Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gane kurenka ta masa kafin tace "ai dukanmu ne masu sa'a a rayuwa."

"Amma ba kamar ni ba." ya fad'a yana rumgumata jikinshi.

"Haka dai kace." ta fad'a itama tana qara shigewa jikinshi.

"Kema masallaci zaki je?" ya tambaya yana kallonta.

"Meka gani to?"

"Naga kema kinyi kwalliya sosai ga kuma doguwar riga, dan sau d'aya na tab'a ganinki da doguwar riga irin haka, shima a lokacin bikinki."

Duka ta kai masa a qirji tana fad'in "kaji mutum wai bikina, kace bikinmu, shagali da wani ango, kuma d'aurin aure da wani ango."

Dariya yayi yace "dama fa ara mishi ke nayi na wannan lokacin kawai, amma ba kiji yanda zuciyata ke tafasa ba."

Da kallo ta bishi tana fad'in "ashe dama ka jima kana sona, amma shine a lokacin dana mareka ka kasa hakura saida ka rama, ba kaji yanda naji zafi ba a ranar, har saida hannunka ya kwanta a kumatuna."


Dariya yayi ya fara cire kayansa yana fad'in "to ai ko yanzu idan kika min laifi ba zan tsaya wasa ba wajen zabgeki da mari, kawai dai nasan yanzu idan na mareki a kumatu , to ni kuma zanji zafin a zuciyata ne."

Mak'ale masa tayi a baya tana kukan shagwab'a tace "hamago kawai, wallahi saina rama marin soyayyata daka min."

Juyowa yayi da ita gabanshi yana kallonta yace "in dai zaisa kiji dad'i to na amince ki rama."

Yana fad'a ya bata kumatun da nufin ta rama, Khairat kam saida ta share 'yar qwallan data taho mata dan sosai taji zafin marin daya mata a ranar, hannu ta d'aga iya k'arfinta dan dama ce ta samu da ba zata bari ta wuceta ba.


Kamar saukar aradu Umar Faruk yaji saukar wani gundumemen bahagon makahon.....πŸ˜‚

_Wallahi kinmin daidai tawajena, hi yasa nake sonki._

*Wasu na mamakin Umar Faruk ya kwana a d'akin Khairat, to ai ban gama sati d'aya na d'akin Khairat ba, dan haka ku tayani lissafi, yau juma'a a labarin Khairat da Umar Faruk, kenan gobe asabar ne zata cika sati, lahadi kuma sai kuzo mu rakashi d'akin amarya Zubysss.πŸ˜‚*

_Koda yake naga mutuniyar ma bata da masoya._
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bansan me zan iya cewa masoyana ba, hak'ik'a kuna sakani farin ciki, comment d'inku na nishad'antar dani, tsakanina daku sai dai ince Rabbi ya bar qauna._ πŸ’žπŸ’•πŸ’—


_Bismmilahir-rahman-rahim_


3⃣4⃣


Kamar saukar aradu Umar Faruk yaji saukar wani gundumemen bahagon makahon kiss a kumatunshi, ji kake

"Muahhhhhhhhh."

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Sakin fuskarshi tayi data rik'e tace "idan kaga hannun Khairat ya tab'a fuskarka yanzu, toka sani shafata ne za tayi."

D'aukarta yayi ya dinga juyi da ita a tsakaiyar d'akin yana dariya yana fad'in "har kinsa zuciyar maza ta tsinke, na d'auka fa marina za kiyi, ashe dai sanin da nayiwa Khairat."

Itama dariyar take kafin tace "kaga saukeni kaje ka shirya lokaci na tafiya."

Sauketa yayi ya qarasa cire kayan jikinshi kafin ya shiga wanka, koda ya fito ta fito mishi da kayan da zai saka, da taimakonta ya shirya tsaf cikin farar shadda da hula da takalmi, kallon kanshi yayi a madubi yana qara daidaita hularshi, saurin d'auke hular tayi a kanshi ta d'ora a kanta tace "kenan ban iya sakawa ba? shine har kake gyarawa."

K'ugunta ya janyo ya had'a da nashi yasa hannayenshi ya fara daidaita mata zaman hular a kanta, murmushi ya sakar mata yace "dubi madubi kiga yanda kika gama had'uwa, shi yasa nace miki ni mai sa'a ne."

A tare suka kalli madubin yana bayanta ita tana gaba, wani irin bala'in kyau ne sukayi ga matuk'ar dacewa da junansu, wayarshi ya ciro a aljihu ya d'auketa photo ita kad'ai sannan ya musu tare, cire hular yayi ya mayar a kanshi yana fad'in "kinsan me zai faru?"

"Saika fad'a." ta fad'a tana d'anewa a bayanshi.

Goyeta yayi yana fad'in "kawai kizo muje tare, saina biya na ajeki gida wajen Mamie, idan na dawo saina biyo na d'aukoki."

Da k'arfi ta wuntsilo ta sauko daga bayanshi tana fad'in "da gaske baby, Allah kuwa ina son zuwa, ina kewar Mammie."

Kumatunta ya kama yace "sosai ma, tukwicin wannan kwalliyar ne na bayar."

Wajen aje jakunkunanta ta nufa ta d'auko qarama ta hannu baka mai walk'iya ta saka wayarta, Umar Faruk na kallo ta bud'a wata jakar ta kwaso kud'i ko k'idayawa ba tayi ba ta zuba a jakar, kallonshi tayi tace "na shirya, zamu iya tafiya?"


Da ido kawai ya mata alama sannan yace "d'auko min sallaya."

D'aukowa tayi ta rik'e a hannunta, shi kuma ya kama hannunta suka fita, saida ya saki hannunta ya rufe k'ofarsu hakan kuma yayi daidai da fitowar Abbakar shima ya shirya zai tafi, Zuby da Saratu kam kallon ikon Allah suke, wato masallacin ma tare zasu tafi kome? anya Umar Faruk bai haukace baπŸ˜‰ ku shinshina kuji, cikin taushin murya Khairat tace,

"Baby, tunda ga yah Abbakar ai saiku tafi tare ko."

Kallonta yayi ya juya ya kalli Abbakar dan baiga fitowarshi ba, cike da k'aunar juna Umar Faruk yace "abokina ka jirani saimu tafi ko?"

Abbakar dake nad'e sallayar hannunshi ne yace "amma ai naga kamar tare zaku fita? taya zan shiga wannan harka ta amare."

Wani wawan tsaki da Zuby taja tare da tashi tabi ta gaban Khairat ta wuce d'akinta, Umar Faruk kam ko kulata baiyi ba yace "kaga muje, dama akwai maganar da nake so muyi da kai."

Saratu dake zaune acan tace "Allah yasa dai ba cewa za kayi ya qara aure ba."

Kafin suyi magana Mama Sa'a tace "ke kuma shine matsalarki, kenan mu nan mutuwa mukayi da muke zaune da kishiyoyin?"

Umar Faruk ne yace "rabu da ita Mama, aure ai ya zama dole yah Abbakar ya qara, tunda ita yanzu ta tsufa."

"Kai tsufan lafiya, waya fad'a maka?" cewar Saratu.

Saida ya kama hannun Abbakar suka nufi hanyar fita yace "da bakinki kika fad'a, ko awa d'aya ba ayi ba."

Khairat ma bayansu tabi ko murmushi ba tayi ba bare dariya, Mama Sa'a kuma harda daga murya tana fad'in "saikin dawo 'yar albarka."

"Mtsssss, tusa kai ba kwarjini." cewar Mama Maimuna dake zaune akan tabarma.

A hassale Mama Sa'a tace "dawa kike Maimuna? ni kike fad'awa haka? ni tsararki ce da zaki shiga harkata?"

"Eh, dake nake kiyi abinda za kiyi, aikin banza kawai, duk kibi kina wani nanik'ewa yarinya ita kuma tana wulak'antaki, kawai saboda tsinannan kwad'ayi."

Aifa tsaye aka mik'e suka fara surfa bala'i Mama Umar Faruk dasu Saratu Ruk'ayya hak'uri kawai suke basu, dan duka mazan sun tafi masallaci Zuby kuma naji tayi banza dasu, saida suka kusan dakuwa sannan suka hak'ura kowace ta shiga d'akinta, amma duk da haka kowace na jefo magana daga d'akin nata.


**************


A mota kam Abbakar da Umar Faruk hira suke sosai data shafesu, Khairat na baya tana jinsu amma tana latsa wayarta har suka isa, tare suka fita da Umar Faruk suka tsaya a k'ofar gidan, saida ya d'an saci kallon Abbakar dake mota kafin ya shafi fukarta yace "ki gaishe dasu Mamie, idan muka taso zan biyo."

Cikin shagwab'a tace "amma fa nidai daka barni har zuwa dare, kaga idan ka dawo daga wajen aiki sai kazo muje."

"Nak'i d'in, ina buk'atar ganinki a kusa dani."

"An gama ranka shi dad'e , yanda kake so haka za ayi."

Tana fad'a ta matsa kusa dashi ta sumbaci bakinshi tana kallonshi ta kece da dariya, "meye?" cewar Umar Faruk.

"Ba komai, saika dawo." duk tayi maganar ne a cikin dariya tare da tura k'ofar gidan ta shiga.

Mai gadi dake alwala cikin shirinshi na masallaci ya taso da nufin gaisheta ta daga masa hannu tare da tsayawa tace "kaci gaba da alwalanka, ba'a so ana tsayawa idan ana alwala, komai mahimmanci abu kar yasa ka dakatar da alwalarka, musamman ma idan abun ya shafi harkar duniya ne."

Tana fad'a ta shige ciki shi kuma ya biya da kallo tare da tunanin yaushe Hajia Khairat ta zama Ustaza haka, yauma farin ciki sosai Mamie da Mammie sukayi, musamman data fad'a musu shiya kawota kuma yace zai biyo idan ya taso, hak'ik'a sunga shiriya sosai a tare da yarsu, kuma sunyi farin ciki marar misaltuwa."

*************


Yana shiga mota ya tayar suka wuce, Abbakar kam kallonshi yake yana dariya, ganin dariyar tayi yawa yasa kalleshi yace "wai miye haka dan Allah? ya zaka sani a gaba kana dariya."

Yanda yayi maganar yasa ya fahimci rai zai iya b'acewa dan haka yace "kalli madubi ka gani."

Gyara madubin yayi ya kalli kanshi a ciki, ganin bakinshi yayi ja kamar yasa jan baki yasa ya fahimci me yake wa dariya, a lokacin kuma ya fahimci dariyar da Khairat take masa, lotus ya d'auka a motar ya goge bakinshi yana hararan Abbakar yana cin magani, girgiza Abbakar yayi yace "Umar Faruk kenan, kamar ba kai ba wallahi duk ka canza."

"Kaga nifa akwai maganar da nake so muyi da kai."

"Ina jinka." ya fad'a yana gyara zama.

"Dama wata tafiya ce ta taso mai mahimmanci, kuma Khairat tace mahaifinta yace dole sai dai mu tafi tare, in kuma banje ba ba zasuji dad'i ba, ni kuma harna ce mata na amince, saboda akwai wani laifi da nayi mata tace zata fad'awa Baba, saboda haka yasa nace na amince, amma ni gaskiya har yanzu bana jin zan iya tafiya tare da ita haka kawai a dinga nuna ni a gari."

Saida ya gama nazartarshi kafin yace "to ita dai rayuwar duniya da kake gani inka biya ta abinda mutane zasu fad'a to babu inda zaka je, sannan a matsayinka na mijinta kuma kace zaka, amma daga baya kace a'a hakan zai iya tab'a darajarka da mutuncinka a wajenta, iyayenta kuma tunda suka ce suna buk'atarka a wajen, tofa akwai buk'atar son ganinka ne a wajen, dan haka ni ina ganin kawai ka bita ku tafi tunda dai ba siyar da kai za tayi ba, matsala d'aya ce kawai nake tunanin za'a samu."

"Matsalar me kenan?"

"Zubeida mana, da ace kafin ta tare ne, amma a yanzu data tare kuma na lura kan yarinyar yana rawa, bai zama lallai ta amince ka tafi ba."

"Nima yaya nayi wannan tunanin tun kafin kayi, amma da yake tamin alk'awarin idan har mun kwana biyu to ba zamu wuce uku ba, a lissafina ranar talata ne tafiyar ta kama, daga gobe kuma kwanan Khairat zai qare, kaga kenan a ranar da zan koma d'akinta ne za ayi tafiyar, kenan ko an shiga kwanan Zuby to kwana d'aya ne."

"Eh to da sauk'i idan hakane, dan haka ka fara shiri kawai ni zanji dasu Baba, sai kuma ka nemi izinin matarka."

"Izini kuma? haba dai, kamar itace mijin."

"A wannan qadamin kam kusan itace, dan ka sani in bata amince ba ba zaka tafi ba, idan kuma ka tafi bada amincewarta ba, tofa ka sani ranar gobe Allah zai tsayar da kai a gabanshi."

"To naji, Sheik Abbakar."

"Sheik Umar Faruk dai, kuma kayi k'ok'ari kafin ku dawo kuzo mana da babban tsaraba."

Dariyar da yake yasa yace "wane irin k'ok'ari kuma, wace irin tsaraba?"

Cikin rad'a yace mishi "baby "

Bushewa sukayi da dariya harda tapa hannu kafin Umar Faruk yace "baka da dama wallahi, taro ne fa zai kaimu ba lune da miel (honeymoon) ba."

Da haka suka isa masallaci kamar wasu abokanai suna hirarsu cikin raha, saida aka gama hud'uba kafin akayi sallah daga nan kuma suka dawo tare suka komo gidansu Khairat dan d'aukarta kamar yanda yace.

*****************


Suna zuwa tare suka shiga da Abbakar har ciki, a lokacin masu aiki na k'awata wajen cin abinci da kalolin girke girke, Khairat da fitowarta kenan daga d'akinta ta gama sallah ta dako da gudu ta rumgume Umar Faruk, "sannu baby , har kun taso?"

Kasa aiwatar da komai yayi saboda fitowar Mamie itama daga d'aki wanda Mammie dama tana zaune a falon, abinka ga yan barikiπŸ˜‚ ba wanda yaji wani abu, sai Umar Faruk daya ji kunya ta rufeshi, suna shirin zubewa qasa dan kwasar gaisuwa Mamie ta qaraso da sauri ta dafa kafad'un Umar Faruk duka biyun tana fuskantarshi tace "a'a a'a, haba d'ana, ai ka wuce wannan a gidan nan, kaima fa d'an gidan nan ne."

Hannunshi ta rik'e tayi hanyar wajen cin abincin dashi tana fad'in "muje ga abinci an gama kuci."

Umar Faruk dai kanshi na qasa ya kasa kallonta sai Abbakar dake kallon falon irin tsari da dukiyar da aka zuba, da kanta taja mishi kujera ya zauna ita kuma mai aiki taja mata ta zauna, Khairat ma da Mammie duka sun zauna, Biba da Saude ne suka bud'a kwanukan suka fara zuba musu abincin, suna gamawa suka koma mafakarsu su kuma suka fara cin abincin.

Ba ruwan Khairat haka kawai take jin son Umar Faruk na gaskiyar na shirgarta, da kanta take d'ibar abincin tana saka mishi a baki saboda taga baya ci, haka yasa ya fara diba kad'an kad'an yana ci, Khairat d'in da Mammie kuma hira suke sosai irin na kaka da jika , Abbakar dai kallon ikon Allah yake yana qara ganin girman Khairat, dan inba mai hak'uri ba babu ta yanda za ace kana rayuwa cikin wannan daular kamar a masarauta, abinci ma na rana kana cin kusan kala uku zuwa hud'u amma ka yarda ka fara rayuwa a gida kamar nasu, haka ma a wajen Umar Faruk abinda yake rayawa kenan a zuciyarshi tare da sake jaddada irin taushin zuciyar Khairat, lallai baka sanin asalin mutum saika zauna dashi sannan zaka fahimceshi.

Suna kammalawa kafin su tashi Mamie ta kalli Khairat tace "ki tashi kije ki shirya kizo ku tafi."

A shagwab'e ta kalli Mamie tace "to Mamie."

Umar Faruk ne yace "a'a Mama, ku barta kawai ta zauna, naga kunyi kewarta sosai, idan na taso daga aiki zan biyo saina d'auketa."

Cike da farin ciki ta kalleshi tace "da gaske baby? gaskiya naji dad'i."

Mak'ale wuyanshi tayi tare da janyoshi kusanta ta sumbaci kumatunshi tare da fad'in "na gode baby."

Mammie dake kusan Khairat ce ta zura hannu ta kama kumatunshi tace "yaron kirki, gaskiya ka kyauta, dan dama muna so muyi shirye shiryen tafiyarmu a gabanta."

Ture hannunta Khairat tayi tana fad'in "kuma shine saikin tab'a min miji , nifa bana son haka."

"Allah sarki, yo mijinki ko mijina? kaji min yarinya kai, kawai dan na ara mikishi saiki wani zak'e dayawa."

Kallon Umar Faruk tayi ta kalli Mammie tace "zak'ewa ma nake? to ai mijin naki ne ke rawar qafa a kaina."

"Kaji wani d'aurin duniya kuma, to nidai ban gani ba, kuma nasan yafi sona."

"To ai gashi nan ki tambayeshi kiji." Khairat ta fad'a tana nunashi da hannu

"Ba buk'ata, danni zai zab'a, bana so kiji kunya a gaban mutane."


Cikin taushin murya cike da jin kunya Umar Faruk yace " gaskiya ne, za tasha a wajenki."

Mammie kam bushewa tayi da dariya had'e da yiwa Khairat gwalo, turo baki tayi tana kallon Umar Faruk, shi kam kasa kallonta yayi saboda wutar tartsatsin da yake ji a kanta, haka suka mik'e gaba d'ayansu zasu tafi, bayan sunyi sallama Mammie tace "nasan dai sai mun had'u a lokacin tafiyarmu ko?

"Insha Allah." ya fad'a kawai.

"To Allah ya nuna mana."

"Ameen." suka amsa.

A hankali Khairat ta taka musu har zuwa k'ofar d'aki sannan suka tsaya, sumbatar bakinshi tayi tare da kumatunshi kafin ta kalleshi tace "Allah ya tsare, saika zo."

Su Mamie dake hangensu yasa ya d'an shafi fuskarta kawai yayi gaba, suna fita suka d'auki hanya saida ya aje Abbakar gida ko shiga baiyi ba ya juya ma'aikata dan lokaci yayi sosai, sai dai zuciyarshi ta qara narkewa da tsananin son Khairat, haka ya koma duk baijin dad'in aikin saboda manyan kayan dake jikinshi, ga kuma motsi da k'amshin Khairat daya isheshi duk sanda ya motsa, ji yake kamar tana jikinshi ko kuma tana sumbatartashi, a haka dai ya gama aikin a daddafe har aka tashi.


Bai wuce gida ba har saida ya tsaya ya siyawa Zuby kayan data buk'ata kafin ya wuce gida, yana isa ana kiran sallah magrib hakan yasa yana shiga d'akinta ya aje mata kayan ya fito yayi alwala cikin gaggawa ya tafi masallaci, bai dawo gidan ba har saida akayi sallah isha'i saboda lokacin qurarre ne kuma suna tare da Ishaq suna hira, suna gamawa ya shigo gidan saida ya fara shiga wajen Baba suka gaisa kafin ya shiga d'akin Mama da sauran iyayen, yana fitowa ya wuce d'akin Zuby.

Ya samu tana nad'e sallayar da tayi sallah, abinda ya qona masa rai da haushi shine, d'akin dai tsaf dashi sai kamshin turaren wuta amma kayan jikinta, tun atamfar safe ce daya fita ya barta da ita ya kuma dawo ya sameta da ita, kuma yanzu ma ita dai ce, ya d'auka kafin ya dawo daga masallaci zai samu ta canza, amma ina alamu dai na ba tayi wanka ba tun na safe, zaune yayi a kukerar robar dake fuskantar gadon ya kalleta fuska ba yabo ba fallasa yace, cike da ladabi tace "sannu da zuwa."

"Yawwa, sannu? ya gida?"

"An gode Allah."

Aje sallayar tayi ta tsaya tana kallonshi, a d'an dak'ile yace "zauna mana."

Zaune tayi bakin gadon tana kallonshi shima wuyanta yake kallo dake tsattsafo da zufa , a shak'e yace "kin duba kayan?"

"Eh yah, na duba."

"To miye babu a ciki?"

Cikin sanyin murya tace "eh to, kusan abinda babu kad'an ne gaskiya."

Da d'an k'arfi yace "to yanzu kamar nawa zai isheki ki siyo abinda babun?"

Nanma a ladabce tace "eh to, ko nawa ka bayar ma zai isa."

D'aga gira yayi sama ya d'an zame daga kan kujerar yasa hannu aljihu ya fito da kud'i, jikka biyar biyar guda biyu ya bata yace "gashi, sai kiyi manage dashi dan kinsan nauyi dayawa ne a kaina."

"An gode Allah ya saka da alkairi." ta fad'a a sanyaye.

Sauran canjin ya mayar aljihu kafin ya sake gyara zama ya kalleta sosai yace "ina son yin wata muhimmiyar magana dake, ina fatan zaki bani hankalinki kuma ki fahimceni?"

"Ina ji yah Umar."

"Zubeida, akwai wani babban taro da aka shirya a Germany, taro ne na manyan mutane wanda zai had'a da iyalensu, mahaifin Khairat na d'aya daga ciki, kuma ya gayyaceni a matsayina na surukinsa, tafiyar zata iya d'aukanmu kwana biyu zuwa uku, shi yasa nake neman alfarmarki kwanan d'ayan, domin zai iya yiwuwa na shiga cikin kwananki domin kinsan tafiyar hali, kosu Mama basu sani ba domin ina so na kammala daku iyalina, ina fatan zaki min wannan alfarmar ki bani kwananki d'aya tak."

Cikin mamakin kalamansa tace "tafiya kuma, har qasar waje, amma kuma kai yaya ka amince ka tafi? ba ka tsoron ko wani abu aka shirya maka."

"Me kuma za'a shirya min? tare fa da Khairat zamu tafi."

"Darammm." taji gabanta ya fad'i, cike da kasa b'oye abinda ke ranta ta mik'e tsaye tace "uhum, yanzu naji magana, kace dai tare da karuwarka zaku tafi, wato harta bud'e maka idon da har kake tunanin fara biyarta a duk inda tayi ko? yah Umar wai yaushe ka zama haka ne? gaba d'aya ka canza kamar ba kai ba, to wallahi in dai izinina ne ake nema ban yarda ba."

Wata wawura daya ma hannunta har yayi qara cikin d'aga murya yace "Zubeida , akan miye ina magana dake har zaki mik'e tsaye kina min ihu, rainani ne ki kayi kome, me yasa zaki d'aga muryarki akan tawa? wai tambaya ma kike yaushe na canza? to a ranar da kika canza na canza nima, akan miye zan zaunar dake ina miki magana cikin nutsuwa ke kuma zaki d'aga min hankali, waye ya koyar dake wannan d'abi'ar? nace waye yace kizo nan ki dinga min abinda ranki yake so, waye." ya qarashe da d'aga murya tare da hankad'ata saman gado.

D'orawa yayi da "kina tunanin izininki nake nema? to baki fahimta daidai ba, ni alfarma na nema kimin ta kwana d'aya wanda shima qila waqala na yishi a can, da har zaki wani ce wai baki yarda ba, to karki yarda mana saime? naga idan zamanki nake a gidan."

"Ba dai alfarmar dana nema bace har tasa kika min haka, to bari ki gani yanzu zanyi maganin abin."

Wayarshi ya ciro daga aljihu ya danna kira, daga d'aya b'angaren ana d'auka cike da karsashi da kashe murya tace "hello baby."

Saida ya lumshe ido saboda yanda yaji har tsikar jikinshi ta tashi, saita nutsuwarsa yayi tare da sauke ajiyar zuciya kafin yace "hello, ya kike?"

Cikin shagwab'a da wata shegiyar kissa tace "ba dad'i, ka tafi ka barni inata jiranka, duk da ina kewar gida amma har kasa naji gidan ya gundureni saboda kayi nesa dani, a gaskiya Faruk sai yanzu nake qara tabbatarwa cewa soyayya *had'in Allah ce*, yanzu fad'a min yaushe zaka taho?"

Baisan sanda wani basaraken murmushi ya sub'uce masa ba, a hankali ya furta "zanzo, yanzu fad'a min tafiyar nan da zamuyi, kina ganin zamu iya dawowa a kwana biyu?"

"Eh baby , dan a ranar da za muje ma a ranar za'a gabatar da taron, kawai dai akwai gajiyar tafiya da kuma ganin gari da zai iya kaimu kwana ukun."

Yanda muryarta ke fita yasa yasa hannunshi yana shafar saitin zuciyarsa da yake jin bugunta yana canzawa , cikin basarwa yace "to a kwana biyu nake so mu dawo, ki shirya zanzo d'aukarki yanzu."

Cike da zumud'i da qwarin murya danta daki dodon kunnensa tace "an gama ranka shi dad'e."

Kashe wayar yayi ya maida kallonsa ga Zuby dake zaune tana sauraranshi, kallon sama da qasa ya mata yace "wai duk wanda ya samu dama ba zai tsaya wasa ba sai k'ok'arin ya dama damarsa, to in dan kwana d'aya ne ki rik'e na yafe miki bana buk'ata, zan tafi a ranar da kwanan Khairat zai zagayo, naga kuma mai hanani abinda naga dama."

Wucewa yayi ya barta a zaune yana fad'in "aikin banza kawai, yara da zaran sun ganka ba kaya a jikinka saisu nemi su rainaka."

Yana fita d'akin Khairat ya nufa ya bud'e da makullan wajensa ya shiga, kayansa ya cire ya shiga wanka, bai jima ba ya fito ya shirya cikin qananun kaya yayi wanka da turare kafin ya d'auki makullin mashin d'inshi dan dashi yake so ya d'auko gimbiyar.

_Yaufa my Khairat utu utu zata hau._😁


*****************


Duk da yaso ta fito amma saida tasa ya sake shiga ciki ya gaishe dasu Mamie kafin ta fito, cak ta tsaya saboda ganin Dream a maimakon Renge roverπŸ˜‚, matsowa tayi kusanshi tace "baby, ina motar take?"

Gemunshi ya tattaro ya had'e guri d'aya yana murmushi, a tunaninta so yake ya gwada soyayyar da take fad'in tana masa shi yasa ya taho da mashin d'in, ba zata bari shirinta ya watse ba dan haka ta saki murmushi ta rumgumeshi tarΓ© da sumbatar kumatunshi kafin tace,

"Karo na farko a rayuwata zan hau mashin, a gaskiya soyayya za tayi dad'i akan mashin."

Cikin dariya ya fara qoqarin hawa yana fad'in "saima kin hau zaki tabbatar."

Rik'e rigarsa tayi tace "ka taimaka min na hau kafin ka hau."

Hannun damansa ya mika mata ta rik'e sannan ta tattare rigarta kafin ta hau, yana hawa ya tayar suka d'auki hanya, tintserewa tayi da dariya ta fara masa cakulkuli tana fad'in,

"Ashe haka mashin yake? gaskiya daga yau ba zan sake hawa mota ba, nima mashin zan siya sabo."

"Ke ke, dan Allah ki bari, za kisa mu fad'i fa, ki bari mana, hhhhhhh." ya qarashe da dariya.

Saida suka hau titi kad'ai ta rabu dashi amma fa tana makale a bayanshi tayi luf kamar mai bacci, surutu kawai take zuba masa shi dai nishadi da farin ciki ma ya hanashi magana, da sauri ta nuna masa wata babban restaurant da zasu wuce ta gabanta tace ai saiya tsaya sunci abinci.

"Dan Allah me zamu tsaya muyi anan? idan yunwa kike ji muke gida sai kisa Ruk'ayya ta dafa miki duk abinda kike so." cewar Umar Faruk.

Cikin raha tace "a'a ni bana jin yunwa , kawai zamu je ne a matsayin masoya kuma muci abinci."

"Um um , nifa bana son shiga irin guraren nan." ya fad'a cikin shagwab'a.

"Ai tare zamu shiga, in dai kana sona kawai muje."

Saida ya rank'wafo bayanta ya kwantota yace "an gama ranki shi dad'e."

Tsayawa yayi kamar yanda take so suka shiga babban restaurant d'in, d'aya daga cikin ma'aikatan ne suka tarbesu da kyakyawar mu'amula har suka samar musu da wajen zama, ana aka basu takardar da zasu duba abinda

Please Login or Register in order to submit comment