Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

" wannan yazama dole nayi haquri sabida banida miji amma yanzu inadashi kaga kenan haquri baikamaceniba " jinjina kai yayi yace " hakane nikuma zanyi iya qoqarina wajan samar miki mafita muje mugaida su Ammi "

Kama hannunta yayi suka fita wajan Maimartaba sukafara zuwa bayan sungaidashi suka zauna kiran jakadiya Maimartaba yasa akayi yasata takira duka matanshi babu jimawa kowa ya halarci parlour addu'a Sarki Jabir yayi sannan yafarayimusu nasiha bayan nan yabama su Ammi dama itama nasiha tayimusu sosai anazuwa wajan hajiya hajara da hajiya Mariya cewa sukayi aysu basuda abincewa duk sunfad'i abinda yakamata amma ni inadawata tunasarwa cewar hajiya hajara auran Yarima Hamut shine aure nafarko kuma auran babban magajin Sarki amma banga anshirya wasu daga cikin al'adun cikin masarautar nan ba musamman shinfid'a farin qyalle asaman gadon Gimbiya dan tabbatar da cikar kamalarta dakuma tabbatar dacewa takawo kimarta cikin masarautar nan to yaya abin yake ko akwai wata matsalane ? "

Nisawa Sarki jabir yayi yace " kemakince al'ada ba addiniba don haka babu wannan maganar yin hakan baidaceba zamani yacanza abubuwamasun canza dan haka anbar wannan shirman kuta....... " hakan bazai yiwuba yazama dole ayi Jabir ina raye bazakuzomin dawasu sauye sauye ba dan haka Jakadiya kije kitanadi farin qyalle kamar yadda akasaba sannan kitambayi gimbiya idan tana cikin tsarki idan kuma tana cikin lalura irin ta mata toki tambayeta yaushe zatayi tsarki semujira zuwa lokacin dazatasamu tsarki se a aywatar da lamarin " Mahaifiyar Sarki Jabir kefad'in haka duban Sarki Jabir tayi tace " koda bayan raina banyarda ajanye wannan al'adarba " zama tayi tashiga yima Hamut fad'a shida Hamidat shiko Hamut sosai hankalinshi yatashi sabida bayaso kowa yasan matsalar dayake ciki ayanzu itama Ammin sosai hankalinta yatashi bayan tagama aka sallamesu suka koma part d'in su

Suna shiga Hamidat tanufi cikin bedroom d'in ta cikin 'bacinrai bin bayanta Hamut yayi zama yayi bakin bed yajawota jikin shi cikin lallashi yace " my B dan Allah kiyimin wani taimako d'aya kicema Jakadiya kina cikin jinin haila sannan kice kwanaki 7 kikeyi kuma jiya kikafara in sha Allah nanda kwanaki 6 zansamu mafita gobe doctor zezo daga China inasaran samun lafiya da taimakonshi da yardar Allah dan Allah My B kiyimin wannan koda shine alfarma taqarshe dazakiyimin arayuwata "

Fesar da iska tayi daga cikin bakinta tace " shi kenan amma idan lokacin yayi babu wata mafita fa yaya zakayi " sake dubanta yayi yace " haba B yakikeyin abubuwa kamar babu soyayya tsakanina dake kisanifa danke nikeyin komi hatta aykin pilot kekinsan bashine ra'ayinaba bakuma shine ra'ayin iyayenaba nawa ra'ayin irin na bro nane ra'ayin iyayena kuwa nazama doctor kekuma nazama pilot shine burinki sabida girman son danikeyimiki nabar ra'ayin iyayena nabar nawa nabi naki sabida nazo gareki nayi gaggawa sanadin hakan nafad'o yau gashi sanadin zamana pilot nacikaro da wannan muguwar matsalar wadda zata'iyasaka kimata raguwa nayi tunanin kece mai lallashina kece maizama dani har abada amma segashi ko kwana 1 kinaneman kigagara zama dani kinbani mamaki Hamidat wallahi kinbani mamaki kintambayeni idan kwanaki 6 suka qare bansamu mafitaba yayazanyi ko to kiji da kyau zan sakeki kuma nasanarmakowa cewa banida lafiya ni Hamut bancika namiji ba bazan iya kusantar mace ba zanyi hakan koda kuwa sanadin hakan baqinciki zaisa narasa rayuwata sannan zuciyata zatababbatar mini cewa nafad'i a soyayyar dana gina da yarinyar datun tana 12 yrs har zuwa 23 yrs amma nasamu fad'uwa godiya zanyi miki ko me Hamidat kodiyar tadace dake Thanks har abada hakan zanta furtawa agareki " yaqarashe fad'ar hakan cikin rawar murya yamiqe yafita afusace

Bayan fitar shi Jakadiya tashigo tambayar Hamidat tayi tabata amsa akan cewa tana cikin jini shiko Hamut fita yayi daga part d'in yanufi part d'in Ammi kaitsaye cikin bedroom d'in ta yanufa zaune yasameta itama tana cikin nazari kwanciya yayi saman bed d'in yad'aura kanshi saman cinyarta yasaki kuka maicin zuciya hatta numfashinshi kaucewa yashigayi sabida tsananin kuka sosai Hankalin Ammi yatashi dafa qirjinshi tayi tashiga yime addu'a tsayin lokaci sannan tace

" Hassan daure kaitafad'in Innalinlahi wa'inna ilaihirraju'uuuu koda acikin zuciyar kane kaji Hassanuna dan Allah nasan zuciyarka akwai taushi da sanyi kaji " fad'i yashigayi cikin zuciyar shi ahankali yaji zuciyar shi tanayin sanyi har yafara furtawa a fili tsayin lokaci sannan yatashi zaune yadubi Ammi yace

" Ammi Hamidat zatabarni Ammi ashe Hamidat bazatayimin halacci ba nafara sarewa inaji kamar bazan warkeba kenan bazan iya amsa sunan...... "

Dakatar dashi Ammi tayi tace " haba Hassan nasanka dahaquri kasani idan Hamidat taqika inada tabbacin Allah zaisakamaka dawadda tafita kuma in sha Allah zakasamu lafiya bakata'bayin tunanin Allah zaijarafceka dawannan laluraba kuma segashi yajarafceka kuma in sha Allah zaisake jaraftarka da sauqi ammafa idan ka'amshi wannan qaddarar hannu 2 kayi godiya ga Allah kayi haquri Huseen yacemin gone doctor zaizo in sha Allah zamusamu mafita zaka warke kaji kaje kaci abinci kayimin alqawarin zakaci " jinjina kai yayi sannan yafita binshi dakallo Ammin tayi cikin tausayawa

Hajiya Fulani yau itace da Ayki kamar koda yaushe tashirya tsaf tanufi part d'in Sarki Jabir tana shiga yamiqe daga zaunan dayake zaishiga bedroom cikin sauri tasha gabanshi dandanan hawaye suka cika idanunta tace " dan Allah Maimartaba idan wani abu nayimaka kasanar dani tsayin wasu shekaru baka kulani idan kasakenine kasanar dani dan Allah nasan matsayina " tsaki yaja yabi gefanta yawuce batare dayace komi ba



Inasake tunasar daku cewa banayin typing ranar Friday

Comments and shine please

_Marmyn Zarah Ce_ 👌🏻🤝🏻
*⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*


*NA*


*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_



```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*


AND NOW
```MUSAYAR RUHI```



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*




*Page 7 & 8*




*S* osai zuciyarta taqara shiga qunci jikinta yayi sanyi sosai fita tayi daga part d'in jiki babu qarfi tana shiga part d'inta tanufi bedroom kai tsaye dubanta Fadil yayi cikin damuwa sannan yamaida dubanshi kan Fadila kafin yace komi Fadila tace " a a yaya basekace komiba mucigaba dayima Mom addu'a Allah yayaye mata damuwarta kaji " daga haka tamiqe cikin damuwa tashiga bedroom shima miqewa yayi yabar part d'in baki d'aya sosai hankalin Hanan yayi matuqar tashi sabida jin sautin kukan Hamut datayi a cikin bedroom d'in Ammi kasa kwanciya tayi hakan yasa dole tafito tanufi bedroom d'in Ammi bayan taji fitar Hamut d'in bakinta d'auke da sallama tashiga jin sallamar Hanan yasa Ammin saurin share hawayen fuskarta zama Hanan tayi fuskarta d'auke damatuqar damuwa duban Ammin tayi cikin raunin murya tace

" Ammina tabbas akwai damuwa atare daku da yaya Hamut dan Allah Ammi meke faruwa koda bazan'iya yin komiba wajan kawo mafita ba amma zan'iyayin addu'a dan Allah Ammina meke faruwa ne ? "

Ajiyar zuciya Ammi tasauke tace " haba Hanan babu komi kinji kinsande halin rayuwa watarana farinciki watarana baqinciki dole akwai haka cikin rayuwa karki damu kinji zewuce in sha Allah nan kusa "

Jinjina kai Hanan tayi tace " hakane Ammina amma bakisaba 'boyemin komiba duk abinda yake damunki kafinsu yaya Hamut susani ni nasani ina tunanin dan nakasance mace d'aya tak acikinsu shiyasa kike fad'amin damuwarki sukuma kiboye musu amma yau gashi Ammina tana'boyemin damuwarta amma tabbas zanshiga damuwa sosai yayana Hamut wanda yake sakarmin fuska yayimin murmushi idan inacikin damuwa yasani farinciki yau gashi yanacikin damuwa banida hanyar sakashi murmushi tabbas dole nashiga damuwa " miqewa tayi jiki a sanyaye zatabar bedroom d'in har takai bakin qofar Ammin tace

" Hanan dawo kizauna " komawa tayi tazauna cikin sanyin jiki yimata nuni tayi tada kwanta saman cinyarta kamar yadda tasaba babu musu takwantar dakanta saman cinyar Ammin ajiyar zuciya Ammi tasauke sannan tace " tabbas inada damuwa Hanan kuma damuwar akankine sauran kad'an kikammala karatunki dakin gama aure zakiyi bansan kokinada wanda kikesoba nikuma banason tauye miki dukkan abinda kikeso amma bazanji dad'iba idan baki aure wanda nikeso ki'auraba tsayin shekaru nike jiran wannan ranar amma bazan iya tusasakiba dukda faruwar hakan zaitona wani sirri wanda banaso yafita amma yin hakan shine zai dauwamarmin da wacce nike tsananin qauna ataredani har abada dukda cewa zan fuskanci qalubale sosai acikin Masarautar nan amma zanjure dan cimma burina kinji damuwata Hanan shikuma Hassan bansan meye damuwarshi ba nima yaqi sanar dani hakan yasakesakani cikin damuwa "

Tashi zaune Hanan tayi tashare hawayen fuskarta tace " Ammin koda akwai wanda nikeso kamar raina wallahi zanfitar dashi na'amshi za'binki zankumayi farincikin za'bin Ammina balle babu kowa ataredani Ammi karatuna nasaka agaba Ammina na'amshi za'binki tun yanzu Ammina kiyi farinciki shikuma yayana Hamut muyimai addu'a babu abinda yafiqarfin addu'a sannan Ammina wane sirrine zaitonu kuma wace irin matsala zaki fuskanta ? "

Murmushi Ammin tayi tarungumota cikinta tace " karki damuwa zuwa lokacin zakisan komi ayanzu banida amsha nayi farinciki sosai kuma nasakeyima Allah godiya dayabani ke matsayin 'ya agareni Allah yayi miki albarka tashi kije ki kwanta kinji " murmushi Hanan tayi tasumbaci kuncin Ammin sannan tamiqe tayimata sedasafe sannan tafita

Jiki sanyaye Hamut yashiga part d'in nashi bin inda akajera kayan abinci dana motsa baki yayi sakejin damuwa yayi cikin bedroom d'in shi yanufa yana shiga yarage kayan jikin shi yashiga wanka tsayin lokaci sannan yafito yana dafe da mararshi sabida yadda yakejin ciwo ko yaya yamotsa shiryawa yayi cikin shigar bacci sannan yafito bedroom d'in Hamidat yashiga zaune yasameta tanayin waya da momcy ta cikin sanyin murya yace

" idan kingama kifito parlour ina jiranki " zuyawa yayi yafita wajan abincin yanufa leder dayagani agefe yabud'e kajine manya guda 2 aciki da yoghurt mai sanyi sekuma nau'ikan abinci kalakala agurin kasa koda qwaqqwaran motsi yayi sabida yadda yaji zuciyarshi tasake shiga qunci sosai tuno maganar Ammi yayi da alqawarin dayayi mata akan zaici abinci hakan yasa yashiga zuba abincin cikin sanyin jiki yafara d'ibar abincin yanaci badan yanajin dad'in shiba sedan alqawarin dayayima Ammi kawai yasa yakeci dede lokacin Hamidat tafito ahankali take taku kamar maitausayin qasa sanye take cikin kayan bacci masu bin jiki sun bayayyana surar jikinta sosai tana qarasowa tazauna daf dashi sosai kwantar dakanta tayi saman kafadarshi tad'aura hannunta saman sumar kirjinshi wadda takwanta luf cikin lokaci kad'an taji kasala tamamaye jikinta ajiyar zuciya Hamut yasauke yace

" yakamata muci abinci ko ? " shagwa'be fuska tayi tace " jikina babu qarfi please kabani " rumtse idanunshi yayi sannan yace shikenan gyara zaman naki ahaka bazai yiwuba " gyara zamanta tayi ledar kajin yajawo yabud'e duban kaji tayi tace " a a my D wannan basuda amfani agareni ayau kabari sezuwa ranar daka warke aranarne zanjini amatsayin cikakkiyar amarya ba yauba yanzu irin abincinka zanci " sosai maganar tadaki zuciyar Hamut amma beko iya cewa komiba bata nashi abincin yashigayi har taqoshi sannan yamiqe yanufi bedroom batare dayacemata komiba yana shiga yakwanta saman bed idanunshi nakallon sama hawaye suka shiga gangarowa tagefan fuskarshi babu jimawa Hamidat tashigo cikin bedroom d'in hawa tayi saban bed d'in takwanta saban qirjinshi tashiga shafa sumar qirjinshi ganin hawaye nasauka tagefan fuskarshi tace

" haba my D nifa karkaga lefina iya gaskiyata nafad'a idan na'boyemaka najekuma na'aykata kuskurefa yaya zakad'aukeni ? Wallahi bazan iya jure lokaci maitsayi batare dasamun kulawar namijiba My D kafahimta naqosa namatsu dazuwan wannan ranar yawancin dare inakasayin bacci sabida tasowar shi'awata tunaka kawai zanyi naji yanayina yacanza My D balle yau gani gaka dan Allah kasanaji sassauci koyayane tunda har kaga na'iyafurtawa duk irin kunyar mace tabbas akwai matsala please help me my D "

Wani irin kunlewa yaji zuciyarshi tayi gawani irin zafi datashigayime jan numfashi yashigayi dasauri dasauri dafe setin zuciyar tashi yayi yashigayin magana cikin wahala

" karkidamu My B nayimiki alqawarin bazan bari kicutuba koda bansamu lafiyaba zansamar miki damafita in sha Allah kuma yau zanyi iya iyawata nasaki kibanbance sauran dararan dasukawuce abaya da wannan daran nayau " daga haka yajawota sosai yasaka bakinshi cikin nata yafara sarrafata sosai yake aykamata saqonni cikin salo ahaka kamar zai'iya aywatar dakomi amma kass itako Hamidat sosai tarikice sake mannewa takeyi ajikin shi sosai yatsinci kanshi dajin tausayinta Zameta yayi daga jikin shi yashiga toilet cikin Sauri tashi tayi zaune tanasauke numfashi sosai takecikin tsananin buqata Shiko yanashiga zama yayi yadafe kanshi yanasakin muguwar ajiyar zuciya gazafin zuciya yanaji sosai Kamar zuciyar tashi zata qone sabida zafi tsayin lokaci sannan yad'auro alwala yafito bai Kalli inda takeba yashinfid'a abin Sallah yatada sallah sauka Hamidat tayi daga bed d'in tabar cikin bedroom d'in Cikin wani yanayi Shiko Hamut kwana yayi sallah awannan daran hakama Hammat da Ammi duk sunayime addu'ar samun lafiya

Washegari misalin 3pm doctor ya'iso Nigeria kasancewar tun jiya yataso Hammat neyaje filin jirgi dakanshi yataho dashi koda Suka'isa cikin masarautar nanfa gulma tatashi kowa yanatambaya me wannan d'an China yazoyi cikin masarauta ayau Kiran jakadiya hajiya Mariya tayi cikin part d'inta itama hajiya tana cikin part d'in duban jakadiya sukayi hajiya Mariya tace

" jakadiya tabbas akwai abinda ake 'boyemana acikin masarautar nan naga hajiya Salma tashigo cikin masarautar nan jiya afusace hadima larai tacemin taji tanacema gimbiya Hamidat bazai yiyuba bazatabari 'Yarta tazaunada namiji irin maimatsala ta Hamut ba tabbas akwai wata aqasa dubada daga airport akawuce dashi asibiti wai yasamu accident segashi yadawo babu alamar ciwo jikinshi Sekuma maimartaba yafara qoqarin hana aywatar da al'adar shinfid'a farin gyalle bayan haka gimbiya tace tanayin jini senan dakwanaki 6 bayan Kowa yasan yanzu ba'ayin haka anatsara komi a yadda yakamata Lalle akwai wani abu hmmmm ayau kam nizan rikita komi jakadiya inaso kiyi duk yadda zakiyi kigano mana wani abu idan kikayi hakan kinada kaso maitsoka nikuma zanje wajan hajiya nazugata Sena rikita komi "

Tashi jakadiya Tayi tace " nikuma sena ganomuku komi "fita tayi cikin sauri part d'in Hamut tanufa zaune tasamu Hamidat itada hadimanta gaidata tayi cikin girmamawa sannan tad'an zauna jim bataga alamar cewa Hamut yana cikin part d'in ba hakan yasa tatashi tafita zuwa part d'in Ammi nanma babu Hamut ba Hammat se Ansar da Hanan zaune gaida Ammi tayi sannan tace

" Allah shi taimakeki Allah yaqaramiki lafiya dama zuwanayi natambaya naga anyi baqo maiyakamata akawo mishi tunda naga shi bad'an Nigeria bane dole za'asamu banbancin cima "

dubanta Ammi tayi tasaki murmushi tace " a a wannan baqon Husain ne kuma lamarine na aykinsu dan haka shi yatanadar mishi komi kuma kinsan halin Husain bayason anashiga cikin harkarshi idan kuma zakishiga tojeki kitambayeshi babu ruwan hajiya kilishi "

zaro ido Jakadiya tayi tace " ina nina isa yarima Hammat a a nabarki lafiya " daga haka tamiqe tafita binta hanan tayi dakallo sannan tadubi Ammi tace " Ammina nifa gaskiya wannan jakadiyar banfa yarda da'itaba tafiye gulma " Murmushi Ammi tayi tace " ay bama itakad'eba akwasu dayawa kede shi'anin gidan sarautar se ahankali " tsaki Ansar yaja yamiqe yace " Allah yasa nakama mata tana gulmana wallahi daga ranar senasaka ancanzamata kamanni " daga haka yabar parlour afusace girgiza kai Ammin tayi tace " shegiyar zuciya kamar Husain shide hassan babu ruwanshi " murmushi Hanan tayi tace " hakane amma shikuma akwai jin kai da miskilanci " murmushi Ammin tasakeyi tace " ay wannan jinine Hanan sarauta gaba da baya kinga kuwa dole ayi jin kai " murmushi Hanan tasakeyi tace hakane kam

a part d'in Hammat doctor yake duba Hamut tundayazo yakeyin aykin har dare amma kamar babu nasara misalin 9:pm doctor yadubi Hamut da Hammat yace

" gaskiya sede kayi haquri nayi duk abinda yakamata nayi amma wa'innan jijiyoyin sunriga sun mutu kwata kwata bazasu sakeyin ayki ba kayi haquri zanbaka magani zakadenajin ciwon marar k......" kafin yaqarasa Hamut yamiqe yace banabuqatar maganin naka nagode Hammat kasallameshi kasa akaishi masaukinshi zuwa safe yakoma china kuje kudawo inason magana dakai "

ganin yadda ranshi ya'baci yasa Hammat yin abinda Hamut yace bayan yasallameshi yadawo zama yayi kusada Hamut d'in idanunshi sunyi jah sabida tsananin 'bacin rai kafin Hammat yayi magana Hamut yadubeshi cikin damuwa yace

" d'an uwana ayau inaso kanunamin qarfin dangantaka nasan babu alfarma agaremu tsakanin ni dakuma kai amma ayau zanroqeka alfarma nakumasan zakayimin ita sabida girman alfarmarne yasa naroqeka nasan duk abinda nikeso kaima shi kakeso natabbatar dahakan ayauma zansake tabbatarwa!!!!!!!!!!! Hammat Inaso kayi auran sirri kaida matata Hamidat ko ita banaso tasan haka idan kayi haka zan......."

" dakata Hamut bazanyiba bakuma zan iyaba kai kasan banida ra'yin mace balle matarka Hamidat yarinyar danayi matuqar tsana ina gaskiya bazan iyaba "

miqewa Hamut yayi yashare hawayen fuskarshi yanufi hanyar fita ja yayi yatsaya yace " tabbas ayau natabbatar dacewa Hammat bazai iya yin musayar ruheey da Hamut ba kasani idan narasa Hamidat tabbas nima zakarasani dama iya haka qarfin dangantakarmu take dukda rayuwa damukayi a ciki d'aya kuma lokaci d'aya dama ba uwa d'ayace tahaifemuba dabazanji damuwaba dan kaqi ceto rayuwataba to amma kasani tabbas zantafi nabarka " hannu yasaka zai bud'e qofar Hammat yayi saurin kamo hannunshi dubanshi yayi yadda hawaye suka wankemai fuska sharemai hawayen yayi yace " zanyimaka duk yadda kakeso amma kasani zuciyata bazata ta'ba son Hamidat ba "

ajiyar zuciya Hamut yasauke yace " hakan nikeso duk ranar dakasota bazan iya yafe makaba inaji ajikina zanwarke nangaba in sha Allah zansaki Hamidat saki batare dakowa yasaniba zamuje ad'aura maka aure da'ita ayau tunda batada iddata akanta zandawo nace mata namayar da'ita kuma nasamu lafiya zakazama miji agareta amma nasirri duk dare zakajemata amatsayin nine kuma yazama dole kakusanceta amatsayin nine tabbas zanji babu dad'i cikin zuciyata amma hakan zaifimin sauqi akan ace wanine ta'aura duk ranar dana warke zakasaketa tadawo gareni komi dad'ewa "

rumtse ido Hammat yayi yace " tayaya Hamut idan bata ganeni takomiba zata ganeni ta yanayi dakuma launin idanuna Hamut tayaya zan'iya kusantar yarinyar dakabama zuciyarka tun tana 'yar qaramarta k........" dakatar dashi Hamut yayi dafad'in zan'iya sadaukar dakomi akan farincikin Hamidat kuma kai d'an'uwanane idan wanine yayi hakan to wallahi sena kasheshi sannan maganar lauyin idanu natanadi ledar dazakasama idanun naka yanayi kuma kayi qoqarin setashi yadawo irin nawa idan kayi haka zancigaba da rayuwa akasin haka kuma mutuwa zanyi zanje nayima Ammi bayanin komi ita kad'e nikeso tasani sabida banta'ba 'boyemata komiba bakumazanfara akan wannan ba "


Comments and shire please
[8/19, 5:55 AM] Aunty Fauza: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*


*NA*


*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_



```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*


AND NOW
```MUSAYAR RUHI```



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



*Page 9 & 10*




*Y* ana fita yanufi wajan Ammin yana shiga Hanan da Ansar dake parlour sukayi saurin miqewa suna gaidashi bai kallesuba baikumace komiba abinda bahalinshiba yana shiga yasamu Ammi tsaye da'alama tana cikin tunani sosai zama yayi sannan yace " Ammi " saurin juyowa tayi sabida ko sallamar shi batajiba sabida tana cikin tunani saurin zama tayi agefanshi kafin tayi magana yayi saurin cewa " shima wannan doctor yacemin bazan warkeba Ammai nikuma har yanzu bancire raiba inaji ajikina zanwarke ko Ammi? " yaqarashe fad'ar hakan cikin rawar murya " saurin kamo hannunshi Ammi tayi tashiga lallashin shi ajiyar zuciya yasauke mai qarfi yace

" Ammi yaya zanyi banaso kowa yasan matsalata bayan ku shine nayanke wata shawara idan har akayimin hakan zansamu sauqin rad'ad'in zafin da zuciyata keyi idan kuma bansamu hakanba tabbas rayuwata tanacikin hatsari Ammi inaso Hammat ya'auri Hamidat amma auran Sirri batare dasanin kowaba koda ita Hamidat d'in banaso tasani koda Hammat zeje mata inaso yaje amatsayin ni bayan nasamu lafiya seyasaketa tadawo gareni idan akayi hakan shikenan babu wanda zaisan inada wannan lalurar kinji Ammi banason auran yawuce gobe sabida kinga nanda kwanaki 6 zasusake tasar da wannan banzar al'adar "

ajiyar zuciya Ammi tasauke tace " haba Hassan karson Hamidat yasaka kafarayin abu cikin rashin tunani kana raye shima Hussain yana raye kuyi tarayya da mace 1 d'aya gaskiya hakan babu tsari Hassan nasan kishima bazai barka kazauna lafiya ba son dakakeyima Hamidat yakai matakin dazakayi mugun kishi akanta kagakuwa hakan zai'iyajawo muku rashin jituwa kaida d'an'uwanka bazanso hakaba kuntashi babu maijin kanku tun yarinta bazanjuri ganin akasin hakaba bayan girmanku kacanza wani tunanin kaji wannan tunanin naka baiyiba "

miqewa yayi zaifita cikin zafin zuciya saurin dakatar dashi Ammi tayi dafad'in " dawo kazauna Hassan ashe akwai ranar dazakanunamin fushinka akaina Hassan karkasa naji cewa Hamidat batadace dakaiba idan har zaka'iyayin fushi dani akan lamarinta to tabbas zance bakudaceba inama hamidat tanasonka kamar yadda kakesonta datarufamaka asiri data zauna dakai natsawon lokaci ahaka dakarfin buqatar tata yagudu daga gareta sabida tsananin soyayya amma babu komi itama tanada uziri mai qarfi sabida kowace mace da'irinta naji zanyarda kasaki Hamidat Hussain ya'aureta amma inada nawa sharad'in nafarko yazama dole kasanar ma Hamidat kalmar saki taji da kunnanta sabida sakin yahalarta dama batada idda akanta sannan kasan yadda zakayi kar wanda yaji labarin sakin sannan karubuta takardar sakin kakawomin kuma kasan yadda zakayi tajikamar kaine kasake mayar da'ita amatsayin mata sannan kuma yazama dole kakoma bedroom d'in sama sabida gujema abinda idanunka zasugani kosuji tsakanin Hussain da Hamidat sannan yazama dole kaguji ta'ba koda hannunta sabida tatashi daga matsayin matarka a lokacin sharad'i na 2 wanda kuma shine maiwuya agareka nasani amma idan kace a a tonima zance a a inaso ka'auri Hanan kuma nima agobe nikeso "

" zaro ido Hamut yayi yadubi Ammi yace " ni na auri Hanan Ammi dan Allah kicanza wani sharad'in bazan iya yin wannan ba matsayin qanwa nad'auki Hanan bayan wannan babu wani kuma gata tayi yarinya dayawa Ammi kinsan banason auran qaramar yarinya batun yanzuba sannan kuma tayaya zan'iya duban Maimartaba dasauran mutane nace zanqara aure bayan kwanaki 2 kacal dayin aure na dole za'ayimin tambayoyin dabani da amsarsu sannan kinsan al'adar Family mu bakata'ba auran wadda ba nijinmuba kuma kinsan Hanan bajinimubace dan Allah Ammi kicanza wani sharad'in naji duk wanda kika fad'i akan Hamidat duk zancikasu in sha Allah amma wannan akwai matsala "

zama Ammi tayi tace " duk nasan dahaka kai babu ruwanka kabarni dakomi kuma ay dakake maganar Hanan tayimaka yarinya sosai aykai yanzu yarinyar yadace dakai sabida itace bazatadamu dawani haqqi nata na auratayya akankaba hasalima tsoran lamarin zatad'ingayi idan baka kulatabama natsuwa zatasamu kaga kenan har zuwa lokacin dazakasamu lafiya bazata nuna qosawaba sannan naji kacigaba dad'aukar Hanan matsayin qanwa zanfijin dad'in hakan dan nasan bazaka tsanetaba idan kasamaranka cewa qanwar kace tun tuni nakeson ka'auri Hanan amma senaga hankalinka yanakan Hamidat kuma kazurfafa sosai shiyasa nabarka nafarayin tunani akan Hussain amma shi inajin shakka akanshi bashida yatsani Hanan sosai fiye dakima nikuma banason Hanan tasha wahala ko kad'an itad'in Amanar zuciyatace Hassan "

saurin kallon Ammi Hassan yayi yajinjina kai yace " amma Ammi nifa gaskiya koda nawarke banajin zan'iya yin mu'amalar aure da Hanan gaskiya zanji kunyar lamarin qanwata wadda narena haba Ammi meyasa baki kai tunaninki kan Ansar ba shine dede ita kuma sun shaqu sosai "

mirmushi Ammi tayi tace " nafika sanin haka ni zuciyata kai taza'bar ma Hanan ba kowaba sannan magana kan bazaka'iya sauke mata haqqintaba bayan kasamu lafiya wannan bayanzu yakamata kayanke hukunciba kajira zuwa lokacin sekabani amsa asannan ne zangamsu daduk maganarka idan ka'amince danawa sharad'in tonima na'amince danaka kuma zanji dakomi "

tashi tsaye Hassan yayi be dubetaba sabida baiji dad'in sharad'in nata na 2 ba yace " na amince " daga haka yanufi hanyar fita dede lokacin Hussain yashigo duban fuskar Hassan yayi yaga babu walwala ajiyar zuciya yasauke cikin zuciyar shi yace " Allah yasa Ammi bata amince dawannan mugun tunanin nakaba " zama yayi a'inda Hassan yatashi yace " Ammi kinji wani banzan tunani da Hamut yayi ko hmmm tayaya zan'iyayin

Please Login or Register in order to submit comment