Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bacci yayi gaba dashi, bashi yatashi farkawa ba sai wajen asuba, mamaki yadingayi yadda akayi yadawo gida can kuma yafa tunanin abinda yafaru dashi da kuma abinda yayi na k'arshe a gurin party nan, cak tunanin sa ya tsaya sanda ya tuno da cewar ashe fa wine Ahmad yazuba masa a kofi shida Yaseera suka sha a lokaci guda bayan yaciyar da ita cake itama ta ciyar dashi.

Kai Samir yadafe tare da ambatar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! A fili a hankali yad'aga hannuwansa sama yana fara cewa"astagfirillah ya Allah natuba, Allah karka kamani da laifin da na aikata cikin rashin sani, Allah ya isa tsakanina dake Yaseera bazan ta6a yafe miki ba tun kafin kije gidana burinki yafara cika a kaina, kinfara bani ruwan maye nasha na kwana batare danasan a wani hali nake cikiba, hak'ik'a zaki yabawa aya zak'inta randa kika shigo gidana." Abinda Samir yake ta fad'a kenan cikin zuciyarsa kafin daga bisani yatashi yaje yad'auro alwala yafara Sallah nafilfili tare da rok'on gafarar ubangiji.


*************
Yaseera kuwa kwana sukayi suna aikata bad'ala ita da Johnson, dakyar tasamu ta lalla6eshi yabarta ta tafi dan k'arfe 11:00am za'a d'aura aurenta da Samir (kunji lalacewa Iyayenta kuma basu binciki ina take ba).

A haka ta lalla6a ta tafi gidan mahaifinta dake Anguwar dosa, lokacin anfara cika 'yan d'aurin aure, a haka tayi horn mai gadi ya bud'e mata gate ta kutsa ka motar cikin gidan.

Bawanda ya tambayi daga inda tadawo, a haka har lokacin d'aurin aure yayi babu ango sai abokansa da kawun sa (waliyyin Samir), abokansa suka d'inga kiransa a waya shiru wayar a kashe a haka har aka d'aura auren babu ango babu labarinsa.

Samir dai yana sane da lokacin da za'a d'aura masa aure, yayi kuma alk'awarin cewa bazai halatta ba dan haka nema yakashe wayar sa tunda ya dinga kiran wayar Aysher tak'i d'auka dan tayi fushi "wayyo Sulty meyasa bazaki d'auki wayata na fad'a miki matsalata ba, na sha giya na kwana cikin maye." Samir ya fad'a a fili hawaye yana zubowa daga fuskar sa,gyara zama yayi, yayi kwanciyar sa saboda har yanzu abar bata sakeshi ba (ni kuwa nace rashin sabo).

Sai bayan yayi azahar sannan yashirya lokacin yafarajin dai-dai, dan haka bai saurari gidansu Amarya ba kai tsaye gidan da Aysher ta sauka ya nufa.

Sallama yasa akayi masa da ita, batayi niyyar fitowa ba amman dan batason matar kawunta ta gane akwai matsala tsakanin su yasata tura masa yaransa da sak'on cewar gatanan fitowa. Fitowar Aysher yayi dai-dai da sauke wani nannauyar numfashi sa Samir yayi, kwalliya tayi mai sauk'i dayake Aysher mai kyau ce dan haka tayi kyau d'in ba k'arya, fuska a had'e ta k'araso gurin sa tafara gaidashi ya amsa yana wadata fuskarsa da murmushi tare da cewa"kaina bisa wuya my Sulty, nasan nayi laifi amman ki tsaya kiji dalilina kimin uzuri pls."
Aysher ta cuno baki tare da cewa"Abban Aslam me zance, tunda daga fara hidimar biki kamanta damu jiya sau nawa ina kiran wayarka shiru ba'adauka ba."

Samir yace"yi hak'uri Sulty, kaina bisa wuya wayar tawa tun da zanyi sallah magriba nasa a silent na manta." Daga nan Samir ya kwashe irin aika-aikar da Yaseera tayi masa a gurin party wanda suka kira da sunan walima yak'arasa fad'a yana zubar hawaye yace"Sulty yanzu ace matar da zan aura tunkafin akawota gida na tafara d'uramin kayan maye, gaba-gaba bansan abinda zata aikatamin ba, nikam in sha Allahu tunda sun d'aura ko ruwan gidanta bazan yadda nasha ba Allah ya isa bazan yafe ba."
Dariyane yakama Aysher ganin yadda Samir ya dage yana fad'a iyaka gaskiyar sa, amman ta kanne ta dinga kwantar masa da hankali har ya sauko ya d'aukesu a motar sa dan zuwa gidan danginsa dake kawo inda anan ake hidimar bikin nasa.


Hango Yaseera nayi tana waya tare da cewar Johnson ya shiryo mata k'wayoyi masu k'arfi da hodar iblis yasa a cikin jaka maikyau zata aiko a kar6an mata dan dasu za'a kaita gidan miji sune rayuwarta.

Misalin k'arfe 5:00pm aka kai amarya cikin kwates na ma'aikatar NNPC (nifanare), 'yan kai amarya basu jima da zuwa ba sukayima amarya sallama dan komawa gidajensu bisaga umarnin uban amarya.
Yaseera bayan fitar yan rakiyarta, ta shiga neman wayar angon nata dan yau kwata-kwata bata sameshi ba wayar sa a kashe, so take ta tambayeshi yadda yaji sanda ya shiga wancan duniyar (maye) amman taji shiru har zuwa lokacin da aka kawota gidan, dan haka d'akinta ta shiga ta d'auko akwatin da Johnson yabawa k'awarta lisa Baby ta kawo mata, ta d'auko cocien (hodar iblis) ta fara zuk'a dan a cewar ta lamarin na yau babbane, zataso taji yadda guy d'in nan yake dan he is extremely hand son, dole sai ta had'a da kayan zuwa duniyar sama, tuni ta fita haiyacin ta ta fara buga kanta da gefen gad'on da ta ke kwance dan ta kwana biyu bata zuk'a ba............

_Shin ya rayuwar Samir zata kasance da 'yar maye. Kuniyoni._




Muje zuwa

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/31/2017, 21:35] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐


*MAFARIN LAMARIN*




DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*

__________

________________
```WE ARE HERE TO EDUCATE, MOTIVATE, AND ENTERTAIN YOU READER'S.```
_________

_________________
📚 zaku iya samun littattafam mu a Facebook 👇🏼
Fb.me/
ZAMANIWRITERSASSOCIATION


📩 zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏼
[email protected]


©Zeetty

PAGE 26-27
Samir bashi ya shigo gidan ba sai wajen k'arfe 9:00pm, da kyar Aysher ta lalla6eshi yataho shi kad'ai dan yace dole sai da ita zasu taho, tayi masa alk'awarin zuwa gobe in sha Allah sai su taho da su Aslam gaba d'aya.
Cikin sanyin murya yayi sallama bai damu a amsa masa ba dan yasan mamallakiyar gidan a yanzu balallai bane tasan mahimmancin sa, d'ak'in sa na da ya nufa wanda ya mayar da gadon Aysher d'akin, dan koda yasa aka loda kayan d'akin Aysher dan a kaimata kano bai yadda ya had'a da gadon ba, gad'onsa ya saka mata cikin kayan saboda daman yafi tsada kuma duk shiya zuba musu lokacin da zasu dawo kaduna.

Gefen makekiyar gad'on ya dafe kansa tare da fad'in "Hasbunallahu wani'imal wakil! Allah ka kawomin canji cikin rayuwata, Allah ka tabbatar min da abinda yake alheri a rayuwata." Yana gama wannan addu'ar ya shige band'aki dan watsa ruwa kotakan amaryar sa baibi ba.


Da asubah ya farka yaje ya d'auro alwala dan zuwa masallaci, yafito falo zai fice sai kuma yafasa ya sakai d'akin Aysher nada, wanda yake d'akin Yaseera a yanzu, ya sa hannu ya bud'e cikin sa'a k'ofar a bud'e take, hango amaryar tasa yayi baje a kan gado tana shak'ar bacci gefenta kayan mayenta ne datasha jiya ta barsu babbaje a gurin, sallati Samir yayi cikin zuciyarta kafin ya k'arasa kusa da ita, ko kayan bacci bata saka ba tun kayan da aka kawota dasu jiya je, bubbugata yafarayi tare da fad'in"kitashi lokacin sallah yayi." Inaa sake gyara kwanciyarta tayi, Samir yakasa hak'uri cigaba yayi da bubbugata dakyar ta tashi, cikin alamun har yanzu tana cikin maye tace"No ka barni ba kullum nake sallah ba, yau hutawa zanyi sai gobe, bacci nakeji kazo mukwanta kaima ka hak'ura." Ta k'arasa fad'a tana yunk'urin jawoshi jikinta da sauri Samir ya bar d'akin dan lamarin Amaryar tasa gaba yakeyi bawai baya ba.

******** ********

Wajen k'arfe 10:00am (na safe) Samir yashirya ya fito tsaf, haryakai bak'in k'ofar fita saiyayi wani tunani, juyowa yayi da baya ya koma d'akin Yaseera haryanzu tana kwance amman idanunta biyu, da sauri ta tashi tazauna tana fad'in "D-lovely good morning, shine jiya ka barni ni kad'ai baka dawo da wuri ba, kamanta kazo ka kwashi garar amaryar da aka kawo maka cos you don't care of me, ko baka sona ne?, shine kawai nasha abubuwana nayi mankas saboda namanta da damuwar da kasani ciki jiya, for good sake nasan ba haka akeyima amare ba, d'okinsu akeyi." Samir dai kasa tanka mata yayi, mamaki da al'ajabi duk ya cikashi, dan bai zaci lamarin Yaseera kai haka ba, girgiza kai yayi kawai yasa kai ya fice dan tunawa da alk'awarin sa da Aysher kuma yau zata koma kano saboda karatu.

Yad'auko Aysher da yaransa ya kawosu gidan, kar6a mai kyau Yaseera tayi musu tare da ajiye musu kayan biki dangin su dubulan da alkaki drinks da cake, sosai ta karb'esu hannu bibbiyu har Aysher na mamaki kodai Samir sharri yakeyi mata dan baya sonta, amman kuma ai Abban Aslam bazai mata k'arya ba, haka dai Aysher tayita wad'annan tunanin har lokacin tafiyarta tayi, tayima Yaseera sallama Samir yatafi rakata tasha tahau mota, dan tayi sallama da gidan kawunta. Dakyar yaran suka rabu da ita wato Aslam da Afnan shi kansa Samir d'in kawai k'arfin hali yayi dan yanzu yak'ara tabbatarwa da cewa yayi rashin Sulty mace tagari.

********* *********

Haka al'amarin zaman nasu ya kasan ce tsakanin Samir da Yaseera, bawani zaman lafiya, Yaseera bata iya girki ba, kullum Samir shikenan wajen yawo a gida jen sai da abinci, baya dawowa gida sai bayan k'arfe 9:00pm, dan haka Yaseera har yanzu takasa samun kan D-lovely d'inta, shawara tayi dan haka takira k'awarta saboda masifar sha'awar da yake damun ta, shawara k'awarta ta bata, sosai Yaseera tayi na'am da wad'annan shawaran.
Gidan su takira a waya cewar a turo mata 'yar aikin gidan su zasu tayata aikin abinci, batare da 6ata lokaci ba aka turo mata su, ta basu odar girkama Samir abincin gargajiya tuwon shinkafa miyar agushi, wanda yaji naman tantak'washi da tsokar nama, gefe guda sun had'a masa lafiyayyen zo6o wanda aka sanya mashi cucumber, cikin mintuna kad'an suka kammala aka shirta a dining table, nan da nan ta sallamesu, fitar su ba wuya Yaseera ta d'auko wata k'waya mai bala'in k'arfi guda d'aya ta nik'a yayi laushi ta watsa cikin kofin da zo6on yake ciki, ko ita bata shan wannan k'wayar saita rabashi 4, amman yanzu ta jefama Samir guda 1, akan cewa ya shanye.




Burin Yaseera yana cika?

Mezai faru idan Samir ya kora zo6on nan?

Ku kasance dani


MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/31/2017, 21:35] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐


*MAFARIN LAMARIN*

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*

__________

________________
```WE ARE HERE TO EDUCATE, MOTIVATE, AND ENTERTAIN YOU READER'S.```
_________

_________________
📚 zaku iya samun littattafam mu a Facebook 👇🏼
Fb.me/
ZAMANIWRITERSASSOCIATION

📩 zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏼
[email protected]

©Zeetty

PAGE 28-29
Samir yau yadawo gida da wuri, kuma a gajiye dan haka kai tsaye ya fara wucewa side d'inshi, ruwa yafara watsama jikinsa kafin ya fito falo ya zauna, kamar yadda yakeyi kullum dan kallon labarai.
Su Aslam suna d'akinsu sunyi bacci tare da mai kula da su da Samir ya d'auko, ba su da wata matsala da Yaseera, saidai bata basu kulawa amman tana jansu a jiki bata musu mugunta.

Cikin salon rausayar ta Yaseera ta k'araso gurinshi, tana karairaya da yauk'i, kan cinyar shi ta zauna tare da rataye hannuwanta a wuyansa, cikin muryan shagwa6a tafara magana da cewa"D-lovely kayafemin duk abinda nakeyi maka, nasan cewa auren nan anyimaka ne bawai dan kana sona ba, amman meyasa bazaka iya taimakawa mahaifina ba akan abinda yanema, wato shiryuwata duk da nasan Allah ke shiryar da bawansa, amman wallahi D-lovely nima inaso nadaina 6atamin ran da kakeyi da daina kulawa dani shine yasani nake shan kayan maye a gidan ka, saboda na manta da wasu abubuwan, amman dan Allah D-lovely kataimaki rayuwata gurin ganin na shiryu saboda na zamowa yarana uwa tagari." Tak'arasa fad'a tana sheshshek'ar kuka.

Jikin Samir yayi sanyi sosai, gashi baya son yaji mace tana kuka dan haka yace"is Okay ya wuce, ki nutsu kigyara rayuwarki da sauran lokacin da yarage miki tashi ki je ki kwanta."

Cikin sharen hawaye Yaseera tace"In sha Allah D-lovely nagode, but yau inason na baka mamaki dan haka nasa an shirya maka girki, masu aikin gidan mu da kansu sukazo nasa sukayi maka abincin gargajiya so pls zo muje kaci, nima very soon zan fara girka maka da kaina, but for the first time a tarihin auren mu yau zomuje kaci girkin gidan ka."

Mamakine yakama Samir, bayason musanta mata tunda sosai shirin take nema, kuma gashi yunwar yakeji daman tunaninsa yasha tea ya kwanta, amman bari yaje yaci abincin da Yaseera tasa aka shirya masa.......
"Come on! D-lovely taso muje pls, don't say no." Yaseera ta katseshi da fad'in haka tare da kamo hanun sa, haka yamik'e yana biye da ita har dining area.
Zaman yayi ta fara zuba masa abincin tuwo da miya, sosai Samir yaji dad'in ganin abincin saboda yakwana biyu baici ba, dan haka ya zage ya narka, saida yaseera ta lura yaci abincin sosai kafin ta zuba masa had'in zo6o, nan ma haka ya dinga sha kamar ba gobe dan yanason zo6o sosai cikin lemukan gargajiya, ya na cikin shan kofin zo6o na uku da Yaseera taketa zuba masa yana kowara, nan labari ya canja gaba d'aya yajisa cikin wata duniyar, yafita daga haiyacinsa ga6a d'aya, Yaseera ya hango ta juye masa zuwa kammanin Aysher, subhanallah da sauri ya jawota kamar mayunwacin zaki, yafara aika mata da sak'on kiss yake aika mata dashi ta ko ina, dayake Yaseera a buk'ace take kuma gata gwana ce sosai, nan ta k'ara rikita Samir da nata salon soyayyar, gaba d'aya suka afka cikin duniyar masoya da kyar Samir ya yunk'ura ya d'auketa sai Bed room d'in sa.
_Asuba tagari._

Haka Yaseera taci gaba da amfani da k'wayar maye tana afkawa Samir, tana kuma samun damar yana biya mata buk'ata yadda takeso, batare da yana cikin hayyacin sa ba takashe wayoyinsa, yaran sa ita ke kaisu School ta d'auko su, ko kuma ta tura mai aiki ta taho da su Napep, abokan aikin sa har gida sukazo nemansa, tace musu yatafi k'auyensu kuma babu network, kowa mamakin hakan yakeyi saboda rashin fad'arsa a gurin aiki abashi izini, gashi Samir yana bin doka, tafe dai tafe dai har aka kwashe sati guda ciff Yaseera ta mayar da Samir d'an maye bashi da aiki saidai ta bulbula masa k'waya cikin lemo yasha daga nan sai bacci, sosai Yaseera take sashi a gaba tana masa dariya gami da cewa"kaima kaji yadda mukeji shege, har kana cewa ka tsani halaiyata gashi a sannu nasaka ciki, kullum cikin maye."
Samir baya iya budar baki yace mata uffan, saboda k'wayar tayi masa k'arfi gashi kullum take bashi guda ya shanye, wanda ita kwatarsa take sha.

************

Gefe guda Kabir yafara samun kan Aysher, dan yanzu idan yaje gidan tana fitowa idan ya aika suyi zance, har labarin yaranta tabashi, dan bai nuna mata yasan mijinta ba, ballantana yaran da suka haifa.

A hakan dai harya samu yashawo kan Aysher ta amince ya kawo sadakin sa, bisa taimakon malamin sa dayayi masa aiki akan haka, kafin akawo sadakin Aysher tayita kiran wayar Samir tasanar masa amman wayar sa akashe, dan haka bata wani damu ba dan yanzu zuciyarta soyayyar kabir ne cike a cikinta.


Muje zuwa


MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/31/2017, 21:35] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐


*MAFARIN LAMARIN*

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*
________
______________
```WE ARE HERE TO EDUCATE, MOTIVATE,AND ENTERTAIN OUR READER'S.```

_________
______________

©Zeetty
📚zaku iya samun littattafan mu a face book 👇🏻
Fb.me/
ZAMANIWRITERSASSOCIATION


📩zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏻
[email protected]

*MY BEAUTY QUEEN HAKIKA INA ALFAHARI DAKE, ALLAH BAR ZUMUNCI.*

PAGE 30-31
Samir yana cikin wannan hali, kwatsam Mama (mahaifiyar sa) ta sauka a gidan saboda jin shirun yayi yawa kuma gashi bata samunshi a waya, bata kuma da number Yaseera. Sanda mama tazo gidan bata samu Yaseera ba ta tafi gurin Johnson suyi sallama zai koma America, kuma tana sauri tabar k'ofar d'akin a bud'e, sallama Mama ta dingayi taji shiru ba'a amsa mata ba gashi yaran duk sun tafi Makaranta, Baba mai aiki ta tafi tahowa dasu, cikin sa'a Mama ta danna kanta d'akin Samir na da wanda yazama na Yaseera a yanzu, sallama tadingayi taji shiru, hango Samir tayi kwance akan gado yanata shek'a bacci, da sauri Mama tak'arasa tana bubbuga sa tare da tambayarsa ko lafiya? Sam Samir baisan tanayi ba, jijjigashi Mama takeyi shiru gashi dai a zahiri yana numfashi amman babu abinda yake iya motsawa a jikin sa. Ihu mai k'arfi Mama ta saki, kafin tafice daga d'akin da sauri wajen kwates d'in ta nufa gidan dake kusa da na Samir taje tafara bubbuga k'ofar da k'arfi, kana kallonta kasan cewar a rikice take, Emanuel yak'araso ya bud'e k'ofar cikin gur6atacciyar hausar shi yafara tambaya"Mama lafiya kuwa (dayake yasanta d'an zaman da tayi a gidan Samir din)."

Kuka Mama tafarayi tana nuna masa k'ofar gidan Samir gami da cewa"Samir gashi can bashi da lafiya baisan inda kansa yake ba, mara bansa da gawa numfashi." Duk da cewar Emanuel bai fahimci abinda take nufi duka ba, amman yad'an gane wasu dan haka yace"Jesus, what is wrong with him?, kwana biyu baya zuwa office, i call him but his phone is switch off, na tambayi Madam tace min he is travel, ashe yadawo babu lafiya, muje Mama barin fito da mota, just now am back, na zo d'aukar wasu taddune daga office."

Ita dai Mama dayake ba fahimtar abinda yake cewa takeyi ba, dan gaba d'aya a rikice take, ko ina a jikinta rawa yakeyi, da sauri ta koma gidan Samir d'in ta shiga d'akin, tayi yunk'urin d'aukar sa amman inaa, bazata iya ba dan haka ta jira har Emanuel ya shigo yana fad'in"excuse!" Mama da sauri tafito ta nuna masa d'akin da Samir yake kwance, kasan cewar Emanuel k'atoton inyamuri maji k'arfi dan haka ya cicci6i Samir yasashi a mota.

*********
Suna isa asibitin dake cikin kwates din, kai tsaye aka wuce da Samir A & E (Accident and emergency) likitoci suka taru akansa dan gano abinda yake damunsa, jikinsu yayi sanyi matuk'a, sanda suka gano musabbabin matsalar tashi, dan haka Dr. Hussain yafito yana sharce gumin dake fuskar sa, ya k'araso ya samu su Emanuel wanda yakasa komawa Office, bayan yakira ya shaida musu abinda ke faruwa. Dr. Hussain yace"kubiyoni zuwa office, pls inason ganin wani na kusa dashi."

Da sauri Mama da Ema suka k'arasa office d'in kowa zuciyarsa cike da son jin abinda yake damun Samir.

Dubansu Likita yayi kafin ya sauke idonsa akan Mama ya k'ura mata ido, kafin yace"daga gani kece Mahaifiyar wannan mara lafiyan, shin zan iya fad'ar matsalarsa a gaban wannan ko kuma yabamu guri?".

"Zaka iya likita, da badan shiba, bansan yazanyi na kawoshi asibiti ba kafad'a kawai ba matsala." Cewar Mama.

Likita yace"wato Mama a zahirin gaskiya binciken da mukayi mungano cewar Samir yasha magungunar maye masu matuk'ar k'arfi, wanda sune sanadiyyar jefashi cikin wannan halin da yake ciki, wanda bamu da tabbas d'in cewar k'wakwalwarsa tanada cikakken lafiya a yanzu, har sai ya farfad'o k'wayar ta sakeshi, wanda zaikai nan da wasu kwanaki, sai kuyita addu'a kar ya samu ta6in hankali, wanda warkewarsa zaiyi wahala sai wani ikon Allah."
Kuka Mama tafara gami da salati tana fad'in"wallahi likita d'ana ba mashayi bane sai dai idan wannan matar tashi ce ta sashi a wannan muguwar hanyar, dan tun farko abinda yasa ya guji aurenta kenan, 'yar maye ce sosai, ya Allah kabama Samir lafiya." Sosai Mama take kuka abin tausayi.

Emanuel wanda bai gama fahimtar bayanin likita gaba d'aya ba, dan da hausa aka yima Mama bayani, sai da yasake tambayar likita cikin harshen turanci yayi masa bayani sosai, nan shima ya shiga cikin tashin hankali tare da fatan Allah yabashi lafiya. A asibitin Ema yabar Mama ya koma office tare da alk'awarin zai fad'awa Yaseera dan suzo asibitin kar hankalinsu yatashi.

A6angaren Yaseera kuwa, tariga su Baba dawowa gida dan haka ta shigo falon da 'yar guntuwar wak'ar ta, bata damu da ganin gidan a bud'e ba, kasancewar basu da wani matsalar 6arayi a kwates d'in, kai tsaye d'akin ta, ta nufa inda Samir yake a kwance wayam tagani sanda takai kallonta kan gadon ta, taga babu mijinta kwance a gurin. A rud'e ta fice daga falon, sukayi kici6is da Anatu (matar Emanuel) zata shigo gidanta, da sauri Ana ta tareta da cewa"thank God! Kadawo, Ema yanata kiran wayana, yana tambayana ko kadawo?, nazo three times kenan."

"Ke Anatu kin cikamin kunne, fad'amin meye yakawoki gurina dan inada matsalar da tafi zuwanki yanzu." Yaseera yafad'a cikin muryar fad'a.

"Sorry Madam, Ema yace mijinka ba lafiya, yana cikin Hospital d'in asibitin nan so yace ya fad'a maka, kar hankalinka ya tashi." Ana tana gama fad'in haka tabar k'ofar falon Yaseera.

A lokacin kuma Baba tadawo daga d'auko su Aslam daga school.

Kai Yaseera ta dafe tare da fad'in"Oh my God! Waye yazo ya ga D-lovely cikin wannan halin har yakaishi asibiti? Kodai Emanuel ne?". Dan haka a fili Yaseera tace"sai naci kutmar uban Emanuel, zai fad'amin dalilinsa na shigomin gida bama nan."

Baba kuwa tanaji Yaseera ta ambaci hakan ta fara fad'in"sai hak'uri Uwar d'akina, labarin dana samu a kwates d'innan shine, shida Anatu yara hud'u suka haifa yanzu haka, kuma har yanzu ba suyi aure ba, wai sai nan da shekara guda mai zuwa, dan haka kinga irin wad'an nan k'abilun balallai bane susan darajar aure, yara 4 fa Uwar d'akina, zaman zina sukeyi wanda Allah ya tsinewa mai...."

"Ke rufemin baki, tambayarki nayi? Duk kin cikani da surutu to dan uban babanki banason ji ba kisan tashin hankalin da nake ciki ba, ki wuce ki cire musu uniform mu tafi asibiti D-lovely ba lafiya."

Cikin sauri Baba ta ja hannun su Aslam zuwa d'akinsu dan canja musu kaya, bataji haushin zagin da Yaseera tayi mata ba dan kuwa tasaba da hakan, ballan tana yau ya hadun mata da ciwon miji.


A hanyarsu ta zuwa asibiti Yaseera takira wayar Mahaifinta cikin Kuka take sanar masa Samir bashi da lafiya, yana asibiti wasu ne suka kawoshi gida yau da asuba cikin yanayi na maye.............



Muje zuwa


MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
[12/31/2017, 21:37] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐


*MAFARIN LAMARIN*

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*
________
______________
```WE ARE HERE TO EDUCATE, MOTIVATE,AND ENTERTAIN OUR READER'S.```

_________
______________

©Zeetty
📚zaku iya samun littattafan mu a face book 👇🏻
Fb.me/
ZAMANIWRITERSASSOCIATION


📩zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏻
[email protected]

PAGE 32-33
Kuka sosai Yaseera taci gaba dayi a cikin motar, tana driving tana face hanci, Baba mai aiki fad'i takeyi sai hak'uri Uwar d'akina Allah yasakama uban gida na.

Cikin wannan halin suka k'atasa asibitin, idan kaga Yaseera saika rantse da Allah bata da wani masaniyya game da halin da Samir ya tsinci kansa a ciki, da tambaya suka k'arasa d'akin da aka kwantar da Samir din.

Da gudu Yaseera tak'arasa gadon da yake kwance kamar gawa, ta kwanta akan kirjinsa tana kuka sosai mai had'e sheshshek'a tare da fad'in"Allah yasaka maka D-lovely, duk mugun daya aikata maka hakan Allah ya baiyanashi, bazamu ta6a yafe masa ba."

Cikin wannan halin Mahaifinta yazo ya risketa, tare da wasu ma'aikatan NNPC gumi ne ya fara tsatstsafowa daga fuskar Alh. Auwal Mataimaki yasa hankici yana sharewa, kallo d'aya yayima Samir yaji tausayin shi yakamasa, tabbas an zalunceshi, shi ba mai shaye-shaye ba an mayar da shi d'an maye k'arfi da yaji, dan sunje ofishin likita yayi musu bayanin duk abinda yake faruwa akan Samir d'in.

Goge k'wallar da ya fara zubowa daga idanuwansa yayi na tsabar tausayama Samir, kafin yafara magana da cewa"Allah yasaka maka Samir Yaron kirki, yanzu daga nan ofishin 'yan sanda zan wuce, zamu kai report dan a fara bincike akan wad'anda suka aikata masa wannan mugun aikin, tabbas ba zamu yafe musu ba ko sassauta musu akan hukuncin da za'ayi musu ba, ko da ace munada kusanci mai k'arfi tsakaninmu.....





Kululululu cikin Yaseera ya kad'a, ta sake fashewa da wani matsanancin kuka wannan na tausayama kanta ne idan asirinta ya tonu.

_Ayi hakuri da wannan._


Muje zuwa


MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[1/2, 15:53] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐


*MAFARIN LAMARIN*

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*
________
______________
```WE ARE HERE TO EDUCATE, MOTIVATE,AND ENTERTAIN OUR READER'S.```

_________
______________

©Zeetty
📚zaku iya samun littattafan mu a face book 👇🏻
Fb.me/
ZAMANIWRITERSASSOCIATION


📩zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏻
[email protected]


*Godiya ga duk 'yan k'ungiyata Zamani writer's association.*

*_Zauren littattafan Hausa group._*
*_Duniyar Marubuta group._*
*_Hausa novels

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment