Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aure kuma aure ba fashi yana gama fadar haka yayi tafiyarsa ya barta nan dur kushe a kasa tana kuka dataga kukan baxai amfaneta da komi ba ta koma kujeta ta kwanta tana tunanin hawa sama bata san me alhaji xaice ba kilama dukanta xaiyi don tasan halin alhaji Dora hannu tayi akai tace ooo ni HudahπŸ˜ͺ na shiga uku ba wanda aka taba yiwa auren dole a gidan sai ni gashi shima ba sona yake ba da karfi tace kai gaskiya ba xai yiwuba...



Lokacin da Hudah ta tafi wurin Dalhat alhaji yace hajiya yarinyar nan tunda akace xata auri Dalhat ta chanxa gabadaya kuma bashi xai hana auren ba ko xata mutu ne sai ta aureshi hajiya tace ni kaina abin na bani mamaki da anyi mata magana sai rashin kunya shi yasa na samata πŸ‘€ daxu sai da Aliyu ya xaneta amma duk da haka kaga abinda tayi kafin ta fita alhaji yace hajiya mun yanke shawarar nan da sati daya xa ayi komi a daura aure nan da kwana 7 kowa ya huta ko me kika gani hajiya ya tambayeta


Hajiya tace yawwa hakan yayi na huta wlh......



🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱
😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰

Story nd written by mufeeda Muazu

bismillahir rahamani raheem

Page 26-30



Hudah tagaji da xaman falo gashi tana jin bacci sosai given up kawai tayi ta fara tafiya a hankali harta kai sama cikin sanda ta murda kofar dakinta kenan alhaji ya daka mata tsawa yace ke..... me nace miki kafin ki fara shiru tayi ba tace komi ba wani tsawan ya karayi har sai da yan hanjin cikinta suka kada jikinta na rawa muryarta na rawa tace ka...ce in... Sameka a nan yace saboda ban isa bako


Kasa magana tayi saboda kukan daya xo mata hajiya tace to uwar kuka me akayi miki na kuka xakiwa mutane shiru ko kuwa hannu tasa ta toshe bakinta alhaji yayi gyaran murya yace ki bude kunnenki da kyau xaa daura aurenki da Dalhat nan da sati daya ko kinaso ko bakyaso tashi ki bani


mikewa tsaye tayi ta fara magana tana cewa dan Allah alhaji kayi hkr wlh bana sonsa ta rarrafa gurin hajiya tace hajiya don Allah kisa baki mana wlh bana sonsa kada kuyi mun auren dole alhaji ya taso da dori nan sa tashi tayi aguje ta shige daki ta rufe komawa yayi ya xauna yana kwafa



ASALINSU

Alhaji Abubakar. Sadeeq Aliyu da Alhaji Aliyu Dalhat haifaffun garin bauchi ne tare suka taso tun suna yara barci kawai ke rabasu makarantar primary daya sukayi secondry ma haka da sukaxo Jami a ne kowa basu sami admission a university daya ba yayinda shi alhaji Aliyu ya samu law a A.b.u xaria shi kuma alhaji Sadeeq ya samu Atbu bauchi yana karanta medicine ya kasan ce sunyi nesa da juna sai da a waya ko in dayan cikin ya samu time ya kaiwa dan uwansa xiyara ana nan wata rana Sadeeq ya kaiwa Aliyu xiyara suna xaune suna hira saiga wasu yan mata su biyu sun tafiya cikin skull Sadeeq ya kalli Aliyu yace abokina kaga abinda nagani kuwa Aliyu yace na gani yanxu yaya xa ayi Sadeeq yace muje mu same su kawai don gsky baxan iya hakuri ba tashi sukayi a lokacin har sunyi nisa sauri sukayi suka cin musu sallama suka farayi musu dayar tace ta amsa Sadeeq ne yace don in ba damuwa muna son magana daku suka ce don Allah kuyi hakuri sauri mukeyi Aliyu yace don Allah kuyi hakuri ku saurare mu koda na minti biyu ne xuwa uku da kyar suka tsaya suka sauraresu wuri suka samu suka xaxxauna


Aliyu ne ya fara magana yace muna xaune nida abokina muka ganku kunxo wu cewa so sai mukaga duk irin choise dimune da farko suna na Aliyu abokina kuma Sadeeq mu yan asalin jihar bauchi ne krat2 ne ya kawoni xaria ina fuculty of law ina final yr shi kuma abokina yana Atbu ya karanta medicine gsky mun gani muna so kuma da aure ni ina son choculate shi kuma yana son baturiya ne dukkansu saida sukayi dariya....


Sadeeq ya kara murmusawa yace duk abinda abokina ya Fada gsky ne yanxu Ku muke saurare muji ta bakinku farar ce ta numfasa tace duk munji bukatunku but muna so Ku bamu lokaci don muyi naxari Sadeeq yace hakan ma nada kyau but muna da bukatar Sanin sunayenku


Farar ce ta kara magana tace ni sunana Jidda othman ni yar garin kaduna ne kawata kuma sunanta Asmau Omar faruq yar asalin bauchi ammah suna kaduna da xama tare da iyayenta muna karanta micro biology 300l wow what a nice course exchanging phone number....


A haka suka rabu kowa na farin ciki


Jidda ta kalli Asmau tace kai gayun nan sun hadau Asmau tace ba kadan ba nace su bamu time ne kawai saboda muja aji Jidda tace ai nagane kawas...


A bangaren su Sadeeq kuwa murna suke sun sami matan aure gasu kawayen juna kamar yadda suke abokan juna Aliyu yace pls Kana xuwa gida ka fadawa su alhaji mun Sami matan aure...



🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱
😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰

Story nd written by mufeeda Muazu

bismillahir rahamani raheem

Page 31 - 35




Sadeeq yace insha Allah Aliyu ya rakashi tasha ya hau mota sai Bauchi



Sadeeq na isa gida wayarsa ya ciro number Jidda yayi dialing kira daya ana biyu ta dauka sallama yace haba Jidda kya kira kiji yana koma gida ai tace lah wai har koma yace Yanxu na sauka shine nace bari in kiraki inji muryarki nd gsky da gske muke ba wasa Jidda tace to gdy nake



Haka soyayya ta kullu tsakanin su har iyaye suka shiga ciki a shekarar da suka gama skull suka sami aiki iyayensu suna mamaki irin abokan takarsu da sun so gina gida daya kowa da part dinsa iyayensu suka ce aa suyi dai kusa da juna saboda halin rayuwa da kuma shaani na mata haka kuwa akayi gidansu kusa da juna rana daya akayi bikinsu



bayan shekara daya Allah ya axurta Aliyu da samun da namiji wanda akasa suna Dalhat wato sunan mahaifinsa sunyi murna sosai


Aliyu Allah bai samu haihuwa ba har lokacin don haka kullum Dalhat yana wurin Aunty Jidda sai da Dalhat ya shekara uku Sannan jidda ta samu ciki murna wurin Sadeeq ko baa cewa komi itama asmau tana da wani cikin tare suka kara haihuwa Jidda ta haifi da namiji aka sa masa sunanan babanta wato othman suna kiransa da shahid ita kuma asmau mace ta haifa mufeeda haka rayuwa ta cigaba da tafiya


Jidda ta Haifa yara shida shahid khairat Aliyu jadeed Hudah sai auta asmau

Ita kuma asmau ta haifi yara bakwai Dalhat mufeeda Haidar hanifa Ryhan julaibib sai auta Jidda



cigaban labari


Koda hudah ta shiga daki babu abinda take sai kuka har dai ta gaji tayi shiru dan Kanta


Safe 8.30pm

Hudah ce ta fito daga dakinta cikin sanda harta sauka kasa bata ga kowa a falon ba dan haka cikin sauri ta nufi kofar fita harta bude taji ance ke ina xaki ba sai ta waigo ba yaya Aliyu ne fita tayi a guje ya bita harta kusa gate sai ga aunty Khairat da yaya jadeed yaya Aliyu yace riketa jadeed guduwa xatayi sai jin alhaji mukayi yace kai jadeed saketa ta tafi gidan uban da xataje yaya jadeed ya sakeni aiko yana sakinta ta falle ta fita daga gidan tasa kafa kenan taji an rikota ta baya ihu take kaman ranta xai fita tana cewa dan Allah yaya shahid ka sakeni babu inda xani wurin Jidda xani sai kuka take janta yakeyi har cikin gida..

Kowa na falo yaya shahid ya tangwarar dani a kasa a tsakiyar falo yaya dady cikin fushi ya daga bulala ya fara xuba mun ina kuka ina ihu duk inda nayi su yaya shahid su taroni....


Ana cikin haka Jidda tashigo aiko da gudu ta koma gida ta fadawa su Abbu da ummi a tare suka fito suka shigo da kyar Abbu ya kwace ni da gudu na koma bayan ummi na buya..


Abbu ya farawa alhaji Fada haba alhaji wanna wani irin duka ne haka kaman kana dukan barawo komai tayi ai kamata yayi ka bita a hankali yarinya ce karama alhaji yace kaman Hudah ne xan rika fada tana fada abin ma girma yayi yau an wayi gari xata gudu hudah na bayan ummi tace wlh ba guduwa xanyi ba wurin Jidda xani....

Alhaji yace kagani ko abbu yace yi hkr alhaji kowa ya xauna hudah dai tana gefen ummi sai shassheka takeyi....


Abbu ya fara magana kamar yadda kowa ya Sani ansa ranar auren Dalhat da hudah wata uku yanxu an komar dashi rana ita yau wato ranar asabar mai xuwa Dalhat dake xaune kai a duke dago yace alhaji ina neman alfarma dan Allah a bari in dan gama shirye shirye alhaji yace baka da wani damuwa duk wani shiri mun Riga mun gama shi.....


Hudah dake gefe sai kuka take ta tashi taje kusa da Khairat tace Aunty Khairat don Allah kisa baki mana a bari sai na gama krt2 Aunty Khairat tace kiyi hkr hudah kiyi biyayya


Ummi ce ta taso ta kama hannunta tace yi shiru ki share hawayenki tashi kije daki ki kwanta ki huta kinji Jidda rakata daki saida taga sun wuce ta juyo ta kalli hajiya tace don Allah hajiya ku kyale yarinyar nan ta hut a haka nan....


🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱
😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰

Story nd written by mufeeda Muazu

bismillahir rahamani raheem

Page 36 - 40



Hajiya tace yarinyar nan bata ji su alhaji sunyi mun dai dai da suka dawo da daurin auren kusa kowa ya huta taje can tayi masa taurin kan ya chasata wlh ummi tace ina nan ba wanda xai taba mun ya hajiya tace masu ya kuje can Ku karata


su hudah na shiga daki hudah ta kalli Jidda a lokacin hawayen ma sun kafe sai kukan xuci tace Jidda kinji abin da su alhaji suka ce ko wai nan da one week ni yanxu yaya xanyi da wannan tsatsauran hukuncin sai kace su auren dole akayi musu yanxu Jidda meye shawara



Jidda ta numfasa tace shawara daya ne hudah hakuri kawai itace mafita tunda dai sun dage abin sai dai addua kawai amma da kika fito ina xaki har akace guduwa xakiyi akai miki irin dukan nan kaman an kama barawo



Hudah tace wlh jidda sharri ne kawai irin na ya Aliyu Jidda tace maiyasa kike sanda a lokacin da xaki fita hudah tace ina tsoron kada inga su yaya Aliyu a falo shiyasa ammah wlh wurinki xanxo Jidda tace to Allah ya kyauta hudah tace ameen



Dakin yayi shiru kowa da abinda yake sakawa a ransa wayar hudah ne ya katse musu tunani da kuka har ya katse bata dauka ba wani kiran ne ya kuma shigowa a kasalance ta daga wayar taga ashe sir Haidar ne karawa tayi a kunne cikin sanyin muraya tace hello sir Haidar yace haba hudah tun jiya nake kiranki baki daga ba yau ma saida ya kusa katsewa duk Nashiga damuwa Allah dai yasa lpy hudah tace lpy klu bana kusa ne sir Haidar yace amma ai kinga missed call ko hudah uhm bata ce komi ba sir Haidar yace nagane duk ajan aji neko to ykk hudah tace lpy klu har suka gama wayar hudah dai ga um sai uhm aje wayar tayi tare dayin tsaki tace hudah wannan mutumin yana son takurawa rayuwata Jidda tace tace tace wani mutumi kenan hudah tace wane kika San ban sir Haidar


Jidda tace mai yace miki ne hudah tace tatsuniyar gixo ai bata wuce ta koki Jidda tace ki dai bi komi a hankali ki kuma cigaba da addua



Hudah ta tashi tace bari in dan watsa ruwa ta shiga toilet Jidda kuwa kwanciya tayi tace bari tamike bada dade da kwanciya ba barci ya dauketa



A falo kuwa hajiya da ummi ne suke tsara yadda bikin xai kasance Dalhat ne ya shigo da leda a hannunsa katine ya tsuguna ya gaida iyayensa yace hajiya su Jidda na cikine hajiya tace eh ummi ce tace mai xakayi musu dan nasan halinka yace ummi ba wani abu xanyi musu ba kati xan basu in kuma tambayesu koda akwai abinda sake da bukata hajiya tace ke ummi ina ruwanki da abinda xaiyi musu kaji tashi kaje suna daki tashi yayi ya haye sama...



Jidda sai barcinta takeyi hankali kwance Dalhat ya turo kofar dakin dai dai fitowar hudah daga wanka kenan gashi daga ita sai towel iyakan shi cinya ko gwiwa bai kai ba kara tayi ko motsi ta kasayi shi kuma ya kafeta da ido ko kyaftawa bayayi


Karar tane ya farkar da Jidda daga barci bata kula da yaya Dalhat ba tace amma ke hudah baki da mutunchi mutum na barci ki tashe shi da kara haka xaki rika yiwa yaya ko hudah tai mata signal ido aiko tana kallon kofa hada ido sukayi da shi aiko ya sha mur yace wato Ku baku da kunya ko to tashi ki fita ki jira mu a falo ban ce ki sauka kasa ba sum sum ta mike ta fita.....


Tana fita hudah tai sauri ta janyo hijabinta ta saka shiko xama yayi a gefen gado yana murmushin mugunta hudah ko sai hararansa take tace malam ka tashi mun a gado don batare da kai akas siya ba murmushi yayi yace calm down saura kwana nawa ne a siya wani tare dani tsaki tayi aiko tasowa yayi yaxo har inda take tana matsawa yana matsawa har takai bango har suna shakar numfashin juna...


Take kafanta yayi ya murde mata baki...





🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰

Story nd written by mufeeda Muazu

bismillahir rahamani raheem

Page 41 - 45




Daga yau sai yau kada ki kuskura ki sake yimun tsaki if not yayi kwafa ita ko huda ba abinda take sai kuka gashi ya fasa mata baki tsawa ya daka mata sai da yan hanjin cikinta suka motsa


Wa kikewa kuka anan xaki tashi ko sai na lallasaki da sauri ta tashi tana goge hawaye gefen gado ya nuna mata ba musu ta xauna cikin shan mur ya fara magana



Dame da me kuke bukata na hidimar biki a tsiwace ta kalle shi da jajayen idonta tace bamu da bukatar komi daga gareka abu guda nikeda bukata a wurinka dan Allah ka taimaka ana daura auran ka sakeni ka bani takardata



Idan ba haka ba kai da xaman lpy har abada don wlh bana sonka na tsaneka Allah ko ganinka bana sonyi murmushin mugunta yayi sannan yace ashe ko xuciyarki xata buga don aurena dake ba saki duk da nidin ma ba sonki nake ba hukuri kawai xanyi biyayya



Saboda haka muxuba mugani ni dake aga wanda xai ci riba ya watso mata katin daya shigo dashi yayi ficewarsa



Yana fita ta kifa kanta a gado tana rera kuka a haka Jidda ta shigo ta sameta taga kati kuma a watse a kan gado dauka tayi ta karanta ya tabbata kenan saura one week



matsowa tayi kusa da hudah ta dafata hkr take ta bata akan tayi hakuri insha Allah wata rana sai labari dagowa tayi tace Jidda hakuri ya xama dole an dai riga an cuci rayuwata an hadani da wanda baya sona kuma nima bana sonsa gara shi namiji ne xai auri wanda yakeso ni kuwa fah wlh Allah sai ya saka mun Jidda tai sauri ta toshe mata baki tace kiyi hakuri kada kice haka iyayenmu baxa su taba xaba mana abinda bashi da kyau ba nasan abinda ciwo but don Allah ina so ki daure ki cije ki maida komi ba komi ba kin san dai ba fasawa xasuyi ba tunda sun kafe kisawa xuciyarki salama gara shi namiji



Hudah tace dan Allah kalli bakina fasa mun yayi fah saboda kawai yayi magana nayi tsaki tun yanxu ya fara xalunta mun inaga kuma na shiga gidan na xama nama kenan



Kema huta kin san yaya Dalhat baya son tsaki dan Allah hudah ki rika kiyaye abinda mutum bayaso ko don a xauna lpy but abinda yayi bai kyauta ba kiyi hakuri



Yanxu wani event kuka shirya mana keda angon naki ta tambaya cike da xolaya tsaki hudah tayi tace wlh Jidda ki kiyayeni tun da sauran girmanki a idona Jidda tai dariya tace tuba nake aunty amarya


Hudah dai bata kara cewa komai ba don ta kula Jidda neman fada takeyi..


A falon kasa kuwa hajiya da ummi su gama tattaunawa yadda bikin xai kasance xasuyi mothers day da kuma walima



Anan falon ya tarar dasu ya gaishe su xai wuce hajiya tace fatan dai komi lpy ko yace eh yana sosa keya ummi ko hararansa tayi da sauri ya bar falon ummi ma tashi tayi sukayi sallama da hajiya ta


A daki kuwa Jidda ce ta tattaro katinan da aka watsa a kan gado tace Hudah kinga katin kuwa wlh sun hadu yaushe xamu fara rabon katin harararta tayi tace rabon kati Allah ya kyauta ba wanda xan ba kati mayar masa dashi xanyi jidda ta mike tare da cewa kinfi karfina hudah tace meye haka ina xaki kuma jidda tace gida mana ta Fada tare da raba katin biyu ta dauki rabi ta aje rabi


Hudah tace jirani insa kaya muje ba musu ta koma ta xauna hudah ko drawer ta bude ta dauko wani material baki da ja tasa sannan ta saka bakin abaya mai ratsin ja ta dan murxa powder sai a lokacin ta tuna da wayarta akan dressing mirror wanda ta aje tun jiya da daddare....




Dauka tayi tare da dubawa 8missed calls da 2massages tana budewa taga duk number daya ne sir Haidar ne....



🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱

For comment 07065642314

😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰

Story nd written by mufeeda Muazu

bismillahir rahamani raheem

Page 46 - 50




xama tayi a gefen jidda tace kinga Jidda tayani duba massages din nan ta amsa wayar tare da dubawa na farkon dai hakuri yake bada ko yayi wani laifi ne aka ki daga wayarsa dayan kuma na magiyace akan dan Allah tayi hakuri ta amshi soyayyar sa suna gama karanta a tare suka dago ido cikin ido hudah ce tayi karfin halin cewa Jidda na shiga uku yanxu ya xanyi



Jidda ta kalleta alamun tana son karin bayani hudah tace Allah jidda ina son sir Haidar tunda randa na fara sa shi a idona daurewa kawai nakeyi Saboda in tsira da mutunci na kada girma na ya xube gashi yanxu ya fito da bakinsa yace yana sona amma sai dai kash yaxo a kurarrar lokaci ya kike gani xaayi wayyo Allah Jidda na shiga uku




Jidda taja dogon numfashi ta dafa kafadunta tace kullum maganata dai daya ce nasan kida hakuri amma don Allah ki kira hakuri Kan wanda kikeyi ki cigaba da addua nima xan tayaki insha Allah komai xai wuce



Hudah wanda tuni hawaye ya gama wanke mata fuska ta rungumeta tace nagode sosai Allah ya bar kauna ya dada hada kanmu Jidda tace ameen ta goge mata hawayen tace yawwa koke fah da kina so ki bata kwalliyarki duk da nasan wannan gayun na yaya Dalhat ne ta fada cike da xolaya harara huda tabita dashi tare da kaimata duka da gudu Jidda ta fita tana dariya



Hudah ma tashi tayi ta dauki wayoyinta da sauran katin da Jidda ta bari ta saka cikin jakarta ta fito anan falon sama ta tarar da Jidda hararar ta tayi tace malama ai saiki tashi mu tafi ko tashi tayi tare dacewa wai ina xamu ne irin wannan wanka haka koda yake bai na tambaya ba koya kika ce hudah dai bata tanka ba dakin hajiya suka shiga bata dakin sai Husna jidda tace Husna ina hajiya take tace hajiya sun fita ita da alhaji hudah tace idan ta dawo kice muna gidan Abbu kada a nemi Husna tace a dawo lpy suka ce ameen



Suna fita farfajiyar gidan Hudah tace Jidda an gyara motarki kuwa Jidda tace eh waike ina xamuje ne hudah tace gidan aunty mufeeda da aunty Khairat nagaji ne da xaman wuri daya Jidda tace to shikenan



Suna shiga gidan Jidda ta wuce dakinta hudah kuma dakin ummi ta shiga suka gaisa Sannan ta fito ta shiga dakin Jidda ta Tarar ta shiga wanka ganin haka yasa tai sauri ta fiddo da I.v din daga jakarta da sauri ta fito ta nufi bq dakinsa ta kwankwasa har sau biyu taji shiru



Shiko yana can ya Fada duniyar tunani yana tuna yadda ya ganta ta fito wanka daga ita sai towel wanda ko cinyarta bai gama rufewaba gasu santala santala Ashe haka yarinyar take da shape gsky komi yaji shi yana mata kallon yarinya tai masa kankanta Ashe ta wuce tunaninsa uwa uba ga tsiwarta yana burgeshi tana magana cikin shagwaba kamar wata karamar yarinya yayi xurfi cikin tunani yaji bugun kofansa firgigit yayi ya tashi ya na mita waye xaixo ya dame shi mikewa yayi tare da xuwa ya bude aiko yana budewa idanunsa sukayi toxali da Hudah nan da nan ya daure fuska....


Ya fara magana ke lpy meya kawoki wurina ai kya bari a kawoki kafin ki kawo kanki har kin kosa nan da kwana bakwai dai wani irin bakin ciki yaxo mata wuya wani mugun kallo ta watsa masa tace Allah ya kyauta da aurenka da rashinsa duk daya ne a wurina don ni ban dauke ka a matsayin miji ba ka bari kashinka yai kwari saika kira kanka namiji bude baki yayi xai magana kenan tako watsa masa kitin tace ga tsiyarka nan




xaro belt yayi ganin haka yasa ta ruga a guje biyota yayi har falo taci saa kuwa ummi na falo da gudu ta buya a bayanta tana cewa ummi kin ganshi ko shiko gogan tsayawa yayi da belt a hannu yana muxurai


Yace dan Allah ummi ki matsa in xane yarinyar nan ummi tace lallai ka girma yanxu ka dubi tsabar idona kace in barka ka dakar mun ya Dalhat cikin fushi yace rashin Kunya fa take munfa .....





🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱

For comment 07065642314

AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰

Story nd written by mufeeda Muazu

bismillahir rahamani raheem

Page 51 - 55



Hudah tana daga bayan ummi tace Allah ummi ni ban tsokane shi ba kawai na daga ganina ya hau cewa wai na kawo kaina tun kafin a kawoni shine nace ai nan ma gidan mu ne ai shine fa ya biyoni da belt ta karshe maganar kamar xatayi kuka


Ummi ta kalleshi tace su yaya Dalhat anyi girman kawai kai bakaji kunya ba ko yau ta saba xuwa gidan ummi ko sai fada take masa Hudah tana bayan ummi tana masa gwalo😜 a kufule yace ummi kina gani gwalo😜fah take mun Allah ummi ki Fada mata ta bar tsokanata in ba haka ba tasan sauran ummi tace yo kai mahaukaci ne da xata tsokaneka fita mun a falo babban kawai kallon hudah yayi murguda masa baki tayi 😏 kwafa yayi ya fita acikin ranshi yaji yarinyar ta kara burgeshi d way yadda take acting kamar yar drama



Yana fita ummi tace ai saiki sauko dodon naki ya tafi dariya hudah tayi tace Allah ya soni ummi da ba din keba yau da yaya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment