Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Magana cikin nishin * da ya fara da shi,

“Bisa wane dalilin ka taso ni ina baccina,. me yasa ku bil adama ba ku cika tausayi ba ne?”
Salmanu ya marairaice murya cikin ladabi’ ‘ -yace, ; “Wani bahagon aiki ne ya zo gabana ranka ya dade, dole na kira ka, ka zo ka sanya hannu ka ceci mutuncin baiwar Allah na…” : ‘. ° Kafin ya rufe baki Adamu ya amsa da . wata irin dariya, ya ce, a “Wai Kumbo da ke zaune gabanka?” , Salmanu ya dago ya kalli Kumbo wadda _ razana ke sata jin neman sakin fitsari a wajen,


sai dai can cikin zuciyarta cike take da farin cikin abinda ke faruwa, wannan sabon bokan nata da manyan aljanu yake aiki wadanda suka sanin da matsalar da ka zo da ita. . Salmanu ya ce, . . – “Ita ce ranka ya dade” -To ka fada mata ta tashi ta tafi gida, da mijinta aka hada baki aka cuce ta” , Salmanu ya marairaice Murya,.= “Ita da tazO neman waraka wajen manya irinku ai ba kwa kora ta ba Ranka ya dade” ‘ – “A taimaka min” . . ‘ka shiga maganar cikin .barin jiki. ’ Adamu yace, “Ina buhun dankalin turawan da ya kawo. miki kamun azumi?” Hajiya Kumbo ta shiga tunani. Ta tuna cewa duk wata mijinta buhun dankali yake direwa kasancewar gidansu na mutane, amma watan azumi har buhuna-hudu yake direwa a raba wa makota buhu biyu, azumin da ya gabata satin kama azumin ya kawo dankalin. ‘ Nan da nan ta gyada kai, “Eh na tuna, buhu hudun nan ko?”

Adamu ya amsa cikin dariya da ihu. “yauwa so! Kin san daga hannun wa suka fito?”? , Ta gwalo ido tana girgiza kai, – “Ban sani ba ranka ya dade” _ — Adamu ya amsa, “Daga hannun Hadiza matar mijinki suka fito, shiyasa na ce duk abinda aka yi miki da — – sanin mijinki..”’ Hajiya ta saki wani irin nishin fargaba ta ce, “Oh ni Allah! Alh. ya ci amanata…” * Adamu yatareta, _—. _ “Duk asirin da zata yi miki ta hannunsa take kawo miki shi take bawa ya kawo miki a zuwan daga gare shi ne, amma lamfa kawai suka yi miki dukkansu, suna nan suna niyyar _ tarwatsa miki rayuwa.. Sai ga Hajiya na son Barkewa da kuka,

– “Na Tuna da haka wallahi, don a da Alh. komai na gindaya ba ya musawa amma yanzu ko jinjirin jaki haka ya ganshi akan yadda yake jayayya dani”

““Ai ta gama da shi,kiris take jira ta Karasa kassara ki, ko yanzu gata can na hango ta zaune gaban wani matsafi suna shirin yo miki aike…”

Hajiya ta dora hannu aka tana ambaton na shiga uku, . Adamu ya cigaba da ruda ta, “Rannan da kika tsefe kai an turo Duna ya saci gashin kanki, gashi can ana kullewa a cikin kwai za a jefa teku, in har hakan ta * kasance to ke da mujiya ba bambanci a idon mijinki”.- Hajiya ta sake rikicewa ta cigaba da kuka . haikan tana roKo da a taimake ta. Sai da Adamu ya. gama tabbatar da imaninta sannan ya ce mata, .

“Zauna ki dakata a nan, na san Aljan Cunkokuwaso za su tura ya je tekun, ni kuma zan tura Migadir ya Kwato ya kawo miki nan ki gani” so,

Da haka Adamu yayi musu Sallama yayi

nishi ya Bace. . Hajiya ta kife kai wajen tana ta faman – kuka, Salmanu kuma yayi Kus yana sauraronta

a zuciyarsa yana saKa yawan kudin da zai wafta. . ; a . Damuwarta ya sanya bata kula da lokacin da Salmanu ya dauko farin kwan kazar gidan gonarsu ba wanda suke da irinsa ya kai hamsin, yadda suke wa Kwan shi ne, suna_ tsaga shi daga Kokolinsa cikin hikima da wata siririyar aska yadda ba zai fashe yayi baraguzai ba, sai su zazzage ruwan su cusa tarkacen da suke so, _ Wani su sa gashi wani allurai, wani sucusa danyen nama wani kyanyasai, wani kuma su. hada gashin da rowan Kwan, sai su mayar da | murfin su like da gam ko super glue yayi ~~ tamkar ba a taba bude shi ba. To Hajiya mai gashi hade da rowan kwai aka dauko mata wanda zuwa yanzu yayi wari. Salmanu yayi tafi da hannu dan janyo hankalinta kasancewar ta kife kai tana ta faman kuka shi kuma yana ta faman Magana ba ta san yana yiba, “Magadir har ya kawo Kwan ya wuce kina faman kuka, ban da abinki meye na kuka bayan. kin gamu da Sarkin Aljan ShakaKiriro ya shiga aikinki da kansa?” . Hajiaya ta hau murzar ido tana kallon Salmanu,

Ya mika mata Kwan ya mika mata wata tasa yana cewa fasa shi mu gani,

Ta karba da Kwarin gwiwarta cikin dokin ~ fasawar, don Allah Allah take ta fasa shi ta san fasawar ce tarwatsa asirin da kishiyar tata ta yi. mata ko take shirin yi

Bayan ta fasa, ba,ita ba hatta Salmanu sai_ . da ya toshe hanci saboda azabar doyi, ya dinga tari yana Karawa da shegantaka, ita ma , hancinta toshe tana bin fasasshen Kwan da kallo, sai ta ga tabbas ma gashin kanta ne, hatta kududunen da tayi masa kafin ta watsa shara yana nan ba su ware ba.

“Malam ka taimake ni mana, me ye abin

_ yi yanzu? Ga sharrinsu dai an dauko shi” .

Tana nuna rubabben Kwan da ta fasa

“Ki tashi ki je gida zaki ga aiki da cikawa, ShaKaKkiriro ya zuciya sosai, na san ba sai an bashi zabi ba, ba zai wa Hadiza da kyau ba”

Cikin farin ciki da doki ta ce,

. “Allah ya sa, ni ko kashe annamimiya ma yayi ita ta sai wa kanta”

“Na fada miki ba sai kin bashi zabi ba, ke dai ki dawo nan da sati guda” Ta shiga zuge jaka cikin jin Kwarin — gwiwa. Salmanu ya dinga satar kallonta yana , tunanin ta inda zai bullo mata in ta ba shi abinda ba shikenan ba. ; . “Malam nawa zan bayar kafin alKalami” Salmanu yayi fuska iyakar fuska, . ~ “Ki bada dubu hamsin” : Ta dan ji dukan zuciya, amma da ta tuna ° bokanta na baya wanda ko kama Kafar wannan bai ba shi kansa yana cajar sama da haka kawai. – sai ta zage jaka ta ciro ta miKa masa, ya tura_ mata wani faifai ta ajiye a kai sannan ta tashi tana yi masa godiya ta fice. Sai da ta jima da fita sannan Adamu da Tanimu suka fito maboyarsu suka shiga hayaniya da ihun murna tamkar sa Balla dakin. Tanimu ya dubi Salmanu yace, : “Yanzu kai Salmanu tuni ka san da ‘_wannan sana’ar ka bar mu muna ragaita a titi?” . ‘* “Rabonmu ne ke nesa” Salmanu ya amsa cikin farin ciki.

Adamu kuma ya ce, ; “Ni kam yanzu na nade hannun riga zan fara sana’ar nan, ko kun tuba ni kam zan Zarce” Cikin shegantaka Tanimu ya ce, , “Ai tuban tafi-da-gidanka zamu dinga yi, muna aikinmu muna tuba, Allah sa su ma masu zuwa wajen namu su dinga zuwa tafe da tubansu” — . Cikin sati daya sana’ar tasu ta shahara, .* Tanimu na da ido a sanin mata da ‘yan siyasa_ kasancewarsa dan bangar siyasar da ya tuba ya ~ fada bokanci, don haka shi ne mai kawo musu_mutane, mata da Alhazai, ‘yan siyasa da ‘yan . kasuwa, su ma a junansu duk wanda ya zo ya sha basaja, aka sace imaninsa in ya tafi sai ya _ fada wa amininsa wani shahararren boka ya bayyana, shi ma in-yazo sai ya fada wa nasa Aminin ta haka tafiyarsu ta fara nisa. .

*************

Tun bayan kwana hudu da auren Salma da Adamu aka kamala duk gyaran da za’a yi wa

gida, aka yi jere aka kuma zuba kayan kanti aka kai wa Adamu Salma kwana goma sha daya da auren. Ranar da za’a kai ta da safen ne Alh. ya shammace shi ya biyo shi gida bayan sallar – asuba, kasancewar kullum daga ya dawo sallar asuba yake shiryawa ya fice, ba za’a Kara ganinsa a gidan ba sai bayan sallar isha, -wataran ma har Karfe goma yana kai wa. Babu ko sallama Alh. ya bankada masa ». Labule ya bi bayansa. . . Suka yi cirko-cirko a tsakiyar dakin suna kallon juna, fuskar Adamu da fishi, fuskar Alh.. _ na nuna halin ko in kula. . Alh. ya sanya hannu a aljihu ya ciro mukullai ya miKa wa Adamu, “Don Allah ka taimaka idan ka dawo ka zarce gidanka, yau za a kai maka matarka” Adamu ya miqa hannu saroro ya amshi makullan, ba tare da ya tanka ba, ya dinga motsa baki kamar yana so ya gode wata zuciyar na kwabarsa cewa bai kamata a cuce ka kuma ka yi wa macucin godiya ba, da haka_ . ya biyewa zuciyar ya Ki godewa, kuma ya Ki

tankawa har Alh. ya gaji da jiran cewarsa ya . kada kai ya juya ya fita cikin kada kai da murmushin mamaki

Adamu ma ya dauke ido daga kallon wucewarsa zuwa kallon mukullan hannunsa, wasu irin abubuwa na zagaya kansa a guje, suna raya masa cewa, ba wai rayuwarsa ce kawai take shirin canjawa ba, shi kansa Adamu ake son acanja. _

Wai shi ne da ya sha mafarkan bacci da ido biyu a auren mace daya kacal wato Husna, shi ne kuma yau da auren wata macen wai ita Salma? Abin sa kuka amma ba hawaye.

Bai bari wata damuwa ta ci Karfinsa ba ya. shirya ya fice harkokinsa. Bai sanar wa

. Salmanu komai game da tarewarsa a gidansa ~ da sabuwar amarya ba, sai da ya tashi tafiya Karfe tara darabinadare, .

“Au! Kai yau fa zaka raka ni siyen baki”

Ya fada wa Salmanu cikin yafe da KoKarin hadiye damywa.

Salmanu ma ya dabe shi cikin mamakin da yake son shanyewa,

“Wai da gaske kake mantawa ka yi ko – kuma tsabar basarwa ce?” Adamu ya hada da dariyar yaKe, “Oho! Ni ma ban san takamaimai a ciki ba” Salmanu ‘ya kame hannu ya rungume a kirji yana bin sa dakallo, To Allah kiyaye hanya, Allah ba da – juriya mai kyau” Adamu ya yi saurin dubarsa saroro, ; “Au wai ba zaka raka ni ba, haka zan tafi. zikau ni kadai?” * ; .
Salmanu yayi dariyar Karfin hali,

– “Kai kadai zaka tafi mana, ka manta kai ~ . kadai Salma ke son gani, ko ka manta sharuddan da ta gindaya maka cewa karka sake kazo mata gida?”dani Adamu ya dinga gyada kai alamar tunawa, ~

“Haka nenatuna”. . .

_ Salmany ya ji-takaicin goyon bayan da Salma ta samo a wajen.Adamu, dubi dai yayi . masa gatse amma bai damu ba ya mayar gaske saboda umarnin Salmanu

Amma duk da haka Salmanu bai nuna a fuska ba, sai ya cigaba da dariya yana cewa, “Idan gidan Salma ya zama nasu su biyu Kila a gan ni, in dai zan iya zuwa wajen Husna ba wajenta ba” Nan da nan fuskar Adamu ta rakito walwala, amma dai bai tanka ba. Salmanu bai damu ba ya cigaba da Magana, * « “Amma ‘idan ba ka sami damar auren Husna ba, to har mu Kare rayuwarmu a idon danginka da Salma zamu cigaba da nuna dama munrabu” ~*~ ‘ Adamu ya banka masa harara tamkar idonsa’zai fado sannan yayi gaba yana mita, – ‘ “Ka kwana biyu ba ka zage niba dama, yau in ka yi min muguwar addu’a ba laifi, to in ‘ Allah ya ba ni Husna ka hana mana” – Ba tare da sallama ba ya fice daga dakin. _ Salmanu ya bishi da kallo cikin tausayi tare da Kara Kullatar Salma. . “Allah ya tsine miki Salma” Ya fada a fili kuma har cikin zuciyarsa so yake Allah ya amshi addu’arsa.

Kamar kullum duk wani abu da ya danganci Salma zuciyarsa ba ta _bashi muhawara bare ya tantance ya zaba, kai tsaye daga can saman zuciyar tasa wani ke bashi zabi. ya aiwatar bisa dole. ° ‘ Yau ma ya so ya ji bijrewa da nuna wa Salma iyakarta, amma ya ji wancan Karfin na son matsa masa murnar zama angon da yake tafiya ga amaryarsa, hakan kuwa ya je mata har da siyayyar kaji da kayan jiKa maKoshi. Ya’ dinga nuna mata doki da zumudi tamkar dama ita kadai ce sauran burinsa a duniya ya kuma samu.

“Ban san kana sona haka ba Adamu”

Da kalmomin da ta dinga zolayarsa da su kenan, shi kuma yana amsawa tsakaninsa da_ ‘Allah,
“Yanzu kin sani Salma, ina son ki fiye da -son kowa a duniya”

In ya fadi haka Salma na jin wani munafikin hawaye na kurdo mata ta samu ta goge abinta, abinda take so kenan wato Adamu, ta kuma samu, in ba shi kadai ne burinta a duniya ba tana jin dai ya fi rabi.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
MUN TSAYA

Kamar kullum duk wani abu da ya danganci Salma zuciyarsa ba ta _bashi muhawara bare ya tantance ya zaba, kai tsaye daga can saman zuciyar tasa wani ke bashi zabi. ya aiwatar bisa dole. ° ‘ Yau ma ya so ya ji bijrewa da nuna wa Salma iyakarta, amma ya ji wancan Karfin na son matsa masa murnar zama angon da yake tafiya ga amaryarsa, hakan kuwa ya je mata har da siyayyar kaji da kayan jiKa maKoshi. Ya’ dinga nuna mata doki da zumudi tamkar dama ita kadai ce sauran burinsa a duniya ya kuma samu.

“Ban san kana sona haka ba Adamu”

Da kalmomin da ta dinga zolayarsa da su kenan, shi kuma yana amsawa tsakaninsa da_ ‘Allah,
“Yanzu kin sani Salma, ina son ki fiye da -son kowa a duniya”

In ya fadi haka Salma na jin wani munafikin hawaye na kurdo mata ta samu ta goge abinta, abinda take so kenan wato Adamu, ta kuma samu, in ba shi kadai ne burinta a duniya ba tana jin dai ya fi rabi.

ZAMU TASHI

Cikin sati biyu dukkansu rayuwarsu ta canja, Salma ta mamaye zuciyar Adamu tsab, duk wata mace a waje kallon Bahuwa yake mata, bata da kyau ko bata da kwalliya ko ma gaba daya sunan mata kawai take amsawa. Salmansa ce kadai mace, ita ce kuma Kawai idan an so ba a fadiba. Duk abinda Salma ke so shi yake’ so, wanda kuwa ta nuna bata so nan take yake jin tsanarsa, saboda haka ya zama tamkar da gaske sabon Adamu aka sake fil Ba wancan mai tsanar salma ba kuma ba wancan mai son — Husna a Kirji ba. Salmanu kansa ya fahimci haka, amma dai ya shanye ba ya tanka masa maganar Salma, ko shi ya kawo masa ma sai ya tankwabe shi da cewa, “Yanzu Salma iyalinka ce, bai kamata mu dinga hirarta ba” Da wannan hujjar suka dauke hirar Salma a tsakaninsu, iyakaci in sun hadu su yi abinda. ya hada su su watse. Sai dai manta Husna da Adamu yayi ba Karamin daga wa Salmanu hankali yake ba, .


musamman in ya tuna labarin da Adamu ya ba ‘ shi na yadda suka yi rabuwar Karshe da Husnan, da alwashin daya ci mata na aurenta nan da wata biyu tun a ranar. .


Wannan ya sa ya cigaba da sake-saKen ta yanda zai bullowa wannan bahagon lamarin, har ya fara jin cewa a wanna gabar zai yanke

_ danyen.hukuncin da zai nuna wa Salma

. iyawarsa. .

*****

Sana’ar bokanci ta cigaba da kawo . manyan kudi, don haka Adamu bai yi gigin

. barinta ya zauna a shago ba, kawai sai ya nemi yaro ya dora shi jira, shi kuma ya cigaba da gashi. .


Abinda ma ya takaice shi shi ne, Salmanu ba ya sakar masa kudi yayi yadda yake so ko .’ dan farantawa Salma rai.

Zasu raba kudin rumi-rumi su uku bayan sun ware na sallamar yaran. da ke yi musu hidima da kuma na siyayyar kayan aiki, amma

. kawai sai Salmanu ya daka wa na Adamu

wawaso, ya sunna masa abinda bai taka kara ya ‘ karya ba, ya ce wai zubin adashi suke, kuma wai kantinsa ya isa ciyar da Salma dai ba wata ba. Adamu ba ya son wannan dabi’ar, amma – ‘ dayake ba ya zargin Salmanu da cutar kudi sai yake shanyewa, yana da tabbacin ko ba dade ko ba jima sai ya fito masa da kudinsa. ~

+++++++++++

Sati daya, biyu, uku, hudu, Husna bata ga Adamu ba, tun tana basarwa musamman daidai lokacin da ta ji labarin ya tare da amaryarsa a_ – unguwar Dorayi, ta ci kuka ta ci ciwon ranta ta matse ta koma ta cigaba da zaman jiran ya . waiwaye ta tunda wata biyu ya dibar wa kansa na aurenta, har aka kusa wata daya da rabi ta fara debe tsammani, juriyarta kuma ta sare. Ta cigaba da damuwa ta cigaba da kuka kuma ta -cigaba da ramewa tare da lissafin ta inda zata _ bullowa wannan mugun ciwo daya sarKe ta.

– Rannan dai da ta ji zuciyarta na neman bugawa kawai sai ta wanki Kafa ta tafi gidan fawarta Amina domin neman mafita.


Ta sami Amina da maKociyarta Jamila suna hira cikin farin ciki.

Amina na ganin Husna ta hau salati da sallallami,

“Wallahi yanzu nake zancenki Husna, ai kawai ki zo mu fasa mu ma mu shallo Adamu”

Husna ta zauna kan kujera jagwaf tana bin su da kallon rashin fahimta,

Amina ta shiga yi mata bayani tana nuna Jamila, .

“Kin tuna ranar da jamila ke tatsuniyar son

” mai gidanta ya sai mata mota yana cewa wai

bata da hankali?” so

Husna na dariyar yaKe ta ce,

“Na tuna, yanzu zai siya ne don ta yi hankalin?”

Suka kwashe da dariya su duka ukun.

Jamila ta mika wa Amina hannu suka tafa sannan ta dubi Husna tana kada mata mukullin mota,

“Tun yaushe na yi hankali, Surajo ya ji . Wuya jiyan nan sai ga sabuwar mota ya samfa min” Husna ta zamo daga kujera tana zaro ido cikin mamaki, . “Da gaske? To duka kika fara ne ya gane in bai sai motar ba ba zaki warke ki bar dukan ba?” Suka sake tuntsirewa da dariya. Jamila ta ce, “Wanda: ya fi shi Karfi na sa yayi masa. mahangurba”™Har yanzu Husna na cikin dokin jin labari, ~ ta ce,“Don Allah ku fada min ku bar wana-ni” . Amina ta hau yi mata bayani. “Wallahi wani sabon boka aka samu mai aiki kamar yanka wuka, saboda tsabar son mota na Jamila sai da ta dangane da wajensa, ba a yi sati biyu ba kuwa kin ga har ta yi motar” _ Husna ta shiga gyada kai cikin mamaki da sha’awa,

“Kai! Ku dama akwai malaman Allah da gaske a duniyar nan?” ‘ Jamila ta kada kai, –

– “Wallahi ni ma abinda na yi ta cewa kenan Husna, kawai kasada na yi na je, amma sai ka yi ta zuwa wajen wasu asirin sai ki ga kamar an shuka dusa”

. “Wallahi tallahi” .

In ji Amina, Sannan ta dubi Husna ta zarce da cewa, “Wai gobe zata je yiwa bokan godiya, shi ne na ce me zai hana mu bi ta muma mu kai tamu bukatar? Ke ki kai Adamu, ni kuma zan kai Kamalu a kama min‘shi a hannu, wannan shegen kallon bal din nasa na dare a hana shi, don ni in akwai abinda na tsana a duniya ba zai wuce kallon bal din ba”

. . Husna ta ji wani dum! Kamar abin bai kai zafin haka ba, duk da ta gan son Adamu ba sanyi ne da shi a zuciyarta ba.

“Kar ki ji wani dar Husna, duniya sai da Kundumbala, ki daure ki Basar ki nemi cikar ~ burinki, Salman banza da zata hana ki samin_. . abinda kike so?”

Amina ta Karfafa mata gwiwa da wannan zantukan — . . Sai kawai ta miqa wuya. _ “A wane Kauyen bokan yake?” Ta tambaya. Jamilace ta amsamata “Nan nan Zawaciki yake, hanyar’ . Panshekara” A sanyaye Husna ta ce,To Allah ya kai mu, zan je. Karfe nawa . _zamu tafi?” Amina ta dubi Jamila. A “A motarki fa za mu; saboda haka ki zaba mana lokaci” , Kai tsaye Jamila ta amsa, “Mujeda la’asar’ -Allah ya kai mu” . Husna ta amsa asanyaye.

**********

Da la’asariyyar ranar yau su Adamu na sanya ran zuwan wani gagarumin dan siyasa_ – mai son tsayaawa a takarar dan majalisar taraiya.

kula da kyau fa! Yau muna buKatar ” takatsantsan don kar mu yi abinda kwabarmu zata yi ruwa, kudi muke so.. kun gane?” In ji Oga Salmanu lokacin da suka sami ’ wayar cewa yammar yau ko ta gobe Honorabul zai ZO. _ “Wane .sirrin damfarar zamu gwada masa?” a Adamu ya tambaya. Salmanu ya dan yi shiru alemar tunani. * Karaf Tanimu ya ce, “A yi masa na alkalamin nan, na ga yana dan rudar da kwanya”’ – Salmanu ya bigi kafadar Tanimu, “Yauwa! Ka kawo shawara mai kyau,a_ nemo, alKaluma a fente” – “Adamu ya tashi da sauri ya shige cikin zuwa taskar ajiyarsu. ya bar Salmanu da Tanimu, -Tanimun na yi wa Boka Salmanu bayanin tarihin Honorabul, — nasarorinsa, — faduwarsa da kuma. abokan adawarsa. ‘ _. Adamu ya jima sannan ya fito, “Akwai alaluma, amma babu Kusoshi”.

Salmanu da Tanimu suka dafe kai saboda. . jimami, kasancewar ba a samun Kusar kusa da – su har sai sun hau Mashin sun je Sabon titi. . –

Adamu bai shiga cikin jamamin ba, kawai sai ya sa kai ya fice yana cewa, :

‘ “Barina samo ta yanzun nan nadawo” : Salmanu na kiransa bai saurare shi ba.

Wannan dalilin ya bana Adamu da Husna * haduwa a wajen da dukkansu ba zasu so ganin ~ juna ba.

Tanimu ya shige ciki domin zama kujerar ‘Adamu ko da zata kama ayi muryar aljanu.

Salmanu kuma ya zauna a kujerarsa ta babban Boka. . ~~ –

Kasancewar sun saka dokar ba a shiga mutum biyu, Jamila ce ta fara shiga, ta yi godiyarta ta kuma bayar da dubu goma na goro

– ta fito.

Husna ce ta biyu. Ta shiga da alamun

tsoro da rashin sabo, Kafarta sai rawa take jiri –

– kuma na kwasarta, dole ta zube a Kasa ba tare da ta Karasa kan buzun da aka tanadawa masu ziyara ba. Yadda take jin dukan zuciya Salmanu ya ji fiye da haka na ganin Husna a gabansa a matsayinsa na boka ita kuma a matsayinta na mai buKata a wajensa. To wacce irin buKata? ‘ Abinda ya fi damunsa da sa shi faduwar gaba – kenan sai kuma fargabar kar Adamu ya dawo ya tarar da ita. Da sauri ya fara shirya ta inda zai Burma – ta. Ko Salmanu bai ci wani Make up ba da – -wahala Husna ta gane shi a yadda ta yi Kasa da kai tana jin kamar Kasa ta dare ta shige. Ba sai _ wani ya bude baki ya fada mata ba, ita da kanta – tana jin ta yi abin kunya, wato zuwa gurin boka a kan saurayi.- Fahimtar hakan da Salmanu yayi ya bashi tasa nutsuwar ta shirya yadda zai shammatota. “Kin zo akan maganar saurayinki Adamune?” Da sauri ta dago kai ta dube shi saboda – mamaki, amma kamar an cije ta, da sauri ta yi – kasa da kai cike da jin nadamar kallonsa, to — mutumin da ba ka kalle.shi ba ma shi ya kallo – abinda ke faruwa a duniyarka, ina ga ka kalle shi? Ta dai cigaba da gyada masa kai alamar Eh” : : , Ya dan shaki iska sannan a kasaice ya ce: mata, , ‘ “Ba ya ce ki jira shi nan da wata biyu ba? Ai yana can yana miki tanadi Hajiya” ‘ Husna ta ji wani yakini da Karfin gwiwa ya dake ta, cikin rawar baki ta amsa,

“Ai wata biyun aure yake nufi, dauke

Please Login or Register in order to submit comment