Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

_*TSANTSAR BUTULCI*_
⚱⚱⚱⚱


_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*


_*MARUBUCIAR*_

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```LOODING......```
_*TSANTSAR BUTULCI*_




_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
____________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_
_______________________






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_



*🅿8*



Kashe mata idonsa guda yayi cikin sigar yaudara yace"Zo ki sammin biscuit d'in naki,naji irinsa zan baki wani kud'in ki siyo"
Jin zancan zai bata kud'i ta siyo wani yasa ta tafi gurinsa da sauri, rik'o hannuta guda yayi yana murzawa, yana lumshe idonsa ya zaunar da ita kan cinyarsa, yana lek'en cikin rigarta,
Ita ko Sumayya sam bata san wace wainar yake toyawa ba,mik'a masa ledar biscuit d'in tayi,tana "yar dariya cike da k'uruciya tace" Yaya Khamis kalli fa na cinye duka saura dudduga,da gaske zaka bani kud'i in siyi wani"

Gyad'a kai yayi yana d'an matsa mata mazaunai,yana lumshe ido,har ya soma futa daga hayyacinsa, ita kuma jin da tayi yana tattab'a mata jiki yasa tayi zumbur!ta mik'e daga jikinsa,tana kallon yanayin sa, tabbas ta tab'aji a makarantar magariba malaminsu ya fad'a cewar babu kyau namiji baligi ya kusanci mace,ko kuma ya tab'a mata jiki,

Kallonsa take sosai taga duk ya zama soko kamaninsa duk sauya, bakinta na rawa tace"To bani hamsin d'in na siyo kaji,ai kaga wannan saura dudduga,idan na siyo wani sai in sammaka"

Mik'ewa yayi tsaya,ya d'auki hularsa yasa yace"Ki kawo min abunci ina d'akin Habibu,idan yaso sai in baki kud'in biscuit din"
Kafin tace komai ya fuce daga falon saboda baya son wani me hankali yazo ya fahimci halin da yake ciki na tsantsar sha'awa.


Kicin ta wuce tana tafiya tana tattare siket d'in dake jikinta, Suwaiba ce tsugune a kchin d'in yayin da Hajiya Gaji take zuba abunci cikin fulas me kyau, tace"Hajiya Yaya Khamis yace"In kai masa abuncin"

Da sauri Suwaiba tace"K'arya kike, babu wani yace ki kai masa abunci,Allah Hajiya kar kibata k'ila in taje rok'onsa zatayi ai kin san halinta"


Mama Zulai dake zaune a kujera "yar tsugo,tana gurza kub'ewa d'anya, wacce za'suyi amfani da ita da daddare tace" Suwaiba bana son abunda kukewa yarinyar nan,fa wai me kuka mai da ita ne"?


Suwaiba tace"Allah Mama Halin Sumayya sai ita,babu mai iyawa sai ke sai babanmu, ni har na k'ago Yayanmu ya dawo, ya suburbud'a mata jiki"


Duka Sumayya ta kai mata a fusace!Tace"To yadawo mama meye ruwana,ai sai ya ganni a gurin da yake sannan zai dake ni, sai an kula kashi yake d'oyi"

Dariya suka sa har Hajiya Gaji dake kicin tace"Lallai Sumayya kin iya cika baki, Allah ya dawo dashi, kin san dama babu ni a masu ceton ki"

Shiru Sumayya tayi batace komai ba,Suwaiba ta karb'i tiren abunci ta futo daga kicin d'in, da sauri Sumayya taje ta tare hanya tana k'okarin k'arbar abuncin, fad'i take"Ai ni yace in kawo masa"

Mama Zulai tace"Ke Sumayya saki mana kar kuyi b'arna mana"

"To ai Mama nifa yace in kai masa shine zata wani ce ita zata kai"

Ganin rigimar tak'i k'are wa yasa Hajiya Gaji tace da Suwaiba ta sakar mata tiran kar su zubar da abunci a banza,

Dole babu yadda ta iya ta sakarwa Sumayya, Hajiya Gaji tace"Sai ki kula da kyau ai kada garin rawar kai kije ki zubar.
A hankali take tafiya dan kar abuncin ya zube, tafara taka matattakalar bene a hankali har ta isa kofar d'akin Yayan nasu, tura k'ofar tayi ta shiga da sallama a bakinta kamar gaske.
Khamis na zaune gefen k'atuwar katifar Yaya Habibu wacce tasha lafiyyan shimfid'a ke kyace yana d'akin kullum sai fidda k'amshi yake mai mugun d'adi,k'amshi da yakama jikinsa kenan,yaran gidan har sun gane k'amshinsa indai yazo guri kowa sai ya gane shine, saboda k'amshinsa na mussaman ne, to haka k'amshin d'akinsa ma ya kasance na mussaman, duk bayan kwana biyu Hajiya Gaji da kanta take hawa saman ta gyara masa d'akin ta feffesa turaran da yake amfani dashi na k'amshin d'aki,ta jawo d'akin ta rufe.
Saboda sanin hali da tayi idan ya dawo yaga d'akin babu gyara,zai iya sawa duk a kwashe kayan d'akin a yi masa sabon fainti sannan a zuba komai sabo,wancan ayi gwanjonsu, shi futar kudi a gurin sa ba komai bane,saboda Allah yayi shi mutum mai son k'yale-k'yale d'an kwalisa,ne ajin k'arshe ga tsabta ko mace albarka, kaya kuwa ko mai tsadar yadi ko shadda zaka ganshi a jikinsa, sabbin takalma sau ciki masu gidan ya tsaya gasunan iri-iri sai idan ya gama amfani dasu ya futowa da k'annasa su mora,duk wata yake d'inka sabbin kaya,ya futar da tsoffafi,ya rabawa mabuk'ata. Babu abunda babu cikin d'akinsa na more rayuwa,


Yanzu ma Khamis na zaune yana kallon tv plasma inda yake kallon wak'okin india,a sky movies, dake shi ma'abocin kallon raye-raye ne yana son yaga suna rungume-rungume suna burge shi.


Sumayya ya ke kallo har ta shigo d'akin ta aje masa abuncin a gabansa,gurin durkusa wuyan rigarta ya zamo k'ananun nonowanta suka d'an futo babu dabara sam bata da niyyar gyarawa,

Shi kuwa Khamis ji yayi kamar ya zura hannu ya cafko guda d'aya ranshi yana ta biyawa da yarinyar.

Tsayuwa tayi tana kallon tv taga an nuno Preetyzeenta tana rawa tana dariya ga dimful d'inta na lob'awa,sai ta k'yalk'ale da dariya kamar wata sokuwa tace"Laaa Yaya Khamis ga me kama dani

K'ungunta ya rik'o da hannusa yana so ya d'orata a jikinsa,ita kuma tana dagewa, yace"Waye yace miki Preety tana kama dake"

Cikin k'uruciya tace"Su Yaya Abdul ne wai irin dariyarmu d'aya da ita"joyowa tayi tana fuskantarsa tace"Kaima kagani ko don Allah muna kamai,kai!gaskiya dani kyakykyawa ce in ina kama da ita"
Tafad'a tana buga tsalle.

Muryarsa tafara sauyawa yace"Zo ki zuba min abunci inci yunwa nake ji"
Yayi hakane don ta k'ara sunkuyawa ya samu nasarar ganin k'irjinta a karo na biyu.

Cike da k'uruciya da rashin sanin meye rayuwa ta sunkuya tana zuba masa abuncin shi kuma yana ta kallonta k'irji.

" Yaya Khamis gash....Shiru tayi ganin ya k'orawa k'irjinta kallo,tayi saurin kallon inda yake kallo, taga abunda yake gani,sai ta mik'e tsaye da sauri tana zumb'ura baki, cikin zuciyarta tace"Lallai ma Yaya Khamis d'in nan ina ganinshi me kirki ashe shima d'an iska ne,dubi yadda yake kalle min k'irji, wata zuciyar tace,kiyi saurin futa kar yayi miki fyad'e, duk da batasan meye fyad'e ba,amma tanajin anacewa a labari ai namiji nayiwa mace fyad'e,da sauri ta nufi hanyar futa daga d'akin cikin tsoro, kiranta yake yana fad'in tazo ta karb'i hamsin d'in biscuit d'in,amma INA!!tuni ta ruga da gudu,bibbiyu ta dunga had'a matattakal benen ta sauka k'asa.


_*Wai wanene Khamis ne?*_




Karku manta wannan littafin na siyarwa naira 200 ga me buk'ata ga numbar nan
08089965176
07084653262
[18/08, 05:28] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

⚱⚱⚱⚱
_*TSANTSAR BUTULCI*_
⚱⚱⚱⚱


_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*


_*MARUBUCIAR*_

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```LOODING......```
_*TSANTSAR BUTULCI*_




_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
____________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_
_______________________






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_



*🅿9*





Khamis Abokin Habibu ne tun na k'oruciya d'ane ga abokin Alh Mado Gwadabe, wanda suke harkar kasuwancinsu a wancan lokacin,shi mahaifin Khamis Alh Auwalu d'an jahar barno ne wato maiduguri kenan, Alh Auwalu ya kanzo kasuwar kano yayi sarin kaya kaya gurin Alh Madu, ya kai can garinsu ya tallata, cikin ikon Allah kasuwancin sai ya k'arbeshi, Alh Auwalu mutum me amana da gudun abun wani, shiyasa ma abotarsu da Alh Madu tayi tsayi saboda shima bayason mutum macinyin amana, ganin irin wahalar da Alh Auwalu ya kesha gurin zuwa sarin kaya,yasa kawai ya yanke shawarar bud'e masa shago a can garin nasu ya zuba masa dukkanin kayan da ake Nema, in yaso duk shekara sai ayi lissafi a futar da riba.
Alh Auwalu na zuwa, Alh Madu ya fad'a masa shawarar da ya yanke, nan take yayi na'am da abun ya dinga godiya Alh Madu yace, ai duk anzama d'aya ya daina godiya,,, sosai suka k'ulla harkokin kasuwancin su komai yana kankama, yana bunk'asa, wani lokacin Alh Auwalu ya kanzo da d'an shi Khamis, in ya shigo Kano gurin abokinsa,nan Khamis suka saba da Habibu,saboda Habibu kullum yana kusa da mahaifinsa yana koyan dabarun kasuwanci lokacin yana d'an shekara goma sha uku. Sosai suka saba wanda har ta kai Khamis yake gudun Mahaifinsa in zai tafi, sai su gudu gida Habibi ya b'oye shi, ganin irin guje-gujen da Khamis yake in zasu tafi yasa Alh Madu ya rok'i alfarma gurin abokinsa kan ya bar masa Khamis d'in, in yaso sai tayi masa transifar na makarantun da yake, zuwa.
To babu wata buk'ata da Alh Madu zai zowa da Alh Auwalu ita bai amunce ba, babu ja'inja ya amunce, yayi tafiyarsa ya bar Khamis a garin Kano.


Habibu da Khamis sun shak'u iya Shak'uwa komai tare sukeyi hatta da suttura iri d'aya suke sanyawa takalma iri d'aya huluna iri d'aya abunci tare suke ci, tare sukayi karatunsu a babbar makarantar nan ta jahar Kano wato BAYARO UNIVASITIY in da suka karanci harkar kasuwanci, ta wani fanni sunyi tarayya gurin hali, ta wani fanni kuma halinsu ya banbanta, ta inda sukai tarayya shine gurin saka kaya iri d'aya duk wani abu d'aya ya siya sai d'an uwansa ya siyo irinsa shima ko da abunci ne, hatta da turare iri d'aya suke fesawa, in suna tafiya baka tab'a banbance waye a cikinsu,sai Wanda yayi musu farin sani, saboda d'aya yafi d'aya tsayi hakanan d'aya yafi d'aya k'iba, Habibu Dogo ne, sosai mai fad'in k'irji, yana tara suma a kansa,kuma yafi Khamis hasken fata, Khamis bai kai tsayin Habibu ba kuma yafi shi kauri kad'an,,, shi yana da san mutane da tsokana ko a cikin abokai ne, sab'anin Habibu da take mai muguwar a k'ida da tsattsauran ra'ayi, ga gaddama da kafiya, shiyasa abokansu basa su musu ya had'asu dashi, baya gajiya gurin tsari, lallai tsarinsa shine dai-dai, yana da mutukar surutu a cikin abokai gami da kwarjini da haiba,ta mutane babba da yaro,kowa nasa ne, bayason raini bayaso ka raina shi,mutum ne mai son girman tsiya shiyasa suke bugawa da Yayarshi Aisha wacce ta girmeshi da kwana uku, lallai sai yace ai ya girme ta sauri tayi ta rigashi zuwa duniyar,girman kwana uku ba girma bane, haka zasuyi ta k'wamawa dashi sai dai ta hak'ura ta kyaleahi domin yafita iya tsari! In yaga tayi shiru sai yai ta yi mata dariya yayi tafiyarsa.

To duk wannan k'walisa da Wanka da wannan matasa sukeyi ba da dukiyar kowa suke ba,face da ta Alh Madu, shi ya sakar musu,bayan sun kammala makaranta, Alh Madu yace duk abunda zai yiwa d'ansa na cikinsa haka zai yiwa Khamis domin abotarsu da mahaifinsa ta mussaman ce,Sam!baya d'aukar zugar mutanan gari
Gaba ki d'aya rayuwar Khamis ta dawo kano sai dai yaje Maiduguri ziyara, tare suke tafiya da Habibu su dawo a tare

Sai da sukai kai shakara ashirin da bakwai ne, Alh Madu ya d'amkawa kowa makulli na shago cikin kasuwa ya zuba musu kaya, sosai yace, su fara zuwa domin su gina kansu,kuma kyauta ya basu,ba bashi ba, cikin sa'a suka fara harkar kasuwanci inda ta fara garawa da Habibu ba'ayi shekara ba ya fara futa kasashen waje,yana had'a hark'allarsa da turawa,kai harda Larabawa Habibu harka yake,mussaman na Dubai,nan sukai masa doyayen riguna na mata masu kyau da jallabiyoyi na maza gami da hula, zai auno kaya ya dawo ya rarraba take,zaka nemi kaya ka rasa, mutane sai suka fara surutu cewa taurarin arzik'i sun sauka daga kan mahaifinsa sun dawo kansa saboda haka shine zai gaji ubansa, ganin cece kucan da mutane keyi yasa kawai ya hana Alh Madu futa kasuwa sai jefi-jefi yake zuwa,tunda in yaje d'in ma sai dai ya zauna yana shige da fuce, shagonsa cike yake da yara masu neman su kafa Kansu,duk ya sakar musu kowa ya samu nashi .
*Kai gaskiya da anyi dattawan arzik'i da kudi lo wani abun duniya bai rufe musu ido ba,masu maida d'an wani nasu*

Sai yake zama a gida kawai tunda lokacin Auwalu ma ya kawo k'arfi shi yake zuwa ya kula da harkar cinikayyar duk ranar da bai futa ba.


To yawon tafiye-tafiye da Habibu yake ne yasa Khamis yayi sabbin abokai cikin kasuwar irin,kullum suna shagonsa ana hira ana birni k'iri-k'iri costoms zasu shigo kasuwar a kan idonsa sai ya share kawai a cewarsa shi bazai wani damun kanshi ba kan kud'i kamar yadda Habibu yakeyi tunda yaga zai iya yayi tayi,bashi da matsalar komai in ya buk'aci kud'i zaije ya cire ne cikin Account din Habibu batare da damuwarsa ba,shima Habibun in ya gani baya damuwa,saboda wasu ne suke shigowa kullum, ganin arhar kud'i yasa Khamis d'iba iya son ransa ya tafi bariki yaje ya kashewa mata,ya shana sosai yayi watsi da kud'i, tuni idonsa ya bud'e da mata tare da had'in gwiwar sabon abokinsa Manniru, shima cikin kasuwar yake, kullum suka tashi daga kasuwa sai su wuce hotal suje su nemi matansu duk kalar da suke so.

Khamis Mutum ne jarabbabe in yaga mace kamar yayi hauka haka yakeji,, kuma yakiyin aure,sai shanawarsa yake.



Kwatsam
A ka aiko Alh Auwalu babu lafiya,dama yana da Hawan jini,da sugar babu b'ata lokaci Alh Madu ya tattara iyalinsa suka nufi Maiduguri hankali a tashe!

Alh Madu ya gigice da ya ga Abokinsa baya iya motsi ko ina na jikinsa ya shika komai sai dai ayi masa,babu shiri ya sa aje ayi vis domin futar dashi kawar waje a bunkici lafiyarsa, anyi komai an gama, a daran Alh Auwalu ya rasu,wannan mutuwa ta gigita alumar musulimi duk Wanda ya bud'i baki zai ce tare dashi yayi sallah juma'a da kayi jiya, ai dama mutuwa bata da kama in lokaci yayi dole a tafi, Alh Mado ya koka da rashin da yayi daga k'arashe ya barwa Allah yabi abokinsa da addu'a.

Bayan sadakar bakwai, da kansa ya tara iyalin Alh Auwalu matarshi Hajiya Laure da "yayansa su bakwai namiji guda shine Khamis kenan,yace" Nine babban abokin Alh Auwalu, ni Alh Madu Gwadabe duk wata dukiyata da Alh Auwalu yake juyawa komai yawanta na barwa iyalinsa har abada ko bayan babu raina ban yarda a tada maganar ba, wannan magana nayi ta ne a gaban iyalina domin Ku zama sheda"


Kuka iyalin Alh Auwalu suke,suna godiya ga Alh Madu suna jinjina nagartarsa, dukiya me tarin yawa wacce ba'asan kanta ba, anyi kyautarta lallai dole ayi wa Alh Madu jinjina.

Wannan furucin da Alh Madu yayi ya mutuk'ar yiwa Khamis dad'i dama ta samu kenan yanzu zai famtama cikin dukiya shi kad'ai ne namiji kuma basu da "yan uba dole yayi yarda yake so da dukiya,

Bai nuna komai ba, ya bar abun cikin ransa, yace" Baba mungode da wannan karamcin naka, Allah ya kara girma yaja kwana, da wannan nake Neman alfarma a barni in zauna nam domin in cigaba da kula da dukiyarnan ganin babu wani tsayyaye"

Alh Madu yace"Wannan shawarar taka tayi kyau nima sai da nayi tunanin haka, dama dole yanzu ka tsaya ka kula da "yan uwanka gami da mahaifiyar ka, na amunce da maganar ka, saboda haka duk wani Abu da kake bukata kazo la tunkareni kar kaji fargabar komai har yanzu kanan a matsayin Habibu a gurina"

Hajiya Laure taita godiya sauran "Yayanta suma sunayi.
Haka
Alh Madu ya tattara Iyalinsa suka tafi yana kewar Abokinsa Alh Auwalu





Karku manta da cewar wannan book d'in na kud'i ne naira d'ari biyu ga me buk'ata ga numbar nan
08089965176
07084653262
[19/08, 12:34] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

⚱⚱⚱⚱
_*TSANTSAR BUTULCI*_
⚱⚱⚱⚱


_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*


_*MARUBUCIAR*_

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```LOODING......```
_*TSANTSAR BUTULCI*_




_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
____________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_
_______________________






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_



*🅿10*





Wannan shine cikkaken tarihin Khamis.
Yanzu ma ya dawo daga Aba ne,a cewarsa yaje sarin takalma sai ya fake da yawonsa ya biya b'ukatarsa da mata, shi mace ko arniya ce mutukar tayi masa sai ya kwanta da ita, duk wannan mugayen halayen nasa abokinsa bai sani ba, saboda sunyi nesa da juna yanzu,sai dai idan d'aye ne ya kai wa d'aya ziyara, haka ma Alh Moddobo kullum cikin ganin girman Khamis yake gami da nagartarsa.




Sumayya ko tana sauka k'asa ta manta abunda ya faru tsakaninta da Khamis d'in ta cigaba da sabgoginta

Kwanan Khamis uku da zuwa Habibu yayi Waya yace"A tareshi a airport misalin sha biyu na rana, gida ya rud'e da murna, yara da manya,hattaa da samarin gidan murna suke da dawowarsa, banda Sumayya duk ta b'ata rai tayi kicin-kincin da fuska duk inda taje ta zauna taji ana zancan dawowarsa gida sai ta bar gurin,k'arashe ma da taga ba'a ta ita,sai ta shig'e k'uryan d'akin Hajiya Tabawa babarsu Suwaiba kenan tayi kwanciyarta.
Karkuce duk tsawon wannan kwana ki ukun Khamis be fasa tab'a jikin Sumayya ba,har indai yaga babu idanun jama'a a guri sai ya san yadda yayi ya tab'a wani b'angare na jikinta.


Umulkairi ce ta shigo da gudu d'akinsu ta buga tsalle ta haye gado, sai murna take,a fili take cewa"Yayan mu zai dawo, nasan tunda naci jarrabawa inada kyauta ta mussaman,wayyo dad'i kashe ni in huta"

Sumayya ta k'ulu iya k'uluwa,juya baya tayi taja tsaki gami da cewa"Aikin banza Aikin wofi kawai"

Umulkairi ta juyo tana kallonta cikin mamaki tace"Dama kina cikin d'akin nan"?

Banza Sumayya tayi mata, Umulkairi tace"Ni kike zagi ko Sumy,ai babu komai nagode Allah,watan cin ubanki ya kama,yaya ya dawo wallahi sai na fad'a masa irin rashin mutumcin da kikayi"


A fusace!Tace"Ki fad'a masa mana don. Allah in kin fad'a masa kar ya barni da raina,ko an fad'a miki tsoransa nakeji kamar yadda kuke tsoronsa, k'arya kike"
Sumayya ta k'arashe maganar cikin raini


Umulkairi ta fidda hannu ta tsinka mata mari a fusace!tace yayan namu shine yake miki k'arya lallai Sumy baki da Hankali"
Da hauka Sumayya tayi kan Umulkairi da duka,dama a fusace take,jin Umulkairin tana murna taci jarrabawa,ita bataci tasan dariya zasuyi mata suyi mata gwalo in yayi musu kyauta shiyasa ta fusata,takama Umulkairi da kokawa fad'a suke sosai,Umulkairi tafi Sumayya k'arfi kuma dama ta girme mata da shekaru hud'u,ita Sumayya mugun girman jiki ne da ita,gashi babu k'arfi, Umulkairi ta yar da ita k'asa, tana niyar gudu itama ta rik'e mata k'afa d'aya ta fad'i k'asa tayi saurin mik'ewa ta haye ruwan cikinta tana duka kamar wata "yar dambe, Umulkairi k'okarin kwatar kanta takeyi,Sumayya duk ta yakushe mata fuska,duk wasu dabaru na fad'a Sumayya ta sani, dak'ay Ummu ta cilar da Sumayya k'asa ta rugu da guda tana dariya,gami da haki!dad'i take shegiya sai kace mage duk ta ya kushe min fuska"
Da gudu Sumayya ta biyo bayanta tana zaginta tana kuka,gashi dai itace taci galaba kan Ummu d'in amma kuka take,Mamansu ta tare ta tana tambayarta abunda ya faru,,k'okarin funcikewa take daga hannun Maman tana son kaiwa Ummu duka,Mama tace"Ke Ummu me ya had'a ku ne, wallahi na tsani tsokanar da kuke mata"

Umulkairi tace"Wallahi Mama itace me tsokana haka kawai ta hau zagina tana zagin yayanmu"

Cikin mamaki Mama ta kalli Sumayya tace"Hakane maganar ko kuwa "

Shiru Sumayya tayi tana share hawaye.
Hakan ya tabbatar wa da Mama gaskiya ne, b'ata fuska tayi tace"Kul! kinji na fad'a miki idan zaki rashin kunyar ki, ki tsaya idan kike, dan baki da hankali Habibun kike zagi, kar in k'araji,kinji ko baki jiba"?
Kuka Sumayya ta fashe dashi,Mama ta shige d'aki abunta,Umulkairi ma tafiyarta tayi,ta cigaba da sabgoginta, Sumayya ko can saman babansu tayi tafiyarta ta kwanta tana kuka har bacci ya d'auketa.

*******
K'arfe goma sha biyu da rabi na ranar Habibu ya sauka a gida, "Yan uwansa duk sun baibaye shi suna gaisawa cike da farin ciki, yake amsa musu, d'aya bayan d'aya ya shiga d'akin iyayen nasa suka gaisa,ya fito yana kallon " yan uwan nasa mata kowacce na zaune sunyi shiru, kallon Rab'ia yayi yace"Ina Sumayya take"

Inda-inda ta farayi domin bata san inda take ba, Umulkairi tace"d'azu tana nan, inaji tana sama gurin Baba"

Habibu yace"Baba,yana waje can na baroshi yana hutawa a waje"
Hajiya Gaji tace"Tana sama tana bacci, d'azu da na hau na ganta,indai ba ta tashi ba"

Shiru sukayi, Khamis ya mik'e da sauri ya nufi hanyar futa, shima Habibu mik'ewa yayi ya kalli "yan uwan nasa yace" Ku bari inje inyi Wanka in huta tukkuna zan zauna da kowacce a cikinku"

Hajiya Gaji tasa dariya, tana fad'in lallai kuwa yau zamu sha kallo da dariya"


Ya k'okarin tafiya yace"Duk wacce batayi abun arzik'i ba a makaranta ai ta san sauran, babu duka babu zagi sai dai taga anayi"
Yana gama maganar ya futa daga falon d'akinsa ya nufa.

Khamis kuwa da yayi saurin mik'ewa ya nufi sama,kai tsaye d'akin Baba ya bud'e ya shiga . aikuwa Sumayya ya gani kwance kan kafet din dake shimfid'e a kasa tana bacci sosai, dake dogon Wanda ne a jikinta da k'aramar riga me dogon hannu, duk sai hallitun jikinta suka bayyana, jikinta ya shika bacci take sosai, kura mata ido yayi yana mata kallon k'urulla wata irin sha'awarta tana bijoro masa, zuciyarsa na ingizashi kan yaje yayi mata abunda ya saba,yanzu tunda bacci take,ko ya samu ya rage rad'ad'in sha'awar da yake ji, motsi yaji alamun za'a hau sama, yayi saurin dawowa hankalinsa,jin ana tab'a kofar d'akin yasa ya wayance da zuwa gaban tv ya tsuguna yana duba kasa-kasai.Habibu ne ya shigo d'akin, suka had'a ido dashi, yace"Kai dama nan ka shigo" Cikin wayancewa Khamis yace"Eh mana ina duba kasat ne, yau kallon hausa film nake sha'awa" Tab'e baki Habibu yayi yace"kallo baya isarka kai kam,ina fata ba'anan zakayi ba,kar ka tashi Sumayya daga bacci"

Khamis yace"Banan zanyi ba, yanzu zan shigo muci abunci ai"

Futa Habibu yayi daga d'akin, Khamis ya mik'e shima yana waiwayen Sumayya, har ya futa yana cizon ya tsa.







Karku manta da cewar wannan littafin na siyarwa ne, naira Dari biyu ga me buk'ata ga numbar nan.
08089965176
07084653262
[20/08, 16:54] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

e: ⚱⚱⚱⚱
_*TSANTSAR BUTULCI*_
⚱⚱⚱⚱


_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*


_*MARUBUCIAR*_

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```LOODING......```
_*TSANTSAR BUTULCI*_




_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
____________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_
_______________________






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_



*🅿11*



Habibu na shiga d'akinsa yayi shirin yin wanka, wani katon towol ya d'aura a jikinsa ya shiga toilet ya wanke jikinsa tas ya futo ya tsaya gaban dressing miroow yana taje sumarsa ya sanya mata mayu ka, dake yanayin zafi bai shafa mai ba, turare kawai ya fesa a jikinsa, ya sanya wasu Jesi kaya irin na "yan ball kayan sun masa kyau sosai, da yake yana bala'in son kwallon k'afa shiyasa yake yawan sanya kayansu, yana son " yan k'ungiyar arsenal in kaji ana musu dashi akan ball sai ka rik'e baki,kallo in ba na ball ba babu wanda yake tsayawa yana mayar da hankali a kansa,sai dai ko labarai.


Khamis ya bishi da kallo lokacin da yake k'okarin zama kusa dashi,yace"Shikkenan an dawo fagen fama, za'a cigaba da fafatawa ko" Habibu yasa dariya gami da bashi hannu suka tafa yace" To me za'a fasa, ai yau sai na futa majalisa na buwaye su"

Khamis yace"Kamar ka sani kuwa d'azu da safe da naje, Lurwanu yake tambayar ka"
Habibu yace"Gani nadawo ai,zamu had'u da juna"

Hira suka cigaba da yi irin ta abokain da suka yarda da junansu, sukaci suka sha suka k'oshi, Habibu ya mik'e kan doguwar kujera yana lumshe ido,bacci na fuzgarsa kad'an shi kuma Khamis kaset d'in da ya d'auko ya sa a DVD ya fara gani,yana cin dariyar d'an Rabilu musa d'an ibro, cikin kaset d'inshi na *Ka kiyayi me nema* ganin film d'in dan Ibro ne yasa Habibu mik'ewa zaune yayi yana dariya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment