Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Xayynebπ’¤π’¤

*Fasaha online writer's f o w*

*Dedicated to my daughter deejart*

π…Ώ4⃣π”µ
π“π“π“π“π“
Ya mutsa fiska yayi ya miqa hannunsa bisa Cikin ta ya jawo rigar dan ta rufe Mata cibiyarta, Amman da yake best d'in roba ce Sam taq'i zama yanda yake son,
ganin ta fara motsa idanuwa tana son bud'e su ne ,
da sauri ya miq'e tsaye a kanta,
bud'e idanuwa tayi cikin mamakin barcin da yai mata daukar ba zata ,
da sauri ta miq'e tsaye dan 4 eyes da tayi da saif a gabanta yana mata duban aikin kenan dana Saki?'
cikin cold voice Nata ta Fara magna
"Yaya saif yi haq'uri wlh bansan sanda barci ya d'auke ni ba ne shiyasa,
kuma banma lpia Allah kuwa ".
ta q'arasa maganr tana shafa gefen wuyanta cikin marairaicewa da son ya tausaya mata.
" mtssss so Ina ruwana da wata rashin lpiyarki ?"
Wannan kuma keta shafa nidai abinda nasani dole ne ki ida mun aiki na,
dan haka maza ki biyoni tun kan na q'ara miki wani marin wlh a dayan kumatun ",π΅
yana kaiwa nan ya juya ya mom ta cikin falon.
Miq'ewa tayi tana gunguni,
Sannan ta kwaso kayan shanyar tabi bayansa zuwa falon, tana tafia kanta na cigaba da Sara mata,
tana shiga ya ce 'taje bedroom nasa ta jona iron ta goge kayan duka ,
Wucewa tayi ciki ba tare da tace komi ba,
a sace ya dinga binta da kallo ganin yanda komi na jikinta ke rawa in tana tafiya yaji kamar ya daukota ya sanyata a qirjinsa
" oh my life "
ya furta yana duq'e Kai q'asa,
mgnr da sukayi da dadynsa jia ke dawo masa aka inda yake cewa ya gaji da zaman sa haka ba mata inda ya gama karatu sa q'arewar ma gama karatu zaune yake a first office ,
to wlh ya fiddo wacce yakeso asan nayi inko ba hakaba saiya Saba masa ,
shi bama wannan ne damuwar saba yanzun shi ko zance bai taba zuwa ba bare ya samu q'warin gwiwar fiddo fiance dinsa a wannan short time din da yai masa shaura a yanzun.
"huuuu !"
yaja numfashi tare da da jawo wayarsa number hesham yayi cull ba jimawa akai hold
"Hey brother ka dawo office ne?"
"OK Alright plsss if you don't mention i wish see you now ,
"_OK see you brother".
Latse wayar yayi da sauri ya miq'e ya nufi bedroom d'in nasa jin wani q'auri da hayaq'i 2 na fitowa a ciki.

tun shigar ta d'akin tana soma fara gugar baifi singlet d'aya da hankicef 2 ba jikinta gaba d'aya gumi ya ida rufeta,
idanuwanta har rufewa suke dan azaba _,
daman tasan muddin rana ta bigeta over tofa necessary ne tayi fever,
hakance ta faru kuwa,
har ta d'ora singlet d'in qarshe ta sa iron d'in tafara gogewa taji tayi baya luuuu ta kwanta ta dafe kanta saboda wani headache da yai Mata shiga d'aya , mafarin knn iron d'in ya fara cin rigar ta fara q'auri wanda iron din har pray mat din data shinfida a q'asa ta fara q'onewa itama,
ga shatin iron d'in ya fito sosai a jiki kuwa.
tanajin hiyaq'in
Amman ta kasa tashi ta zare wayoyin,
Ko hannun ta ma ta gagara motsawa.
da sauri ya q'araso ya zare socket d'in ya tada iron d'in tsaye,
lokacin ne hankalin sa ya juya kanta da zumar masifeta ganin halin da take ciki ba q'aramin tausayinta ya tsarga masa ba, sai faman wash"!Wash!.take Nana tawa idanuwan ta suna rufewa suna kuma bud'ewa ,
" dan Allah yaya saif help me" , .
fad'i take hawaye na zuraro Mata,
daman muddin kanta ya soma mata ciwo tofa tabbas ne hawaye ya biyo baya , xuq'unnawa yayi ya d'ora hannun sa a kanta yaji da zafi sosai,
hannun sa ta kamo ta riqe gadagam ta d'orasa a wuyanta nanma yaji wani sabon d'umin masassara zau ya Kama jikinta,
janye hannun sa yayi ya miq'e ya nufi toilet ba jimawa ya fito da white mdn boket da ruwan d'umi a ciki ,
da farin towel ya zuq'unna gabanta ya fara sanya towel din yana Matso ruwa yana goga Mata a saman wuyanta da Kanta da cikinta ,
ya d'auki tsawon 25 mints yana Mata hkn sannan ta fara sauke ajiyar zuciya,
alamun
masassarar ta sauka knn ,
ta rufe idanunta sakamakon barcin daya kuma d'auke ta, ajiyar zuciya ya sauke ya dafe kansa yana tuhumar xuciyarsa akan ita ta jawo wa deejart wannan ciwon ta hanyar horon da yai Mata cikin garjejiyar Rana! Cikin ransa yakejin kamar ba dad'i dad'i, yamutsa fuska yayi kad'an ya jingina da bango,
da sauri ya miq'e tsaye sakamakon mgnr hesham daya jiyo a falo ,.
Kai tsaye ya fita wajen falon ,
ya hango hesham zaune a d'aya daga kujeren falon ya d'ora qafa d'aya bisa d'aya yana latsa waya , .
Sam saif bai son hesham yasan tana cikin bedroom d'insa dan haka ya daure yaje ya zauna a d'aya daga kujerun falon suka tafa sannan hesham yace wlh brother ynxunn na dawo office na gaji tilis shiyasa Saida na warwatsa naji qarfi sannan na fito,
Hope dai lpia kake Nema na ?"
tamqe kansa saif yayi ya juye kalar not well ya dubi hesham yace a ransa na canxa shawara ba yanzu ne lokacin da Zan fad'ama damuwana ba , sauke ajiyar zuciya yayi yace
"Do not ,
infact iam in condition sick ne brother shiyasa na kiraka kaje pharmacy ka d'auko min medicine na fever because I did not go with me ,.

" oh my brother sannu Bari naje na duba to ,".
Da sauri hesham ya fita ,
bayan sa saif yabi da kallo ,.
ya runtse idanunsa dan jin ciwon q'aryar da yarinyar can ta sashi yi lokaci d'aya ba tare da shirin saba.
cije lips d'in sa ya d'anyi ganin dawowar hesham ne yasa ya saki lips din ya karbi maganin yasha ya kwanta yayi kamar barci ya d'auke sa ,
a ransa kuwa Allah 2 yake hesham ya fita dan yaje yaga kota farka ?
Yayi sa'a kuwa yaga ficewar tasa.
da sauri ya miq'e tsaye ya nufi bedroom d'in Kai tsaye ......


By
Xayynebπ’¤π’¤
π“π“π“π’π’π’
π“π“π“π“π“π“
*doctor deejart*

π’‰
By
Xayynebπ’¤π’¤

*Fasaha online writer's f o w*

*Dedicated to my daughter deejart*

π…Ώ5⃣π”µ
π“π“π“π“π“π“
gaban ta ya isa ya zuq'unna,
har lokacin bata farka ba. numfashin ta ke sauka a hankali gashi kuma lokaci na tafiya,
shi kansa so yake ya fita amman jiyake in ya tsallaketa ya wuce bai wanzar mata da adalci ba ,
duban 'yar best d'in rigarta yayi duk ta jiq'e sakamakon ruwan da yai using dasu wajen gasa mata some areas na jikinta,
duk rigar ta shanye mata jiki musamman mamanta da sukayo sama abinsu,
har kan nipple Nata saida shaitinsu suka fito sakamakon bra da babu a jikinta.
wani baq'on feeling ne yakejin sa a jikinsa,
gabansa na d'an bugawa das! das! ,
gani yayi tayi wani juyi ta takure jikinta waje d'aya,
ga alamun sanyi ya Fara shigar ta,
ajiyar zuciya ya Saki ya dubi watch d'in hannun sa q'irar daimon yaga 6 saura na marece, tsoki yake sonyi amman ganin yanda take motsawa yasa ya dakatar dashi,
tar ta bud'e idanuwan ta,
ta dubesa da su cikin yanayi na rauni,
miq'ewa tayi zaune da d'an saurin ta,
ta kai duban ta ga inda take guga,
ganin q'unar da kayan wajen sukayi gaban ta yayi wata irin masifaffiyar fad'uwa tasan taja wa kanta wani q'arin laifin ne kuma,
cikin son a tausaya mata ta dubesa murya na rawa 2 tace "pleasss yaya saif wlh bada niyya nayi hakan ba kayi haq'uri na roq'eka!"
kallo ya bita dashi har saida tayi saurin sinne kanta qasa nan ta Lura da yanda rigar jikinta ta fiddo mata shatin breast Nata.
cikin dabara ta janyo q'afafunta ta rungumesu a qirjin nata,
ta zagayo hannayen ta ta d'ora kanta a q'afafun tana cigaba da d'an satar kallon sa,
dan ganin koya Lura da kayan da take boyewa.
ba tare da yace mata komi ba ya miq'e tsaye ya fita,
da kallo ta bisa tana boyayyar ajiyar zuciya dan ga alama bazai mata fad'a ba kmr yanda ta zata,
tabe 'yan siraran jajayen labbanta tayi a ranta tace Ashe yafara tausayi?
gani tayi ya shigo da rigarta a hannunsa ya miqa mata ko magana bai ba.
karba tayi ta zura rigar ta nad'a mayafin a kanta Wanda iyakarsa a wuyanta ne, miqewa yayi ya nufi hanyar fita saida yaje bakin q'ofa ya d'an dakata kad'an sannan yace
"You can go"
Abinda ya furta knn.
wani dad'i taji da yace ta tafi,
shagwabe fuska tayi ta q'arasa gabansa tace plssss yaya saif
"will you accompany with me?"
a d'an fusace ya dubeta yace
"accompany yhu?"!
miyaci q'afafunki ne to ke em ?''
But listen to me I can't,
Ya harereta tare da sake furta
" lazy girl"!,
marairecewa tayi tace
"sunmin _nauyi ne my foot yaya saif, shiyasa ban iya takasu sosai plsss KO bakin q'ofa ne ka kaini kaji yaya saif?"
ba q'aramin tausayin ta yakeji ba kuma data gad'i hakan kuwa yanzun,
dan shi yaja mata wannan matsalolin yake gani.
juyowa yayi ya ya nad'e hannayen rigarsa ya d'an duq'a sannan ya
Sungumeta yayi waje da ita.
ita kuwa sai cusa fuskarta takeyi can cikin q'irjinsa,
cikin dabara take shaq'ar numfashin ta a jikinsa tana d'an sakin murmushi,
Sai runtse idanunta takeyi ta hanyar sanyayyen ferfume nasa da take shinshina tana lumshe idanuwa.

Ji tayi ya dureta a q'ofa,.
ya jawo q'ofarsa ta sa ya rufe yayi ficewar sa a gidan gaba d'aya ma ko kallon ta bai kuma yi ba ma.
gwalo tayi masa tace "na q'aru dakai ay daiπ‰".

Shashen su ta shige Kai tsaye.
bayan sallar ishae ne suna zaune ita da momma ta shige jikinta tana Mata shagwabar ice take son sha ita,.
Shafa gashin ta momma keyi tace
"Yaushe ne zaki San kin girma ne deejart?"
Tun d'azun fa nike cewa munyi broke na ice cream a gidan nan,
ki Bari insha Allah gobe nasan dadynki zai shigo miki dashi.
"Kai momma ta,! yanzu har gobe bansha ice cream na ba ?"
"Eh man yauda gobe ay d'aya suke wajen Allah deejart"
Momma Bari naje side d'insu jawaher wataq'il can suna da".
Kallo momma ta bita dashi tasan deejart da kafiya kan abinda take so.
"To shiknn "
Abinda momma tace knn.
Kai tsaye hanya ta canza ta nufi side d'in su kakus.
har kusa dashi taje ta zauna lokacin water melon ne da banana da apple, anyi yankasu.
hjy zulfa ta kawo masa suna zaune suna fira yayin da suke shan kayan marmarin da spon fork,
hjy zulfa tace
" ya dai deejart?"
Shagwabe fuskarta tayi tace grand ma ice cream na fito nema ne namu yayi broke since yesterday Allah sa kuna da a nan?"
girgiza Kai tayi tace
"Kwata 2 bakwa gajiya da shan zaq'i duk bayan minti ko deejart?"
Sunkuyar da Kai deejart tayi tana murmushi.
kakus yace
" bar damun mun amarya ta , ya dubi deejart yace "jeki a fridge d'ina ki d'ebo iya son ranki nima Mahmoud ya shigo mun dashi d'azun,.
" yawwa kakus thanks ta furta tare da d'an sumbatar gefen fiskarsa ta miqe tsaye taje ta d'ebo guda 5 ta yi musu gud night ta nufi side d'insu.

Su basma ta iske sunyi rashe rashe a d'akinta bisa gado suna fira sai dariya suke q'yalqyatawa,
gefen su ta zauna ta aje sauran ice cream din a gefe,
ta bud'e d'aya ta soma tsoma spon a ciki tana d'ebowa tana sha,
Kafad'arta jawaher ta ingiza tace
" to ay muma sai ki bamu namu robar ko?
dan bake kad'ai zaki sha sa ba ehe π¤¥."
Basma tace real my sis jawaher ,.
Miemie kuwa batace komiba sai miq'a hannu da tayi ta jawo roba d'aya, ta watsawa deejart harara tace
" kuma kuka tsaya tambayar ta ay".
deejart tace
"dan Allah nidai karku shanye mun yanzun nan naje gun kakus na samo abina,
So kuma kuje Ku samo naku man",

"ba zamuje d'in baπ,inji miemie ta cigaba da fad'in
"Kuma Wanda kika d'auko d'in zamu sha".
Murmushi deejart tayi ,.
tura musu ice cream d'in tayi suka d'auka daman ita miemie tuni ta fasa Nata takusan shanye Rabin sa,
ita kuwa deejart d'ibarsa take kmar ba sha take ba ma.
Jawaher tace
"kudai musha ice cream ladies hhhhhhh.
gaba d'ayan suma suka kwashe da dariya basma ta dubi deejart tace " sis ya kika q'are da yaya saif kuwa?"
Jawaher da miemie kuwa duba jikinta suka hauyi KO zasuyi cin Karo da saitin duka a wurin
deejart ta .....

By
xayynebπ’¤π’¤
π“π“π“π’π’π’
π“π“π“π“π“π“
*doctor deejart*

π’‰
By
Xayynebπ’¤π’¤

*Fasaha online writer's f o w*

Bazan mancekibaπ *maman uswan* β¤
Ta fasaha online writer's, .
*writer of illar goyo*.
πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊAllah dai ya bar zumunci, π„π¤ ya qara had'a kawunan duk 'yan q'ungiyar mu ta *fasaha online writer's*,.


*Dedicated to my daughter deejart*

π…Ώ6⃣π”µ
π“π“π“π“π“π“
deejart ta janye jikinta tace
" what happened jawaher ,?"
why you did check my body also why?"
tayi mgnr a sanyaye.
Jawaher tace
"mtsss dubawa nake inga inda jikinki yai shatin duka manπ¤·π»β€β™€".
" waye zai dakan to?"
"Yaya saif man" cewar miemie,
"Yeah true guys"
inji basma,
ta cigaba da fad'in "ya kuka q'aqare da shi kuwa deejart? "
Tabe lips deejart tayi Wanda iyakarsa labbanta.
ta d'anyi shiru sannan tace
"bai dakeni ba amman ya sani masassarar dole sisters"!
dukkansu har had'a bakuna suke wajen furta " what sort of a fever sis ?"
Nan deejart ta fad'a musu yanda suka q'arke da yaya
saif,
matuq'a sun tausaya wa deejart kuwa.
Miemie tace "amman sisters ay yaci ace munsaba da wahalar man d'in nanπfa yanzu".
kawai muyi forget nasa ,
nan suka canza firan tareda fad'in tsohon mugu yaya saif.

Washe gari friday deejart ce tai saura bata fita hospital da wuri ba,
su jawaher tun wuri suka nufi school dan test da suke da.
wajen kakus taje tayi zamanta saida tym ya q'arato sannan ta je tayi wanka ta shirya cikin fararen kayanta na likitoci riga da wando 'yar hijab din iya wajen kafad'arta ta tsaya, kayan ba q'aramin bayyana Mata sihirtaccen kyanta suke q'ara yi ba,
ta fito taiwa momma sai ta dawo,
Kai tsaye shashen kakus taje tai masa bye bye sannan ta fito nan barandar motors na gidan.
a nan ta iske yaya saif da yaya Mahmoud zaune a fararen kujeru,
yaya saif dagashi sai singlet da tree quater suna duba wata new news paper mai magana akan harkar wasan qwallo,
hankalin su ya d'auku a mujallar.
dan haka yi tayi kamar bata gansu ba ta nufi motarta zata shige,
taji muryar Mahmoud yace
" doctor abin ba magana kuma ?"
(Haka samarin gidan ke kiranta da doctor)
d'an dakatawa tayi ta juyo ta dube su. caraf idanunta suka fad'a a na cikin yaya saif,
gani tayi yayi mata wani kallo mai Kama da harara ya d'auke kansa kuma ya cigaba da duba mujallar yana xuq'o q'aramin juice din strawberry yana sha abinsa ko kallon ta bai kuma yi ba,.
ajiyar zuciya ta sauke a d'an boye sannan ta baro wajen motar bayan ta cilla Jakarta a ciki ,
ta q'araso ta na fad'in " morning yaya saif &yaya Mahmoud,".
i hope you're well,?
ban lura daku bane a wajen shiyasa",
ta na kaiwa nan tayi shiru tana kallon tyme a siririyar agogon hannunta.
ko d'ago kai saif bai ba bare yaji mitake cewa.
dubansa Mahmoud yayi ya girgiza Kai kawai yace a ransa "nasan bazaka amsa ba daman,
dan hiyaq'in kai kawai ,but
da yaran nan zasu gane dasun bar shiga shirginka.

"So yaya Mahmoud Zan wuce banson nayi late,
ta fad'a hkn tana son danne damuwar ta,
dan tana takaicin dizgi a rayuwar ta shi kuwa yaya saif habitat Nasa ne any tym.
sai lokacinne Mahmoud ya yi firgigit ya dawo seti,.
Wayancewa yayi yace
" ok ,
if you don't worry why not I accompany to you hospital ?"
Murmushi tayi tace
"Never mind yaya Mahmoud thanks, natafi sai nadawo
dariya yayi yace baki son rakiyar tawa dai doctor na ganoki ay ammn ba komi ay,
Shike nan to
safe journey",
Murmushi tayi tace "thanks yaya Mahmoud".
a haka ta shige motarta taja ta
tabar estate d'in.
ta gefen idonta take watsawa saif harara a boye,
a ranta take fad'in "can kaji da baq'in halinka,
Matarka dai zata banu wa halinka
wlh yy saif"!π.
Saida ta bacewa ganin Mahmoud sannan ya lumshe idanuwa tare da dafe saitin xuciyarsa.
a hankali ya bud'e idanuwansa ya dafa kafad'ar saif yace
"My brohter wlh haq'uri na ya kusa q'arewa inaga ,
dan gskia
nagaji da boye boyen nan,
zuciya na tana wahala a banza a wopi a kan abinda nasan bazaifi q'arfi na ba gskia!."
duban sa saif yayi yace" i 'dont understand you Mahmoud?"
Ina maganar ka ta dosa knn?"
Mahmoud yace
"saif a duk duniya wlh inma na babban mahaukaci,.
Deejart ce mace q'waya 1 q'wallin q'wal da ta samu waje a zuciya ta tayi Kane Kane ,
gaskia indai an zauna family meeting namu zan fad'a wa kakus itace muradina,
wato matar aurena ta har abada".
rasa miya samesa saif yayi a lokacin, kamar ansa gatari an sassare lungu da saq'o na jikinsa yakeji,
ga bakinsa yayi masa wani irin nauyi ya gaza furta ko e ,
a ciki
dafasa yaji Mahmoud yayi yace "koya kace ne
My brother?"
Murmushin dole saif ya q'wato a fiskarsa yace
"Allah sa alheri brother,
dariya Mahmoud yayi yace ameen brother na,.
Amman dan Allah Ina Neman wani alfarma a wajen ka",
()
A hankali saif ya dubesa da kansa ke wani irin Sara masa lokaci guda.
" i listen to you brother "
Abinda ya furta knn
Mahmoud ya ce
"Yawwa brother please and please i beg you_,
ka daina d'aure wa 'yan matan gidan nan fuska,
kaga dukkansu q'annen mune ba dad'i iri hkn, example ma yanzu deejart ta gaishemu, ammn kanaji kayi birus da ita,.
uwa ba kaji taba?" Haba my brother gskia ba dad'i irin hkn,
Dan Allah ka daina
q'untata musu haka".
d'agowa saif yayi yace "ba laifina bane brother yaranne sun cika rawan Kai especially ma jawaher da basma,
dan ita ta miemie ta d'anso ta biyo doctor kum...,,,
dakatar dashi Mahmoud yayi yace karma ka had'a hiricin su jawaher dana deejart dan ita bama waje 1 aka d'ebosu ba,
nutsuwa da rashin so don rashin magana duk ta musu zarra,
Amm duk da hkn ka dinga sake musu my brother ba raini ay kamr ynda kake thinking nasu a kai OK?".
Jaridar hannunsa ya miq'awa Mahmoud ba tareda yace komiba ya miq'e tsaye ya dafe gefen kansa dake cigaba da Sara masa,
What happened to yhu my brother ?".
Cewar Mahmoud.
Saif da q'yal ya samu ya kalato Kalmar "banji dad'i ne tun dana tashi yau ,
shiyasa ma ko office bn jeba brother,
Bari na d'an shiga ciki na kwanta,
may be nasamu relaif d'in ciwon".
Mahmoud yace
" to shiknn my brother Allah sawaqa Bari nima naje nay shirin office.
Saif yace "OKey brother saika dawo to".
daga haka bai sake furta komi ba ya tura d'akin sa ya shige harda rufowa.
Kan bed ya fad'a yarasa gane mike muntsinin xuciyarsa haka ?
tun da Mahmoud ya furta son deejart har yake ikirarin zai shaidawa family yaji zafin masassarar daya tashi da ita a jikinsa ta q'aru nin kin ba ninkin,
Jin bakinsa yayi yana furta" why" Mahmoud why?"!
kana fad'in hakan naji d'aci a maq'oshina,?"
Plsss brother ka janye maganar nan taka ga deejart".!
Tuni masassarar ta ida rufesa ruf, haq'oransa sai rawar sanyi suke jikake kaf! kaf !kaf,!
Lumshe idanuwa yayi yana mai runtse idanunsa gam ya jawo bedsheet ya lullube jikinsa,
yanajin wayarsa na Ringing Amman ya kasa miq'a hannunsa ya jawo ta,
duk da yasan dadyn sa ne ke kiran sa dan ringtone nasa na daban yasa masa shida momynsa.

Tun isar deejart hospital d'in take fama da marasa lpia bata wannan room bata wancan room ,kozama tayi yanzu anzo ace doctor patient ta farka ,kokuma takasa barci ,ko kuka take, ko haihuwa ta q'iya, dole take tashi ta koma dan sake dubasu,
mutanen dake aiki da ita suna matuq'ar bata girma sbd tasan darajar mutane,
bata da wulaqanci wa jama'a marasa lpia kamar yanda sauran wasu likitoci keyi yanzu in suka had'u da patien.
duk da su kuwa sunsan deejart yarinya ce q'arama amman akwaita da hangen nesa.
Fitowarta knn a labour room ta na cire safar hannunta tana tuno yanda ta karbi haihuwar wata mata yanzu ,
gskia tayi matuqar shan wahala matar nan, da q'yar samu kan babyn ya fito deejart ta ida jawo sa ,
Zama tayi a office d'in ta tayi tagumi,
A ranta take furta ita shiyasa ko aure tayi bazata yarda miji yai mata ciki ba kuwa,!
dan ganin yanda Mata ke wahala a wajen haihuwa,
dan dayawa Mata sunsha sumewa a wajen haihuwa sbd tsabar wahala,
Miq'ewa tayi ta nufi laboratory tana fiddo wasu result,
ta jima sannan ta koma office tana dubasu one by one.
Jitayi an turo q'ofa an shigo.
tare da furta "hello,
d'aga kanta tayi a hankaki tare da zare medical glass d'in idanunta ta aje gefe.
Batace komiba ta mayar da hankalin ta a abinda takeyi,
dafa tebur din gabanta yayi yace
"Hajja doctor deejart gani na dawo ban dai yi zuciya ba ataimakawa bawan Allah nan dai Wanda kefama da sick of love deejartπ‘".
duban sa tayi da fararen idanunta tace " Abbas mafi cancanta ka haq'ura dani dan gskia a ra'ayina ban auren mai mata,
sbd gujewa fitina ni kuma gashi Sam wlh ban iya fad'a ba Abbas.
tad'an dakata sannan ta cigaba da fad'in "to bare Kai matan ka har 2 fa?",
ko wata ba'aiba fa da bikin ta 2n,
kuma kasan yanda muke da sameera amaryar taka,
Nicefa best friend Nata ,girgiza Kai tayi tace God forbid ban iya cin amana ba gaskia a rayuwa ta"
So gskia Kai haquri".
zama yayi a kujerar gefen ta yana qoqarin riqo hannunta da sauri ta janye tana watsa masa harara ,
Murmushi yayi yace afuwan sarauniyar kyawawa ta duk duniya,
Hararar sa ta kumayi tace "ka kiyaye i hate sort of this play"!
So be careful!!;"
da yake d'an duniya ne sai ya wayance da fad'in alright it is pass doctor,
Yamutsa face tayi tace " da dai yafi."
Abbas duban ta kawai yake a ransa yake furta Allah yayi halitta a nan,
komi yaji a jikin yarinyar nan, abubuwan har rawa sukeyi koyaya ta motsa jikinta kuwa,
duka duka ko 3 wks basu yi ba da had'uwa shima a kamun bikinsa da amaryarsa sameera ya ganta ,
Matuqa gaya ya zautu da ganinta dan yarinyar ta tafi da duk wani tunanin d'a namiji Wanda ke wajen ,da yake tasan class d'inta tabi ta d'aure fuska a yanda taga mazan wajen na Kai mata caffa ,
Tuni ya raya a ransa a lokacin wlh da yasan da irin babys d'in nan da mima zaiyi da sameera a aure?
Cikar breast da q'ugu ta d'ararwa matansa nesa ba kusa ba,
gata 'yar shafal 2,
jikinta a murje yake na tsabar Hutu da ya ratsata,
ga kyau da Allah ya bata,
Cikin dabara yasan tarihinta ta bakin sameera har inda take aiki da gidansu kuwa ta fad'a masa.
Ita atunaninta dan mutuncin da yake tsakanin ta da deejart ne shiyasa ya tambayetan,
shikuma abin ba hakaba a wajen sa.

Sauke ajiyar zuciya yayi a hankali ya furta
"Deejart "
dubansa tayi da dara-daran idanunta, batace komi ba amman kuma tana nuna alamun saurarensa.
Hakan daya fahimta ne yasa shi fad'in "tun tsawon sati d'aya knn nake bibiyarki ,
duk da kinmin tuni akan halaq'aru da sameera wlh inkin amince a yau duk Zan iya sakin su dan naga na aureki deejart wlh sonki a jini na yake deejart"
Zaro idanuwa tayi tace "inaga Kai bakada nutsuwa Abbas wlh ,
Ka saki matanka fa kace because of me is that?"
Lallai hakan ya nuna mun Kai bakada confidence na zama da matan ka sake for God,"
"A'a deejart ki fahimceni i do not mean that bec,,,
Dakatar dashi tayi tace "I have done the talk,"!
ta duba agogon hannunta taga 5 saura na marece,
Ta miq'e tsaye tare da d'aukar bag d'inta,
ta dubesa fuskarta a d'aure tace
" time up,
" lokacin tashi na yayi Zan rufe office na ",
ganin yanda yake shirin yimata magiya ne yasa ta bar office d'in,
waje ta fito
ta miq'awa messengern ta key tace " baba lado ka rufe min office ka ijiye mun keys d'in hannunka in nazo Zan karba ",
"To" to shiknn doctor deejart a sauka lpia".
Tace "

Please Login or Register in order to submit comment