Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

sCopied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels Group
Hausa novels and fashion Group
Cool novel, makeup and kitchen1 Group
And
WOMEN24 TV Group

WHATSAPP NO:+2349030159301




[4/2, 6:17 AM] Hayat: 🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️



[4/7, 11:43 PM] Hayat: 🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️

*short story*


*true* *life story*


*LABARI/RUBUTAWA*


*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*


*MARUBUCIYAR* 📚🖊️

🤦 *ZAMANINMU* 🤦


*AND NOW* 👇



🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*



*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*



*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .



PAGE 3️⃣3️⃣➡️3️⃣4️⃣


📝Tun a cikin motar yake faman tunani hakan yasaka shi rage gudun motar,A hankali yake tafiya harya karaso kofar gidan Mama kafin ya fito dan jiyake yi wani sanyi Yana neman rufe jikin shi.yana shiga falon yaji shiru ba kowa, Anan bisa doguwar kujera ya konta Yana mayar da numfashi.


Can jikin baccin daya fara daukar shi yaji muryar Mama cikin kanshi,tana tayar da shi.Cikin alamun jin bacci ya fara kokarin bude idonshi Yana amsawa "Na'am Mama"Yana tashi zaune.


"Meye ya sameka baka jin dadi ne ka konta anan?" Cewar Mama da take tsaye kusa da shi.


Murza idonshi yayi Yana cewa "eh banjin dadin jikina ne,daga asibiti nake,idan akwai lemu mai sanyi ku bani nasha magani na"komawa yayi ya kontar da jikinshi Yana dafe kanshi.


Mama juyawa tayi tana jin tausayin dannata Yana tsarga jikinta.


Bayan ta kawo mai tashi yayi dakyar ya koma motar,Jim kadan ya dawo da ledar magungu nan ya zauna.

Dubawa yayi dan ganin yadda zai sha.bayan ya gama Shan maganin ya koma cikin dakin anan Kan gadon ya konta bacci mai nauyi ya dauke shi ba tare daya sani ba.

Ganin haka yasa Mama ta koma falo ta saka Asabe ta dafa mai abinci mai dadi kafin ya farka.



Zulaihat tunda ta shige daki ba abinda take yi banda aikin tunani,A karshe da abin yayi Mata yawa kawai ta saka kuka na babu gaira babu dalili.


Saida tayi mai isarta kafin tayi shiru tana faman ajiyar zuciya.Har wuraren karfe shabiyu da Yan mintina kafin ta wanke fuskarta ta fito falo.


Kitchen ta koma da waya a hannunta tana dannawa.


Dubawa tayi ganin Nafisa bata ciki yasa ta gane ta koma dakin su.


Girki ta fara kokarin dorawa saboda yaranta,tanayi tana Kara gyara wurin.saboda zulaihat ba baya ba wurin tsafta da kolliya,dukda yanzu kishi ya saka ta rage wasu abubuwan.



"Yauwa reza nagode ,Dan haka yanzu yadda za'ayi ki turoman nomber account dinki zan Kara maki wani abu saboda wannan albishir da kika yiman"cewar Ihsan da take tsaye jikin windown cikin falon su,tana leken bakin gate.

Juyowa tayi tana cigaba da cewa "Na dade Ina jiran jin wannan daddadan labarin ban samu ba sai yau,yanzu na tabbatar da cewa Zulaihat ba asiri ba ko tsafi zatayi akan Habib to ya gama tasiri,domin koba komai mun gama da su,Kuma mune mukayi nasara,na gano cewar ta sanadinta Habib ya fara neman Mata,Ni ce wadda tsautsayi ya fara ritsawa saboda sanadin mutuwar son da nake yimai yasa na bashi kaina,Amma daga baya ya gujeni ya tafi zai auri wata Yar kwailar yarinya saboda Yana tunanin na zama karuwa bani da sauran amfani a wurin shi,to wannan shi ne hukuncin duk Wanda yaci amanar mu"shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya saboda wannan maganganun da tayi sun tuno Mata da ko ita wacece?,da irin rayuwar da tayi da Habib tun kafin ta karasa yin wayo kamar haka.ba tare data Kara furta Koda kallama daya ba ta katse wayar tana fadawa cikin kujera tare da fashewa da kuka,Dan koba komai har yanzu akwai sauran burbushin soyayyar Habib a zuciyarta,Amma abinda yayi Mata shi ne yake danne wannan son.



Ta Jima a haka tana kuka, kasancewar ba kowa a gidan duk sun fita,saida ta gaji dan kanta kafin ta koma toilet ta wanko fuskarta to konta zuciyarta cike da tunani.




A bangaren Habiba kuwa yauma haka Innajo ta tasata a gaba da aikin gida tunda taga Malam ya fita,ita ce wanke-wanke da shara ga aikin dambu ta ce sai tayi yau shi zasu ci.
Haka tayi ta fama har gabannin sallar azahar kafin ta karasa.wanka tayi ta shirya cikin doguwar rigar atamfa a cikin irin Wanda Habib ne ya dinko mata.


Dambun da Inna ta zuba Mata tasan bazai isheta ba saboda wata azababbiyar yunwa da take addabar ta,Dan tun koko da kosai na safe malam ya tisata a gaba ta sha kafin ya fita.kwanon ta dauka ta juya dakinta tana girgiza Kai.




Habib shi ne bai farka ba sai bayan karfe daya,shima Mama tayi ta faman tayar da shi kafin ya tashi,Dan ita Baccin ya bata mamaki.



Arwallah yayi kafin ya gabatar da sallar shi anan cikin falon,ya Kara shingidawa akan abin sallar.

Asabe ce ta shigo da sallama dauke a bakin ta.tray'n kayan abincin ta aje a gaban shi tana cewa "Yallaboi ga abincin nan"tana juyawa.



Bude idonshi yayi kafin ya kalli abincin cikin slow voice ya ce "nagode "



Zubawa yayi Yana c,Amma ji yake yi abincin baya yimai dadi,A haka dai yadan tsakura kafin ya mike Yana tattare maganin shi da wayoyin shi.


Lekawa yayi cikin dadin Yana cewa "Mama ni na wuce sai gobe mun biyo da Habiba ta gaishe ki"

"To Allah ya sauwake,sai kun zo kaci gaba da hakuri kaji ko,shi komai yayi farko zaiyi karshe"cewar Mama da take shan kankana.


Amsawa yayi da "Amin"kafin ya juya Yana barin cikin gidan.


A hankali yake tuka motar saboda wani mugun faduwar gaba da yaji Yana damun shi......




















✍️✍️✍️✍️✍️✍️





*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*













👏👏👏👏👏.
[4/7, 11:43 PM] Hayat: 🗡️ 🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️

*short story*



*true* *life* *story*



*LABARI/RUBUTAWA*




*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*




*MARUBUCIYAR* 📚🖊️



🤦 *ZAMANINMU* 🤦



*AND NOW* 👇



🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*




*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*




*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .




PAGE 3️⃣5️⃣➡️3️⃣6️⃣




📝 Addu'a ya fara karantowa,haka yayi ta maimaitawa har saida ya ji zuciyar shi ta fara sanyi ,faduwar gaban ta ragu kafin ya karaso bakin gate din gidan.bayan mai gadi ya bude mai gate a hankali ya karasa Yana daidaita parking din motar.





Labulen jikin windown ta saki tana ajiyar zuciya,tunda ya shigo take kallon shi harya fito daga motar,sosai taga ya rame a fili ta furta "ko meye yake damun shi?maimakon yayi kiba sai aga ya rame?"dage kafadarta tayi alamun ko a jikinta kafin da sauri ta shige dakinta,saboda taji alamun zai shigo falon.tana shiga ta saka key saboda zuwa yanzu haushin shi take ji Yana karuwa a zuciyarta.shiyasa bata so su hadu dan komai Yana iya faruwa.



Shigowar shi ya ji gidan shiru kaman ba kowa,Dan haka shima ya shige dakin shi saboda baya jin yunwa cikinshi a cike yake.





A ranar ma haka Suka wayi gari ba tare da ya sakata a idon shi ba,shiko yayi alkawari bazai je dakinta ba hakkin shi da yake kanta ya hakura tunda haka ta zaba.




*WASHE GARI*


Haka washe gari ma baibi ta kan zulay ba ba yayi ficewar sa,ko break ba tsaya yiba.

Gidan su Habiba ya nufa,yayi sa'a kuwa Malam Yana nan bai fita ba kasuwa ba.

Har kasa ya duka Yana gaishe da sirikin nashi.bayan sun gaisa ya fara yimai bayani "Am daman inaso ka bani izini zamuje da Habiba ta gaishe da Mama,sai muje asibiti a yimana awo,kafin ranar sai a kawo results din".Yana dan sosa kanshi alamun jin kunya.



Malam nisawa yayi kafin ya ce "to Habibu ba matsala,nidai na baka amanar Habiba domin kuwa nasan ba zaka cutar da ita ba,Allah ya kiyaye ku gaishe da Maman taka"cikin gidan ta shige Yana cewa "Bari na turota sai ku wuce yanzu kafin rana tayi.




Jingina yayi da jikin motar Yana kokarin Kiran Doctor Hasan Kira dan sanar da shi gasunan zasu taho yanzu.


Harta katse bai yi picking ba,kawai saiya kyaleshi.

A cikin gidan kuwa dakyar Innajo ta bar Habiba ta fito a cewar ta ai bata gama yimata aikin cikin gida ba.saida malam ya bude Mata ido da fada kafin tayi lakwas tana mamakin yau ita malam yake yiwa fada haka.



Yana ganin ta fito ya shige mota,itama gidan gaba ta shiga da Sallamar ta,Amsawa yayi kafin ya tashi motar Suka fara tafiya.kasa ta Kara yi da kanta tana cewa "Ina kwana"tana wasa da dan zobenta na silver mai kyau.

A takaice ya ce "lafiya Lau"Yana duban gefen titi.




Zulaihat kuwa tana jin fitar Habi itama ta fita yau ko aikin komai bata yiba sai ruwan tea data sha kofi daya.Aikin gidan da girki Nafisa ta barwa .







Har suka karaso gidan Mama cikin su ba Wanda ya Kara furta komai.

Sauka yayi Yana cewa "fito muje"yayi gaba.

A hankali ta fito tana bin bayan shi har suka karaso cikin gidan.A bakin kofar ya tsaya yayi sallama kafin ya shiga.Haka tayi ta binshi a baya kaman wata jela.



Mama tana jiyo sallamar su ta nufo falo tana yimasu sannu da zuwa.

"Sannu ku da zuwa "cewar Mama tana zauma Kan kujera.

Shima zama yayi Yana cewa "mun karaso,ba dadewa zamuyi ba saboda Ina so muje asibiti kada rana tayi.

A kasan kafet din ta zauna.mama tayi saurin tarota tana cewa "Haba diyata ya zaki zauna a kasa,zo nan kusa da ni ,ki dauke ni kaman maman ki kinji"tana zaunar da ita a kusa da ita.

Ita dai Habiba sai faman sussunne Kai take yi dan duk jinta take yi a takure.

Cikin ladabi ta gaishe da ita.sosai Mama ta yaba da tarbiyar yarinyar,Dan bata manta bayanin da Habib yayi Mata akanta ba.



Sakawa tayi Asabe ta kawo Mata kayan motsa Baki,da ruwa.Amma Habiba kin cin komai tayi,har suka wuce asibiti.


sosai Ihsan take Shirin barin garin kaduna,Dan tayi alkawarin a ranar da za'a daura auren Habib,to ita a ranar zata bar garin.


Zulaihat tana fita ta samu dan sahu derect gidan su tace ya kaita dake a hayin rigasa.


Tun a cikin adaidaita ta bashi kudin yana tsayawa ta sauka,cikin sauri ta nufi cikin gidan.


Tun daga kofar falon ta fara rusa kuka da kurururuwa kaman wadda akace Babanta ko Mamanta sun rasu.

Da sauri mutanen gidan suka fara rige-rigen fitowa.ganin ita ce da sanyin safiyar nan yasa kowa yayi turus Yana kallon ikon Allah,Dan sunsan karshen zancen nata.Ummanta girgiza kanta tayi ta koma cikin daki.

Sai kanwarta ce Jamila ta rukota tana tambayar ta "Wai Aunty zulaihat lafiya kike wannan kukan?Haba wallahi harkin tsorata mu"ta zaunar da ita a akan kujera.


Haka tayi ta faman rarrashinta, Amma kememe zulaihat taki tsagaita kukan nan.


Suna haka sukaji an daka masu wata muguwar tsawa data saka Suka sauko daga Kan kujerar ba tare da sun saniba.

"Ashe zulaihat baki da hankali bansani ba?nidai nasan baki rasa ci ba,Baki rasa sha ba,sutura,abinci sai Wanda kike so zaki dafa keda yaranki,Amma da yake kin saka *ZAFIN KISHI* a ranki kin hana kanki sukuni,duk kinbi kin tsangwami kanki saboda Habibu zai Kara aure,to ki kawo min aya ko hadisin da ya ce kada namiji ya Kara aure,ko Kuma ance tunda ya aure ki bazai Kara aure ba saboda ya faranta maki rai?to wallahi tun kafin na fara bata maki rai ki tashi ki koma dakin ki"ya juya a fusace,Dan idan Yana ganinta to zai iya rufeta da shegen duka.


Cikin azama ta fice waje da gudu,saboda tasan hakin Abbansu yanzu Yana iya rufeta da duka.haka ta fita daga gidan tana kuka.


Umma kuwa takaici ne ya hanata fitowa,duk iya kokarinta na ganin ta nusar da Zulaihat akan ta rinka danne kishinta,Amma abin ya faskara.saita bata Mata rai.tasan zulaihat tana da *ZAFIN KISHI* tun tana Yar kankanuwar ta.




Daidai karfe goma da rabi Suka shiga asibitin.

Office din Doctor Hasan ya nufa tana biye da shi.

Bayan sunyi musabiha Yana ta tsokanar shi kafin aka yimata Habiba gwaje-gwaje.


Doctor Hasan fita yayi ya barsu a office din.ita dai Habiba shiru tayi,shiko sai Danna waya yake yi.dukda Yana jin ya fara jin yunwa,saboda baiyi break ba da zai fito.



Tunda Doctor Hasan ya shigo yake kallan abokin nashi,a zuciyar shi yake mamakin "ya akayi haka ta faru".cikin sanyi ya zauna Kan kujerar shi Yana Kara nazarin result din abokin nashi daya gani.


Nisawa yayi Yana cewa "Am please my friend,yauma result dinka bai kammala ba,saboda Basu karasa wasu gwaje-gwajen ba,Amma nayimaka alkawarin ranar daurin auren ni zan taho da su kafin mu fita gidan su amaryar,Dan nasan yanzu idan ka tafi hidimomi zasu Sha kanka ba lallai ne ka samu time din dawowa ba".Yana kallan fuskar abokin nashi.



Habib dage kafadar shi yayi,alamar ba damuwa kafin suka fito.Har bakin motar ya rako su kafin ya juya zuciyar shi cike da wasi-wasin abinda idon shi ya nuna mai,Amma zai gwada da kanshi dan ta tabbatar da gaskiyar al'amari.


Haka ya ja Motar suka bar harabar asibitin......









✍️✍️✍️✍️✍️✍️













*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*











👏👏👏👏👏.




*Short story*

*true life story*

*LABARI/RUBUTAWA*


*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*



*MARUBUCIYAR* 📚🖋️

🤦 *ZAMANINMU* 🤦


*AND NOW* 👇

🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

_Amincin Allah ya_ _kaimaka aduk inda kake_ , _mutum mai_ _karamci_ _taimako da kulawa bazan iya manta yadda ka_ _nunaman halacci ba_ _shiyasa a kullun kake_ _Kara zama a cikin_ _KALBINA wato OGA S A_ _ABUBAKAR bafullatanin_ _usili ina Addu'ar Allah ya_ _taimakeka a dukkan_ _al'aa ka tainame ni a_ _lokacin da nake da_ _buka🥰😘💃💃.




*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*



*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .




PAGE5️⃣➡️6️⃣


📝Sune basu farka ba har saida aka fara tayar da ikamar sallah kafin shi ya fara motsawa,sannan itama ta bude idonta,akan shi take konce shiyasa bai tashi ba har saida ta mike kafin shima ya nufi toilet da niyar yin arwalla.itama dakinta ta wuce.bayan ya idar da salla Wonka ya shiga,Dan so yake yi ya kammala shirinshi da wuri sai ya biya asibiti Dan ganin jikin yarinyar nan kafin ya wuce office.

Zulaihat tunda ta idar da sallah ta leka dakin su Ahmed Dan ganin ko sun tashi,kamar yadda ta tsammata hakan be kuwa,domin akan abin sallah ta riske su sun idar suna haddar islamiyya kasancewar anyimasu hutun boko.suna ganinta duk suka duka suna gaisheta,amsawa tayi tana cewa yarinyar da take kula da yaran tayi sauri tayi masu wanka kafin ta karasa girki Dan zuwa tahafis.cikin ladabi yarinyar ta amsa,kafin ta juya zuwa kitchen.cikin kwarewa take hada masu kayan break,a cikin lokaci kalilan ta kammala suyar doya da kwai sai ruwan zafi data hada Dan jiya da dare raga ya shigo da bread.

Tana fitowa ta tadda yarinyar mai suna Kubra harta kammala shiryasu cikin uniforms kalar marown da jikunan su na litattafai.Ahmed ne a gaba sai Khadija tana bimashi sai karaminsu Arfat.masha Allah sunyi kyau kasancewar sun dauko hasken Zulaihat.

Abinci ta gabatar masu cikin wadatacciyar tarbiya suka fara cin abinci bakin su dauke da basmala.dakinta ta wuce Dan kimtsa jikin ta kafin mai gidan nata ya fito.

Wata doguwar rigar atamfa ta saka kalar black blue dinkin ya mata das kacancewar jikinta daidai wadaida ne kibarta Bata yi yawa ba.daurin dankwali tayi irin Wanda ake cema *AISHA TSAMIYA* sosai yayi mata kyau Dan zulaihat ma'abuciyar zafta ce.

Shima ya karasa Shirin shi cikin uniform dinshi kalar na yan sanda,sosai suka haskashi sai kanshin turare yake bazawa.


Kusan a tare suka fito Yana rataye da jakar kayan aikinshi sai wayoyinshi guda biyu daya rikesu a hannu.

Cikin takunta mai bala'in daukar hankalinshi ta nufi inda yake,shiko sakato yayi Yana kallan ta yanda ta Kara komawa yarinya shakaf,dukda daman ba wasu shekaru ne da itaba,Dan ko lokacin daya aureta tana da shekara shatara ne zuwa yanzu da sukayi yara ukku ba zata haura ashirin da bakwai ba,hakan yasa bazaka gane ita ta haifi yarannan ba.


Baisan ta karaso ba sai ji yayi tana huramai iskar bakinta akan idonshi,a hankali ya rufe idonshi Kanan ya budesu tar akan kyakkyawar fuskar ta.
Hannunshi ta kama zuwa dinning table,Dan ta lura baya gajiya da kallonta.kujera ta ja mai ya zauna,jakar shi ta ajiye kafin ta fara zuba masu abinci.Agogon dake daure a tsintsiyar hannunshi yake duba ganin har karfe takwas ta gota yasa a hankali ya "furta my wife na kusan makara fa"Yana rike hannunta.


"Tau sorry yi sauri kaci,banso ka tafi baka ci abinci ba kada yunwa ta hanaka yin aiki"ta bashi amsa tana tura plate din doya gabanshi.


Cikin nutsuwa yake cin abinci bai wani ci na kirkiba yadan kurbi tea kadan kafin ya mike Yana goge bakinshi da tishue.jakar shi ta dauka har bakin motar shi ta raka shi ya shiga tayi mai Allah kiyaye,har ya tayar da motar tana daga mai hannu kafin ta koma cikin gidan Dan ci gaba da wasu ayyuka.




Yana fita direct asibitin ya nufa,lokacin daya shiga tana bayi yarinyar dake kula da ita sun shiga tare tana brosh.

Bai wani dade a zauneba suka fito.a bakin gadon ta zaunar da ita kafin ta gaishe shi,amsawa yayi Yana kallan peshent din kafin itama cikin raunin murya ta ce "Ina kwana"tana Mirza yatsun hannunta.


"Lafiya Lau,ko akwai inda yake maki ciwo ne?Ya tambayeta Yana kallan yadda ruwa ya jika mata gashin gaban goshinta.


"Babu naji sauki,Dan Allah ka mayar da ni gida yanzu innajo tana ta nemana,Kuma nasan saita duke ni"sai hawaye cur cur suna shatata ta cikin idonta.


Sosai ta bashi tausayi,yarinya karama kamar wannan ace tana dauke da hawan jini haka ai abin akwai damuwa .baice komai ba sai kayan daya tsaya ya siyar mata akan hanya ya fito da su Yana cewa "ga wannan kuyi amfani da su kafin doctor yayi discher dinmu sai na mayar dake gida ko?Yana kallan yadda hawaye ke fitowa daga idonta.

Itama bata amsaba illa faman hawaye da takeyi.

Fita

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

1 Comments On ZAFIN KISHI
avatar
abasu-kala

11 months ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment