Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan kawai anyine dan a tozarta Samir d'in._
[11/19, 6:57 PM] Zeetty: _Dan anga yafara tara Iyali, tun Samir bai d'auki maganar da mahimmanci ba, har yad'auka, dan haka lokaci guda yafara canjama Sulty shi, abu kad'an idan tayi saiya rufeta da masifa da bala'i, wata rana har dukan ta yakeyi agaban Aslam, tun yaron baya fahimta har yafara ganewa, a haka Maryam k'anwarta tazo takawo mata ziyara wata rana ta risketa jiki duk shatin bulala kamar wata Jaka, hankalin Maryam yatashi dan haka takira yayan su Isah a waya tana sanar masa, hankalin sa a tashe ya k'araso gidan ganin irin dukan dake jikin k'anwarsa wani tausayin ta ya kamashi._
_Bayan ankaita asibiti binciken likita nafarko daya fara ganowa shine, Aysher tana d'auke da hawan jini, Dr.Muhammad ransa ya6aci dajin haka, yakuma tausayama 'yar sa, dan yasan may be tana fuskantar matsala a gidan mijin ta, dan su kansu yagama canja musu baya zuwa gidan, idan suka had'u da Isah saidai Isah yayi mishi magana._


_Bayan ankirashi awaya an sanar masa suna asibiti fad'a yafarayi tare da borin kunya yana fad'in"akan meye za'ad'auki matar sa a kaita asibiti batare da sanin shiba, saboda an gama rainashi anga bashi da kud'i ko meye?,_ _ran Isah ya 6aci dajin haka, dan haka yaso bashi amsa, amman Mahaifinsa ya dakatar dashi, tahanyar nunama Samir cewar sunyi kuskure yayi hak'uri._
_Hakadai Zaman yaci gaba da kasan cewa, dan wata rana idan yayi mata dukan ma kulleta yakeyi a d'aki, dan gudun kar 'yan gidan su, suzo suganta ballantana a taimaketa._
_Abokan sa suna ka'ara ingizashi musamman wani mai suna Kabir da cewar matuk'ar baya k'untatawa Aysher bazai huce takaicin abinda mahaifinta yasa akayi masa ba (Kajifa mai karatu)._
_Dan haka yak'ara kaimi wajen sambad'o mata rashin mutumci, horo da yunwa, baya bata kud'in cefane, akwai sanda tasiyar da Gold d'inta tabashi kud'in yaja jari, yace 'yan damfara sun kwashe kud'in, idan yatashi zaginta kuwa sai yace"Shashasha wawuya wadda batasan ciwon kanta ba, muguwa irin mugaye masu bak'in hali, mai farar k'afa", wannan zagin yana damun Aysher tasha zaunar dashi tace "meye laifin datayi masa", sai yace"Mahaifinta yasa an koreshi a aiki, dan mugunta kuma duk inda yaje neman aiki mahaifinta yasa an toshe ba'a d'aukar sa, dan haka itama tayi bankwana da jindadin gidan aurenta."_

_Dukan dayayi mata nak'arshe shine wanda ya sumar da Aysher, yatsallake yabarta a kulle a d'aki, Isah yakawo matarsa ziyara gidan Aysher yatarar gidan shiru sai kukan Aslam, kuma ya buga ba'a bud'e ba, dan haka yakira aka 6alle k'ofar anan yatarar da Aysher yashe a tsakar gida alamun bata numfashi, cikin tashin hankali yad'auki Aysher dan zuwa Asibiti._
_A wannan lokacin Aysher har targad'e yayi mata a guri biyu, (wannan wane irin zalinci ne kadaki mace, sannan ka kullota a gida kota rayu, kota mace, lallai dole a raba auren nan, dan Samir mugu ne, bason Aysher yakeyi ba), tunanin da Isah yakeyi kenan a ransa._
_Toh bayan Aysher tawarke Samir yagama borin kunyar sa da bayarda hak'uri, dan Isah yace saiya sakar musu k'anwa, Dr.Muhammad ne yakashe rigimar da cewar Samir yayi alk'awarin bazai sake bugun Aysher ba, nan take yayi wannan alk'awarin dan yanason matar sa tsabar talauci ne kawai da kuma zugan abokai._
_Bata sake zani ba, dan duka da zagin cin mutumci sai abinda yak'aru a gurin Samir, a haka aka samu cikin Afra, albarkacin cikin yarage mata wasu abubuwan, har aka haifi Afra, idan kaga Aysher dole kasan tana cikin wani hali duk ta rame ta lalace, Kabir yacema Samir" Hakanne dai-dai abokina, kaci gaba da aiki dole idan mahaifinta yaganta ransa ya6aci, kaga karama abinda yayi maka akan 'yarsa."_
_Sosai Samir yake amfani da shawaran da Kabir yake bashi, aganinsa bashi da wani aboki masoyi sama da Kabir d'in._
_A haka dai har aka haifi Afra, wulak'anci salo-salo ga kyara da hantara a gaban 'ya'yanta, idan tayi magana ya wanketa da mari, Aysher tak'i fad'a a gida, dan a cewar ta akwai lokacin da zata rabu dashi, lokacin da Allah yasa yasamu aiki, zata nemi ya sauwak'e mata._

*Mai karatu kaji irin halin da Aysher ta tsinci kanta a gidan auren ta, menene ra'ayinku?.*

A hankali Samir yadawo daga duniyar tunanin daya tafi, yaji ihun yaran sa a falo, dasauri ya mik'e yafito ya samesu yace"kuzo kuje kushiga mota natafi gurin Momyn ku", da sauri Suka ruga suna cewa"Abba yunwa mukeji."

"Zan siya muku abinci a restaurant kuyi shiru" dan bayason damuwa, mafita yake nemowa kansa, baya fatan Aysher ta tona masa asiri a gurin mahaifinta bayan alk'awarin da ya d'aukar masa na cewar yad'aina gasa mata aya a hannu............



MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐


*MAFARIN LAMARIN*




DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*



©Zeetty


*I Dedicated this page to you Gimbiya kilishi, babu wanda yakaiki son MAFARIN LAMARIN, SADAUKAR WA GAREKI*.


PAGE 9-10


Lokacin da Aysher ta iso kano gidan Iyayen ta, Mahaifin ta tasamu a k'ofar gida yana zaune yana alwalar sallah azahar, ya ta gaidashi ya amsa tare da tambayarta" lafiya kuwa Aysher da rana tsaka haka?"

Tace"Lafiya lau Baba"
Shige ciki toh barin je masallaci.


Da fara'ar ta ta shige gidan, ta samu Mahaifiyar ta tana tsakar gida, d'agowa tayi taga Aysher cikin fara'a tace"lale marhabin da mutanen kaduna barkan ku da zuwa kunsha hanya."

Aysher dai batace mata komai ba saima fara'a da taketayi, ta shige falon su.

Bayan ta samu Nutsuwa tayi sallah tare da cin abinci, Mahaifin ta ya aiko kiranta zuwa falon sa, ta mik'e ta tafi, ta sameshi a zaune gaisheshi tafara yi kafin yasake tambayar ta "ko lafiya tazo haka, kuma batare da yara ba?."

Tace"Baba dan Allah ku gafarceni akan wannan hukuncin da nakeso na yanke, Baba dan Allah kubani goyon baya na rabuwa da Abban Aslam, yanzu ne nakeda wannan lokacin, yanzu ne zan nuna masa cewar niba mai farar k'afa bace kamar yadda yake cewa tunda saida yayi arziki na nemi rabuwa dashi, Baba na tabbata duniya bazata zageni ba akan hakan, baza'ace na rabuda shi dan talaucin sa ba."

"Bangane abinda kike nufi ba Aysher, yimin yadda zangane."

Aysher tace"Baba so nake Abban Aslam yabani takadda ta na rabuwa dashi har abada."

A razane Mahaifin nata ya kalleta tare da tambayarta dalili.

Taci gaba da cewa"Baba Abban Aslam bai ta6a canjawa ba, akan abinda yakemin abaya, kamarsu duka, zagi da cin mutumci, duk kuwa da irin jan kunnen dakai da yaya Isah kukayi masa baidaina ba, nayi hakuri ne banzo na fad'a a gida ba, saboda jiran irin wannan lokacin dan idan kuka raba auren mu a wannan lokacin duniya zata zageku, ace dan bashi da kud'i ne, sai yanzu Baba dan Allah karku takuramin na koma gidan sa, banason ko ganin fuskar sa ne."

"Bawanda zai takuraki, sha kurumin ki k'anwata, Allah miki Albarka."

Bawanda yasan da shigowar sa (Yaya Isah) tsakanin Baba da Aysher sai jin maganar sa sukayi,

Dan haka Baba yakasa bata amsa, gaishe da mahaifin nasa yafarayi, kafin yace"Baba kaduba maganar yarinyar nan dakyau, ni daman nayi mamakin jin shirun Aysher, amman kowa yaganta yasan tanacikin damuwa, Baba bazata koma ba, mu nuna masa cewa akwai banbanci, ni kaina Baba abinda yake mana a lokacin raina yana 6aci, dan akaine kake dakatar dani, abarshi yazo muji daga gareshi."

Kai kawai Baba ya gyad'a musu kafin yace Aysher ta tashi ta tafi, bayan fitar ta suka ci gaba da tattaunawa, shima abin ya6ata masa rai, wato Samir baiji duk maganar dayayi masa ba da nasiha ai talauci ba hauka bane.


*********

Misalin k'arfe 5:00pm Samir ya iso k'ofar gidan surukan nasa, kana ganin sa kasan yana cikin damuwa, ya taras da Yaya Isah a k'ofar gida, fitowa yayi bayan ya gyara parking, tare da bud'ewa yaransa sufito, da sauri suka ruga zuwa cikin gidan kakan nin nasu.

K'arasawa yayi gurin Isah, ya mik'a masa hannu sukayi musabaha, kafin yafara gaishe da Isah, Isah ya amsa ba yabo babu fallasa, tun daga nan jikin Samir yafara yimasa sanyi, dan da alama Aysher ta fasa kwan.

Dan haka yace ma Isah"Abokina dan Allah Baba yana nan kuwa?."
"Eh yana ciki Bismillah daman kai nake jira kazo na wuce gida, mushige daga ciki."

Kai tsaye falon Baba suka shiga, bayan gaishe-gaishe, dakin yayi Shiru dan haka Samir yafara magana kansa a k'asa"Baba nayi laifi ku gafarceni, ku taimaka Aysher tadawo dakin ta, mu reni yaranmu ni da ita, dan Allah Baba."


Isah yayi farat zai fara magana Baba ya dakatar dashi kafin yace"Bakomai Samir ayanzu komai yana hannun Aysher idan ta amince zata dawo dakin ta falillahil hamdu, idan kuwa bataso bazamuyi mata dole ba, dan ita keda za6in zama dakai, nidai takaicina guda d'aya ne, rashin jin maganata da bakayi ba, amman bakomai, wannan yaron (Isah dan baya kiran sunan sa, d'an fari ne) muje ka turo masa Aysher."
Tare suka fice dan barin falon, mintuna kad'an saiga Aysher ta shigo hanunta d'auke da hanun yaranta Aslam da Afnan tayi sallama tashigo, da sauri Samir ya mik'e tare da rik'o hanun ta, ya zaunar da ita jikin sa har rawa yakeyi, idanuwan sa cike suke da hawaye, yafara magana da cewa"Sulty baikamata ki yanke mana irin wanna hukuncin ba, Sulty baikamata su Baba suji wannan maganar ba, haba Sulty yanzu idan kikamin haka kinyi adalci kenan, kiduba yaran mu, zasu koma marayun dole, Sulty dan Allah tashi kishiga gida ki kwaso kayanki mu wuce gida dan Allah."


Shiru Aysher tayi masa kamar bazatayi magana ba, kafin daga baya tad'ago babu alamar karaya a fuskarta tafara magana"Abban Aslam kayi hak'uri nariga nayi rantsuwa wallahi bazan cigaba da zama dakai ba, sanda kake zagina, kana cimun mutunci baka duba yaran mu ba, asalima a gaban su kake duka na da zagina harda cimun mutumci, kayi hak'uri Abban Aslam, arzikin ka bazai saka naci gaba da zama dakaiba, bazai rud'eni na manta da abubuwan dakayi min ba, na barka 'ya'ya kuma nabarsu a hanun Allah, zai dubamin su, akwai marayun da suke rayuwa babu uwa babu uwa sun bar duniya, wasu ma *GIDAN MARAYU* (Littafin Sistoh na Beauty Queen), anan suke rayuwa dan haka Allah yadubamin su, rok'ona gareka shine tunkafin rayuka su gama 6aci, ka sauwak'emin cikin ruwan sanyi ayau kafin kabar gidan nan." Tana gama fad'in haka tabar d'akin, kotakan yaranta bata biba.


Shiru Samir yayi dan shikam ko sama da k'asa zasu had'e bazai ta6a sakin Sulty Aysher ba.







MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: [11/26, 8:51 AM] Zeetty: 💐💐💐💐💐


*MAFARIN LAMARIN*




DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*



©Zeetty




Dis page is Dedicated to *AYSHER* All over the world, *_Sosai nake sonku, Sosai nakeyi daku up up Aysher._*



PAGE 11-12


Samir dayaga duk antashi anbarshi a falon har uwar gayyar wato Aysher, cikin sanyin jiki yakamo hannun yaransa, a hankali yayi musu magana kamar mai rada yace"Kuje kuyima Momy sallama zamu tafi." Afnan da nok'e tare da cewa "Abba mudai kabarmu anan ko kuma a tafi da Momy", dariyar yak'e yayi cikin dauriya domin kuwa gab yake da fashewa da kuka yace" Kuje Afnan, Aslam kama mata hannu Momyn ku zata dawo very soon, kuma saboda school ne kuma exams zaku fara dana barku."

A hankali Aslam yakama hannun kanwarsa suka shige cikin gidan, shi kuma Samir yafita dan jiransu a mota, ya sunkuyar da kansa akan sitiyari yafad'a kogin tunani, Isah ne yafito ya bubbuga masa glass d'in motar ya d'ago da kansa da sauri ya kalleshi, Isah yace keep calm my friend, gasu Aslam nakawo maka, muna jiran takaddar Aysher pls koda text msg ne ta waya kayi mata mun hutar dakai zuwa. Cikin sanyin murya Samir yace"haba Isah kaifa babba ne, kaida zaka dai-daita al-amarin kuma kaine mai ruwa da tsakin ayi sakin?", murmushin takaici Isah yayi kafin yace"ashe kasan da hakan baka dubi girma naba kake dukan k'anwata da azabtar da ita a gaban yaran cikin ta", girgiza kai Isah yayi kafin yakara cewa"Aslam shekarun shi 6 yanzu, Afnan 3½ but yanzu da suka shigo cikin gida cewa sukeyi Momy kitaso mutafi, Abba bazai sake dukan ki ba da zagin ki, kinga ai yadaina tunda muka dawo gidan 'yan gayu, toh Samir tayaya zaka goge wannna hoton a zuciyar yaranku for God sake?, jeka kawai akwai Allah amman wallahi saika saki Aysher." Yana gama fad'in haka yasakai yabar gurin, cikin sanyin jiki Samir ya saka yaranshi a mota yajasu sai Kaduna.


A gida komai ya cakud'ema Samir aikin Office ga hidiman yara, lallai yasara Matar shi Aysher, ashe ba karamin aiki takeyi ba a gidan, shiyake musu wanka break fast, lunch da dinner kuma saidai suyi take away, yara sun dawo marayun dole idan kagansu dole su baka tausayi, Samir yana bama kanshi kwarin gwiwar cewa wannan week end din idan yatafi kano tun friday sai sunday zai dawo shida matar sa, yakira wayarta yafi a kirga baya zuwa da'alamar ta canja layine saboda shi, Ohhh shikam Kabir yakaishi yabaro da muguwar shawarar daya dinga bashi.

Haka al'amuran suka cigaba da tafiya har zuwa ranar juma'a, sai da Samir yajira aka taso 'yan school kafin yashiryasu yadauki hanya zuwa kano, kaitsaye gidan su Aysher yafara tsayawa yatura yaran tare da fad'a musu cewar zaizo anjima shida Baba Mu'azu (Kanin Mahaifinsa).

Aysher taji dad'in ganin yaranta, nan kakar su tafara nan da nan dasu, Maryam ma 'yan matan ABU anzo hutu, dawowanta tak'ara zuwa yayar tata tana sake tuno mata wasu abubuwan data manta dasu wanda akayi agaban ta, kalmar mai *_MAI FARAF K'AFA_* sosai yake 6atawa Aysher ranta idan harta tuno dashi.

Da daddare Baba Mu'azu yazo tare da Samir, Baban Aysher suka fara sallama dashi, bayan yafito tare da dogon gaishe2, Baba Mu'azu yafad'i dalilin zuwan nasu" wato Mal. Muhammadu yaron nan Samir tazo gurina tare da sanar min irin aika-aikar dayayi hak'ik'a ni kaina banso zuwa ba saida yad'aukomin Mahaifiyar sa, dan Allah ayi hakuri adubi zuri'an da Allah yafara basu, Uwata ta koma d'akin ta dan Allah."


Shiru Baba yayi dan yana bala'in jin kunyar Mal.Mu'azu amman hakan bazaisa a fasa hora Samir ba dan haka yafara bama Mu'azu labarin irin gashin ayar da Samir yayima Aysher harda kiranta da yake _MAI FARAR K'AFA_, duka da zagin cin mutumci, sau biyu ina zuwa har gida nayi masa nasiha ashe baya shigarsa, baifasa ba dan haka ni babu abinda zace anan kuyi hak'uri. Shiru Mal Mu'azu yayi kafin yace"Naji takaicin wannan lamari, naji haushi uwata tanada gaskiya wallahi danasan hakane da ban zoba, ni kunya duk ta kamani, sai kaje kanemo abokan naka da suke baka shawara suzo maka bikon matar ka, ba ruwana."
Cikin 6acin rai yayima Alh.Muhammad sallama yatafi kotakan Samir baibi ba.

Alh. Muhammad ma tashi yayi yashige gidan yabar Samir a zaune tagumi yayi shi kadai yasan abinda yakeji cikin heart dinsa.
[11/26, 10:29 AM] Zeetty: Haka Samir yagama hutun karshen makonsa yakoma batare dayasamu had'in kan Aysher ba, har abokansa yakawo mata Aysher tayi musu tass (haka masu sunan suke akwai hakuri, amman fushin su bakyau).

A haka dai har aka shafe wata guda batare da Aysher ta sauko daga dokin nak'in data hauba, tarantse bazata koma ba, dole Samir yad'auko Mahaifiyar sa yakomar da ita kaduna saboda kula da yara.


Ranar wata Asabar Samir yashirya kamar kullum amman wannan karon da takaddar sakin Aysher mai d'auke da saki 1, yatafi kano tare da alwashin zaiyi ma Aysher saki d'aya ko zata sauko su mayar da auren su, idan harta huce kuka yayi sosai kafin ya rubuta saki d'ayan, sosai yakeson Sulty, amman kaddara da son zuciya gashi yarabasu.

Koda yaje batare daya ja dogon lokaci ba yasake bama Aysher hakuri, amman tace tanakan bakanta dan haka yad'auko takadda idon sa sanye da bak'in glass bazaka gane yanayin dayake ciki ba, ya mikawa Aysher farin envalope d'in tare da check na kud'i, kafin yadaure saboda kukan zuciyar da yakeyi ya durk'usa yana cewa" Sulty kigafarceni, ina fatan zaki huce very soon nazo mu mayar da auren mu, ki zauna da yaranki, ga kud'i kirike a hanunki zan aiko miki da motar ki dana siya miki, ki taimaka ki bani sabon number ki koba komai zamuyi zumunci albarkacin su Aslam, ki d'aukeni yaya abokin shawaranki pls."

Cikin sanyin jiki Aysher takarba ta saka masa number tana mika masa wayar tabar falon da sauri saboda wani kuka daya taso mata.


Samir ma ikon Allah ne kawai ya mayar dashi gida kaduna, kamar amafarki yasaki Sulty shi.




Muje zuwa dan yanzu za'afara chakwakiyar.



MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐


*MAFARIN LAMARIN*




DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*



©Zeetty


PAGE 13-14

Cikin sanyin jiki Samir yajawo motar sa tare da barin k'ofar gidan, wayar abokin sa Kabir yakira yake shaida masa cewar yaufa ya saki Sulty, wani ihu Kabir yasaki tare da cewa"Like seriously abokina?", shiru Samir yayi yakasa bashi amsa dan yana tunanin wannan farin cikin da Kabir yakeyi kuma na menene?.


"Hello! Samir kanajina kuwa, da gaske kasaki Aysher?."

"Eh Kabir zanyi maka wasa ne da wannan zancen da ko a mafarki banyi tunanin faruwar shi ba?."

"Kayi hak'uri abokina kad'auki hakan a matsayin jarrabawa, kaidaga hutu ma ya sameka, karabu da jangwam, kaidai Allah baka wadda tafita kawai." Cewar Kabir.


Samir yayi wani huci tare da fesar da iska mai zafi, kamar Kabir yana kallon sa yace"Har'abadah bazan samu kamar Aysher ba, dagaske nayi rashin da bazan ta6a mayarwa ba, nidai fatana tasamu mu dai-daita kafin ta kammala iddar ta mu maida auren mu, bari dai zankira ka idan nasauka zan wuce kaduna ina hanya."


"Okay saika kira Allah tsare."

Wani ihu Kabir yasaki, tare da cewa "Alhamdulillahi yau burina yacika, zan samu gwarzuwan zuciyata, shege harda wani cewa zaka maida ita kafin ta gama idda, ai duk yadda yaza'ayi saina zuge ka baka mayar da ita ba, har sai tagama idda lokacin kuwa tazamo allura cikin ruwa, barin harzarta zuwa na fara kaima mahaifinta gaisuwa, yasan da zamana tun wuri." Zancen da Kabir yakeyi kenan shi kad'ai yana zaune a fine time restaurant, ya mik'e dan barin gurin.


Dole ne na hanzar ta zuwa gidan su Aysher yanzu danyi mata jaje, daman bata san ina daga cikin abokan Samir ba, shiyasa nak'i zuwa bata hak'uri karta ganeni, tsarina ya lalace (Kabir ke fad'in haka cikin zuciyar sa).

```******```
Aysher kuwa tana shiga falon Mahaifiyar ta da takaddar sakin a hannun ta, neman guri tayi tazauna kafin tafara kuka mara sauti.
Umma batayi yunk'urin hanata ba, saida tayi mai isar ta tayi shiru dan kanta, kafin Umma tayi magana"atoh daman shi mutuwar aure ai ciwo ne dashi, banda haka wane irin baki ne da nasiha banyi miki ba?, amman keda Yayan ku da Mahaifinki kuka kafe akan maganar shegen taurin kai irin naki kamar mutanen farko, tare da goyon bayan su, kiyimin shiru gaki ga gidan na." Tana gama fad'in haka tamik'e tabar falon.




MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: [12/1, 8:28 AM] Zeetty: 💐💐💐💐💐


*MAFARIN LAMARIN*




DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*

_Happy Maulud to all 'Darika muslim Brother's & Sister's around the world._


*Ina maka murnan zagayowan watan haihuwarka AHMAD YAKASAI, Allah k'aro shekaru masu albarka.*


_Kucigaba da kasancewa dani domin fuskantar sak'ona danakeson isarwa a wannan labarin, lamarin sosai yana faruwa kamar yadda wata tayimin magana ta Pc kamar haka:-_


*+23480534553.....*
_Assalam Maman Hanan sunana Maman Ayman, dan Allah kici gaba da labarin MAFARIN LAMARI jinshi nakeyi kamar labarina kike bayarwa, sai dai akwai dan banbanci, amman wlh yadda Samir yakecema Aysher mai farar kafa haka mijina da danginsa inaso naji yadda karshen labarin zaizama,muna tare dake ubangiji yakara miki basira, inayinki sosai burina wata rana nazo naganki marubuciyar DABI'A da Mafarin lamarin labaru masu taba zuciya nagode, kiyi saving number na dan Allah, sunana Maman Ayman._


*AMSA*
_Wslm! Nagode Maman Ayman Allah bar zumunci, naji dad'in addu'arki, zanyi saving number ki, In sha Allah idan nagama rubutawa zanyi miki wasu tambayoyi idan badamuwa, Nagode. Maman Hanan ce_



©Zeetty


PAGE 15-16

Bayan Sallah magriba Kabir yazo k'ofar gidan su Aysher, ya faka motar sa a gefe yakulle motar yafito, kai tsaye gurin Mahaifin Aysher ya dosa yayi masa sallama ya amsa, ya durk'usa har k'asa ya gaidashi ya amsa fuska a sake, can Alh. Muhammad yace"Sai dai bangane waye ba.?"

Sosa kai Kabir yayi da mukullin motar sa kafin yasake duk'ar dakai alamar mara gaskiya yace"Baba gaskiya baka sanni ba, nadai zone zan wuce natsaya mugaisa, zantafi a huta lafiya." Yak'arasa fad'a bayan yamik'e dan barin gurin.
Mamakine sosai yakama Alh. Muhammad amman saiya saki fara'a yadinga shima Kabir albarka, sosai Kabir yaji dad'i dan haka yace in sha Allahu zandinga zuwa muna gaisawa Baba idan nazo anguwar nan.

Bakomai yaro nagode sai kazo d'in.

Mota Kabir yakoma yashige zuciyarsa cike da murnan tarkon sa na farko ya d'anu (ma'ana yafara samun sa'a).

Sosai Alh.Muhammad ya kwantar wa da Aysher hankali, dan duk yadda taso da mutuwar auren bayan anyi mata kuma lamarin ya bugeta sosai. A hankali kuma komai ya wuce mata, ta maida hankali wajen kammala iddar ta, gefe guda kuma Isah yafara mata chuku-chukun samun makarantar School of Nursing dake Aminu kano teaching Hospital.

Samir ma yana kiranta lokaci zuwa lokaci dan bayason takura mata da kira, so yake saita huce sosai kafin ya dawo da maganar komen ta, koda kuwa ace tagama iddar tane, sosai Kabir yake k'ara zugashi dan ganin yacire Aysher a ransa, ballantana ma da Samir d'in yasake samun k'arin girma a NNPC d'in aka mayar dashi Abj, sosai Kabir yace dan yarabu da Aysher ne cigaba ma yanzu yafara gani yasa ido. Maganar sa basa samun matsuguni a zuciyar Samir yadda suke shiga haka suke fita, dan yanzu a shirye yake koda kuwa ace zai sake komawa gidan jiya (talauci) indai zaisamu sulty ta dawo zai hak'ura.

Aysher takirashi tayi mishi murnan samun k'arin girman da yayi, yaji dad'in haka sosai godiya yashiga yimata kafin yace"Dan ma bana tare dake Sulty dukiyar nan ai duk na banza ne, kigafarcini dan Allah."

"Komai fa yawuce Abban Aslam, haka Allah ya nufa, ni dai bayan komai ya lafa kataimaka kasamowa su Aslam Uwa dan Allah, Mama ta huta itama dan lokacin hutun ta kenan bazai yiwu tayi fama da jikoki ba tagama daku." Tak'araaa fad'a tana dariya.


Mamakine cike a zuciyar Samir "wato Sulty yana mata maganar komawarta gidan shi, ita kuma tanayi masa maganar yayi aure."

Huci yasaki mai zafi kafin yace"Nagode da shawara, d'auka ba dole bane nagode Sulty sai anjima." Kashe wayar yayi Aysher tabi wayar da kallo "kai Abban Aslam akwai rigima, nikam ai nagama zama dakai (tafad'a a zuciyarta)."

*BAYAN WATA UKU*

Abubuwa dayawa sun faru, ciki harda komawar Samir NNPC na Abj, tubda yasaki Aysher baisake zuwa kano ba, sai dai suna waya sosai da Aysher.
Aysher kuma takammala iddar ta, a dai-dai lokacin da admission d'inta na samun makarantar Nursing yafito, dan haka takira Abban Aslam take sanar mishi akan yayi mata addu'a tafara a sa'a.

Takaici ne ya lullu6eshi (Lallai Sulty bata da tausayi) dan haka yace"Sulty manya, karatu ma kika koma, babu ranar aure kenen ko.?"

"Abban Aslam ai nasan saika rigani aure, dan Allah kadaure kayi zama hakan ba girmanka bane, idan kayi nikuma sai nafara niyya."

"Kedai Sulty wato nacire rai a shigowa layin zawarawa kenan, shikenan, zan d'aure naduba maganarki kodan gujewa fad'awa halaka, dan nikam ba dutse bane, inada lafiya sha'awa dole nayita, dan ma Allah yana kareni, amman zan gud'aure nayi auren kodan ragema kaina zafi, bari idan nakoma gida zankiraki muyi wata shawara."

Sosai Aysher taji haushin maganar Samir, dan gwanine wajen iya sosayya, wato aure zaiyi kuma yadinga

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment