Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bita da kallo tace jimin shegiyar yarinya zaki dawo ki same ni ne".


Wani irin kallo daddy ya mata wato wannan yarinyar take son aurawa dansa yarinya mara tarbiyya amma bari ya kyaleta tayi gaban kanta babu ruwansa.


Batare da Al'ameen ya sani ba domin bayanan aka karba masa auren Zainab a gurin mahaifinta ranar mami kamar ta zuba ruwa a 'kas tasha dan farin cikin har ta 'kagu lokacin biki yayi ta ganta tare da Al'ameen muradinta.



Afeeyah kam iya damuwa tayi saidai ba yadda zatai har daddy ta samu da kukanta amma yace tayi hakuri matar mutum kabarinsa komai me wucewa ne.


Al'ameen yasan da zancen domin Afeeyah ta kira shi a waya ta fada masa amma yai burus kamar abin bai dame shiba saidai bazai taba kallonta matsayin mata ba.


Biki ya matso ya kankama sai shiri akeyi mutari ma da tawagarsa sukayo mota guda harda hajiya ranar farin ciki a gurin Fati ganin mahaifiyarta.


Suna zaune a bangaren baki sai kalle-kalle suke mami tasa nana ta kai musu abinci da abin sha me kyau wanda basu taba ganin irin saba.


Shigowa mami su gaisa da yake a cikin farin ciki take saita saki fuskarta har tana tambayarsu.


"Sannun ku da zuwa hajiya fatan kunzo lafiya akace tun asuba kuka taho amma baku zo da wuri ba.

Saude data yago cinyar kaza tace" wallahi nake fada miki da wuri muka taho 'yan ro santi ne suka tare mu".

"Ro santi kuma"? Mami ta fada cikin rashin fahimta.


Saude tace eh wallahi sune suka tare mu sunaiwa driven mu rashin arziki".


Dariya Afeeyah tai sosai tana cewa wai yan road safety kike nufi"?.


Mami tace" oh sune yan ro santi"? Gaskiya ne bari na dawo" ta fada tana mikewa domin zama dasu ya isheta .


A ranar su Afeeyah suka je aka tsara musu lalle ita da Fati sunyi kyau sosai duk da basa tare da walwalar wacce ake neman cusawa Al'ameen din aurenta.


Da yamma wajen magriba suna kitchen mami ta shigo dawowar ta kenan daga gidan hajiya Binta 'kanwar ta ganin basa part dinsu yasa tayo kitchen.


Juyowa Fati tai jin motsi a bayansu ganin mami yasa tace sannu mami ina yini"?.


Dan kallonta mami tai a yankwane kamar baza ta amsa ba cikin basarwa tace lafiya kune za ayi wa sannu".


Kallonta ta mayar wajen Afeeyah wacce ke ta aikinta kamar batasan da zuwanta ba tace" Afeeyah idan kun gama kI sameni a part dina zan aike ki gidan uncle dinki Nasiru ki kaiwa Zainab wasu kaya tana can".


Cikin kunar rai Afeeyah tace to mami".


Juyawa mami tai tana fita a kitchen din sannan ta leko tana cewa" ke kuma ki shirya kayanki domin ranar da 'kyauyawa zasu koma tare zaku tafi aje can aci gaba da bikin agwagi kinji na fada miki" tafiyarta tai babu abinda ya dameta.


Afeeyah data gama kulewa da lamarin mami tace wallahi bazan bari haka ta faru ba dole na fadawa daddy bari ya dawo gidan".


Kai Fati ta girgiza a'a Afeeyah karki haka bana bukatar ace ta sanadiya ta mami da daddy sun samu matsala ki kyale kawai ni kaina nafi son na koma garin mu".


"Meyasa saboda bakya bukatar zama damu ko"?.


"A'a ba haka bane ".


"Haka ne mana Fati tunda gashi kin fada da bakin ki".


"Ba ina nufin haka ba ki yarda dani" Fati ta fada a damuwance.


"Shikenan na yarda dake".
.

Page 25 to 26
Sai bayan sallar isha Afeeyah ta shirya tare da Fati suka tafi kaiwa Zainab sakon magungunan da mami ta basu .


A palon aunty Maryam matar uncle Nasir suka samu Zainab tana tsakiyar kawayenta sai shan kamshi take tana nuna isa".


'Dan tsaki Afeeyah tai cikin takaici ta aje mata jakar maganin babu ko magana ta juya zasu tafi Zainab ta dakatar da ita".


"Ke mene haka zaki aje min, kaya babu bayani waye ya aiko ki".


Ba tare da Afeeyah ta juyo ba tace I think kina da ido saiki duba bom ne a ciki".


Fati dake tsaye jikin kofar falo tana jiran Afeeyah tazo su tafi tace kaya ne mami ce tasa a kawo miki"'


Cikin tsawa Zainab tace ke bakauyiya na sako dake ne 'bace min da gani"'.


Wata kawarta dake kusa da ita tace wannan me kamar 'kanzon fa daga ina me take anan ".


Cikin harara Zainab tace na tsane ta matuka yar talakawan kauye ce mabaraciya ce jahila ba kowa ba.


Juyowa Afeeyah tai tana kallonsu tace kamar yadda su o'o masu ido ba dan ciki suke yan maula talakawan birni ba ki iya bakin ki ina daidai dake sakaryar mata.".".


" oh da gaske? kai amma abin yayi kyau saiki daura niyya ni roba ce ina daidai da kugun kowa".


Kiran mami Zainab tai ta fada mata abinda ba'ai ba suna zuwa gida mami ta rufe su da bala'i musamman Fati da batasan tabi Afeeyan ba.


Harda aibata ta da mata gori iri iri Fati saida tai kukan bakin ciki yadda mami taci mata mutunci ta zagar mata iyaye akan abinda batasan ta aikata ba.


Da zazzabi me zafi sosai Al'ameen ya kwana har akai kiran sallar asuba baiyi bacci ba saida yai sallah akan sallayar baccin ya washe shi .



Haka ya wuni bai fito ba a ranar yana part dinshi duk da yana ganin kamar wasa ne ba aure za'a daura masa da tabarya ba.


Saida lokaci yai yaga daddy ya shigo cikin shiri tare da muntari baban fati muryarsa da alamar yana cikin matukar damuwa yace.


"Daddy wai dan Allah da gaske aure za'a daura min da wannan yarinyar? zainab fa"?.


"Eh Al'ameen mamin ku naso kayi fatan hakan ne mafi alkhairi a rayuwar ka".


"To amma daddy bana sonta wallahi ko kadan".


"Na sani hakuri shi baya 'baci tashi ka shirya muna jiran ka kuma ka cire damuwar dake ranka".

Kai kawai ya iya dagawa cikin dagulewar lissafi yayin da su daddy suka fita daga bedroom din nashi.



Matar mutum kabarin shi haka Al'ameen yana ji yana gani daddy ya bada sadaki aka daura masa aure da Zainab kamar ya dora hannunsa aka yayi ta kuka😭 haka yaji zuciyarsa sai tafasa take.


Abokansa sai gaisawa suke suna taya shi murna basu san dawar garin ba harda masu tsokanar sa saidai yai murmushin dole".


Jin an rude guri ya sake dauka yasa zuciyar Al'ameen ta tsinke zuwa wani lokaci yaji ana ambaton an sake daura auren Al'ameen Mustapha Rich da amaryarsa Fatima Zarah Mukhtar😱🙊.


Wani irin zaro ido yai yana kallon daddy wanda ya rike masa hannu bayan an kammala komai ya sashi a mota suka tafi gida.


Zaunar dashi daddy yai cikin bada hakurin lallasi me tafe da nasiha yace".


"Aminullahi kayi hakuri da abinda ya faru bawa baya tsallake kaddarar sa matar mutum kabarinsa tunda har kaga auren nan ya yuwu karkai fushi da maminka daga Allah ne shine ya baka Zainab ba tinsasawar mami bace .

sannan ina mai sake baka hakurin akan rashin neman shawarar ka ko amincewar ka na sake daura maka wani auren da yar uwarka Zarah.


Kai Al'ameen ya girgiza yana cewa karka damu daddy gata kayi min na gode kuma na karbi zabinka domin ka iya zabi me kyau".


"Da gaske kayi farin ciki da aura maka Zarah danai".


"Kwarai daddy domin ina sonta tun kafin yanzu kuma ina son samun ka na sanar dakai dama".


Murmushi me kyau dady yai cikin nuna farin cikinsa ya rika jerowa Al'ameen addu'a mai kyau.


Fati na zaune a bedroom tana kwalliya Afeeyah ta shigo tana guda har saitin kunnen Fati".


Toshe kunne Fati tai tana cewa au kin sauko kenan harda gud'a? a lallai abu yayi kyau".

Dariya Afeeyah tai tana kallonta tace dole nayi guda na dad'a domin ke nakewa".


"Ni kuma meye hadina da guda a garin dame? Zainab zakije ki yaryarawa amma kya zo ki kama gaibu".


"Waye ya fada miki wallahi ke nakewa domin kin zama amarya".


"kamar ya? Amarya a ina?.


"A gidan yaya Al'ameen yanzun nan na shiga part din dasu hajiya inda suka sauka naji daddy yana fada mata kiyi farin ciki Fati kin samu miji me kyan hali".


Gaban Fati daya yanke ya fadi zuciyarta ta sauya burgu muryarta na rawa tace dan Allah Afeeyah da gaske kike ko wasa"?.


"Haba Fati wallahi babu wasa a cikin abinda na fada miki da gaske an daura muku aure yanzu ke matar Al'ameen c.........


Ai bata karasa jin abinda Afeeyan zatace ba da gudu ta mike tana fita a bedroom din.


Kamar an jefota haka ta shiga part din su hajiya tana kuka hajiya dake goga goro tuni ta ajiye tana cewa.


"Fatima lafiya kike kuka"?.

Durkusawa Fati tai a gabanta cikin kuka tace hajiya dan Allah ki taimake ni wallahi bana son auren".


Hajiya dake kallonta a kaikaice tace jimin sakarya au dama dalilin kukan kenan daga daura auren ko kwana daya ba'ai ba kike neman saki kul na hane ki kada na sake jin kin furta wata magana anan ranki zai baci".

Kuka sosai Fati keyi jin abinda tace zata tashi ta tafi hajiyan ta hana ta".


Kamar yadda Fati tai kuka haka mami ta rika tumuwa a kasa tana kururuwa an cuci dan ta sai rirrike ta mutane keyi.


💰DAN MILLIONAIRE💰


😘YUSRAHMS ABUBAKAR

Page 27 to 28.
Washe gari tun asuba Al'ameen yabar gidan ya nufi lagos mami bata sani ba iya daddy ne ya sani domin yaje shiga part din yaji kukanta da alama batai bacci ba sai kawai ya juya ya fita.


Satin su hajiya uku suka tafi kauyensu batare da sun samu koda kallon arziki agun mami ba.


Fati kuwa sai boyewa take saboda tsananin tsoron haduwarta da mami take kamar wacce zata dau ranta.


Abin yana damun Afeeyah saidai ba yadda zatai a halin yanzu mami ta sake korar yar aiki mutum daya Fati ce ke aikin mutum uku a kitchen kamar jaka gashi Afeeyah bata isa ta taya taba ko a boye ne..


Satin Al'ameen uku ya dawo ranar mami da Zainab suna zaune a palor ya shigo tsallen murna Zainab ta daka tana mikewa da gudu taje zata rungume shi ya daga mata hannu.


Mami dake kallon su tace amma da wannan shashashar baturiyar ce ko ba'a daura muku aure ba zata rungume ka ko".


Dan hade rai yayi daidai Fati ta fito da cooler a hannunta batare data lura dasu ba .

Yace" Zarah".

A firgice ta juyo ganin wanda batai tsammani ba tsaye bayanta ya bude mata hannuwa alamar tazo gare shi yasa a rude ta nemi hanyar guduwa.


Rikota yai batare da kawaici ko jin kunyar mami ba ya rungume ta tare da cewa I miss u fatan kina lafiya".

Zaro ido tai jikinta na rawa dago fuskarta yai yana sakar mata kyakkyawan kiss me dumi a lips din ta sannan ya saketa.


Tana jinta free ta ruga da gudu tana shigewa part dinsu mami da haushi ya gama cikata tace kayi asara dai wallahi ka rako maza duniya meye abin so a jikin wannan yarinyar "?.


Bai bawa mami amsa ba sai Zainab daya kalla yana cewa kinga yadda tarbiyya take ya kamata ki koya nine na kirata amma neman guduwa take saboda kunya ke kuma saboda sakarci kin wani taho a guje zaki rungume ni kada ki kuskura ki sake ko a mafarki ne".


Yana fadin haka ya wuce kuka Zainab tasa tana zama a gurin yayin da mami bakin ciki ya hana tace komai.


Ganin ya dawo yasa ta fara shirye shirye a raka Zainab gidansa taro ta sake kira sosai na dangin ta Zainab taci wanka sukai mata rakiya".


Fati kam daddy ne da kansa shida Afeeyah suka je gidan ya sake zaunar da ita ya mata nasiha sosai sannan suka taho.


Al'ameen na zaune a palor idonsa a rufe yaji an shafa fuskarsa yana bude ido yaga Zainab zaune kusa dashi ta manne masa bai kula taba ya mayar da idonsa ya rufe.


Cikin shagwaba tace wai Al'ameen me yasa ka fiya tauri kamar dutse ne ka sani nice matar ka wacce na dace dakai wannan bakauyiyar bata da wani amfani yar aikin muce kawai".


Ganin bai kula taba yasa taci gaba Al'ameen yaufa ranar farin ciki ce a gare mu daren mune zamu raya shi please ka tashi" ta karasa maganar tana kwantar da kanta a kafadarsa.


Tun tana jiran tashinsa har bacci ya dauke bai motsa ba sai wajen sha biyu ya barta a gurin ya mike yana shiga bedroom dinsa Fati kam tunda su Afeeyah suka tafi ta kwanta tana kuka daga nan bacci ya dauke ta.


Washe gari da wuri ta tafi makaranta domin daddy ya bata driver Zainab kam tana palor inda Al'ameen ya barta tana sheka bacci".


Lokacin data farka rana tayi sha biyu da rabi kallon palon take yi cikin takaici tare da jan tsaki kamar zatai kuka cikin masifa ta soma magana.


"Amma wallahi Al'ameen yayi mugun raina min hankali wato anan ya barni na kwana ji yadda jikina yake min ciwo dan yaga ina sonsa shine zai wulakanta ni kome"?.


Mikewa tai tabar palon bata daina maganganu ba tana shiga bedroom ta kira mami da kukan ta tafada mata karya son ranta.


Wanda Al'ameen na zuwa maimaakon mami ta karbe shi da fara'a daya gaida ita bata amsa ba sai hade rai datai tana jefa masa tambaya.


"Dakyau Al'ameen ka kyauta wato dama baiwa nakai maka ko yanzu kai a ganin ka kayi daidai kenan"?.


"Ka kulle kofar bedroom kace Zainab bataje dashi daga gidan uban taba sai a palor ta kwana ".


"Da safe ka watsa mata ruwan fridge mai sanyi wai hutu dama taje gidan ka prisoner dinka ne babu maganar yar aiki hatta wankin motar ka itace zatai saboda dama abinda ya dace da ita kenan".


"Humm lallai kam ina ita wannan dod'addiyar jahilar yar kauyen meye take a gidan dama aiki ne ya dace da ita".


"Wato ka fifita sashin mahaifinka da zabinsa akan na mahaifiyar ka ko"?.


Mamaki ne sosai ya kama Al'ameen jin sharrin da Zainab ta 'kuga masa alhali tunda aka kaita magana bata hada su dashi ba".


Jin mami tace dakai fa nake tunanin me kake? Wato saboda ka mata gargadin karta fada min shine ka kasa ban, amsa ko"?.


Kallon ta yake kamar sa na sauyawa zuwa yanayi na fushi yace wai mami ita Zainab dince tace na fada mata haka"?.


"Eh ko kana son kace tai maka karya ne da kukanta ta kira ni dazu".


"Ok shikenan zan tafi ki huta lafiya mami".


"Ina zakaje baka bani amsa ba "?.

"Ina zuwa mami dole sai mun zauna dan bazan dauki rainin yarinyar nan ba".


Tun kafin mami tai magana ya fita a palor ransa a bace.


Zainab na palor zaune tana danne danne a waya kamar walkiya haka ta ganshi cikin palon sakamakon tasan karyar data shirga masa yasa da sauri ta mike zata gudu".


Wata irin damka ya mata wanda cikin azabar radadin da hannunta ke mata ta kwalla kara tana sakin wayarta".

Muryarsa kausashe yace" ki tsaya iya matsayin ki idan tsautsayi yasa kika sake kuskuren fada wa mami abinda bansan dashi ba saina kusa kashe ki wawuya".


Kuka ta saki domin rikon dayai mata bana wasa bane hannunta yayi jawur ya tara jini yafi awa rike da ita saida ya tabbatar ta wahala ya saketa cikin bacin rai yabar gurin.


Kuka tai sosai domin hannunta ya kumbura amma a ranta yanzu ta fara indai bakanta masa ne a cewarta tunda ya nuna baya sonta".



Hanyoyi da dama ta soma bi na jan hankali amma kullum labarin daya ne ta gaji da zama haka amma tasa a ranta zata fito ta masa zanga-zanga.


Wata daya dayin bikin nasu amma babu abinda ya sauya kullum itace a 'kar.


Tana tsaye da bayan sallar magriba a gaban dinning bayan yar aiki ta gama dinner ya shigo a gajiye sosai yanayinsa zai fada maka haka.


Tararsa tai tana kashe murya tace" sannu my hero gaskiya yau ka gaji da yawa Al'ameen muje na maka tausa da wanka ga dinner na jiranka".

Ta gefen ta ya wuce yana cewa bana bukata".


Tsaki taja mai karfi wanda ya dakatar da tafiyar da yake yi ganin ya tsaya a dake tace".


"Ahaf dan ina tausaya maka ma shine zaka nemi tozarta ni karka manta ba wani abin arziki kake bani ba ".

"Karka manta akwai gwarazan maza a gabanka soja suna kawai kaci domin baka da wani amfani gurin mace saidai ka kalle ta da ido".


"Tunda kai famkon namiji ne babu wani katabus da kake dashi kai muna maza sunan ka mata maza domin babu wani abu da zakai tunkaho dashi famko kawai".


Wata irin juyowa yai da dukkan karfinsa wanda tasa ta kwasa da gudu ta shige part dinta .


"Famkon namiji"? Ya fada cikin mamaki wato kallon da take min kenan lallai zan nuna miki iyakar rashin kunyar ki" juyawa yai yana shiga part dinsa.


Misalin karfe tara na dare Zainab na kwance akan gado taji an bamko mata kofa da karfi cikin tsoro ta zabura tana mikewa ta diro daga kan gadon.


Ganin wanda batai zato ba yasa ta sake rudewa ga wani yanayi da tsantar fushi da take hangowa a cikin idanun shi.


Jikin tane ya soma rawa ta kankame guri daya cikin tashin hankalin meya kawo shi.


Har inda take yaje yana sa hannu a gaban rigar baccinta da dukkan karfinsa ya yaga ta.


Yana mata wani kallo me ma'anoni da nuna ta shirya famko ya kawo mata ziyara".

Tana kokarin guduwa ya cafko ta yana dora ta akan bed din ya bita ya danne domin yayi alkawari yau saita gane bata da wayo.


Fati na kwance a daki bacci ya fara daukarta sama-sama take jin ihu da kuka tayi zaton mafarki take sai gashi kamar ana matso mata da kukan kunnen ta.


Tashi zaune tai cikin magagin bacci jin muryar zainab tana a taimake ta zata mutu yasa ta mike da sauri tana fita.


Har part din zainab din ta shiga cakk ta tsaya tare da zaro ido tana dafe kirji zuciyarta na bugawa jin zainab na cewa".


"Wayyo Allah na shiga uku na lalace Al'ameen zaka kashe ni na tuba kayi hakuri wayyo wayyo umma mami kuzo ku taimaka min zai illata ni ".


Muryarta harta dashe kamar me mura bata fita sosai jikin Fati na shaking ta juyo har tana tuntube ta fita daga part din.


Koda ta koma bedroom dinta kasa kwanciya tai balle ta runtsa saboda fargaba gani take kamar idan ya rabu da Zainab gurinta zaiyo".


Zazzabi ne ya rufe ta da gari ya waye tana zaune bakin gado tana tunani Al'ameen ya shigo ganinsa yasa ta mike zumbur tana jada baya.


Muryarta na karkarwa tace kayi hakuri dan Allah bani da lafiya".


Bai daina binta ba harta kure bango sannan ta tsaya tana yarfa hannu kamar wacce ta yanke".


Da dan mamaki a fuskarsa ya karasa inda take yana daukota ya dawo da ita bakin gadon cikin alamar tambaya yace.


"Lafiya hakurin me kike bani"?.

Kuka Fati ta fashe dashi tana cewa" dan Allah kar kamin abinda kaiwa Zainab".



Sai sannan ya gane manufar ta murmushi yai yana rike hannuwan ta yace .


"Zarahh amfanin zunubi romo babu 'kira mezai ci gawayi ita ma laifi tamin babu abinda zanyi miki ki kwantar da hankalin ki ke ta musamman ce kinfi karfin yi anan".


Dan sauke ajiyar zuciya tai jin ya dora hannunsa akan fuskarta yana goge mata hawaye.


Kallon cikin idonta dake cike da tsoro yai yana cewa" shikenan karki damu komai ya wuce, kinsha magani"?.

Kaita daga masa".

Kwantar da ita yai yana rufa mata bargo bai sake magana ba ya sakar mata kiss a saman lips dinta sannan ya fita da kallo ta bishi tana sauke ajiyar zuciya.


Al'ameen ba rabuwa yai da Zainab ba saida yai mugun horata na sati tayi kuka tayi ihu ta kira agaji amma babu mai taimako tsabar azabar data sha ko tafiya ta gagare ta.


Fati da ta daina ganin wulgin Zainab din yasa ta yi tunanin ko bata gidan amma data tambayi yar aiki sai tace batajin dadi tana part dinta.


Breakfast ta hada a madaidaicin kyakkyawan tire ta shiga part dinta daidai ta fito daga toilet alamar wanka tayo sai bin bango take dakyar tana cije baki cikin dabara take daga kafarta.


Ganin Fati tsaye yasa ta doka mata wata muguwar harara tana cewa".

"Uban me ya kawo ki fita min a daki".


Aje tiren Fati tai kamar baza tai magana ba sai kuma tace yaya jikin naki"?.


A fusace Zainab tace jikin uwar wa munafika dama ce miki akai bani da lafiya"?.


Dan murmushi Fati tai tana kallonta tace" ke kuwa kike rashin lafiya ga breakfast nan na kawo miki".


"Uban breakfast malama get lost wallahi ki shiga hankalinki zan miki mugun rashin mutunci".


Dariya Fati tai tana kallonta tace" ah haba dan gurgu da wacce kafar"?.


Iya cika Zainab ta gama 'kulewa ji take inama zata iya kama Fati dasai ta dirzata son ranta yau din nan".


Juyawa Fati tai zata fita tace to Allah ya sauwake nina wuce".


"Kima tsaya da na nuna miki iyakar ki"'.

"Rufe mata kofa Fati tai tana cewa idan ma na tsaya babu abinda zaki iya yi min".


Page 29 to 30.
Kwana biyu Zainab data samu lafiya ta warke haka ta hada kayan ta cikin akwati ta koma gidan mami da kukanta.



Mami ranta ya 'baci dan haka tace Zainab tayi zamanta baza ta koma ba sai Al'ameen yazo ya bata hakuri.


Shiru tun suna zuba ido har mami ta gaji ta kira shi a waya cewa yazo tana nemansa.


Yana zuwa ta rufe shi da fada dakyau Al'ameen nagode da kake nuna ban isa dakai ba ina matsayin mahaifiyarka wato kana son zabin uban ka amma ka'ki nawa ko".


Kamar baisan akan me take magana ba yace" mami meya faru ne".


"Oh bakasan meka aikata ba kenan yanzu Al'ameen Zainab ba matar ka bace amma kai mata fayde saboda rashin hankali".


"Amm mami nine tace nai mata fayde da yaushe wato dama shine dalilin tahowa gurin ki don tamin sharri"?.


"Kana nufin karya ta maka"?.


"Umh ban san komai ba".


"Shikenan duk da haka bazata koma ba sai kazo biko".


Murmushi yai yana mikewa yace to mami nizan tafi sai wata ran maybe nan da wata biyar".


Da kallo ta bishi tana cewa idan ma shekara biyar zakai duk inda kaje duk shawagin da zakai a duniya karshe dai gida zaka dawo".


Dakatawa yai batare daya juyo ba yace" albarkar ki da addu'ar ki nake nema dan zan dawo miki da kyakkyawar tsaraba🙈".


Jin haka yasa mami washe baki ciki farin ciki tace Allah sarki Aminu na Allah ya tsare min kai a duk inda kake sannan tsarabar kayo min me yawa saboda yan uwa😱😀". ,


Fuskarsa har lokacin da murmushi annuri ya bayyana yace.


"Karki damu mami wanda ba familin mu bama saiya ga wannan tsaraba kuma
fatana tsarabar ta amfanar da al-umma"😁.


Sosai mami ta zage ta masa addu'a har dariya ta bashi yasan dazai fada mata manufarsa baza tace 'kala ba kila fitina cema zata tashi".


Kwana biyu a tsakani Al'ameen suka bar kasar shida Fati zuwa bangkok domin zaiyi wani uziri acan tare da abokinsa Aliyu suka tafi shima da matar sa Ummul-khairi (maman Affan).



Fati taji dadi tafiyar da sukai musamman da suka hadu da maman Affan mace mai kirki babu ruwanta da girman kai duk da kuwa ta girmewa Fatin".


A wasu kyawawan estate masu kyau da tsaruwa suka sauka da yake sun debo gajiya sunayin wanka da sallah a daddafe fati taci abinci saboda bacci hakan ma saida Al'ameen ya matsa mata.


Washe gari sakamakon ba kowa sun tafi gurin aiki yasa maman Affan ta shigo gurin Fati dan duba lafiyarta.


A makeken falon ta sameta zaune tana kallon Tv ganin su yasa cikin murna ta mike tana karbar Affan dan shekara daya da rabi.


Cikin fara'a ta kalli maman Affan tana cewa" sannun ku da zuwa maman Affan ga guri zauna gaskiya naji dadi".


Maman Affan dake murmushi tace karki damu ai mun zama yan uwa tamkar 'kanwa haka na dauke ki".


"Na gode maman Affan kuma nima na dauke kI matsayin aunty na na yarda dake zan iya fada miki dukkan matsala".


Kai maman Affan ta jinjina tana cewa gaskiya Zarah kinyi dacen miji Al'ameen mutumin kirki ne na sanshi tun kafin na auri Daddyn Affan".


"Amma fa saidai sojoji suna wuyar sha'ani sai kina hakuri kila auren ku baifi shekara ba ko"?.


Kai Fati ta girgiza" a'a banfi wata uku bama".


Zaro ido maman Affan tai tace tab kice kune a ruwa yanzu kuke cin amarcin ku honey moon kuka zo ba aiki ba".


Wanne amarci ana zaune lafiya".


"Amarci wanda kika sani saidai ina miki fatan Allah yasa Al'ameen ba irin daddyn Affan bane dan har yanzu ina shan wahala a hannunshi gashi dai na haihu amma wani lokacin sai nayi kuka nake samu ya rabu dani".


Cikin fargaba Fati ke kallon ta domin ta fahimci me maman Affan din ke nufi lokaci guda ta rude taji dama bata

2 Comments On DAN MILLIONAIRE
avatar
zainab-ibrahim-8

11 months ago

Reply

Thank

avatar
zainab-ibrahim-8

11 months ago

Reply

Than

Please Login or Register in order to submit comment