Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hamidat in sha Allah ita alkairi ce agare ka inaso kad'auka tamkar akwai soyayya a tsakanin ku sabida mu gatane mukayi maka babba sannan akwai wani abu wanda zanja hankalin ka akai kasande yadda al'adar cikin masarautar nan take ko ? ta shinfid'a wannan farin Kayllan to inaso kadaure kayi abinda yadace karkusa muji kunya ina alfahari da wannan biyayyar taka tashi kaje kashirya komi na tarbar amarya "

Sosai Hamut yaji zuciyar shi tajagule cikin sanyin murya yace

" Amma ranka shidad'e wannan abun fa ba addini bane kuma shi wannan abun yanabuqatar shirri maiyasa baza'a denashiba Abiy ? "

Ajiyar zuciyar Sarki Jabir yasauke sannan yace
" inda za'a denayin shi to tabbas dasenafika yin farinciki matsalar daga Hajiya ne tashi kaje Allah yayi muku albarka "

Jiki babu qarfi Hamut yafita part d'in shi yakoma ganin mahaifiyar Hamidat yasashi tsayawa cikin girmamawa ya gaidaka yatsina fuska tayi ta amsa a daqile nufar hanyar saman yayi cikin sauri Hamidat tadakatar dashi dafad'in
" dakata Hamut idan akwai wacce ta tsan tsanta tazauna a saman nan to nice dan haka yazama dole a canza tsari matsayina yafi qarfin haka " d'an juyowa Hamut yayi yadubeta yace " hmmm ashe haka kika d'auka ? to amma inaga kin manta banbancin rufaffen abinci mai zafi da bud'add'e wanda yahuce Siyama zabi gareta har tana qonani a dukkan sassan jikina musamman zuciya ta kyakkyawan wasan dazan buga zefiyin kyau a can kinga kenan Siyama ce tadace a can sabida ita basaura bace ni kad'e keda ita har abada "

Yanagama fad'in haka ya juya yahaye saman cikin takun shi na isa yake haura matakalar benan juyawa Hamidat tayi cikin 'bacin rai takoma gun mahaifiyar ta fad'awa tayi a jikin ta tasaki kuka cikin 'bacin rai tashiga lallashinta had'ida fad'in

" Hamidat kibar kukan nan nasan yadda zanyi kinga waccan Hajiyar wato kakarku duk itace da wannan munafurcin amma zanyi maganin kowa kwantar da hankalin ki kinji " jin kalaman mahaifiyar ta yasatajin dad'i amma cikin zuciyar ta kalaman Hamut ne keyimata yawo tasan tabbas yayi mugun cin zarafinta

Misalin 05:30 aka shirya kai amarya Ammi tayima Siyama nasiha sosai bayan haka Sarki Jabir ma yayi mata sannan mahaifinta a wannan ranar tayi kewar mahaifiyata sosai tasan da tananan itama datayimata nasiha wajan kai Siyama part d'in Hamut hadda su Hajiya Mariya dan suga qwam da Hajiya Fulani uwa uba harda kaka sosai wajan Siyama yayi mugun had'uwa duk da cewa cikin qaramin lokaci akashirya komi duban kowa kaka tayi tace

" to ai se atafi ko damasu ganin qwam damasu zuwa dan Allah to aje mungode Siyama da Hassan sede ta Allah ehe nan kusa zan sake ganin wasu Hassan da Hussain d'in amma banda mai irin halin Hussain "

Haka kaka ta tarkata kowa yazama se Siyama kawai babu jimawa Jakadiya tashiga gaisuwa tafara kaiwa

" Allah ya taimakeki Gimbiya Siyama matar Yarima mai jiran gado Allah yasanyawa wannan aure albarka Allah yabaku Hassan da Hussain a wannan daran ranki shidad'e zan shinfid'a kyallan al'adar masarauta Allah yasa muga abinda akeson gani g........ "

Dakatar da ita Siyama tayi dafad'in " ya isa haka Jakadiya kiyi abinda yakawoki kifita " jin haka yasa Jakadiya saurin miqewa tashinfid'a sannan tafita miqewa Siyama tayi tadubi saman bed d'in afili tace

" hmmmm nice yau zan kwanta a bed d'aya da Hamut kumama wai har a......"

Kasa qarasawa tayi ta rumtse ido ta tana jinjina yiyiwar abun

Mameen Zarah & Sudees ce
[8/19, 5:56 AM] Aunty Fauza: [8/8, 10:03 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah😍: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*


*NA*


*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_



```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*


AND NOW
```MUSAYAR RUHI```



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
[8/9, 1:20 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah😍: PG 79 & 80

Tsayin lokaci Siyama tad'auka tanayin wannan tunanin jin sallamar Hamut yasata dawowa cikin hankalin ta ajiye ledojin hannun shi yayi yacire babbar rigarshi ya aje saman bed itako Siyama se a lokacin tafarajin wani irin bugun zuciya kauda kanta tayi daga gareshi shiko dubanta yayi sosai kafin yayi magana Hamidat tabanko qofar tashigo ganin shigowar Hamidat yasa Hamut saurin janyo Siyama jikin shi sosai yarungumeta yana kissing wuyanta cikin wata irin murya yashiga cewa

" Hayateey a yau ina matuqar farinciki da wannan ranar namatsu kizo a matuqar matse nike dake Hayateey a yau cinyeki zanyi kidaure karkiyimin kuka zan biki a hankali "

Ganin Hamidat a tsaye takasa motsawa yasa Siyama sakar mata murmushi tana rungume a jikin shi shagwa'be murya Siyama tayi tashiga cewa

" kar kadamu Habeetty na a yau komi kakeso zan baka sabida ina matuqar ji dakai na dad'e ina mafarkin wannan ranar ashe zan ganta gas...... "

Kafin taqarasa Hamidat tadakamusu tsawa dafad'in

" ya isa ya isa hakanan wannan wane irin iskancine ? agabana ko kunya ma bakuji hmmmm ke Siyama Wallahi senayi maganin ki tunda kika shiga gonata kai kuma Hamut inasonyin magana da kai "

Sake matse Siyama yayi a jikin shi yace " Hayateey rabu da ita ni banmasan dacewa tanagunba sannan ke kinyarda inje yaufa ke kad'e kaidani " a yanzu kam Siyama tafahimci soyake ya quntatama Hamidat ko maiye dalilin shi oho tafad'i hakan cikin zuciyar ta tsinkayo muryar shi tayi yana fad'in " Hayateey kice wani abu mana "
Cikin kissa tace " babu lokaci Habeetty taje taitajira har zuwa lokacin danaga dama kaji nihdey kacehh tah tafeeh dan Allah zatahh takuraminnhh dan Allah Habeetty na "

Kafin Hamut yayi magana Hamidat tajuya afusace tabar bedroom d'in ganin tafita Siyama tafarayin qoqarin janye jikinta daga nashi kasawa tayi sabida ya matseta sosai cikin 'bacin rai tace

" kai malam ai sekasamu damar sakina ko tundatatafi "
'Dan tsaki yaja yasaketa yace. " dama ai lalurace tasakani riqeki badan hakaba ke baki isa nakai hannuna jikin kiba "

Sake fusata Siyama tayi tace " ai wallahi nice yakamata nafad'i haka sabida ni sabuwa nike fil kaifa sauran watane gaskiya nikam an cuceni da aka had'ani da sauran wata "

Jin wannan kalmar tasaka Hamut jin 'bacin rai fiye da nada cikin 'bacin rai yace
" Siyama kishiga hankalin ki dani idan bahakaba zakisha mamakina ammafa kisani duk abinda kike taqama dashi to nima ina taqama dashi amma akan wannan maganar zanyi miki uziri sabida bakisan komi ba "

Yanagama fad'in haka yanufi toilet babu jimawa yadawo dubanta yayi yace
" kitashi kiyo alwala idan kinga dama " ta'be baki tayi sannan tamiqe tanufi toilet d'in tad'an d'auki lokaci kafin tafito koda tafito yana tsaye saman abin sallar bin bayanshi tayi yatada sallar suna idarwa Siyama tamiqe takoma bakin bed tsayin lokaci yana rero addu'o'i kafin yamiqe yadubeta sosai yace

" ga kayan tarbar amarya nan kamar yadda kowane ango yakeyi ina fatan kema zakiyi duk abinda Amarya keyi ? "

Wani irin kallo tayi mishi kafin tace

" idan ma kana nunanin ni ina d'aukar kaina a matsayin amarya to kayi kuskure sabida ni har abada bazan ta'ba d'aukarka a matsayin miji ba "

Jinjina kai Hamut yayi yatunkarota sosai se dayazo gaf da ita har tana iya jiyo numfashin shi kafin yace

" nine yakamata ince haka bakeba sabida ni senasaka kiji dole ma a qarqashina kike amma nifa babu yadda zakiyi dani amma zanyi miki tambaya 1 wannan farin gyallan yaya zakiyi dashi sabida qimarki za'a nuna anan zaki yarda anunata ko zaki qiya kizubdata ? " wannan yarage naki dan ni bamatsalatabace "

Sosai maganganun Hamut sukasaka Siyama cikin rud'ani sabida tabbas tasan maganar shi gaskiya ce to amma batajin zata iya bashi kanta miqewa tayi cikin sauri jawota yayi tafad'a jikin shi yamatseta sosai cikin mugunta sannan yace

" hmmmm kinanufin nima zan yarda muzama d'aya dakene ? ina bazan ta'bayin hakanba " yanagama fad'in haka yasaketa had'ida turata saman bed d'in yamiqe yanufi kitchen wuqa yad'akko yafito nufota yayi da wuqar ganin shi da wuqa kumagashi yatunkarota yasa Siyama tsorata saurin miqewa tayi cikin tsoro tafara ja baya binta yadingayi har takai jikin bango d'ago wuqar yayi ganin haka yasa Siyama rumtse ido tashiga cewa

" Dan Allah kayi haquri karka kasheni naji nayarda kai miji nane "

Murmushin mugunta Hamut yasaki sannan yace " Siyama qiyayyar danikeyimiki batakai hakaba bazan iya jimiki koda qaramin ciwoba amma natanadar miki hukunci namusamman "

Yanaqarashe fad'ar hakan yajuyo hawa saman bed d'in yayi ya aje wuqar yanad'e hannun rigarshi can sama sannan yad'akko wuqar yada'ba makanshi dede dantsen hannun shi ayko jini yafara shatata saman wannan farin qyallan rumtse ido Hamut yayi sabida yadda wani irin mugun zafi yake shigar shi Siyama kuwa zaro ido tayi tanufeshi cikin sauri yadakatar da ita dafad'in

" dakata karkisake kiqaraso gareni a yau naceci kimarki badan keba sedan Ammi na nayi hakanne sabida bazan iya aikata komi dakeba dan bakikai matsayin ba "

Daga haka yamiqe yana dafe da hannun shi sabida mugun zugin dayakeyi yanufi toilet babu jimawa yafito yafita daga bedroom d'in baki d'aya bin kan bed d'in Siyama tayi da kallo sosai tsakiyar farin qyallan yajiqe da jini wata irin nannauyar ajiyar zuciya Siyama tasauke takasayin magana tunanin ta kuwa tsayawa yayi cik tsayin lokaci sannan Hamut yadawo sanye da jallabiyar bacci mai ruwan qasa dogon hannu gareta hakan yasa babu wanda zai iya ganin yankan hawa saman bed d'in yayi yakwanta daga gefe batare dayacema Siyama komiba

Itako binshi kawai takeyi da kallo qugin da cikin ta keyi yasata tashi d'aukar ledar daya'aje mata tayi tashiga kitchen tahad'o abinda zataci sannan tadawo bayan tagama tashiga toilet tayi wanka tafito tayi shirin bacci itama saman bed d'in tahau ta kwanta nesa dashi sukabar qyallan a tsakiya

Washegari

Duk yadda Jakadiya zatayi wajan sace farin qyallan ya gagara hakanan akafito dashi gaban kowa aiko kafin kace mai cikin masarautar yad'auki murna da sautukan busa sarewa wani saban shagali akashigayi su Hajiya Mariya kuwa baqinciki har zuci kimanin 2 weeks aka d'auka ana shan shagali sabida yadda akayi bikin cikin gaggawa

Turkiya

Hammat zaune cikin office hannun shi riqe da waya yanajuyata zuwacan yamiqe yabugi saman table d'in gabanshi cikin 'bacin rai yace

" wai mai Abiy yakenufi danine shida Ammi ? yau kimanin 2 Weeks amma babu wanda yakirani abun mamaki ma wai hadda Bro na kenan hakan yananufin sun manta dani kenan ' ina hakan bazai ta'ba yiyiwaba "

Cikin zafin rai yashiga kiran wayar Sarki Jabir sedayayi kira yakai sau 3 kafin yad'aga tun kafin Hammat yace komi Sarki Jabir yace

" Furuci d'aya tak nikeso kafurta min shine nasakin Hanan idan ba wannan ba to banason jin komi daga gareka "

A wannan ranar akuma wannan lokacin sabida wannan furucin Hammat yaji wani irin bugu da zuciyar shi tayi wanda shi kanshi beyi tsammanin hakanba bekuma ta'bajin irin wannan bugun zuciyar ba kashe wayar yayi batare dayace komi ba komawa yayi yazauna yanasauke ajiyar zuciya afili yashiga furta

" Hanan saki toma maiye idan nasaketa kay a a bazan iya yin hakan ba karnayima kaina wouta to amma ai basonta nikeyiba kenan Abiy da Ammi fushi sukayi dani kenan ? Idan kuwa hakane yazama dole nakoma Nigeria zancigama dazama da Hanan kodan nahuta tun yanzu nafara kasa bacci sabida tunanin wannan zumar ta Hanan komawa Nigeria yazama dole agareni Abiy na yana matuqar sona danabashi haquri zai yafemin yamayarmin da Hanan "


Hmmmm Hammat kenan to bari mugani idan hakan zai yiwu ko kamakara ko akasin hakan zamugani

Nigeria

A safiyar yau ne
Sarki Jabir yatara kowa cikin babban parlour shi ciki kuwa hadda Hajiya wato kaka bayan yabud'e taron da addu'a sannan yafara dacewa

" Alhamdulillah a yau ne zansanar dakowa wanu 'boyayyan sirri wanda babu wanda yasanshi dagani se Hajiya kilishi yau kimanin 18 years kenan a yau inaso kowa yasani cewa Hanan ba marainiya bace tanada cikakken asali mai kyau wanda kowa zaiso yasameshi kuma yayi tinqaho dashi Hanan 'yace ga Sarki Mahamud Nuhu Wanda kekan kujerar sarautar nimon a cikin qasar Merlin Hajiya abinda zebaki mamaki anan shine Nuhu shine wannan yayan naki wanda ya'bata tun shekaru da dama Hanan satota akayi a ranar sunanta agabaro qasarta da ita wannan kad'an kenan Hajiya a lokacin da aka......"

Kafin yaqarasa Hanan tamiqe cikin kidima da wani irin yanayi wanda ita kanta batasan wannene ba fad'uwa tayi asume kanta Ammi da kaka sukayi sunakiran sunanta Hanan Hanan


Masha Allah Alhamdulillahi ala kulli halin a yau nakawo qarshen Book d'in musayar Ruheey book 1 semun had'u a na 2 amma kafin nan zan bud'e saban group iya masuyin comment sune zansaka koda mutun 2 ne inde zasuyi Comment yawadatar amma duk Wanda yasan yabiya kudin wannan book d'in tun kafin namayar dashi free to yayi min magana nasakashi cikin saban group sabida saukemishi haqqin shi kuma nima in sha Allah zangyara yawan typing nima kaina nasan yayi kad'an duk wacce tasan zatayi comment sosai a book 2 na Musayar Ruheey to tayimin magana anan ne zakuga asalin musayar Ruheey

Nagode sosai masoyana Allah yabar zumunci ana tare 😊🤝🏻💖

Mameen Zarah & Sudees ce 🤝🏻

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment