Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da zanyi magana akai, Habibu naji dad'in hukuncin nan,kuma ina alfahari da kai gurin ganin ka kare min Martaba da ta iyalina,tabbas kazama d'aya tamkar da dubu, a zahirin gaskiya akwai wani k'udiri a raina Wanda ya dad'e shekara da shekaru,kuma Wannan kudirina akanka yake ina fatan zaka yi min biyyaya kamar ko da yaushe"


Habibu yace"Duk abunda ka umarce ni dashi zanyi mutukar bai sab'awa addinin Allah ba"


Alhaji Madu yace"Alhamdulilahi, so nake ka auri Sumayya"


Wani irin gingirim Habibu yaji a kansa,yayi masa nauyi sosai, yace"Alhaji anya wannan lamari zai yi wu"


"Babu abunda zai hanashi yiwuwa Habibu babu haramci idan ka auri yarinyar nan, tunda baku sha nono d'aya ba"


Habibu ya girgiza kai fuskarsa da damuwa yace"ina tunanin halin da yarinyar zata shiga mutuk'ar ta gane,cewar Ku ba iyayenta ba ne,kuma mu ba "yan uwantq na jini bane"



Alhaji Madu yace"Nafi ka tunanin wannan Abu,domin ina tunanin zuwan wannan ranar,to amma ni akwai abunda nake hangowa a game fa rayuwarta,Habibu kaine nawa ina kyautata zaton zaka rik'e min ita da mutumci da amana"

Shiru Habibu yayi yana share gumi, yace"Hakane Alhaji,bani da abun cewa a wannan al'amari sai dai in ce Allah ya sanya alkairi a ciki"


Alhaji Madu yace"Ameeen ya rabbi nagode sosai, inayi maka fatan alkairi a rayuwarka,ina fatan Allah ya saka ka haifi "yaya masu albarka da biyayya"

Habibu yace "Ameen Alhaji"
Mik'ewa yayi zai futa, Alhaji Madu yace"Ai yanzu za'ayi ta ta k'are kaje ka kira min iyayenka,da ita Sumayya"

Habibu ya sauka k'asa domin cika umarnin mahaifin nasa,a zuciyarsa yana ganin wannan abu da kamar wuya wai gurguwa da auran nesa, A zuciyarsa baya jin son Sumayya kuma baya jin k'inta shidai gashi nan dai.






Karku manda da cewar wannan book din na kud'i ne naira Dari biyu ga me buk'ata ga numbar nan
08089965176
07084653262
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

⚱⚱⚱⚱
_*TSANTSAR BUTULCI*_
⚱⚱⚱⚱


_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*


_*MARUBUCIAR*_

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```LOODING......```
_*TSANTSAR BUTULCI*_




_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
____________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_
_______________________






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_



*🅿20*



Dukaninsu, suna Zaune gaban Alhaji Madu, har da Sumayya,tana kusa dashi kanta a k'asa, gabanta yana wata irin fad'uwa.

Alhaji Madu yayi gyaran murya, kana yace"Alhamdulilahi, Allah nagode maka daka nuna min wannan ranar da raina da lafiyata, Hausawa sukace ranar wanka ba'a b'oyan cibi, babban abunda yasa na taraku anan shine,ina so in fad'awa Sumayya Wacece ita,saboda wani dalilina, Sumayya ta d'ago kai tana kallonsa,gabanta ya cigaba da fad'uwa duf-duf-duf. Hajiya Zulai ma jikinta sanyi k'alau yayi,tasan dama dole akwai zuwan wannan ranar.

Alhaji Madu ya kalli Sumayya yace" Yake "yata ta ruwan sanyi, hak'ika kece mafi soyuwa a zuciya,Sumayya Allah ya d'ora min son ki da tausayin ki,duk cikin " yayan da na Haifa, inaso in warware miki wasu muhiman abubuwa da suka shafe ki,ina fatan, zaki d'auki k'addara ki rungume ta hannu bibbiyu, domin kin san da cewar ko wane bawa yana tafe ne,da tashi k'addarar me kyau ko mara kyau"
Alhaji Madu ya ajiye maganar yana jan numfashi.
Sumayya ta d'ago kanta tana kallonsa,idanunta suna zubar da wasu zafafen hawaye tun kafin taji maganar da Babansu zai fad'a mata,tasan ba mai dad'i bace.
Kuka take sosai da sosai.

D'akin yayi tsit! Alhaji Madu ya cigaba da cewa"Sumayya a zahirin gaskiya ni da kika d'auka a matsayin mahaifin ki,bani na haife ki ba,haka nan kuma Hajiya Zulai ba itace mahaifiyar ki ba" Nan Alhaji Madu ya warware Sumayya yadda akayi aka same ta har ta girma a hannusa, ba tasan Wacece ita ba.

Suman zaune Sumayya tayi a gurin tana zazzare ido,in ta kalli wancan sai ta kalli wancan, a d'akin duk ta furgice! Manyansu sune suka san labarin Sumayya shiyasa basu gigita ba, irinsu Rabi'a da Ummu Suwaiba dana k'asa dasu sune suka gigita jin ashe Sumayya ba jininsu bace tsintar ta akayi.


Mik'ewa tayi tana rangaji jiri na d'ibarta takama hanya zata futa,daga d'akin da alama bata cikin hayyacin ta,tsallake mutane kawai take,tana kallo suka bita dashi, tazo dai-dai gurin da Habibu yake zaune ta tsaya tana rik'e kanta, luuuuu! Ta afka jikinsa, yayi saurin rungume ta a gigice ya mik'e tsaye da ita a jikinsa,yana kallon Auwal yace"Maza kaje ka futo da mota.

Tashin hankali, Sumayya ta sank'ame dafara na futowa daga bakinta,hankalin Alhaji Madu ya tashi ainun, addu'oi yake tofa mata. Hajiya Zulai tana kuka take cewa"Wannan magana Alhaji daka sani baka fad'a ta ba, amma ban san manufarka ba, ina tsoran halin da yarinyar nan zata shiga"

Alhaji Madu yace"Ki kwantar da hankalin ki,komai zai zo da sauk'i Insha Allah ina da munufata a kan haka da nayi.


Jikinsa na tsuma ya sungume ta ya sauka k'asa da ita,kai tsaye waje ya futa,inda motarsa take ya nufa,Auwal ya gyara parking ya shiga da ita a jikinsa,Auwal ya kunna mota,zasu tafi sai ga Khamis ya tawo a gigice yazo ya bud'e motar ya shiga,yana jin kamar ya k'wace Sumayya daga hannun Habibu amma babu fuska,wani mugun kishinsa ne yake damunsa.


Haka sukayi tafiyar babu me cewa komai Habibu yana ta aikin goge mata kumfar da take futowa daga bakinta, Shi kuwa Khamis banda aukin kallonta babu abunda yake.


Dogon suma Sumayya tayi Wanda har sai da aka sama ta abun zuk'u numfashi,awa uku sanam numfashin ta ya dawo dai-dai



Tun kafin ta bud'e idonta wasu hawaye suka fara zubo mata,wannan ya tabbatar wa da Habibu cewar ta dawo cikin hayyacin ta,kiran sunanta yayi cikin taushin murya,ta bud'e idonta tana kallonsa, hawaye jage-jage!


"Kiyi shiru ki bar kukan nan da kikeyi domin zai iya janyo miki wani ciwon ki d'auki k'adarar ki, wannan ba yana nufin cewar mun cire ki daga cikinmu ba, ko angano iyayen ki, ko ba'agano su ba,kina nan a matsayin " yar uwarmu,kuma "ya ga Alhaji Madu Gwadabe, saboda haka,babu wani banbanci da zaki gani ko wani sauyi in sha Allau ki rik'e a zuciyarki cewar badan a tozar taki aka fad'a miki wannan maganar ba, fad'in ta shine alkairi a gare ki"


Shiru tayi tana zubar da hawaye, tarasa wane irin tunani zatayi k'wak'walwarta duk ta toshe, ita duniyar ma gaba d'aya batai mata dad'i, duk maganganun da Habibu yake wasu bata fahimtar su.


Khamis ne ya zauna kusa da k'afafunta,ya rik'e hannuta yana murzawa cikin sigar rarrashi yace"Sumy kiyi hakuri kinji ko bana son kina kuka kinji ko,mutukar muna Raye bazaki wulakanta ba,Insha Allahu nayi miki alk'awarin duk inda iyayenki suke zan shiga in futa in nemo miki su"

Wannan magana da Khamis yayi ta sanya Zuciyar Sumayya sanyi, tana kuka tace" Yaya Khamis kayi min alk'awari ko"?

D'aga kansa yayi yana murza mata hannu.

Habibu duk bai lura ba,yace "Ki goge hawayen ki, nima zan taya Khamis muje mu nemo miki su,amma sai kin kwantar da hankalin ki"

Sumayya ta goge hawaye n ta tana sauke ajiyar zuciya.

Habibu ya kalli Khamis yana fad'in bari inje in kira likata yazo ya duba jikin nata mu tafi gida"


D'aga kai kawai Khamis yayi, domin bazai iya magana ba,muryarshi zata iya tuna masa asiri.

Habibu yana futa,Khamis ya k'ara matsawa jikin Sumayya sosai,yana goge mata hawayen fuskarta a wayance ya d'ora hannunsa a k'irjinta wai yana gyara mata hijab, Sumayya ta ture hannusa tana k'okarin mik'ewa zaune,ya taimaka mata ta zauna, karyar da kai yayi yace"Sumy a kwai abunda nakeso in fad'a miki dama"

Sumayya tace"Ina jinka Yaya Khamis.

Lumshe ido yayi cikin sigar yaudara yace" Wallahi ina mutukar kaunar ki, ina mutuk'ar sonki da tausayin ki a rayuwata,ina so ki yarda dani ki aure ni"


Wani irin kallo Sumayya tayi masa, tana girgiza kai,batayi mamaki ba,domin ta dad'e tana kallon so da k'aunarta a k'wayar idonsa,yayin da ita kuma bata jin son sa ko guda d'aya a cikin ranta


Khamis yace"Idan kin amunce kawai zanyiwa Alhaji magana sai a tsada mana rana kamar tasu Rabi'a"

Girgiza kai tayi kawai tace"Ka bari inyi shawara"

Khamis yace"Shikkenan ina fata kiyi shawarta alkairi,amma akwai abunda nakeso in fad'a miki ki kula akai shine, Ki kula da Habibu domin baya k'aunar ki duk wannan maganganun da yake miki dad'in baki yake miki, cutar ki zaiyi, kar ki k'ara yadda dashi yana tab'a miki jiki,domin lokacin da kika suma ma, shine ta d'auko ki, a mota ya dunga tab'a miki nononki, nine na hana shi nace yaji tsoran Allah domin yana kallonsa.


Sumayya ranta ya b'aci idan da akwai abunda ta tsana a duniya bai wuce a tab'a mata k'irji ba, ta tsani namiji ya kalle mata kirji shiyasa kullum cikin hijabi take,wato yanzu Yaya Habibu dan ya san ba su had'a dangata ta komai ba shine yake tab'a ta Lallai dole tayi taka tsan-tsan da samarin gidan kar su lalata mata rayuwa,
Wannan shawar zuciyarta take bata. Habibu ya shigo tare da likita ya duba ta, sosai ya sallame ta,,,,, suka tafi gida Habibu shike tuk'a motar saboda Auwal ya tafi kasuwa an da meshi da waya,to shima Habibu yanzu haka jiransa ake a kasuwarsu, akwai wasu bak'i da zasu sallama kuma zasu fara raba kaya a shaguna, sai waya ake masa.



Duk yana kallon irin shishshigewar da Khamis yakewa Sumayya girgiza kai yayi kawai,yana so ya fuskaci wani abu daga gurin Khamis din,murmushi kawai yayi a zuciyarsa har sukaje gida.


Sumayya ta kasa sakewa a gidan sukuku kullum babu walwala, idan ta hau sama gurin Babansu nan ma bata dad'ewa take saukowa kowa ya fuskanci sauyi a gurin ta, haka dai suka cigaba da tafiya da ita,babu Wanda ya nuna mata sauyi ko banbanci matan gidan da yaran gidan,itace kawai takasa sakewa.



****
Bayan sati uku da Faruwar al'amarin Sumayya ta saki jikinta har ta fara mantawa,sai dai idan ta tuno da cewar ita ba wata tsiya bace,kuma bata da iyaye sai ta shiga d'aki tayi ta kuka,ta gode Allah.


Ranar Lahadi da safe,Alhaji Madu yasa aka kira masa ita, taje ta gaidashi ta zauna kusa dashi kanta a k'asa, kafin ya fad'a mata dalilin kiran sai da yaja ta da wasa,kamar yadda ya saba,sannan yace"Sumayya ina so in aurar dake kamar yadda zan aurar da su Rabi'a, ina fatan zaki zauna lafiya da mijin ki"

Cikin fad'uwar gaba ta d'ago kanta tana kallonsa tace"Babanmu wanene mijin, ni da bani da tsayyayn saurayi,, ni kam bana son Khamis Babanmu"

Murmushi yayi yace"Ashe akwai maganar Khamis
A k'asa Sumayya"

D'aga kai tayi tace"Kwana ki yace wai yana sona zai aure ni"

Alhaji Madu yasa dariya yana fad'in shine baki fad'a min ba"

Sumayya ta sunkuyar da kanta gabanta yana fad'uwa!


Alhaji Madu yace"Na riga na d'ade da wani burina a raina da babu wannan burin da babu abunda zai hanani aurar dake ga Khamis domin nagartarsa,amma kash! Duk nagaratarsa bai kai Habibu ba, ina mutuk'ar so inga na aurar dake ga yaron kirki Habibu"


Dafe k'irji tayi tana zazzare ido bakinta na karkarwa tace"Wane Habibu kake nufi Babanmu"?


Murmushi yayi yace"Ina da wani Habibu ne bayan nawa"

Sumayya ta gigice sosai tana fad'in don Allah Babanmu ka janye maganar nan, kayi min rai, Babanmu Yaya Habibu ba tsaran aure na bane, Yaya Habibu yaya na ne. Bazan iya rayuwar aure dashi ba"

Ganin yadda ta gigice yasa Alhaji Madu kwantar mata da hankali gami da yi mata misalai, dawa amma Sumayya takasa fahimta komai kuka take,

Lallab'ata yayi yace"Ta daina kuka zaiyi tunani janye maganar ta kwantar da hankalin ta.


Sumayya tashiga k'unci da damuwa tana ganin kamar bata da gata shiyasa za'ayi mata auran dole, ita a ganinta da ta auri Habibu gwara ta auri Khamis sau dubu domin tana ganin shi yafi Habibu sakin fuska,kuma shi ya furta yana sonta da bakinsa,sab'anin Habibu da tunda suka dawo daga asibiti wata magana bata k'ara had'ata dashi ba, tsakaninta dashi gaisuwa CE kawai,wataran ma in ta gaidashi baya amsawa,tana ganin Habibu bazai iya kula da ita ba saboda shi babu abunda yasa agaba sai harkar kasuwancinsa.


Jin Alhaji Madu bai k'ara tayar mata da maganar ba yasa ta kwantar da hankalinta,a ka cigaba da sabgogin bukin su Rabi'a da ita,wanda ya rage saura "yan kwana ki.


*****
Yawan zurgar zurgar dasu ke ne yasa bai samu zama da mahaifin nasa ba sai ana saura kwana sati d'aya daurin aure suka zauna a d'akin Alhaji Madu suna tattaunawa maganar katin d'aurin auran ya d'auka yana dubawa, sunanshi ne a sama shi da Sumayya sai na Suwaiba da angontq sai na Rabi'a itama da angonta, nan ya sauko daga saman da katikan a hannusa Abdulsamadu ya baya yace yaje ya rarrabawa mutane, Hajiya Gaji takarb'a ta bawa su Hajiya Zulai kowa ya rabawa danginsa, nan Yaran gidan sukaga sunan Sumayya cikin katin ita yayansu, mamaki suka dunga yi sosai daga bisani sukayi shiru da bakinsu,


Sumayya na makaranta lokacin tana dawowa suka had'u da Abdul samadu da katin a hannusa sai ta karb'a tana dubawa, abunda tagani ya gigitata, Zubewa tayi a gurin ta suma Wanda yayi dai-dai da shigowar Khamis soran ganin abunda yake faruwa yasa baiyi wata-wata ba,ya d'auki Sumayya Abdul ya bi bayansa suka hau dama,D'akin Habibu ya shiga da ita lokacin baya ciki Abdul yaje ya bud'e firji a d'auko ruwa me sanyi ya watsa mata, ta sauke ajiyar zuciya, ganin ta farfad'o Abdul ya sauka k'asa da saurin domin fad'awa Yaya Habibu abunda yake faruwa.



Katin d'aurin Auran Sumayya ta nunawa Khamis tana wani irin kukan me ban tausayi.

Khamis ya karanta yafi sai goma wani zazzafan gumi yana zubo masa, wato shi za'a munafurta kenan,tabbas shima akwai nasa shirin insun San wata basu San wata ba, rarrashin Sumayya yake sosai yace"Ki kwantar da hankalin ki wannan aure indai ina Raye baza'a daura miki shi da Wannan azalimin mutumin da baya k'aunar ki, zan tsaya miki tsayin daka gurin kwantar "yan ciki, zan gudu dake, in b'oye ki sai k'ura ta lafa sai in dawo dake,ko kuma muje a daura mana aure tare,in boye ki inda bazasu ganki ba, INA fatan iin yarda da wannan Shawarar tawa"

Sumayya ta d'aga kai tana wa Khamis godiya ta amunce ya gudu da ita, idan anga bata nan ai dole a hakura da daurij auran.
Habibu ne ya shigo yaga Khamis kusa da Sumayya yanai mata magana k'asa-k'asa kome yake cewa oho.






Karku manta da cewar wannan littafin na siyarwa ne naira Dari biyu ga me bukatar cigabansa ga numbar nan
08089965176
07084653262

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment