Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dalhat ya xaneni jiddah dake gefe tace haba dai wasa yake miki irinta masoya harararta hudah tayi tace ummi kin ganta ko ummi tace kunfi kusa ni kunga tafiyata tashi tayi xata shige daki hudah tai sauri tace ummi gidan aunty khairat da aunty mufeeda tace haba Ashe shiyasa a kayi kwalliya haka gashi kunyi anko eyee twince din ummi kunyi kyau naso ace rana daya xan aurar daku murmushi mukayi nace ummi Jidda ma ai ta fitar da miji kinsan waye Jidda tai sauri ta toshe mata baki


Ummi tace ke Jidda meye haka kikeyi jiddah tace Allah ummi karya take mun hudah tace ummi idan mun dawo xan Fada miki kuma ma kin sanshi ummi tace to hudah a dawo lpy ku gaishesu da kyau suka amsa da ameen ta shige daki tana murmushi



Hudah tace Jidda bari in dauko jakata a daki Jidda dake waje tace malama ga jakarki nan na dauko kina chan kina fama da surutu mutum yaita xuba kamar ruwan famfo hudah data fito tace eh din anyi bakinki ko nawa kuma sai na fada bari mu dawo Jidda ta mika mata jakarta gashi ni nagaji da riko hudah ta amshi jakarta mota suka shiga Jidda ce ta xauna wurin driver hudah kuma tana gefenta horn sukayi idi mai gadi ya bude musu gate



Suna fita titi Jidda ta dan kalli hudah tace ina xamu fara xuwa xatayi magana kenan wayar hudah ya fara ringing dago wayar tayi don ganin mai kirar ganin sunan yaya Dalhat tace hudah mun shiga uku yaya Dalhat ne ke kira hudah tace dauka mana kiji mai xaice parking tayi gefe guda ta daga wayar tace hello yaya magana ya fara cike da isa yace ina xaku duk inda kuke Ku dawo gida yanxu xatai magana ya katse wayar hudah tace lpy meyafaru Jidda tace wai yaya Dalhat yace duk inda muke mu dawo gida hudah tai tsaki mtsww dallah shareshi kawai in mun dawo ya kashemu Jidda tace gsky ina tsoron yaya Dalhat kinayi kamar baki san muguntar sa ba...



Hudah dai ta kafe sai sun tafi hakanan Jidda ta tada mota sai gidan aunty khairat sukayi horn mai gadi ya bude masu gate suna shiga parking sukayi direct cikin gidan suka shige a falo suka tarar da ita tasowa tayi tana faraa ta taresu tace maraba da amare hudah ta daure fuska tace haba aunty khairat ni bana so fah Jidda tace kinji aunty khairat kyaleta rigima takeji



Falo suka koma hudah ma ta kariso cikin falon ta xauna a one seater kawai sai ta fashe da kuka aunty khairat tace haba hudah har yanxu baki hakura ba kiyi hakuri don Allah kiyi hakuri kiyi biyayya wata rana sai lbr Jidda tace wlh hudah bata jin magana kullum haka nake fama da ita



Hudah ta dago da jajayen idonta tace ya kukeso inyi ne dan Allah kun San yadda nikeji ne xuciyata kamar ta fado kara ta saki tace wayyo Allah na shiga uku aunty khairat don Allah ki boyeni a nan....




masoya na ina muku fatan alkhairi Allah ya bar kauna


🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱

For comment 07065642314

😰
😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰

Story nd written by mufeeda Muazu

bismillahir rahamani raheem

Page 56 - 60



Aunty Khairat tace ba dani ba ke wai kanki daya kuwa to wlh ki fita idona in rufe ni banga laifin yaya Dalhat first class ne wanda ko wacce mace take burin samu gashi ke kin samu amma kina wulakantawa hudah kuwa ko magana ta kasa banda hawaye ba abinda take banxa sukayi dani suka cigaba da hirarsu har Jidda take tambayar ina yara taga bata gansu ba Aunty Khairat tace suna hadda wayar hudah ce ta fara kuka tana neman agaji



ciro wayar tayi daga jaka numbern sir Haidar ne ya fito baro baro murmushi tayi ta daga wayar sallama tayi su Jidda kuwa duk sun xuba mata ido a bangaren sir Haidar amsa sallamar yayi tare da cewa ranki ya dade har kin sani cikin tunanin ko nayi wani laifin ne na kira har so ba adadi




nayi text nan ma shiru don Allah hudah ki tausaya mun wlh ina sonki so na gaskiya hudah ko murmushin dole tayi har saida hawaye suka xubo mata tana tausayinsu hello.....hello hudah kinyi shiru kina jina kuwa dogon numfashi taja a Sanyaye tace ina jinka time dinda ka kira wayar bata kusa dani ne kayi hakuri sir Haidar yace ah bkm to don Allah yaushe xan ganki don Allah karki ce aa pls ki taimakeni hudah tace to shikenan kaxo gobe in Allah ya kaimu by 4pm



Sir Haidar yayi godiya sukayi sallama Aunty Khairat tace dawa kike waya hudah tace wani course mate din mu xaixo ya kawo mana wani handout ne Jidda xatai magana hudah ta harareta Ashe aunty Khairat ta gani tace meye kuma na hararata saboda kin girbo karya bakiso ta fadi gsky ko to wlh ki fita idona in rufe inba haka ba su yaya shahida xan sa suyi maganinki hudah tayi narai narai da ido kamar xatayi kuka tace aunty alama nayi mata ta taso mutafi saboda har gidan Aunty mufeeda xamu aunty Khairat tace ai shikenan ku gaisheta da kyau


Tashi sukayi Jidda tace to aunty sai anjima duk suka rataya jakarsu aunty khairata tayo musu rakiya har inda sukai parking motarsu suna sallama sai ga babansu muftahulkhair wato mijin aunty kharat xuwa karisowa yayi da murmushi dauke a fuskarsa yace ah Jidda keda amarya ne a gidan namu gsky naji kamshi ya cika gidan ya fada cike da xolaya murmushi sukayi dukansu sannan suka gaisa motar su sukayi mai gadi ya wangale musu gate suka fice aunty Khairat da mijinta suka koma ciki


Suna fita kwalta suka hau sosai hudah tace Jidda kin san waye ya kirani daxu kuwa Jidda tace sai kin fada hudah tace sir Haidar ne wai don Allah yana so yaxo gidan mu shine nace yaxo gobe karfe hudu na yamma Jidda ta dan kalleta sannan ta maida hankali a tukin da takeyi


Sannan tace hudah Kanki daya kuwa kin San dai weekend ne kowa na gida bakya tunanin wani abu hudah tace abinda yasa nace yaxo tausayi ya bani kuma gsky ina sonsa dole in fada masa gsky baxan yaudareshi ba Jidda tace wannan gsky ne dai dai tai parking mota a farfajiya gidan aunty mufeeda



cikin falon suka shiga tare da sallama har sau uku shiru baa amsa ba kamshi ne ya bugi hancinsu alamun ana girki a kitchen ai da gudu suka shiga kitchen din aunty mufeeda na hada salad kawai sai ganinsu tayi kamar anjeho su aunty mufeeda tace wai mai yasa ku bakwa girma ne kullum haka kuke kamar wasu kanan yara ta kalli hudah tace harda ke amaryar yaya nan da nan ko ran huda ya baci duk wani annurin dake fuskarta ya kau ta shagwabe fuska kamar xatayi kuka tace Allah aunty bana son ana kirana da wannan sunan



Aunty mufeeda tace wai ke hudah meyasa bakya jin magana ne to wlh kiyi dai a hankali kunfi kowa sanin halin iyayen mu tunda suka furta to kome xakiyi ba fasawa xasuyi ba Aunty mufeeda ta dafa ta tace kiyi hakuri hudah insha Allah ba xaki tabe ba hudah ta share kwallar daya xubo mata batace komi ba jidda ce tai magana tace aunty kullum sai na Fada ma but taki ta kwantar da hankalinta aunty mufeeda tace to iyayen magana bari inxo gidan miji xaki fito dashi don banga ampanin xaman ba Jidda tace aunty skull dinfa aunty mufeeda ta tsaki ta juya ta cigaba ta aikinta hudah tace aunty inasu hibba aunty mufeeda tace sun fita da dadynsu juyowar da xasu kawai sai ganin yaya Dalhat sukayi a kofar kitchen fuskar nan babu annuri yayi shigar kanan kaya sun amshi jikinsa kai gsky Dalhat ya hadu ba karya



*waye Dalhat*

Dalhat matashin saurayi ne wanda shekarunsa basu wuce talatin da biyar ba kyakkyawa ne ajin farko dogone shi yanada haske ba sosai ba irin choculate din nane hanci dogo bakinsa dan daidai yayi law ya karanta yanxu haka ya gama PhD dinsa yana aiki a. A.b.u xaria lecturer ne a fuculty of law......


🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱
😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰

Story nd written by mufeeda Muazu

bismillahir rahamani raheem

Page 61 - 66




Hudah na hada ido da Dalhat da gudu taje bayan Aunty mufeeda haka ma Jidda Aunty mufeeda tace ku lpynku klu kuwa Jidda ce ke nuna mata kofa kallon kofar tayi don taga me Jidda ke nuna mata yaya Dalhat tagani da dorina a hannunsa fuskar nan babu alamun wasa a cikinsa itama kanta sai data tsorata rufe kofar yayi ya fara takowa a hankali aunty mufeeda tace ina yini yaya



cikin daurewar fuska ya amsa da lpy klu tunda taga haka bata kara cewa komi ba magana ya farayi cikin isa mufeeda dake da Khairat Ku kuke goyawa yaran nan baya suke iskancin da sukaga dama ko aunty mufeeda xatayi magana ya katseta cikin tsawa yi mun shiru kallon Jidda yayi yace ke mena gaya miki cikin rawar murya da in ina tace hu...hudah ce ta...wani tsawan ya daka mata tace mene Jidda wanda tuni hawaye ya gama wanke mata fuska tace hudah ce tace a kyaleka kawai mu tafi kawai



Jidda tace don Allah yaya kayi mana hakuri baxamu kara ba yaya Dalhat yace kuxo nan hudah tayi karfin halin cewa baxa a xo ba wai kai ina ruwanka damu ne duk kabi ka takura ma rayuwa


Kara fusata yayi yace eh lallai ke mufeeda matsa kafin in hada dake aunty mufeeda ganin da gaske yakeyi yasa ta matsa su hudah kuwa suka fara neman hanyar guduwa amma ina ba hanya ya tufe kofar taku daya yayi ya rikosu da hannnu daya


hudah ce ta fara kokarin kwace wa amma ta kasa saboda irin rikon da yayi musu ba na wasa bane dukansu yakeyi ta koina da dorina sai kuka suke suna bashi hakuri ko sauraronsu baiyi ba saida yayi mai isarsa sannan ya kyalesu



Kallon mufeeda yayi dake gefe tana hawaye yace ke kuma lpy me akayi miki tai sauri ta share hawayen tace haba yaya irin wannan duka haka Saboda kawai sunxo gidana ai dai kayi musu hakuri harsu koma tsawa ya daka mata yace xakiyi mun shiru ko kuwa falo ta fita ta bashi wuri don tasan halinsa xai iya dukanta baxaiji kunyar dukanta ba



Su hadah na gefe sai kuka suke ido ya kada yayi jajir Dalhat yace kuyi mun shiru ku taso Ku wuce ba musu suka tashi falo suka fito aunty mufeeda na xaune ta xabga uban tagumi tana tunani irin xafin xuciya na Dalhat gsky tana tausayawa hudah



Dalhat yace mata mun tafi agaida yara da mai gidan in sun dawo a sanyaye ta amsa fita yayi jidda ta dau mayafinta ta fita hudah ce tai karfin halin yi mata sallama ta fito a tsaye yake ya jingina a jikin motarsa



motarsu suka nufa yana ganin haka ya karisa wurinsu ta baya basu san da xuwan mutum ba sai jin kawai sukayi anja musu mayafi xasuyi ihu sai sukaga yaya Dalhat ne shiru sukayi yana jansu har suka kai wurin da ya aje motarsa ya bude front seat ya jefa hudah ya rufe Jidda kuma ya jefata baya



Idon nan murtik kamar arne yayi layya har suka mika titi ba wanda yayi magana sun kusa gida wayar hudah ya fara ringing hannu tasa ta ciro wayar ganin number ne ba suna yasa bata daga ba har ya katse kira aka karayi still dai wannan numbern ne wani kallo ya watsa mata mai cike da tuhuma


Fige wayar yayi ya daga shiru yayi daga can bangaren kuwa Haidar ne yace hello sweet heart jin shiru yasa ya kara cewa hello kina jina kuwa Dalhat ya katse wayar cikin tsananin kishi wanda bai san yanada ita ba


Dai dai kofar gida horn yayi mai gadi ya bude masa gate ya shiga gidansu hudah yana yin parking ko waccensu ta murde kofa xata Rita sukajita gam a rufe


budewa Jidda yayi ta fita ita kuma hudah kin bude mata yayi kallonsa tayi cikin karfin hali tace ka bude mun xan shiga gida....




🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱
For comment 07065642314

😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰

Story nd written by mufeeda Muazu

bismillahir rahamani raheem

Page 66 - 70


HIQAYA ONLINE WRITER'S ✍🏼


Daure fuska yayi yace idan kuma naki fah kwallah ne ya xubo mata tasa hannu ta goge shiru ne ya biyo baya tsawon 3minute Dalhat ne ya katse shirun da cewa waye ya kiraki a waya yanxu hudah tai shiru ba tace kala ba har ya gaji da jiran amsa tsawa ya daka mata har saida ta firgita yace bada ke nakeyi ba cikin muryar kuka hudah tace ni ban san kowaye ba dada harxuka yayi idanunsa suka rune nan da nan jikinta ya fara rawa tace Allah yaya ban san kowaye ba


Dalhat ya buge bakinta da karfi hudah ta rike bakin tana kuka mai ban tausayi cikin rashin damuwa da kukanta ya fara magan da kakkausar murya xakiyiwa mutane shiru ko kuwa ni xaki rainawa hankali mutum ya kiraki a waya harda cewa swt hrt sannan kice baki sanshi ba to bari kiji wlh ki kiyayeni idan ko hmm kwafa ya bude kofar yace dallah fita mun a mota fitowa tayi rike da baki tana kuka harta juya xata wuce ta dawo tace masa mugu kawai Allah sai ya saka mun tayi wucewarta ciki Dalhat yana mota yana tunanin rashin kunya irin na hudah lallai akwai aiki don saina gyara mata xama ya Fada tare da yin reverse ya bar gidan



Hudah koda ta shiga parlour jidda da yaya shahid ta gani xaune da gani hakuri yake bata Allah sarki hudah baiwar Allah ba mai share mata hawaye wasu xafafan hawaye ne suka xubo mata xata wuce yaya shahid yace ke xo nan ba musu a hankali take tafiya harta je tace gani kallonta yayi sama da kasa har time din hawaye bai daina xuba a fuskarta ba



Yaya shahid yace kukan me kikeyi bayan duk abinda ya faru ke kikaja saboda rashin jin magana irin naki kina so ki koyawa Jidda hudah da ranta ya baci ta kalli Jidda tace ke kika fada masa haka yaya shahid ya katseta da cewa to mara Kunya ba ita ta fada mun ba nine na fahimci haka ki kiyaye ni👉🏼 ya nunata sannan yace ta tashi ta bashi wuri


Hudah ta tashi jiki a Sanyaye ta nufi sama direct dakinta ta shiga ta rage kayan jikinta ta dauki wayarta ta koma gado tana kunnawa text ta fara gani da numbern da aka kirata cikin bude bude ga abinda yake cewa


Assalamu alaikum fatan gimbiyar tawa tana lpy daxu na kiraki so bana jinki sai na kashe hope everthing is fine urs Haidar hafeex


Hudah tai murmushi tace Allah sarki Ashe sir Haidar ne reply ta tura masa kamar haka


Waalai kumus salam lpy klu d time dat u call me I was busy driving thanks 4 caring


Ta tura masa sir Haidar na xaune shida hajiyarsa yaji karar text dauko wayar yayi don ganin sakon meye yana dubawa yaga Ashe gimbiyar tasa ce murmushi yayi ganin text din amsa ya bata kamar haka

thanks dear love u extend my greeting 2 sis Jidda



Shigowar text dinsa yayi daidai da shigowar Jidda dakin waigowa hudah tayi ta harari Jidda tace maiya shigo dake dakina ai kamata yayi ki bishi dakinsa sai yaci gaba da lallashinki a can in ga karshen soyayya mtsw....tayi tsaki ta koma ta bude text din da ya shigo murmushi tayi data gama karantawa Jidda dake gefe ta dada mata duka a baya tace yar iska dariyar me kikeyi ta fige wayar hudah tace malama kibani wayata tunda ba da yaya shahid aka siya mun ba Jidda tace baxaa bayar ba hudah bata kara cewa komi ba Jidda ta bude wayar ta dudduba duk text din saida ta duba



Tashi tayi daga inda take ta koma kusa da hudah dake kwance ta dafata bata dago ba Jidda ta leka taga Ashe kuka take mara sauti fuskarta duk hawaye Jidda ta goge mata fuska tace jiddah tace haba hudah don Allah kiyi hakuri man ki daina kukan nan haka nan hudah ta tashi ta xauna tace Jidda kenan hakuri dai hakuri kullum itace kalmar haba dubi irin wulakancin da yayi mana a gidan aunty mufeeda kaman mu da girman mu da komi yayi mana duka kamar wasu yayan sa duk dai saboda kina dayakeyi kenan baxa muyi xumunci ba


Kuma aike kinada wanda xai lallasheki ya baki hakuri kiji sanyi a ranki nikuwa fah ba mai kaunata sai kace wata mujiya tana kaiwa nan ta fashe da kuka Jidda ta rungumeta tana lallashinta har sai da tai shiru Jidda tace nima abin na damuna sai dai ba yadda xamuyi tunda anfi karfin mu Hudah taja dogon numfashi tace Jidda Allah idan aka cigaba da matsa mun xan bawa kowa mamaki Jidda tace aa hudah kada kije ki aikata abinda nan gaba xaki kuka dashi muyi hakuri mu cigaba da addua insha Allah komi xai xama tarihi.....





🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱
For comment 07065642314

😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰

Story nd written by mufeeda Muazu

bismillahir rahamani raheem

Page 71 - 75


HIQAYA ONLINE WRITER'S ✍🏼




Hudah tace jidda abin yayi yawa ta ko ina ba sauki Jidda tace hakane addua itace kawai mata hudah tace to Allah yasa mudace Jidda ta amsa da ameen hudah tace yawwa Jidda kinga text ko Jidda tace eh na gani ammah ai number ne waye hudah tace sir Haidar ne Ashe shine ya kira mota shine yaya Dalhat harda duka na Saboda nace ban san number din ba muryar namiji yaji Ashe Jidda tai dariya harda shewa tace Allah hudah ki yarda dani yaya yana sonki hudah ta harareta tace karya kike dayana sona koda bana sonsa lallashina xai rikayi ba ya rika sani kuka ba Jidda tace irin tashi salon soyayyar ne haka hudah tace salon soyayyar mugunta ba Jidda tai dariya tace baxaki gane ba kila sai xuwa nan gaba so back to business yanxu ya kike so ayi hudah tace so nake ki tura masa da address din gidan nan gobe xaixo jidda ta dafe kirji ta xaro ido 😳 ke hudah yaxo yayi miki mene hudah tace ke dadina dake tsoro kamar farar kura to bayani kawai xanyi masa mu bawa juna hakuri


Jidda tace mai xai hana idan mun hadu a skull sai kuyi duk maganar da xakuyi hudah tace aa gara dai yaxo kuma ya rokeni don Allah in bashi dama yaxo gidan mu jidda tace hudah rashin jin maganarki da kafiyar ki ke Janyo mana Fada wata rana harda duka haba hudah tace yi hakuri Jidda daga wannan ai shikenan Jidda tace ya xanyi dake bani wayar hudah ta dauki wayar ta mika mata Jidda ta rubuta address ta tura masa tace gashi nan na tura masa ni bari in shiga gida wurin ummi hudah tace ki cewa ummi tayi hakuri ban shigo nabata labarin ba kamar yadda nace ina tsoron haduwa da yaya Dalhat ne Jidda tayi mata gwalo 😜 tace gara ai da so kike ki tona mana asiri ko ta fadi haka tare da fita daga dakin hudah ma tashi tayi tabi bayanta suka sauka falon kasa hajiya ce a falon tana kallo Jidda tai mata said a safe ta fita hudah kuma ta rakata waje sukai sallama ta shigo gida ita kuma ta wuce gida



Jidda na shiga harabar gidan su taga motarta tayi mamaki kwarai don a iya saninta a gidan Aunty mufeeda suka bar motar Ashe bayan da ya sauke su ya koma ne ya dauko motar koda ta shiga cikin gidan ummi bata falo don haka direct dakin ummi ta shiga ta tarar da ita a gefen tana xauna tana waya Jidda ta samu wuri ta xauna har sai data gama wayar tace ummi mun dawo ummi tace to sannunku da dawowa ya naga idonki yayi ja kuma jikinki duk shedar bulala Jidda ta dukar da kai tace bkm ummi ta daka mata tsawa tace xaki Fada mun wanda ya dakeki ko sai na kara miki da nawa cikin rawar murya Jidda tace yaya Dalhat ne yabi mu gidan Aunty mufeeda yayi mana duka nida hudah ran ummi ya baci sosai tace mai kuka yi masa Jidda tace bkm wai meyasa muka fita ummi ta dauki waya ta kirashi tace duk abinda yakeyi ya bari yaxo tana nemansa dama ba nisa yayi ba yana waje ya shigo a rude ganin ummi ranta a bace ga kuma jidda a kasa ta dukar da kai sai da gabansa ya fadi yace ummi gani




Ummi tace na baka 2mins kira mun jidda Kuxo tare yace to sannan ya fita hudah kuwa bayan ta dawo daga rakiyar Jidda a falo ta xauna wurin hajiya tace hajiya don Allah ki saka baki a daga auren nan wlh ban shirya ba hajiya tace lallai wuyanki yayi kauri to ai sai kije ki samu su alhaji suda suka yanke hukunci amma bani ba hudah taja bakinta tai shiru sai hawaye dayake ambaliya hajiya tana kula da ita tana kuma tausaya mata amma dole ta nuna mata su suka haifeta ba ita ta haife su ba


Kowa yayi shiru hajiya ta maida hankalinta ga kallon da takeyi ita kuma hudah tana nata sanaar wato kuka Dalhat ya shigo da sallama hajiya amsa hudah ta tashi hajiya tace dawo ki xauna ina kuma xaki hajiya xata tashi Dalhat yace kiyi xamanki ummi ce dama take neman hudah tace muxo tare....



🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱

For comment 07065642314

😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰

Story nd written by mufeeda Muazu

bismillahir rahamani raheem

Page 76 - 80


HIQAYA ONLINE WRITER'S ✍🏼




Hudah ta balla masa harara tace hajiya karya yakeyi ummi baxa tace muxo tare ba hajiya tace xaki rufe ma mutane baki ko sai na fasa shi mara kunya kawai waye xaiyi miki karya hudah tai shiru bata kara cewa komai ba tana xaune ko motsawa batayi ba kuma bada niyyar tashi hajiya tace kefa yake jira hudah tace hajiya Allah dukana xaiyi idanunta suka kawo kwallah shi kuma duk sai yaji kunya ya dukar da kai hajiya tace ko yanka ki xaiyi sai kinje ba yadda ta iya dole ta dauki mayafinta yana gaba tana biye dashi suna fita ya juyo ya kalleta yace kawo hannunki harararsa tayi tace indai saika rike hannuna ne sai dai a fasa don ni ba yar isaka bace irinka matsowa yayi daf da ita yace nine dan iska ko lallai xanyi maganinki saura kwana nawa ne yace bari kuma na fada miki kika kuskura kika fadawa ummi na bigeku wlh ranki sai ya baci don haka ki kula da kalamanki cikin jin haushi da kalamansa tace sai dai ka kasheni said na fada Dalhat yace muxu ba mugani yayi gaba abinsa hudah na biye shi a baya har suka shiga gidan a falo suka tarar da ummi da Jidda



Hudah ta samu gefe kusa da Jidda ta xauna tace ummi gani ummi ta kalleta dakyau tace hudah meya samu idonki yayi ja haka Dalhat gabansa ya fadi yana adduar kada hudah ta tona masa asiri hudah tace ciwo yakeyi ummi cikin fada ummi tace hudah yaushe kika fara karya idan idonki na ciwo wannan shedanfa xaki fada mun gasky ko sai na kara miki hudah da

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment