Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»Ώ[22/11, 06:24] AngelπŸ’žπŸ’žπŸ’ž: πŸ’¨ *CHASING MY HEART* πŸ’¨
A Tsakanin So
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

Page 1 to 4
Free page

*Littafin the chasing my heart, a tsakanin so, na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take son complete dinsa zata samu akan naira dari shidda 600, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057....*


GARIN KATSINA
Da safiyar wannan rana sanyi ake yi sosai a garin na katsina, garin yayi buji yayi hazo-hazo, idan mutum ya d'aga kai ya kalli nesa dashi sai yayi tunanin hayaki ne yake tashi, a irin wannan ne lokaci yake ja ba tareda an ankara ba kasancewar rana bata fiye fitowa sosai ba, mafi akasarin mutanen dake zirga-zirga a waje suna sanye ne da sweater da hular sanyi, wasu har glass suka saka suke rufe idanuwansu, some with face mask....
Santa ce wadda take dauke da gidajen mutane masu karamin karfi, gidaje dake akan santar mafi akasari kananu ne wasu ginin kasa ko shafe babu, babu kwalta a santar amma mota zata iya shiga saidai akwai wajen da idan taje dole ta tsaya, tsit santar take kasancewar yara sun tafi makarantar boko...
Wani gida ne na hango flat house wanda yake dauke da katon kyauren karfe amma babu get, soron gidan yana da girma, idan mutum ya shiga gefenshi kewaye ne, nesa kadan madafa ce opposite da ita empty room ne, akwai rigiya, dakuna ukku ne a cikin gidan, room and parlour daga gefe dama, sai two bedroom opposite dashi, randar ruwa na hango, gidan yana da girma, yasha paint da tale a malale, ko'ina tsaf-tsaf....
Bedroom ne babba wanda yake dauke da bathroom, katon royal bed ne wanda yake dauke da wani expensive bed sheets with pillows manya da kananu, a gefe closet ne tareda dressing mirror wanda yake shake da kayan makeup tareda designer perfumes, shoes rac daga gefe, the other side sofa ce tareda glass table, a both right and left side na bed, bedside drawer ne, wasu flames na hango wanda suke dauke da drawing, a gefe fridge ne, wani designer carpet ne mai laushi a malale akan tale dake bedroom din....
9:30am wall watch din bedroom din ta nuna, wata breathtaking Babe ce er kimanin shekaru goma sha shidda zaune a tsakiyar royal bed din tana jingine da pillow ta rufe rabin jikinta da blanket, waya ce kirar iPhone 11 a hannunta kanta a duk'e tana shafata, tana sanye da sleeping gown baka, ta yafa veil kadan a saman kanta, rabin gashin kanta a bayyane yake, idanunta sun nuna daga bacci ta tashi....
MashaAallah, fara ce sol har yellow skin dinta yake saboda haske, she is gorgeous, Allah ya hore mata kyau, she's chubby daidai ita yayinda figure dinta suka k'ara k'awata kyawunta, slender in shape, eyelashes dinta zara zara ne baki, eyes dinta farare ne sol kamar madara, tana da yalwataccen eyebrow yana kwance gashi yawo-yawo yayi luf-luf, pupil dinta black ne sosai, ga iris dinsa kamar ita ta zauna ta tsara abunta, tana da long pointed nose tareda small cute lips dinta pink sai sheki suke kamar tayi applying lipstick, tsagun rumawa ce a both cheeks dinta tareda gefen fuskarta, ya fito rau tareda k'ara k'awata kyawun fuskarta, she's cute and gorgeous, alluring and mesmerizing, tabbas wasu rakiyar wasu sukayi a duniyar kyau....
Ta dafe kai tareda zaro manya-manyan idanunta da alama wani abu ta tuno, tayi jim, murmushi ne yayi escaping akan lips dinta har dimple din dake makale a both cheeks dinta suka bayyana, white teeth dinta masu haske sukayi appearing sai lighting suke, ta sauke hannunta wanda yake dauke da kunshin jan lalle, wanda ya matuk'ar kawatashi, tareda maida hankalinta akan wayar dake hannunta tayi snapping video....
Hotunanta tayi selection tayi forwarding wa wata number, tareda mata voice call ganin tana online, ashe video call ta danna bata lura, tace,
"Kiyi hakuri k'awata mantawa nayi amma ga hotunan nan na turo maki...".
Ta tsinke ba tareda ta lura da video call tayi ba, ta juya tareda matsar da iPad dinta dake akan bedside drawer tayi dropping iPhone din, ta yaye blanket wanda ta rufe jikinta dashi ta zuro kafafunta tareda durowa daga saman gadon, OMG her leg, kafafunta farare ne sol sumul-sumul kamar na new born, ta mik'e heading to the bathroom, ta tsaya cak a sanadin tsuwwa da wayarta ta soma, ta juya da sauri goshinta ya bugu da kofar bathroom, ta dafe wajen tana murzashi tareda b'ata fuskarta, veil dake a saman kanta ya sub'uce, yadda veil din yake a kanta kamar ta kunsa kallabuna ne a ciki amma abun mamaki yana warwarewa ya fadi kasa yalwataccen gashinta kanta ya bishi wanda har ya kai gadon bayanta, mai kyau, wara-wara kamar rubber ga cika....
*********
Abuja
Wani Handsome and breathtaking guy ne zaune a katon office dinsa wanda yake cikin kamfaninsa wanda daya ne daga cikin kamfanoni masu yawa da suke mallakinsa wadanda suke a garuruwa daban-daban dake a fadin Nigeria, Abdurrahman, waya ce mak'ale a kunnansa saidai har kiran ya tsinke ba'a yi picking ba, ya zare wayar daga kunnansa tareda zubawa majigin manya-manyan idanunsa, fuskarsa dauke da mamaki, yace,
"Rumaaa...".
Saida yayi jim sannan ya k'ara dialing numbar....
Rumana ta durkusa tareda picking veil, ringing dinshi na daban ne, ba tareda ta kalli majigin wayar ba, tayi picking call din tareda kanga wayar a kunnanta heading to the dressing mirror....
Daga daya bangaren Abdurrahman ya sauke ajiyar zuciya sannan yayi mata salaam a hankali cikin husky voice....
"Salaam alaiki...".
Daga daya bangaren Rumana ta janyo stool dake gaban mirror ta zauna, smile ne yayi escaping akan lips dinta, tace,
"Wa alaikassalaam...".
Ji tayi ya kira sunanta...
"Rumana".
Tace, "Na'am yaya Abdurrahman".
"Na kira amma baki dauka ba".
"Ehhh hakane".
Abdurrahman yayi relaxing akan kujera ya lumshe idanunsa ya bud'e, under his breath yace,
"Why?".
"Na shiga bathroom kenan naji k'arar wayar wajen fitowa na kume kai da kofa kaga har yanzu wajen yana min zafi daurewa kawai nike don kadda ace na cika raki...".
A shagwab'e ta ida maganar wanda hakan yanayinta ne...
"Waye zaice kin cika raki inyi maki maganinsa...".
Saida tayi dariya, yace,
"Ehhh... Sorry nine na janyo maki...".
"Huh...".
"Huh kuma?".
"Bazan hakura ba...".
Abdurrahman ya zaro idanu saying,
"Kika ce?".
"Sau biyu kana laifi sannan kuma ba kayi min laifi ba amma kake bani hakuri...".
Abdurrahman ya ware idanu yayinda smile yayi escaping akan lips dinsa yace,
"Ohhh... Kiyi hakuri na daina maki turancin.... Kin tashi lafiya?".
"Lafiya lau... Ina kwana?".
"Lafiya lau... Rumaaa na rasa yadda zanyi zuciyata kamar zata fashe nikeji... Na rasa matar aure, na rasa wacce zata soni saboda Allah, duk wadda tazo idanunta akan dukiyata yake...".
Ya karasa maganar kamar zaiyi kuka, fuskarsa dauke da damuwa....
Rumana tace, "Kayi hakuri yaya Abdurrahman ka cigaba da Addu'a...".
"Na gode sosai Rumaaa... Akwai abun da kike bukata?".
Tayi jim, yace,
"Idan akwai kika b'oye kin san abun da hakan yake nufi...".
Rumana tace, "Uhmmm... Akwai gown da niqab da nike so, zan tura maka hotunansu...".
"Shikenan?".
"Ehhh...".
"Kin tabbata?".
"Ehhh na tabbata...".
"Alright then... Ki gaida man Abba da Umma...".
"Zasu ji, ka gaida min Momy...".
Cikin wasa yace,
"Ni d'an aikenki ne, ki kirata ki fada mata da kanki.... Koda yake zan fada mata... I will call you later, I'm hanging...".
Yayi hanging kiran ya dafe kai tareda lumshe manya-manyan idanunsa, fuskarsa dauke da damuwa....
**********
Rumana ta zare wayar daga kunnanta tareda dropping dinta akan dressing mirror, ta turo baki saying,
"Mutum yana bahaushe amma magana daya biyu sai ya had'a da turanci, bana tunanin zai sauya...".
Ta mik'e ta heading to the bathroom, ta zare kayan dake a jikinta tareda shigewa bathtub ta lumshe idanu yayinda ruwan yake ratsata, ta dauki lokaci tana cuda jikinta da kumfa kafin ta sakarwa kanta shower, bathrobe ta zura, ta d'aura karamin towel a saman kanta, saida tayi brush sannan ta fito, ta k'arasa gaban mirror ta warware towel dake saman kanta ta jawo hand dryer ta busar da dogon gashinta ta tajeshi sannan ta mulkeshi da mayukan gashi ta kara tajeshi ta had'eshi ta saka mashi ribbon, tayi applying cream, powder kawai ta shafawa fuskarta ta fesa body spray, ta bude closet dinta, kayan sakawa kala-kala sukayi appearing, closet din yana da girma sosai, kayan sakawa dake cikinsa masu kyau da tsad'a, bangaren gown daban, bangaren atamfofi daban, bangaren komai daban, lace, material, hijab, abaya da sauransu amma babu kananan kaya a ciki, atamfa ta dauko dinkin riga da skirt ne, kayan sunyi mata matuk'ar kyau, ta rik'e kugu ta juya ta k'ara juyawa tana mai k'arewa kanta kallo da daya mirror wacce take tsaye, glass zalla, looking lovely and breathtaking, skirt din pieces ne ya matseta amma kadan itama rigar pieces ce ta matse wurin boob sai ta bada fad'i a kasa, hannun rigar karami ne style din yayi kyau din yayi suiting dinta, figure dinta sunyi appearing, smile ne yayi escaping akan lips dinta ta zuba necklace gold mai dogon chain, earrings, ring da bracelet daga ganinsu suna da matukar tsad'a, ta zura stilettoes masu sling back heel, skirt din ya rufe takalman kasancewar yayi mata tsayi, ta kama handle tareda murd'awa ta tura kofar saidai wani sanyi ne ya doki fuskarta da sauri ta koma da baya ta janyo long hijab har kasa ta zura sannan ta fita ta shiga daya dakin dake bedroom and parlour, set din kujera masu tsad'a da kyau guda biyu ne a falon, center table tareda fridge a gefe, saida tayi salaam sannan ta shiga....
Wata kyakykyawar mata barumaya dake zaune akan one seater ta amsa mata, saida ta gaidata sannan ta cire takalman dake kafarta tareda zare hijab, ta zauna akan sofa, saying,
"Umma... Sanyi ake fa sosai... Yaa Abdurrahman yana gaidaki...".
Umma tayi murmushi saying,
"Ina amsawa... Kunyi waya kenan?".
Rumana tace, "Ehhh kafin in shiga wanka ya kirani...".
Umma ta gyad'a kai kawai yayinda Rumana ta maida hankalinta akan majigin wayar dake a hannunta....
Umma tayi zuru tana tunani fuskarta dauke da damuwa, a hankali tears suka soma gangarowa daga fuskarta....
Rumana bata lura ba kasancewar baki daya hankalinta yana akan waya, pictures din wata gown tayi sending wa Abdurrahman tareda na niqab, sannan ta duba Reply din da Besty dinta tayi mata.....

_Maasha Aallah_.

Murmushi ne ya sub'uce mata, cikin ranta tace,
"Besty na kenan... Aysha Abdul'aziz Muhammad...".

Typing tayi....

_Hmmmm_

Reply aka yi mata....

_Kinyi kyau, you looks gorgeous_

Smile ne yayi escaping akan lips dinta tayi reply....

_Na gode_

Reply aka yi mata....

_Alright then, tabbas naji d'ad'i sosai da ya kasance na samu godiya daga gorgeous, breathtaking and beautiful kyakykyawa kamarki_

Ta ware idanu tana k'ara kallon magijin wayar dake hannunta...

_Keh Aysha Abdul'aziz Muhammad ban san tsiya_ 😹

Reply aka yi mata.....

_Ba ita bace_

Rumana ta k'ara zaro idanu, tana k'ara duba numbar, tabbas itace, tayi typing....

_Toh wacece?_ πŸ€”πŸ™„

Reply aka yi mata.....

_Wacece ko waye ba? Please kyakykyawa ki daina mayar dani mace bayan ni namiji ne, ki duba dp dina koda yake anyway ba Aysha bace Brother dinta ne Adeel_.

Reply tayi.....

πŸ˜¨πŸ˜±πŸ™†πŸ» _Meyyy? Amma wayarta ce koh? Ita da kanta ta bani numbar tace in tura mata hotunana_

Reply aka yi mata......

_A'a wayata ce, wayarta taci screen_ πŸ€—

Rumana ta zaro idanu tareda dafe kai, tace,
"Ohhh ni... Na taresu, shikenan ya gama kalleni...".
Sai a lokacin ta lura da d'azu video call tayi mashi....
Dagowar da zatayi taga Umma a yanayi na damuwa, hawaye suna bin fuskarta, da sauri ta saki wayar ta mik'e ta k'arasa inda take, ta kama hannunta saying,
"Umma... Umma... Umma... Miye ya sakaki kuka?".
Umma tayi mata pointing katon frame na hoton Abdurrahman, breathtaking handsome saurayi mai KAMANNI da Rumana sak, banbancin kawai shine ita macece shi kuma namiji ne sannan tana da tribal marks a fuskarta yayinda shi kuma ba ya dashi....
Umma tace, "Abdurrahman... Abdurrahman yana bani tausayi yaron kirki amma ya kasa samun wadda zata soshi saboda Allah, saboda tarin dukiyar dake gareshi... Kina gani duk wadda ya nuna yana so sai ta gama yaudararshi ta wankeshi ta samu dukiya a wajanshi sannan ta gujeshi, wasu kuma Allah ne yake taimakonshi ya gane ba don Allah suke sonshi ba.... Y'an mata sai bibiyarshi suke saboda tarin dukiyar dake gareshi... Ya rasa wacce zata soshi saboda Allah...".
Rumana tayi rau-rau da idanu tareda goge hawayen dake akan fuskar Umma saying,
"Umma Addu'a zakiyi mashi... Ba kuka ba...".
Umma tace, "Abdurrahman, kina gani duk da mahaifinki yaqi yarda akan ya gyara gidan nan amma sai ya turashi Makka sannan ya saka aka gyara gidan... Kanne en mata guda ukku Abdurrahman yake dasu a garin nan amma daga Abbanki har en uwanshi an rasa wanda zai bashi diya, yaron nan daga ganin yadda yake cikin damuwa za'a gane aure yake so...".
Rumana tace, "Umma ki fahimci su Abba, a yadda abun nan yake, cikinsu duk wanda yace ya bashi diya cewa za'ayi saboda kudinshi ne...".
"Hakane kuma...".
Rumana tayi jim fuskarta dauke da damuwa, cikin ranta tace,
"Kadda ka damu yaya Abdurrahman zan taimaka maka in nuna maka inda zaka samu wacce zata soka saboda Allah, wacce zata zauna da kai koda zaka rasa duk abun da ka mallaka na tarin dukiya...".

Rumana ta mik'e heading to her bedroom, throughout the rest of the day tayi shine tana kitsawa tana kwancewa akan abun da zuciyarta take kitsa mata, tana son ta taimaka mashi amma akwai risk, musamman idan ya gane itace....
Da daddare, tana zaune akan praying mat har aka yi kiran sallar Isha'i, ta tada sallah, saida tayi shafa'i da wutiri, ta linke praying mat tareda zare hijab dake a jikinta, a tsakar gida ta samu Abba da Umma ta gaidasu tareda daukar kwanon abincinta, saida sukayi hira sannan ta wuce bedroom ta rage kayan dake jikinta ta d'aura towel ta wuce bathroom ta jima cikin bathtub tana durje jikinta da sabula masu kamshi sannan ta sakarwa kanta shower, tayi brush tareda dauro alwalla, ta shirya cikin half night gown, ta zauna a gefen gado tayi zuru tana tufka da warwara akan tayi ko kadda tayi, yana cikin damuwa, tana son ta taimaka mashi saidai akwai risk a ciki, what if ya gano itace? Saida tayi jim sai kuma ta janyo k'aramar waya keypad dake a cikin locker ta saka sim da ta siya kwanakin baya wanda babu wanda ya santa dashi....
Sau ukku tana rubutawa tana gogewa, na hudun ne mistakenly ta danna send, ta fasa ihu ganin har ya shiga, kuma babu dama ta goge, koda editing ba tayi ba, ta mike tana kaiwa da komowa fuskarta dauke da tashin hankali akan abun da zai biyo baya idan ya gane itace, babu so a ciki, babu sonshi a cikin zuciyarta, taimakonshi take son tayi domin ya fahimci inda zai samu wacce zata soshi saboda Allah, wadda zata zauna dashi koda zai rasa dukkanin abun da ya mallaka na dukiya, under her breath tace,
"Kayi hakuri yaya Abdurrahman duk abun da na rubuta ba daga zuciyata yake ba, na rubuta ne domin in taimaka maka in fahimtar da kai a inda zaka samu wacce zata aureka ta zauna da kai duk rumtsi ta kaunaceka saboda Allah...".
Ta kakkab'e bed tayi addu'a tareda light off ta kwanta akan bed tayi lamo kamar tana bacci amma ba bacci take ba, ta jima sannan ta samu bacci yayi awon gaba da ita....
*********
_ABUJA_
Katon mansion ne sosai wanda yake dauke da katon part guda daya sai kananun part daga gefe, swimming pool, garden, parking lot, katon mansion ne sosai, wanda yake cike da security da bodyguard....
Katon parlour ne, wanda yake dauke set na luxury kujeru a akalla guda shidda masu kyau da tsad'a, Abdurrahman Ahmad Almustapha, saurayi d'an kimanin shekaru ashirin da hudu, yayi nisa a tunani, Mommy tana mashi magana amma shiru, saida ta kira sunanshi sau ukku sannan yayi firgigit saying,
"Yeah.. Mommy...".
Fuskarta dauke da damuwa tace,
"Abdurrahman ka rage sakawa kanka damuwa ka cigaba da addu'a, Allah yana tare da kai, ka tashi ka wuce ka kwanta...".
Tareda mata good night ya wuce upstairs to his bedroom, ya rage kayan dake a jikinsa ya d'aura towel ya wuce bathroom, yayi tsaye tareda sakarwa kanshi shower, ruwa suna dukanshi, damuwa tayi mashi yawa, yana da buk'atar aure, yana da buk'atar abokiyar rayuwa, yana da karfin sha'awa yana tsoron shiga halaka, ya kashe shower ya daura towel yayi alwalla tareda applying cream, yayi wa kanshi wankan turare, gutun boxer kawai ya saka ya fad'a akan katon royal bed dake a dakin, idanunsa suka sauka akan flame na hotonsu dake a bedroom din, suna matuk'ar KAMANNI, idan ya kalli fuskarsa yana hango fuskarta, idan ya kalli fuskarta yana hango fuskarsa, banbancin kawai shine ita macece shi kuma namiji, da kuma tribal mark da take dashi, da ace thesame age suke babu abun da zai hana a kirasu da tagwaye, under his breath yace,
"Rumana...".
Har bacci ya soma daukarsa, blinking wayarshi tayi hade da ringing na shigowar text message, kamar ya share sai kuma ya zura hannu ya dauki wayar, ya bude idanunsa kadan domin ganin miye, bai san lokacin da ya ware idanunsa ba ganin miye a ciki, ya saba da irin wadannan sakonni, ba yau ya fara cin karo dasu ba, har ya kai ba ya karantawa yake gogewa, amma ya rasa dalilin da yasa wannan sakon ya dauki hankalinsa....

_Ina Sonka So Na Gaskiya Saidai Ance Wasu Ne Suke B'ata Wa Wasu Suna Sai Kaga Mutum Ya Dauka Duk Haka Mutane Suke Saboda An Cuceshi Ya Warke... Hakan Ne Ya Faru Dani, Ina Son Bayyana Maka Kaina Amma Ina Gudun Kadda Kayi Tunanin Nima Saboda Kudinka Ne, Ranar Wanka Ba'a Boyon Cibi Don Haka A Yau Zan Bayyana Maka Matuk'ar Kaunar Da Nike Maka, Na Jima Ina Crushing Dinka Tun Da Yarinta, Na Girma Da Sonka A Raina, Idan Aka Kirga Shekaruna Kadan Za'a Cire, Sauran Nayi Sune A Cikin Begen Sonka Tun Ban San Miye So Ba, Har Daga Baya Na Fahimci Matuk'ar Son Da Nike Maka.... Believe Me, Ina Sonka Ne Saboda Allah, Kuma Zan Zauna Da Kai Koda Zaka Rasa Dukkanin Abun Da Ka Mallaka Na Dukiya... Daga Mai Kaunarka Har Karshen Lumfashi... Abdurrahman Angel..._

Ya jima ya juya sakon, ya karanta ya k'ara karantawa, ya rasa abun dake janshi, ya samu kanshi da dialing numbar saidai tana ringing ba'a picking, saida ya ajiye miss call ukku, typing text message yayi ya tura....
_Wacece Ke?_
Smile ne yayi escaping akan lips dinsa ya kwanta akan bed yayi lamo, bacci mai dadi ne yayi awon gaba dashi, rabon da yayi bacci sosai kamar ranar har ya manta, ya rasa dalili...
***********
Kiran sallar Subh ne ya tayar da ita daga baccin da take, ta mik'e tareda karanta addu'ar tashi daga bacci sannan ta duro daga saman gado ta wuce bathroom....
Umma ta lek'o tashinta sallah ta jiyo sautin ruwa a bathroom, ta juya ta koma, saida ta sakarwa kanta shower sannan tayi alwalla, ta shimfid'a praying mat tareda zura long hijab saida tayi raka'atanul Fijr sannan tayi sallar subh, bayan ta gama akzar na safiya ta jawo wayarta ta bud'e data, message ne suka soma shigowa, suna shigowa babu kakkautawa kasancewar tana da groups na novel da yawa, saida gabanta ya yanke ganin an turo mata message da numbar da k'awarta Aysha Abdul'aziz Muhammad ta bata ta tura mata pictures, jim tayi tana kallon majigin wayar tana k'ara kallon message da aka turo mata....

_Ya Kikayi Shiru Ya Kamata Ki Bada Sako In Hada Da Hoton In Bata_

Saida tayi jim sannan tayi mashi reply....

_Kace Mata Rumana Abdurrahim Rumah (Rumaaa) Ta Turo Hotunan Kuma Ta Kyauta, Na Gode Da Abun Da Tayi Min_

Aka yi mata reply....

_Sure... By The Way Sunana Adeel Abdul'aziz Muhammad Brother Din Ayusher_ 😊

Tayi mashi reply....

_Okay_

Yayi mata reply....

_Idan Kin Bani Dama Ina Son In Bayyana Maki Sirrin Dake Raina, Wani Yanayi Ne Wanda Na Tsinci Kaina Tun Daga Lokacin Da Nayi Tozali Dake A Screen Na Wayata_

Rumana tayi jim tana kallon majigin wayar sannan tayi mashi reply....

_Ni Kuma _πŸ€”πŸ™„

Adeel yayi mata reply....

_Yeah_

_Ina Jinka_

_Sunanki Ya Hadu, Rumana Abdurrahim Rumah, Ya Min, Yana Burgeni, And You Are Damn Cute, Gorgeous_

Rumana ta dafe kai tana kallon reply gani tayi yana recording voice, voice ya turo mata, wata husky voice ce take magana, saying,

_Rumana Ina Sonki, Na Kamu Da Matuk'ar Sonki_

Da sauri tayi dropping wayar yayinda gabanta ya yanke ya fad'i, tunawa tayi da text message na jiya, da sauri ta bude locker ta zaro wayar, miss call dinsa ta gani tareda text message....

_Wacece Ke?_

Saida tayi jim sannan tayi mashi sending message....

_Yaa Abdurrahman... Ina Daya Daga Cikin Cousin Dinka Mata Guda Ukku Dake A Jihar Katsina_

Under her breath tace,
"Kayi hakuri yaya Abdurrahman duk abun da na rubuta ba daga zuciyata yake ba, na rubuta ne domin in taimaka in fahimtar da kai a inda zaka samu wacce zata aureka ta zauna da kai duk rumtsi, ta kaunaceka saboda Allah...".

Rumana ta mik'e tana kaiwa da komowa tana mai zullumi akan kadda ya gane itace, what if ya gane ita? Shin ta ya zata mashi bayani kenan? Shin zai fahimceta kuwa? Shin waye dauka zaiyi mata....
Ta zauna a gefen gado tana zance zuci...
"Anya kuwa ban yi ganganci ba... Idan ya gane nice akwai damuwa... Sunana Rumana Abdurrahim Rumah, anfi sanina da Rumaaa kasancewar both iyeyana sun fito ne daga dangin ruma, shekaruna goma sha shidda amma kasancewar ina da jiki da tsayi kadan shiyasa wasu suke ganin kamar na wuce hakan, ina da kyau sosai, good looking farar barumaya mai matuk'ar kyau fiye da tunani, ina da haske sosai har yellow skin dina yake, domin idan mutum ya kalli kafata zaiyi wahala ya banbance tsakanin hasken saman kafata da hasken kasanta... Natural beauty.... Ina da dogon gashi wanda yake wara-wara kamar rubber ya sauko har gadon baya... Na kasance ma'abociyar saka long hijab in rufe fuskata da niqab... Saboda tsayin gashin kaina ina yawan mashi gammo ne in tamkeshi da kallabi ta yadda koda sili guda daya ba'a hangowa... Kalmar Rumatsa ta zauna akan bakina domin zaiyi wahala mutum ya zauna tare

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment