Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinda yake cin raina kenan yar uwa kika riga ni furtawa mutum da hankalinsa bazai kai yarsa wannan gidan ba".

Gadoji tace nima sheda ce ina marsida yar gidan Bala sai daga gida ake kai mata abinci mijin ya kasa riketa kuma ai kinsan mijin nata Sado (Sa'idu) dakin su daya da ilyan".


Laraba tace mukam ai taushe zamu zo mu kwasa ina ruwan mu dama irin su abuh ai sai ana basu tantirai kuma nasan zataci ubanta a gurin Halima domin ita bata zama lafiya da surukai".


Aliyah tace yo matar da ko naman miya ne sai a gaban ta ake rabawaa dan kar a cuceta duk cefanen da yayanta zasuyowa matan su saita burkice kowacce leda idan kaje kasuwa baka biyo ta dakin taba kuna zaune zata fado muku daki ba sallama🙊".


Lami dake dariya tace kice Saude abar hankata baki Abuh karamar bazawara za ai sakin uwar miji ba sakin wawa ba".


Duk gurin dariya suka kaure daidai Saude ta fito da katon tire fal da abinci ta ajiye tana cewa dariyar me kuke"?..


Lami tace dariyar farin ciki kawata sai aurar da yaran mu muke asirin mu a rufe tuna hakan ne ya samu dariya".


"Wallahi kuwa lami ai abin da dadi zuma da madara muci kartai sanyi dan nasa mana kitse a ciki .


Hummm ayya Saude kin 'baro🙄😖😠😕.



💰'DAN MILLIONAIRE💰


Page 15 to 16
Zaune suke a palor misalin karfe tara na dare daddy dake rike da wani photo ya mikawa Al'ameen yana cewa.


"Aminullahi wannan 'yar gidan abokina ce Mudansur sunan ta Afnan ban sanii ba ko tayi maka saika aure ta".


Da sauri mami ta amshi photon daga hannunn Al'ameen tana cewa me laifin wannan yarinyar ta hadu kawai ka nema masa ita".


Hade rai Afeeyah tai tana kallon daddy tace nidai a shawara ta abar min dan uwana ya huta ya nutsu daga baya zai samu wacce yake so da kansa".


"To uwar iyayi wa ya sako dake" mami ta fada tana harararta.


Murmushi daddy yai yayi kyau Afeeyah kin fadi gaskiya amma bari naji ta bakinsa Al'ameen kana son ta"?.


" a'a daddy" shine kawai abinda yace .


"Ji banza " mami ta fada cikin haushi".


Dariya Afeeyah tai tana kallon mami tace gaskiya ne yaya Afnan bata dace dakai ba kalleta fa fiyu da ita kamar an zana d'aya .


Duka mami ta kawo mata tana cewa jakin uban ki Afeeyah".


"A'a daina zagin ta mana karki debe mata albarka tabi 'ya'yan kaji🐣🐤🐥.


Amma tsakani da Allah alhaji meye abin kushe a wannan yarinyar".


"Babu amma tunda baa kece zaki zauna masa da ita ba shi kuma yace baya yi shikenan abar maganar".

Mikewa mami tai irin tayi zuciyar nan tace saida safe".

Har hada baki daddy da Afeeyah suke wajen cewa Allah ya tashe mu lafiya".


"Zan kama kine Afeeyah zaki min bayani".



Bayan wata daya Abuh ce ta shigo gida da kukan ta Saude dake kan tabarma tace lafiya kukan me kike ko keda ilyasun ne yaron nan ya fara bani haushi ba wata uwar ya bamu ba tun kafin a kaiki gidan sai wulakanta ki yake zaici kwal ubansa😜😂".


Kai Abu ta girgiza a'a ba shi bane Sa'adu ne dan gidan me gari".


Ba shiri Saude ta mike na shiga uku meya hada ku zaki yayo min masifa😁".



"Abu na kuka tace wai Fati yake so😱".

"Wacece Fati kuma ina ruwanki koma wa yake so tunda kina da naki".


"Kefa Fatin nan gidan yake so".

A zabure Saude tace me karya ne akan hakan kike kuka".


"Wallahi ba karya bane yanzu na wuce su suna waje akan dakali suna hira".


"Kan bala'i wato Salamatu dan me gari kika yiwa asiri ko aiko sai kowa yaji a garin nan kina zuwa gidan boka bari gari ya waye tabdijan wallahi da sake dan kinga bikin shekara ya kusa kada yarki tasha kunya agaban dunbin jama'a na gari da gari".


Tari dabai kama Salamatu ba bataiwa Saude ba ta tura mata aniyarta domin batasan ma wani Sa'adu nason Fati ba".


Kasa nutswa Saude tai saida ta sayar da akuyarta ta dangana gurin boka akan ya karkatar da hankalin Sa'adu kan Abu ".


Yaji ya tsani Fati haka ta juyewa boka dukkan kudin sisi bai bari ta dawo dashi gida ba amma fa ya mata aiki domin tun a ranar labari ya sauya akala".


Da dare sai akace Abuh tace inji Sa'adu wata irin faduwa gaban Salamatu yai cikin tashin hankali ta kalli fati dake kallon Abu".


Dariya Saude keyi tana juyi da habaice habaice tace dadi na da gobe saurin zuwa maza Abuh shirya kije kada ki bata masa lokaci tsuntsun soyayyar🕊 ya dawo kanki ahayye ayyuriri nanaye nisa tazo kusa".


Kallon Fati Salamatu tai cikin tausayawa tace kada ki damu Allah yasa haka ne mafi allhairi kinji babu komai kai Fati ta daga cikin damuwa sosai amma batace komai ba"'.


Tashin hankali ne karara ya bayyana da kiyayyar 'kauye🏕 a fuskar mami lokacin da daddy yace mata ta shirya yana son zai gano danginsa".


Cikin cika da batsewa tace amma alhaji mezai hana kaje kai kadai".

"Saboda me" ya tambaye ta cikin mamaki.


Kai tsaye tace" dole sai munyi gayya me zamu ciyo"?.


A garin daya tare dukkan zuriya ta kike cewa me zaki ciyo Aisha tun ba yau ba na fahimci bakya kaunar zuwa dangi na saboda a kauye suke amma ki sani sune komai nawa idan kika 'kisu nine kika 'ki fito fili kice mustapha bana sonka basai kinbi ta bayan gida ba".


Zaro ido mami tai ni da yaushe nace bana sonka"?.


"Yanzun nan kika fada tunda bakya bukatar asalina kinga son karya kike min yaudara ta kikeyi".


Kuka mami ta kama yanzu alhaji shedar da zakai min kenan"?.


Mikewa daddy yai ransa a hade yace na fada miki ki shirya idan kuma baki canza halayen kiba zan dau mataki a kanki".

Yana fita tace na shiga uku ni Aisha wannan tsinannan 'kauyen kuma zanje daga wannan masifar takau sai wannan😢.



Humm mami manya 'kauye🏘 tushe da asalin kowa😘 duk wanda bashi da 'kauye to bashi da asali😠 tsintaccen kan hanya ne🙄.


Washe gari motoci biyu suka dauka yayin da Zainab tace baza ta bisu kauye ba ta wuce gidan su kafin su dawo".


Da matukar murna Muntari ya tari yayan nasa nan aka hau yi musu hidima da bajinta duk wani abu dazai burge su na gargajiya".


Afeeya dake shan fura ganin mami tayi gurum yasa tace wai mami bazaki ci komai ba to kisha wannan akwai dadi".


Cikin bacin rai mami tace zanci 'kaniyarki fa Afeeyah ni abokiyar wasan kice"?.

"Yi hakuri mami " daga haka bata sake magana ba".

Sadiq kam dama ya shiga gari idan yazo baya zama guri daya kamar kifi🐟".


Al'ameen da yake suna tare da daddy a dakin muntari yace dad nifa yunwa nake ji".


"Kuma Aminullahi ga abinci iri daban daban sai wanda kake so".

"No daddy ba irin wannan nake so ba".


"Uhmm wato sai kwai ko wannan abincin yafi wanda kake ci a birni sa lafiya da gina jiki".



"Nidai daddy mubar maganar samo min mafita Allah ina jin yunwa sosai".

Daddy dake kallon shi yace to Aminullahi hanya mafi sauki ga yaji da mai nan a kusa dakai dauki ka cinye ni amma ka fara ta 'kafofi na saboda kar na gudu😂😝".


Dariya wacce babu shiri Al'ameen yai yana kallon daddy yace haba dad idan na cinye ka babu wanda ya kaini asara".


Muntari dake gefe yace to yanzu me kake so a dafa maka".


"Am small dad in son samu ne dan wake".

"Shikenan karka damu bari yanzu zansa ayi maka" mikewa yai yana fita".


Al'ameen dake kallon photon Abni dake screen wayarsa yace daddy bari naje gurin grand-mah".


"Ok yayi ka gaishe ta"

Al'ameen na fita daidai Fati ta shigo da bokitin ruwa a kanta tana cewa wash Allah umma ki sauke ni".


Da sauri Salamatu ta fito daga daki tana cewa meyasa kika ciko".


"Umma bana son na koma ne".


Zama Salamatu tai tana hada kayan wanke wanke Fati tace barshi zanyi umma ki huta".


To Allah ya miki albarka".


"Ameen umma motar waye guda biyu a kofar gidan nan masu kyau".


"Ayya Fatima yan uwan kine suka zo daga birni da yayan babanki Mustapha yana dakin baban ku kije ki gaishe shi".


"To umma " fati tace tare daa mikewa kusa gwaruwa tai da al'ameen da sauri taja baya tana cewa yi hakura dan Allah ban ganka ba sannu da zuwa ".


"Thank" yace daga haka bai sake magana ba yai hanyar waje cikin mamaki ya tuna yarinyar nan kamar ba ita yake dauka a hannu ya sayo mata chocolate ba shakka babu amma girmanta ya gani sai yaga ta cika masa ido.



Yana zuwa gidan ya tarar da Sadiq acan da ido ya masa magana cikin tsokana Sadiq yace .



"Lah hajiya kinsan me Al'ameen yace wai ya yaga kin kara tsufa sosai kin ragargaje kiji fa hajiya kamar wata kwarya".


"Rabu dashi Saddiqu lokaci ne shima wata rana zai taka wannan matsayin".


"Matsala ta dake hajiya bata suna meye zakice Saddiqu just kice Sadiq".


"Bazan ce jas Saddiq dinba karka dameni😂😜".


Al'ameen ta kalla tana cewa zauna mana Aminu kana tsaye kamar wata bishiya".


Zama Al'ameen yai cikin hade rai yace ba suna na Aminu ba Al'ameen nake".

Hajiya dake kallonsa domin yana kama da kakansa wato mijinta tace.


"Bazance Alemin din ba da Aminu zan kira ka ya zakai ubanka Aminu ya rada maka a haka suka sha minti da goro da naman suna".


"Nidai na fada miki suna na Al'ameen"'


"To kinji hajiya ni Sadiq shi Al'ameen sai ki gyara".

"Bazan gyara ba duk wanda na kira karya amsa ".


Kallon Al'ameen tai tana cewa" Aminu ya batun aure naji har yanzu shiru"'.


"Babu ruwan ki in zanyi in bazan yiba wannan ganin dama tane".


"Karya kake sai kayi d'an kare da fari kamar...........


Sai kuma tai shiru bata karasa ba murmushi Al'ameen yai dan ya gane nufin ta yace.


"Karasa man da fari kamar wa zaki ce kuma kin manta ba d'an kare zaki ce ba saidai kice dan kwikwiyo🐩😂.


Dariya Sadiq yai yana kallon hajiya yace hajiya kinji fa saidai kice d'an kwikwiyo ba d'an kare ba".


Da sanda hajiya ta nuna shi tana cewa kai kuma kayi man shiru bansan shishshigi zuwa dangin miji da ganamasgo ka rufe min baki".


Dan zaro ido Sadiq yai ciki tsokana yace na rufe ruf🤐 hajiya me ran karfe ki shirya idan zamu koma dake zamu tafi kiga birni ki huta kiyi 'kiba".


"Ni ka rufa min asiri da zuwa birni bazan iya rayuwa acan ba".


"A haba dai hajiya me yasa"?.


"Abincin kune bazan iya ci ba gara na zauna anan naci wanda na saba dashi".


"Wanne kalar abincin ne baza ki iya ciba"?'.


Cikin tsufa hajiya tace kaga ta farko wacce na tsana andosi da kwai dinnan".

Dagowa Al'ameen yai cikin mamaki yace" me andosi kuma? abinci ne? ni ban ma sanshi ba".


Dariya sosai sadiq keyi yace hajiya kina burgeni wato indomie kike nufi itace andosi".


Hajiya tace "Eh da wannan abin me kamar tsutsa da kuke ce masa damaroni da sifagatin du bana ci ko an kawo min daga gidan muntari".


Sadiq dake rike da ciki yace lallai kam hajiya yi shiru haka ciki na ya fara ciwo makaroni da spagetti ni kuwa abinci na kenan".


"Shiyasa gaka nan kamar iska ta bushe kun 'ki al'adun hausa sam".


"To hajiya yanzu ba gani nazo ba saina cika ciki na da rama da zogale kafin na tafi"'.


"Daka kyauta Saddiqu ina iyalin taka ne Ri'kayye ko tana gida nasan da daita kuka zo da yanzu ta karaso"


Cikin mazu Sadiq yace bansan wata Rikayye ba idan mata na kike nufi sunanta Ru'kayyah".


"Ita nake nufi mana saboda bakin ciki shine ka 'ki zuwa da ita".

Batare da Al'amin ya dago ba yace hajiya meye abin bakin cikin dan kawai baizo da ita ba"?.


Hajiya data balli goro tace kai kuma kamin shiru ba dakai nake ba tuzurun banza kalleka kato dakai idan anan ne kana da 'ya'ya wajen biyar".


"Ai hajiya daina fada 'ya'ya biyar sai kace na hada dangi da kaji uku ma sun isheni shiyasa bazanyi aure da wuri ba".


"Ashsha kayi ta banza bari ai Mustaphan zaizo ya same ni zanji idan shine ma yake karanta maka kada kayi auren da wuri saiya bani amsa".


Page 17 to 18.
Basu bar gidan hajiya ba sai bayan sallar isha a kofar gida saman dakalin Al'ameen ya zauna sa'banin sadiq daya shiga cikin gida".


Yana nan a zaune Sa'adu yazo yasha wanka ya sako gwanjola irin takalmi sau ciki na roba"'.


Kallon sa Al'ameen yai tun daga kai har kafafu lokaci guda murmushi ya 'kwace masa ganin sai wani buda kafada yake".


Fati ce ta fito tana nufar inda yake tsaye wanda ko minti biyu basuyi ba Abuh ta karaso gurin da 'kawayenta tana haki tace".


"Amma Sa'adu me nace maka ba nace kada ka sake zuwa gurin Fati ba nice nake sonka ba ka amince rannan a dandali ba saboda kai mun rabu da ilya".


Shiru Sa'adu yai cikin takaici Fati tace wai dan Allah Abu meye hakan me na tare miki da bakya son gani na cikin farin ciki"?.


A gadarance Abu tace ban sani ba bani da lokacin ki kai kuma muje ".

Kamar rakumi🐪 haka Sa'adu yabi Abu zuwa dandali kamar yadda ta bukata 'kawayen Abu na yiwa Fati dariya da habaici suka bar gurin".


Wasu zafafan hawaye ne suke zuba a idanuwan Fati gashi gobe ne gasar nuna samari yanzu ita ya zatai da rayuwar ta cikin takaici ta juya zata shiga gida".


Al'ameen dake kallon ta yace " madam ji mana ".


A firgice Fati ta kalli inda yake tana goge hawayen fuskarta"

Jitai yace mene sunan ki"?.

Muryarta na rawa sakamakon kukan da take tace suna na Fatima".


"Ok yayi jeki" kawai yace yana mayar da hankalin sa kan waya wucewa tai ta shiga gida.


Cikin shishshigi da cusa kai Saude ta shiga dakin da mami suke tana cewa Aisha a karo muku abincin ne".


"A'a ya isa haka mun gode".


"To shikenan bari na kawo miki wata kyakkyawar fura ko zaki sha".


Fita tai tana daukowa ta kawo mata sannan ta musu saida safe ta fice tsaki mami taja tana rakata da harara tace ko ina ruwanta dani mayya bazan sha ba aikin banza kawai".


'Yar dariya Afeeyah tai tana gyara kwanciyar ta yayin da mami take ta maganganu da fada ita kada kadai.


"kawai an kawo mutum wannan mugun kauyen an ajiye duk zafi babu wata ni'ima ko jin dadi ba a.c haba wallahi bazai yiwu ba dole gobe na samu alhaji idan shi bazai koma gida nikam na gaji zan tafi".


Shiru kawai Afeeyah tai tana sauraron mami da mamakin furucin ta amma batai magana ba saboda gudun abinda mamin zata ce mata saidai bata jin dadin yadda take kushe 'kauyen mahaifin nata domin itama tana son garin ".


Washe gari Al'ameen bai tashi bacci da wuri ba har rana tai saida Sadiq ya tashe shi yana mikewa ya rike kansa tare da cewa.


"Subahanallahi wannan karar haka kamar zata fasa min kunne kuma daga ina me suke".


Sadiq dake shirin fita yace bazan jira kaba domin an fara wai wani biki suke na nuna samari" yana fadin haka ya fice.


Shiru Al'ameen yai kamar kuma an tsikare shi ya mike cikin gaggawa yai wanka ya shirya yana fita yaga Salamatu ta fito daga daki.


Bayan sun gaisa yace ina Zarah".


Cikin mamaki tace wace haka"?.


Tunawa yai sai kuma yace oh Fati nake nufi tana nan".


"A'a wallahi bata nan ta dade da fita ban sani ba ko tana gurin bikin wasan samarin can nasu da suke".


"Ok" yace yana fita daga gidan harya kusa zuwa yaji kid'an na hawa kansa domin makad'a ne da yawa da maroka na gari da gari suke taruwa su zo".


Juyawa yai ya fasa zuwa hango wasu gajerun bishiya masu ni'imtacciyar inuwa yasa ya nufi gurin dan yadan huta".


Yana karasawa yaji ana shashshekar kuka cikin mamaki ya soma dube dube can ya hango me kukan zaune ta kifa kanta".


Har zai rabu da ita sai kuma ya tuna duk wanda ya sharewa wani hawayen sa Allah zai share masa shima".


Tunani ya farayi to me zaice mata zuwa wani lokaci da yaga bashi da mafita yai gyaran murya".


Da sauri ta dago a razane wanda shi yana mamakin ganinta a gurin ita ma tana mamakin ganin sa".


"Kukan me kike"?.


Shine tambayar dayai mata kaita girgiza tana cewa" ina kuka ne saboda dazan aje abin fada zanyi abin kunya yau ranar fitar da gwani ne a dandali".


"Kamar ya"? Me kuke yi idan kunje"?.


Gyara zama tai tana cewa da farko idan kowa yaje me kira zai rika kiran suna mutum da budurwar shi su fita fili ya bata kyautar zobe da agwagi guda uku shikenan sai su fita wasu su shigo.


To kowa ya sheda ya gani wace nada saurayi kuma baza a kada mata kalangun tayi kwantai ba idan kuma baka da saurayi kowa saiya sani ayi ta maka dariya".


"Toke yanzu bakije ba kina nan idan aka kira sunan kifa kisa saurayin naki ya rude".


"Ni bazan je ba".


"Saboda me"?'

"Idan naje ma babu amfani wazan nuna wanda yake sona yayata Abu tamin 'kwacen sa bani da kowa".


"Zaki are ni"?.

Cikin rashin fahimta tace aron me".

Basarwa yai tare da cewa muje na ga abinda kuke yi a bikin.


Badon taso ba jikinta a sanyaye ta mike suka tafi dandalin shake yake sosai da mutane suna zuwa sai zance da yamud'id'i da munafirci ake ana ta kallon Al'ameen'.

Me shela ne ke cewa anzo gidan. Muntari na alhaji attajirin yan kauyen nan me taimako muntari gwani me 'kwazo ina babbar 'yarsa Abu ta fito mana fili da nata gwanin".


Fita Abu tai tana hura hanci yayin da Sa'adu ya fito ya tsaya a gefen ta yana cire zobe ya bata sannan ya bata agwagi guda biyar.


Lallai su Saude za a sha dafgen nama🍖.


Suna fita me hela ya sake rafka cikiya ina 'yar uwarta Fatima ta fito fili da nata gwanin itama".


Jikin Fati tai yadau rawa cikin nadama da dana sanin inama bata zo gurin ba .


Kaurewa akai da surutu kowa da abinda yake fada wasu na mata dariya wasu na tausaya mata".


Ina Fatima ne ko mu buga miki gangar bandaro me kwantai" maroki ya fada yana le'ke -le'ken inda zai hangota".


"Ehhhh kawai a kad'a mata mu cashe " guri ya kaure ehhh a buga ehhh a buga.


Al'ameen da abin ya bashi dariya shiga cikin filin yai yana murmushi yaiwa me hela magana".


"Heeee a saurara jama'a ina mewa Fatima dariya😂? To ka rufe bakin ka🤐 ina maison jin jarumin💪 Fatima? To bude kunnen ka👂 dakyau ina mai nuna Fatima da yatsa👉? To ka sauke hannunka ina me son ganin gwanin Fatima ya matso kusa ya bude idonsa 👀yai kallo inji wannan zankadedan saurayin yace shine saurayin Fatima"'


Me hela ya fada tsit guri yai kamar sun mutu kowa idonsa nakan Al'ameen wasu suce ba mutum bace aljani ne wasu suce daga ina ta samo wannan.


Fitowa filin Fati tai tana mamaki kare tan da Al'ameen yai a haka idan ka kalleshi zakai tunanin zaiyi girman kai.


Kudi masu yawa Al'ameen ya baiwa marokan da makadan wanda me hela da lasafika a susuce ganin kudin da baiyi zato ba yace.


"A saurara Fatima me 'kashin arziki ce tafi karfin kaji koda na turai ne balle agwagi masu wuni a cikin kwata😂".


"Sannan ku kalli zoben💍 daya bata na gwal ne babu wacce ta samu koda na azurfa dan haka dole yau a yabe ta itace ta cinye gasa a wannan shekarar musbahu ku bamu sauti".


Kid'a🎶 da algaitu🎺 ne ke tashi kamar gidan sarki suna kuma yabon Fati da mata kirari suna kod'ata sun samu kudi sosai a gurin Al'ameen saida ya tabbatar daya wanke Fati tas daga jin kunya".


Abuh na komawa gida taje ta fadawa Saude abinda ya faru tsaki Saude tai to saime inace ba saurayin nata bane idan ya tafi shikenan ta fito rana karki wani ma damu kanki".

Da salon munafirci Saude taje ta karancewa mami komai harda abinda ba'ai ba saida tai 'kari.


Mami kam bata juri zuga ba tuni ta cika tayi fam waya ta dauka tana danna masa kira yana dagawa tace duk inda kake kome kake kazo yanzu ina son ganin ka".


Yana zuwa ta balbale shi da masifa Al'ameen kana hauka ne? Akan me zakaje ka 'barnatar da kudin ka saboda ka kare wata banzar yarinya".


Tun kafin yai magana Afeeyah tace kai mami kamar ya banzar yarinya yar uwar sace fa kuma koba haka ba duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi".


"Ke kuma rufe min baki bake nake tambaya ba dakai nake".


"Gashinan ta fada miki mami duk wanda ya taimaki wanI Allah zai taimake shi"'.


"Hummm shiyasa kaje ka zubar da ajinka a gurin yan kauye a gaban mutane sama da kirge wai yaushe ka lalace da shashanci haka ne".


"Mami ki fahimta yarinyar nan sister nace fa yar uwa tace jinina ce da ita da Afeeyah duk daya ne".


"A wajen ka sakarai ba wacce kuke uwa daya uba daya da wacce kuka hada kakanni saboda mutuwar zuciya kace daya suke".


"Maamii gaskiya maganar sa koni Fatiman nan tana burge ni wallahi amma komai mami idan ba kece kika zabe shiba baiyi miki ba " Afeeyah ta fada da yanayin damuwa".


"Ke dalla 'kyale ni yar iyawa gwana saina fadi abinda ke raina ".


Mikewa Al'ameen yai yana cewa good night mami".

Ya fita daga murya tai yadda zai jiyota tace kowa ya kwana lafiya shi yaso" murmushi yai yana rokon Allah daya shirya masa mahaifiyar tasa.

We will meet👪 again.
See👀 you next time


Typing📲 +234 905 527 3614.


Yusrah Musa Abubakar Gimba.

Page 19 to 20.
Tun asuba Saude da Abu suke gyaran agwagin nan kamar wanda suke gyaran saniya gari na wayewa Abu takai markade aka dafe su"'.


Wani abin mamaki a fanteka aka zuba guda uku wai gidan me gari za'a kai haka suke yi biyun sune na budurwar .


Dariya sosai Afeeyah tai ita bataga abin farin ciki dan an baka wadannan agwagin ba tunda babu riba".


Kai da kafa harshi Saude ta dafe duk kayuwan ta debo a wata langar kwano me tsatsa tana kaiwa Salamatu ".


Kai Salamatu ta girgiza tana cewa" a'a alhamdulillah na gode".


" iheee bakin ciki kike ne Salamatu dan 'yarki bata samo ba kome"?.


"Eh shi nake yi".

"Aiko zaki mutu da bakin ciki domin Abu sai zaman gidan me gari su o'o kuwa bamusan inda za'a hara ba ko kuturu ko makaho waya sani".


Ta fada tana dariyar mugunta tare da daukar langar kayukan ta koma dakin ta".


Daddy na zaune tare da Muntari daren da ana gobe zasu koma Abuja muntari ke cewa'.


"Nikam yaya inaso yara na suyi ilmi sosai amma sa idon 'kauyen nan ya hanani sakat gashi ita Zainaba har ana zancen aurenta".

"Daddy yace toba tana da 'kanwa ba 'yar gidan Salamatu ko har ita za'ai auren"?.


"A'a iya zainabun ce ita har yanzu bata samu tsayayye ba tukuna dai".


"Ok mezai hana mu tafi da ita tunda kana so tai ilmi sai a sai mata makaranta".


Muntari yace da naji dadi yaya wallahi inason dana yai karatu".


"Shikenan babu damuwa ka sanar da mahaifiyarta gobe da wuri kafin mu wuce ya kamata ta sani".



"Eh zan fada mata duk da nayi shedar Salamatu bata da matsala".


Washe gari jin harda Fati zasu tafi yasa saude tace tab kace su Aisha zasu debi masifa yarinyar da kauye ma idonta a tsaye yake balle tana birni .


Nasiha sosai Salamatu taiwa Fati duk da a ranta bata son rabuwa da yarta ta kamar yadda itama Fatin bata kaunar binsu.


Da kukan ta tashiga mota suka tafi yayin da Afeeyah ke mata dariya tana cewa ayya keda dawowa sainan da shekara uku Allah sarki".


Da fati iya hawaye take jin abinda Afeeyah ke cewa yasa ta soma shashsheka".

Al'ameen dake driving Sadiq na kusa dashi ya joya yana cewa mene haka zan sa'ba miki ba jiya kika gama cewa she's our sister ba".


Murmushi Afeeyah tai tana kallon Fati tace sorry sis ita kam Fati babu bakin magana har sukaje gida".


Cikin fushi na sun taho da Fati yasa mami ta fice fuuu daga motar daddy ko kasheta baiyi ta shige cikin gida".


Afeeyah kam bedroom dinta takai Fati tana cewa sannu da zuwa gidan mu ki kwantar da hankalin ki nan tamkar gidan ku ne ki dauke ni matsayin 'kawarki".


Murmushin dole Fati tai tana cewa nagode".


"No baki da matsala Afeeyah ta fada tana shiga toilet tayo wanka da alwala sannan ta fito tana cewa fati kema kije kiyi wanka".


Shiga toilet Fati tana mamakin kyausa kamar ka kwanta a kasan tayis din sai 'kyalli yake kamar mirror.


Ganin bata ga ruwa ba ta leko tana cewa wai ina ruwan kuma banga baho ba sai wani kwale-kwale😀 ko a ciki ake wanka"?.


Dariya ce ta kama Afeeyah saida tagama

2 Comments On DAN MILLIONAIRE
avatar
zainab-ibrahim-8

11 months ago

Reply

Thank

avatar
zainab-ibrahim-8

11 months ago

Reply

Than

Please Login or Register in order to submit comment