Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

DOCUMENT COMPILED BY SHURAIHU USMAN
TYPING HABIBULLAH MUHAMMAD KABARA
POSTED BY NAJIBULLAH MUHAMMAD
**MATSATSUBI**💥💥
LITTAFI NA UKU✍️✍️
PART A ❤️❤️
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️
TYPING: Habibullah Muhd Kabara ✍️✍️
Tom mun dawo bakin aiki...
Ina mana barka da JUMA'A fatan Allah ya maimaita mana❤️✍️🙏
Marubucin littafin ya ci gaba da cewa....
Lokacinda su jafar suka tsinci kansu a cikin wata
sabuwar duniya a samaniya sai suka kidime
suka cika da tsananin mamaki
domin kuwa komai akan iska yake yawo hatta
gidaje d dabbobin garin kuwa ba atsaye suke ba
awaje guda
su kuwa mutanen garin sun kasance masu wata
irin halitta tamkar dodanni kuma jikinsu kwari
gareshi kamar dutse
kaurin jikinsu da tsayinsu duk iri dayane babu
wanda yafi wani
gaba daya jikinsu lullube yak da gashi
kowannensu na da kaho guda biyu akansa
sunada manyan kunnuwa kamar n jaki kuma
idanuwansu da bakunansu irin na mutane ne
sosai amma hannunsu 'yan kanana ne kamar
dosana su akayi suna tafiya ne acikin iska
kamar ana cilla kibiya duk da cewa basu da
fukafukai
su kuwa su jafar idan suka daga kafafunsu da
nufin suyi tafiya sai suga ana juyasu acikin iska
kamar katantanwa bisa dole suka tsaya waje
guda suka cure su biyar din
gaba daya mutanen garin babu wanda ya kalle
su bare yace
ci kanku, kuma duk wanda sukayi kokarin yiwa
magana baya sauraronsu
haka dai sukaci gaba da tsayuwa awaje daya her
tsawon wani lokaci
kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaga
gungun mayaka sanye da kayan karafa
kimanin su dari sun taho garesu cikin
matsiyacin gudu acikin iska
wadannan mayaka suma irin mutanen garin ne
kowannensu na dauke da wani irin lafcecen
makami irin wanda su jafar basu taba ganiba
da zuwan mayakan sai suka yiwa su jafar
kawanya ya zamana babu 'yar kafa wadda zasu
iyabi su wuce
daya daga cikin mayakan ya fiddo wani abu
acikin rigar karfensu mai kama da madubin
karfe ya shafe shi
saiga hoton fuskar sarkinsu ta bayyana akai
sarkin ya kasance mai rafkeken kai wanda yafi
na kowa girma agarin kuma shi kaho dayane
akansa hakama idon sa da kunnensa duk dai
dai ne
wanda ke rike da madubin ya dubi sarki yace
ya shugabana gamu nan tare da bakin me
kakeso ayi musu?
kodajin wannan tambayar say sarkin ya
kyalkyale da dariya cikin wata Irin murya mai
kama da karar karafa yace
yauwa kuyi maza ku kawosu fadata hakika burin
mu na daf da cika domin abin da muka dade
muna nemane bamu samuba to yau sune
sukazo suka kawo kansu
yana gama fadin hakan ne dakarun suka cafke
su jafar sukayi sama dasu suka cilla aguje cikin
iska nanfa sukayi ta gifta garuruwa da birane da
kauyuka iri iri har suka iso wata babbar alkarya
wadda tun akofar birnin sukaga an rubuta
BARKA DA ZUWA BIRNIN HARJULUL MULK
birnin harjulul mulk ya banbanta da sauran
biranen dake wannan duniya, domin gidajensa
da komai nasa akan turba suke waje guda,
ma'ana babu wani abu dake yawo asama cikin
iska,
koda aka shigar dasu cikin birnin sai suka ga an
sauko kasa ancigaba da tafiya akasa bisa turba,
abindaya basu mamaki shine gaba daya biranen
birnin anyi sune da zallan karfen zinare
kuma an kawatasu da kayan alatu fiye da
tunanin kwakwalwa
haka kuma mutanen garin da mutane masu irin
halittar su jafar wato b dodanni bane dukkansu
al'amarin daya jefa su jafar cikin matukar
mamaki kenan
koda ganin su jafar ahannun dakarun tsaro sai
jama'ar suka kura musu idanu suna mamakin
ganin su
babu wanda yace dasu kala har akayi tafiyar
kusan rabin sa'a sannan aka iso wani babban
gida mai tsananin fadi da tsawo
wanda idan mutum ya daga kansa bai isa ya
hango rufinsa ba
har yanzu dakarun suna rukunkume dasu jafar
ko kyakkyawaan motsi basa iyayi
da kofar gidan sarki sai wata kofà mai siffar
kwai ta bude kanta ,kai tsaye dakarun suka
shige dasu jafar ciki sannan kofar ta rufe kanta
da shigarsu sai suka ga wasu ma'aikata
azazzaune kan kujeru da tebura
akan kowanne tebur wani farin allon tsafine
gaba dayan ma'aikatan kowa na rike da wata
siririyar sandar tsafi
ajikin kowanne allon tsafi ana ganin abinda yake
faruwa awata duniyar daban
akalla za'a iya samun allon tsafi guda miliyan
dubu daya awannan tamgamemiyar fada
hakama adadin mutanen dake sarrafa madubin
yake
daga can karshen fadar kuwa bisa wani gini mai
tudu sukayi arba da wani katon allon tsafi
wanda yafi gaba daya sauran girma,
zaune agaban allon sarki arbir ne zaune
yakurawa su jafar idanu yana murmushi
abindayà daurewa su jafar kai kenan cikin
tsananin mamaki jafar ya dubesu alokacinda
dakarun nan suka watsar dasu agabansa
tamkar an watsar da tsummokara jafar yace
yakai sarki azbir ya akai kazo nan alhalin mun
rabu dakai tun acan duniyarka abakin rijiyar nan
data zukemu
sarki azbir ya mike tsaye yazo gabansu jafar
wadanda ke zaune dirshan akasa ya tattashesu
tsaye
sannan ya rike hannun jafar yace
ka kwantar da hankalinka yaka jafar ku sani
cewa yau kun fado hannun sarki azmul gallar
mai mulkin birnin harjulul mulk
birnin da shine mafi girma da daukaka acikin
wannan nahiya ta duniyoyin sama
inason ka sani cewa sarki azmul gallar ya tsani
sauran duniyoyin dake can kasa
wato kamar irin duniyarku kuma bashi da wani
buri wanda yafi ya shafesu gaba daya daga
doron kasa
yayi binik ya gano cewa idan yana son ya
hallakar da duniyoyin dake doron kasa dolene ya
kera wani sundukin tsafi mai tsananin haske ya
aikashi izuwa can duniyoyin kasa
hasken wannan sundukine zai narkar da
wannan duniyoyin gaba daya
yanzu haka angama kera wannan sunduki
amma an kasa aikashi saboda so ake asamu
mutane irinku acikin wannan sundukin guda
uku ko sama da haka
sannan sundukin zai iya tafiya
haka kuma sundukin babu wanda zai iya sarrafa
sundukin face ni kadài
shiyasa sarki azmul gallar ya kamoni ya kawoni
nan
kuyi duba izuwa can kuga abin mamaki
cikin sauri jafar, jelisa, gulzum, da mazalish
suka juya suka dubi inda sarki azbir yayi musu
nuni
kawai sai. sukayi arba da ita
ba kowa bace face katuwar macijiyar nan mai
kawuna barkatai wadda ta had! yesu
cikin tsananin tsoro suka ja da baya gaba
dayansu
adaidai wannan lokacin ne macijiyar ta sauko da
kanta guda daya kasa ta wangame shi kamar
zata hadiye komai dake wajen
bisa mamaki sai suka ga sarki azmul gallar ya
fito ta cikin bakin macijiyar yana kyalkyla dariyar
mugunta yana fita daga bakin macijiyar ya dafa
kanta yace
jeki abinki uwar macizai na sallame ki
kamar walkiya macijiyar ta bace bat sarki azmul
gallar ya dubi su jafar daya bayan daya ya jinjina
kai sannan ya sake bushewa da dariya wacce
tayi dai dai da irin ta mutane ba dodanni ba
kamarsa
azmul gallar ya dubi su jafar yace
gaisheka takadirin yaro kaine wanda ya zamewa
boka shamharu alakakai
kuma kaine mai shirin zama alakakai agareni
amma bazan baka damar yin hakanba
ka sani cewa ahalin yanzu ka bankado sirrin
boka shamharu domin kaine sanadin bude
KUNDUN TSATSUBA
tabbas gaba daya sirrikan tsafin boka shamharu
na nan cikin littafin KUNDUN TSATSUBA na
farko
nikuma nawa suna nan acikin sabon KUNDUN
TSATSUBA na biyu wanda yanzu haka
mahaifinka ruziyal yana kam aikin ruvutashi
acan duniyarku tareda aljni rafkamagu da boka
hajarul makarus wadanda ke taimaka masa
wajen ziyaràr sarakunan duniya suna basu
labaran abubuwan al'ajabi
ya zama dole agareni na tsaida wannan aiki
nasu ta hanyar ta hanyar kulle sabon KUNDUN
TSATSUBA da kubar MUFTAHUL ZARBIL
yanzu haka kubar MIFTAHUL ZARBIL na nan
ajikin kundun na farko
wanda kuka fara karantawa kubar ba zata
zaruba daga jikinsaba ta kowanne hali harsai
kun gama karanta littafin
gama karanta littafin kuwa zaikai tsawon
shekara goma sha tara da "yan watanni kuma
lokacin zaizo daidai da lokacinda za'a gama
karanta sabon KUNDUN TSATSUBA zai zo dai
da lokacin da za'a hattama rubuta kundi na b!yu
idan na bari aka kai wannan lokacin za'a san
sirrina
ya zama wajibi agareni na kera sabuwar kubar
MIFTAHUL ZARBIL
wannan kubar kuwa bazata keruba face na
narkar da duniyarku gaba daya
da narkakkiyar kasar duniyar kune zan iya kera
kubar MIFTAHUL ZARBIL
yanzu sai ku shirya don zan sauya muku halitta
ne yadda zan iya c!ka burina
koda sarki azmul gallar yazo nan azancensa sai
hankalinsu jafar ya dugunzuma
yeli$a,mashrila, da sarki azbir suka kama kuka
saboda sunji ance za"a sauya musu halitta
kuma koba komai sunsan ba karamar wahala
zasu sha ba akan wannan aiki wata kilama su
iya rasa rayuwarsu
jafar, mazalish, da gulzum kuwa kokadan basu
razanaba dajin wannan batu na sarki azmul
gallar
cikin rashin tsoro da gadara jafar ya dubi sarki
azmul gallar yace
yakai wannan sarki inason ka wayar mini dakai
akan matsayin boka shamharu awajenka
domin na fuskanci cewar kusan burinku daya
shin yanason ya mallaki komai da kowane dake
duniyar kasa, kai kuma kanaso ka hallaka komai
da kowane dake duniyar kasa,
kodajin haka sai azmul gallar ya bushe da dariya
yace
yaro baka fahimta sosaiba ai tsakanina da
shamharu babu komai face matsananciyar gaba
kamar yadda na fada muku cewar bazan iya
kera kubar MIFTAHUL ZARBIL ba saina narkar
da duniyarku haka shima shamharu bazai iya
tsaidaku daga karatun KUNDUN TSATSUBA na
farko ba harsai ya narkar da wannan duniyar
tamu
kusan kuwa abune da bazai taba yiwuwaba
agareshi.
Mu hadu a part B don Jin cigaban wannan KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️
**MATSATSUBI**💥💥
LITTAFI NA UKU ✍️✍️
PART B ❤️❤️
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️
TYPING: Habibullah Muhd Kabara ✍️✍️
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA..
Kafin wani daga cikin su jafar ya kara cewa
komai sai sarki azmul gallar ya dubi dakarun
nan da suka zo dasu jafar take suka kama su
suka hada da sarki azbir suka nufi wni bangare
daban dasu
sai da akayi wata 'yar doguwar tafiya dasu
sannan aka shigo wani katon daki
babu komai acikin dakin face tarin wasu manya
manyan tukwane na gilashi
acikin tukwanen ruwan zafine launi launi yanata
zabal bala
wani ruwan sai kaga ja ne, wani kuma shudi,
wani kore kai atakaice dai babu irin kalar d
babu
ba tareda bata wani lokaciba dakarun nan suka
daure su jafar d wata sarkar tsafi
wadda da zarar su jafar sunyi yunkurin kubuta
zasuji kamar ana tsotsar jinin jikinsu
bisa dole suka rungumi kaddara ,wani abin
mamaki shine aljani gulzum yafi wadannan
dakarun girma da kwarjini
amma sarrafa shi suke kamar dan mitsitsin
yaro da babba
koda su jafar suka ga anyi musu mummunan
dauri haka sai hankalinsu ya dugunzuma suka
rasa abinda yake musu dadi tsoro ya baibaye
zuciyar su ta fara bugawa da sauri
nantake dakarun nan suka kama sarki azbir da
karfin tsiya suka nufi wata kwalba mai dauke da
shudin ruwan zafi
nan take sarki azbir ya kama ihu da koke koke
yana rokon su kyaleshi
al'amarin daya kara dugunzuma hankalinsu
jafar kenan
don basu san dalilin dayasa sarki azbir ya
firgice haka ba her yake kukaba
adaidai wannan lokaci ne sarki azmul gallar ya
shigo cikin dakin yana kyalkyla dariyar farinciki
kawai sai ya dakawa dakarun nasa tsawa yace
me kuke jirane dashi?
maza ku jefasho cikin kwalbar mana
kafin azmul gallar ya gama rufe bakinsa tuni
daya daga cikin dakarun yasa hannu biyu ya
bude murfin kwalbar mai kma da katon faranti
aikuwa yana budewa aka jefa sarki azbir a ciki
aka rufe ,tamkar an sanya alli acikin ruwa haka
jikin sarki azbir ya dinga zagwanyewa
tun yana ihu ana jin muryarsa har muryar ta
dishe
ahankali gaba daya jikin nasa ya narke ya
cakude da ruwan cikin tukunyar ya dinga
hautsinewa yana bori kamar kwalbar zata fashe
jim kadan kuma sai aka g ainihin siffar sarki
azbir ta dawo
kuma ya dinga rikida ya zama abubuwa iri iri
kamar kyanwa, maciji, kunama, da sauransu
saidaya zama abu dari da daya
acikin darin ne ya zama wani irin mummunan
gwaggon biri ya zana zama hakan sai kwalbar
ta fashe da kanta
gwaggon biri ya tako da kafafunsa yaje gaban
sarki azmul gallar yana mai sujjada
alamun yin biyayya,
cikin tsananin farinciki azmul gallar ya bishe da
dariyar mugunta
duk wannan abu dake faruwa au jafar n gani
kuma tuni sun fara kuka da bakin ciki
jafar ya dubi gulzum yace
amma dai kaji kunya tunda karfinka da
girmanka ya zama na banza bazaka iya ceton
mu ba
gulzum yayi tsaki yace
amma dai kai banzane waya gaya maka cewa
karfi da girma zaiyi tasiri anan?
ina tabbatar maka da cewa ko boka shamharu
ne ya kuskura y fado nan ya zama nama sai
yadda akayi dashi
bare ni daban zama komai a ilimin tsafiba
ita kuwa yeli$a saita dubi mazalish tace
yake ma'abociyar hikima, ina rokonki daki
hanzarta tunanin kubutar damu
inba haka b yanzun nan za'a mai damu irin
ahinda aka maida sarki azbir
kodajin wannan batu sai hawaye ya zubowa
mazalish tace
yake kawata kiyi sani cewa. hikima ko karfi ko
sihiri ba zasuyi aiki anan ba
domin sunzo gidan kakanninsu
inda kunsan ma abindana sani da kun
gwammace mutuwa gaba daya yanzu take
ina bakin cikin sanar daku cewa idan har sarki
azmul gallar ya mai damu burarrika to har abada
babu wanda zai iya dawo damu ainihin siffar
mu face shi kadai
ku sani cewa idan aka samu acikin sundukin
haske aka tura mu duniyar mu to mun tafi
kenan ba zamu sake dawowaba
bare ya dawo damu ainihin siffofin mu
ku sani cewa alokacinda sundukin hasken zai
narkar da duniyarmu to tareda mu zata narke
kunga shikenan tamu ta kare
mazalish na gama fadin hakan kenan
sarki azmul gallar ya tsaya da dariyarsa
sannan ya dubi su jafar yace
to idan akwai wanda yakeda wasiyya ga
danginsa ko 'yan uwansa saiya fada kafin n
jefaku acikin kwalbar tsafi tabbas zan taimaka
nakai wasiyyar
mazalish ta share hawayenta tace
inada wasiyya amma ga masoyina JARUMI
HUBAIRU abokin gaba LU'UMANU
inason ka bashi labarina ka fada masa cewa na
baro kasata saboda shi, na kashe mahaifina
saboda shi kuma na rabu da mahaiyata
sabodashi don kawai y zama abokin rayuwata
wannan shinè kadai burina lallai banaso na.
mutu ba tareda hubairu yasanni ba a duniya
kodajin wannan batu sai sarki azmul gallar yayi
yace
ai wannan mai saukine nayi alkawarin zan idar
da wannan wasiyya,
waye kuma zai sake bayarda wata wasiyyar
daga cikinku? azmul gallar ya tamb@ya
jafar ya dubeshi yatsine cikin raini yanzu kai
nan nufinka shine zakayi amfani damu wajen
biyan bukatrka mu kuma mu hallaka?
to kasani cewa buktarka bazata biyqba kuma
zamu dawo nan mu yakeka mu tarwatsa
dukkanin irinka
kodajin wannan batu sai sarki azmul gallar ya
tuntsure da dariya ya karewa jafar kallo sama
da kasa sannan yace yakai jafar kai kuwa mene
takamarka?
ka sani cewa nafiku karfi, sihiri da komai tayaya
zaku iya yakata harku sami nasara akaina?
jafar yace bana takama da komai face sa'a
ka sani cewa babu wanda yayi tsammani cewa
zamu iya dauko kundun tsatsuba bare har mu
iya samo kubar miftahul zarbil mu budeshi
gashi yanzu harmunyi nisa acikin karatunsa
muna kan shafi na ashirin da daya
bana mamakin cewa zamu iya kubuta daga
hannunka harmuje wata duniyar inda zamu
hadu da wani takadirin wanda yafika shaidanci
azmul gallar yayi murmushi yace ai yaro kayi
kuskure babu wani mahaluki kmata tsakanin
duniyarku ta kasa da sauran duniyoyin dake
nan sama
da wannan kalami nake muku sallamar karshe
ina maiyi muku fatan riskar ajalinku @saukake
cikin "yan dakiku kadan
yana gama fadin hakan ne dakarun nan suka
kama jafar, yeli$a, gulzum, da mazalish suka
tsomasu acikin kwalaben nan masu ruwan zafi
nan take jikinsu y fara narkewa tun sunayin ihu
har suka kasa
ahaka dai har siffofin su suka juye izuwa na
burarrrika kamar yadda aka maida sarki azbir
koda aka fito dasu daga cikin kwalaben wato
bayan kwalaben sun farfashe da kansu
sai suka jeru su hudun suka zube gaban sarki
azmul gallar suna masuyi sujjada agareshi
cikin tsananin farinciki azmul gallar ya kece da
dariya sannan ya dubi dakarunsa yace
ku tafi dasu izuwa dakin sundukin 'aske
cikìn biyayya dakarun suka iza keyar burarrikan
shida sukai gaba saida sukayi tafiyar rabin sa'a
cif sannan suka iso wani tangamemen daki
babu komai acikin dakin face wani mulmulallen
karfe mara nauyi asamansa ankifa wani
zagayayyen gilashi mai siffar kwai
wanda ta cikinsa na iya hango wasu kujeru
guda shida dake cikin sa
kujera ta farko nadaga gaba sauran kujerun
kuwa guda biyar suna bayanta ajere reras
agaban kujera ta farko kuwa wadansu yan
kananan ramukane guda huda ja, fari da ruwan
dorawa
kowanne rami arufe yake da gilashi amma
akwai siririn tsinken tsafi ajikinsa
da shigowa cikin wannan daki saisu jafar
sukayì arba da wannan gabjejen sunduki na
farin karfen gurar ruwa
nanfa suka wangame baki suna kallon surar
dukda sun kasance acikin siffar burrai kasan
cewa mamaki sukeyi
batareda bata lokaciba sarki azmulgallar ya
nuna su jafar da danyatsa
kawai sai suka bace bat basu bayyanaba sai
acikin sundukin karfen
sarki azbir ne agaba,
jafar yelisa ,gulzum, mazalisha
na daga kujerun baya koda suka tsinci kansu
cikin wannan sunduki sai suka mimmike tsaye
sunata dukan gilashin daya rufesu don su sami
damar fita amma abanza kamar suna dukan
dutse
koda sarki azmul gallar ya ga haka sai ya sake
nunasu da hannunsa na hagu
t@ke suka koma suka zauna, zamansu keda
wuya sai sarki azbir ya taba daya daga cikin
tsinkayen tsafin dake gabansa
yin hakan keda wuya sai wani irin haske mai
tsanani ya baibaye sundukin tareda wata irin
iska
cikin gaggawa azmul gallar da dakarunsa suka
ruga waje suka rufe kofar dake dakin
bayan kamar dakika goma sai dakin ya kama
girgiza
nantake sundukin ya tunbuke kansa daga jikin
wasu turakan karfe da aka daurèshi ajiki yayi
fitar burgu tacikin wata tangamemiyar fada
koda sundukin ya baiyana asararin samaniya
saiya juya ya kalli kasa ya fara azabbabben
gudu dauke da burarrrika shida acikinsa sai dai
wannan gudu da sundukin yake yafi gaban
kwatance domin zai iyq cin zango miliyan dubu
acikin dakika biyar
WANNAN SHINE ABIN DAYA FARU GASU
JAFAR BAYAN SUN FADA CIKIN SHAFI NA
ASHIRIN DA DAYA ACIKIN KUNDUN TSATSUBA
Al'amarin gimbiya sima kuwa lokacin data ruke
mashì ta nufi jarumi hubairu gadan gadan da
niyar sokeshi
kawai sai akaga sararin samaniya ta cika da
wsu fararen abubuwa masu kama da balbelu
cikin sauri sarki lu'umanu ya daga kansa sama
ya fara nazarin abubuwan don yaga ko menene
itama gimbiya sima saita tsaya kyam tana
kallon sama.
MU HADU A PART C DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️🙏
**MATSATSUBI**💥💥
LITTAFI NA UKU✍️✍️
PART C ❤️❤️
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️
TYPING: Habibullah Muhd Kabara ✍️✍️
#LEGENDs.
Marubucin littafin ya ci gaba da cewa....
KODA abubuwan sukayo kasa kasa sai akaga
ashe sarki hudes ne mahaifin aljani abtarul
hudes
tareda sauran dakarun musulmi dukkansu sunyi
shigar fararen tufafi rike da makaman yaki kuma
suna ta firfita tutar musulunci mai dauke da
kalmar shahada
koda ganin haka sai gaba daya dakarun sarki
lu'umanu suka firgice
saboda kwarjinin dakarun muslunci
cikin dacin rai sarki lu'umanu ya zare takobinsa
ya yi tsalle sama ya dira kan daddumarsa ta tsafi
sannan ya dubi dakarunsa ya daka musu tsawa
yace
me kuke jirane ga makiyan mu maza ku taresu
kafin su sauko kasa
da ike akwai sauran dakarun nan na shamharu
tareda lu'umanu sai suka bude fukafukansu
sukayi sama
wato suka tari sarki hudes aka fara rubdugu
asararin samaniya
shikuwa sarkin lu'umanu sai yayi amfani da
wannan dama ya nufi inda jarumi hubairu ke
daure da niyyar sare masa kai
koda ya iso kansa ya daga takobinsa ya kai
masa sara awuya da nufin ya tsinkeasa kai
kawai sai yaga an kare saran da wata zabgegiyar
takobi mai ban al'ajabi da matukar girma
wadda ta haddasa tartsatsin wuta da kara mai
firgitarwa
koda ya dubi wanda ya rike takobin saiyaga
ashe
sarki hudes da kansa ya kawowa hubairu dauki
duk d jarumtaka da sadaukantaka irin ta
lu'umanu sai daya firgita ya dan ja da baya ya
tsaya yana shawarar ya gudu ko ya tsaya sarki
hudes ya dakawa lu'umanu tsawa yace
yakai tsohon makiyin allah ai na gane cewa ba
kaine ainihin lu'umanu ba
tabbas aljani zarmukune ya shiga jikin gangar
jikin lu'umanu
ina umartarka daka hanzarta fita daya jikinsa
yanzu yanzu nan
ko kuma n gama dakai yanzùn nan
kuma daga yau idan na kara haduwa dakai ako
ina saina kasheka in baka tuba ba a daina
taimakon mushrikai
koda fadin haka sai lu'umanu ya kece da wata
irin mahaukaciyar dariya
wacce ta kasance bata ainihin muryarsa bace
lokaci guda kuma aljani zarmuku ya fita daga
jikin lu'umanu
take gangar jikin t fado kasa bisa daddumar
tsafi
sannan aljani zarmuku ya dubi sarki hudes ya
dubi sarki hudes ya nunashi da yatsa yace
yakai tsohon abokin gaba kayi sani cewa
tsakanina dakai tsohuwar gabace
akalla nayi yaki dakai akalla sau dari uku d
arba'in da hudu idan muka sake gwabzawa
yanzu
shine cikon na dari hudu da arba'in da biyar
tsakanina dakai ba gudu ba ja da baya kuma
bakin rai bakin fama
kayi sani cewa irina guda dubu ne masu shiga
sarki lu'umanu
ayanzu haka jarumi hubairu ya kashe daya daga
cikin mu saura dari tara da casa'in da tara, don
haka koda
ka kasheni kayj abanza akwai sauran yan uwana
suna nan
cikin fushi sarki hudes ya sake dakawa aljani
zarmuku tsawa a karo na biyu yace
kai la'anannen allah kayi sani cewa koda kunkai
miliyan dubu bazan gaji da yin fada dakuba har
saina karar daku
dani daku mu zuba mu gani dan halak ka fa$a
kafin zarmuku ya kara cewa wani abu tuni sarki
hudes ya zare takobi ya kai masa wawan sara
akafada cikin zafin nama aljani zarmuku ya goce
sannan ya rikida ya zama haske ya shiga jikin
sarki lu'umanu kamar an tabe baka haka
lu'umanu ya mike tsaye zumbur ya zare
takobinsa suka fara artabu, dama tundazu an
dade ana gwagwarmaya acan sararin samaniya
koda aka fara wannan gumurzu tsakanin hudes
da zarmuku sai waje ya sake rikicewa gab daya
ya zamana band@ ihun maz@je da karafkiyar
karafa babu abinda kunne keji
aljani zarmuku cikakken kafirine wanda ya tsani
musulunci da musulmi ya dade akan wannan
akida tasa,
kuma ya jima yan@ hada rundunar bakaken
aljanu don su murkushe musulman aljanu na
duniya baki daya amma burinsa bai cikaba
ya sha haduwa da sarki hudes amma idan gamo
yayi gamo yaga zai hallaka saiya tsere wannan
guduwar da yake yi zuciyar sarki hudes
ba karamin sosuwa takeyiba
don haka wannan karon shima yaci alwashin
wannan karon bazai sake sakewaba yabarshi ya
gudu
lokacinda aka sami sa'a bakwai ana wannan
dauki ba dadi sannan dakarun sarki hudes suka
samì nasarar gamawa da dakarun lu'umanu ya
zamana sun kashesu gaba daya
don haka ya rage saura sarki hudes da zarmuku
kawai ats@kiyar sararin samaniya suna
gumurzu
tuni awannan lokaci gimbiya sima ta fadi kasa
sumammiya sakamakon bala'in gumurzun da
akeyi da tartsatsin wuta
ihun mazaje da karar makamai
suma mutanen garin gaba daya sun fashe
wasu sun sume wasu $un haukacebisa ganin
aljanu kiriri anacikin fafayawar ne sarki hudes ya
sami
nasarar yiwa zarmuku wani mummunan sara
ahannun sa n dama
take hannun ya gutsire ya fadi kasa
zarmuku ya kwalla ihu cikin tsananin jin zugi
nantake ya rikide ya zama wuta, wutar tayi feshi
ga hudes ga hudes da niyyar ta konashi
cikin ikon allah sarki hudes ya yi kabbara
koda wutar ta sauka ajikinsa saita zama ruwan
sanyi
nanfa zurmuku yaci gaba dayin tsafi yana zama
mugayen abubuwa don ya lahanta sarki hudes
amma saiabu ya gagara
koda sarki hudes yaga zarmuku zai bat masa
lokaci saiya shiga karanta wadansu manyan
addu'o'i masu dauke da ismul a'azam
aikuwa sai nanda nan sihirin tsafin zarmuku ya
karye ya kasa yin komai babu yadda baiyiba don
ya bace amma ya kasa
cikin zafin nama sarki hudes ya sakè daga
rantsatstsen takobinsa ya kaiwa zarmuku sara
da
nufin ya tsargeshi gida biyu
kawai saiyaga anyi sama da zarmuku kamar an
janyeshi da kugiya cikin sauri sarki hudes ya
daga kansa sama don
yaga wanene
sai sukaga bakan gizone ya bayyana kuma shine
ya dauke zurmuku
cikin abinda bai wuce dakika dayaba bakan
gizon
ya sake sure gangar jikin lu'umanu wacce ke
sharbe akan dardumar tsafi,
ya sake kaiwa jikin sima sura da nufin ya
dauketa
sai sarki hudes ya lullube ta da fukafukansa
yana
mai cigaba da karanta addu'o'insa
kawai sai yaji wani irin ihu da karaji dga bakan
gizon lokaci guda bakan gizon ya bace tareda
zarmuku
da gangar jikin lu'umanu
koda ganin faruwar hakan sai dakarun sarki
hudes suka kama kabbara cikin farincikin
samun
nasarar wannan yaki
waziri kuddaru kuwa saboda farinciki saida
kwalla ta zubo masa
adaidai wannan lokacin gimbiya sima da jarumi
hubairu suka farfado
koda gimbiya sima ta kyalla ido taga mashinta
saita ruga ta dauka ta nufi inda jarumi hubairu
yake da niyyar ta tsireshi cikin zafin nama sarki
hudes ya sha gabanta ya
kama mashìn ya ruburbusheshi tamkar
nukakken
kashi
sannan ya shafeta da gefen dan yatsansa take
ta
sake faduwa kasa sumammiya
wannan abu daya faru ba karamin mamaki ya
baiwa jarumi hubairu ba yana mai cewa aransa
yanzu sima ce ke kokarin hallakani?
adaidai
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

1 Comments On MATSATSUBI BOOK 3
avatar
abasu-kala

3 months ago

Reply

Good really enjoy the book waiting for Miftahul Zarbil

Please Login or Register in order to submit comment