Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwana d'aki d'aya da matar wani kishin sa wanda bata ta6a jinsa ba sai a ranar taji yasauka a Heart d'inta, dan haka a hankali tace"Toh Abban Aslam saika kira, Allah taimaka."

"Ameen Sulty nagode."


*YASEERA*
Yarinya ce yar gata a gurin iyayenta Alh. Auwal Matamaki da Matar sa Dr.Salma, ita kad'aice 'ya mace cikin su uku da Allah yabama iyayen ta, kuma itace k'arama, yarinyace marajin magana, a turai tayi karatu tun daga Secondry har jami'a, babanta babba ne a NNPC na Abj, Mahaifiyar ta kuma lecturer ce a jami'ar gwagwalada dake Abj.
[12/1, 10:36 AM] Zeetty: Dawowar Yaseera gida tadawo dawasu miyagun halaye na shaye-shaye da bin maza, dan tun tana shekara 14 takware da mu'amala da maza sanadiyyar fyad'e da wani bature yayi mata, shikenan Yaseera tazama idan ba'ayi mata ba batajin dad'i, kafin daga baya tagano wannan rayuwar tafi komai dad'i, a hankali takoyi shan kayan maye harda giya da hodar iblis(cocaine), har allura take yima kanta, a can turai (America) tayi alk'awarin aure da wani bature d'an asalin k'asar america, har zobe yabata itama tabashi kowa yasaka a hanun shi.

Dawowar ta gida bayan kammala karatunta Mahaifinta ya girgiza da ganin wannan al'amari na halayen d'iyarshi guda d'aya tilo Yaseera, hankalin sa baisake tashi ba saida ta sanar mishi alk'awarin auren da sukayi da johnson. Sosai hankalin Alh. Auwal mataimaki yatashi dajin haka, dan haka a ranar da aka dawo da Samir k'ark'ashin sa a Abj sati biyu yad'auka yana lura da d'abi'un sa, a hankali yagano yanada halaye masu kyau, dan haka yabinciki Samir ina matarshi, dan binciken dayasa akayi mashi akan Samir d'in anshaida masa bashi da mata. Samir ya sanar mishi cewa"sun rabu, bisa ga wani kaddara amman yanasaka ran dawowarta komin daren dad'ewa."

Alh. Auwal bai tsananta tambayar shi ba, saima fatan ganin lokacin dayayima Samir, kafin yabashi labarin yarinyar sa Yaseera, da rayuwar datayi a turai da sabuwar halayyar data koya acan, yak'ara dacewa "na yaba da halayenka Samir shiyasa kakai matsayin nan a d'an shekarun ka dafara aiki, kanada hakaye masu kyau dan sosai nayi bincike a kanka, yanzu haka taimakona zakayi, kayi jihadi Allah zaibaka lada wajen auren ta, nasan idan ta aure ka zaka taimaka wajen nutsar min da ita, hakan bazai hanani idan katashi dawowa da uwar 'ya'yanka ba nasa hannu wajen zuwa maka bikon ta, dan Allah kataimakamin nayi tunanin aurar da Yaseera a wannan lokacin shine zai kautarmin ita daga fad'awa auren k'asurgumin k'aton arnen nan bature wato Johnson. Ina jinka meye ra'ayinka.?"

Gumi sosai Samir yafara sharewa kafin yace"Naji buk'atarka 'yalla6ai, kabani lokaci zanje nayi shawara nan da kwana biyu zakajini."

"Dan Allah kayi shawara maikyau, nagode saina jika."

Yamik'e tare da ficewa daga office d'in Alh. Auwal d'in.


Muje zuwa

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐


*MAFARIN LAMARIN*




DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*

*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*[email protected]*

©Zeetty

PAGE 17-18

Da daddare Samir yakira wayan Aysher yake shaida mata yadda sukayi da uban gidan sa, bai 6oye mata komai ba, dan haka jikin Aysher yayi sanyi tana tunanin wacce Abban Aslam zaikawo gidan sa, a matsayin Uwar 'ya'yansa karo na biyu shin mai irin wannan halayen da d'abi'un ta cancanta tabama yaranta tarbiyya kuwa.? (Tambayar da Aysher take yima kanta kenan a cikin zuciyar ta).


"Hello! Aysher kinajina kuwa.?" A sanyaye tabashi amsa da cewa"Inajinka Abban Aslam wallahi jikina ne yayi sanyi danaji halayen Yaseera, amman da farko harna fara murna da farin cikin su Aslam zasu samu sabuwar uwa ashe abin ba haka bane."

Samir yace"toh yaza'ayi Aysher nida aka taimakawa, dan ni akaran kaina bazan iya samo matar aure a karo na biyu ba gaskiya, dan haka zan amince da Yaseeran kawai tunda alfarma yanema da kuma neman shiriyar ta da gudun fad'awa auren kafuri, idan har ta shiryu ta dalilina ai inada lada." Ya numfasa yana jiran yaji ko Aysher zatace wani abu amman yajita shiru dan haka yaci gaba da cewa"ai duk laifinki ne, Allah ma munayi masa laifi ya yafe mana ballantana d'an adam, na baki hak'uri Aysher kink'i hak'ura daga k'arshe ma dan tsabar takaici wai kinkoma makaranta, hmm duk laifin Isah ne amman bakomai, Allah yasa mudace."


"Ameen thumma ameen, bakomai naji bayanin ka, ka'amince masa kawai Allah yasa hakan shine mafi alheri, lallai zamuzo kaduna muna 'yan d'aukar amarya, abani kwangilar had'a kayan aure." (Aysher tafad'i haka cikin dauriya da raha domin 6oye damuwa daya ziyarci zuciyarta na wucin gadi.)

"Mtswww kinji matsalar ki ba, wato ko irin kishin nan bakyayi alamar kindena sona, toh sai anjima zankira ki idan naje gidan, dan munyi waya da Mahaifin ta yace duk shawarar dana yanke naje gida na sameshi, idan har na amince sai a kirata mugaisa dan haka sai kinjini."


A sanyaye Aysher tace"toh Allah yakaimu saika kira d'in, nagode Abban Aslam." Suka katse wayar.

*******

Wata kyakkyawar matashiyar budurwa na hango, tana kwance akan wani makeken gado hanun ta rik'e da waya tana chat da saurayinta Johnson, tana fad'a mishi yadda tayi missing d'inshi sosai. Gefen ta roba ne mai d'auke da lemon Fanta wanda tayi mishi sirki da codein tare da k'wayar tramol tana shansa a hankali, wani sanyin dad'i ne yake ziyartar zuciyar ta yayin da take shan wannan fantan (haka take yi, koda yaushe friedge d'in dake d'akin ta baya rabo da lemu ka, wanda akayi masa sirki da sinadarun kayan maye dangin su giya, da k'wayoyi, har jikin ta yasaba da shansu, ko da tasha baya sakata maye, batare da sanin iyayen ta ba). Muryan yaseera harya bud'e tsabar shaye-shaye.

Da daddare Samir ya dira gidan su Alh. Auwal Mataimaki, kai tsaye akayi masa masauk'i a falon bak'i. Mintuna kad'an saiga Alh. Auwal yafito yana duba agogon hanun sa, hannu yabama Samir sugaisa, amman Samir yakasa mik'a masa, durk'usawa yayi yana gaisheshi ya amsa fuska d'auke da fara'a"lafiya lau Samir, ya gidan da yara?"

"Duk lafiya Alhamdulillah."

"Masha Allahu, Malam Samir lallai kacika alk'awari, ya ake ciki?, Allah yasa muji alheri."

Kai Samir yasake duk'arwa k'asa kafin yace"eh yalla6ai bakomai na amince Allah sanya mana alheri."

Fara'ar dake d'auke a fuskar Alh. Auwal bazai misaltu ba fad'i yake"Alhamdulillahi Samir nagode Allah yayi maka albarka, bana buk'atar komai daga gurin ka sai sadaki, nan da sati biyu masu zuwa za'a d'aura aure saika sanar da manyan ka, barin shiga na turo maka ita."

Kafin Samir ya baci amsa Alh. Auwal ya mik'e tare da ficewa daga d'akin, yana sa6a babban rigar sa.


Samir harya gaji da zama a falon saboda jimawa da yayi a zaune, ita kuma bata shigo ba, ya d'auki ruwan da aka kawo masa tare da lemo, ya zuba ruwan a kofi yakafa a bakin sa yafara sha, wani kamshi yaji yafara ziyarta hancin sa kafin ya hangota tashigo falon, jikin ta d'auke da wasu matsatstsun riga da siket mai lak'abin (Jahannama ga fasinja), k'afar ta kuwa d'auke yake da wani dogon takalmi mai tsini, siririya ce sosai Yaseera.

Ta k'araso cikin salon yauk'in ta idanuwan ta sunakan Samir, _kai wannan guy d'in yayi bala'in had'uwa, zan aure shi kafin na auri Johnson, shi yana Nigeri'a, Johnson yana Amerika._ (Cikin zuciyar ta Yaseera take fad'in haka).

"Hi! My dear watz up?."

Samir daya tsaya yana k'are mata kallo, zuciyar sa cike da takaicin irin shigar rashin mutuncin dake jikin ta, shi sam tun shigowar ta kallo d'aya yayi mata, batayi masa ba dan baza'a had'ata da Sulty d'inshi ba.

A firgice ya juyo dan jin an hure masa ido.

Cikin gabjejiyar muryar ta tace"haba D-lovely inayi maka magana kayi shiru why, Dad yace zamuyi aure nan da 2 weeks dan haka i can't wait to see dat day, saboda sosai kayimin dan haka zan shayar dakai zumar da baka ta6a shan irin sa ba, me kace.?"

Shiru yayi mamaki yana sake rufe shi, jiyayi ta kawo masa wani irin runguma da sauri ya mik'e daga gurin, yana fad'in"subhanallah Yaseera meye haka, kanki d'aya kuwa?."

"Toh D-lovely inason na nuna maka yadda nake sonka ne, karka bani kunya mana kanayin abu kamar ba wayayye ba, meyasa kazo mud'anyi romancing before katafi, karage zafi."

"A'a nikam natafi sai na sake dawowa, daga ganin ki bakya cikin hayyacin ki."

Yaseera tace"Okay D-lovely sai kadawo d'in, tashi d'aya naji na kamu da wani irin soyayyar ka gami da zazzafar sha'awar ka, nifa yanzu codien na sha kwalba d'aya kawai D-lovely kaga ai bansha da yawa ba."


"Uhmmm baki sha ba kam, sai nazo bye."

Samir bai jira cewar ta ba yafice a falon da gudu, dan ganin tana shirin kawo masa wani runguman.


Da daddare yakira Aysher a waya, tana d'auka yafara magana wanda daga jinsa tasan yana cikin damuwa yace"Sulty kinga abinda kika jawomin ko?, wai yau da 'yar codien nayi gamo matar da zan aure, totally batayimin ba k'afuwan ta kamar marad'in acca, jiki kamar sanda, baki ga abinda tayimin ba daga zuwa na (kwashe labarin abinda yafaru a gamuwar sa da Yaseera yayi, yafad'ama Aysher)."


Tausayinsa sosai ne yakama Aysher bayan yagama bata labari a hankali tace"kayi hak'uri kawai Abban Aslam kataimaka masa waje gyara masa tarbiyarta kamar yadda yanema Allah zai dafa maka, in sha Allah zaka samu lada."


Cikin murya mai rauni Samir yace"daman nasan haka zakice, bazaki ta6a jin haushin hakan ba, bakomai nagode wallahi da ace ban amince masa ba tun farko, wallahi da na fasa, shiyasa yayimin dabaran cewa sai na fara amince masa kafin naganta, saboda yasan halin 'yar tasa bakomai sai da safe."
Diff ya kashe wayar baijira cewar Aysher ba.



Muje zuwa.....



MAMAN HANAN
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: [12/6, 12:43 PM] Zeetty: 💐💐💐💐💐


*MAFARIN LAMARIN*




DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*

*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*[email protected]*

©Zeetty

🍀🍀🍀 *SABODA ABOTA* 🍀🍀🍀
Na
Fatimah Muhammad (Ummancy)
*_Hak'ik'a na jinjinama wannan hazik'ar marubuciyar tamu, wanda tayi mana bayani akan yadda mu'amala yake kasancewa tsakanin Mace da Namiji, Matan aure masu zuwa gurin aiki, dan Allah kuyi amfani da darasin da kuka karanta cikin littafin Ummancy, Up up Fatima, sai munjiki a sabon littafin ki Allah k'ara basira._*

PAGE 19-20
A wannan daren Aysher kasa rintsawa tayi, dan haka ta d'auro Allah tafara jero nafila dan neman za6in Allah tsakanin ta da Samir.

Washe gari bayan Samir yagama breakfast kafin yatafi office yake shaidawa mahaifiyar shi maganar Yaseera 'yar gidan ogan shi, sai dai ya 6oye mata mugayen d'abi'unta da kuma dalilin dayasa mai gidan shi yabashi auren ta.

Sosai taji dad'in maganar dan itama rashin mata kusa da d'an nata yana damunta, dan haka tashiga jero addu'o'i tare da sanyama lamarin Alheri.
Shi dai Samir fuska ya k'ara had'awa, ko amsa addu'ar nata bayayi, ya kai duban sa kan yaranshi yace"Aslam da Afra ku shirya tunda kuna hutu idan nadawo daga office mu wuce kano."

Ihun murna yaran suka shigayi da tsalle suna fad'in "yeeh! Yau zamuga Momy da Mama."
Cikin ran Samir tausayin yaran sa ne yasake kamashi, _Aysher hakkina nida yaran nan idan yatashi tambayarki bazakiji dad'i ba._ (Samir ke fad'in haka cikin zuciyarshi).

Mama ce ta katse mishi tunanin shi da cewa"Samir tafiyar dare zakayi da yara k'anana haka?."

Ya bata amsa yana tafiya bayan yad'auki briefcase d'inshi"a'a Mama yau bani da aiki sosai, dawuri zandawo mutafi kema idan zakije saiki shirya mutafi tare."

"Ai kuwa zanje, ka saukeni Garin Malam, daga nan saina sanar musu da biki."

"A'a Mama dan Allah karkiyi wani gayya tunda bana farko bane, uban amaryan da kanshi yace babu wani taron biki (yafad'i hakane saboda bayason azo aga kalar amaryan tashi, abinka da surutun mutanan k'auye 'yan garinmu lol)."

Mama tace"toh saika dawo dai Allah tsare."

"Amin." Ya amsa tare da ficewa daga falon.

``` *******```
Samir sun shiga cikin garin kano ana kiran sallah magriba, domin saida ya fara tsayawa a hanya ya sauke Mama a garin Malam (wani d'an k'auye ne farkon shiga kano, kafin a k'arasa kura).

Su Aslam yatura cikin gidan Kakan ninsa (gidan su Aysher), shi kuma yayi saurin d'aura alwala domin shiga masallacin dake k'ofar gidan su Aysher, ya samu jam'in sallar magriba da akeyi.

Da gudu yaran suka shiga gidan, suka tarar Aysher da Mama suna Sallah, dan haka neman guri sukayi a falon suka zauna, Mama ce tafara idar wa dan haka kallon su tayi tana murmurshi tace"A'a maigida takobi, saukar yaushe a garin namu?." Gaisheta Aslam yafarayi kafin yace mata"yanzu mukazo Daddy ne ya kawomu."
Mama ta mayar da kallonta kan Afra tace"kishiyata ko gaisuwa baby? Sai kumburo baki kikeyi."

Afra cikin shagwa6a tace"ba kink'i kulani ba, sai Aslam kike kulawa shikenan ai bari Momy ta idar da sallah nasan zata kulani."

Baki Mama ta rik'e tana fad'in "ohh ni na shigesu, toh kiyi hak'uri kinji kishiya."

Dariya Aysher taketayi musu yaran sunbata mamaki, rabon da tagansu wata biyu kenan, sun k'ara girma sosai.

"Aslam da Afra drama kenan, kunzo zaku takura Mamana da surutu ko?." Cewar Aysher

Aslam ne yafara gaisheta kafin Afra, k'arasawa jikin Aysher sukayi suka kwanta, lokaci d'aya suka sauke ajiyar zuciya. Aslam ne yafara magana da cewa"Momy anbamu hutu, Dady yace zamuyi sati d'aya anan kafin yadawo yatafi damu, wai bikin shi saura sati biyu Momy zakizo?, yauwa Momy meye ake nufi da *gida idan babu mace kango ne?."*

Ajiyar zuciya Aysher tayi kafin tace"Ohh Aslam surutu da tambaya, toh wanne zan fara amsa maka a ciki?, waye yake cewa gida idan babu mace kango ne?."

Cikin sauri Aslam yace"Daddy ne mana kullum sai yayita fad'an haka, bayan yad'auko hoton mu da akayi mana babba ranar da muka koma kaduna yanata kallo, Momy har kuka Dady yakeyi."

"Shiii ya isa haka, zan fad'a maka abinda ake nufi da kalmar amman saika k'ara girma, kuma zanzo bikin Dady."

Mama dai tana gefe ta zuba musu ido, bata sako musu baki ba, cikin zuciyarta fad'i takeyi _yaran Aysher Allah ya sako musu dabara da wayau, Allah dai ya raya._

Wayar Aysher ne yake kuwwar neman a gaji, alamar kira yana shigowa tana dubawa taga Samir ne dan haka tayi hanzarin d'auka.

"Hello."

"Kizo ina falon Baba." Abinda ya fad'a kenan baijira cewarta ba ya katse kiran.
[12/6, 1:08 PM] Zeetty: Ta shiga falon da sallama, ya amsa mata kafin tanemi guri ta zauna, ta fara gaisheshi ya amsa babu yabo babu fallasa.
Falon yad'auki shirun wasu 'yan mintuna shiru bawanda yayi magana, Samir ne yagaji da shirun dan haka yayi gyaran murya kafin yafara magana da cewa"Sulty ina cikin damuwa, nayi dana sanin ka6ar wannan aure na Yaseera yarinyar gaba d'aya bata da hali, muryan ta kamar na Maza lamarin nata sam babu sha'awa, Sulty duk kece kika janyomin *Mafarin lamarin* da'ace angani da mata Oga bazai ta6a yimin tayin auren 'yar sa ba."

Aysher ta bud'i baki zatayi magana wayar Samir yafara kuwwa alamar kira yana shigo masa, ya duba number da ake kira yaga bak'uwar Number ce dan haka ya share yak'i d'auka, ba'a hak'ura ba aka sake kira, Aysher tace"kad'auka kagani mana ko waye."

Dan haka Samir ya danna yad'auka amman yak'i magana. Daga d'aya 6angaren yaji ana magan. "Hello! D-lovely kana jina Amaryace Seera Baby."

Na shiga uku! Kalmar da Samir ya fad'a kenan tare da katse kiran, yakalli Aysher yace"Sulty itace fa, nikam wannan yarinyar wace irin mayya ce haka, a ina ta samu number na?, danni bani na bata ba da hannu....." Wani kiran ne yasake shigowa Aysher tace"kad'auka kaji abinda zata ce maka dan mu gama magama dare yanayi (ta fad'a cikin alamun kishi)."

Samir ya d'auka bayan yasa maganar yadda Aysher zata iya jin abinda Yaseera take fad'a.
"Hello! D-lovely wai baka jina ne, toh daman zan fita zuwa club ne shine Dad yace saina tambayi izinin ka, amman fa baisan cewa club zanje ba dan Allah karka fad'a masa, shine Dad d'in yabani Number ka, toh ya kake gani naje?, zan na samo abin ta6awa ne wata k'ila ma nayi sa'ar samun cocein (hodar iblis), dan na kwana biyu bansha ba tunda Dad yasa aka kwashemin kayan maye na a gida, shiyasa nakeso ayi auren nan nasan bazaka takurani ba ko D-lovely?. Wata rana ma zan baka kasha, zan koya maka shiga duniyar sahara kajika a sama-sama......."

Diff Samir yakatse wayar yadafe kansa da hannu.
Yakalli Aysher hawaye yake fitarwa mai ciwo yace"Sulty i'm finished! Natashi daga aiki nikam, kinji tsinanniya zata koyamin yadda akeshan kayan maye, Sulty shin ko baki yafemin bane?, hak'k'inki yafara tambayata tunkafin aje ko ina, barin je nikam auren nan nafasa saidai sanadiyyar haka a koreni daga aiki."


Muje zuwa

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: [12/10, 4:46 PM] Zeetty: 💐💐💐💐💐


*MAFARIN LAMARIN*




DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*



©Zeetty


_Na sadaukar da wannan page d'in gareku, Maimunat Idris Sani Beli da Fauziyya D. Sulaimain, Ubangiji ya kara basira sosai nake biye daku._


PAGE 22-23
Mik'ewa Samir yayi da niyyar barin d'akin, Aysher tayi saurin shan gabansa tare da cewa"Abban Aslam kakwantar da hankalinka, babu abinda yafi k'arfin ubangiji so u have to calm down ur mind pls dawo kazauna muyi shawara. A sanyaye Samir ya dawo ya zauna akan kujera, ruwa mai sanyi Aysher tafara bashi yasha lokaci d'aya yasauke kofin tare da ajiyar zuciya.

Aysher ta kalleshi cikin sanyin muryarta tace"Abban Aslam ka kwantar da hankalinka, kaucewa wannan aure ba k'aramar matsala bace tunda kariga ka amsa da bakinka banason kazama k'aramin mutum mai magana biyu, tayiwu Allah ya nufeka da wannan auren ne ta dalilin haka Yaseera ta shiryu......."
A fusace Samir yace"Ni zan shiryar da ita, wannan kangararriyar yarinyar?."

"Ba nufi na ba kenan Abban Aslam, Allah ne mai shiryar da bayinsa amman tayiwu kaine sanadiyar hakan." Aysher ta fad'a cikin sanyin murya.

Shiru Samir yayi yakasa cewa komai, nan dai Aysher taci gaba da bashi shawarwari tare da kwantar masa da hankali har saida yasamu nutsuwa. Kafin ya dubi Aysher yace"ke yaushe zakiyi auren toh? Tunda yaukam nak'ara tabbatarwa da cewa bakya sona, bazaki iya komawa aure na ba."

Dariya Aysher tayi kafin tace"Kacika rigima Abban Aslam yaushe-yaushe nafara karatu? Wata biyu kenan fa amman kanayimin maganar aure, saina gama karatu, bismilla ga abinci." Tak'arasa fad'a tare da jawo farantin da Mama ta shiryo abinci a ciki. Kad'an Samir yaci abincin, yakalli Aysher cikin tu6une fuska yace"Sulty zantafi dare yayi, gasu Aslam zasuyi one week, sai kutaho tare dasu lokacin bikin zandawo gobe kafin na wuce."
Murmushi Aysher tayi ganin yadda Samir yake magana kamar dole tace"bakomai sai kazo din, Allah yakaimu lafiya ka kularmin da kanka."
Mik'ewa Samir yayi tare da k'ara d'aure fuska yace"Ina ruwanki da ni da zakice na kula da kaina, sai da safe."

Ficewa yayi a gaggauce, baijira cewar Aysher ba.
"Abban Aslam rigima." Aysher tafad'a tare da mik'ewa bayan ta tattare kayan abincin dake falon.

```******```
Kabir yana d'aya daga cikin wad'anda suke zuga Samir kan amincewa da auren Yaseera, dan tsakani da Allah Samir ya yadda da Kabir d'ari bisa d'ari.

Kabir yana lissafe da ranar da iddar Aysher zata cika, dan haka tana cika ya garzaya gidan tunda yaje gidansu Aysher sau uku yana aika yaro ayi mishi sallama da ita, yaron sai ya dawo da amsar cewa"tace koma waye yayi hakuri, ba zata samu damar zuwa ba." Zuwanshi uku ana bashi wannan amsar dan haka ya hak'ura tare da k'arama Aysher lokaci, cikin zuciyarsa ya d'aura aniyyar cewa bazaije bikin Samir Kaduna ba tunda yasan Aysher dole taje.

Yaseera na hango kwance akan makeken gadonta, takira Johnson a waya suna magana cikin harshen turanci tace"Haba Jonh nace maka karka damu, idan nayi wannan auren zanzo na aureka, nifa kawai inaso naji yadda guy d'in yake ne, dan haka nakeso na aure shi, kota wane hali saina koya masa shan kayan maye."

Shiru Jonhson yayi kafin kuma daga bisani yace"okay ina jiranki promise? (alk'awari)."

"I promise u my love (Nayi maka alk'awari masoyina)."

Shirye-shiryen biki ya kankama sosai gidan Alh. Auwal mataimaki suke shiri,, Yaseera amarya dakanta take yima kanta shiri tasha wancan, ta matsa wancan, haka dai. Bangaren Samir babuwani shiri dayakeyi tunda uban ango ya hutar dashi kayan lefe, dan haka ya zuba ido shidai kawai sadaki yake jira ranar tayi yaje ya bayar, Mama tanata shiri danma Samir ya dakatar da ita gayyato jama'a.


Alh. Auwal mataimaki da kansa yakira Samir ya shaida masa waliman da abokansa suka shiryama ango da amarya tare da rokon alfarman Samir yataimaka yaje, hakanan Samir ya amsa badan yaso ba.
Ana gobe d'aurin aure Aysher ta sauka a garin zari'a badon ranta yaso zuwa ba, sai dan takura mata da Samir yayi, a gidan wani kawunta ta sauka dake zaune a kaduna anguwar sarki ta sauka ita da yaranta.


A kuma ranar ne za'ayi walimar da Alh. Auwal ya shaidama Samir, dan haka Samir baisamu had'uwa dasu Aysher ba a wannan ranar.
[12/10, 5:06 PM] Samir ya isa wajen da Alh. Auwal ya fad'a masa domin yin walimar bikinsa da abokansa suka shirya ba don ransa yaso ba, tare suka tafi da wani abokin aikinsa mutum d'aya wato Ahmad, amma abinda ya fara gani ne a gurin ya bashi mamaki, waje ya cika da 'yan mata da samari a takaice dai party aka shirya, kuma sabanin yanda ya zata zaiga manyan mutane sai yaga qawayen Yaseera. Haka dai ya zauna ba dan yana so ba kawai dan ya isa wajen ne, haka akayi party ba yabo ba fallasa, Ansha kayan shaye shaye a wajen, shima Samir haka aka bashi wine ya kwankwada ba tare da yana da masa niyar akwai alocohol (giya) a ciki ba........


Muje zuwa

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/31/2017, 21:35] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐


*MAFARIN LAMARIN*




DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*
*_We are here to educate, motivate, and entertain you reader's._*



*INA JINKU A ZUCIYATA*
*_Beauty Queen_*
*_Mmn Noor_*
*_My madaya_*

*Alfahari nakeyi daku sosai.*
*_Zauren littattafan hausa_*
*_Duniyar marubuta_*
*_Mace mutum group_*
©Zeetty


PAGE 24-25

Sai wajen 12:00am aka gama dinner wanda suka kirashi da sunan walima, irin bad'alar da sukayi a gurin baki bazai iya fad'arsa ba. Ahmad abokin Samir shima dayake dan duniya ne, yana d'an kora ruwan giyar dan haka yasha abinsa son ransa, haka Ahmad yakama Samir zuwa gurin mota dan lokacin Samir baya cikin haiyacinsa, Amarya taso sutafi tare da Samir amman Johnson dayazo mata biki yahanata zuwa a cewar sa yakama musu hotel suje su kwana dan yima juna bankwana kafin lokacin nasu bikin (subhanallah! Kunji wani lalacewa Allah shirya mana zuri'a).

Aysher bata samu halattar gurin walimar ba kamar yadda Samir ya gaiyaceta, dan batason zuwa taga Samir da wata a matsayin matar da zai aura (kishi), dan haka kawai ta zauna a gidan kawunta inda ta sauka kenan, kiran wayar Samir ta dingayi bayan anyi sallar magriba, dan taji yaushe zaitafi walimar amman shiru ba'a d'auka ba har wajen isha, Aysher duk ta damu a ganinta ko Samir yayi fushi ne dan tak'i zuwa gurin walimar auren sa. Dan haka ta dinga kira akan cewa yayi mata kwatancen gurin walimar amman shiru har zuwa k'arefe 11pm (na dare) tanata kira bai d'auki wayar ba, dan haka Aysher ta hak'ura da kira ranta a 6ace"meyasa Abban Aslam baizaiyi mata uzuri ba (tunanin da Aysher takeyi kenan cikin zuciyarta)."
Rashin sani! Dan kuwa Samir tunda zaishiga masallaci sallah magriba yasa wayar a silent saboda zafinkan maganar zuwa gurin walimar nan ya manta bai cire ba, dan haka duk kiran da Aysher takeyi masa baisani ba, bai kuma d'auko wayar ya duba ba har zuwa lokacin da ya isa gurin walimar ya kora ruwan kwalba (giya) cikin rashin sani.

Kai tsaye gidan Samir, Ahmad ya nufa da shi bai direshi a ko'ina ba saida yakamashi har cikin falo ya shigar dashi kafin ya juya dan zuwa nashi gidan.
_Mama bata gidan, tana gidan wasu 'yan uwanta dake cikin anguwar kawo, saboda gyare-gyare da Alh. Auwal mataimaki (Uban amarya) yasa aka sakeyima gidan tare da sabon fenti dan zuwan amarya._

Samir a falon ya baje,

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment