Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ya matsa, juyowa tayi ta dubesa tace " yadai?"
jitayi yace
"patient ?"
waye haka aunty?"
Yana maganar ne kamar mai koyon ta,
Runtse idanunta tayi gam dukkansu sannan ta bud'e su ta ce
"Kaine patient"!
gani tayi ya zaro fararen idanunsa ya zubesu a nata yana binta da kallo fuska a d'aure.
gaban ta ya wani irin fad'uwa dan saitaga kallon sak irin Wanda yake musu a gida in sun 6ata masa rai !!!
A hankali ta janye idanuwan ta a nasa ta riq'o hannun sa tace "yi haq'uri to bakai bane"
Sai lokacin ya Saki fuskarsa.
Ita kuma taja hannun sa suka fice a room d'in Dr hasan na biye dasu yana murmushi a ransa yake rayawa a kwai rigima ga alamun saif kuwa....
h
XayynebπŸ’€πŸ’€
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ’ŠπŸ’ŠπŸ’Š
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
*doctor deejart*

πŸ’‰
By
XayynebπŸ’€πŸ’€

*Fasaha online writer's f o w*

*Dedicated to my daughter deejart*

πŸ…Ώ1⃣8βƒ£πŸ”΅
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
Inda Dr hasan ya barsu kakus har lokacin suna nan babu Wanda ya motsa,
shigowar suce itada saif hannayen su sarq'e da na juna yasa dangin saurin miq'ewa suka yi cirko cirko suna kallon saif,
yayinda shikuma yake liq'e da Dr d'in sa.
Kakus ne yace afara shirye shiryen tafiya gida kawai.
ay ko nan da nan su mahmoud suka fara d'aukar abinda ya kamata su d'auka suka fita waje suna shiga motocinsu,
zuwa lokacin momyn saif har ta gaji da son ruq'o hannayen d'an nata yana gocewa,
dan gani yake rabasa da Dr d'in sa zatayi,
iyayen na lura da hakan sai dai kawai su girgixa kansu.
haka dr hasan ya misu rakiya har suka shisshiga motocinsu suka tafi,
gaba d'ayan su kakus ya umarcesu dasu tafi shahinsa zai yi magana dasu.
bayan duk an hallara waje d'aya anyi tsit Ana sauraran bayanin kakus a lokacin deejart na kusa da momyn saif sai mamanya dake kusa da momyn saif d'in itama sai patient d'in nata dake 6arin damanta uwa ya shige jikin ta tsabar qwalailaita irinta saif haka take furtawa a ranta, dn har d'an zakud'awa take intaga shigewar tai yawa amman dukda haka saiya biyota, idanuwa suka had'a da Mahmoud Ashe yana Lura da hakan gani tayi ya sakar Mata murmushi tare da girgiza Kai alamun tabar gujewa saif d'in,
Sunnar da kanta q'asa tayi ita kanta tasan inda a cikin nutsuwar sa yake ba zaiyi mata Wannan shisshigewar ba,
amma fa a tunaninta.
Kakus ya fara magana da cewa
"Alhamdulilla ala kullihalin,
'Yan uwa na da 'yayana da kuma jikokina,
Maq'asudin taraku a nan dan in q'ara nausar daku mu godewa Allah a kowane irin hali,
rayuwar mu d'in nan dai gaba d'aya Allah ya tsaro mana ita tun kan a haifeka duk a abinda zai samu bawa yana cikin kundin rsyuwar sa a rubuce.
Wato Kai mai arxiq'i ne ko maras shi?
Kai shiryayyene ko batacce?
kai rayayyene ko matacce?
Kai mai lafia ne ko maras ita?
Zaka rayu cikin dad'i ko cikin wuya?
Kai d'an wuta ne ko d'an aljanna?
dadai sauran abubuwan,
to Kunga babu wanda yasan Wannan amsoshin sai ubangiji Allah mahaliccinmu buwayi gagara misali,
to cikin hakanne ta faru ga saifullahee,
yayi mummunan hatsari kuma sai gashi yasamu lpia baccin har mun kusan fidda rai gashi,
sai kuma lokacin da muke murnar samuwar lpiar tasa wata sabuwar qaddara daga cikin qaddarorin uban giji daya rubuto masa ta sake samunsa ta shafewar tunani,
to da hakane nike jan hankullanku daku yi haquri ku iyayensa da 'yan uwa a dinga add'ua koda yaushe dan ita add'ua tana matuqar kaiwa ga gaci, to alhamdulilla abinda yasa na ce muzo nan knn Kuma na gabatar muku dan haka kowa ya tashi yaje yayi abinda ke gabansa na sallame sa.
Nan dangi suka ce insha Allah zasu sanya saif a kowce salla tasu cikin add'ua akan Allah ya kawo masa sauqi za'edan.
Kakus qwarai yaji dadin hkn anan take yaita kissafowa Wanda zai kaisu aikin hajji a Wannan shekarar dukda yasan bakasawa sukayiba saidai kawai yana burin yaga yanawa dangi da 'ya'ya da jama'ar Annabi bauta da dukiyar sa.
nan sukayi godia suka tashi ,.
Baba barsu shine babba a dangin kakus dan sunxo ma tanga a shekaru ya isa wajen kakus yace " Alhj Abdul samad malaman islamiyoyinnan da makarantr Allo da ka kaiwa sadaq'ar buhunnan hatsi da shinkafa sunzo godia lokacin kana asibiti wajen saifullahee,
sun ban saq'o na d'in bin godia da add'uar samun lpiar kowa da gamawa duniya lpia.
Kakus yace masha Allah Allah shine abin godia,.
Ina Mahmoud da akram da sauran matasan?
duk sukace
"gamu kakus"
Yace yawwa kuje Kusa wad'an nan shaddojin da atanfofin a motocinku ku Kai gidan marayu da sansanin 'yan gudun hijira a matsayin sadaq'a
dukkansu suka amsa da
"tho kakus"
Suqa miq'e suka fita suka nufi s.t - room d'in inda kayan suke.
Akram da hesham tunanin su d'aya sukeyi a ransu suke cewa "da fa saif na lpia lau da shine jagoran tafia duk in za'a kai sadaq'a wani waje.
Allah sarki brother Allah baka lpia,,,,

A can cikin falo anata daga da saif ya saki deejart ta shiga ciki ya q'iya, sadda dadynsa ya zare masa idanuwa ya d'aure fuska sannan ya saki hannunta a sanyaye ya zauna wajen ya gama kai da q'afafu.
momyn saif d'in ce kakus ya umarceta data jasa su tafi cikin gida.
A can deejart ta samu ta shiga toilet tayi wanka ta shirya cikin kaya marasa nauyi ta fito falo ta iske ammy na jera abinci a dng table,
Ata baya ta rungume ta ta kwantar da kanta a bayanta ta lumshe idanuwa tace
" momy i am feeling hungry ☹"
Juyowa momyn tayi tace "to deejart ay gashi nn na gama girki zauna kici,
ta langwabar da kanta knn zata fara shagwaba su basma suka shigo falon,
waje suka zauna a kujerun dake kan dng suka Fara bud'e kulokin abincin jawaher tace
" woww momy badai iya girkiba,
Basma ta ce "ay shiyasa kikaga kullum nake liqe da ita a kiching Ina daukar cos,
momy tace to sarakan surutu yanxu dai maza aci abinci Nina shiga zanyi salla"
bayan tafiyar momy ne deejart taja kujera ta zauna sai hararar miemie take tace " kekuma daga zuwa mlm kin ba mgn kin wani fad'a wa cin abinci uwa mai sickness want food"😏
Ko saura ranta miemie bataiba tacigaba da cin abincin ta tana fad'in "ay indai kan cooking d'in momy ne kiceman ma abinda yafi haka"
Basma tace "hyyyy guys ansu lilla mana a gama cin abinci tukun,
Jawaher ta na faman matse dariya tace khazalika haq'qun ya ustaziyya basma"
harara basma ta sakar Mata sauran kuwa dariya suke musu a haka suka ci abincin,
bayan sun gamane jawaher ta ce" wlh baqaramun tausayawa yaya saif naiba q'warai sisters,!
Basma tace Uhmm wlh kuwa sis ciwo daga Wannan sai Wannan, Kai ALLAH yai mana maganin abin yakuma basa lpia, ameen suka amsa dukkansu,
Miemie tace yanzu ma daga wajen sa muke ganosa yanacen mynsa na fama dashi yaci abinci amman yaq'i"
"What a pity!"
deejart ta furta tare da dafe kai tayi saurin duban agogon hannunta taga lokacin shan maganin sa yayi da sauri ta miq'e tsaye tace "sisters zanje na basa maganinsa ko zaku zo muje tare ne?"
Jawaher tace
"no,
jeki kawai in kin dawo kya iskemu a wajen kakus.
"OK sai na dawo"
ahaka ta fice tabarsu suna ida q'arasa gyara wajen da sukaci abincin.
A can shashen momynsa ta shiga da sakkamarta hannunta d'auke da tiren magani ta q'arasa zama kusa da momyn saif tace
"Momy Ina yayan yake?"
momy tace " yawwa deejart qwamma da kikazo kingan sa can d'akin sa ya shige bayan nayi nayi dashi yaci abinci yaq'iya wlh sam ,
Harsu Mahmoud da suka dawo suka shigo tanan sunyi iya yinsu yaq'i ci,
nidai kaina na kaisa dakinsa ko Allah zaisa yatuno wani abu har yaci abincin Amman saif yaq'i ya, shiyasa inagafa rabakun da akayi d'azun ne yasa shi yin Wannan kumbure kumburen, dan Allah ga abincin sa can a flask ki d'auka kije d'akin da kanki kiga kozai karba daga wajenki zama da yunwa ay bazai yuwuba"
"to momy dama magaungunan sa nazo bashi bari in Kai masa abincin in yaso saiya sha maganin".
yaww deejart kina mana qoqari ay Allah miki za6i dai na q'warai"
Sunkuyar da kanta tayi a kunyace ta isa wajen abincin ta d'auka ta nufi d'akin saif d'in dashi.
Tana isa tasa q'afa ta tura q'yauren d'akin sbd kayan dake hannunta, q'ofar ya bud'e ta shiga ta mayar ta rufe.
a gefen gadon sa ta hangesa yayi zaune ya tsurawa tafin hnnunsa idanuwa kamar mai Neman wani abin a ciki.
zama tayi a gefensa bayan ta aje kayan q'asa kusa dasu Wizen 5 na marece ne a lokacin data kakki watch d'in ta.
A hankali ya dire Mata fararen idanuwan sa a fuskarta Yana kallonta,
Yanayin kallon nasa dayake Mata na tuhumane,
Tasan qilan dan ta gudu d'azun ta barsa shiyasa.
gani tayi ya matsa daga wajen sosai alamun fushi yk,.
ya kwantar da kansa a bedsheet dake saman gadon sa ,.
Murmushi tayi ta had'a hannu wa 2 tace"afuwan my patient "πŸ‘bazan sake gudu na barka ba ,
Kagama na Kama kunne naπŸ™‰".
A gain ya sake d'auke Kai gefe yaq'i q'ara kallonta ma.
Murmushi ta q'ara Saki,
a hankali ta rarrafo har ta iso wajen sa ta d'ora hannayen ta a kumatunsa ta tallafo fiskarsa nan da nan idanunsa suka shiga cikin Nata a Karo na 🀞🏻.

XayynebπŸ’€πŸ’€
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ’ŠπŸ’ŠπŸ’Š
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
*doctor deejart*

πŸ’‰
By
XayynebπŸ’€πŸ’€

*Fasaha online writer's f o w*

Oni xayynebπŸ’€πŸ’€πŸ€”
Ashedai masoyan *Dr deejart* har sun kai haka????????"

Uhmmmm,,,
ALLAH sarki☺,
Gskia fans godia Nike matuq'a,πŸ™πŸ»
ALLAH ya bar zumunci🀝 a tare a koda yausheπŸ˜„
A koina kuke ma
Alherin Allah ya isar muku.πŸ€—

*Dedicated to my daughter deejart*

πŸ…Ώ1⃣9βƒ£πŸ”΅
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
Q'asa q'asa tayi masa da idanuwanta tana kallonsa,tana d'an lumshe su tana bud'ewa kuma.
a hankali ta 6allo magani a sacet nasa ta matso kusa dashi sosai dan har gwiwarta ta hau tasa tace
"haaaaa bud'e bakinka ka karbi magani,,,"
maganin ya tsaya kallo ba tareda ya furta komiba sai daga bisani ya noq'e kafad'ar sa alamun a'a ya zaiyi ya bud'e ne ..?"
Murmushi tayi ta sake 6allo wani maganin q'arin jini ta ce
"kalle ni yaya saif, haka zaka yi,,,
nan ta tura maganin a baki tabi da ruwa,
Shikuma idanuwan sa suna biye da ita yana kallon yanda take yin.
ga mamakinta d'an murmushi taga yayi ya karbi maganin nasa dake hannun ta ya tura a bakinsa shima yabi da ruwa ya had'iye,,,,
a haka dai taita 6allo masa sauran magungunan yana turawa a baki yana had'iyewa..
Murmushi ta sakar masa tace
"yayi kyau my friend give meβœ‹,
ganin ta d'ago tafin hannunta yasa shi shima d'ago Nasa Amman bai San mi zaiyi dashi ba sai ya tsaya kalkonsa kawai,.
hannun nasa ta janyo ta had'a da Nata ta tafa,
tace haka nake nufi,
Sannan ta had'a yatsunsu waje d'aya🀞🏻 tace
"daga yau Kai my friend d'ina ne mun zama abokai,
A hankali ya furta "miye friend doctor?"
gyad'a Kai tayi tace friend sune ''Wanda suka yarda da juna har had'uwar jininsu yasa suke kasantuwa a tare,.
Kamar ni dakai dai d'in nan haka,.
Ay kayarda dani ko?
ya g'yada Kai alamun eh".
tace yawwa kuma nima na yarda da kai, shiyasa ma sbd jida Kai da nike fiye da sauran friends d'ina kaga yanzu nan har abinci Zan baka a baki,
ta fad'i hakan tana mai jawo abincin gabanta ta d'ebo da cokali ta nufi bakinsa dashi .
Gintse lips d'insa yayi dan bai San ya zai bud'e bakin ba, da idanuwa kawai yake binta wato yana neman q'arin bayani.
"ohhhh my God"!
ta furta tare dafe KaiπŸ€¦β€β™€.
d'agowa tayi ta dubesa sosai ta furta a hankali.
"Kalle ni to friend,
duban ta d'in kuwa yayi yaga ta bud'e bakinta tana zura abincin a ciki tana taunawa,tayi haka yakai sau 6 sannan
tace
" to kaima haka zakayi Amman yi yanxu muga..
ilai kuwa shima ya bud'e bakin nasa, itama ta matso da hannunta ta zuba masa abincin a bakinsa yafara ci, da wayau da dabara irin nasu na likitoci tasa ya cinye abincin nan duka,
sannan ta janyo flate d'in yankakkun kayan lambu tana basa a baki sha,
har saida ya d'auke kansa alamun ya q'oshi sannan ta q'yalesa.
gani tayi yakamata ace yayi wanka hakan, amman tarasa yaya hakan zai yiwu,?
Jin an turo q'ofar d'akin ne ya sata saurin juyawa dan taga waye?
baq'ara min dad'i tajiba na ganin Mahmoud ne ya shigo, da sauri tace
"Yawwa yaya Mahmoud naso shigowar ka daman,
zama yayi tare da fad'in" to doctor gani to ay nazo"
A xuciyarsa kuwa wata sabuwar soyayyar deejart ce ke ruruwa a zuciyar sa kullum,
anata 6angaren kallon da Mahmoud ke mata takan rasa sukuni wayewa tayi da fad'in
"yaya Mahmoud ya kamata fa yaya saif yai wanka hakan gskia ,dan har q'arfin jikinsa ma zai q'aru,
yanzu kajasa kutafi toilet ka nuna masa yanda zaiyi wankan a misale da jikinka saika fito kabarsa, nasan brain d'in sa nada q'oqarin d'aukar abin da aka koyar dashi, kuma tabbas nasan indai ka nuna masan hakan zai iya,
Kuma kaima naga yana yarda dakai, koya ka gani yaya Mahmoud?''.
d'auke idanuwan sa yayi a kanta sonta har rinjayarsa yake yakeji , sauke ajiyar zuciya yayi yace"hakan ma nada kyau doctor"
Miq'ewa tsaye yayi ya miq'awa saif hannu yace "come my brother,
hannu shima saif d'in ya miq'a masa ya ruq'osa yana murmushi ya miqe tsaye suka nufi toilet d'in,
Amman saif yana tafiya yana waiwayen doctor din tasa ita kuwa ganin hakan yasa ta sakar masa murmushi tare da d'aga masa girarta guda d'aya a haka har dai suka shige toilet d'in.
Sauke ajiyar zuciya tayi ta kwashe kayan abincin ta fita dasu zuwa,,,, ,,,,,,,


XayynebπŸ’€πŸ’€
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ’ŠπŸ’ŠπŸ’Š
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
*doctor deejart*

πŸ’‰
By
XayynebπŸ’€πŸ’€

*Fasaha online writer's f o w*

Q'awa ta gari wato my nmcy
*zee calm*
Ina alfahari dake a koda yaushe,,,
i love u😘

*Dedicated to my daughter deejart*

πŸ…Ώ2⃣0βƒ£πŸ”΅
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
da dare misalin qarfe 8:00,
deejart ce zaune a gaban gadonta tana tunanin kayan da zata sa, Sam batason zafi shiyasa bata d'auko masu nauyi ba , wata doguwar rigace 'yar hyalen 2 mai siraran hannuwa Sai 'yar himar d'in kayan Wanda iyakarta kafadu ta zura plat shoes d'inta ta nufi dakin momyn ta.
ta isketa tana had'a kayan gugar da d'an lami mai musu guga ya kawo, q'arasawa tayi ta rungume momyn tata ta baya cikin sigar shagwaba tace
"momy Ina dady na?"
du yau ban gansaba fa sai a asubiti da nan gida,
nida saimu hade dashi yakai sau nawa a rana☹".
Momyn ta juyo ta jawota gefen gadon suka zauna tace" deejart d'ina bnda abinki ay dama bazaku had'e ba ay, inda yau busy yake amman naji shigowar sa wataqil yana shashen kakus na kune,
"Yawwa momy to Bari naje can na samesa daga nan kuma zan wuce gun yaya saif na basa magunguna sa.
" to shiknn Sai kin dawo"
shashen kakus ta shiga ta hango dadynta da dadyn saif da kakus suna magana,daga gani magana ce mai muhimman ci sukeyi,,,
q'in ida shiga tayi taja baya tana shirin barin wajen,,,
abinda kunnen ta yajine yasata saurin la6ewa jikinta na d'an rawa rawa,
Kakus ne ke cewa"lokaci na tafia na auren yarannan bayan Wannan lalurin daya samu saifullahee da tuni munyi taronda zamuyi mun tsaida ranar d'aurin auren inda lokacin da aka sanya yayi har ya wuce,,
bazamu jada ikon Allah ba a ce za'a bar aure ba sbd ciwon saifullahe bazaa ce zaaqi hada sunnar manzo ba , dan haka zamu tsaida rana kawai ta d'aurin aure,
Saifullahee kuwa in Allah ya bashi lpia
Shikuma sai ayi nashi daga baya.
kakus yayi d'an shiru sannan ya maida gilashin idonsa yaci gaba da fad'in
"gashi shi Wannan shashashan Mahmoud har yanzu yaq'i kawo mana za6in sa,
itama deejart shiru?
dadyn saif ne ya fara magana da fad'in" hakane baba insha Allah kamar yanda aka da niyyar auren yarannan za'ayi insha Allah,
Inda Allah ya qaddara ba rabon da saif d'in za'ayi bikin tare,
kuma maganar Mahmoud mi zai hana a had'a su shida deejart ayi bikin?''
dadyn deejart yace
"Kakawo shawara d'an uwa Nima kuwa kamar kasan na kimsa hakan a zuciya ta ,.
Kakus yace
"to shiknn Masha Allah, ALLAH yai muku albarka kuje kusanarwa sauran 'yan uwa nan da qarshen Wannan watan za'a yi taro, wato nanda sati 1 knn za'ayi taron family da 'yan uwa,
kuma kunsan dai a ranar da akasa rana sati d'aya ne tsakani ake d'aura auren ni a tsarina kuma yanda nakeyi fatan kun fahimta?"
dukkansu suka amsa da "eh, ALLAH kaimu lokacin baba, kuma zamu sanarwa sauran kamar yanda ka umarta insha Allah zuwa gobe,,,,,
Iyakar nan deejart ta ji tayi saurin barin wajen sbd motsin alamun zasu fito dataji ,,.
Waje tasamu a kwanar shashen saif ta dingi sharar q'walla zuciya ta na suya mai had'e da q'una , tana kuma sake tuna mata wai ita za'a had'a da yaya Mahmoud?!.
zuq'unnnwa tayi a wajen tana shessheqar kukanta anan ta jima sannan ta rarrashi kanta ta nufi dakin saif d'in,,
ta murd'a qofar ta shiga jikinta a mace. ,,
A kan gado ta hangosa kwance, amman duk ya zazzalo da rabin jikinsa a q'asa kansa na kallon sama kamar mai tunanin wani abu,,
da sauri ya miq'e zaune yana murmushi danjin dad'in ganin doctor d'in tasa ,..
a hankali ya furta
"doctor" !
gefen gadon ta zauna tana kallonsa itama tana masa murmushin dole dan yanda takejin zuciyarta na tafarfasa ,....
da q'yar ta bud'e baki tace
"em my friend"!!!
da sauri ya rarrafo ya kwantar da kansa a cinyarta.
gani tayi ya sanya hannu ya shafo,,,,,
.
XayynebπŸ’€πŸ’€
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ’ŠπŸ’ŠπŸ’Š
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
*doctor deejart*

πŸ’‰
By
XayynebπŸ’€πŸ’€

*Fasaha online writer's f o w*

*Dedicated to my daughter deejart*

πŸ…Ώ2⃣1βƒ£πŸ”΅
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
#gani tayi ya sanya hannu ya shafo hawayen fuskarta da har lokacin basu daina zurarowa ba, gashi kuma duk ya jiq'e mata gaban hymar d'inta da lema.
Tashi yayi ya riq'o hannayen ta ya had'a da nasa ya matse su gam waje 1, wani irin yarrrrrr deejart taji, a lokaci d'aya kuma kukan yai sama ko q'asa, d'ago kanta tayi a hankali ta dubesa taga ya girgiza Mata Kai ya matso ya Ciro hymar d'inta ta yana goge hawayen fuskarta dashi.
Jitayi wani farin ciki na ratsata batasan sanda ta kamo hannunsa ta manna da nataba wani ta d'ora lips d'inta a hannunsa ta d'an sumbacesa kad'an,
sannan ta miq'e tsaye shima ya miq'e tsaye da sauri ya isa q'ofar fita ya kakkare q'ofar da hannayen sa alamun bazata je ko inaba dan shi a zatonsa fita zatayi,
Murmushi tayi batasan miyasa takejin farin ciki da yayewar damuwa ba indai tana kusa da yaya saif,
hakan ya jima yana faruwa da ita tuni ba tun yau ba kuwa,
baccin ta d'auko magungunan nasa inda suke a jiye a gefen lakar sa ta koma bakin gadon ta zauna tare da ya fito sa da yatsarta na tsakiya alamun yazo.
da sauri ya q'araso ya zauna yana sakar Mata murmushi dan yaji dad'in da yaga ba tafiya tayi ta barsa ba,
abinda ke damunta yanzu shine wazai dinga kula da yaya saif yanda ya kamata in sun yi mata auren nan?"
Shan maganin sa a Kari?"
cin abincin sa cikin dadin rai?"
duk ya saba ita take masa hakan to yanxu duk randa yaga bata ya abun zai kasance?"
Ita kanta yanzu ji take wata sabuwar q'allafar son kasance wa dashi a kowane bayan minti takeji son yi,
Sam bazata ji dad'i ba in aka rabata da friend d'inta,
Jitayi kamar ana laso mata fuska da harshe mai tsananin taushi da gumi, firgigit tayi ta dawo daga tunanin ta, abinda ya bata mamaki bai wuce friend d'inta dayake shanye Mata hawayen fuskarta ba cikin yanayi na matuq'ar tausayin halin dayaga doctor d'in tasa a ciki ba.
Idanuwa ta zaro bayan ya janye bakinsa a fuskarta tahau shafa fuskarta d'in babu wani danshin hawaye kuwa da saif ya barsa yai Mata saura a baby face d'inta kuwa.
Murmushi taga yanayi Mata yana sinne Kai gefe matsowa tayi kusa dashi sosai tasa hannayen ta ta d'ago fuskarsa tace
"friend kalleni nan"
d'agowa yayi ya zuba mata fararen idanuwan sa a nata,
da sauri ta runtse nata idanun gabanta na halbawa 6al!! 6bal!! 6all!!,,,
daurewa tayi ta bud'e idanuwan amman taq'i yarda su sake had'a idanuwan.
Cigaba tayi da cewa
"Waya koya maka hakan nan da kaimun yanzu,,?"
Janye fiskarsa yayi gefe yaq'i magana. da sauri ta sake juyo da fuskar tasa,
" fad'amun mana friend? "..
fad'amin,,,,,
komu 6ata kuma bazan q'ara zuwa gun ka ba☹".
da sauri ya zuq'unna a gabanta ya riq'e hannayen ta ya fara maganar sa a hankali yace
"doctor ni na yi"
duban sa tayi tace
"Kamar ya Kai kayi?"
"Hakanan"
yasake bata amsa yai shiru abinsa ba tareda ya sake furta ko( A )ba a bakinsa.
Murmushi tayi tare da shafo wajen da ya sanya bakinsa a Kai ,, uhmm ho my friend dan kaga Ina kuka shine kamun haka ko?"
Murmushi yayi yana mai d'aga Mata Kai alamar "eh"
to shiknn yanzu dai zo kasha magungunanka kar lokacin ya wuce,
Fara basa tayi yana karba yana sha , a haka har yagama sha.
ta juya ta jawo plate d'in abincin sa tana fad'in "friend ya kamata xuwa yanzu fa ace kan nazo in momy ta kawoma abinci ka dinga ci da kanka basai wai kajira nazo ba,
kada ulcer ta kamun min friend kasan bazan so hakan ba ko?"
q'in tanka Mata yayi taga ya ta6e lips dinsa ya kuma d'aure fuska alamun yaq'i abinda tace d'in a ransa,,
d'an d'aga murya tayi tace "dole ne kuwa ka koyi cin abinci da kanka friend.
Gani tayi ya tashi daga gabanta ya koma q'arshen gadon ya had'e Kai da gwiwa.
Jitayi kuma ya bata tausayi kuma , miyasa ta d'aga masa murya ne ma ita wai?''
miq'ewa tayi ta isa wajen sa ta zauna tasa hannun ta ta d'ago da kansa tace " in kaji haushin abinda na fad'a ma friend Kai haq'uri to plzzzz,,,
murmushi taga yayi alamun ya haq'uran,,
Itama murmushin tayi ta kamo yatsun hannunsa tana wasa dasu tace
"am friend abinda yasa nace ma ka koyi cin abinci da kanka ko ba tareda niba kaga su dady aure suke son yimun"!!!
ta qarashe maganar tana jin wani maq'aqi 2n d'aci a zuciyar ta.
Jitayi yace
" doctor aure ?"
Miye aure kuma?"
girgiza Kai tayi ta had'a tafukkansu waje d'aya wani irin d'umammen gumi 2 mai dad'i taji yana ratsa mata jiki , a hankali ta runtse idanuwan ta,
Jin ya girgiza Mata hannu da nasa hannun dake cikin Nata sannan tayi saurin ware manyan idanuwanta fararen tar dasu a kansa.
a hankali ta ce
"In akace aure friend shiknn fa ana nufin bazamu sake ganin junaba a kusa 2 Sai dai in mijina ne zai dinga zauna wa a kusa Dani haka ,
Jitayi yace
"doctor to shiknn ni Zan fad'awa dady d'in yai mana auren tare sbd mu rinqa zama kusa 2 kamar yanda kikace.
Maganar tasa ba q'ara min mamaki ta bata ba sosai.
duban sa tayi tace
"Shikenan my friend mubar maganar nan,
oya oya zo nabaka abincin ka kar ya surace ya huce."
maq'e kafad'arsa yayi" yace em em ni anan Zan ci doctor "
dafe kanta tayi tace
" hooooπŸ€¦β€β™€ my friend, yau sarauta ta motsa knn ko?"
Uhmm to Bari na kawo ma inda kafi son ci anan yau".
Miq'ewa tayi tsagwayam ta je ta d'auko masa abincin ta dawo ta zauna ta fara basa, shima yasa Mata q'wallafar saiya bata abincin da kansa shima,
dole ta yarda kuwa yana bata a haka har suka gama.
Miq'ewa tayi zata fita mayar da kayan,
taji ya riq'o mata hannayen ta,
duban sa tayi taga ya marairaice alamun zai bita.
dawowa tayi ta zauna a gefen gadon tace
"Noooo friend ka zauna karka fita, kaga dare ne yanzu bare mufita a estate d'in nan zuwa wurare, duban agogon hannunta tayi ta cigaba da fad'in
" yanzu kaga 10 saura ka Bari gobe maje yawon shaqatawar ko friend,? ".
Noq'e kafad'ar sa yayi yace " a'a'
ya matso ya d'ora kansa a q'irjinta ya kwantas yana jujjuya kansa bisa breast d'inta yana fad'in "em em doctor zanje ni dai" jitayi jikinta yayi sanyi nan take,
jin kwanciyar kansa a dukiyar fulaninta hakan ba q'aramin susu tata yayi ba,
Jitayi sunyi baya luuuumm sun kwanta a gadon a tare,
runtse idanuwan ta tana fad'in
" friend ka,,,,,

XayynebπŸ’€πŸ’€

XayynebπŸ’€πŸ’€ce
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ’ŠπŸ’ŠπŸ’Š
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
*doctor deejart*

πŸ’‰
By
XayynebπŸ’€πŸ’€

*Fasaha online writer's f o w*
.
Gaisuwa ta musamman gareki swt ht d'ina
*rahmat nalele*😘

*Ayush ilyasu* kema kina heart d'ina fa irin q'waran gaske d'in nanπŸ˜˜πŸ˜‰

*Dedicated to my daughter deejart*

πŸ…Ώ2⃣2βƒ£πŸ”΅
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
#runtse idanuwan ta tayi tana fad'in
"Friend mu tashi zaune man,
kaga tafiya zanyi na kwanta barci,
dare yayi kada momy ta duba ni a d'akina taga ban nan kaji friend?"
Manne kansa ya sakeyi a inda yakejin wasu irin tausasan abubuwa guda 2 Wanda d'an tunanin sa da yake dashi bazai iya tuna masa ma'anar suba, shidai abinda yasani shine kawai yaji dad'in yanda yake tuttura kansa a abubuwan

Please Login or Register in order to submit comment