Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsakaninmu kuma zan iya aurenki, bare kuma kina matsayin matata, dan haka dan Allah kar kisa damuwar da har zata haifar miki da wata matsalar, ba zanso hakan ba kuma zan iya yin hushi dake idan kika ja mana matsala."

Murmushi ta sake yi tace "shikenan yah Umar, na daina insha Allah ba zan sake ba."

"Yawwa yarinyar kirki, tashi muje to Baba nasan ganinmu."

Hijabi tasa suka fito, a qofar d'akin yace "kije zan kira 'yar uwarki."

Da kai ta masa alamar to ta wuce d'akin Baba, da sallama ya shiga d'akin Khairat dake kwance akan qafar Mammie da basu jima da zuwa ba tare da Mamie, kallonta yake harya zauna yana kallon bandejin dake kanta, gaishe dasu Mammie yayi ya d'ora da "ya mai jikin?"

"Ah jiki da sauk'i." cewar Mamie.

"Allah ya qara sauk'i, ya kiyaye gaba."

Da "ameen." suka amsa.

Kallonta yayi yace "Khairat, Baba kesan ganinmu a d'akinshi yanzu, zaki iya tafiya?"

Ta d'an dafe kai ta tashi zaune tana kallonshi, saida ta daidaita zamanta tace "zan iya mana, muje kawai."

Tsaye ya mik'e tare da mik'o mata hijabinta tasa, hannunta ya kama suka fara takawa a hankali, suna daf da fita daga d'akin ta kalleshi tace " kuyi hak'uri Faruk dan Allah karku d'ora min laifi, nima ba'a son raina bane."

Murmushi ya mata yace "karki damu, muje."

Yana rik'e da ita har sukayi sallama d'akin suka shiga, kusa dashi ya zaunar da ita kafin suka maida hankalinsu ga Baba, kallonshi Baba yayi yace "amma ba naga mahaifiyarta sunzo ba?"

"Eh Baba suna ciki."

"To ka musu magana mana." cewar malam.

Tashi yayi ya koma d'akin ya kirasu suma dan ayi gabansu, zaune sukayi suma ana kallon kallo, Baba ne yace "to alhamdulillah kowa ya hallara, kuma ba komai yasa na taramu ba sai dan kawo qarshen matsalar data kunno mana kai, da farko ina so nasan musabbabin matsalar danta hakane zamu yaki matsalar dan gudun sake faruwar haka anan gaba."

Khairat ya kalla yace "Khairat, kinyi wata magana a lokacin da Zuby ta some wacce nake tunanin kinsan komai, shin zaki iya fad'a mana meya faru?"

Kallon Zuby tayi ta kalli Mama ta kuma kalli Umar Faruk kafin ta kalli malam ta fara magana cikin taushin murya da rawar murya tace "sanin kanku ne inhar cacar baki zai had'ani da Zubeida, to sai tasa iyayena musamman mahaifina, jiya ma hakane ya faru lokacin da Papa ya aiko mana da kud'i nida ita, bayan bata karba ba saida ta fad'a min baqar magana da banji dad'inta ba, kuma Ruk'ayya da aunty Saratu shaida ne dan suna wajen, shi yasa ni kuma naci alwashin kawo qarshen matsalar ta hanyar bayyana mata mahaifinta na gaskiya, dama kuma nasan Bala tunda jimawa, kuma shine ya fad'a min ita 'yarsa ce da suka haifa bata hanyar aure ba, shi yasa nace yazo ya karb'eta koba komai zata san mahaifinta na gaskiya."

Ajiyar zuciya malam ya sauke yace "to Zubeida kinji dalilin da yasa tayi haka, kuma inhar za abi ta gaskiya to kece kika tunzurata har tayi haka, a zahirin gaskiya ba zamu ce tayi kuskure ba, koba kamai ta taimakeki wajen sanin mahaifinki na gaskiya wanda mahaifiyarki ke b'oye miki, laifinta kawai data tona abinda bai kamata ace ta tona ba, da tayi hak'uri wataqila lokaci ne zai bayyana hakan, dan haka ina rokonku da ku gafarci junanku ku kuma yafewa juna, rashin had'a kanku da ku kaki yine ya janyo hakan, yana da kyau kusan shifa aure ibada ne, kuma qarin aure ma Allah ne ya hallata mana shi, fad'a da kuke da junanku sam bai dace ba, idan kuka had'a kanku kuka zauna lafiya, shi kanshi mijinku zaifi samun nutsuwa da kwanciyar hankali, haka kuma Allah zai qara yalwata mishi arziqinshi, dan haka ina sake baku hak'uri tare da shawartarku daku yafewa junanku dan Allah dan soyayyarku da Allah."

Kallon da yake musu yasa Khairat sauke ajiyar zuciya ta kalli Zuby tace "kiyi hak'uri Zubeida, ki yafe min? nima kuma na yafe miki abisa komai."

A cije Zuby tace "na yafe miki, nima ki yafe min."

"Ba komai 'yar uwa." cewar Khairat.

"To masha Allah, sai kuma ke Zubeida, ina so kisan abinda ya faru qaddara ce kuma jarabawa, kiyi iya qoqarinki wajen cinye wannan jarabawar, hakan zai qara hauda imaninki a wani mizani da zai qara miki qarfin imani, kuma karki saki ki kalli mahaifiyarki da wani ido dama idon rahama ba, haka shima mahaifin naki ki girmamashi dan saikin kyautata musu ne duniya da lahirarki zasuyi kyau, kiyi koyi da sahhabai da tabi'ai wajen hak'uri nuna soyayya da kuma cinye jarabawa ko wace iri ce, ki zama jarumar gaske wajen shanye abinda ke zuciyarki, kuma karki tab'a kallon Khairat da abun, hakan zaisa shaid'an ya sake galaba a kanki, kuma ki sani iyaye nada girma da darajar da babu mai ita a duniya idan kika cire Allah da manzonsa Annabi Muhammad (S.A.W)."

Sosai malam ya mata nasiha daga bisani kuma sauran iyayen suma suka tofa albarkacin bakinsu, a haka suka tashi daga zaman cike da fatan alkairi, amma fa duk abinda aka tattauna ta bayan kunnan Mama yabi ya wuce, dan tayi niyyar saita d'auki fansa akan Khairat dama shi kanshi Bala...


*Wasa farin girki*

_Ku biyoni dan jin me kuma zaici gaba da faruwa yanzun._


_Wannan sadaukarwa ne ga *Ummu Fawzan,* sama da tsawon lokaci har yau tana tambayata lafiyar mahaifiyata, wanda zaiso mahaifiyarka babban masoyine wallahi, ina sonki sister_
29/08/2019 Γ  14:33 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


*MUJI TSORON ALLAH AKAN DUK ABINDA ZAMUYI*


_Bismmilahir-rahman-rahim_


5⃣6⃣


Kwance take akan qafafunshi suna hira yana shafar kanta, bacci ne ya fara d'ibarta yanata surutu amma yaji shiru, leqa fuskarta yayi yace "wai bacci ki kayi?"

D'an bud'a ido tayi ta kalleshi lokaci d'aya kuma ta maidasu ta rufe, dariya yayi yace "lallai aiki fa ya samu."

"To shikenan tunda dai bacci kike, kinga gobe kenan ba zuwa gida gaskiya, dan ba zan kaiki ba kije kina musu bacci ba a gida."

Tunda yaji shiru ya tabbatar bacci take bilhaqqi, dan da idonta biyu da zata tashi ta fara mishi rigima, gyara mata kwanciyar yayi yana kallon fuskarta yana yawo da yatsunshi a tsakanin fuskarta da qirjinta, saida yaji bacci na shirin d'aukarshi shima sannan ya tofa musu addu'a ya kwanta yana qara matseta jikinshi kamar za'a rabashi da ita.


*************


Da safe kuma fitowa sukayi cikin shiri ita da Zuby saboda zai kaisu gidajensu ne duka su wuni, tare suka fita bayan sunyi sallama da mutanen gidan, gidan baya Zuby ta bud'a ta shiga Khairat kuma gaba, saida ya fara aje Zuby a gida ya shiga tare da Khairat dansu gaisa, duk sallamar da sukayi Mama bata amsa ba, gaisheta sukayi shima shiru ko kallo, tausayinta ne ya kama Khairat dan haka ta d'an matsa da nufin ta mata magana, da hannu ta nunata tace "karki kuskura wallahi, kinga raunin kanki yanzu zan miki wanda ya fishi, wallahi na tsaneki bani bake har abada, kuma zaki gani a cikin qwaryar cin tuwanki , bake kad'ai ba harda shi banzan Balan daya taimaka miki, wallahi saikun gane kurenku, saina nuna muku nayi nisan da bana jin kira, kuma kamar yanda banji tsoron bakin iyayena ba wallahi ba zanji tsoron bakin wasu ba, dan saina nuna muku bakin mahaifiyata na yawo dani har yanzu, zan ajiye sauran imanin daya rage mini domin na tarwatsa ratuwarki, kuma abin kunya ba gareni farau ba bare ya qare kaina, dan haka ba zan sake jin kunyar wani ko wata ba akan abinda nayi, tunda wasu sunyi fiye da abinda na aikata, kuma ki zuba ido kiga abinda zai faru, ba dai kin tona min asiri ba, to kema zan tona miki naki asirin, wallahi sai kinji abinda nida 'yata mukaji, ku b'ace min daga gida, har kai bana son sake ganinka."

Da qyar Khairat ta iya tashi ta kama hanya, Umar Faruk na bayanta shima yana tunanin abinda Mama ta fad'a, tunda suka shiga mota babu mai magana harya ajeta gida suka shiga, ba wani kuzari haka suka gaisa sannan ya barta, yana fita Khairat ba tayi nauyin baki ba wajen fad'awa su Mamie abinda Ma'u tace, Mammie ce tace ta Allah ba tata ba kuma babu abinda zata gani sai alkairi, haka dai tayi wurin ranar ba walwala ba kuzari, sai bayan sallah isha'i yazo ya d'auketa daga nan suka wuce suka d'auko Zuby, wacce itama tayi wunin ba dad'i ba walwala, gidan suka wuce suka zuwa kowace tayi d'akinta Umar Faruk kuma yabi bayan Zuby dan itace dashi, saida ya tabbatar da Zuby taci ta qoshi kafin ya nufi d'akin Khairat, duk da ba komai take son ci ba da qyar tasha yaghourt ta kwanta itama.


*DAGA WANNAN RANA* komai ya sauya sosai da sosai, Zuby ta zab'i zaman d'aki indai tana gida, shi yasa take jin dad'in tafiya school dan tafi sakewa acan, gida kuma ta daina kula kowa sai kula da Umar Faruk ke bata, ko akasi yasa sun had'u da Khairat a tsakiyar gida bata kulata, hakan kuma yana wa Khairat dad'i dan kowa harkar gabansa yake yanzu, cikin Zuby cikin ne mai dad'in raino , danko ciwon kai ba tayi sai cin abinci kamar tashin hankali, komai so take taci komai sha'awa yake bata.

Sab'anin na Khairat dake wahalar da ita, sam bata son cin abinci sai Umar Faruk da Mama sun matsa mata take ci, shima kuma tana cinshi zata amayar, ga yawan zazzab'i, wani lokacin kuma matsanancin ciwon ciki da kasala, idan ta fara haka zata dinga rusar kuka tana matsar ciki, hakan yasa kowa yafi tausayinta fiye da Zuby dake garas da ita, Khairat uwar kwalliya amma yanzu wanka ma sai Umar Faruk ya taimaka mata take yi , harta manta rabon data d'iga kwalli a fuskarta, daga kwanci sai kwanci bata iya zaune na tsawon lokaci, hakan kuma ya shafi har zuwa wajen aikinta, danta daina zuwa yanzu saboda larura, gashi kuma yanzu Papa ya bud'e mata tattalin arziqinta tunda ya gane duk abinda take akanshi ne take, sai dai babu wani anfani da hakan yayi saboda bata cikin qoshin lafiya bare ta mori kud'in, kuma yanzu Umar Faruk ne ke musu duk abinda suke so, saboda bud'i kullum Allah yake masa.


Mama kuma ba zama, kullum a tafiye take tana shiga lungu da saqo na gari dan ganin ta tarwasta Khairat kamar yanda take, kamar yanda ta fad'a ta murje idonta ta nuna kamar ba komai daya faru ta qara shiga duniya, tayi sabbabin qawaye yan duniya wanda suka qara kaita suna shirin barota, a cikinsu ne wata ta kaita wajen wani babban malamin tsibbu suka kai kukansu akan Khairat da Bala, a take ya fad'a musu zai nakasasu suje gida kawai su kwanta aiki ya qare, cike da kwankwanto Mama taje gida tana tunanin aikin malam d'in.


*************


Yau ma kamar kullum Khairat ce a d'akin Mama kwance akan gado da d'an dabino a bakinta tana tsutsa, Mama ce tayi sallama ta shigo ta zauna qasa tana fad'in "to taso ga abincinki kici."

Juya baya tayi tace "wallahi Mama bana son ci, dana ci amai zanyi."

Kallonta Mama tayi tace "Khairat, kin rainani ko? idan da mijinkine ya miki magana d'aya da kin taso."

Juyowa tayi tana kallon Mama ta tashi zaune, gyara siket d'inta tayi daya tattare sannan ta sauko qasa, janyo kwanan tayi tasa hannu ta fara laquta, tun kafin takai baki take jin amai na taso mata amma saboda Mama sai tayi k'arfin halin kai lomar, bata kai ga had'eta ba amai ya taho mata da gudu ta tashi tayi qofar d'akin ta tsugunna ta fara qheqashi, saida tayi kamar zata amaye kayan cikinta sannan ta kurkure baki ta dawo d'akin, a galabaice ta kwanta qasa tana rufe ido, Mama dake jin kamar ta zubar mata da qwalla ne ta d'auki wayarta ta kira Umar Faruk, yana d'auka tace "dan Allah kazo gida, abin yarinyar nan ya fara bani tsoro wallahi, tun jiya har yau babu wani abinda ya shiga bakinta ya zauna bata amayeshi ba."

Cike da tausayi yace "shikenan Mama ganin nan zuwa, tana kusanku ne?"

"Eh gata." ta fad'a tana bawa Khairat wayar, tana d'orawa a kunne yace "baby, kina so kisa gwarzon mijinki kuka?"

Murya qasa qasa tace "a'a bana so."

"To indai hakane ki fad'a min abinda kike so na taho miki dashi yanzu?"

Shiru tayi tana tunanin abinda zata fad'a, duk iya tunaninta bata tuna wani abinda take sha'awar ci ba, a hankali tace "baby ba komai, ni kawai kai nake so kazo nayi kwance saman jikinka."

Dariya ce ta kubce mishi yace "shi kad'ai kike so?"

"Eh." ta fada tana turo baki gaba, cewa yayi "to ki d'auka an gama saboda kai da kaya ai duk mallakar wuyane."

Cikin shagwab'a tace "uhm uhum, wayo ko? to na yarda kai da komai naka duk mallakina ne."


"Dama haka nake nufi nima, gani nan zuwa."

"Sai kazo." tana fad'a ta kashe wayar, bawa Mama tayi tanata juyi a tsakiyar d'akin, Yusuf ne ya shigo ya nufi wajenta ya zauna yana cin gyad'a, juyowa tayita kalleshi tace "d'an tanti me ake ci ne haka?"

"Guciya." a cewar yaron.

Ruf da ciki tayi ta tokare hannayenta ta amshi ledar gyad'ar ta cika hannu ta fara b'arewa tana ci, ganin tana ci yasa yaron ya sake mik'a mata ledar gaba d'aya ya tashi ya fita, jim kad'an sai gashi ya shigo da wata a hannu, suna haka kuma Umar Faruk ya shigo, kusanta ya zauna yana aje ledar hannunshi yana fad'in "Ina kuma aka samu gyad'a?"

Yusuf kawai ta kalla ba tayi magana ba, Mama kuma tuni ta tashi ta fita dan tasan sai sun saiyar da halinsu a gabanta ma, ganin Mama ta fita ta matsa ta d'ora kanta akan cinyarshi tana kallon fuskarshi, shafa fuskar yayi yace "tashi kiga abinda na kawo miki, kuma nasan zaki soshi sosai."

Janyo ledar yayi ya fara fito da abin ciki ita kuma ta tashi zaunen, kifi ne soyayye ga bala'in zafi πŸ˜‹ zaiyi dad'in ci, da sauri ta rufe hancinta tana fad'in "meye wannan kuma? ka rasa me zaka siyo min sai kifi."

Kallonta kawai yake ya kasa magana, cike da b'ata rai tace "dan Allah baby ka fitar dashi wallahi amai zai sani."

Shi kuma mamaki ma ya hanashi motsi gani yake kawai dagangan takeyi, bud'a baki tayi tace "bab......" da gudu ta qarasa fita daga d'akin sai kuwa amai, ganin haka yasa ya tashi yabi bayanta, kallonta yake tana yunqurin aman sosai daga ruwa sai gyad'ar da taci, d'akin ya koma ya d'auko kifin ya nufi d'akin Zuby dashi dan yasan ita tsaf zata handameshi, wucewa yayi yaji su Mama Sa'a na magana akan wahalar da Khairat kesha, da sallama ya shiga ya samu tana bacci, daddabata yayi ta tashi zaune da d'aurin qirji saboda zafin dake akwai, aje ledar yayi qasa yana fad'in "ga kifi nan."

A yamutse ta kalleshi tace "wallahi yah Umar bana son turaren nan naka, tayar min da zuciya yake sosai da zaka daina anfani dashi da naji dad'i."

Murmushi yayi yace "to nama fita daga d'akin gaba d'aya, kici dai kinji ko."

Binshi tayi da kallo harya fita, qasa ta zauna ta samu kifin nan taci abinta sosai ta qoshi, saida ta gala ta fito ta wanke hannaye ta koma d'aki....


Kwance ya samu Khairat a tsananin galabaice abin tausayi, duk ta rame ta fita hayyacinta sai ido masha Allah, a lokacin Mama na d'akin ta kalleshi tace "Umar Faruk, ko dai zaka kaita gidansu ne ta wuni, wataqila idan taje ta d'an saki jikinta har taci wani abu, amma inba haka ba da matsala gaskiya, kuma idan zaku tafi ka biya asibiti adubata dan Allah."

"To Mama."

Kallon Khairat yayi yace "tashi mu tafi ko."

Lokacin kuma wani bacci ne yazo mata, da qyar tayi tsaye tasa hijab dan yanzu zamanta d'akin Mama yafi yawa, slipas d'inta tasa tace "muje."

"Haka zaki tafi?" cewar Umar Faruk, kallonshi tayi kafin tayi magana Mama tace "to danAllah wanda yake takanshi me kake tsammani dama."

Haka suka wuce suka kama hanyar asibiti, kuma wannan fitar ita ta zama silar qara lalacewar komai, zaune suke gaban Sadiya bayan ta gama fad'a mata abinda ke damunta, had'e hannayenta tayi tace "cikin naki yakai wata nawa?"

Kallon Umar Faruk tayi shima ita yake kallo kafin tace "uhum, wallahi ban sani ba."

Dariya suka saka mata ita da Umar Faruk kafin tace "yanzu ciki a jikinki kice baki san watanshi nawa ba? kai Khairat Allah ya shiryeki wallahi."

Umar Faruk ta kalla tace "yallabai, dole zamu mata Γ©co (scanning) muga lafiyar cikin nata, dan ciwon cikin shi yafi zama matsala, zai iya yiwuwa cikin ne ya shiga cikin mara ko ya fita daga mahaifa, amma yanzu idan muka mata eco sai muga lafiyarshi."

"Ba damuwa madam."

Tsaye tayi tace ma Khairat ta taso, shamakin dake tsakanin gadon mai jiya suka shiga ta kwantar da ita, da mamaki take kallon Khairat dan a iya ganinta bata ga ciki a jikinta ba, photon ne ya fito suka fito daga wajen, zaune sukayi ana kallon juna sannan ta sauke numfashi tace ,

"Khairat kin tabbatar kina da ciki?"

Da mamaki Khairat tace "alamu na nuna min haka, kuma a asibitin nan ne aka fara fad'a mana haka."

"To a gaskiya ni dai banga wani ciki ba a jikinki Khairat."

"Me?" cewar Umar Faruk, d'orawa yayi da "me kike nufi da da bata da ciki? dubi fa yanda ta koma saboda laulayi, kuma a hakan ne bata da ciki."

Khairat ma kallonta tayi tace "Sadiya, kin tabbatar da abinda kike fad'a kuwa, ko dai cikin yabi wata hanyar ne daban kamar yanda kika fad'a d'azu, amma inba haka ba ina shan wahala fa sosai."

"Wallahi na tabbatar da haka, idan kuma baku yarda ba kuje wani wurin a duba muku."

Kallonta Umar Faruk yayi ya kama hannun Khairat suka fita, kai tsaye wata asibitin suka nufa, nanma dai abinda aka fad'a musu kenan, saida sukaje asibiti har hud'u duk sakamako d'aya ne, tashin hankalin da Khairat ta shiga yafi wanda Umar Faruk ke ciki, kuka ta dinga yi a cikin motar har suka isa gida, tare suka shiga kuma da kanshi ya fad'a musu halin da ake ciki, Mamie da Mammie dake shirye shiryen komawa india ma duk hakalinsu ne ya tashi suma, nan ya barta ya tafi da niyyar dawowa da dare ya d'auketa.


**************

Tun tafiyar Umar Faruk Khairat ta rikice musu cikin gidan, wani zazzafan zazzab'i ne ya rufeta mai tsananin zafin gaske, har saida Mammie ta dinga sakawa hijabinta ruwa suna rufeta dashi, ba kuma zazzab'i kawai ba ciwon qafafu da hannaye kamar ba'a jikinta, zafi take ji mai rad'ad'in gaske wanda bata tab'a jinshi ba bare ta kwantata, hawaye kad'ai ke iya fita daga idonta ta kuma nemi addu'a a bakinta ta rasa sai a zuciyarta kad'ai take iya istigfari da tasbihi, Mamie ganin abin bana qarau bane yasa suka kira Umar Faruk yazo, har d'akinta da take kwance ya shiga, kallonta yake sosai har yana karkace kai, so yake ya fahimci abinda idonshi ke hango mishi a tare da ita d'in, wani murmushin takaici yayi ya cije gefen labb'anshi ya kalli Mamie yace "zamu tafi gida, komai zaiyi daidai."

Da kanshi ya d'auketa ya kaita mota sannan suka wuce gida, da kanshi ya shiga da ita cikin gida kai tsaye d'akin Mama ya wuce da ita, duk uwayen gidan binshi sukayi suna tambayar lafiya, yana cikin fad'a musu Khairat ta bud'a ido, fashewa tayi da qara mai k'arfin gaske tana fad'in ya mayar da ita gida wajen Mamie, rik'eta ya fara yi yana so tayi shiru amma ina shure shure kawai take, zaune yayi kusanta cikin daka tsawa yace "kalleni nan."

Bud'a ido tayi ta sauke a kanshi take ta kuma d'auke idonta, hakan ya tabbatar mishi da abinda yake zargi wato sharrin shed'anu ne, janyota yayi jikinshi ya rumgume yasa bakinshi a kunnenta yana mata karatu, fizge fizge ta fara sosai tana gunjin kuka tana so ta k'waci kanta, wani shegen rik'o yayi mata yasa ta kasa kubcewa, har saida ta fara rera kukan a hankali tana sauke ajiyar zuciya sannan ya kwantar da ita, a haka kuma bacci ya d'auketa, tashi Umar Faruk yayi ya fita yana ci gaba da fad'awa su Mamie abinda ya faru, a haka ya fita sallah magrib yana mamakin sabon al'amarin daya b'ullo musu.


**************

Tana farkawa ta sauko daga kan gadon ta fito duk a yamutse da ita, Mama na k'ofar d'akin akan sallaya taga fitarta, bata mata magana ba saboda ganin yanayinta, Zuby ce ta fito daga d'aki suka kalli juna, wata shegiyar qwafa Khairat tayi ta wuce d'akinta, Zuby ma tab'e baki tayi ta wuce sabgar data fito da ita.

Tana shiga d'akin taji ya mata zafi sam ba zata iya zama ciki ba, a turmuje ta ciro akwatinta ta fara had'a kaya, Umar Faruk na shigowa na nufi d'akin Mama, da hannu ta masa alama tana d'akinta, wucewa yayi kai tsaye yana shiga ya tsaya yana kallonta, qarasowa yayi ya zauna gefen gadon yana fad'in "yadai, tafiya zamuyi ne?"

Ko kulashi ba tayi ba sai ci gaba da had'a kayan da tayi, tsaye yayi bayanta dan yaso ya fahimci halin da take ciki, cikin wata irin murya da baya yinta inba marar lafiya ya samu ba da zai taimakawa ba yace "ke."

Cak ta tsaya amma bata juyo ba, sake maimaitawa yayi cikin amon murya yace "dake nake, kalloni nan."

A hankali ta juyo ta sauke idonta a kan nashi, amma saboda bala'i da kwarjini da tsoro kawai saita zube qasa ta fashe da kuka cikin muryar da daga ji ba tata bace ta fara cewa ita kawai ya kaita gida bata san zama anan, banza yayi da ita ya d'auki cup ya zuba ruwa ciki ya fara yan karance karancenshi duk yana kallonta, koda ya gama tofawa a cikin ruwan ya taso yayo kanta, tana ganin haka ta zabura ta tashi tsaye tana ja da baya tana fad'in "a'a, a'a, karka matso kusa dani, kar kayi fa, wallahi zaka cutar da ita a banza, zafa ka iya kashe abinda ke cikinta, a'a zaka jamata fa."


*Allah my sister na,😭 na tuna lokacin da kika sha wannan wahalar, a lokacin da naje gidanki da niyyar jinyarki, amma a qarshe sai tare muka dawo gida,😭 kai anga rayuwa fa, wallahi wannan ciwon na Khairat da nasa bawai qirqira bane, sak irin ciwon da sisterna tayi ne, Allah ka qara karemu daga sharri masharranta*πŸ‘

Saboda an saba gwagwarmaya irin haka yasa bai kula da abinda suke fad'a ba, hannu yasa ya d'ibi ruwan ya watsa mata ruwan, wata qara ta kwamtsa tana numfashi sama kamar zata d'auke rai, cikin gunjin kuka take fad'in "ka daina, ka daina haka."

Fuskar nan a daure ya aje cup d'in ya zauna kan gadon yana fuskantarta yace "fad'a min, meya kawoku jikinta, meta muku da kuke neman cutar da ita, akan wani dalili kuka shiga jikinta? kuma idan kuka min qarya wallahi jikinku zai fad'a muku."

Cikin wata irin tsawa yace "maza zauna nan."

Zaune tayi inda ya nuna mata tana susar jiki saboda rad'ad'in ruwan daya zuba mata a jiki, cikin muryar daba tata ba ta fara magana....

_Ikon Allah, lallai ta bakin Mamien mu tace namijin duniya, yau kam na tabbatar, to amma kuna ganin zasu fad'i gaskiya ne?_

*WASA FARIN GIRKI.*
29/08/2019 Γ  14:33 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*TASKU*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜

_*My BK,* ina tayaki murnar fara wannan novel naki mai cike da abin al'ajabi, Allah ya baki ikon kammalashi cikin qoshin lafiya da hazaqa, fatan alkairi masoyiyar *Meerah.*_


_DEDICATED TO_


*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Ohhh my sweet

Please Login or Register in order to submit comment