Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakan? " dubanshi Ammi tayi tace " ayko yazama dole kayi sannan inaso kasa aranka cewa aure ne zakayi nad'ind'ind'in da Hamidat banawani lokaciba kamar yadda Hassan yake tunani nasan daga lokacin daka auri Hamidat kishi zaisa Hassan yafarajin son hamidat yana raguwa cikin zuciyar shi zuwa wani lokaci zai manta da'ita daganan semusanar dakowa komi shiyasa nabashi umarnin auran Hanan dan kar yayi 2-0 " miqewa Hussain yayi yace

" maine Ammi Auran Hanan ga Hamut ina Ammi zakisaka yarinya taqara renamu yarinya qarama gaskiya ni kam bangoyi bayan hakaba sannan bazan iya yin auran dindindin da Hamidat ba sabida banasonta ko kad'an kuma bazan sotaba wallahi badan karfin soyayyar danikeyima Hamut ba dabazanyi wannan auran sirrin ba amma zatagane shayi ruwane wallahi senayi maganinta kuma ni bazan iya auranta na dindindin ba yana warkewa zansaketa suqarata can koma yabar sonta nikam babu ruwana " daga haka yanufi hanyar fita girgiza kai Ammi tayi tace

" jeka masifafan banza kawai aykai dama ba'ataba dedetawa dakai kwata kwata bakada fahimta wannan zuciyar taka maizafin tsiya Allah yanunamin lokacin dazatayi sanyi natabbata dakaine nasakama irin sharad'in Hassan bazamu kwashe lafiya ba ni bansan ina kakakwaso wannan zuciyar banzarba da shegen taurin kai ga kafiya kayimata duk abinda kagadama ita taja dama ance idan bakayi sharar masallaciba tokayi tarumfar kasuwa dama kaine dede Hamidat d'in "

sosai Hammat yaji zuciyar shi tasakeyin zafi sosai yana fita yadubi inda Hanan da Ansar suke kiransu yayi sukataso cikin sauri babu magana yafalle Ansar damari yace " maganar mekukeyi kasa kasa kamo kunnan Hanan yayi yamurd'e daqarfi har sedataji kamar zata saki fitsari sabida azabar zafi qara tasaki hakan yasa Ammi saurin fitowa kafin taqaraso Hammat yayi magana kasa kasa yadda Ammin bazatajiba " idan har Ammi ta tambayeki akan cewa kinason Hammut kikace eh to wallahi sekinyi nadama " saurin sakinta yayi yafita daga parlour kafin Ammi taqaraso kuka Hanan tasaki dede lokacin Ammin taqaraso rungumeta tayi tashiga lallashinta itako kanta yad'aure tarasa gane mai Hammat yake nufi tayaya zatace batason Yayanta wanda tafiji dashi duk cikin su

tofa yaya kenan kuyi haquri dawannan sunqi bamu wuta wannan kad'e nasamuyi sabida babu wuta shima sedanakai cajin wayar in sha Allah gobe zanyimuku Akwai banbanci idan basubamu wutaba zankai carjin in sha Allah kuyi haquri badaga ni bane daga nefa ne naso page d'in yau yafi haka yawa to amma yaya zanyi tunda babu carji awayar Affuwan

sannan gawata sanarwa wata baiqar Allah wato Zarah bala tayi alqawarin biyama mutun 2 kudin book amma wanda yayi sharhi mai kyau akan book d'in duka biyu bawai wannan book d'in kad'e ba zaku'iyayin sharhin akan ko wanne book d'in daga Mugun Sartse return har Musayar Ruheey Allah yabama mai rabo sa'a

Comment and shire please

_Marmyn Zarah Ce_ 👌🏻🤝🏻
[8/19, 5:55 AM] Aunty Fauza: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*


*NA*


*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_



```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*


AND NOW
```MUSAYAR RUHI```



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*




*Page 11 & 12*




*S* akin ajiyar zuciya Hanan tayi cikin sanyin muryarta tace Ammi babu komifa ay idan dasabo nasaba da halin yaya Hammat " zame jikinta tayi daga na Ammi ahankali kai tsaye bedroom tanufa bin bayanta da kallo Ammi da Ansar sukayi cikin sauri Ansar yataso yanufo Ammi cikin damuwa yace Ammi wai yaushene zamu tafi Skul mubar qasar nan baki d'aya muhuta da zalincin Yaya Hammat " wata irin ajiyar zuciya Ammi tasauke sabida se yanzu tama tunadacewa Sarki Jabir yasanar da ita maganar tafiyar su Hanan Skul anan kusa gakuma wannan lamarin to yaya kenan duban Ansar tayi cikin kulawa tace " karka damu nan kusa zakutafi tunda Maimartaba yayi min maganar tun kwanaki dasuka wuce yakumace saura kadan komi yagama kammala ammafa bawaje d'aya zakuyi karatu da Hanan ba " zaro ido Ansar yayi kafin yasakeyin magana Ammi tadakatar dashi da hannu sannan tanufi hanyar fita daga part d'in Kai tsaye part d'in Sarki Jabir tanufa takuwayi sa'a yana ciki d'ago idanunshi yayi yadubeta sannan ya'amsa sallamarta idasa shiga tayi tazauna gefanshi cikin girmamawa suka gaisa sannan tanumfasa da'alama wani nazari takeyi bai katsetaba kimanin 10 minutes sannan tafara dacewa

" Maimartaba wani babballamari ne yakawoni nikam narasa mafita sabida lamarin yacikaro da wannan babban boyayyan sirrin namu Wanda babu wanda yasanshi daga Allah sekuma ni da Kai Hassan yazomin dawata magana nikuma nayiwata subutar baki akan lamarin Wanda idan hakan takasance tofa yazama dole wannan boyayyan sirrin namu yafito fili fitowar shi kuwa wata babbar matsalace wadda zata haddasa tashin hankali cikin masarautar nan sannan musamu babbar matsala Ni da Kai wajan Mama shine nazo muyanke shawarar datadace "

Miqewa tsaye Sarki Jabir yayi yashiga kaiwa da komowa sannan yadubi Ammi yace " Hajiya Kilishi tokuwa koma meye wannan yazama dole abarshi dan banshirya shiga cikin tashin hankali ba yanzu lokacin bayyana wannan sirrin baiyiba idan lokaci yayi nida kaina zan bayayyana komi sanar dani wane lamarine Hamut yazomiki dashi ? "

Sake sakin ajiyar zuciya Ammi tayi sannan tashiga sanar dashi wannan lamarin duka sosai Sarki Jabir yashiga kallonta cikin alamar
tuhuma sannan yace

" Tayaya hakan zata yiwu hajiya Kilishi ? hmmm kodama babu wani boyayyan sirri tayaya kike ganin Hamut zai iya jure kallon Hamidat a matsayin matar Hammat ta sirri bayan kinfikowa sanin yadda yake azabar sonta inada tabbacin bazai iya jurewaba me kike tunani idan lamarin ya bayyana bayan wani lokaci mai jama'ata zasu d'aukeni karfa kimanta cewa ni Sarki ne ko yaya baikamata asameni dawata 'barakaba sannan kisan wani abu idan har muka amince dahaka tofa babu shakka wata lalurarce zatakama Hamut badda wadda yake ciki yanzu sannan a qarshe kisani Hanan batadace da Hamut ba idan kikayi duba da wannan sirrin wannan lamarin bazai ta'ba yiwuwaba kibarni da Hamut nasan maizanyi shikuma Hammat dama baso yakeyiba Hanan kuma nanda 1 week zata tafi Skul itada Ansar lokaci d'aya zasutafi amma kowa waje daban Ansar Saudiyya zashi sabida hakan yake ra'ayi itakuma Hanan batada za'bi shine naza'bar mata dakaina ita Turkiya zata dan haka kufarayin duk wani shirye shirye "

Daga haka yabar parlour binshi da kallon Ammi tayi tsayin lokaci tana zaune sannan tamiqe takoma part d'in ta tana shiga tasanar dasu Hanan maganar tafiya Skul sosai kowa yayi murna cikin farinciki Hanan tace

" To Ammi amma maiyasa ba'a had'amu waje d'aya ba ni Turkiya shikuma Saudiyya ? zamufijin dad'i idan waje d'aya muke "

Murmushi Ammi tayi tace " to anki had'aku d'in salon kuji dad'in yin shiririta ko kamar yadda kukeyi nan dubi Ansar yaci ace tuni yarigaki tafiya Skul amma sabida shiririta yatsaya wai shi dole seya jiraki kinga kenan idan aka had'aku shiririta zakuyi " Ammi nagama fad'in haka tanufi bedroom dede lokacin Hammat yashigo ganin shi yasa Hanan saurin juyawa dakatar da ita yayi dafad'in " zonan Hanan " jiki babu kuzari tajuyo tanufoshi zama yayi kafin ta'iso gareshi yace

" Had'omin abinci kuma saura kiyimin shirme " babu musu tanufi kitchen abinci kala kala tahad'o mishi dan tasan halin shi kafin yazauna yaci abinci dawuya amma idan yazauna yanaci sosai bakamar Hamut ba dabayason cin abinci mai nauyi cikin natsuwa ta'aje komi agabanshi sannan tashiga bubbud'e mishi cikin sanyin murya tace " wanne zakaci yaya " dubanta yayi fuska tamke yace " yau kuma wata sabuwar fitsararce kikazomin da ita ? zakizubamin abinci ko senayi ball dake ? "

Cikin rawar jiki tashiga yin abinda yace faracin abincin yayi cikin yanayi kamar bayaso tsayin lokaci sannan yagama har yakammala cin abincin Hanan tana gefanshi kamar kodayaushe har seyagama sannan takwashe kayan yauma haka bayan takwashe kayan tanufi kitchen Ansar yadubeshi cikin d'anjin shakka yace

" Yaya Hammat nanda 1 week zamutafi Skul nida Hanan ni Saudiyya itakuma Turkiya sake tamke fuska yayi sosai yamiqe cikin sauri yanufi bedroom d'in Ammi shiko Ansar duban Hanan yayi yace " zuwa rana irin tayau zamuga wanda yaya Hammat zai dingayima zalinci " batare da Hanan tace komiba tanufi bedroom Hammat yana shiga Ammi tadubeshi tun kafin yayi magana tace

" To uban masifa maikuma yafaru ? " sake tamke fuska yayi yafesar da iska daga bakinshi sannan yace " Amma Ammi baikamata nasan lokacin tafiyar yaran nan Skul ba sede naji lokaci d'aya kuma asama gaskiya hakan baiyimin dad'i ba "

Sosai Ammi take kallonshi cikin mamaki kafin tace " to ay banice zakayima wannan tambayar ba mahaifinku zakayima tunda shine yashirya komi nima sede naji yace nan da 1 week zasutafi kuma ayni banga dalilin wannan tuhumar takaba tunda kamar kaga hanjin cikin su kakeji " jin haka yasa Hammat fita rai 'bace binshi da kallo Ammi tayi afili tace " ikon Allah wannan hali naka Husain Allah yacanzamaka shi "

Cikin tsananin damuwa Hamut yayi sallama cikin part d'in Sarki Jabir gaidashi yayi cikin girmamawa sannan yazauna dubanshi Sarki Jabir yayi sosai yaji zuciyar shi babu dad'i sabida yadda yaga Hamut d'in yayi muguwar rama kamar wanda yad'auki lokaci mai tsayi yana jinya ajiyar zuciya Sarki Jabir yasauke sannan yace

" Hamut dukda naga bakadawata lafiya amma hakanan zakayi haquri kajagoranceni wajan wani mihimmin taro wanda za'ayi a Jodan nanda kwanaki 3 zakatafi amma taron zai d'auki kusan 2 weeks anayin shi bayan angama inaso kazauna acan kahuta kaji idan matar ka zata'iya binka sekutafi tare idan kuma tace a a shikenan bazamu matsamataba amma tafiya da'ita zaifi kodan maganin wannan matsalar banzar al'adar zanturamaka doctor wanda zaid'inga dubaka acan nasan zakaji dad'in zama a can Hassan kasani damuwarka tamkar damuwarmuce idan kasakadamuwa cikin zuciyar ka tamkar muma kajefamu cikin damuwarne kad'auka wannan wata jaraftace daga Allah kuma Allah bayajefama bawanshi wata jarafta face se bawan yazama yanada imani idan har kayi imani tofa dele se Allah yajarafceka yagani zaka'iya cinye wannan jarabawar Hassan nasanka akwai haquri dan Allah kaqara akan wanda nasanka dashi ka'aje wannan shawarar da zuciyar ka take rayamaka akan wai Husain yayi auran sirri da matarka Hamidat wannan babu hanyar billewa acikinta kacigaba dayin haquri watarana se labari tashi kaje Allah yayi maka albarka "

Sosai Hamut yaji jikinshi yayi sanyi zuciyar shi tasake karyewa cikin rashinjin karfin jiki yamiqe yafita kai tsaye part d'in shi yanufa yana shiga idanunshi suka sauka kan Hamidat kauda kanshi yayi yanufi bedroom muryar Hamidat tadakatar dashi dafad'in

" My D ina buqatar shan iska koda nasamu sauqin abinda ke damun jikina " rumtse idonshi yayi cikin jin zafin furucinta yace " kina'iya fita sannan inaso kishirya nanda kwanaki 3 zamutafi Jordan Maimartaba yaturani zan wakilceshi wajan wani taro " tsaki Hamidat taja tace " hmmmm nikam badan Maimartaba bane yace muje danace kaje kai d'aya kawai sabida koda nabika bansan wace irin rayuwa zamuyi dakaiba matsayin mata ko qanwa amma zanbika sede inaso daga yau nazama tamkar qanwa ceni agareka ba mata ba sabida bazaka iya bani abinda miji zaibama mataba qanwa kuwa kaga babu wannan lamarin kwata kwata ammafa idan maganata tayimaka zafi kayi haquri yaya Hamut nide nasan gaskiya nafad'a dazaran mundawo yazama dole kasamu mafita kasan wannan "

Tana gama fad'ar haka tamiqe tabar part d'in sosai Hamut yaji wani irin zafi cikin zuciyar shi baisan sanda yaji wasu irin zafafan hawaye masu quna suna sauka saman kyakkyawan kumatun shi ba daqyar ya'iya d'aga qafarshi yanufi bedroom cikin kuncin zuciya

Washe gari misalin 10:am Hammat yashiga part d'in Maimartaba duban hajiya hajara yayi dake gefan Sarki Jabir yatamke fuska sosai yace " ina buqatar zanyi magana da mahaifina kuma banabuqatar kowa " cikin sauri Hajiya hajara tamiqe tafita daga part d'in duban shi Sarki Jabir yayi yace

" Wai kai Hammat yaushe zakabar wannan halin ne ? kasani duk matar datake matsayin matata tofa tamkar uwace agareka dan haka yazama dole kabama kowace mace girmanta " sake tamke fuska yayi sosai yace " gaskiya de Dad kayi haquri ammafa ni babu wata mace dazan dauka kamar uwa dama nazone nasanar daku anturani Egypt janje wani ayki kuma gaskiya zanjima zuwa gobe zan tafi " duban shi Sarki Jabir yayi sosai yace " Allah yabada sa'a amma inaso kasani dazaran kadawo yazama dole kayi aure " saurin kallon shi Hammat yayi yace " amma dad ......" dakatar dashi Sarki Jabir yayi yace " nagamayin magana " daga haka yafita zuwa fada


Marmyn Zarah ce 👌🏻
[8/19, 5:55 AM] Aunty Fauza: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*


*NA*


*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_



```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*


AND NOW
```MUSAYAR RUHI```



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



*Page 13 & 14*



*_Assalama alaikum inayima kowa barka da Sallah Allah ya'amshi ibadummu amin Allah kuma yamai maita mana fatan alkairi gakowa_*





*R* ai 'bace Hammat yafito cikin 'bacin rai yace " tobasenadawoba sannan har za'a matsamin akan nayi aure alokacin daban shiryaba ina nikam inama tunanin anya anma haifi yarinyar dazan aura ? " garasawa yayi part d'in Ammi dan sanar da ita Hajiya hajara cikin sauri tashiga part d'in Hajiya mariya tana shiga tadubeta ganin Haisam a zaune yasa tace " Hajiya mariya inaso muyi magana " jin haka yasa Hajiya mariya saurin tashi suka nufi cikin bedroom binsu da kollo Haisam yayi cikin zuciyar shi yace " Allah yasa kugane abinda kukeyi badede bane " daga haka yamiqe yabar part d'in suna shiga Hajiya hajara tace

" Hmmmm Hajiya mariya yau naji abinda kunnuwana suketasonji wato Maimartaba yau yayima Hammat maganar aure zaiyi tafiya ayanzu yana dawowa yace dole yayi aure kinga kenan lokaci yayi da Kumsat itama zatayi aure dan kam senayi duk yadda zanyi wajan ganin Hammat ya auri Kumsar yazama dole nayi shirin komi kafin dawowar shi " murmushi Hajiya mariya tayi had'i tafa hannu tace " yazama dole kiyi shiri ko yazama dole nayi shiri ay atunanina Hammat da Amina yadace sbaida idan kika lura ay ......"

" Dakata Hajiya mariya bangane abinda kikeson kiyiba tayaya kinsan tuni nikeda wannan burin shine kema zakizomin dawata banzar magana idan kema so kikeyi Amina ta auri jinin saurauta to ay ga Ansar nan gakuma Fadil baseki za'bi d'aya daga cikinsu ba ? Murmushi Hajiya mariya tasakeyi tace

" Ina idan kinaganin sunfi Hammat riba toke maiye zai hana kiyi hakan kumama idan banda abinki ay Amina duk tagirmesu tayaya kike ganin hakan zai yiwu karki manta kowafa yanadanashi burin ni aganina baikamata wani yaji kanmuba kowa ya'iya allonshi ay seyawanke karki manta koda nice nasamu bazan manta da abokiyar makircinaba hakama kema ina zaton haka to kar wannan yasa wasu suji kanmu "

Wani shi'umin murmushi Hajiya hajara tayi tace " hakane iya ruwa fidda Kai amma nasan tabbas nikeda nasara dukda cewa babbar matsala ta shine Mama sabida tananan akan wannan al'adartasu wadda basa auran wani bare se jinin saurauta muma dayaya tabari aka auromu " murmushi Hajiya mariya tasaki irin namugunta tace " hmmm ay kinga wannan tsohuwar yakamata museta mata hanyafa idan mukabarta tofa Allah babu abinda zamusamu cikin masarautar nan " wata 'yar qaramar shewa Hajiya hajara tayi tace" barta ankusa zuwa dede lokacin dazamu qaramata gudu zuwa lahira " haka sukacigaba da tattauna mugun nufinsu

misalin 9:pm Hajiya Fulani tashiga part d'in Sarki Jabir cikin tsananin damuwa a kishin gid'e tasameshi gaidashi tayi cikin girmamawa kamar kullum ko kallonta baiyiba balle ya amsa cikin damuwa sosai tace " ranka shidad'e dama maganar makarantar su Fadil ne naji cewa su Ansar zasutafi nanda sati 1 amma naji bakayimin maganar su Fadil ba kaga shi yad'an jima yanajira to senayi zaton had'asu kakesonyi dasu Ansar shiyasa banyi magana ba " wani irin mugun tsaki yaja yace " tashi kibani guri jin muryarki ta'isheni haka idan kuma kikacigaba dazama zakisha mamaki ........ " kamar Yaya fa Maimartaba ? " Cewar Hajiya Kilishi dake tsaye bakin qofar part d'in tun bayan shigowar Hajiya Fulani qarasawa ciki tayi tazauna tadubeshi sosai tace

" Gaskiya Maimartaba hakan baikamataba nikam abinda kakeyima Fulani yafarabani tsoroma kenan har yaran nakama abin yake neman shafa ina gaskiya ni bazan iya jurar hakanba idan har baza'ahad'a su Fadil dasu Ansar tafiya Skul ba tofa suma su Ansar d'in sede suhaqura sutazama har zuwa lokacin daka canza tsari dan kam bazan iya jurar zargin jama'a ba sabida wallahi nasan nice abin zagi tunda nice mai yara barima nace nasanar dasu sudakatar da duk wani shiri bayanzuba " tana gama fad'ar haka tamiqe zatabar parlour dakatar da'ita yayi dafad'in

" Dakata Hajiya Kilishi to meye kuma nayin fushi bayan bakiji nace hakaba nifa tare nanemar musu Skul amma senaga kamar mahaifiyar tasu batabuqatar hakan shine dalilin dayasa nike ganin kamar batashiryabane " girgiza Kai Ammi tayi tace " haba Maimartaba itakam maiye nata idan kace ayi akwai wanda zaice a a ? dan Allah kayi adalci atsakaninmu dakuma tsakanin yara dan gujema fad'awa cikin fushin Allah da azabar shi dan Allah kar kasa nima nadinga zargin kaina wajan hanaka yin adalci sabida nice babba duk cikinsu kuma munada kyakkyawar fahimta ni da Kai dan Allah Maimartaba kaji tsoran Allah "

Ajiyar zuciya yasauke yadubi Fulani wanda raban daya d'aga ido yakalleta har tamanta yace " kiyimusu duk wasu shiryeshiye tare zasutafi Ansar da Fadil Hanan da Fadila idan akwai wani abu kituromin Fadil ko Fadila susanar dani ke basekinzoba " murmushi Hajiya Fulani tayi tace " in sha Allah zanyi yadda kace nagode Allah yaqara girma ina godiya agareki Aunty Kilishi Allah yaqaramiki tsoran Allah " daga haka tamiqe tafita jiki a sanyaye binta dakallo hajiya Kilishi tayi cikin tausayawa shiko Sarki Jabir fuskar Hajiya Kilishi yake kallo dawoda dubanta tayi gareshi kafin tayi magana yace

" Basekince komiba Kilishi banada amsar baki banace ga lefin Fulani agareniba zuciyatace kawai ta tsaneta lokaci d'aya babu dalili nasha bambayar kaina meye dalili amma har yanzu nakasa ganoshi badan babu saki a gidan sarautaba idan babu wani dalili mai qarfiba datuni nasaki Fulani kodan itama tahuta to amma babu dalilin yin haka " nannauyar ajiyar zuciya Ammi tasauke tace " gaskiya yakamata kadage da addu'a dukda nasan kanayi to amma kaqara Allah yashiga tsakanin nagari da mugu " shima ajiyar zuciyar yasauke yace amin dubanta yayi sosai yace " wato Hajiya Kilishi akullum jinki nikeyi sabuwa fil cikin wannan zuciyar tawa " yata'ba setin zuciyar shi kuma har qarshen numfashi ahaka zaki dauwama " murmushi tayi tace nagode sosai amma inaso acikin kasona na soyayyata dake cikin wannan kyakkyawar zuciyar taka karabashi 2 kabama Hajiya Fulani rabi zanyi matuqar farinciki idan kayi hakan " rumtse idonshi yayi yace " bazan iya hakanba kiyi haquri amma daga yau zuciyata zata dinga tunasar dani cewa Hajiya Fulani tanada alfarma awajan abar qaunata har abada yanzu tashi muje ciki wannan kamshin turaran naki yajawo miki magana ina matuqar son wannan turaran naki "

Murmushi Ammi tayi tace " ayya shiyasa yamantar dakai cewa yau ba Hajiya Kilishi keda haqqin sauke maka buqatar takaba ? Hajiya Fulani ce kabata duk kulawar da wannan zuciyar taka tayi shirin bani dan Allah " tana kaiwa nan tayi saurin miqewa tafita tana shiga part d'in ta babu jimawa tafito tanufi part d'in Hajiya Fulani tana shiga tasamesu zauna saman Cushion d'aya itada yaranta suna kallon Sunna TV sallamarta yasa suka maido hankalin su wajanta cikin sauri Fadil da Fadila suka miqe suka isa gareta rungumeta sukayi suna gaidata cikin farinciki shafa kansu tayi suduka had'ida saka musu albarka sannan taqarasa ciki nufar bedroom kowa yayi sukabar iyayen nasu cikin farinciki Hajiya Fulani tashiga yimata barka dashigowa bayan sun gaisa Ammi tadubeta sosai tace

" Hajiya Fulani ayau zanyimiki magana akan abinda yake faruwa tsakanin ke da Maimartaba gaskiya lamarin yanacin zuciyata batun yanzuba amma kasancewar lamarine na tsakanin miji da mata kuma ni ina matsayin kishiya baikamata nashigaba sabida nima dole ina cikin abun zargi sabida zaman kishi lamarin yanada wuya idan ke baki zargeniba to babu shakka wasu senun zargeni sede ni nasan har ga Allah kowannen ku zuciya 1 nike zaune dashi tsayin 18 yrs kuna zaman rashin jituwa a tsakaninku amma nayi tunanin ko wani lefi kikayi mishi to amma yau nayimishi magana akan haka abin mamaki shima bashida wani dalili hakanne yasa nazo nabaki shawara koda yau 1 ki'aje matsayin kishiya agareni kid'auka Aunty kice zatabaki shawara yakamata kisake dagewa da addu'a aduk lokacin dakikayi sujjata kidinga karanta wannan addu'ar barinayimiki misali da kaina dan nima karki cireni cikin zargi halin kishi ne

ALLAHUMMA DAMMIR KILISHI KAIDIHA WA SHARRIHA WA AMALIHA ) ALLAHUMMA DAMMIR HAJARA KAIDIHA WA SHARRIHA WA AMALIHA ) ALLAHUMMA DAMMIR MARIYA KAIDIHA WA SHARRIHA WA AMALIHA )

harama shi kanshi Maimartaba daduk wani wanda kikejin zuciyarki bata amince dashiba dasauran wasu addu'o'in neman tsari da kariya daga dukkan sharri in sha Allah zakiga kariyar Allah Allah yayi jagora sannan a garshe inaso yau kiyi amfani da wannan turaran " tamiqamata wani tsadadjen turare dake hannunta dashi nikeyin amfani akoda yaushe Sabida Maimartaba yanason shi sosai kije gareshi cike da karfin gyuwa kinji fatan alkairi Hajiya Fulani "

Sosai Hajiya Fulani tayi farincikin wannan shawara ta Ammi godiya tayimata sosai tamiqe dan rakota cikin sauri Jakadiya tabar bakin parlour daga la'ban datake tun shigar Hajiya Kilishi cikin part d'in amma takasa jin komi sabida sautin Tafsir d'in dake tashi cikin parlour nufar part d'in Hajiya hajara tayi cikin sauri

Bayan Hajiya Fulani taraka Ammi takoma part d'in ta cikin farinciki yau shiri tayi namusamman zuwa part d'in Maimartaba cikin 'bacin rai Hajiya Hajiya tamiqe tashiga kaiwa da komowa sannan tadubi Jakadiya cikin fushi tace " ayko yazama dole kibi duk wata hanya dan ganomin mai suka tattauna akai idan kikayi haka kinada kaso mai tsoka idan kuma kika kasa zan rage matsayin ki agareni zanbama wata damar shiga cikin lamarin mu na sirri " risinawa Jakadiya tayi cikin girmamawa tace angama Hajiya bani wani d'an lokaci kad'an " jinjina Kai Hajiya hajara tayi sannan tace " kya iya tafiya cikin sauri tafito wasu hadimai dake shirin shiga cikin part d'in suka dubeta bayan tawuce suka ta'be baki hadida cewa " hmmm su Jakadiya kenan iyayen kulma tunda kika ganta cikin part d'in Hajiya hajara a wannan lokaci tabbas wani munafincinne " jin kamar motsi yasa sukajabakinsu sukayi shiru suka idasa ciki

Sallama Hajiya Fulani tayi tashiga cikin part d'in Maimartaba baya cikin babban parlour hakan yasa tashiga cikin qaramin parlourn nanma bayanan kallon gofar bedroom d'in shi tayi sosai zuciyarta tashiga bugawa cikin qarfin hali tanufi qofar tsayin lokaci tana tsaye sannan tatura tashiga zaune tasameshi bakin bed yana duba wasu takardu dake gabanshi jin kamshin turaran Hajiya Kilishi yasashi saurin d'agowa amma seyaga Hajiya Fulani ce dukda bahaka zuciyar shi tasoba amma yaji wani sauyi sauke idanunshi yayi had'ida amsa sallamarta wadda yajima baya amsawa a fili sede a zuciya zama tayi agefanshi tanason yimai magana amma takasa tsayin lokaci har bacci yafara daukarta shiko kamshin wannan turaran yasa yamakasayin komi se faman juya takardun yakeyi tashi yayi yamaidasu sannan yashiga toilet tsayin lokaci yafito yashirya kwanciya dubanta yayi yakauda fuska sannan yatadata yace

" gyara kwanciyarki " mamaki abin yabata sosai sabida raban data kwanta saman bed d'in shi har tamanta babu musu tamiqe tazare abayar dake jikinta kyawawan kayan baccin jikinta suka bayyana tahau saman bed d'in saurin nufar makunnin wuta yayi yakashe sannan yadawo kwanciya yayi bayan ya kwanta cikin shakka da fargaba Hajiya Fulani tamatso jikinshi sosai yaji jikinshi ya tunasar dashi amaryar tashi amma kuma zuciyar shi tana qin haka rungume shi tayi sosai tasaki kuka tana fad'in

" Tabbas haqurina yakusa qarewa buqata tana neman halakani Maimartaba dan Allah kakulani koda

Please Login or Register in order to submit comment