Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

GWARZON SADAUKI
Littafi Na Daya (1)
Part A
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
Kurkuku ne wanda aka gina dakunsa da katangarsa da zallan duwatsun wuta. Kofofin gidan gabadaya da tagoginsu an yi su ne da bakin mummulallen karfe mai kaurin kamu guda. Tsayin katangar wannan kurkuku kamu sittin ne don haka duk wani fursuna da ke cikinsa bai taba tunanin haurewa ba. Akalla akwai zaratan dakaru guda dubu daya da đari biyu. masu gadin wannan kurkuku wadanda su kansu ababen tsoro ne saboda kwarjininsu gami da surarsu ta manyan sadaukai domin ido ba mudu ba ne amma ya san kima.
A daidai wannan lokacin fursunoni na tsaitsaye a tsakiyar wannan kurkuku suna yar hada- hadarsu kamar yadda suka saba. Wasu suna wasan motsa jini wasu hira suke yi!wasu kuma suna kai kawo. Dama kullum an ware musu irin wannan lokaci domin samun nutsuwa. Kwatsam! Sai suka ji motsin bude katuwar kofar gidan wacce tsawonta da fadinta kamu sittin-sittin ne. Karar bude kofar ta cika dajin gabadaya da amsa kuwwa kai ka ce wani katon dutse ne ya mirgino da gudu. Ita dai wannan kofa ana budeta ne da wata irin na'ura mai dauke da kaca da kuma hakoran mawanin karfe mai juyawa. Dakaru ashirin ne ke iya juya mawanin sannan kofar ta bude a tsawon dakika dari uku da sittin.
Kofar na gama budewa sai fursunoni suka ga dakaru kimanin guda arba'in sun tuso keyar wani mai laifi wanda aka daure hannayensa da kafafunsa da manyan sasari kai ka ce giwa a ka janyo.
Shi dai wannan mai laifi ya kasance matashin saurayi wanda shekarunsa baza su haura ashirin da shida ba. Ya kasance kyakkyawa ne mai kirar sadaukai. Fuskarsa cike take da murmushi kawai sai kalle-kalle yake yi yana duban tsawon katangar gidan da kuma tsarin kofofin da tagogi.
Bayan an shigo da wannan saurayi tsakiyar kurkukun a lokacin da aka rufe kofar shigowa sai aka tsayar da shi cak aka fara kallon kallo tsakaninsa da Sauran fursunonin gidan. Kowa sai ya tsaya ya daina abin da yake yi. Su dai fursunonin gidan mamaki suke yi kuma suna tambayar junansu suna cewa wannan kuma wane takadari ne haka har da za a daure shi cikin manyan sarkoki. A saninsu duk wani gawurtaccen ma laifi a duniya idan aka kawo shi wannan kurkuku nanbirnin Kisra risina yake ya kama kuka da nadama to amma shi wannan gashi da murmushinsa ya shigo ko kuwa bai san Irin masifar dake ciki ba ne.
Wata irin muguwar rayuwa ake yi cikin wannan kurkuku wacce mai karfi ne kadai yake tsira. Ba a raba abinci a cikin nutsuwa sai masu Karfi sun fara dibar nasu sannan in ya yi ragowa marasa karfi su diba. Idan mutum ba samu ba sai dai ya kwana da yunwarsa. A kullum akan dauki gawa guda biyu ko uku a cikin wannan kurkuku saboda bakin zaluncin da ke faruwa a tsakanin fursunonin.
Idan fursunoni za su kwana suna yaki a tsakaninsu ko kallonsu dakaru ba za su y ba. amma a da zarar fursuna ya karya doka guda daya take dakaru za su ufe shi da luguden duka sai sun ga ya suma sannan za su kyale shi kuma a dauke shi a kai shi wani kuntataccen daki wanda ko kwanciya zai yi ba zai iya mike kafafunsa ba kuma daki ne cike da shara, tsutsa ga doyi sauro da kudaje ma sun ishi mutum masifa.
Ana cikin wannan kallon kallo tsakanin bakon fursuna da sauran fursunonin gidan kenan sai wata kofa daga can wani bangare ta bude, shugaban dakarun gidan ya fito tare da wasu tsirarun dakarunsa masu ake masa baya suka durfafo inda bakon fursuna yake.
Shi dai Shugaban dakarun wannan kurkuku ya kasance wani garjajen kato mai sura irin ta mutanen farko Kallo daya za ka yi masa ka san cewa sadauki ne kuma jarumin gaske mai fasa taro. Shigarsa ta fita dabam da ta sauran dakarun gidan domin rigarsa, takalmansa da doguwar safar hannu duk na karfe ne Takubba biyu ne rataye a bayansa.
Duk jikinsa a murde yake cike da kwanji ga jijiyoyi burdin-burdin. Sai da suka iso daf da bakon fursunan yadda tazararsu ba ta wuce taku biyu ba sannan suka tsaya cak shugaban dakaru da bakon fursuna aka yi kallon kallo na tsawon dakiku biyar sannan Shugaban dakarun ya yi dan guntun murmushi ya dubi bakon fursunan ya ce.
"Sunana Gadaraz ni ne shugaba a wannan kurkuku Ya kai bawa Insam na yi maka barka da zuwa gidan mutuwa. Labari ya iske ni cewa sau biyu kana samun nasarar guduwa daga can kurkukun cikin gari ana kamoka da kyar to ka sani nan ba a iya guduwa. Duk fursunan da aka shigo da shi nan sai dai a fitar da gawarsa amma bai įsa ya fita a raye ba. Yau tsawon shekaru goma sha hudu kenan da kafa wannan kurkuku ni da jama'ata muna gadinsa babu wani fursuna da ya taba karya wannan tarihi. Ka sani muna da dokoki guda tara a gidan nan. Dokoki biyar daga ciki idar ka aikata su za a yi maka hukuncin
dukan kawo wuka gami da horo nai tsanani Ragowar dokoki guda hudu kuwa hukuncin kisa ne a kan su. Ina mai yi maka gargadi da ka kiyaye wadannan dokoki wadanda za a sanar da kai su yanzu take idan kana son ka tsira da lafiyarka da rayuwarka."
Koda gama fadin hakan sai shugaban dakaru Gadaraz ya dubi wani Badakare ya ba shi umarmi.
Badakaren ya bude baki ya ce.
"Doka ta farko a gidan nan ita ce. "
Caraf sai bawa Insam ya tari numfashin Badakaren ya ce. "Dakata ba na bukatar jin dokokinku lna son na karya kowace doka daya bayan daya har guda taran yadda za a iya hukunta ni. Daga yau ina mai tabbatar maku da cewa babu wata doka da zata yi aiki a kaina sai dai akan sauran fursunoni.
Ko da jin wannan batu sai dakarun dake kewaye da Gadaraz suka daga kulakensu za su afkawa Bawa Insam amma sai Gadaraz ya daka musu tsawa ya ce, "Ku dakata ka da ku tabashi.
Da jin haka sai dakarun suka ja da baya suka tsaitsaya. Gadaraz ya dubi Insam ya bushe da dariyar mugunta. Lokaci guda kuma ya murtuke fuskarsa ya ce "Da kyau haka nak s ha ga jarumi mai dakakkiyar zuciya da karfin hali irin ka. Ai ka rage mana wahala tun da ka zabi hanyar da ta fi sauki a garemu. Mu dama amfaninmu a gidan nan horo tsaro da hukunci! Burinmu kawai a aikata laifil Ga fili ga mai doki! kai ku kwance masa duk sarkokin dake jikinsa kuma a nuna masa dakinsa na kwana amma da zarar ya karya doka daya a zartar da hukunci a kansa."
Ko da jin wannan batu sai mataimakin Gadaraz cikin alamun fargabaya ce "A'a ya shugabana Sarkiya gaya min cewa wannan yaron yana da matukar hadari don haka bai kamata a kwance masa sarkokin nan ba.
Gadaraz ya daka wa Bartus tsawa ya ce 'Ai so nake na ga iyakar hadarin nasa. Maza ku kwance masa sarkokin na ce."
Da jin haka sai wasu dakaru biyu suka zaro mukullai suka kwankwance sarkokin dake jikin hannayensa da kafafuwansa. Saboda dadewar daurin duk shatar karfe ta fito a kan hannayen da kafafun. Ko da Insam ya ga an kwance shi sai ya yi mika gami da murnushin murna domin ji ya yi kamar ya samu yanci ne daga matsayin bawa, shi kuwa Gadaraz sai ya juya da baya ya nufi kofar da ya fito dakarun dake tare da shil suka bi shi a baya. Wani Badakare daban ya dubi nsam ya ce ka biyo ni.
Ba tare da wata gardama ba kowa sai Insam ya bi Badakaren a baya suka nausa wani 6angaren daban na gidan. Duk wannan abu dake faruwa sauran fursunonin gidan suna ta kallon bakon bawa insam. Ko da aka nufi cikin gidan da shi sai ya ga gabadayan fursunonin gidan sun biyo su a baya. Hakan ne ya sa Insam ya fahimci cewar lallai akwai wani abin da ke shirin faruwa don haka sai ya yi shirin tarar ko mene ne a ransa.
Lokacin da aka iso wajen da rukunin dakunan barcin fursunonin yake sai Insam ya hango wani babban daki guda đaya wanda ya bambanta da sauran dakunan. Zaune a kofar dakin bisa wata kujera wani narkeken kato ne bakar fata, kansa ya sha askin kwallon molo, ga katon yari guda biyu a kunnuwansa. Yana da saje gami da murtukaken gashin baki. Wannan bakin mutum ya kasance mummuna kuma dogo ne sosai domin gabadaya gidan babu mai tsawonsa da kira ta sadaukai face sadauki Gadaraz.
Fursunoni ashirin ne a zagaye da kujerar ta wannan bakın mutum ke zaune suna fadanci. Kai da gani ka san shi ne shugaban fursunonin wannan gida. Duk fursunan da ya zo wucewa ta gabansa sai ya zube kasa bisa guiwoyinsa biyu ya yi gaisuwa sannan zai wuce. A cikin fursunonin dake kewaye da shi akwai masu yi masa fifita, akwai mai yi masa tausa sannan akwai masu dauke da faratan ya'yan itatuwa da abinci da ababen sha kala-kala.
Shi dai wannan bakin bawa ana kiransa da suna Barsad A iya rayuwa Barsad bisa binciken da aka yi ba a taba ganin ya yi murmushi ba sai daí dariyar mugunta. Kullum da koyaushe fuskarsa a murtuke take babu annuri. Zuciyarsa cike take da zunzurutun rashin tausayi da zalunci. Shi kansa bai san iyakar adadın mutanen da ya kashe ba a rayuwarsa.
Yanzu ne dubunsa ta cika aka kamo shi da kyar aka kawo shi wannan kurkuku sakamakon laifin haura gidan Sarkin Kisra da nufin yin sata shi da yaransa mutum arba'in aka yanke musu hukuncin daurin rai da tai.
Lokacin da Bawa Insam ya zo zai wuce ta gaban Barsad sai ya kau da kai ya yi kamar bai ganshi ba ya wuce gaba yana biye da Badakaren dake masa jagora. Kawai sai ya ga Badakaren ya ratse g fe guda ya tsaya cak ya juyo baya wasu fursunoni kimanin su ashirin suka taho da gudu suka yi wa Insam kawanya. Daya daga cikin su ya dube shi a fusace ya ce.
"Kai wannad bckon fursuna ka yi ganganci da ka ki sauraron dokokın gidan nan guda tara dazu. To ka sani wancan na zaune shi ne Sarki a gidan nan, hatta dakaru ma shakkarsa suke bare kai fursuna. Dole ne ka rinka gaishe shi sau uku kullum kana durkuso bisa guiwoyinka a gabansa, wannan yana daga cikin dokokin gidan nan guda tara.
Sa'adda Insara ya ji wannan batu sai ya kyalkyale da dariya sannan ya dubi fursunan da ya yi maganar ya ce, "Yau an sami Sarki na biyu a gidan nan, ni ma sai dai a rinka gaisheni kamar yadda ake gaishe shi."
Kafin Insam ya gama gama rufe bakinsa tuni fursunonin da suka kewaye da shi sun lullube shi da duka, Sun durkusar da shi kasa. Kawai sai aka ga ya yunkuro sama ya watsar da su duka wasunsu suka yi sama tamkar da majajjawa aka janye su suka gwaru a jikin gini suka zubo kasa. Fursunonin suka sake tasowa da sauri suka ugo kansu aka ruguntsurne da fada.
Duk fursunan da nsam ya nausa sa ga ya baje a kasa ya kasa mikewa idan kuwa kafarsa ya doka ko hannunsa sai dai a ji ya kurma ihu sakamakon karyewar kashinsa.
Kafin cikar dakika dari da ashirin ya bazar da fursunonin ashirin a kasa an rasa dayansu da ya iya mikewa tsaye.
Ko da ganin haka sai sauran fursunonin da ke wajen gabadayansu suka yunkura za su afkawa Insam amma sai Barsad ya daka musu tawa suka tsaya cak! Barsad ya mike tsaye daga kan kujerar da yake zaune ya tako da kafafunsa tamkar wani toron giwa ya zo daf da Insam ya tsaya kai ka ce zaki ne a gaban kyanwa saboda bambancin girmansu. Barsad ya sunkuyar da fuskarsa daidai kan ta Insam ya ce.
"Kai yaro ai ba a sarki biyu a birni guda. Shekarata bakwai a gidan nan ba taba samun tsageran da ya yi mini rashin kunya ba sai kai!
Tabbas kwarin zuciyarka ya burgeni sai dai ka yi a banza domin yanzu zan kared maka ruhin numfashinka."
Sa'adda Insam ya ji wannan batu sai ya yi murmushi kuma ya juyawa Barsad baya cikin jin izza gami da yarda da kai ya ce "'Ba za ka iya kashe ni ba face kwanakina sun kare ka ja mutuncinka da kimarka in ba haka ba kuwa za ka ji kunyar da ba ka taba ba.
Kafin Insam ya gama rufe bakinsa, tuni Barsad ya kawo masa Wawan mangari a wuya. Cikin zafin nama Insam ya sunkuya hannun Barsad ya doki iska.
Nan fa suka kacame da masifaffen fada, ya zamana cewa Barsad na kai wa Insam naushi da bugu hannu da kafa yana karewa da hannu da kafa. Duk sa'ad da suka hada jiki sai ka ji kamar duwatsu ne suka hadu! Nan fa mamaki ya kama gabadayan fursunonin da dakarun dake wajen Sai da Insam da Barsad suka shafe kusan dakika dari uku da arba'in suna gwamarzuwa amma dayansu bai sami nasarar nausar wani ba.
Ko da suka ga wannan naushi da bugun da suke wa juna babu nasara sai suka ja da baya suka yi cirko-cirko suna kallon juna kamar zakaru.
Kowannensu tunani da mamaki yake a cikin ransa bisa ganin yadda karfinsu ke neman zuwa daya.
Nan fa suka fara tunanin dabarar da ya kamata su vi don sam nasara. Kawai sai Barsad ya daga hannunsa guda take wani daga cikin yaransa yajefo masa takobi ya cafe.
Ko da ganin haka sai Insam ya daka tsalle sama daga inda yake tamkar daga cikin baka aka harba kibiya ya yi wata irin alkafira a sama ya fizgo wadansu kulaken guda biyu daga hannayen dakarun tsaron gidan yarin, sannan ya dira kasa bisa kafafuwansa yana mai gyara tsayuwa.
Gabadaya dakaru da fursunonin dake wajen ba su san saadda suka kama yi wa Insam tafi ba saboda ganin irin wannan gagarumar bajinta da ya yi. Dole ne Insam ye burge duk wanda ya ga yadda ya iya wulkita jikinsa a sama tamkar mazari.
Nima dai Abubakar Saleh inkiya Mijin soja dake yi maku typing sai da na tafa wa Imsam ganin irin namijin kokari da yayi kuma nake cewa mu hadu a wani lokaci dan jin cigaban wannan labari.
Domin samun Complete dinsa dama wasu littattafan zaku iya tuntubata 08138873799
GWARZON SADAUKI
Littafi Na Daya (1)
Part B
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
Cikin fushi Barsad ya dubi dakarun da fursunonin yana mai daka musu harara. Nan take kowa ya yi sauri ya sunkuyar da kansa kasa. Faruwar hakan ke da wuya sai Barsad ya rugo izuwa kan Insam yana mai kwarara uban ihu mai matukar firgitarwa. Karar taku sawun kafafunsa suka cika dodon kunne, ihun nasa kuwa ya firgita kowa dake wajen amma shi Insam ko gezau bai yi ba. Kawai sai ya kara gyara tsayuwarsa yana jiran isowarsa.
Barsad na riskar Insam sai suka ruguntsume da sabon azababben yaki mai matukar hadari da ban tsoro Barsad ya rinka kai wa Insam Sara da suka da takobi cikin tsananin zafin nama shi kuwa Insam ya rinka karewa. Duk sa'adda takobin Barsad.ta hadu da kulaken sai dai ka ji karar haduwar karafa kuma tsartsatsin wuta na tashi sakamakon cewa kulaken da karfe aka yi su.
Nan fa Barsad ya dage iya karfinsa yana kokarin tafkawa Insam mùnanan sara domin ya tsarge shi gida biyu amma sai abu ya gagara.
Haka da suka ci gaba da baki gumurzu wanda ya tashi hankalin káwo da ke wajen saboda kuskúre daýa za su yi ya janyo hallakar dayansu. Shi ma Insam yana ta kokarif ya gabžuwa Barsad külaken a fuskarsa ko a kansa ámma bai sami sa'a ba.
Koda süka shafe kusan dakika dari bakwai a cikin wannan hali sai suka saüya salon fadan suka hada da kai wa junasu naushi da bugu hannu da kafa, sai ga shi kowannensu yana amfani da damarsa da hagunsa. Nan fa suka fara hadawaljunansu jini da majina amma kuma kowannensu na iya jure naushi da bugun takar jikinsu ba na ljini da tscka ba hne Da zarat dayansu ya fadi kasa sai a ga ya yi zumbur ya mike an ci gaba da wannan gumurzu. Ana cikin haka ne makaman hannunsu suka zube suka cakume da kokawa su fadi nan su tashi can, suka rinka fadawa kan tarkace da gine-gine, Idan kan teburi suka fada ko kan kujera sai dai ka ga sun ragargaje babu abin da ya daurewa kowa kai face ganin yadda duk girman Barsad a kan Insamsai ga shi karfinsu na neman zuwa daya domin a wannan gumurzu kare jini biri jini ake yi.
Kwatsam sai aka ga kowa ya danki wuyan kowa suka shake junansu sa ga shi idanuwansu sun zazzaro har humfarfashinsu ya fara daukewa. Tsulum sai aka ga Gadaras shugaban dakarun ya bayyana a gabansu tamkar aljan. Kawai sai ya sa hannayensa biyu ya doki wuyan kowannensu akanwata jijiya. Take duk su biyun suka sulałe kasa sumammu.
Faruwar hakan ke da wuya sai Gadaraz ya dubi wadansu dakau guda hudu dake tsaye a wajen sannan ya bace bat daga wajen.
Nan take dakarun hudu sukayi wa Insam da Barsad kama-kama suka daukesu daga wajen.
Lokacin da Barsad da Insam suka farfado daga dogon suman da suka yi suka tsinci kansu a inda aka kawosu sai hankulansu suka dugunzuma, ba don koma ba sai saboda cikin wannan kuntataccen faki aka kawosu aka kulle.
Tsananin doyin da dakin ke yi ne ya sa Insam ya kama toshe hancinsa. Koda ganin haka ya sa Barsad ya bushe da dariya mugunta ya ce Yaro kai ne ba ka saba da warııan dakin ba sau bakwai ina kwana anan Yau ba kai ba barci kuma gobe da matsanancin zazzabi za ka fita daga nan."
Shi dai Insam|ko kallon Barsad bai yi ba. kawai yana kallon ginin dakin ne, yana hazarin ta inda zai fita. Da ya kalli ginin dakin da rufinse ya ga ginin dutse ne ba za fasu ba sai hankalinsa ya tashi amma da ya dubi tagar dakin kararna daga sama ya ga an zuba mata wadansıu sandunan rodina guda tara sai ya yi murmushil Sai dai kuma babu yadda zai iya kai wa inda tagar take dole sai da taimakon Barsad.
Insam ya mike tsaye ya kama kai kawo yana takun da bai wuce uku ba saboda kankantar dakın. Daga can sai ya koma ya zauna ya fuskanci Barsad ya ce da shi, "Idan za ka ba ni hadin kai ba za mu kwana a han dakin ba."
Sa'ad da Barsad ya wannan batu sai ya kyalkyale da dariyar mugunta ya ce, Amma kdai ka taba samun tabin hankali ko? Ta ya ya za nu iya fita daga cikin wannan dakin ina mai tabbatar naka da cewa ko giwaye biyu jaka kulle a cikin dakin nan ba Su isa su balle kofa ko tagarsa ba bare mu, Insum ya gyada kai ya ce "Ni dai kawia ka yi abin da na ce ka yi, za ka sha mamaki."
Har Barsad ya yi nufin ya ki sai wata zuciyar ta ce da shi "To ka kure karyarsa mana ka gani ko tsafi yake yi bai isa ya iya yin komai ba tur da babu mai iya tagaza tsafi a gidan nan muddin Gadaraz na nan.
Gama ayyana hakan ke da wuya sai Barsad va dub: insam ya ce "Me kake so na yi maka?"
Insam ya ce, "'So nake na hau kan wuyanka ka daga ni sama hannuna ya kai kan waccan tagar, indai hannayena suka kai kanta zan iya zare rodukan jikinta mu fice."
Ko da jin wannan batu sai Barsad va ce "Idan har ka iya zare wadancan rodukan guda tara. daga yau zan sauka daga kan matsayin na shugaban fursunonin gidan nan na baka. "
Insam ya yi murmushi ya ce. 'Ai kuwa kujerarka ta zama tawa."
Gama fadin hakan ke da wuya sai Barsad ya tsuguna bisa guiwoyinsa shi kuma Insam sai ye hau kan kafadunsa ya zauna. Barsad ya mike tsaye da shi tamkar wani karamin yaro ya dauka.
Insam ya sa hannayensa ya kama rodin guda biyu wadanda kowane guda aya kaurin sa ya kai na tsintsiyar hannun Insam Kawai sai Insam ya fara fara kokarin jijigo rodunan biyu, nan take kwanjinsa ya kumbura, jijiyoyin jikinsa suka kumbura, fuskarsa ta rinka tabewa yana ciza leba.
Ba zato ba tsammani sai Barsad ya ga gini ya fara tsagewa a hankali sai ga shi rodunan gusa biyu sun fara zarowa daga cikin ginin dutsen.
Karar tsagewar ginin ne ya kai ga kunnen wasu dakaru dake can nesa kadan su biyu sai suka durfafo inda kofar dakin take domin su ga abin da ya yimotsi.
Ihun wani fursuna a can baya ne ya dake hankalinsu suka nufi can din, inda suka jiyo ihun.
Damar da lnsam ya samu enan ya zare rodunan guda biyu kawai sai ya sake kama wadansu rodunan biyu ya ci gaba da zarosu. Nan da nan ya hada zufa sosai Cikin dakiku kadan ya gama zaresu su ma kawai sai ya yunkura zai zura kansa cikin tagar ya fice daga dakin amma sai Barsad ya yi caraf ya riko kafafunsa ya ce da shi.
"Kai ka khau kan wuyana ka sami damar fita ni kuma kan wuyan wa zan hau?"
Insam ya ce Ai dole na na miko maka hannuna ka kama na janyoka ka fita ko don saboda ka cika alkawarin da ka daukat mini na ba nil shugabanci."
Barsad ya ce "Haka ne kuma ni ba ha karya alkawari amma ka sani cewa dokar da muka karya yanzu hukuncin kisa ne a kanmu ya za
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

4 Comments On GWARZON SADAUKI Book 1
avatar
maimunatu-7

3 months ago

Reply

Inasan litafin nan pls

avatar
maimunatu-7

3 months ago

Reply

Inasan litafin nan pls

avatar
daiy

3 months ago

Reply

Replying to maimunatu-7

Ki downloading ki karanta ko ki karanta shi anan shafinmu amma ki sani kafin ki iya downloading dole sai kinyi subscribtion na shafinmu wanda mafi karanci shinw 1k Naira

avatar
atiku

29 days ago

Reply

Zansamu complete littafan nan a pfd kuwa

Please Login or Register in order to submit comment