Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tabe lips ya ce ''(never) har abada kuwa ni in duq'awa mace Ina tunanin ba'ayi irin taba mlm!!", dan haka kadaina sakoni a shirgin wadannan q'warinan yaran".
Yana kaiwa nan ya cigaba da latse latsen wayarsa.
daga Mahmoud d'in har deejart binsa suka dinga yi da kallon mamaki.
A hankali cikin rawar murya ta sake cewa ,
" a'a yaya Mahmoud bashi neba ma ay".
" to shiknn doctor yanzun abin na-nan na hure miki kokuwa ya fita?"
da sauri tace
"ya fita ay tun d'azun ma".
" to shikn. ".
Wani d'an farin akwatin sarq'a ya fiddo a al-jihunsa yace " amshi doctor karki bud'e a nan sai kin koma d'aki".
Karba tayi tare da gewayesa ta fice a d'akin .
A wajaje daban daban taita hango su jawaher na zance dasu akram.
Girgiza Kai tayi kawai ta shige shashin su, ta shiga d'akinta ta aje akwatin sarqar nan a gadonta ta shiga toilet ta watso ruwa ta fito ta zura sleeping dress nata sannan ta hau gado ta kwanta.
ta lumshe idanuwa ranta fal tunanin abinda yaya saif yayi Mata sai murmushi takeyi Wanda takasa sanin miya jawosa,
Ringing d'in wayarsa taji d'aukowa tayi ta duba sunan Abbas ta gani tsoki tayi ta aje wayar , jin yaq'i daina kiran ne yasata cewa "natacce" kashe wayar tayi dukkan ta.
ta jawo bedsheet ta rufe jikinta baccin tayi addu'ar kwanciya barci dan tagaji matuq'a yau, ta murgina knn taji ta danne abu mai tauri ya kuma shiga jikinta sosai "wash"!
Tace ta miq'e zaune ta duba,
Ashe abin da yy Mahmoud ne ya bata, ita tama manta shaf dashi.
Bud'ewa tayi wata sarq'ace ta gold mai masifar kyau da 'yan kunne da xobenta da @warwaro sai daukar ido suke, kaida ganin su kasan nera tayi kukanta wajen.
Haqiqa ba qaramin burgeta sukai ba kuwa.
wata 'yar farar hankicif ce ta fado a cikin akwatin sarqar.
Hannun ta takai ta d'aukota ta warwareta a hankali.
gani tayi an rubuta da manyan haruffa kamarhaka,,,,π“
*MY DOCTOR DEEJART*π“

Tunani ta tsaya yi, mai yaya Mahmoud yake nufi da wannan *MY* d'in tasa kenan?"
zuwa can ta saki sanyayyen murmushi tace "nasan ma q'ilan *MY* d'in tana nufin tasa a 'yan uwance kenan.
Murmushi ta sake yi tace "Allah sarki yaya Mahmoud kyawun halinka yasha ban ban dana wannan maq'etacin yaya saif
Kuma ma...,,,,
maganar tata ta yanke sakamakon wata irin zugin zafi da cikinta da dokin wuyanta, ystsunta sukaja @ lokaci d'aya,
wato inda saif ya mammatse mata su knn " "wayyyyyyo Allah na mommy dady na!!!!!"
ta fad'a da q'arfin gaske.
saiga ammy da dadynta sun shigo d'akin da gudu kuwa har suna Karo da junansu wajen son isa ga 'yar tasu q'wallin qwal guda d'aya wacce sukejin ta kamar rai!!!

Xayynebπ’¤π’¤
π“π“π“π’π’π’
π“π“π“π“π“π“
*doctor deejart*

π’‰
By
Xayynebπ’¤π’¤

*Fasaha online writer's f o w*

*Dedicated to my daughter deejart*

π…Ώ1⃣1⃣π”µ
π“π“π“π“π“π“
Har gaban gadon suka qarasa suna tambayar ta lpia?.
Rasa mizata ce musu tayi da qyar dabara ta fad'o Mata ta dubi momy dake riqe da ita tace
"Momy nafito a toilet knn santsi ya kwashe ni ya yar dani a gado shiyasa".
Dady yace" ai kamata yayi kiyi add'ua deejart bakiyi wannan qara ba haka, bakiji yanda kika razana mu ba da momynki"
Sinne Kai tayi a jikin momyn tace "zafin ne yasa bansan sanda nayi hakaba dadyβΉ".
Murmushi yayi yace to shiknn deejart Allah bamu Alhairi kada kimanta da add'uar barci fa"..
" to my dady thanks night"..
Kanta ya shafa ya sumbaci goshin ta sannan ya fita yabar momy tana riqe da ita.
Duban ta deejart tayi tace "momy kije ki kwanta kema.
momy tace "deejart dubeni nan"
A hankali ta d'ago ta dubi momyn nata tace "miyafaru ne momy?"
"Yanzu deejart duk cikin samarin ki bazaki tsaida d'aya Wanda zai zama miji a garekiba kina ganin dai yanda su jawaher suka tsaida su akram a matsa yin mazajensu kuma kakus ya daga miki afa matuq'a inda yace tare za'a had'a bikin ayi sa gaba daya,
Kuma kinsan al'adar gidan nan bassa sa rana a biki ranar daurin aure kawai ake tsayarwa.
Keda saif ne da Mahmoud kadai kukai saura baku fiddo xabin kuba kuma kunsan lokacin da kakus dinku ya q'ayyade muku naku fito da zabinku kuma ya kusa ko?"
a hankali ta sunnar da Kai q'asa tace "eh momy"
Momyn tace "saura kwana nawa ne to wa'adin ya cika?"
deejart ta dan tsaya tunani zuwa can tace"momy I think remains 2 weeks ne"
Momy tace "to wlh kusan abinyi dan in tsohon kakus d'in nan naku yasa doka 'ya'yansa bamai q'etareta bare mu 'yan uwa.
Kuma duk inya sanywa mutum lokaci kan abu har lokacin yazo vaiba kunsan yanda yakeyi?"
Idanuwa ta fiddo waje a tsorace tace "a'a momy"!
Momy tace" yanda yakeyi shine zai zaba maka d'aya daga cikin families d'in danginsa ya aura makashi ko ita,
KO ka so shi ko kar ka soshi wannan yarage wajen ka inda yabaka dama kaikuma kaq'i amfani da"
Nima nan dadyn ki shi ya auramun shi sai akayi sa'a kuma muka aminta da juna gashi har mun haifeki yanzu , dan haka kar kiga kakus na sakar muku fuska kuzaci zaku samu sassauci akan umarnin sa,,
Uhmmmm wlh Ina gaya muku duk Randa ranar tacika kaf zai d'ebe wasan jika da kakan dake tsakanin ku dashi ya gwada muku ainihin kalar tasa,
Dan haka ki tsaya kiyi tunani akan fidda mijin qwarai deejart,
Momy ta kwantar da ita ta kullubeta da bedsheet dinta ta tofeta da add'ua tace "mu kwana lpia 'yata ".
Da qyar ta qaqaro murmushi dan gaba d'aya maganganun momy sun kashe mata jiki ,
a hankali tace " me too night momy".
Momyn ta tafita tare da switch off d'in bulb d'in d'akin.
tana ganin fitar momy ta ture bedsheet din ta miq'e zaune ta yi zuru zuru duk tsoro ya cika mata ciki kuwa.
xuciyarta ta tuno Mata Abbas kota yarda da shine? "
Girgiza Kai tayi alamun a 'a,
sulaiman ya fad'o mata d'an kawu hasan, wato d'an uwansu ne nan cikin estate din yake da matarsa d'aya.
sake girgiza Kai tayi tace "banson mai Mata nikam,
ga d'an gidan kawu jamilu,
salis shima ganin ba fuska yasa ya q'yaleta bawai dan ya bar son taba.
Shi kuma saurayine baida Mata , amman kuma Sam bai mataba a tsarin namijin da take burin aure.
Gefe d'aya kuma ga samarin da ke Mata dafifi wajen kira, tama rasa inda suke samun number ta.
Runtse idanunta tayi ta koma ta kwanta tana fad'in solve my problems ya Allah,"
a-haka har ta kwanta bacci bata samu mafita ba.
A bangaren saif kuwa tun lokacin da Mahmoud ya bawa deejart abin nan yaji kansa yai masa wani gingirinmin, wani abu ya taso masa yana son kamar zai tokare masa maq'oshi tuni zufa ta fara 6arko masa a duk wani matsirar gashi ta jikinsa kuwa.
Jiyayi kamar ciwon sa na-neman dawo masa ,
yanaji Mahmoud na masa magana yai masa banza dan wani mugun haushin sa da yakeji kamar ya rufesa da duka, tun bana ma da yace yama ta kyautar sarqa, kamar ya shaq'osa yake ji @ lokacin,
ba jimawa su akram suka dawo suma daga zancen.
Mahmoud yace "yawwa Guy's q'wamma da kuka dawo ko ba komi nasamu abokan fira inda wannan miskilin yaqi tayani firar."
dariya su kasa sukace " q'yale wannan guy d'in kawai Mahmoud ciwon rashin mai son sa yake damunsa hhhhhh,
In da dai mu muna da namu masoyan kuma har iyaye sun sani ay Alhamdulilla yanzu fatiha kawai ya rage a shafa mana".
cewar akram, sauran suka amsa da "kana ruwa guy wannan hakan take , wata sabuwar dariyar suka Saki.
Mahmoud ya girgiza Kai tare da cewa" kayya brothers ay kuwa Ina tsammanin kaf samarin gidan nan namu bamai farin jinin 'yan mata kamar saif,
Tuni suka tasowa Mahmoud suna fad'in "a banza dai inda har yanxu yaq'i gwada mana fiance tasa bare mu-shaida hakan".
Mahmoud yace
" wlh ni abinda yake sani farin ciki nakusan fita tarkon kakus saura saif kuma aiki ya ragewa",
Tafawa sukayi tareda cewa kasamo Mata knn? ai qwamma ka daina biye halin wancen dodon matan,"
Hararsu saif yayi yace "plzzz kun cikin kunne da shouting kaina ciwo yakemun so I want sleep now.
In this your chapter what is this for?"
Mahmoud yace
"a'a saif Kai ne dai baka ga amfanin firar tamu-ba mu munga amfanin ta kam, hesham yace" qwarai kuwa Mahmoud fad'a masa dai,
Saleem yace "Mahmoud wacece ka tsayar a fiance taka ?"
anan gidan take koko?"
Tsoki saif yaja dan tunanin yanda yake zaton Kalmar deejart zata fito a bakin Mahmoud a-matsayin fiance tasa jiyayi kamar tsanar Mahmoud na d'arsuwa a ransa ba tareda ya Ankara ba.
Jiyayi akram yace "mlm daina mana tsoki dan bada Kai suke-ba ,kawai in baka son firar hanya a bud'e take saika fice".
" bazan fita d'in ba d'an iska kawai dakai"!.
Saleem da heesham dariya kawai suke misu hesham yace "Amman akram d'an iska ne Kai wlh ya zaka tada patient a makwancinsa ne?"
Akram yace "patient ko kuma dai piteena?
sbd baka ganin maganganun daya gama watsawa su miemie masu zafi d'azun?
d'an iskan wai shi nan marar lpia."
Mahmoud yace "yanzu he is feeling better fa,
Ku barsa ya q'ara hutawa haka nan, kunga yayi kwanciyar sa ma ya shareku kune ya Bari da 6a6atu,
kuma ni batun in fad'a muku wacece fiance na ?
A ina take?
ku bari in lokacin yayi zaku sani, wato ranar da kakus yake Tara dukkanmu da dangi da 'yan uwa in za'a yi mgnr aure wato ina nufin in kowa zai fad'i ra'ayinsa akan wacce yake so ko
take so, OK? "
Yes guy hakanma is OK, cewar su saleem.
Mahmoud yace but we change chapter now,
guys tomorrow is Saturday we did,,,,,
Ya d'an dakata sukuma suka ida
" muna da wasan qwallon raga hhhhh"
"Yeah,guys"
cewar saif ya fad'a haka yana mai tashi zaune,
Mahmoud yace dayake an tabo inda kafi wayau ba,
gashinn ay har ka miq'e,
Murmushi saif yayi yace "komi zakuce naji ba komi, Amman harda yarannan a wasan wannan satin ne?"
Akram yace "suwaye yara kuma malam?"
Heesham yace
"ay kasan su deejart yake nufi.
Saleem yace
" ay kuwa saif kasan dole ne,
inda an Saba duk week end dasu ake yi daga kan table tennis har xuwa foot ball data basket Ball d'in wato wacce zamuyi goben knn.
Mahmoud ya amshe da fad'in
"Saif ko kana tsoron deejart ta sake winner naka?"
Yamutsa fuska yayi yace " Ku kuke ganin hakan,
But Allah kaimu goben lpia",
a haka dai suka cigaba da da firarsu.
Washe gari da misalin 5 na yamma a filin wasan kowa na sanya da kayan wasan basketball,
maza Nada green din Riga da wando, Mata Nada red kuma dukkansu matan wandunan iya gwiwa rigunan kuma dai dai q'ugu,
Kowace tayi parking gashin ta sun d'auresa da wani d'an farin scarp,
Mazan kuma wandunan iya cinya sai rigunan marasa hannuwa.
Ba'a jimaba suka Fara wasan deejart ce ta Fara yi da basma tuni ta bugamata 2 winner a lokaci d'aya sannan miemie ta shigo filin wasan, sun jima suna gagatawa a q'arshe deejart tabata winner deejart nada mark 8 miemie Nada 3 , mazan kuwa sai tafi suke mata raf raf suna fad'in "aikinki na kyau deejart",
Tuni miemie tayi waje tana cixon lebe jawaher ta shigo suka Fara.
saif kuwa takaici ne ke naniq'arsa,
ganin yanda take tsalle 2 a wajen jefa q'wallon a kwandon, mamanta kansu suma girgixawa suke a cikin rigarta. gani yake duk ita mazan wajen ke kallo.
Ji-yake da da yanada ikon Hana wasan nan daya yi,
sai dai Ina .!
sun Saba da shi duk q'arshen sati.
Mtsss yaja tsoki ya sake fad'in wannan manyan breast d'in Nata wai bata ma jin nuyinsu ne?"
Bai Ankara yaji Ana yeeeeehhhhh, lokacin jawaher Nada ci 6 deejart Nada 10,
Hutu suka tafi in few minutes,
Bayan andawo su akram suka tura saif a filin wasan ma'ana dashi da deejart za'a gagata knn yanzun,
lokacin q'wallan na wajen deejart tana tsaye ta Kama q'ugunta da hannayen ta ta dafe, ta danne ball d'in under poot d'inta,
(q'arqashin q'afarta)
suna jefawa juna wani kallo Wanda suka d'ai sukan ma'anarsa.
d'aga ball d'in tayi sama ta tullo masa suka Fara q'oqarin qwaceta a hannun juna by mistake ya taka qwallan ta darjesa ya fadi q'asa,
itama garin tarbo ball din takalmin qafar ya tad'eta tabisa q'asan suka zube tare,
ta fad'a a qirjinsa tayi male male.
wato q'irjinta ya sauka a nasa sun had'e waje d'aya.
Tuni wajen ya d'auki ihu da sowa.

Xayynebπ’¤π’¤
🏓🏓🏓💊💊💊
🏓🏓🏓🏓🏓🏓
*doctor deejart*

💉
By
Xayyneb💤💤

*Fasaha online writer's f o w*

*Dedicated to my daughter deejart*

🅿1⃣2⃣🔵
🏓🏓🏓🏓🏓🏓
Wani irien taushi yaji tamfar bread,
a qirjin nasa, gashi kuma breast d'in nata duk sun cike masa ciki, da yake ta rabo daga saman qirjinsa ta yo setin cikinsa,
jin hankalin sa naneman tashi lokaci d'aya,
dagewa yayi ya tureta a cikinsa ya miqe tsaye yana faman yarfa mata harara, ita miqewa tayi tana kakkabe jikinta tana rama hararar a kai kai ce,
Tuni su akram da su jawaher suka da'u sabuwar shewa suna fad'in "yeeeeeeee by mistake ne by mistake ne,
a cigaba da wasa gayu".
Lokacin saif ya dauki qwallan nan suka Fara wasa da deejart, yayi nan ta yi nan wato sunabin juna a qoqarinsu na kwace qwallan a hannun junansu,
take ya dinga sarrafa qwallan cikin qwarewa a hannunsa yana sakawa a kondon, dayake ya zartata tsawo miq'a kawai yake yana tilla qwallan a raga sakamakon ita da saita had'a da tsalle sannan take jefawa.
Wasa ya da'u zafi lokacin saif nada ci
8 deejart nada 1,
Su kuma sauran 'yan wasan suna daga saman bene suna fad'in
" saif! saif! saif !,
tuni wani qululun haushin 0-n da saif ke bata ya kamata.
Shikuwa yana Lura da yanayin sarewarta murmushi yayi a ransa yace "yarinyar nan waya fad'a miki barno gabas take.
Kuma sai yaji ta basa tausayi cikin gangan ya dinga sakar mata qwallan dan tasamu ta qara yawan marking itama.
amman kuma ta kasa,
dan xuwa lokacin ba q'aramar gajiya tayi ba, tsallen ma daqyar take yinsa, tana ta qoqarin ta sanya qwallan a raga ta kasa,
sai jitayi an sungumi qugunta da hannu an d'agata sama ta saka bal din a basket d'in sannan ta ji andireta,
Wani sabon sowar su heesham ke tashi suna fad'in
" yahhhhhhhh akwai temako ,! akwai temako,! 'Yan uwa.
Ita kuwa tun daga jin qamshin turarensa ta tabbatar da saif ne ya d'agata,
Jin ya direta yasa tai saurin juyawa dan ta qara tabbatarwa idanunta.
Idanunta suka fad'a a nasa , wani mayaudarin murmushi ya kasheta dashi tare da kashe Mata ido d'aya , tuni wata irin fad'uwar gaba da kasala ta sameta,
a lokaci d'aya
taji saukar hakan a jikinta , tare da jin wani abu na fizgarta a lokacin gameda saif d'in.
Samun kanta tayi da sakar masa murmushi itama,.
ta miq'a masa hannun ta, shima ya miq'a mata nasa🤝.
suka riqe hannayen juna gam gam dukkansu wani feelings sukejin na surarowa a jikinsu a lokacin, jin taushin fatar hannayen junansu dan ita hannun ta har gumi yake fitarwa na laushi.
a hankali ta furta "thanks"
janye fiskarsa yayi a kanta tare da hannunsa sannan ya daure fuska tare da tabe lips yace
"Riqe godiyar ki dan wataqil tai miki rana nan gaba,
Yana kaiwa nan su akram suka sauko dukkansu a benan suka d'agashi sama suma matan suka d'agata sama suna murna , a haka sukaci gaba da wasan basketball d'insu har lokacin tashi yayi
Kai tsaye shashen kakus 'yan matan sukayi saman sofa suka hangesa yana jan cazbi, da gudu suka qarasa suka zagayesa suna fad'in " munyi missing naka kakus,
"Bawani kunyi missing nawa 'ya'yan nan kuna can kuna wasanku kun mance ni"
Akram ya shigo shida heesham da saleem d mahmoud suma zama sukayi a wajen,
Basma tace ''yawwa su yaya Mahmoud Ku zauna muna son magana dakai,
"To basma gani fatan dai ba laifi naiba?"
Kusan dai hakan cewar miemie,
To shiknn Ina sauraranku 'yan q'annena".
"Basma taci gaba da fad'in " ya kamata a yaye yaya saif a cikinmu"Mahmoud yace
"Kamar ya knn basma?"
Shiru tayi takasa cigaba da mgnr, jawaher tace" inba zaki iya magana ba sister ni bari nai masa,
Tace "yaya Mahmoud inda dai yaya saif dukkanmu ya fimu q'warewa a wasan nan , kaga kawai ya koma d'an kallo in munayi koko ya Ku kace su yaya saleem?"
Saleem yace "inda kunfi son hakan ay shiknn".
Murna suka dinga yi sannan suka fice a shashen,
kakus ya dubi deejart yace
" likita kedai baruwanki da hayaniyar sauran yaran can , tunda suka shigo sai yanzu kunnuwana sukayi tsit da suka fita sbd surutun su cwai cwai cwai."
Akram dariya sukayi suna fad'in
"Kakus ay suma d'in hakan suke"
Kakus yace "kayya dai , kudai kawai fatanmu Allah kawo lokaci Ku kwashe matanku Ku tafi can da hayagagarku.
nan dai deejart ta sulale a wajen ta barsu dan takasa jure kallon da Mahmoud ke jifarta dashi Wanda irinsa Abbas ke Mata.
tuni ta sanyawa wannan kallon nasa alamar tambaya❔.....
Kai tsaye dakinta ta shiga tayi wanka ta sanya doguwar Riga ta atamfa ta fito ta nufi shashen su jawaher Dan tambayar su ko sunsan ma'anar kallon Mahmoud gareta kuwa❓
indai suka bata amsa kamar yanda take tunani tofa lallai zata.....
🏓🏓🏓💊💊💊
🏓🏓🏓🏓🏓🏓
*doctor deejart*

💉
By
Xayyneb💤💤

*Fasaha online writer's f o w*

*Dedicated to my daughter deejart*

🅿1⃣3⃣🔵
🏓🏓🏓🏓🏓🏓
Tayi sa'a kuwa basuyi barci ba kowace tana riqe da waya suna chat suna hadawa da shewa,.
Sukuwa tayi ta fad'a a tsakiyar gadon da suke a Kai , tace "sannunku uwayen surutu,
suna ganinta suka aje wayoyin jawaher tace " Kai Amman wasan yau yayi masifar dad'i sis deejart, Amman kwatsam wannan mugun yaya saif d'in yawani zo ya bata mana ta hanyar kayan dayai ta bamu wlh,
Murmushi deejart tayi tace ni ba wannan ya kawo niba sisters, .
Basma tace ina xuwa kubari naje na zubo mana girki dan natabbatar dukkanmu yunwa mukeji "
Miemie tace "whl kuwa sis basma 💯 ma kuwa 'yar albarka,
yi sauri muna nan muna jiranki,
da sauri ta sauka a gadon ta shiga kicen,
Bata d'auki mintoci ba sai gashi ta dawo dauke da q'aton faranty na abinci, shinkfa ce Friedrich wacce tasha had'in coslow a ciki , saukowa sukayi dukansu sukaci abincin suka qoshi sannan suka koma kan gadon,
Jawaher ta yi zaqal tace ladies kunga zance na ya tabbata amman da har kuna musamun ay"
Miemie tace nami knn?"
Son da yaya Mahmoud ke gwadawa deejart man a kaikaice, cewar jawaher.
tuni kingin suka da'u shewa sukace ''gskia mun yarda da hasashenki jawaher,
Yaya Mahmoud ya matowa son ki deejart kawai kiyarda , koba komi kinyi dacen mutum na gari mai darajja mace da lallabata sakamakon na hannun damarsa wannan mugun yaya saif din da bai dauko halin saba".
Deejart jitayi ranta ya sosu jin yanda suke kushe yaya saif suna yabon Mahmoud ita kanta tarasa gane kanta tun tashinsu a wasa ba'a minti 2 yaya saif bai fad'o Mata a rayuwar tabah" mikenan hakan ke shirin faruwa da ni?
Abinda take tambayar kanta knn tun d'azun.
Basma ta girgiza cinyar ta tace " deejart bakice komi ba fa? Kuma kun dace wlh da zaran ya furta miki Kalmar so ki amince kar kakus ya miqa miki wani daban kuma,,,,
" plzzzz sisters Ya isa hakan dan Allah✋".
dukkansu sakato sukayi ganin yanda lokaci d'aya yanayinta ya juye.
Jawaher tace " abinda yasa mukace hkn sis sbd d'azun a filin wasa lokacin da yaya saif ya d'auke ki d'in nan munajin sanda yaya Mahmoud ke cewa
" haba mana saif mixaisa ka tabamin iyali bacin kasan deejart itace burin rayuwata?
a matsayin matar aurena ta har abada"!
Sai kuma yayi shiru dn ankara da yayi kamar a zatonsa a zuciya yake mgnr,
in ta q'aice miki wlh hankalin sa bai kwanta ba saifa sanda yaya saif ya direki a q'asa.
Jawaher na kaiwa nan tace ''koba hakan ya faru ba ladies? "
"Hakane kuwa jawaher cewar su dukansu.
tsoki deejart taja tace " ni ba soyayya ne a gabana ba".
Har had'a baki suke wajen cewa" ke ko deejart? "
To miye a gabanki knn?"
amsa ta basu Kai tsaye da cewa
"aiki na".
" lallaikam cewar miemie🤔".
Basma tace "karonki da kakus wlh kuwa deejart duk randa dubunku ta cika.
Yamutsa fuska tayi tace" mubar firar nan kawai",
Miq'ewa tayi tace inada tiyata gobe lahadi a hospital namu so zanje na kwanta da wuri dan Karna makara".
Jawaher da miemie suka miqe tsaye sukace Bari mu wuce tare to sis. nan dai su kaiwa basma gud night suka fice kowace ta shiga side d'insu.
Deejart ta jima kan ta kwanta barci tana tunanin wai yanxu ita yaya Mahmoud ke burin aura?"
Sake yamutsa fuskarta tayi tace "tab da sakal wlh!".
A haka ta jima tana juyi kamin barci ya kwashe ta cike da mafarkin yaya saif, Wanda take thinking ya akayi ya biyota har a barci.
da misalin 10 na safe ta shirya tsab cikin uniforms d'inta ranta cike da tsoron wani mugun mafarki da tayi a kan yaya saif,
koda taje asibitin da q'yar ta samu ta shiga tiyatar nan ma.

Saif ne zaune a d'akinsa gaban laptop d'insa yana tura wasu saq'onni ta @ gmail Mahmoud ya shigo , ya zauna a gefensa ya d'an kwanta a gadon ya jawo wayar saif yana duba gallery sai jin qarar message yayi a wayar ya shigo,
a saman sikrim d'in wayar ta nuno masa message d'in kamar haka,,
*message from x*
*Please zuma na, Inason in ganka yau dan Allah idanuna suna mafarkin sake son ganin kyakkyawar face dinka a Karo na 2 a rayuwata*
Iyakar sa knn rubutun.
Shi saif ma hankalin sa ya riga ya tafi ga muhimman abubuwan da yakeyi.
Baisan ma saqon ya shigo ba,.
ta6osa Mahmoud yayi yace" guy gafa wata sabuwar cika nan taimaka message.
Saida ya ida abinda yake sannan ya rufe laptop d'in ya amshi phone d'in ya duba,
Tsoki yaja baccin ya karanta message d'in ya aje wayar.
Mahmoud yace "wacece x kuma saif?
dan nidai cikin girlfriend naka ban San da ita ba.
tsoki saif ya sake yi yace "sunanta xeenat q'anwar mas'ud ce friend d'inmu duka 2 bamufi sati da had'uwa ba, lokacin naje wajen mas'ud din yasa ta kawo mana drinks,
ga yanda yake cewa a satinne ta dawo daga ingland karatu amman ta bi tawani nacemun wlh brother yanda kasan mayya haka take yarinyar nan xeenat.
gata bata da tarbiyya ko kad'an.
Tuntserewa mahmoud yayi da dariya yace " ko dai itace amaryar tamu saif kk 6oyewa?"
Had'e rai yayi yace
"Allah tsareni mahmoud da auran irinsu,
Plsss mubar mganr nan Ina son in fita yanzun ko zaka rakani ne?"
"Zuwa Ina knn saif?"
"ban sani ba mlm in zaka rakani muje kawai".
Kwanciya mahmoud yayi a gadon yace " bazan jeba jeka abinka, yau bazan fitaba dan na qudura a zuciya ta yau d'in nan zan fad'a wa doctor sonta da yaimun illa a zuciya"
ya qarshe maganar yana lumshe idanuwa tareda shafa saitin xuciyarsa da hannu.
dan haka Ina nan Ina sauraron dawowarta,
nasan bazata jima ba yau zata dawo inda yau lahadi kaga kuwa fita bata ganni ba,
Sbd ance da zafi zafi kan bugi icce brothe"r.
Tun da yafara mgnr saif gaba d'aya wuta ta d'auke masa, ya rasa cikin hankalin sa yake koko?
Wai miyasa ne ya ke damuwa da lamurran yarinyar ne?
Miyasa duk Wanda ya furta sonta a gaban sa yake jin ya tsanesa ne?"
Hakan me kenan to yake nufi?"
"Son ta yake nufi saif,"
Abinda xuciyarsa ta basa amsa knn,
Da sauri ya girgiza Kai ya na fad'in "no no no my heart na lie, bazan sota ba"
Ya Kama kansa ya danne da q'arfi yake furta hakan.
cikin sauri mahmoud ya ruq'osa yana cewa" saif mike damunka?
Wace ce ke baka so?"
A Ina take kuma ?"
In kana nufin ita xeenat d'in ay ba a so dole ko ?
plxxx ka nutsu brother kabar sa damuwa a ranka plzzz".
Saif baice masa komi ba ya d'auki keys d'in motar sa ya fita ko ganin gabansa baiyi sosai, ba abinda ke masa kuwwa a q'walwa irin abinda mahmoud yace yanzun game da deejart, wato zai fad'a Mata son ta garesa ,
mahmoud da kallo ya bisa kamar ya bisa yakeji dan ganin yanayin da yake ciki Amman sai ya fasa ya tabe baki tare da fad'in
" Allah kyauta "ya koma yai kwanciyar sa.
saif kuwa na fita mota ya fad'a ya bata wuta da qarfi ya figeta har wata q'ara kakeji ta motar, "q'uuuuuuuu,,,,,!!!

kakus na zaune a wajen shida su dady magana suke masa" ko jinsu bayyayi ma.
Kakus kuwa ya dage

Please Login or Register in order to submit comment