Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tuni hawaye ya wanke mata fuska tace yaya Dalhat ne ya dake mu a gidan aunty mufeeda ran ummi ya baci ta wanke shi da mari har sau biyu ji kake tasss......ummi tace gasu nan ka kashesu nace inga gawarsu tunda har xakayi musu irin wannan duka kaman ka samu jakuna to wlh ka fita daga idon in rufe Dalhat kuwa sai hakuri yake bata ga xafin mari daga karshe tace lallashe mu sannan kuma tace ya raka hudah gida kuma wlh idan ya tabata ranshi sai ya baci ba yadda ya iya hakanan ya rakata bai kulata ba har suka shiga gidan lokacin ana kiran sallar issha saboda haka yana fitowa masallaci



Hudah kuma dakin hajiya ta shiga ta tarar da tana sallah fitowa tayi ta tafi dakinta don yin sallah koda ta idar tai wanka ta rage kayanta wayarta ta dauko ta Kunnu tana game Husna ce ta shigo dakin tace Aunty hudah hajiya na kiranki hudah tace tana ina ne Husna tace tana dakinta a tare suka fito Husna ta xauna a falo hudah ta shiga dakin hajiya tace hajiya gani hajiya tace to ai naganki miko min kofin can na kan dressing mirror hudah ta dauko ta mika mata hajiya tace magani ne ki shanye yanxu ki bani Kofin hudah ta ya mutsa fuska tace hajiya ni lafiyata klu baxan sha ba hajiya ta daka mata tsawa nan da nan ta shanye ta mika mata Kofin xan tashi ta harareni ta koma ta xauna hajiya ta dauko wani magani ta hada da madara peak ta hadah ta mika mata ta shanye tana bata rai hajiya ta dauko wani turare a kwalba tace wannan a ruwan wanka xaki xuba safe da dare kuma wlh idan kika aje sai ranki ya baci



Tashi ki bani wuri harta tashi hajiya tace kinyi wanka ne hudah tace eh hajiya tace shikenan saiki fara amfani dashi gobe hudah tace to hajiya hudah ta fita jiki ba kwari yaxaayi a rika bata irin wannan abun bayan ita ba auren soyayya ba a dakeka a hanaka kuka a falo ta tarar da Husna tana kallo hudah tace Husna dan aje mun turaren a dakina Kan dressing mirror



🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱

For comment 07065642314

😰😰😰😰😰
Auren Dole
😰😰😰😰😰



Bismillahir rahamanir raheem


Story And
Written
by
mufeeda Muazu


Page 81,, 85


HIQAYA ONLINE. WRITERS ✍🏼



Hudah na xaune a falo tunani kala kala a cikin ranta hajiya ta fito daga daki ta kalli yaran nata guda biyu tace lpy naga kunyi jugum kowa ta tsira ma tv ido kunci abinci kuwa Husna tace aa dama muna jiranku ne hajiya tace ai sai ku taso ga alhaji nan ma ya dawo ku taso muje dining suka nufa a can suka tarar da su yaya shaheed da alhaji Husna tayi saving din kowa san nan tasa nata abinci suke ci ba mai magana sai karan chokula kawai kakeji Husna ce tace alhaji dama kawai a hada auren Aunty hudah dana yaya shahid alhaji yace Allah ko auta to ai yayan naku bai kawo mata ba Husna tai sauri tace yanada budurwa ni na Santa shahid da ya tsaya kallon Husna yana harararta tunda ta fara magana ita bata San ma yanayi ba ya daka mata tsawa yace ke kiyiwa mutane shiru mara kunya kawai kema auran xaayi miki kowa ya huta πŸ™„ Husna ta shagwabe fuska kaman xatayi kuka tace alhaji kagan shiko alhaji yace kyaleshi auta ba wanda xai miki aure yanxu kinji Fada mun waye budurwan shashid yaja kujera xai tashi alhaji yace ya koma ya xauna ba yadda ya iya hakanan ya koma ya xauna Husna tace Jidda ce ta gidan ummi shahid dukar da kai yayi ji yake kaman ya nutse saboda kunya



Hajiya da alhaji sunyi
Farin ciki da jin haka hudah tana xaune kaman hoto batace komi ba alhaji yace Husna ngd da wannan Albishir naki alhaji ya juyo wurin shahid yace shine tuntuni kuka boye mana shahid dai bai ce komi ba hajiya tasa albarka alhaji yace ranar daura aure sai asa rana hajiya tace hakan yayi har suka gama hudah bata tanka ba haka kuma ba wanda yabi ta Kanta tashi tayi ta tafi dakinta falo suka koma sun danyi hira kadan kowa ya tashi falo ya rage daga alhaji sai hajiya Husna tana dogon kujera tana barci alhaji yace hajiya bawai naga kuna ta shirye shirye ba walima kawai xaayi Don bamu son bidiar nan hajiya tace to alhaji yadda kace haka xaayi



A bangaren Dalhat kuwa tunda ya fita bai koma gidan ba saboda bacin rai wai akan ya daki su hudah ne ummi ta mareshi a gabansu saboda su raina shi gidan wani abokinsa ya tafi a can yaci abinci suka sha hira sai wurin tara ya tashi sukayi sallama ya rako shi har wurin motarsa sai da ya shiga mota yaga kati shi kwata kwata ya manta dashi sauri yayi ya ciro ya mika mata abokin yace Ahmad gashi don Allah kada kace komi abin ne yaxo cikin gaggawa don Allah kaba wa sauran ni gobe xan koma Ahmad ya am tare da cewa wacece wannan mai saar Dalhat yayi murmushi yace ai kasanta hudah ce Ahmad yace gaskiya kayi Saar mata Allah ya Sanya alkhairi Dalhat ya amsa da Ameen sukayi sallama ya tafi Dalhat na shiga gida part dinsa ya wuce yayi shirin barci

Asubah tagari


5.30am hudah ta tashi tai sallah tunda tai sallah bata koma ba tayi axkar ta dauko Qur ani tayita karatu har gari yayi haske Sannan tayi addua ta gyara dakinta tsar Sannan ta shiga wanka harta shiga ta tuna da turaren da hajiya ta bata fitowa tayi ta dauka ta xuba a ruwa take toilet din ya gauraye da kamshi tai wankanta ta gama harta shirya bata daina kamshin ba kai wannan turare da kamshi yake ta Fada a xuciyarta kwalliya tayi sosai wanda rabonta da irin shi tun kan ace xata auri Dalhat



Ta fito fuskarta cike da walwala da farin ciki a corido ta hadu da hajiya hudah tace lah hajiya wurinki xanxo ina kwana hajiya ta amsa tace hudah kinyi kyau ga kamshi hudah tayi murmushi tace ngd hajiya



🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱

For comment 07065642314

😰😰😰😰
Auren Dole
😰😰😰😰😰



*Bismillahir rahamanir raheem


Story And
Written
by
mufeeda Muazu


Page 86 - 90


HIQAYA ONLINE. WRITERS✍🏼*



dining suka wuce suna xuwa hudah ta gaishe da alhaji sannan ta gaishe dasu yaya shahid Husna ta gaisheta hudah tace alhaji yau ni xanyi saving din kowa alhaji yace da kyau hudahna kowa yayi farinciki da sauya warta ta saki jiki tana walwalarta kuma suna mamakin sauya warta haka suka ci abinci suna hirarsu gunin shaawa ita Kanta hudah bata san meke faruwa da ita ba saboda yau tunda ta tashi takejin farin ciki ko don xataga abin kaunarta ne sir Haidar oho suna gama karyawa kowa ya tashi hajiya tace in sameta a daki falo ya rage daga hudah sai yaya jadeed hudah tace yaya yau naga kowa sai farin ciki yakeyi a gidan meyasa jadeed yace saboda mun ganki cikin farinciki hudah tace lallai yaya kuna so inyi farinciki xakuyi min auren dole uhm jadeed yace hudah ki daina wannan maganar muna sonki muna son farincikinki kiyi hakuri ki dauki auren nan a matsayin kaddararki Husna sako tace aunty hudah hajiya na kiranki hudah tace to ta tashi ta tafi dakin hajiya ta sameta a xaune tana duba wani Littafi hudah tayi sallam ta shiga wuri ta samu ta xauna



Hajiya ta dago ta kalli yar tata tace maganinki xaki sha hudah ta bata rai tace hajiya ni baxan sha ba saida hajiya tayi da gaske sannan tasha hajiya tace gobe mai dilka xataxo saiki shirya hudah tace hajiya gobe xanje skull fa hajiya tace ai keda makaranta kuma sai dai bayan aurenku idan ya yarda sai ki cigaba hudah ta rushe da kuka tace hajiya ya xakuyi mun haka don Allah ku fada masa ya barni in cigaba da karatuna hajiya tace kiyi shiru ki share hawayenki insha Allah xai barki jin haka yasa xuciyarta yai Sanyi ta goge fuskarta tace Allah ya yarda hajiya ta amsa da ameen



Hudah tace hajiya bari inje wurin jiddah hajiya tace adawo lafiya dakinta ta koma ta dauki wayarta da mayafinta sai gidansu Jidda a falo ta tarar da Abbu da ummi ta tsugunna ta gaishe su sannan ta wuce dakin Jidda bata dakin gefen gado ta xauna tajiyo karar ruwa a toilet alamun tana wanka agogo ta kalla karfe goma da rabi na safe bata ida kallon agogon ba wayar dake hannunta ya soma kara ta duba fuskar wayar sir Haidar ne daga wayar tayi tare da yin sallama gaisawa sukayi ya shaida mata yana fitowa 11am idan ya shigo xai kirata


Jidda ce ta fito daga wanka tace kai hudah iriin wannan kwalliya haka ga kamshi da kike xubawa duk dakin ya gauraye da kamshi duk dai saboda sir Haidar ne hudah tayi tsaki mtsww tace ke wlh kin cika fassara to wannan tsinannen kamshi da kikaji inayi to wani turare ne hajiya ta bani wai in rika sawa a ruwan wanka da kuma wasu shegun magungunar da aketa bani ni banga dalili ba Jidda tayi shewa tace Amarya kin sha kamshi kice gara in fara lallabaki tun yanxu kona samu tabarraki hudah tayi tsaki mtsww tace dalla malam kiyi sauri ki shirya ya kusa xuwa Jidda tace to wai tsaya a ina xaa sauke shi hudah tace anan gidan mana Jidda tace kin san yaya Dalhat na nanfa kada ya ganshi yayi masa wulakanci kin san dai halinsa hudah tace insha Allah ba xai ganshi ba can garden xamu xauna Jidda xatayi magana kenan wayar hudah ya soma ringing ta daga wayar yace gani a waje naga gida iri daya guda biyu wanne xan shiga



Hudah tace ka daga Kanka sama xakaga hoton flower daya green daya red sai ka shigo inda kaga green yace gashi nan shigowa fitowar mu yayi daidai da shigowarsa farfajiyar gidan so ba bata lokaci ya fito hanyar garden muka bi yana biye damu har muka isa wurin xama katon kafet ne shimfide a kasa.....



🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱

😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰



bismillahir rahmani raheem


Story
And
Written
by
mufeeda Muazu


Page 91to100



Salam masoya littafin auren dole ina mai baku hkr a bisa shirun da kukaji wannan ya farune saboda ayyukan da sukayi min yawwa but yanxu komi yayi dai dai ngd



Har garden hudah ta kaishi katon kafet ne shimfede a kan kafet grass din dake wurin Hudah tace mishi bismillah ka xauna ta fada tare da xama sir yayi murmushi ya xauna Jidda da Hudah suka gaishe shi a tare amsawa yayi cike da faraa shimfide a fuskarsa daga ganinsa kasan yana cikin farin ciki ganin haka hudah tace Allah sarki gsky ina tausaya mana cikin xuciya take wannan maganar sunyi shiru na dan wani lokaci jiddah ce tace bari in kawo ma babban bakon namu ruwa hudah tace yi sauri Jidda wlh sam na manta Jidda tace ai dole ki manta saboda farin ciki hudah ta harareta tace dallah kiyi sauri kada ya gaji da jira Jidda ta tafi tana dariya sir Haidar yayi murmushi yace hudah kuna burgeni keda yar uwanki uhm kawai hudah tace sir Haidar yace hudah yau gani a gidanku fatan xaki karbe ni hannu biyu hudah tayi murmushi dai dai lokacin Husna taxo da sallama tare da aje tray a kusa da sir Haidar ta tsugunna ta gaisheshi ya amsa cike da faraa hudah tace Husna ina Jiddan take Husna tace tana can yaya Dalhat ya kirata hudah ta xaro ido πŸ‘€ tace dama bai tafi ba Husna tace eh hudah tace shikenan jeki Husna ta tashi tafi hudah ta juyo wurin sir Haidar tare da yin murmushi tace dan Allah kayi hakuri sir haidar yace ah bkm ai ruwa lemu da snacks ne a tray din da Husna ta aje hudah ta xuba masa ruwa da lemu a Kofi ta aje masa yace to ngd da kulawa sir Haidar yace Husna Kanwar mu ce ko don naga kuna kama sosai kaman an tsaga kara hudah tace eh itace auta sir Haidar yace da kyau tare da aje kofin lemu



jiddah kuwa tunda ta fito da tray xata kawo Dalhat ya tsareta wai ina xata kai kuma motar waye a compound Jidda ta rude saiga Husna tamika mata tray din tace takai garden Dalhat ya dakawa Jidda tsawa yace bada ke nakeyi ba motar wanene wato ke kin kawo kai aure kike so ko har kin fara kawo samari ko ya rike hannunta xai fara janta tace yaya Allah ba bakona bane wurin hudah yaxo sakinta yace hudah lallai xata gane kurenta dan ina ne don nasan bakinku daya da ita Jidda tace don Allah yaya kayi hakuri wlh ba soyayya sukeyi ba wani mugun kallo ya watsa mata hakan yasa taja bakinta ta tsuke fita yayi daga falon su hudah kuwa tana garden ana hira da sir haidar jefi jefi saboda rashin sabo hudah taga shirun yayi yawa ne yasa tace bari duba tagan ta mike kenan sai ga Jiddan komawa tayi ta xauna Jidda tace don Allah kuyi hakuri aikine ya tsareni sir Haidar yace ah bkm ranki ya dade sunyi shiru na dan time Jidda tace sir muna mai baka hakuri abinda xamu fada maka ba daga mu bane haka Allah ya tsara sir haidar yace to ina jinku Jidda ta xayyane masa duk abinda ke faruwa game da hudah akan auren da xaa yi mata daga karshe tace dan Allah yayi hakuri sun xabi su fada masa gaskiya ne saboda hudah na sonka sosai shiyasa hudah dake gefe tuni hawaye ya wanke mata fuska sir Haidar kuwa jikinsa duk yayi sanyi ya dukar da kai shiru ya ratsa na tsawon 5min sir Haidar ne yayi karfin halin dagowa idonsa ya kada yayi ja yaga hudah na xubar kwallah yace bkm Jidda na fahimce ku kuma ngd da baku rufeni ba Allah ya saka da alkhairi hudah kiyi hakuri haka Allah ya kaddara insh Allah xamu cigaba da xamunci a karshe kuma ina rokon alfarma a gurinku Jidda tace toh Allah yasa baxai gagare mu ba sir haidar yace baxai gagara ba insha Allah



Idan ba damuwa Husna nikeso a bani nidai ina son jininku don Allah ku taimaka mun hudah ta goge fuska tace insha Allah xanyi kokari but ka nemi soyayyarta sir Haidar yayi godiya tare da aje musu kudi mai yawa yace suyi hakuri dashi bayawa sunyi sunyi ya barshi yaki hakanan sukayi masa godiya har wurin motarsa maigadi ya bude masa gate ya tafi haka suka rabu cike da damuwa.......
🌱🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱🌱
For comment 07065642314

😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰




Bismillahir rahmani raheem


Story
And
Written
by
mufeeda Muazu



Page 101. 105


Dedicated dis page 2 my cwt sis First Lady🌹




Yana fita daga gate din Jidda da hudah suka juya cikin gidan cike da damuwa ashe duk abinda sukeyi Dalhat yana hangensu ta window suna komawa ciki kuwa ya fito ya bisu koda suka shiga bakowa a falo xama sukayi hudah ta dauki remote ta kunna tv ko xataji saukin xugin da xuciyarta keyi minti kadan sukaji an bugo kofa da karfi dago Kan da xasuyi ne suka hada ido Dalhat cikin daurewar fuska ya kariso har inda hudah ke xaune kirjinta sai dukan tara tara yakeyi jikinta harya fara rawa Fada Fada ya soma magana waye yaxo gurinki hudah tai shiru batace komi ba tsawa ya daka mata bada ke nakeyi ba hudah ta dago Kanta hawaye ya wanke mata fuska tace lecturer din mune Dalhat yace oohh dama abinda kukeyi kenan an tura ku karatu kuna soyayya jidda tace Allah yaya ba soyayya mukeyi ba Dalhat yace rufemun baki kafin fasa shi Jidda taja bakinta tayi shiru ya dawo Kan hudah yace dukda ba sonki nikeyi ba baxan dauki shashanci ba wlh na kuma ganinki da wani ranki xai baci



Hudah ta goge kwallar daya xubo mata tace da kake cewa baka sona nima ai ba sonka nikeyi ba kuma duk wanda yace yana sona sai na kulashi mari ya kai mata jikake tass rike wurin tayi ta dago xa tai magana ya kara mata a dayan kuncin sai data ga wani haske kamar wuta ta fashe da kuka ta tashi ta nufi hanyar fita Jidda ta tashi xata bita Dalhat ya hanata hakanan ta koma ta xauna badon ranta yaso ba hudah kuwa tana fita compound din gidan idonta yakai wurin wani katon karfe da gudu taje ta dauki karfen tana waigowa ta ganshi ya kofa ya harde hannun a kirji yana kallon ikon Allah dai dai time data juya da gudu dai dai ummi da yaya shaheed suka shigo gidan da sauri yaya shahida ya bi bayan hudah ita kuma ganin yaya shahid ya biyota ta kara da gudu



Shima ya kara da gudu ummi kuwa sai xabga salati takeyi tana kiran hudah ita kuma hudah ina hankalinta ya tafi tana xuwa ta daga karfen ne yaya shahid ya rike yana kokarin kwacewa amma ina ya kasa yaya Dalhat yace barta kawai mara kunyar karya kawai shima yayi ya kasa kowa na mamakin irin karfi haka itako hudah ba abinda take sai kuka taki kula kowa duk cikansu sun rasa yadda xasuyi da ita ummi ta hau fada wai me yaya Dalhat yayi mata haka ta inda take shiga batanan take fita ba jiddah tace ummi anya huda ba aljannu ne da ita ba sai a lokacin hudah ta bude ido tace kalau nike banida komi yaya shahid yace saki karfen nan hudah tace baxa saki ba mari a dauketa dashi ba shiri ta saki taje ta rungume ummi tana kuka tace ummi wlh yaya Dalhat bai sona Allah idan aka daura auren nan kasheni xaiyi hawaye duk ya bata mata fuska ummi ta goge mata fuska sannan tace shahid ku biyoni falo ta rike hannun hudah suka shiga kowa ya xauna shiru falon yayi baka jin komi sai shasshekar kukan hudah



Ummi ta fara magana cikin bacin rai tace shahid da kai Dalhat duk wanda ya kuskura ya kara taba hudah wlh sai ranshi ya baci kun girma baku san kun girma ba Dalhat yace ummi wlh duk ke kikesa su raina mu ummi tace yi ma mutane shiru ku tashi Ku bani wuri hudah tai musu gwalo sunji haushi amma ba yadda suka iya haka nan suka fice ummi tayita lallashin hudah hartai shiru sai dai fuskanta sun kumbura tace ummi xan tapi gida jiddah ta taso suka fita tare a gate suka hadu da yaya Dalhat ya taresu yace ke bar ganin kina gaban ummi wlh kika shigo hannuna sai kin gane kurenki ke kuma Jidda bari alhaji ya dawo kema aure xa ai miki kowa ya huta marasa kunyar yara kawai......

🌱🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱🌱

For comment 07065642314.

😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰




Bismillahir rahmani raheem


Story
And
Written
by
mufeeda Muazu



Page 106 .110



Dedicated dis page to my friend classic Feedoh



Wucewa sukayi ba wanda yace masa komi shiko gida ya koma ya hada kayansa xai koma wurin aiki dama ya sa ba tafiyar dare yana gama hada kayansa ya fito ya nufi dakin ummi ya durkusa har kasa yace ummi yau insha Allah xan koma wurin aiki ba yabo ba fallasa tace Allah ya tsare Dalhat yace Ameen sannan tace ina fatan ka sallami amarya da kawayenta yace aa ummi sai nadawo ranar alhamis kuma ma ai basuce suna bukatar wani abuba ummi ta bata fuska tace ooo sai sun tambaya tayi kwafa Dalhat yace kiyi hakuri ummi bari inje banki in dawo bata daice komi ba harya fita yana fita yaci karo da Abbu a waje ya duka ya gaishe shi Abbu yace Dalhat wai yaushe xaka koma ne Dalhat yace yau insha Allah Abbu yace amma shine har yanxu baka fara shiri ba kafiso kayi tafiyar dare ko Dalhat ya sosa keya yace na shirya ummi ce tace wai sai na sallami su Jidda shine xanje banki in dawo sai in tafi



Abbu yace kai wannan ummin taku akwai rigima Dalhat dai murmushi yayi baice komi ba Abbu yace kada ka damu nixan bada Sannan yace umminku tace anan xaku xauna xansa a gyara muku part din can da bakowa Dalhat yace Abbu Don Allah ka rokar mun ita ta barni in tafi da ita xaria kafin in gama gidana Abbu yace kayi hakuri Dalhat kabi maganar mahaifiyarka na dan lokaci kadan ne Dalhat yayi wa mahaifinsa godiya tare da yi masa sallama abbu yayi masa fatan alkhairi Dalhat ya koma ciki ya dauko jakarsa ya saka a mota yaje yayiwa ummi sallama Allah ya tsare kawai tace a sanyaye ya fita gidansu hudah ya shiga yayiwa su hajiya da alhaji sallama cikin kulawa sukai masa Allah ya tsare hanya yaji dadin haka ya fito ya dauki hanyar xaria ankai akwati doxin kaya na gani na Fada gsky kaya sun burge kowa amma banda amarya wanda tunanin irin xaman da xatayi a gidan wanda baya sonta bata sonsa amarya tasha gyara sosai kaman ka taba jini ya fito ga kamshi mai dadi datakeyi


Yau Jumaa kuma yaune xaai walima amarya hudah na kwanace a daki ba abinda take sai kuka Jidda ta shigo dakin ta ganta a cikin wannan hali Jidda taxo ta xauna kusa da ita tace haba Sis don Allah kiyi hakuri ki daina kuka kinga fah ga kawayen mu can da yan skull din mu a falo hadah ta kalleta kallo irina tuhuma tace a iya sani na bamuyi gayya ba Jidda tace eh hajiya ce tace in gayyato su hudah tayi kwafa tace dai dai ne Jidda tace yanxu dai kiyi hakuri ki tashi kiyi wanka ga mai kwalliyi can tana jiranki hudah tace ba wankan da xanyi malama ki tashi ki bani wuri ni na kulama farin ciki kikeyi tayi tsaki ta juya baya Jidda tayi juyin duniya fur huda taki tashi hakanan ta hakura ta tashi ta fita wurin aunty Asiya taje kanwar hajiya ta Fada mata hudah fah ta tubure tace ba xatayi wanka ba gashi lokaci na tafiya aunty Asiya ta fusata dama ita akwaita da fada dakin sukaje yadda Jidda ta barta haka suka sameta Aunty Asiya ta maka mata duka a baya ta juyo da niyyar masifa tayi toxali da aunty Asiya Jidda kuma na bayanta hudah ta bata rai Aunty Asiya tace tashi ki shiga wanka ba damar musu don tasan aunty Asia sarai tashi tayi tana Kunku nai ta shige toilet Jidda kuma taje ta kira mai kwalliya


bata Jima ba ta fito daga wankan aunty Asia na xaune a bakin gado ga Jidda da mai kwalliya kuma Jidda ta mika mata kayan da xata sa toilet ta koma ta saka kayan ta fito tana tura baki mai kwalliya ta tsantsara ma amarya kwalliya na gani na Fada Sannan akayiwa Jidda Dalhat kuwa bai shigo bauchi ba sai bayan sallar jumaa....


🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱

For comment 07065642314

😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰



bismillahir rahamanir raheem


Page 111- 115



*story nd written by Mufeeda Muazu*



*Dedicated dis page 2 my swt twin Sis Hanifa Muazu Allah ya barmu tare😘*




Amarya kuwa da kyar aka samu ta tsaya akayi mata kwalliya gashi tayi kyau sosai kaman ba ita ba inba wanda ya Santa sosai ba baxaka ganeta Dalhat kuwa yana shiga part dinsa ya nufa saboda cika da gidan yayi wanka ya farayi ya dan kwanta don ya huta

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment