auwal yace."Da kai nake magana kaji abinda nace kuma ka sunkuyar da kanka 'kasa, shin ya maganar auranka da Sayyada."!? Ya kara maimaita masa maganarsa ta farko.

Ys dago kansa sam babu walwala a tare dashi yace."Abbah koma meye a tsakani na baku wu'ka da nama ni bani da ta cewa akan wannan al'amari."

Baba Ladidi tace"Bamu gane wannan maganar taka ba so muke kayi mana bayani yanda zamu gane inda ka dosa ba kace ka bar mana komai a hannunmu hakan yana nufin ko auran aka daura itama Sayyadar zaka bar mana ita kenan."

Yace."Iya abinda zan iya cewa kenan saboda nasan idan nace muku ga ra'ayi na ba zaku amince ba ni na hakura zan bi ra'ayin ku na amince da auran Sayyada."

Baba Marka tace"To yanzu kayi magana mai ma'ana." Sayyada na bakin kofar daki a la'be taji lokacin da yace ya amince zai aureta sai ta ruga daki da gudu ta kwanta kan gadon karfe na Baba ta ringume pillo tare da lumshe ido tana murna da farin ciki itama zatayi aure taji abinda su Sakina sukeji kullum idan sukaje gidan kawarsu Sakina da akayi mata aure babu hirar da sukeyi sai ta aure Sakina tayi ta basu labarin yanda ake kwanciyar aure da dad'in da ake ji....Sayyada tayi ta mutsu mutsu a lokacin tun bata gane sha'awar namiji ba har ta gane domin duk lokacin da zasuje gidan Sakina suyi irin wannan hirar haka take wuni jikinta a sanyaye tayi ta shiga bandaki tana wanke gabanta.....Duk sanda ta tuno Sakina tace musu mijinta na tsotsar mata nono sai tayi ta mamaki! Sai ta dinga hango Sadam! itama nayi mata haka idan kuma ta kalli gallafirin nonon nata sai taji rashin dad'i domin a ganinta ba zai ta'ba cika masa hannu ba duk da ta girmi Amina ta fita nono sai dai kuma ita tafi Aminar fad'in 'kugu da d'amamman ciki tamkar wacce bata cin abinci....


Baba Ladidi ce ke ta rangwada bud'a tana fad'in"Alkawarin Allah ya cika babu shakka Sadam! baka ta'ba burgeni ba irin yau insha Allahu zakaji dad'in zama da Sayyada kai dai kawai abinda zance maka shine ka kyautata hakuri Allah ya sanya alkairi."

Sulaiman kuwa tun sanda Sadam! din ya nuna amincewarsa kan auran ya kasa d'ago kansa so yake kawai ya dai-dai ta kansa sam baya so su fuskanci halin damuwar da yake ciki hakika zai sha fama da zuciyarsa mutukar Sayyada ta kufce masa....Hankici ya ciro ya goge gumin fuskarsa ya d'ago kansa suka had'a ido da d'an uwan nasa wanda yaso ya fuskanci wani abun amma kawai sai ya basar ya dauke kansa 'karshe ma tashi yayi ya bar gurin Sayyada na hango abinda ke faruwa a tsakar gidan tana ganin ya bar gurin ta fito tana 'boye fuska, Alhaji Auwal yace."Kunyata ake ji ne Sayyada."? Fuska a rufe ta gaishe shi taje bayan Baba Marka ta 'buya ranta fari tas tas Allah ya kusa cika mata burinta Amina kuma sai dai ta mutu da ba'kin ciki.

****
Kwata-kwata Sadam! baiyi niyyar kwana ba a garin yaso kawai ya juya tunda ya gama abinda ya kawo shi dukaninsu suka nuna rashin amincewar tafiyarsa sai ya hakura kawai yabi ra'ayinsu ya bari sai da safe sannan ya dauki hanya.......Karfe goma sha d'aya saura na dare yayi sallama da majalisar su Bashir malamin su Sayyada kenan na isilamiyya kai tsaye gidan ya nufa....Shiru lokacin da shiga duk suna kwance a tsakar gida kasancewar lokacin zafi ne Baba Marka da Baba Ladidi da Sayyadar Alhaji Auwal kuwa da Sulaiman suna can 'bangaran Kawu Tanko can zasu kwana.....Hasken wayarsa ya kunna yana haskasu can ya hango Sayyada na motsi idanta biyu dama taji lokacin da ya shigo kunyar tashi take kasancewar rigar dake jikinta 'karama ce mai hannun shimi dake sam bata son zafi duk da ta kasance siririya sam bata kaunar zafi shiyasa idan zata kwanta take sanya karamar riga don tasha iska....Ganin tana motsine yasa yayi saurin dauke hasken wayarshi daga kanta ya nufi masaukinsa.

Sayyada ta bishi da kallo tana lumshe ido....Yana shiga dakin ta mike da sauri ta shiga dakin Baba Ladi,

2 Comments On NI DA YAYA SADAM
avatar
hauwa-abdullahi

1 year ago

Reply

I love the story

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to hauwa-abdullahi

Thanks be with us for more stories

Please Login or Register in order to submit comment