Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiryawa sannan taje ta kunna mata ruwan ta fito.


Sanin datai cewa bada son ran mami Fati ta biyu su ba yasa tasa kawai aka kawo musu abinci part dinta".


Kwanan Fati biyu daddy ya sai mata school ta fara zuwa itama driven ta daban .


Korar yan aikin gidan mami tai mutum uku tabar biyu cewa meye amfanin fatin idan ba bauta ba".


Tasa ta a cikin 'yan aikin batare da sanin daddy ba hakan datai ya 'kona ran Afeeyah dan haka itama take shiga kitchen din tana koyawa fati wasu abubuwa.


Ina Fatima ban ganta ba jiya da yau lafiya kuwa"?.


Kau dakai mami tai tana cewa tana kitchen ita da su nana".


Cikin mamaki daddy yace me take yi a kitchen din"?.


Rasa abinda zatace mami tai ta kama kame-kame daidai Afeeyah sun fito ita da Fatin jikin su duk a 'bace.


Daddy da ransa ya soma baci ganin yadda suka fita hayyacin su ya kalli mami cikin fushi yace".


"Aisha yanzu sune kika mayar kitcinonin ki yara nane fa amma zaki wani tura su kitchen sun zama kuku ne".


Ganin daa Afeeyah tai daddy ya damu da yawa yasa cikin son kare mamin tace.

"Lah daddy ba ita ta tura muba kasan ban iya girki ba kuma gashi kullum lokaci yana ja gidan wasu zanje shine nace bari na koya abin kunya ne ace kamar ni ban iya komai ba".


Sauke ajiyar zuciya mami tai a boye jin Afeeyan ta ceceta mikewa daddy yai yana cewa shikenan amma ku rika aikin baya baya sannan ku rika lura da wuka kada ku yanke.

"To daddy mun gode zamu kiyaye" cewar Afeeyah.

Barin gurin yai mami dake shirin tashi ita ma tace tunda kin biyewa wannan yar kauye wahala yanzu kika fara shanta ".


Kai Afeeyah ta girgiza ba tare datai magana ba shigowar Zainab kenan ko zama batai ba ta kalli Fati a 'kyamace tana cewa".


"Ke village girl dauko min abin sha a fridge sannan ki wuce kitchen ki zubo min abinci me zafi".


Wani kallon baki da hankali Afeeyah ta mata tana cewa itace zatai miki bauta aiba yar aiki bace idan bazaki nemi nana ta kawo miki ba ki barshi".


Ke na sako dake ne gada wacce nake yinan".


"Kin sako dani tunda kika ambaci yar uwata bazatai ba kinji na fada miki".


Tsawa mami ta saki tana hararar Fati tace ke dalla wuce ki mata abinda take so sa'ar kice ita".


"Maamii" Afeeyah ta fada ranta a bace.


Ke kuma zaki ci ubanki Afeeyah idan baki min shiru ba".


Barin falon Afeeyah tai yayin Fati ta wuce kitchen ta zubo mata abincin tare da dauko juice ta kawo mata .


Banza jaka yar kauye akuya" zainab ta fada tana dauko spoon.


Juyowa Fati tai tace duk sunan kine gaskiya kin more jaka akuya toga dusa nan da ruwan tsami na kawo miki saiki fama".


"Keee tsaya dan kan uwarki".


A haba dai na tsaya saboda ke baki da wannan matsayin babyn daud'a jeki wanka da brush kafin na saurare ki, domin wari kike"😁🙊.


Sai kuma ta fashe da dariya tana kallon Zainab tace ki fama ina zuwa idan dusar bata isa ba akwai wata a kitchen kice meeeyyy🐐🙈 zan zo na karo miki dan wallahi ganin ki ya tuna min da tinkiya ta🐏.


Tana fadin haka ta bude kofa ta shige tana cewa sorry idan kinji haushi na kinsan mu villagers bamu iya magana ba".


Cizon yatsa Zainab tai cikin takaicin tsayawar datai ta zuba ido Fati ta fada mata son ranta amma bari ta shiga part din saita fasa mata baki.


Al'ameen dake tsaye a kofar palor ya jinjina kai yana karasowa zai wuce ganin sa da uniform din army yasa Zainab ta fahimci tafiya zaiyi cikin sauri tace".

"Yaya Al'ameen".


Cikin mamaki ya juyo jin yadda ta kira sunan a tausashe yasan akwai abinda zata ce".


Mikewa tai tana zuwa har gaban shi ta ciro wani zobe daga cikin karamin abu me kyau tana mika masa".


Batare daya karba ba yace na mene"?.

Murmushi tai cikin karya murya tace kaima ka sani kawai ka fuske ne Allah Al'ameen ina cikin matsala na rasa yadda zanyi da rayuwa dole na fada maka cewa na kamu da ciwon sonka😱.



Wani irin kallo ya mata zai wuce bai tanka ba ta sake shan gaban sa idon ta da hawaye cikin magiya tace".


"Na roke ka Al'ameen ka soni ko kadan ne kaji tausayi na kada zuciya ta tabuga na mutu".


"Da kin huta da matsalolin duniya ke dan kin raina min hankali nine zan soki are you out of your sense😠.


A'a ina cikin hankali na koda na zauce to lallai sonka ne ina kaunar ka kuma da aure".


"Ashe zaki mutu baki aure ba babu abinda zanyi da mace irin ki kada ki batawa kanki lokaci zuciya ta tamace daya ce kuma bata raye dan haka na kulleta".


"Dan Allah Al'ameen ka bude ta gani nazo zan maye maka gurbin wacce ka rasa".


"Ta ya kenan".


Zoben ta mika masa amsa yai yana jifa dashi yace ko mata sun kare saike bazan aure kiba babu abinda zanyi dake bakya cikin kalar matan da nake son kasancewa dasu".


Kuka ta saki lokacin daya wuce ta yana shiga part dinsa hannu ta dora aka tana cewa .


Na shiga uku zuciya ta baki min adalci ba meyasa zaki kamu dason mutumin da ko kadan jinin mu bai hadu ba".


Bayan wasu watanni Fati harta saba da tsangwamar mami data Zainab domin duk wanda zasu kare ta basa nan Afeeyah taje gidan su mami Al'ameen bayanan daddy ba zama yake ba".



Kullum zuba ido Zainab keyi da kwadayin ganin Al'ameen amma shiru wai mushiriki yaci shirwa .


Suna Zaune a palor Afeeyah data fito ganin yadda zainab ta barbada kwalliya a fuskarta zata fita gurin bikin 'kawarta yasa cikin tsokana tace.


"A'a yau kuma harda su biri🐒 muka samu a gidan namu lallai kice zamuje wasa".

Cikin alamun tambaya Fati tace biri dai? Ke kuma a ina kika ganshi"?.


Afeeyah dake shirin fita tace gashi zaune akan kujera ya dora kafa daya kan daya yana kallon fuskarsa a mudubi".


Kallon Zainab dake duba mudubi Fati tai sai kuma ta kalli Afeeyah suna hada ido suka kwashe da dariya".


Cikin bacin rai Zainab tace ke dan uwarki nice birin"?.


Dakatawa da dariyar Afeeyah tai tana nuna ta da yatsa tace" kul kada ki kuskura na sake ji kin ambaci uwata saina zubar miki da hakora".


Fita Afeeyah tai daga palon yayin da fati ta mike zata bar palon itama taji ance "Zarah".


A firgice ta juyo ganin Al'ameen tai tsaye sanye da kananun kayan da sukai matukar yi masa kyau kuma ya kara kyau da 'kiba.


Dan murmushi tai tana cewa sannu da dawowa".


Bai amsa ba sai zama dayai yana cewa dafa min wani abu naji ko kin iya girki".


Yar dariya tai tana nufar hanyar kitchen a rayuwa Al'ameen yana burgeta da sam bashi da girman kai idan wani ne ko karasa kallonta bazai ba".


Zainab datai suman zaune muryar ta na rawa saboda bakin ciki abinda yace yanzu tace.


"Amma gani ka rasa wa zakasa ta hada maka breakfast sai wannan kucakar 'kazama yar kauye"'.

Itace ta cancanta nasa domin tafi ki matsayi kucaka 'kazama kece sunan kine dake hakan ya dace".


A fusace ta mike tana nufar kitchen din tarar da fati tai tana kokarin kunna gas ta buge mata hannu tana huci tace.


"Ke dalla matsa min jaka ".


"Jaka dai" Fati ta maimaita.


Cikin karaji tace eh nace jaka dabba jahila kibar kitchen dinnan domin Al'ameen nawa ne nice zan aure shi dan haka ki fita daga gona ta ko kallonsa na sake gani kinyi saina faffasa miki ido".


Dariya Fati tai Allah da gaske amma sai naga wanda kike wahalar da kan naki a kansa bakya gabansa son maso wani kike".


"Inji uban wa" zainab ta fada tana yowa kan Fati".


Cikin dakewa Fati tace inji uban ki ke bari kiji bafa ki isa ki shiga tsakani na da dan uwana ba indai akan ala'kar mune bakin ciki zaisa zuciyarki ta buga dare daya ki mutu Al'ameen baya sonki".


Wuka Zainab ta dauko tana kawo wa Fati wani irin wawan yanka gocewa Fatin tai a bisa tsautsayi ta yanke ta a hannu".


Rike gurin da jinin ke fita Fati tai tana dagowa zatai magana zainab ta dauke ta da mari.


Itama Zainab din babu zato taji zazzafan marin ya sauka a kuncinta wanda a gigice ta fasa kara".


Tana kallon Al'ameen basu ankara ba suka sake jin karar mari mami ce ta shigo daidai Al'ameen ya mari zainab shine itama ta mari fati dan tasan a kanta ne".


"Mami" Al'ameen yace ransa a bace.

A fusace ta juyo gurinsa tana cewa rufa min baki wanda baisan ciwon kansa ba akan wannan tsinanniyar yarinyar shine zaka fidda hannu ka mareta".


Cikin tsawa mami ta kalli Fati da hawaye ke fita daga idonta tace ke kuma yau saikin bar gidan man tunda ke shedaniya ce kinzo kin hana mu zaman lafiya ".


"Mami ina zataje da zakice yau saita bar gidan ba laifin ta bane nawa ne".


"Sakaran banza dama ai nasan laifin kane basai ka fada ba".


"Ke kuma kafin naci uban daya haifeki kije ki tattare tsunmokaran ki ya mayar dake.


Fita Fati tai tana zubar da 'kwallar bakin cikin zagin da mami tai mata ita daman hanyar garinsu take neman komawa".


Cikin mamaki shigowar Afeeyah kenan ganinta janye da akwati yasa tace lafiya ina zuwa haka".


"Nice na kore ta domin hatsabibiya ce".


"Kika koreta kuma mami ina zataje kenan"?.


"Ruga zata koma can gayyar tsiya kauyen su".


"Haba mami me kike cewa haka dan Allah kiyi hakuri".


"Wallahi tunda na rantse saita bar gidan nan a yau bazan yi kaffara ba".


Al'ameen dake tsaye yace Zarah⭐ muje".


Mami dake hararar Fati tace ka manta baka ce wata🌙 ba".


Daidai zasu fita yayi murmushi yana cewa to ai nine watan mami munyi ruga".


"As as as ta kaji idan kaga dama kaima karka dawo ka zauna acan".


Kuka Afeeyah ta fashe dashi tana shigewa part dinta mami data bita da kallo tace zaki kuka ki gaji har hawayen ki ya kare kora ce na kore ta kuma babu yadda za'ai dani"'.

Bintu Musa Abubakar.


Page 21 to 22.
Gidan Sadiq Al'ameen yakai Fati cikin mamaki Sadiq yace ina fatiman zataje na ganta harda akwati ga fuskarka da damuwa lafiya"?.


Kai Al'ameen ya girgiza yana kallon Sadiq yace" zata cigaba da zama anan".


"Me yasa"?.


"Saboda wani dalili" Rukayya ya kalla yana cewa" please auty na ga sister na zata taya ki zama".


Murmushi Rukayya tai ok babu damuwa 'kani na sannunki da zuwa Zarah ko".


"Eh sunan ta kenan "Al'ameen ya fada yana zama a dinning .


To ai bakai na tambaya ba ".


"Idan kin tambayeta tamkar kinyi da nine".


Cikin tsokana Rukayya tace a'a fa Al'ameen kodai-kodai".


Aje cup din daya hada tea yai yana cewa kodai kodai me.


Da ido Rukayya ta nuna masa kodai son fati yake".


Kafada ya daga yana cewa kibar ma wannan tunanin sam ba haka bane nida soyayya munyi ban kwana balle wani aure".


"Humm yadda kake dinnan inaga mace daya ma ta maka kadan saidai biyu".


Ni biyu ma sun min kadan saidai hudu".


"Aiko zamu duba cikin dangi mu zabo maka".


"Ba wannan maganar bana ra'ayin aure a cikin dangi idan ma zanyi gara bare".

Mukam munfi so ka samu a dangi zanyi ta maka addu'a".


Bana bukatar auren dangi Idan abinda kika fada ya faru zan baku kyautar visa kuje honeymoon duk kasar da kuke so".


Rukayya tace tab aiko zan dage har fata na yaci kuma wallahi saika yi alkawarin daka dauka".


Bai amsa mata ba sai mikewa dayai yana kallon Sadiq sannan ya kalli hannun fati yace please kadan duba ta taji ciwo da wuka a hannunta.


Yana fadin haka ya fita dan bayason yawan tambayoyi da kallo Sadiq ya bishi tareda girgiza kai kafin ya fara duba mata hannun.


Al'ameen bai koma gida ba sai dare daddy daya dawo ya tarar da Afeeyah idonta sunyi ja kuma sun kumbura ya tsareta da tambayoyi.


Kasa fada masa cewa mami ce ta kore ta tai yayin da mami tai wi'ki-wi'ki tana rarraba ido alamar rashin gaskiya da kad'uwa.


Mami daddy ya kalla yana cewa ina fatima Zarah take"?.


Hautsinawa cikin mami yai ta rasa abin cewa sai kallon daddyn da take da tsoron idan yasan ta koreta kila itama yau tai kwanan gidan.


Da fari Al'ameen yayi burus ya dauke kai kamar baya falon sai da yaga ran daddy yai masifar baci sannan ya gyara musu al'amarin da cewa.


"Amm daddy Zarah tana gidan Sadiq taje musu wuni ne yanzu zanje na daukota".

"Ok babu damuwa ai tunda tana can dama rashin ganinta ne yasa hankali na ya tashi".


Mikewa Al'ameen yai yana fita a palon daddy dake kallon mami wacce tun dazu take susa kamar me ciwon 'kazuwa ko sabuwar kamu yace.


"Dama tana gidan Sadiq amma kika barni nai ta ihu da baki na"?.

Sauke ajiyar zuciya mami tai tana godewa Allah da yasa Al'ameen ba garin su ya mayar da ita ba tace".


"To ai alhaji nayi tunanin zakai fada ne kace nabar bakuwa kuma budurwa tana yawo".


"Akan me zanyi fada dan taje gidan dan uwanta ai zumunci tai yarinyar nada hankali".


Kallon Afeeyah dake goge sauran hawayen fuskarta jin fatin na gidan Sadiq yai yana cewa".


"Me akai miki ke kuma kike kuka gashi idanuwanki harsun kumbura.


Sauke kai Afeeyah tai tana cewa daddy banda lafiya ciki na ke ciwo".


"Kuma baki daa lafiya bazaki fada a kaiki asibiti ba kuka yana magani ne"?.


"Daddy nasha magani tun dazu na samu sauki"'.


"Shikenan Allah ya rufa asiri".


"Amin tace".


Daidai fati tayi sallama tana zama ta gaishe da daddy".


Amsawa yai yana kallon bandejin hannunta yace ciwo kika ji Zarah da yaushe"?.


Kafin fati tai magana Afeeyah tace daddy dazu ne a kitchen Zaina.........


Dafe kirji mami tai tana tarin karya harda shidewa saboda kada Afeeyah ta fada".


Ruwa Al'ameen ya miko mata karba tai tana sha kamar gaske fati data fahimci mamin bataso daddy yasan gaskiya tace".


Daddy dazu a gidan auty Rukayya na yanke da wuka a kitchen shine yaya Sadiq ya samin magani a gurin".


Ayya sannu Zarah ku daina daukar abu me had'ari irin su wuka kuna nisa dasu kinji".


"To daddy na gode"


Shikenan afeeyah tashi kije ku kwanta".


"To daddy good night".


"Ok daughter sleep well Allah ya tashe mu lafiya".


Mami ganin datai sun rage saura su biyu a palon yasa ta kalli daddy tana cewa" alhaji dama wata magana nake so muyi".


"Ta me"? Daddy ya tambaya.


Gyara zama mami tai tana dan yin kasa da muryarta kadan tace akan Al'ameen ya kamata ace yanzu yayi aure domin zamansa haka nan bazai yuwu ba na samo masa matar aure".


"Tofa a ina take yar waye"?.


"Tana gidan nan yar 'kanwata Binta nake so ya aura gatanan Zainab".


"Kece kika riga masa shiga masallaci ko shine kikaga alamar yana sonta".

"A'a kawai ta dace dashi ne dan Allah alhaji ka amince".


"Shikenan zan same shi da safe naji daga gare shi".


Cikin faduwar gaba domin tasan bazai taba amincewa ba mami tace alhaji ba wani jin ra'ayinsa umarni zamu bashi idan tashi zamu biye bazai taba aure ba kullum saidai yasa hoton wannan baturiyar a gaba yana kallo screen din wayarsa photonta ne hatta cikin laptop dinsa photonta ne akai bana tunanin yana aiki ma yadda ya kamata idan kaje bedroom dinsa photonan ta sunfi goma a bango ta riga ta shanye shi babu yarinyar da yake kallo matsayin mace balle yaji yana sonta".


"Haka dai kikace kuma, haka kike gani da zato a naki tunanin zuciya bata da 'kashi muddin ya samu wacce yake so da kansa zai nuna ta".

"Alhaji baka yarda ba kenan saboda kai Al'ameen duk abinda zaiyi daidai yayi a gurin ka gaskiya ni ban amince ba ka sashi yai aure".


"Zaiyi idan lokacin sa yayi wannan ba wata matsala bace kada ki manta gadona yai domin kafinki nima haka naso wata mai suna Hauwa amma da ban sameta ba nace bazanyi aure ba har abada kwatsam babu zato na hadu dake dan haka shima zaiyi ki rabu dashi kada ki sake dora masa wata damuwar".


Son Al'ameen ya rufe maka ido kwata-kwata baka ganin laifinsa ko"?.


"A'a ba haka bane kece dai kikewa abin gurguwar fahimta ni duk yarana daya suke a gurina dan haka kibar wannan maganar lokuta da dama ina tunanin kamar kin fara gigi alhalin tsofa bai kama kiba".


Ni zan wuce ki kawo min abin sha" yana fadin haka yabar gurin kamar mami zatai kuka ta mike tana bin bayansa.


Bikin Abu kam ya karaso 'kememe mami tace baza taje ba daddy ko kadan bai nuna damuwa ba saboda ya kudurin aniyar indai bata jeba suna dawowa zai kara aure.


Kamar tasan abinda ke ransa sai ranar tafiya tace zataje baiso haka ba amma ya rabu da ita a tari gaba.


Harda Rukayya Zainab ma ta bisu wai zata gano kauyen su Fati wanne kalla ne.


Ranar daurin aure sukaje kwana biyu zasuyi Rukayya kam suna sauka ta debi yaranta ita da Sadiq suka tafi gidan hajiya acan zasu zauna domin sun saba sosai.


Fati da Afeeyah gari suka shiga Zainab da batasan garin bama haka ta fita yawanta ita kadai har kasuwar garin.


Lokacin da suka dawo Fati ta tsaya a gurin babarta Afeeyah kuma ta shiga gurin mami cikin fada mami ta kalleta tana cewa.


"Wato Afeeyah kin biyewa wannan shegiyar yarinyar ko wai kune har kasuwa wani ya sai muku nama dan ubanki saiya sa muku magani a ciki.


Cikin mamaki Afeeyah tace ni kuma mami da yaushe waye ya fada miki"?.


"Nice domin na ganku da idona" Zainab ta fada tana sakin murmushi tare da yimata gwalo.


Takaici ne ya kama Afeeyah wato sharri Zainab ta kulla musu jin mami tace wallahi kika kara binta yawo saina ci ubanki".


Yasa ranta a bace tace nifa mami ba muje kasuwa ba karya tayi min".


Ita kike cewa ta miki karyar saboda baki da kunya wannan yar 'kauyen ta koya miki rashin arziki".


Shiru Afeeyah tai karshe ma ta mike zata bar dakin mami tace gidan uban wa zakije ko yawon barbadancin zaki koma".


Kamar Afeeyah zatai kuka tace babu inda zanje fa kawai cikin gidan zan shiga".


"To cikin gidan da zaki shiga kin aje wani abu ne"?.


"Gurin yan uwana zanje".


"Dakyau sannu me yan uwa mu kuma daga gidan marayu muke ko? to dawo ki zauna har gobe da zamu tafi babu inda zaki sake fita" dawowa Afeeyah tai tana kwanciya akan katifa cikin tsantsar bacin rai.


MRS AL'AMEEN AHMAD CE😜.

Page 23 to 24.
Washe gari suka koma Abuja Fati da kukanta ta shiga mota dan cewa tai baza ta bisu ba ta dawo gida kenan saboda tsangwamar mami da take sha dakyar dady ya lallameta suka tafi".


Wanda suna komawa mami ta hura wutar sai daddy ya daurawa Al'ameen aure da Zainab wani lokacin har kuka take da hawaye a gaban sa.


Afeeyah na zaune a palor misalin karfe bakwai da rabi na safe Fati ta fito ganin ta yasa ta tsaya tana cewa .


Na dauka kina kitchen muje kada lokaci ya 'kure ".


Afeeyah dake duba abu a waya tace a'a ke kadai zaki nan da kwana hudu domin ina period idan yayana yaji sai yafi kwana goma baici abinci a gidan nan ba".


"Wanne yayan naki"?.


"Al'ameen mana ya Sadiq yana can gidansa da matarsa me zai kawo shi yin breakfast gidan nan.


'Yar dariya Fati tai tana zama kusa da ita daidai Al'ameen ya fito batare daya kalli inda suke ba yace.


"Naji abinda kika ce " yana fadin haka ya fita a palon rufe baki Afeeyah tai".


Fati dake kallonta tace to kinji abinda yace" mikewa tai suka shiga kitchen din dama saboda shi ne bazata taba kayan aiki ba.


Al'ameen gidan Sadiq ya wuce a dinning ya same su Amir da Aisha sai fada suke kamar kaji ga driver yana jira zai kaisu makaranta.


Zama yai yana hada tea bai kalli kowa ba cikin tsokana Sadiq yace sannu matashi ziyara ka kawo mana da safen nan kenan".

Al'ameen dake shan tea yace no breakfast nazo yi kawai".


"Ina na gidan ku" cewar Sadiq.


"Yana nan kawai na fito naji yaran nan suna zance period shiyasa bazan iya cin abincin gidan ba".


"To ai nima period din nake" Rukayya ta fada cikin boye dariyarta.


Aje cup din Al'ameen yai tare da sauya fuska zaiyi magana sai kuma ya fasa yana mikewa ya fice.


Da kallo suka bishi Sadiq ya girgiza kai yana cewa Al'ameen na rasa wanne kalar 'kyan'kyami gareshi ace mutum bazai ci abincin me period ba saboda me"?.


Dariya Rukayya tai tunda haka kawai idan yayi aure basai ya dauki yar aiki ba saiya samo namiji".


"Tab Al'ameen dinne zai dau namiji dan aiki a gidansa lallai har yanzu bakisan waye shiba bari na wuce hospital kada na makara da yawa".


Al'ameen na zuwa gida ya soma sheka amai kamar ba gobe karshe ma zazzabi ne ya rufe shi amma duk da haka bai fasa ba domin Lagos zasu wuce yasa kayan army dinsa kawai ya tafi".


Kwana uku da faruwar haka suna zaune shida Sadiq a palor ranar weekend cikin tsarguwa Sadiq ya kalli Al'ameen yana cewa".


"Wai kai na tambaye ka mana murmushin me kake tun dazu"?.


"Babu murmushin jin dadi ne kawai saboda na fahimta na gane wata gaskiya".


"Gaskiya ta me kenan".

"I am in love".


Zaro ido Sadiq yai cikin mamakin furucin Al'ameen din jin zancen nasa kamar mafarki yace.


"Da gaske kake ka samu wacce kake so"? Lallai zanso ganin yarinyar me sa'a data sace min zuciyar dan uwa na wacece ita a ina take ka sanar dani"?.


"Ok zan fada maka amma ba yau ba saboda tsaro ita din tauraruwa ce me haske zuciya ta saida ita ina sonta so me tsanani ma".


Sadiq da dadi ya gama cika shi cikin farin ciki yace mene sunan ta"?.


Dan shiru Al'ameen yai kamar me tunani sai kuma yai murmushi yana kallon sadiq yace Zarah "'

"Zarah yar waye" Sadiq ya tambaya.


Al'ameen yace no zaka santa ba yanzu ba tana da daukar hankal...........


Bai karasa ya dakata tare da kafe guri daya da ido muryarsa cikin wani yanayi yace" Zarah no one but you, I love u with all my body and heart bana iya hada ki da kowa".


Kallon inda yake kallo Sadiq yai wanda har saida yadan zabura yana dafe Al'ameen cikin mamaki yace" wai dama Fati na nan gidan kake nufi"?'.


"Eh ita bansan ya akai ko kuma yaushe bane haka nan rana daya na tashi naji na kamu da ciwon sonta kuma zan aureta ina da ra'ayin zama da ita zuciyata ta Abni ce amma yanzu ta Zarah ce .


"Wow gaskiya na taya ka murna ka kuma yi dacen mace idan har ka aureta domin tana da tarbiyya.


"Haka ne kyawawan dabi'unta ne suka rinjaye ni amma alfarmar da nake nema a gurin ka shine ya zama sirri tsakanin mu kada kowa ya sani".


Murmushi Sadiq yai cikin tsokana yace babu wanda zan fadawa masoyi zasu sani da kansu".



Bayan watanni uku Al'ameen na zaune a gaban su mami yana sauraron kiran da sukai masa'.


Daddy yace" wato Aminullahi dama batu ne akan aure ka samu wacce kake sone"?.


Kai Al'ameen ya girgiza a'a daddy babu".


"To maminka ce tace ya kamata a hada ku aure kai da Zainab shin me kake gani hakan yayi maka".


Caraf mami tace wanne irin yayi masa bashi zamu biye ba .


Daddy da hankalinsa ke kan yanayin da Al'ameen ya shiga yace bake na tambaya ba saiya yarda idan bai amince ba dole abar batun".


Kuka mami ta saka tana cewa shikenan nikam na kade na gama yawo alhaji meyasa kake min haka ne.


Hade rai daddy yai yana cewa Al'ameen tashi kaje kada ka damu Allah ya baka wacce kake so ta maye maka gurbin waccan.


"Amin daddy na gode" Al'ameen ya fada cikin jin dadi yana mikewa ya fita.


Mami dake goge hawaye tace yanzu alhaji haka ak......'.

Katseta daddy yai saurara Aisha bansan shashanci mubar maganar shiru mami tai tana sauke ajiyar zuciya takaici ya gama cika ta.


Yau da gobe tafi karfin wasa daddy ya gaji da nacin mami ta hana shi sakat tabi ta hargitsa kanta ta hargitsa gidan saida ya amincewa abinda take so.


Suna zaune Zainab ta fito cikin shiri zata fita tana kallonsu babu gaisuwa sa'kam-sa'kam tazo zata wuce.


Cikin tsawa mami tace ke gidan ubanwa zakije da yammar nan.


Dan tabe baki Zainab tai tana cewa bikin kawata ake zanje mata gurin event data gayyace.


Mikewa tsaye mami tai koma ciki babu inda zakije".


Zaro ido Zainab tai tana cewa tabdijan kinsan yadda muke da ita kuwa.


Mami tace dan ubanki ni kike cewa tabdijan ina matsayin yayar mahaifiyarki zaki iya fadawa Binta.


Zainab dake kad'a key din mota tace sosai ma saidai idan batai min abinda zance matan bane kinga ni kina bata min lokaci na wuce dan banga me hana ni naje ba .


Tana fadin haka ta bude kofar palor ta fita tana wa'ka mami data

2 Comments On DAN MILLIONAIRE
avatar
zainab-ibrahim-8

11 months ago

Reply

Thank

avatar
zainab-ibrahim-8

11 months ago

Reply

Than

Please Login or Register in order to submit comment